Hausa Novels Raina Kama Book 3 Hausa Novel

Raina Kama Book 3 Page 32


Raina Kama Book 3 Page 32
Viral

BOOK 3 ????3?2?

??END!! ?????

……………Ban San yanda zan musalta muku halin dana tsinci kainaba bisa ga wannan tukuyci na Galadima, saidaifa kafin wani dogon lokaci dukkan Wanda keda alak’a dani yasan da zaman wannan k’yauta, y’an uwa sai tayani murna sukeyi.
Y’an gidanmu dai saida sukaji wannan bak’ar al’adar tasu ta hassada, amma sun d’an danne zukatansu sukaimin murna.

Washe gari bayan d’aura auren Sauban da aunty mimi Galadima yaja gayyar abokansa da yayuna sukaje aka bud’e wajen saloon d’ina. Akuma ranar ma’aikata suka fara gudanar da aiki, dan a can naje na iske Galadima ni da tawa tawagar, na gana da dukkan ma’aikatana tare da basu umarnin duk Wanda ya shigo wajen a ranar amasa abinda yakeso k’yauta, Washe gari sai a fara na kudi.

Bikin Sauban ya gudana cikin k’ayatarwa, itadai aunty mimi koda aka d’aura auren shikenan, tace wane biki kuma a shekarunta, ana gama shagalin na Sauban tareda amaryarsa Ni’imatullah d’iyar Mom da biyu, itama ta tare gidan mijinta professor Ibraheem Macid’o, musalta muku yanda mukasha shagali 6ata lokacine.

Bayan bikin da kwana biyu Galadima ya fara koya min mota, koya motar da taso zama shiririta, wai dole saidai na zauna a cinyarsa ahaka za’a koyan, banida yanda na iya dole nayi hakan, cikin amincin ALLAH a sati biyu nagama kwarewa, kwana biyu da faruwar hakan na yaye su Amaturrahman bisa dagewar Ubansu akan shima k’annensu yakeso, danga Munubiya da ciki????.
Dole nayi wannan yaye yara suka koma wajen Momma.
Kwanaki 10 cif dayin yayen saiga bak’ona yazo, karkuso kuga murna wajen Galadima, wai hanyar samuwar ciki ta bud’e.
Ni dai shiru namasa ban tankaba. Randa kuwa nayi wanka ai babu d’aga k’afa, ALLAH mai iko da falala kuma ya amince masa, koda wata ya dawo babu jini babu alamarsa, hankalina ya tashi na birkice masa, sai yayta tuntsuramin dariya da fad’in “Yarinya an fad’a miki nid’in na wasane, zan zama Abbu a karo na biyu, ALLAH yasa su zama 3+3=6”.
Tashinai nabar masa falon ina zun6ure-zun6ure, shikam yayta tuntsura dariya.
Nima nayi farin ciki da samuwar cikin, tunda naga hakan shine burin mijina da farin cikinsa, sai kuma fatan ALLAH ya sauke mu lafiya, dan wannan karon dai mun sa6a ni da Munubiya.

BAYAN WATA 6

Cikina ya fito sosai, ina samun tattali da kulawar mijina, kai kace wannan shine cikin farko daza’a Haifa masa, ga shak’uwa mai yawa dake tsakaninsa da yaransa, abin akwai birgewa mai yawan gaske.

Ranar wata juma’a kawai mukaga an tashi da wani gagarumin biki dabamusan na miye ba a masarautar, dama kusan kwanaki uku kenan bak’i nata sauka, ni dai harna kasa hak’uri na tambayi Galadima, yace, wlhy shima bai saniba.

Ana sakkowa daga massalaci sallar juma’a aka hana Galadima shigowa gida, papi ya umarcesa da zuwa ya zauna inda aka tanada dominsa.
Mamaki ya kamasa ganin gurin dank’am da jama’a, addu’a kawai aka gudanar papi yabada umarnin fara abinda ya tara mutane, daga baya koma mikenan jawabi zai biyo baya.
An umarci Galadima da tasowa zuwa saman daddumar dasu Abie da manyan sarakuna ke zaune, ya zauna a tsakkiya shidai zuciyarsa na faman tsitstsinkewa da bugun mamaki.

Turaki ya mik’e a tsanake zuwa gaban mai martaba Sarki Jalaludden Abubakar, yay gaisuwa tare da risinawa sannan ya zare rawanim dake kansa, gaba d’aga wajen aka d’auki kabbara, Abie yay k’asa da kansa yana share hawaye, shidai dan anfi k’arfinsane kawai, amma daba yanke wannan hukuncinba wlhy.

tuni bugun zuciyar Galadima ya k’aru ganin Turaki ya nufo garesa, zaiyi maganar papi yay masa alamar yay shiru??.
Dole ya maida bakinsa ya tsuke yana had’iyar yawu da k’yar.
Tsohon Sarki Jalaludden ya taso da taimakonsa Turaki ya cire hular saman kan Galadima aka d’ora masa sabuwa dal, sannan aka fara nad’a masa rawani akai, jikin Galadima sai tsuma yakeyi, ya kafe papi da Abie da ido ko k’yaftawa bayayi, shikad’ai yasan a halin dayake ciki, zufa sai tsatstsafo masa take a kowacce mahudar gashi dake a jikinsa.
Tsaf aka gama nad’a masa rawani jama’ar wajen suka d’auki kabbara, yayinda za’a saka masa alk’yabba sai dogarai suka baza riguna ana masa kirari.
Galadima yay k’asa dakai idonsa na kwararar hawaye lokacin da kunuwansa ke jiyo masa jawabai daga bakin sank’ira.

“ALLAH ya d’auki rawani ya maida bisa kan matashi kuma adali tsohon Galadima a yau yazama Sarkin wannan masarauta ta gagara badau bisaga adalcin tsohon Sarki mai murabus a yau, masarautar gagara badau tayi sabuwar amarya, a halin yanzu Mai martaba Muhammad Sameer Saifudden Abubakar shine Sarkin wannan adalar masarauta, ALLAH ya tayashi rik’o, yabashi ikon koyi da k’yawawan halaye irinna manyan wannan gida”.

Tuni waje ya harmutse da surutai, kowa na fad’in albarkacin bakinsa.
Galadima kam saida papi ya rungumesa a jikinsa sannan yafara samun nutsuwa, yayinda aka kawo Matawalle shima aka zaunar aka nad’a masa rawanin wazirci, shine zai zama wazirin d’an uwansa Sarki Muhammad Sameer Saifudden Abubakar.
Ai tuni guri ya rinca6e, babu maijin zancen wani, kafafen yad’a labarai da social media duksun d’auka, masu murna nayi masu bak’in cikin nayi, (kusan shigabanci, dolene kasamu masoya da mak’iya??).

Mama Fulani da labarin ya Isar mata zarewa tayi, sai surutai take Wanda ba kowa ke fahimtaba, Gimbiya zulfah kuwa yanke jiki tayi ta fad’i wanwar, koda aka zuba mata ruwa ta farfad’o saita kama aman jini zuciyarta yariga ya buga.
Ba’a katse su papi daga abinda sukeba aka nemo doctor dazai dubata, saidai bata d’auki wani dogon lokaci ba tare ga garinku nan.

Haka duniya take, lokacin da wani ke zuwa sannan wani ke ficewa, hakanne ga gimbiya Zulfah, tatafi a randa Galadima ya zama Sarkin gagara badau.????????????

Ni kaina da labarin zaman mijina Sarki yau babu zato ya zomin saina rikice, na rud’e, ganin lamarin nake tamkar tatsuniya ko mafarki, ga ciki, nama rasa murna zanyo ko kuka.
Ban fita a wannan magaginba saiga zancen halin da gimbiya zulfah take itada mama Fulani, saikuma ga abinda ya girgiza kowa shine mutuwarta.

***

Koda aka buk’aci jawabi daga bakin Galadima kasawa yayi, shifa ganima yake a mafarki komai ke faruwa, shima Matawalle ya kasa cewa komai, sai zirar da hawaye kawai sukeyi Wanda hakan ya birge kowa da bada mamaki.
Abubuwa sun rinca6e fiye da yanda bakwa zato a masarautar gagara badau, bayan an sallaci gawar gimbiya zulfah aka kaita makawancinta na gaskiya y’ay’anta na kuka da y’an uwanta.

Kiri-k’iri ganin mijina ya gagareni har dare, Abdurraheem sakin k’ulafucin Uba sai kuka yake yak’iyin barci, su Amaturrahman da sukayi nasu na lallashesu sai suka kwanta, dan sunsaba da yayi sallar isha’i yana tare dasu, amma yau shiru babu amo babu labari.
Nikam sainaji abin yana cizon zuciyata, indai wannan mulki zaisa mijina yin nesa dani bana farin ciki, saigani da kuka rurus.

Sai misalin 12pm Sarki Muhammad Sameer yasamu rakkiyar zuwa sashenmu.
Ina zaune afalo nayi tagumi naji alamar mutum tsaye a kaina.
A firgice na d’ago kaina ganin mijina saina mik’e a firgice tare da fad’awa jikinsa na saki kuka.
Shima rungumeni yayi sosai yana sakin nasa kukan, sannan ya d’aukeni cak zuwa cikin bedroom d’in ya ajiyeni a saman gadon, kuma rungume juna mukayi muna cigaba da kukan mu.
Tsawon lokaci muna haka, sannan yafara dakatar da nashi yana lallashina. “Munaya kinga abinda su papi sukaimin ko, ni dai banason sarautarnan, amma sunk’i saurarena, wlhy banaso munaya, banaso nidai”…. Yakuma fashewa da kuka.
Tausayinsa saiya kuma kamani, nakuma rungumesa tsam a jikina, abinda kaga ya saka Galadima kuka aiba k’arami beneba kuwa. Daure zuciyata nayi na shiga lallashinsa.
Na kuma rungume sa sosai cikin nutsuwa ina fad’in, “Mijina ba komai ne ake tuntu6e dashi bisa shiryawa kaiba, wani abun tunkan kasan tuwarmu gudan tsoka rubutaccene a littafin k’addararmu, babu wani d’an Adam da alk’alamin k’addararsa ke a tafin hannunsa, gudun zuciya yafi na k’afafu sauri, idone kawai ke iya banbance fari da bak’i, baki kuwa d’and’ano kawai yake tantancewa, aikin kunne kuwa jine kawai da banbance k’arar sauti, baka tunanin duk mutum mai baiwa ALLAH ke ba damar banbancewar? Irinku kune kuka cancanci mulkin al’umma, domin kuwa bashine burinku ko damuwarkuba, kune zaku iya adalci da tausayin na k’asa daku, ka amince dayin wannan sadaukarwar ga iyayenka da al’ummarka, domin samun damar k’ar6ar sakamakonka wajen adalin Sarki mai tarin rahma da jin k’ai. Zuciya da tunani duk mallakar gangar jikice, haka gudanar jini da motsin ga6o6i, su papi sune sukasan tayaya ka cancanta kaida d’an uwanka, har suka d’auki wannan nauyin suka d’ora muku, Ku kar6i yau d’unku da hannu biyu, domin jiyanku tazama labari, Ku hidimtawa gobenku domin Ku ribantu da jibinku, wannan shine kawai masalaha mai k’ayatarwa ga mu ahalinku, masu ganin baka kaiba saisu ajiye makamansu su tabbatar da ka kai d’in, kazama RAINA KAMA mijina, kosu amince, ko karsu amince kaine RAINA KAMA”.
Tsam ya rungumeni yana fad’in “kece RAINA KAMA munaya, domin a dalilinki ne suke ganin nayi feeling, har ake ambaton ni da sarauta har Abadan, su ganin auren talaka shine k’ask’anci, shine ke nufin ka koma k’asa, a yak’ininsu saika auri y’ar wani mashahurin Sarki ne darajarka ke a idonsu, sun manta ba talaucine ya rarrabe tsakaninmu ba, Wanda yafi wani bautar ALLAH shine mafifici a cikin bayi, su Papi sun tabbatar min kina d’aya daga cikin manufofinsu na bani Sarauta, sunason tabbatarma duniya da mai sarauta zai iya auren d’iyar talakawa, basai y’ar mai mulki irinsaba, sunason duniya tasan shima talaka akwai baiwa da darajar da ALLAH yamasa fiye da mai mulki, sunason duniya tasan ba mai mulki bane mafi k’ololuwar daraja a cikin bayi, kowanne Bawa da tarin daraja da baiwar da ALLAH ya masa, kinga kuwa kece RAINA KAMA my heartbeat, ko ni kin zamemin RAINA KAMA balle su da suke tunani ba daidaiba”.
Kasa magana nayi, muka rungume juna tsam cikeda so da k’auna.

An cigaba da gudanar da gagarumin biki na wannan nad’in sarauta, kwanaki 5 cif akayi anayi, danma mutuwar gimbiya zulfah ya rage armashin bikin.

bayan lafawar komai da sati biyu mukaje India Galadima ya maida dukkan harkokinsa nacan ga Sauban daya zama tilas ya d’auki matarsa su koma can, dole kuma ya ajiye aikinsa duk da sonsa da yake, su Vijay zasu cigaba da kulawa da komai, idanma suna buk’atarsa zai cigaba da kawo shawarwari.
Mun dawo da kwanaki biyu aka gama kammala aikin Company d’insu na nan Nigeria, Wanda dole su Vijay sukazo suka aiwatar da komai, zuba masa kaya da d’aukar ma’aikata da dukkan abinda yakamata ayi.

Wata d’aya cif a tsakani aka basa umarnin shirya fara gudanar da mulki, Shiga fada da nad’e-nad’en sarautu da zaiyi, dakuma Neman matar aure dazai k’ara.??????

Wannanfa Abu ya tayarmin da hankali sosai, ga cikina ya tsufa, aiko na birkice masa naita kuka, kai wlhy kishiya da ciwo, duk dauriyarka saikaji babu dad’i, musamman idan kana son mijinka kuma.
ALLAH Sarki Momma Uwa ta gari, itace taita kwantarmin da hankali da kalamai masu sanyaya zuciya, hakama Galadima yayta lallashina da nunamin muhimmancin lafiyata kodan tsohon cikin dake jikina, itama Munubiya da Innarmu haka, nima da naga mijina da kowa na son ganin kwanciyar hankalina saina kwantar d’in, na kar6a k’addarata da hannu biyu.
Da farko d’iyar Mom akace ya aura, bankuma San yanda akayi ya zameba yace yabani wuk’a da nama na za6o masa dukkan wadda tamin, koya take wlhy zai aura shikuma.
Kusan sati biyu daya bani sainaita nazari da hasashen wazan za6a masan, haka kawai matashiyar budurwa Hafsat da muka ta6a had’uwa a jirgi ta fad’omin a rai, lokacin inada cikinsu Amaturrahman, tamin wani taimako da Galadima ya yaba mata sosai, Wanda harna kamashi yana satar kallonta, amma a time d’in saiya basar kamar yanda halayyar tasa take, Nima sai banja maganarba, mukan gaisa da Hafsat miss xoxo time to time, amma mun dad’e bamu had’uba, inagama tun taron sunan su Abdurrahman da tazo.
Muna zaune dashi na lalubo hotonta da mukayi ranar suna tare na nuna masa.
“My king wannan ta makane?”.
Kar6ar Hoton yay yana kallo, yay wata irin zabura yana ajiye hoton gefe da hararata, “Kina zargin ina sontane komi?”.
Murmushi nayi ina d’auke hoton, nace, “yanayinka da amsarka kawai ta wadatar dani ranka ya dad’e, danason ma kanason miss xoxo da tuni na had’a wannan alak’ar wlhy, ALLAH yabamu zaman lafiya”.
Duk yanda yaso bijirewa da nuna ba haka bane ban sauraresaba, na nunama Momma photo aka shiga binciken miss xoxo. A cikin sati biyu aka gama komai, duk da itama ta nunamin bata aminceba.
Duk da kishi na cina haka na jajirce tsakanin borensu, babu 6ata lokaci akasha biki.
Da kaina namata rakkiya d’akin mijinta a maimakon rakkiyar jakadiya da har yau bai za6aba., nai k’ok’arin danne kishina nai mana addu’ar zaman lafiya. Na dawo d’aki ina kuka da rungume y’ay’ana, akuma asubahin farko na farka da nak’uda. Wadda har aka wuce dani asibiti Sarki Muhammad Sameer bai fitoba, yanacan yana lallashin amaryarsa daya maida cikakkiyar mace a daren jiya.
Na sauka lafiya na haifi d’a namiji mai kama dani sak, sai daga baya labari ke kaiwa kunnen Sarki Muhammad Sameer, ya rikice da murna, gashi babu damar binmu a asibiti, dole ya hak’ura har muka dawo.

Fad’an farin cikin samun wannan haihuwa ga Sarki 6ata lokacine, hakama su Abie da tsohon Sarki da a yanzu suka koma daga gefe suna koyama yaransu dabarun mulki.
Washe garin suna kuma Sarki Muhammad Sameer ya zauna a fada, tare da yin wasu nad’e-nad’e, hardasu Badi a ciki, sarkin mota da Sarki k’ofa sunce iya wuya suna tare dashi.
Haihuwar danayi Ce ta d’auke hankalina daga damuwar kishin mijina da wata, duk da bana nuna kishin dama a fuska balle Hafsat ta fahimta, dan Alhmdllh tarbiyyarta tasa muke zaune lafiya, saima k’ok’arin jan yarana da take a jikinta, yarona yaci suna Abdul-fatah, papi kenan, daga Hafsat kuma Sarki Muhammad Sameer yace ya tsaya, mata biyu sun ishesa, ALLAH yamusu zaman lafiya.

Rayuwa ta cigaba da gudana cikin nasarori, wajen saloon d’ina nata ha6aka, da kud’in shigarsa na d’auke kaso mafi tsoka na nauyin gidanmu, mahaifina ma yasamu sarauta da Sarki Muhammad Sameer ya nad’ashi, hakan yamin dad’i sosai.
Munubiya itace mai kula da ladies mirror, office d’inma ita ke zamansa time to time, danni banida wannan damar a yanzu, fitarma sai wadda ta zama tilas nakeyi.

Sarki Muhammad Sameer nada watanni takwas akan mulki ALLAH yayma mama Fulani rasuwa, tsakaninta da papi wata 1, wannan rasuwa biyu ta matuk’ar girgizamu, dan Sarki Muhammad Sameer kusan zarewa yayi akan mutuwar papi, yabasa gudunmawa mai yawa a rayuwarsa, wadda mantata abune mai matuk’ar wahala a garesa, mai makon babansu Nuren ya hau mulkin, sai yasa aka nad’a Nuren d’in. Sarki Nureddin ALLAH ya tayaku ruk’o baki d’aya.

Babu dad’e da nad’im Sarki Nureddin akasha shagalin bikin Saleem da Feena, bikin dayay armashi sosai, dan itace last mace dasu innarmu zasu aurar, saura y’an k’ananun y’ay’ansu Aryaan, Aiyaan da Ahmad, Wanda a yanzu sun zama samari masha ALLAH, dan duk suna sa2 a secondary school, jirama Sarki Muhammad Sameer yake su kammala ya had’asu da Khaleel su wuce karatu.

A yau kuma Munubiya ta kawo mana ciyara da y’ay’anta Meenal, Ameen da k’aramar Ai’sha muna ce mata Islam. Munsha hira sosai, taita mamakin yanda nake zuba mulkina, yo matar Sarki uwar gida wasace??????????????????.

 

BAYAN WASU SHEKARU

Rayuwa ta shud’a ababen dariya Dana kuka sun faru iri-iri, an haifi wasu wasu sun rasu, hak’urin zama Na yau da kullum, wataran a 6ata ma koka 6atama wani.
Zuwa yanzu kam munyi rashin wasu daga cikin iyaye y’an uwa zuwa kakanni, ALLAH yayma Abbanmu rasuwa shida wasu matan gidanmu biyu, inno ma haka, yayinda innarmu ta gama takaba sai danginsu sukazo suka tattarata zuwa k’asarta ta haihuwa, muna kuka tanayi hakama jama’ar gidanmu da y’an anguwa, Dan bamason tafiyar tata, amma hakan gatane a gareta komawa cikin ahalinta, a gagara badauma kam mun rasa da yawa, tsohon Sarki jalaludden Abubakar ALLAH ya masa rasuwa sakamakon ciwon hanta, wadda ya dad’e da ita a jiki Ashe, wannan ma shine dalilinsa na dagewa akan Abie ya kar6a mulki. Saida rayuwa tazo gangara yake sanar ma Abie d’in Wanda shima zuwa yanzu girma ya kamashi sosai, Dan yatsufa komai ma sai an masa, danma ALLAH yabashi gwarzuwar mata Momma, dukda itama girman ya kamata bata gajiyawa da hidimarsa.

Sarki Muhammad Sameer Saifudden Abubakar, adalin Sarki da talakawa ke alfahari da mulkinsa, musamman ma matasa da akullum cikin bin hanyoyin inganta rayuwarsu yake, suna zaune lafiya shida wazirinsa kuma d’an uwansa, babu wani y’an ubanci ko k’iyayyar juna, k’yawawan zukatansu sun sakasu kawo canji mai yawa a wannan masarauta, da farko su Talba ne sukaso kawo musu hargitsi, tunda suka fahimci haka sai aka sakasu barin k’asar tilas suda iyalansu, tun daga nan masarauta tadawo dai-dai.
6angaren Harun ma ya fito tun lokacin daya cika shekaru goma, amma bisaga karamci Na adalin Sarki Muhammad Sameer saiyasa aka kawosa fada, yay masa hidima mai yawa, wadda ta sakashi kuka da gurfana gaban Sarki Muhammad Sameer Neman gafara da nadama akan abinda ya aikata, Muftahu da ayanzu yake rik’e da sarautar matawalle yay murmushi yanama Sarki Muhammad Sameer magana da ido akan ya yafe masa tunda yayi laushi, Sarki Muhammad Sameer ya jinjina kansa yana murmushin nan nasa Na k’asaita da cizar lips.
Yafewar da Sarki yamasa Ce tabashi damar Neman gafara ga Uwargida Sarauniya Munaya itama, babu wani ja’inja tace ta yafe, ba’a barsa ya zauna masarauta ba, anmasa hidima mai yawa da aure aka sakashi komawa wata k’asa, Dan bawai kowa ya gamsu da tuban nasaba, ayanzu kuma Sarki da wazirinsa basa buk’atar duk wani mai ru6a66iyar zuciya a kusa dasu.

Sarauniya Munaya uwargidan sarki mai fad’a aji a wannan masarauta, jarumar mace mai nagartacciyar zuciya, hamshak’iya wadda ayanzu tazama babbar mace jerin manyan mata sahun faro wajen dattako da mulki dama dukiyar itada y’ar uwarta Munubiya.
A yanzu yaranta takwas a duniya, Amaturrahman, Abdurrahman, Abdurraheem, Abdul-fatah, Ai’sha, Zeenah, Saifudden, jalaludden Auta kenan, Ai’sha da Zeenah da suke kira da Safah da marwah tagwayene, bayan haihuwar Abdul-fatah tayisu suma, daga nan sai mai sunan Abie, dakuma auta takwaran tsohon Sarki babansu matawalle konace waziri, ayanzu kam duk sunzama manya, musamman su Amaturrahman da suke manya duk suna a jami’a, suna k’asar India tareda uncle d’insu Sauban da ayanzu shima yazama babban mutum, yazama babban d’an kasuwa bisaga jagorancin dukiyar d’an uwansa, yayinda su Aiyaan da Khaleel, Aryaan, Ahmad ke taimaka masa, kaga matasan samari abokan juna kenan, kansu ahad’e yake su hud’unnan, sune yanzu duniya ke yayi take son gani a fanin na’ura mai kwakwalwa wato Computer, Wanda ayanzu Abdurraheem da Abdurrahman suke k’ok’arin dannesu, Dan matasan samarin biyu sun zama magada kwakwalwa irinta mahaifinsu Sarki Muhammad Sameer suma.
Itama Hafsat yaranta hud’u, biyu mata biyu maza, wad’anda duk suka taso a hannun Munaya, akwai zaman lafiya da k’aunar juna tsakanin Hafsat da Munaya mai birgewa, Wanda ya kawoma Sarki Muhammad Sameer kwanciyar hankali da k’yautata musu gwargwadon k’arfinsa, kamar yanda suma suke k’yautata masa da dukkan iyawarsu.

Yaran Munubiya itama 6, Dan itama 8 d’inne ta haifi biyu babu rai, Ameen yana tare dasu Abdurraheem, yayinda meenal takanyi Rabin rayuwartane a masarautar gagara badau, saboda batada k’awa wadda tawuce Amaturrahman. Inhar basa Masarauta to sunacan gidansu meenal d’in, sun zama y’an mata ababen birgewa, ita meenal tana masifar son Abdurraheem ne shikuma k’asaita da muskilanci irinna ubansa Sarki Muhammad Sameer tariga tazama jinin jikinsa, yata basar da ita kenan, wannan Abu Na cimata rai, amma aduk sanda ciwonsa zai tashi tafi kowa shiga damuwa, idan kuma taga yanda Ameen da Amaturrahman ke soyewarsu saita kumajin kanta a damuwa, shikam Abdurrahman Niger ya tsallaka, Dan d’iyar Sarki Issifa da Sarauniya Ayusher Rabi’a (Amatullah) yakeso da k’auna, ya rikice sosai, haka kawai saiyayi shiri wai yatafi yima Inna Hutu, nanko wajen Amatullah yaje.

Wannan hutune Na k’arshen shekara daya kasance duk yaran suna Nigeria, saboda bikin su Aryaan da akasha babu dad’ewa.

Sarauniya Munaya kishingid’e a kilisarta hadimanta nata hidima a gareta, matasan samarin y’ay’anta suka nemi ison shigowa gareta.
Izini ta basu, tareda sallamar dukkan Hadimanta.
Abdurraheem da Abdurrahman suka shigo, Kansu d’aya, kamanninsu d’aya, halayyace kawai ta banbantasu, Abdurraheem halin Sarki Muhammad Sameer ne gaba d’a a jininsa, yayinda Abdurrahman yazama mai irin halayyar Uncle Sauban da Abie.
Har suka zauna idonta Na kansu, sukai zama irinna k’asaita suna gaisheda mahaifiyar tasu.
Fuskar Sarauniya Munaya d’auke da Murmushi ta amsa, takai dubanta ga Abdurraheem dashi ko kad’an bashida yawan magana.
“Abdurraheem saunawa zan maka magana akan aske sumarnan ne?”.
Lips d’insa ya cije (d’an gado kenan??) yanad’an 6ata fuska.
“A gafarceni Ummu, wlhy zan Aske, jiya nafita zanje shagonki askin sai takawa yayi kirana ya Sani wani aikin, amma Ummu shima Abdurrahman kimasa magana ya yanke wannan k’umbar, ALLAH k’yank’yaminta nake…….”
Harara Abdurrahman ya zuba masa, zaiyi magana Sarauniya Munaya ta katseshi tana tashi zaune, “Abdurrahman naga hannunka”.
“Ummu karki yarda da gulmar yaronnan ALLAH, yatsa biyunefa”. Ya k’are maganar da kuma harar Abdurraheem daya ta6e baki ya cije lips.
Sarauniya Munaya tace, “Yimani shiru, nabaku nanda dare wlhy kowa ya cire k’azantar jikinsa, ina kuma fata anje an bama Abie magungunansa?”.
“Eh Ummu, Abdul-fatah ya bashi, yanzuma daga sashensu muke barci yakeyi, amma su Amaturrahman nacan sun cikama Momma kunne da surutunsu Na tsiya itada Meenal”.
Murmushi Munaya tayi, Dan ita babu abinda take gani tattare da Abdurraheem sai Mijinta, shikuma Abdurrahman rashin iya R kawai ya gado shida Safah da Marwah duk basu iya R ba, to ga Saifudden nanma akwai k’asaita tsiya, d’an k’arami dashi sai mulkin tsiya, ga jarabar son girma, bawani girman jalaludden yayiba amma inkaga yanda yake basa umarni saikaci dariya, hakama yaran Hafsat.
Sarauniya Munaya tacigaba da hira da yaranta da musu nasihar tsare mutuncin Kansu kamar yanda ta saba.
Wayarta da sak’o ya shigo ta d’auka tana dubawa.
Sarkine da kansa.
Gaskiya ina buk’atar jin d’umin my mata.
Murmushi Sarauniya Munaya tayi tana kallonsu Abdurraheem da suka satar kallonta, idan kaga irin wannan murmushi ga mahaifiyarsu to akan Abbun sune kawai.
Tad’an hararesu tana fad’in “Takawa ba yana fada ba?”.
“A’a yana turakarsa, Dan zamu shigo nan mukaga fitowarsa daga fada”.
Nanma murmusawa Munaya tayi kawai, ta tashi zaune tana gyara zaman alk’yabbarta, “Kuje Sweetheart Na nemanku, amma Ku dawofa da wuri, kunsan yau ranace ta musamman da takawa ke zaman hira damu, karkuyi sakacin dazata wuceku, akwai sak’o a d’akina saman mirror Ku d’auka akai mata, zan kirata namata bayani”.
A tare suka amsa da to Ummu.
Ta mik’e ta shiga bedroom d’inta, mintuna kusan biyar saigata ta fito tabi wata hanya da zata sadata da sashen Sarki Muhammad Sameer kai tsaye batare da kowa ya gantaba, wannan tsarinsane, Dan baya buk’atar wata jakadiya a tsakaninsa da matansa, yace suke rura munafunci a tsakanin matan Sarki.
Kallon juna Abdurraheem da Abdurrahman sukai, sukayi murmushi tareda tafawa, soyayyar iyayensu Na masifar kashesu, burinsu shine suyi koyi, tafawa sukayi sannan suka mik’e domin cika umarnin Na zuwa wajen gwaggonsu Munubiya, Dan ita kad’ai ummunsu take kira da Sweetheart.

Sarki Muhammad Sameer Na kishin gid’e a k’ayataccen falonsa dayaji kayan more rayuwa, lap-top yake sarrafawa hankalinsa kwance, sai tataccen ruwan tuffa dake ajiye a gefensa, k’amshin matarsa gimbiyarsa komansa da yajine ya sakashi d’ago k’yawawan idanunsa yana kallon k’ofa tareda amsa mata sallamarta yana zare medical eyeglasses d’in idonsa.
Tunda ta shigo ya dakata da danna lap-top d’in ya zuba mata ido kawai, cikeda tafiyar k’asaita ta isassun mata ta k’araso gareshi. Zata zauna gefe ya kamo hanunta yana tashi zaune sosai ta zauna saman cinyarsa, su duka ajiyar zuciya suka saki, ya sark’e idanunsu a waje d’aya yana mata murmushin da ita kad’ai take samun ganinsa a fuskarsa, cikin matso da fuskarsa gab da tata ya hura mata iska tafara farfar da idanu.
Lumshe idonsa yayi yana cijar lips, a hankali ya furta I love you my Queen, my Everything? ”.
“i love you too my king”. Munaya tafad’a a hankali itama cikeda salo.
Bashida za6in daya wuce had’e bakinsu, dukda girma ya kamasu harda manyan y’ay’a da zasu iya aurarwa soyayyarsu bata tsufaba, tun anayi a afalo harya d’auka abarsa suka shige bedroom.

Bayan wasu y’an lokuta suka fito wanka fuskarsa kowanne d’auke da murmushi, Munaya ta kalli mijinta cikeda so da k’auna.
“My king miya faru kabaro fada da wuri haka?”.
Murmushi Yamata mai saka zuciya nutsuwa, ya zauna kusa da ita yana kwantota jikinsa, cikin magana rad’a yace, “kewarkice kawai, jinai bama Na fahimtar komai da ake a fadancin, sai gizo kikemin kawai, shiyyasa Na buk’aci shigowa Na huta, bagashi Na huta d’inba?”. Yay maganar cikin d’age gira d’aya da kashe min ido d’aya”.
Murmushi nasaki ina kuma shigewa jikinsa, nace “Anya kuwa a tarihin masarautar nan anta6a Sarki irinka?”.
Murmushi Sarki Muhammad Sameer yayi yana d’ago fuskarta da sark’e idanunsa cikin nawa, “miyasa kika fad’i haka?”.
Murmushi nima nayi ina shafa k’irjinsa, “Kaine Sarki Na farko dakan gana da iyalansa aduk lokacin da yaso, babu maganar jiran dare, kaine Sarki Na farko dakan ware wasu ranaku Dan zaman hira da dukkan iyalansa kawai amatsayi Na Uba ba sarkiba, lamarinka akwai k’ayatarwa yalla6ai”.
Hararta yayi dajan hancina, “bazaki manta da sunannan ba ko?”.
Dariya mai d’aukar hankali nayi ina fad’in, “kaida sunanka, yalla6ai Na yalla6iyarsa”.
Shima dariyar yayi yana kuma rungumeni a jikinsa, “Wlhy kin zuba rashin ji sosai My mata, bak’aramar wahala nashaba lokacin auren Contract d’in nan, naga alamar tsiwarki Safah ta gado gaba d’aya, yarinyarnan batada tsoro ko kad’an, ga iya magana, tafi Marwah wayo sosai”.
“Ai Marwah miskilanci da gatan da Hafsat ke musune ke d’awainiya da ita kawai, yarinyarnan miskilancinka ta gado itama, itada Abdurraheem da Saifudden da Khadeeja (d’iyar Hafsat) wlhy duk hallayarkace, rashin son hayaniya, miskilanci, k’asaita da basar da Abu tamkar bai damesuba, rashin iya r, ga salon cizar lips irin naka da Abdurraheem keyi shida auta jalaludden, nifa saidai naita kallonsu idan sunayi, Dan kai nake hangowa gaba d’aya a zamanin k’uruciya, musamman Abdurraheem ”.
Sarki Muhammad Sameer yay murmushi da sumbatar goshina, a hankali yace, “my mata k’yan d’a……?”.
Nace, “yagaji ubansa”.
Yace “kin gama magana Sarauniyar sarakuna, time d’in barci yayi”.
Bai barni nak’ara maganaba ya jani saman gadon tareda ja mana bargo mara nauyi.
Har barci ya kwashesa ni nakasa nawa, Na zuba masa idanu ina tuna abubuwa masu yawan gaske da suka faru a tsawon shekaru 25 da aurenmu, Galadimana Muhammad Sameer yanzu yazama Sarki Muhammad Sameer, mutum mai tarin k’asaita, mulki, k’yawawan halaye masu nagarta, hak’uri, kawaici, dattako, iya zama da mutane, tausayin Na k’asa da shi, k’yauta da k’ok’arin tsare gaskiya, wad’annan duk halayyarsace dake kuma k’aramin k’aunarsa da addu’ar y’ay’anmu koyi dashi, Na matsar da fuskata kad’an ina manna masa Sumba a la66a, yad’an bud’e ido yamin murmushi dakuma sanyani a jikinsa. Daga nan nima barcin yay awon gaba dani.

Sai bayan sallar la’asar sakaliya Na baro sashen Takawa, nafito sainaji sha’awar lek’a Hafsat, Dan duk yau bamuga junaba saboda tayi bak’i a yammacin jiya, tsakaninmu ma akwai k’ofar dake sadamu da juna batareda rakkiyar kuyangi ba, saidai abinda yasaka jikina sanyaya iske Hafsat a k’aramin falonta tareda bak’inta suna zugata akan zamanmu, ta mik’e tsaye karta yarda Na cigaba da mulkarta, kowa yasan nama fi sarkin mulki, Dan sai abinda nace yakeyi koda a fada, itako tazama tamkar wata sa d’akarsa.
Fushin daya tasominne yasani daka musu tsawa.
Bilyn Abdull da Hafsat suka rikice, ko kad’an basusan da zuwan Sarauniya Munaya falonba, hakama Maman kadee da Aysha DanSabo da Rano, party zarah, Ummu Basheer, khaleesat hydar, Ummi Ai’sha, Faxy fashion, Zee Bawa, zee Yabour, Ayusher Muh’d, Mamugee, Asmy b Aliyu, Silmzy, Feedohm, Bily galadanci, Safiyya Huguma, kdeey duksun rud’e, Dan dama sune bak’in Na Hafsat miss xoxo.
Hafsat ta mik’e tana nufar Sarauniya Munaya datayi fushi zata fita, “Please gimbiya ki saurareni, ko kad’an niban d’auki zugarsuba, dama jira nake su gama Na kora musu bayanin bakina”.
Jin wannan magana sai Sarauniya Munaya ta tsaya cak, sannan ta juyo da baya tana danne fushinta da maye gurbinsa da murmushi.
Dawowa tayi ta zauna duk tana kallonmu, cikin sanyin murya tace, “kunason sanin yanda aikai nasamu dukkan fada da matsayi a zuciyar mijina Sarki Muhammad Sameer fiyeda kowacce mace bayan mahaifiyarsa?”.
A tare suka amsa da eh.
Tai murmushi da zame hular alk’yabbarta tayi baya, sannan ta kuma gyara zama da nutsuwar maida dukkan hankalinta garemu tafara bamu labari tun daga kan harmutsi da halayyar gidansu zuwa yanzu damuke tare da ita a yanzun.
Wannan shine mak’asudin fitowar labarin RAINA KAMA ga sauran Fan’s.
Gaba d’aya sai jikinmu yay sanyi, domin labarin ya girgizamu, Sarauniya Munaya ta cancanci fiyema da hakan ga Sarki Muhammad Sameer Saifudden Abubakar, babu abinda zamuce saidai binta da fatan alkairi, itama k’awarmu Hafsat miss xoxo mu bita da addu’ar samun k’auna ta musamman a zuciyar Sarki Muhammad Sameer, dukda itama Alhmdllh tana samun dukkan kulawa a garesa.
Mun bama Sarauniya Munaya hak’uri da Neman yafiyarta akan jahiltar abinda bamu saniba, lallai idan kaga mace Na mulkin gidanta karka zargeta, Dan bakowacce bace take zama Sarauniya a gidan miji bisaga bigiren kauce hanya, wata k’yawawan hallayartane suka siyamata wannan matsayin da girman da soyyar ga mijin da ahalinsa, domin ayau labarin Munaya ya tabbatar mana da haka, hardajin sha’awar kasantuwa masu koyi da k’yawawan halayyarta.
Mun yarda lallai Mahaifansu Munaya Inna da mama Rabi’a RAINA KAMA ne, Galadima, kuma a yanzu Sarki Muhammad Sameer shima RAINA KAMA ne, Munaya & Munubiya suma RAINA KAMA, Momma RAINA KAMA. Abie RAINA KAMA, kai jama’a dayawa a wannan labarin sun zama RAINA KAMA KAGA GAYYA!! ??????
Atake a wajen tace ta yafe mana, takuma gayyacemu zuwa sashenta inda tasa aka had’a mana beta ta musamman????, dazan Baku labarin garar arzik’i da abinda wad’anan guys d’in Na HASKE sukayi dakunsha dariya, saidai ina tsoron suburbud’a alk’ur’an???????????????????.

Abin kallo bai k’are manaba sai da daddare, bayan sallar isha’i kai tsaye sashen Sarauniya Munaya akayo masa rakkiya, Dan wannan rana tana cikin ranakun dayakan kasance da iyalansa ba a matsayin sarkiba, matsayin miji ga matansa, sannan uba ga y’ay’ansa.
Yanda ya zauna yana wasa da dariya dasu, kowa Na k’ok’arin fad’ar abinda ke bakinsa, yayinda matansa suka sakashi tsakkiya da yaran 12 cif, k’ananun duk suka a jikinsa kowa farincikin ganin Abbu Na tare dashi, sunci sunsha a tare, zuwa k’arfe 10 suka d’unguma sashen su Momma, acanma hirar ta gudana mai cikeda farin ciki ga wannan ahali, murmushi ya Gaza d’aukewa a fuskokinsu, kowanne yanajin tsantsar so da k’aunar junansu a cikin jininsa da ayukansa……….?????

Kamar yanda Nina k’aunarku da kewarku ta mamayeni a lokaci d’aya??.

Tammat bi hamdullah.

Na godema Ubangijin al’arshi daya horemin dama da kwarin gwiwar kai wannan labari k’arshe dayay ta tafiyar hawainiya tamkar bazai k’areba??, kuskuren danayi ALLAH ya yafemin, abinda Na fad’a dai-dai ALLAH ya taramu a ladan Baki d’aya, bakina bashida Kalmar furtawa agareku masoyana, kun nunamin d’unbin k’auna da soyayya akan wannan labari, ina rok’on ubangiji ya amfanar damu da alkairan dake cikinsa, kuskuren kuma mu watsar dashi gefe domin girman ALLAH, Dan kunsan d’an Adam azijine, Nina ina a layinsu ni bilyn Abdull, ALLAH kabamu ikon koyi da k’yak’yk’yawa, ya nisantamu daga mummuna, ALLAH yasa munada Rabin sake had’uwa a buk Na gaba.??????

 

ALLAH ka gafartama mahaifina, kakai rahma da Ni’ima kabarinsa, ka azurtashi da yalwatacciyar rahman tareda dukkan sauran y’an uwa musulmai da suka kwanta dama??????.

 

ina Neman afuwa ga dukkan Wanda Na 6atamawa a yayin rubuta wannan littafi da Sanina ko’a rashin sani, Nima Na yafema duk Wanda ya 6atamin, ALLAH ya yafe mana Baki d’aya.??????

Akwai kuskuren danayi a salon wannan labari, domin kusan Munaya ke bada labarin ga k’awayen miss xoxo, amma mantuwa kansani shiga ciki, hakan tafaru bisa d’an rikicewa bayan dawowata daga hutun azumi, ina fatan zakumin afuwa, kuma zakuga gyara anan gaba insha ALLAH, domin wani lokacin gazawama nasarace, saika Gaza kake d’aukar hanyar gyara, ALLAH ya ganar damu baki d’aya, Rufaida Umar ina godiya sosai, Dan kece kika farkar dani kafin kowa??????????

 

Takuce sai

BILKEESA IBRAHEEM MUSA
(Bilyn Abdull??????)

 

ALLAH ya sake had’amu da alkairinsa.??????

 

I love you wijiga-wujiga, mazga-mazga, manya-manya, irin trillions d’inan my sweet fans????????????????????????.

I miss you wlhy?????

SANARWA

Yakamata y’an uwana musulmi mu farga wajen yawan binciken lafiyarmu akai-akai, Dan cutar ciwon HANTA ta yad’u a cikinmu sosai, gashi mafi yawanmu bamu saniba??, sai taci k’arfinmu muke farga saboda bamuda yawan kulawa Na binciken lafiya sai ciwo ya kwantar damu, gashi anata d’aukar ciwo ta hanyoyi da dama, wlhy wani abokin mijina suna hirar yanda a yanzu idan anzo tantance matasan da aka d’auka aikin Uniforms mafi yawan matasanmu Na arewacinmu suna d’auke da ciwon basu saniba, Dan ALLAH ki lalla6i mijinki kuje a abincika lafiyarku data y’ay’anku domin sanin halin da kuke ciki, ALLAH ya cigaba da bamu lafiya yakuma tsaremu baki d’aya, ciwone mai had’arin gaske da ake kamuwa dashi harta hanyar toilet. Karmuyi sakaci domin ALLAH??????.
https://2gnblog.blogspot.com/

Ya RABBI ka gafartama kakanninmu da iyayenmu baki d’aya, yayyenmu, k’annanenmu, y’ay’anmu, k’awayenmu, mazajenmu damu kanmu??????

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply