Hausa Novels Raina Kama Book 3 Hausa Novel

Raina Kama Book 3 Page 29


Raina Kama Book 3 Page 29
Viral

BOOK 3 ????2?9?

https://2gnblog.blogspot.com/
……………..Gaba d’aya sun kasa yin breakfast, suna cikin zaman jigum-jigum suka jiyo bud’e gate da shigowar mota. Samha ta fita da hanzarinta danson ganin wanene, fitowar tata tayi dai-dai da fitowar Galadima daga cikin mota fuskarsa d’auke da wani irin k’ayataccen murmushi daya fidda sirrin k’yawunsa.
Da gudu ta taho garesa, yakan mata fad’a akan son rungumarsa ko Sauban amma yau saigashi ya bud’e mata hannu dakansa tazo ta shige jikinsa.
Ihun murnartace tasaka su Momma fitowa da hanzari suma
Ganin Galadima ai sai duk sukayo kansa itada aunty Mimi, itadai munaya gefe ta tsaya tana sharar hawayen farin ciki.
Abie dake kallonsu daga cikin mota ya saki murmushi yana share hawaye, yana k’asa d’aya da iyalansa amma bai ta6a sanin muhallinsu ba sai yau, dukda bai shigaba gidan yamasa k’yau.
Galadima ya ture Samha daga jikinsa ya rungume Momma da aunty Mimi yana sakin wani irin kuka daya matuk’ar tada hankalinsu.
Da sauri suka d’agosa hankali tashe suna tambayarsa mike faruwa? Kodai ALLAH yayima Abie rasuwane?.
Cikin kuka da dariya yace kowa ya rufe idonsa .
Babu musu sukabi Umarninsa, har Munaya dake gefe.
Yace, “kun tabbatar kowa ya rufe?”.
A tare suka amsa masa da eh.
Ya murmusa da goge sauran hawayensa sannan ya juya ga motar ya bud’e, hannun Abie ya kama da taimakonsa ya fito rik’eda sandarsa mai k’yau dazata dinga taimaka masa wajen tafiya, Dan har yanzu tafiyar batai kwariba.
Saida Abie ya jingina jikin Mota ya tsaya da k’yau sannan Galadima yace, “Kowa ya bud’e idonsa”.
Har rige-rigen bud’ewa suke.
Akusan tare Aunty Mimi da Munaya da Samba suka kwalla k’ara, Momma kam sai tayi luuu sai gata a k’asa kawai ta sume.
Abie da Galadima dasu Munaya duk kanta sukai suna kiran sunanta, shima Abie ya tuzgud’e zai fad’i, Dr Ajay daya kawosu yay hanzari rik’esa yana fad’in “A sannu dai Sir, k’afafunka basukai k’warin wannan hanzarinba”.

Da gudu Munaya takoma ciki sai gata da ruwa, ta zuba a hannu tana shafama Momma, da k’arfi takawo Numfashi.
Bin yaran nata tayi da kallo tana fad’in “mafarki nakeyi ko yarana? Nasan irin mafarkin dana sabane dama, ba takawa Na bane ba”.
Cikin dariya da kuka Aunty Mimi tace, “Wlhy shine Momma, shine agabanki ba mafarki kikeba, Momma Abie d’inmune wlhy tallahi kinji Na rantse”.
Zumbur Momma ta tashi daga jikin Aunty Mimi, Abie dake tsaye har yanzu bisa taimakon su Galadima ya murmusa yana fad’in “Zeenah ki cire kokwanto, da gaske wannan Saifudden d’inkine ba Wanda yasaba zuwa miki a mafarkiba kinji”.
Tasowa Momma tayi garesa, ta shafa fuskarsa domin tabbatarwa, takuma binsa da kallo tundaga sama har k’asa, lallai da gaske wannan Saifudden d’intane bana mafarkiba, Ai sai kawai ta rungumeshi babu kunya ko tunawa dasu Galadima a wajen.
Sai duk’ar da Kansu duk sukai suna Murmushi.

Gaba d’ayansu kowanne soyake ya nuna ajintarsa ga Abie domin nuna masa gamsuwa da farincikin samun lafiyarsa, aka kawo masa y’an Uku ya had’a duka ya rungume yana maijin k’aunarsu har cikin jininsa, Khaleel ma yana nanik’e dashi.
Munaya dai nadaga gefe bata zak’eba.
Idon Abie ya sauka akanta, Murmushi yamata yana fad’in “’Diyata zo mana”.
Takowa tai cikeda jin kunya tazo gabansa ta durk’usa, cikin girmamawa ta gaisheshi da masa addu’ar k’arin samun lafiya mai d’orewa.
Ya amsa yana mai k’ara jin farin cikin kadancewarta suruka agaresa uwa ga jikokinsa.
Galadima ma yakasa d’auke ido daga gareta, sai yaga tamasa y’ar rama tsakanin jiya da yau.
Breakfast d’in dabai samu shigaba d’azun aka baje domin ci, amma shi Abie kasancewar an hanashi cin wasu Abubuwan Kuku yay azamar tanada masa Wanda yake buk’ata.
Daka gansu kasan suna tareda matsanancin farin ciki .
Koda suka kammala Galadima ya taimakawa Abie shiga d’akin Momma, shima ya haye sama shida matarsa.
Tun’a falo ya d’auketa cak yana juyi da ita cikin hajijiya, babu shiri Munaya tahau k’yalk’yata dariya da k’an k’ame wuyansa da hannayensa tana cusa kanta cikin k’irjinsa.
A haka suka k’arasa cikin bedroom, ya jefa abarsa saman gado yabita tareda jan bargo yay musu runfa.

An hanani ganin abinda akeyi??, sauk’inma inada mijin Nima????.

Farin cikin da wannan ahali suka tsinci Kansu wlhy 6ata lokacine, Momma kam sai ko ganinta bama ayi????.

A gurguke please????.

Walwala da farin cikin wannan gida tadawo kam, ga nutsuwa mai saka zukata samun damar yawan ibada, ko yaushe suna manne da Abie, sai idan time d’in hutunsa ne yayi, Galadima yayma kowa gargad’i akan sanarda tashin Abie, burinsa kowa yaga abin mamaki, 100% Momma ta yarda da shawararsa, hakama Abie.
Yanzu dai kam sun yanke shawarar Isa k’asarsu ta haihuwa ranar salla k’arama, zasu azumi na kwanaki 20 a india, su biya Saudiyya suyi Umrah ta kwana goma su isa Nigeria a ranar salla ayi idi dasu.
Gaba d’aya azumi saura kwanaki 6 a farashi.

 

******

AZUMI

Alhmdllh kowanne musulmi yau ya tashi da azumin watan Ramadan mai mai albarka, saidai irin masu ak’idar saimun gani da suka kasance k’alilan acikin wasu k’asashe irin namu Na yankin Africa.
Duk da shayarwa hakan bai hana ni zama cikin jerin masuyiba, dan raino dai bani nakeba, tsakanina da yarannan idan sunji yunwa, koyaushe suna tare dasu Momma, sunyi 6ul-6ul dasu tamkar y’an watanni 6, amma har yanzu suna cikin wata Na hud’une ma kacal.
Tunda safe Galadima ya fice, Na d’an tashi nai gyaran saman sannan Na sakko, yau babu maganar shiga kitchen, Dan tunda Abie ya dawo nakoma nike mishi girkin abinda zaici, wataranma nakan had’a da namu muma, babu abinda zan cema wad’annan mutane sai godiya, soyayya dai mai cike da k’auna ina samunta a garesu, ni da mijina kam ai sai hamdala, yana tattalina da tarairayata, saidai d’an sa6ani Na yau da gobe Wanda baka Isa raba ma’autara da Shiba, shima kuwa bai wuce wasu awanni muke shiryawa ba, inko Momma ta lura ma takan kiramu tamana Nasiha, hakama Aunty Mimi.
A falo Na iske Abie daga can gefen falon inda wasu kujeru biyu suke da kanta mai d’aukeda buks Na karatu, tundaga kan Na addini har zuwa Na makaranta dadai sauransu, zaune yake yana nazarin wani littafi da banga sunansa ba saboda tazarar dake a tsakaninmu.
Sai Samha dake falon kwance a kujera tana kallon film, zaman gyalena Na gyara, Na taka a nutse zuwa garesa, saida Na durk’usa a gabansa sanann nace “Barka da safiya Abie”.
‘Dago k’yawawan idanunsa da Galadima ya gado yay yana kallona, ya zare medical eyeglasses d’in idonsa yana Murmushi, “’Diyata barka dai, kin tashi lafiya?”.
Kaina a k’asa ina murnushi nace, “Lafiya lau Abie, ya ibada da k’arin k’arfin jiki?”.
“Alhmdllh d’iyata, ai jiki kam sai godiyar Ubangiji, Muhammad fa?”.
“Ya fita tunda safe”. Na fad’a cikin kuma duk’ar dakai.
Murmushi Abie yayi, ya maida eyeglasses d’insa yana fad’in “ALLAH ya dawo dashi lafiya to”.
A saman la66a Na amsa, sannan Na mik’e da k’yar zuwa d’akin Momma.
Abie ya bita kallo zuciyarsa cikeda k’aunar wannan yarinya, irinta yaytama y’ay’ansa addu’ar samu amatsayin abokiyar rayuwa, Alhmdlh Ubangiji ya amsa masa, saura Sauban kuma.

Nidai nashiga Na gaida Momma, Na iske tanama su Amaturrahman shiri, da alama wanka tamusu, Na gaisheta cikeda girmamawa kamar yanda Na saba, itama ta amsamin da kulawa tareda d’an jana da hira tamkar yanda ta saba, nad’an jima a d’akin, harta fito tabarni Na gyarashi tsaf kamar yanda nakeyi tun bayan dawowarmu, Dan tuni Na dakatar da Samha ni nakeyi.
Na fito da nufin shiga Na gaida aunty Mimi saina isketa tama fito falo, anan muka gaisa Na zauna muka d’ora da hira tamkar yanda muka saba, mafi yawama firar ta Sauban Ce, Dan kowa yayi missing d’insa, yace azumi da kwana 3 zai zo sai salla zai koma, Galadima bai hanashiba, dukda yana tareda tattalar kud’i a tsakaninnan saboda sun masa k’aranci, to saima papi ya d’auki nauyin zuwan Na Sauban da komawarsa.
Mund’an ja lokaci Muna hira barci yafara rinjayata, mik’ewa nayi Na gudu sama, nad’an rage kayan jikina Na haye gado sai barci.

Kusan 10am saiga Galadima ya dawo, bai iske kowa a falonba, da alama barci suke kokuma suna harkokin gabansu a ciki, kai tsaye d’akin su Momma ya nufa, yay knocking aka bashi izinin shiga.
Abie Na zaune saman abin salla ya idar da sallar walha, yayinda Momma ke zaune bakin gado tana bama Abdurraheem Magani saboda zazza6in dake jikinsa.
Galadima ya zauna a saman sofa yana gaidata da tambayar miya sami Abdurraheem d’in?.
Cikeda kulawa ta amsa masa tana gogema yaron inda maganin ya 6ata masa a wuya da fuska.
“Tunda muka tashi yau Na kula bayajin dad’i yaronnan, inagafa yakamata ka kaishi a bincikasa, basai mun zauna wata 6 ta cikaba, tunda kasan ciwon yana zama iri daban-daban, karmuyi tunanin ko irin nakane azo ba hakaba, Dan Na kula yafika yawan laulayi shikam, Abdurraheem baya had’a sati biyu da isashsshiyar lafiya”.
Jin jina kai Galadima yayi, tausayin d’an nasa Na ratsashi, ya had’iye abinda ya tsaya masa a mak’oshi da k’yar yana amsar Abdurraheem d’in daga hannunta.
Abie daya shafa addu’a ya maido hankali garesu.
Mik’ewa Galadima yay yakoma inda yake yana gaisheshi, Abie ya shafa kansa hakama Abdurraheem, cikeda tsokana yace, “Like Father like son”.
Dariya Momma tayi, yayinda Galadima yay Murmushi mai k’ayatarwa har hak’oransa Na bayyana.
Yace, “Abie ai dakai suke kama duka, Amaturahman cema tad’an d’ebo mamansu kad’an”.

[8/19, 6:14 PM] ??????Da Rarrafe??????: Abie yay Murmushin jin dad’i, yana shafa kan Abdurraheem da yay barci, gaskiya Galadima ya fad’a, dan shima tun randa yafara ganinsu ya lura da haka.
Sund’an ta6a hira, har Galadima ke kawo maganar Aunty Mimi akan yakamata tayi aure hakanan, domin zaman bashida amfani haka, ko wani yamaka k’yak’yk’yawar fahimta wani bazai makaba, tunda ba wuce auren tayiba.
100% iyayensa sun gamsu da zancensa, sunkuma amsa masa da isha ALLAH zasu zama Na musamman da ita.
Kwantar da Abdurraheem yay musu sallama akan zaije yad’an rage barci.

Tunda ya shigo yay tozali da Munaya barbaje a gado, murmushi yad’anyi yana cire Bottoms d’in rigarsa harya k’araso cikin d’akin, hanging d’in rigar yay sannan ya zauna saman sofa yana cire takalmansa, mitsawar da Munaya tayi tana juya kwanciya yad’ago ya kalleta, aransa yace hajiyata ko an farajin azuminne?.
Harya gama hidimarsa yazo gefenta ya kwanta bata saniba, dayake ba motsi mai k’arfi yay tayiba, Dan yasan batada nauyin barci, gudun karta tashi yay tayin komai a sannu.

*****

Duk musulmin ALLAH Na k’warai daya wadatu da ibada inhar lokacin salla tayi ko barci yake saiyaji a jikinsa, kokuma yayta mafarkin ana sallar, hakance ta kasance ga Munaya da Galadima, kusan atare suka farka, kowanne bakinsa d’auke da addu’ar tashi barci.
mamaki ya kamani ganinsa gefena, Dan bansan yama dawoba, ya min murmushi nima Na mayar masa da murtani ina shafa fuskarsa.
Cikin lumshe ido nace, “Yaushe ka dawo?”.
Hannunsa ya d’ora saman nawa dake kan fuskarsa, yad’an rufe ido ya bud’e akaina, murya k’asa-k’asa yace, “Tun d’azun mana, kinata barci abinki”.
Yatsine fuska nad’anyi ina zame hannuna da k’ok’arin tashi. Nace, “Wlhy barci bai wani isheniba shiyyasa nad’an rage yanzu kafin time d’in shiga kitchen”.
Shima tashi yay zaune yana jinjinamin kai.
Shiya fara shiga wanka, saida ya fito sannan nima Na shiga nayo.
Koda ya fita salla ya dawo bai koma cikiba, sai suka zauna a harabar gidan shi da Abie suna hira, dayake kullum Galadima cikin bashi labarin abubuwan da suka dingi faruwa yay lokacin yana jiyya, wani yay murmushi, wani dariya, wani kuka, yana kuma yabama Galadima bisa ga gwarzan takar dayayi ta kare mutuncin ahalinsa da rik’e martabarsa.
Har time la’asar suna zaune a wajen, da taimakon Galadima Abie yataka zuwa massalaci, dan inhar yana gida haka sukeyi, bayan sun dawo awajen suka sake zama, Galadima ya kirani nabama Samha System d’insa takai masa.
Da to Na amsa, Na hau sama Na d’akko nabata.

K’arfe biyar dai-dai muka shiga kitchen ni da Samha da kuku, sai Hadiman gidan guda biyu dake taimaka mana da wasu ayyukan.
Cikin nutsuwa muka gabatar da dad’ad’an abincin bud’a baki, wasu namu Na Hausa wasu kuma Nan.
Gab da magrib muka gama, munbarsu k’arasa komai Na k’imtsa kitchen d’in da shirya abincin.
Wanka nakesonyi ga Amaturrahman Na kuka, Momma kuma tace babu inda zani saina shayar da ita.
Dole Na zauna ina dungure kanta. Oho batasan ma inayiba, itadai taji abinda take buk’ata a baki kawai. Ganin tad’ansha na d’auketa muka haye sama dan karma Momma tace saita k’ara.
Na iske Galadima yana wanka, ni bammasan ya shigo cikiba, Na kwantar da Amaturrahman Na kuma sauka, nasan dole yana d’akin za’a kira salla, dabino da ruwa Na d’oro a k’aramin tire nazo Na ajiye, ina ajewa kuwa yana fitowa.
Sannu da aiki yamin, Na amsa ina manna masa Sumba a hannunsa dana kama, nai saurin shigewa bathroom.
da kallo ya bita yana murmushi, ya kalla hannunsa data sumbata shima ya sumbaci wajen.
Fitowata wanka yay dai-dai da cikar lokacin kiran sallar magrib, a bakin gado Na iskesa zaune Amaturrahman Na kwance kusa dashi tana wuntsil-wutsil da k’afafu, idonta nakan hasken globe, shikuma yana kallonta yana murmushi da video d’inta awaya.
Batare danayi tunanin komaiba Na k’araso garesa da nufin bashi dabinon, amma saiya jawoni nafad’o jikinsa, dukda laimar ruwan dake jikina.
Babu wani k’arin bayani ya d’aura bakinsa saman la66ana, idanu Na waro masa Na tsorata da mamaki, amma saiya kashemin ido d’aya da cigaba da abinda yake.
Kusan mintuna biyu nasamu ku6ta. Ina yunk’urin tashi ya kuma hanani.
“O ALLAH, azumi fa kakai my King, shine kafara da jan magana mai makon Neman ruwa ko dabino?”.
Wani miskilin murmushi yayi da huramin iska saman ido. Farfar Na fara da idanu.
Yakuma Murmusawa, “Bazaki ganeba babie na nayi missing d’inkine, kinga ai lada biyu, gatakai azumi gata d’abbak’a sunna, ni ai ga dabino Na nan, yawunki kuma shine ruwana”. Ya k’are maganar yatsansa a la66ana.
Tura kaina nayi a jikinsa ina Murmushi.
Ya rungumeni da shafa bayana shima yana murmushin.

K’arshe dai sai a d’akin mukai sallar magrib sannan muka sauka k’asa shan ruwa.
Jinai gaba d’aya kewar y’an gidanmu tazomin a yau, Na tuna yanda muke had’uwa k’wanmu da kwarkwata a runfa shan ruwa, murmushi naita saki dajin kewarsu mai yawa da d’okin son ganinsu.
Aunty Mimi data lura dani tace, “My K’anwa yadai?”.
Nakuma fad’ad’a fara’ata ina cewa “Na tuno gidane kawai Aunty”.
Murmushi duk sukayi, Galadima dake gefena ya mintsini cinyata kad’an, d’agowa nai Na kallesa ina d’an 6ata fuska, gwalo yay min kad’an yana d’auke kai cikeda basarwa tamkar bashi yayiba.
Saida na tabbatar bamai kallonmu sannan nima na rama, aiko zafin yasakashi kad’an garage ya 6arar da kunun da yake sha, yay saurin rik’ewa.
Sannu muka shiga masa, na Fiske abina tamkar banyi komaiba.
Muna had’a ido ya cije lips da min gargad’i da ido akan zai kamanine.
Nima gwalo namasa.

Abinda basu saniba tun farkon fara lamarin Abie da Momma suna kallonsu, dan haka yanzu sai suka kalli juna suna murmushi.

A gurguje please???????

?????????

Kwan uku da fara azumi Sauban ya iso India, bak’aramar birkicewa yay da ihun ganin Abie ya samu lafiyaba, hardasu kuka rurus, Abie ya rungume Autansa d’aya zama sangamemen Saurayi yana mai jin farin ciki da k’aunarsa. A ranar sai sabuwar murna ta tashi kuma, haka muka wuni cikin farinciki biyu, na zuwan Sauban da gimama farincikin daya riska.
Haka azumi yacigaba da gangarawa, kullum saina kira su Abbanmu da sauran jama’ar gidanmu namusu barka da shan ruwa, hakama y’an uwana sunta turomin sak’on massages kenan kulum namin barka da shan ruwa.

Azumi na kwana 15 muka kai Abdurraheem Asibiti, Yakuma samun binciken kwararrun Likitocin zuciya, suka dubashi da k’aramin dabaru wajen kula da rainonsa, sai magunguna da zai iya sha a matsayinsa na yaro k’arami.

Dukkan sayayya da Galadima zaiyi ya kammalata, harma ya tura mana kayanmu ta jirgin ruwa.
A kwanakin bashida wani sukuni, yawan shigi da fici na damk’a amanar harkokinsa kawai yake ga mutane, dan zai jima a 9ja bai dawoba a yanda ya hasaso, inma ya shigo India bazai dinga wuce sati biyu zuwa uku ba zai barta, shima saboda Company nasune, danma yanata k’ok’arin ganin sunzo sun kafa reshe a Nigeria dan shima yabada gunmawa ga k’asarsa.

Muma dake cikin gidan bawani zaman mukeba, munata kimtse-kimtsen kayan gidan waje d’ayane. Da sallama da mak’wafta da abokan arzik’i da akai sabo.
A wannan yanayinne na gane Ashe yayan Dhibya Gopal soyayya suke da Samha, wannan ne kusancin dake k’ara k’arfi tsakanin Dhinya da Samha, ban sanarma kowaba, haka itama ban mata maganaba, tunda gashi ALLAH ya kawo sanadin da zasu nisanci juna cikin sauk’i, babu yanda za’ayi aure ya iya yuwuwa a tsakaninsu, yaudarar juna kawai sukeyi, Su Dhibya y’an k’abilar Hindu ne, kuma mabiya wannan addini masu tsananin ak’ida, Galadima ya ta6a sanarmin iyayensu sun dad’e basu saki jiki dasuba saboda kasancewarsu musulmai kawai, Gopal kusan sa’anni suke dashi amma babu wata shak’uwa tsakaninsu. To tayaya suke tunanin k’ulluwar aure a tsakaninsu inba Gopal musulunta zaiyiba, hakan kuma abune mai wuyar gaske, dukda ba’a yanke hujunci da ikon ALLAH.
Ana gobe zamu wuce saudia Galadima ya sallami Khumar da kuku, wad’anda suke kuka da idanunsu na bak’in cikin rabuwa damu, muma kuma hakanne, sai da Galadima yamusu bayani akan badan shima bayason rayuwa dasu ya sallamesuba, sai dan karya tauye hak’insune, yabasu Dama suje su nemi wasu ayyukan, duk sanda ya shigo k’asar zai nemesu su dawo kan aikinsu insha ALLAH.
Sunyi murna sosai da bayaninsa, haka muma munji dad’in hakan, domin kuwa dai ba’a rabuba kenan.

KOMAI YAY FARKO…??????

Zai iya zama k’arshe watan watarana, yau ga Abie daya shigo India cikin tsananin ciwo da fidda rai daga rayuwa zai barta cikin farin ciki da k’warin gwiwar rahma da falalar ubangijin al’arshi. Fuskokinmu kawai sun isa shaida maka muna cikin farin ciki muma.
Mun tafi cikin kewar India da jama’ar cikinta, musamman ma Momma da Abie da tunda suka shigota sai yaune zasu barta.
Tunkan mu Isa Galadima ya sanya Sultan nema mana masauki.
Muna sauka kuwa cikin mutunci akazo aka d’aukemu zuwa matsakaicin gida dazai d’aukemu babu wata takura.
Har kuka saida nayi a 6oye ganina a inda ban ta6a zato ko tsammaniba, kasa mai tsarki.
Hutun wannan ranar kawai muka samu, washe gari muka duk’ufa ibada da godiyar Ubangiji bisa ga ni’imomi dayay mana badan munfi sauran bayinsa da komaiba.

Tsawon kwana goma muna bautar Ubangiji, a randa ake saran ganin wata jirginmu ya d’aga zuwa k’asarmu ta haihuwa, Abie da Momma sunfi kowa zumud’i da k’aguwa.
Babu wanda yasan da zuwanmu sai Sarkin Mota, shima kuma bashi da tabbacin dawa za’azo d’in, Galadima dai yace ya saka a gyara masa 6angarensa da inda su Aunty Mimi ke sauka.

*****

Jirginmu ya sauka 9ja k’arfe 11:30pm. Mu muka fara fitowa, Abie da Galadima suka zama k’arshe.
Abie na sauka a jirgin yana Murmushi da hawaye, tareda shak’ar iskar k’asarsa daya bari tsawon shekaru, yama fidda ransa da kuma dawowa cikinta har Abadan.

Sarkin Mota da dogaran Galadima suna zaune a airport d’in suna jiran isowarmu.
Ganinmu da yawa yabasu mamaki, amma saisuka zube suna gaishemu, a cikinsu babu Wanda ya gane momma da Abie, Bama zai yuwu su ganesu d’inba, tunda sanda yabar k’arsar duk basa a wannan matsayin, sai dai iyayensu, wanda a halin yanzu mafi yawa acikinsu duksun rasu ma.
Dole saida muka k’ara da motocin haya, Momma da Abie suka shiga wadda sarkin Mota ke ja, Ni da Galadima da Samha muka shiga ta haya d’aya, Aunty Mimi da Yaa Sauban da yara suka shiga d’aya.

Mun Isa Masarautar tsit babu yawan hayaniya alamar mafi yawan al’ummar cikinta sun nutsu waje d’aya, sai wasu tsirarun hadimai dake kai kawo mussamman masu tsaro.
Duk muka fito amma banda su Momma, Galadima ya nufi mortar dan son taimakawa Abie fiwo, Sarkin Mota kuma na k’ok’arin biyan masu motarnan kud’insu.
Fir Abie yak’i fita, yace d’an uwansa mai martaba ne kad’ai zai fiddashi a motar, duk rok’on da sukai masa fir yak’i, gashi yanata sharar hawaye da handkerchief.

Galadima yasan yanzu Mai martaba ya shiga ciki, maybe ma matar dake dashi taje.
Rasa yama zaiyi yayi.
Momma Ce tabashi shawarar kiran wayar mai martaba, cikin damuwa Galadima ya kar6a wayan Sauban dabe dad’e da barin k’asarba, sim card d’insa zaifi saurin aiki fiye da nashi.
Hadiman gidan sund’an fara fuskantar akwai matsala gameda tsayuwar su Galadima, dan wannan ba halinsa bane.

ALLAH ma ya taimaka Mai martaba baiyi barciba, yana zaune ne yana duba wasu takardu, matarsa ta biyu na tare dashi dan yau kwanantane. Ya dad’e yana kallon wayar da nazarin mai kiransa, dan ba kowane keda Number mai martaba, sai jiga-jigai irinsu Galadima d’in.
Tamkar bazai d’aukaba yad’ai d’auka tana gab da katsewa a kira karo na biyu.
Cikeda girmamawa Galadima ya gaishesa sanann yay masa bayanin shine.
Da farko mai martaba tsorata yayi, dan babu Wanda yasanar masa Galadima ya dawo, cikin hikima da girmamawa Galadima yayma mai martaba bayanin yafito yaga abin mamaki a k’ofar sashensa.
Sosai mai martaba yayta juya kalmar abin mamakin, hakama matarsa, alk’yabba ta d’akko masa ya saka sannan suka fito a tare.
Jakadiya na niyyar tafiya makwancinta taci karo da mota a k’ofar turakar mai martaba, mamaki ya kamata, zatayi magana saitaga Galadima dake tsaye a jikin motor, ta rusuna tana gaisheshi, kamar yanda yasaba ya d’aga mata hannu cikeda izzar mulki.
Bata fita a mamakinba taga mai martaba da matarsa sun fito.
Galadima baice komaiba sai bud’e murfin motar da yay yana nunama mai martaba ciki da hannu.

Jikin baiwar mama Fulani mai kai mata rahoton motsin kowa na rawa ta nufi sashenta, hartayi shirin barci ma ta sallami Kuyanginta, amma dayake baiwar tanada fada sosai a wajen ta saita mata knocking k’ofa.
Cikeda masifa da izza mama Fulani ta bud’e k’ofar, jikin baiwarnan na rawa ta zube k’asa tana fad’in “Ki gafarceni ranki ya dad’e, abinda nagano yafi k’arfin barinsa zuwa safiya, yalla6ai Galadima ya shigo fada shida sauran iyalan tsohon sarki, maimakon yawuce sashensa tamkar yanda ya saba saiya nufi turakar mai martaba kai tsaye, gashi can naga yana nuna masa Abu amota, ban tsaya ganiba na nufo gareki ya uwar gijiyata”.
Ai mama Fulani bata tsaya bata amsaba ta figi alk’yabba ta saka tana fitowa, baiwarnan ta take mata baya.

A can kuwa Mai martaba da mamaki ya kalli Galadima, amma sai Galadima ya girgiza masa kai yana sake nuna masa cikin motar.
Matsawa mai martaba yayi sosai domin ganema idonsa abinda d’an d’an uwansa keson ya gani, Momma ta kunna fitilar dake motar dukda haske mai k’ayatarwa daya haske ko ina na masarautar.
Koda mai martaba ya lek’a saiyay baya a zabure, cikin rawar baki da nuna motar yace, “Sameer yaushe kuma ka fara shirya min wasa da hankali har irin haka?”.
“Ka gafarceni ranka ya dad’e, abinda kagani zahirin gaskiyane, wannan d’an uwankane ya dawo gareka cikin k’oshin lafiya da hukuntawar Ubangiji”. Galadima ya k’are maganar da rank’wafawa ya taimakama Abie ya fito, itama Momma ta fito.
Hakan sai yayi dai-dai da isowar mama Fulani wajan. Da fuskar Momma mai d’auke da k’asaitaccen murmushi tafara tozali, ta k’araso gabanta da sassarfa tana rik’o hanunta da fad’in “Zeenah!”.
A take Momma ta juya gareta, dan ko a mafarki bazata manta mai wannan muryarba, batareda tunanin komaiba ta rungumeta.
Yayinda shima takawa ya rungume Abie daga can.

Tun a wannan daren labari yafara karad’e masarautar, wasu kan basu aminceba kwata-kwata, burin kowa gari ya waye yayi kallon zahiri ba jita-jita ba.
Dole matar mai martaba ta koma sashenta, dan mai martaba yace Abie a sashensa zai kwana, jiyake idan ya barsa zuwa wani sashe tamkar da safe zai wayi gari yaga ba hakaba.
Itama Momma a sashen mama Fulani ta kwana tilas, yayi da mukuma muka nufi namu da yasha gyara ko ina yake need tamkar muna k’asar.

Yau dai kam na murzu wajen Galadima, acewarsa murnar sallah ce, dukda gajiyar tafiya darashin samun isashen barcin da muka tara a Saudia bai d’agan k’afaba, a cewarsa yamayi k’ok’ari, kwana nawa.

WASHE GARI

A Washe gari antashi da farin ciki guda biyu a masarautar gagara badau, Murnar Salla da dawowar Abie.
Dan zuwa safiya kam tabbataccen labari daga bakin sank’ira ya isa kunnen kowa, harma da k’yak’yk’yawan albishir na halattar sallar idi tareda Abie.
Kafin kace mi labari yafara fita wajen masarautar, su papi ma tun a Daren Galadima ya kirasu da wayar Sauban dake hannunsa.
Batareda sanin ya akayiba saiga magana tafara shiga kunnuwan jama’ar gari da y’an jarida, wasu gidajen TV Dana redio suka fara sanar da wannan zance dawasu ke k’arya tawa kansu tsaye…………….???

 

 

ALLAH ya gafartama iyayenmu??????
[7:09 PM, 8/21/2019] +234 813 508 4146: Typing??

 

??HASKE WRITERS ASSO….

?RAINA KAMA…!!?
(Kaga gayya)

Bilyn Abdull ce????
_______
Tawan miss xoxo tawa ni kad’ai, wannan gaisuwar takice ke kad’ai da babbar murya my dear, ALLAH ya bar mana zuminci mai d’orewa har Abadan, ke ta dabance a zuciyar bilyn Abdull, ina yinki irin Trillion’s d’innan wlhy, na gaisheki da gaba d’ayan ahalinki da tawagar y’an Group d’inki na HOME OF NOVELS baki d’ayansu, alkairin ALLAH yakai gareku har gadon barci My Hafsy????????????.

_________

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply