Hausa Novels Raina Kama Book 3 Hausa Novel

Raina Kama Book 3 Page 3-4


Raina Kama Book 3 Page 3-4
Viral

~BOOK 3~ ????3? & 4?

…………….Suna Isa plaza Saleem ya fito, dan yana ganinsu ne ta CCTV, Galadima yay k’asa da glass 6angaren da yake, idonsa akan Saleem dake fitowa, ya k’araso yana rissinawa da gaisheshi, hannu kawai ya d’aga masa, Saleem ya mik’a masa key d’in motar yana fad’in “gashi ranka ya dad’e”.
Kansa ya girgiza masa, sannan ya bud’e baki yana fad’in “ai Kaine da kanka zakaja motar, mu zamu bika a bayane”.
Da “to” Saleem ya amsa, ya juya ga motar ya shiga.

Haka suka tafi su Galadima a gaba Saleem nabin bayansu, suna tafiya Galadima nayin waya har suka isa inda aikai musu kwatance, wajen wata ma’aikatane, motocine birjik a wajen, alamun sunada yawa a ciki, daga d’an nesa suka tsaya, kusan mintuna biyar saiga wani dattijo ya fito tsakanin motocin jikinsa na rawa, harya k’araso wajen motar su Galadima idonsa akansa yake, ta window ya lek’o, amma sai Galadima yay masa nuni daya zagaya ya shigo.
Ya zauna a d’arare yana gaishe da Galadima, cikin y’ar sakin fuska Galadima ya gyara zama yana kallonsa, “Baba Rabilu ka kwantar da hankalin, insha ALLAH zaka ku6ta kuma zaka samu y’ancinka, ni namaka wannan alk’awarin, bazaka ta6a taimakona nabari ka wulak’anta ba insha ALLAH, a hankali iyalanka da duk wani dake tare dakai zai fahimci baka mutuba, yanzu mi sukeyi cikin nan d’in?”.
Baba Rabilu ya had’iye yawu, muryarsa na rawa yace, “Ranka ya dad’e ban saniba wlhy, amma abinda na fahimta shine lallai sunfara farga dakai, dan naji jiya mai wani a cikinsu yana waya wai kaima lokaci yayi dazasu maka irinna mahaifinka, dan kana neman zamewa rayuwarsu barazana”.
Murmushi Galadima yayi, yana cije lips, “karka damu baba Rabilu, wannan ai a hannun Ubangiji yake, yanzu dai ga mota nan ankawo, saika kar6a, zakayi gaba, mukuma zamu bika a baya da y’ar tazara, inason kafinma su d’auki hanya komai zai wakana, su Ameer a shirye suke suma”.
“shikenan ranka ya dad’e, ALLAH dai yabamu nasara, kaikuma yabaka kwarin gwiwa da k’arfin zuciyar abinda ka faro, ka ruguza rundunar wad’annan azzaluman da kullum cikin zaluntar bayin ALLAH suke ba a saniba, wasu kuma sunsani tsoronsune ya hanasu magana ko d’aga murya…..”. ya k’are maganar cikin sharar hawaye’.
Shiru kawai Galadima yayi yana kallonsa, shima zuciyarsa sai suya da k’una takeyi, saidai yanata ambatar sunan ALLAH kodan neman sassaunci, ajiyar zuciya ya sauke da furzar da huci, yace “shikenan muje ko, dan zamu iya rasa damarmu”.
Jin jina kai Baba Rabilu Yayi, ya fita yana rufo k’ofar, hawayen da suka cikama Galadima idone ya sakashi d’aukar glasses d’insa ya saka yana had’iye abinda ya toshe mak’oshinsa, yagaji hakanan, buk’atarsa yanzu kawai k’arshen al’amarinnan yazo kowa ya huta, shima ya gina rayuwarsa data y’ay’ansa cikin salama.

Sun isa k’ofar gidan Alhaji Shehu Darma, amma baba Rabilu ya tsayane nesa da gidan, sai motar su Galadima Ce ta k’arasa har gate.
Mai gadi yasan Galadima, dukda bawani zuwa gidan yakeba sosai, dan haka babu wani bincik’e-bincike ya barsa ya shiga.
Gidane babba na alfarma, Wanda kallo d’aya zaka masa kasan lallai an kashe dukiya ta musamman.
Galadima yana zaune a mota bai fitoba, sarkin mota ya fita domin nema masa iso, mintuna dabasu wuce 3 ba saiga P.A d’in Alhaji Darma tare da Sarkin mota, shine ya bud’e ma Galadima mota ya fito yana mai masa barka da zuwa.
Yay masa iso har cikin gida falon Alhaji Darma na saukar bak’i masu muhimmanci. Zamansa babu jimawa aka cika masa gaba da kayan ciye-ciye, kai kace jiranshi suke, motsi Galadima bai yiba balle ya nuna alamar zaici, saima latsa wayarsa kawai yakeyi hankalinsa kwance, ga iskar AC na ratsa ga66ansa, kamar daga sama yaji ance “laaah Kaine a gidanmu yau?”.
Da farko sharewa yay yak’i koda motsawa, mikuma ya tuna saiya d’ago a nutse ya zuba k’yawawan idonsa a kanta, gabansa yad’an fad’i, wannan ai yarinyar da suka ta6a had’uwane a jirgi, sannan itace suka kuma had’uwa a airport har yayma Munaya Abu dantaji haushi, to mitakeyi ana……..?
Tunaninsa ya kuma katsewa lokacin da ta tafa hannayenta guda biyu a saitin fuskarsa, firgigit ya dawo hayyacinsa, amma saiya basar kawai ya maida kansa ga wayarsa yana cigaba da danne-danne.
Tana niyyar yin magana saiga Alhaji Shehu ya shigo, Galadima yakuma saita camera d’in wayarsa danya ga yanayin da Alhaji Darma zai shiga idan ya gansu.
Ilai kuwa da mamaki ya kalli yarinyar, ya bud’e baki kamar zaiyi masifa saikuma ya had’iye yana fad’in “kekuma waya kawoki nan Rumaisa?”.
Dariya tayi cikin nuna ita ta6ararriyace zata fara zaro zance ya harareta, sannan ya nuna mata k’ofa da hannu, “wannan ai iskancine, ya za’ayi daga yin bak’o kiwanizo ki tsaya masa akai, kedai uwarki tagama lalataki, ta6ararki tayi yawa w…….”
Katseshi Galadima yay da fad’in Afuwa Alhaji, maybe itama uzurintane ya kawota”.
“Shikenan Sameer, amma abunne babu dad’i ai”.
“babu komai”. Galadima ya fad’a cikin lumshe ido.
Gaisuwa sukayi da tambayar juna Ahali, Alhaji Darma yace, “ina Haneefa? had’uwa tayi wahala, siyasa ta 6oyemu, tunda kunk’i bani dai”.
Murmushi kawai Galadima yay baice komaiba.
Alhaji Darma daduk yakasa nutsuwa da wannan zuwa na Galadima ya mik’e yana fad’in “kad’anci wani Abu Sameer, ina zuwa dan ALLAH”.
Galadima ya jinjina kai kawai, Alhaji Darma na fita ya murmusa, bodyguards biyu da suka shigo tare dashi d’aya ya fita, d’ayan harzai fice saiya dawo baya kad’an, wani Abu ya ajiyema Galadima ya fice shima da sauri.
d’auka Galadima yay ya saka a aljihu, sannan yamik’e alamun shirin tafiya, hakan ya nuna dama can abinda yazo nema kenan. A tsaye Alhaji Darma ya iskeshi, cikin mamaki yace, “Sameer yana ganka a tsayene?”.
Cikin murmushin dole Galadima yace babu komai Alhaji, zan wucene, dama hanyace ta biyo damu, shine nace bara na shigo mu gaisa an dad’e ba’a had’uba”.
“Aiko ka k’yauta, ALLAH dai ya saka da alkairi, ai kafi Haneefa da saitazo k’asar sau nawa bata tuna damuba”.
Nanma dai murmusawa Galadima yayi kawai.
Har harabar gidan Alhaji Darma ya rako Galadima, saida yaga ya shiga mota sannan hankalinsa ya kwanta, ya sauke ajiyar zuciya yana goge zufar fuskarsa data wuya.

Sarkin mota yay murmushi, “Ranka ya dad’e yanzu kam komai ya kammala, d’an shegiyarnan shima yazo hannu”.
Galadima baice komaiba sai ciza lips kawai da yayi. Guri suka kuma samu suka tsaya, duk motsin shiga da fitar gidan akan idon sune, suna nan zaune har Motocin Darma suka fito, suna fara tafiya baba Rabilu ya take musu baya, su Galadima kuma suka fara binsu nesa-nesa, can tafiya tad’an fara Nisan daba mai yawaba wani go slow Mara dalili ya tsayar dasu, Ameer daya zama mai bada hannu a yau a hanya data rabu biyu cikin hikima ya nuna motar da Alhaji Darma yake ciki yana sanarma driver d’in ya fito ya duba tayarsa.
driver dake shirin fad’ama Ameer bak’ar magana Alhaji Darma yamasa tsawa akan ya fita ya duba mana, jikinsa na rawa ya fita, shikuma Alhaji Darma ya maida kansa ga duba newspaper d’in hannunsa.
Da Sauri Baba Rabilu ya fito daga motar da yake ya maye gurbin driver Alhaji Darma, akuma time d’in Ameer yabasu hanya, shikuma wancan Driver yana can sagare da baki wai yana duba tayar mota, ganin motar tayi gaba sai yashiga k’ok’arin binta, Ameer ya dakatar dashi da fad’in anfa matsarne saboda ta tare hanya, bagasu a wannan hannunba inda zakaji dad’in dubawa”.
Tsaki driver yayi yanama Ameer kallon banza, ya matsa ga Motar dake a fake ya shiga yana k’ananun magana, “wlhy Alhaji yaronnan k’arya yakeyi, irin y’an iskan yarannan nema fa masu shan kwayarsu suyi mankas suzo sunama mutane dabanci a titi, yakamata ad’au mataki akan irinsu”.
Shiru dai yaji Alhaji bai amsaba. daga nan shima sai yayi shiru, duk zatonsa ko Alhaji baya buk’atar magana ne.

A can kuwa tuni baba Rabilu yayi ciki da Alhaji Darma, dan harya d’auki hanya Su Galadima na binsa a baya, Alhaji dai baisan wainar da ake toyawa ba, hankalinsa nakan jarida????.

Su kuma can sun d’anyi nisa da tafiya Driver dai yaga yanata surutu Alhaji ko tari bai yiba, saiya waigo yana kallon bayan, babu shiri ya taka birki da masifar k’arfi, jikake k’uuuuuu!!!! Gabbbb! Ya bigi motar gabansa, mota saita fara katantanwa a titi, nanfa mutane suka tsaya kallon abin al’ajabi, sauran motocin Alhaji Darma ma duk suka tsaya. Da k’yar dai wannan mota ta tsaya, jama’a suka zaro driver da k’yar, nan mutane na kaya-kaya akaisa asibiyi karya mutu tunda yana numfashi, sukuma bodyguards d’in Darma hange-hangen ina za’a ganoshi shima suke, saidai alama ta nuna motar mutum 1 nema a cikinta.
Tofa babbar magana, an dai d’auki driver da gaggawa zuwa asibiti, yayinda bodyguards suka shiga jaje sukuma. Kafin kacemi gari yafara d’auka ta silar social media, saikuma y’an sanda.

Jin mota ta tsaya Alhaji shehu ya d’aga kai danya tambayi ko lafiya? yasan dai ko quarter d’in inda suka nufa basuyiba, to miye na tsayawar?.
Baki bud’e yace, kai Antoni miye haka? gidan uwarwa ka kawoni nan kuma?”.
Baba Rabilu ya lek’o da kansa yana Murmushi, “Aboki aiba Antoni baneba”.
A matuk’ar firgice Alhaji Darma ya jefar da jaridar hannunsa, jikinsa na rawa da taune harshe yace Alhaji Rabeelu? Dama baka mutuba?”.
“Mutuwa ai sai kwana ya k’are abokina, ganidai yau kam harda tuk’aka”.
Cikin matuk’ar tsawa yace, “Karya kake munafuki, wlhy ka mutu saidai idan fatalwa kayimin, dafa hannunsa na kasheka shekaru 19 kenan?. Toko fatalwarka Ce yanzu itama zan kuma kasheta”. ‘yay maganar yana waige-waigen neman makami, amma babu.
Baba Rabilu ya bud’e motar ya fita yana dariya, bud’e ma Alhaji Darma k’ofar shima yana fad’in “maza fito ka kuma kashe fatalwata…..”
Aiko a harzuk’e ya fito, saida kuma wata rikitarce takuma kamashi ganin Galadima tsaye a jikin motar dake kusada wadda yake, ya hard’e hannuwansa a k’irji yayi wata tsayuwa mai sunam firgita mak’iyi. baya Alhaji Darma yay taga-taga zai fad’i ya dai samu ya dafe mota jikinsa na tsuma, cikin rawar murya yake nuna Galadima da hannu yana fad’in “S…S..Sameer! ba yanzu muke tare dakaiba a gidana?”.
Galadima yay wani murmushin gefen baki yana gyara tsayuwa, eyeglasses d’in idonsa ya cire sannan yasa handkerchief ya goge fuskarsa, glasses d’in da handkerchief ya maida cikin aljihu, cikin d’age gira yace, “Nine kuwa tabbas SD, dan yau kaiba mai wancan sunan dana Sani bane a gaba na……..”.
Katseshi Alhaji Darma yayi, “kai Sameer! Kardai ka yarda da zancen wannan fatalwar?, wlhy fa Fatalwane, shekararsa 19 da mutuwa, karka yarda da munafuncinsa, kafa tuna nid’in wanene a wajenku, ta ya za’ayi na iya cutar daku? Ka yarda dani domin ALLAH”.
murmushi Galadima yakuma saki, ya taka a hankali zuwa gabansa, yatsansa d’aya ya saka yana shafar girarsa, yace “SD aishi mugu dama bashida kama, bakasan yanzu babu kasuwancin dayafi yad’uwa a duniyaba sama da cin amanar juna, kuma na jikinka ke maka. Waynot ka Adana kalamanka ko zasu maka amfani nan gaba k’ad’an”. Yay Salute nashi yana ra6ashi ya wuce zuwa cikin gidan.
“Sameer! Sameer!! ka saurareni mana”. Alhaji Darma keta fad’a kamar zai had’iye harshensa.
Ko sau d’aya Galadima bai juyoba yay ciki abinsa.
Wannan damar Alhaji Darma yay amfani da ita wajen harin baba Rabilu, amma sai su Ameer suka zagayeshi, cikin mamaki ya kalli Ameer d’in, danya ganesa sarai.
Ameer ya d’aga kafad’a yana ta6e baki alamar bashida matsala??……………..???

 

??????yau dai typing d’in rowa nayi muku, gaba d’aya banajin yin typing d’in, kuyi manage kawai????????????????????.

 

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu??????_*
*_typing??_*

?? *_HASKE WRITERS ASSO….._*

*_?RAINA KAMA…..!!?_*
_(Kaga gayya)_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply