Hausa Novels Raina Kama Book 3 Hausa Novel

Raina Kama Book 3 Page 28


Raina Kama Book 3 Page 28
Viral

BOOK 3 ????2?8?

……………..Har yamma Galadima bai dawo gidanba, abincin ranama da aka ajiye masa sai d’aukeshi akayi, sainaji inajin tausayinsa, dan nasan yanacan ba zaune waje d’ayaba, yawan harkoki dayakeyi kansa kullum yake yawo tamkar wata motar haya, shidai kullum burinsa ya iya d’aukar nauyin ahalinsa, bai yarda zama rago ko jira daga waniba koda ace papi ne, ya yarda yasha wahalar nema amma ta gumin halak, sa6anin matasanmu da kullum burinsu nakan gwamnati ko alhajin anguwarsu ko d’an siyasa, ko alhajin da yafi kowa arzik’i a danginsu. Akwai wata kalma da Galadima yata6a fad’ama sauban Wanda akulum Na tunata tana k’ayatar dani. Lokacin inada tsohon cikinsu Amaturrahman, da yawan cin abincinnan Na masifa, aranar jikin Abie yad’an motsa, sai yakasance nikad’ai aka bari a gida sai hadiman gidan, cikin barci yunwa ta addabeni, hakan yasani farkawar dole Na sakko k’asa da k’yar, kitchen Na shiga nasami madara Na d’umama kafin kuku yad’an girkamin wani Abu, fitowata daga kitchen d’in keda wuya sai Galadima da Sauban suka shigo, da alama ya tuk’osane, dan idan yana cikin damuwar tashin ciwon Abie Momma hanashi driving takeyi. Da mamaki Sauban ya kalleni da cup a hannu yana fad’in “Yanzu nan Aunty duk hadiman gidannan saikin shiga kitchen da kanki a wannan halin? Aiko yau saisun gane kuransu”.
Ya tafi fuuuu cikin fushi saina dakatar dashi ina murmushi. Nace, “A’a Yaa Sauban, kabarsu please, nice ban sasunba nayi da kaina, amma aiga shican nasaka kuku wani aikin”.
Galadima dake zaune saman kujera ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya idonsa a lumshe tamkar baisan mi mukeyibama ya bud’e baki cikeda k’asaitar nan tasa yana fad’in, “Ai duk Wanda ya dogara da k’arfin wani to lallai nasa na cikin jerin k’arewa a sahun marasa amfani, dan zai dawwama cikin bibiyar samu daga waninsa shikuma bai amfanu datasa fik’irarba, kazama mai k’arfin zuciyar gina kai ba zaman jingina da bangon waniba”.
Yana gama fad’ar haka ya tashi ya haye sama, dagani har Sauban da kallo kawai muka bishi, kowa na fassara zancensa dalla-dalla, ni abinda na fahimta kai tsaye bada Sauban d’in yakeba, akwai abinda yafaru daga can inda suka fito, amma saiya za6i mu yamana sharhi bisa dalilin dashi yabarma kansa Sani. (ALLAH dai ya ganar da matasanmu domin tashi su nemi na Kansu ta hanya mai k’yau basu cigaba da dogaro a bangon wasuba.??????).

Tun d’azun yake tsaye akanta amma bata saniba, ta Lula duniyar tunani mai zurfi, ga Abdurrahman dake gefenta yanata mutsu-mutsu da k’ananun kuka amma batama jishiba.
Agabanta yay wani durk’uso mai birgewa, yakai fuskarsa daf da tata yana hura mata iska a saman ido zuwa hanci.
Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke tareda dawowa hayyacina cikin zabura, yay azamar damk’e hannuna da fad’in “My Mata!?”.
Ajiyar zuciya na sauke tareda dai-daita dan fahimtar shine, na zuba masa idanu cikin mamaki nace, “Yaushe ka shigo?”.
Murmusawa yayi sannan yamik’e daga durk’uson dayay agabana, batareda ya bani amsaba ya fara k’ok’arin cire farar rigar suit d’insa. Mik’ewa nayi na taimaka masa, sannan nadawo gabansa na warware tia.. ‘Din da bottoms d’in pink d’in rigarsa ta ciki. Sai wani faman lumshe idanu yake da bud’esu akaina, bansan miyake tunaniba.
Ina cire bottom d’in k’arshe na rigar ya rik’e hannuna, idanu na d’ago na kallesa, ya sakarmin wani k’asaitaccen murmushi yana matsoni jikinsa sosai, a saman la66a ya furta “Kinyi k’yau sosai, amma mikike tunani haka?”.
Da mamaki na kalli kaina, sanye nake doguwar rigar shadda milk color, anmata simple aiki da brown d’in zare, an k’awatashi da stones, Wanda sune suka fidda ainahin k’yawun d’inkin, sai siririyar sark’a data kwanta a wuyana d’as, nayi d’aurin Maryam babangida daya kuma fidda ainahin suffata ta bahaushiyar asali mai rik’o da al’ada. Yanda nake bin jikina da kallo haka Galadima kebi shima da idanunsa, na maida kallona ga face d’inshi dake kadaran kadahan, bai d’aureba kuma babu walwala sosai tare dashi.
Gira d’aya ya d’agemin sai kuma yad’an ta6e baki yanajan hancina da had’e yatsunsa biyu na k’arshe????alamar komai yaji.
Nad’an murmusa ina k’ok’arin barin wajen dan naga alamar miskilawan suna kusa.
Ruwa naje na had’a masa, na fito ina goge hannuna da towel.
Durk’ushe na iskeshi gaban Abdurraheem da cup d’in ruwan dana ajiye danshi a hannunsa. Ya d’ago yana kallona dad’an murmushi a face d’insa, “kinsan minake gani a jikin Abdurraheem kuwa?”.
Kaina na girgiza masa alamar a’a.
Kallonsa ya maida ga yaran yana cigaba da murmushinsa. Yace, “Kamannin Abie”.
Takowa nayi Inda suke Nima Ina murmushi mai sauti da fad’in, “Nadad’e da wannan tunanin a raina, saidai nabarma zuciyatane har sai randa zan gansu a waje d’aya, Ashe kaima kana lura?”.
Wata y’ar dariya yayi, wadda tafi kud’i tsada awajensa. Yace, “My Heartbeat ALLAH kin iya haihuwa”.
Ba k’aramar dariya maganarsa tabaniba, aiko nashiga k’yalk’yalawa. Shiko ya shagala da kallonta saboda birgeshi da dariyar tata tayi, burinsa dama yaganta cikin farinciki.
Bayan na tsagaita da dariyar na kallesa Ina d’aga kai da kashe masa ido alamar kallonfa?.
Mik’ewa yay tsaye ya dawo inda nake tareda rank’wafowa kaina yana dafa hannayensa biyu asaman gadon gefe da gefena. Kusancin namu yasakani d’anyin baya kad’an ina kallon cikin idonsa, yakuma matsowa, na matsa, yakuma again, Nina still na matsa, saida na haye gadon sosai shima yay balance yanda yake buk’ata sannan ya kwanto gefena kusan Rabin jikinsa a nawa, har lokacin idonsa na sark’e da nawa. Galadima yay bala’in Sanin sirrin kallo, inhar ya sark’e idanunsa da nawa duk wani hope d’ina nemansa nakeyi na rasa, yatsansa kawai naji saman la66ana yana zagayawa ahankali, santsin hannunsa Dana lips gloss d’in Dana sanya sunayin kamar susa, kasa jurewa nayi na lumshe idanuna a hankali.
Galadima ya murmusa da bud’e baki da k’yar yana fad’in, “Kin cancanta, kin cancanta zama matar Muhammad Sameer Munaya, ked’inki da dukkan halayyarki irinta Muhammad Sameer ke buk’ata ga matarsa, ko ayarda ko kar ayarda nasan nama sauran maza zarra, dan matata tafi ta kowa, kinzama fitila mai hake gabana da bayana, kinzamarmin bango abin jingina lokacin danawa yanemi rushewa, shigowarki rayuwata na dai-dai da farkawata daga nannauyan barci mai cikeda rud’ani, nabaki dukkan zuciyata ki jani a sannu danna cigaba da ribantuwa da ni’imomin da ALLAH ya azurtaki dasu, I love you so much Munaya, I love you har a aljanna matsayin uwargidan matana”.
Bansan lokacinda hawayen farinciki suka fara zirarominba, na bud’e idanuna dakai hannu saman kwantaccen sajensa ina shafawa a hankali, cikin wani yanayi nace, “Ka cancanci fiye da haka mijina, dan kanada zinariyar zuciya, kaimai tarin tsoron ALLAH ne dabin dokokinsa, a wannan zamanin samin matashin saurayi mai kud’ad’e da mulki a hannunsa dabaya wata masha’a abune mai wahala, baka kasance mazinaci ba, baka kasance mai shaye-shaye ba, ko sigari wannan bakasha, kulum cikin Neman halalinka kake Dason k’yautatama iyayenka dana k’asa da kai, kaimai ibadane, salla bata wuceka, mai yawan tsayuwar dare, mai yawan bitar littafi mai girma dake d’auke da zancen ALLAH ne, mai yawan sadaka da taimakon mutanen da bakuma had’a addiniba, bakada wata majalissa ta abokai daza’ace gaka cikin jerin masu cin naman wani ko zind’en wani, abinda ke gabanka da Wanda ALLAH ya halatta maka kawai kakeyi, mijina tayaya bazaka samu nasaroriba a rayuwarka? Ubangiji mai ni’imane ga dukkan Wanda ya ra6u samun ni’imar, babu wani Bawa dazai tsinci kansa a ta6ewa inhar yabi dokokin Ubangiji da koyi da manzon tsira, babu cuta mafi rad’ad’i da ciwo kamar bijirema Umarnin ALLAH Wanda ayanzu shike wahal da matasan duniya irinka, burunsu kawai su hole su mori k’uruciyarsu, sun manta babu tagomashi mafi k’yak’yk’yawan farashi irin morar k’uruciya bisa ga Umarnin ALLAH, yadda da k’addara, samu ko rashi, tsayawa matsayin da ALLAH ya ajiyeka, kaucema dukkan wata bad’ala, matasa sune k’ashin bayan al’umma, lalacewarmu ta saka al’ummar tafiya a karkace a halin yanzu, da’ace zamu gyara da kowa ya mik’e, dolene Momma da Abie suyi alfaharin samun d’a irinka, dolene Aunty Mimi da Yaa Sauban suyi alfaharin samun d’an uwa irinka, dolene su Samha dasu Amaturrahman suyi alfaharin samun Uba irinka, dolene k’asarka da addininka yayi alfaharin samunka, saidai duk nice nafisu sa’a da alfaharin samunka a matsayin miji uban y’ay’ana, inaji inama y’ay’yana su gaji k’yawawan hallaya da d’abi’u irinna mahaifinsu, saidai kash ina cike da fargabar tsoron kalmarnan ta bahaushe dakance Bakowanne tauntsu bane ke raira kukan gidansu wani tun a koyan tashi yake canja salo. Mijina ka more, ka matuk’ar morewa da k’yawawan hallaya, irinku kunada tsadar samu a cikin al’umma, da mutane zasu gane dasun fuskanci ba k’yawun fuska dana jiki bane abin alfahari, zinariyar zuciya da hallaya shine abin alfahari da d’agawa, saidai kash, burin samarin yanzu da y’ammata k’yawun fuska dana halitta, nauyin aljihun wayewa, basa tunanin mika tara mizaka taras, sannan mika barma bayanka da ahalinka Wanda ko bayan shekaru aru-aru tarihi bai Isa mantawa da kai ba, da inada dama sainabi matasan mata da maza dukna musu allura sunzama kamarka mijina, inasonka, ina sonka, zan fad’a a hankali, nafad’a da k’arfi, na fad’a da kuwwa, na fad’a da ihu agaban kowa kuma, Kaine duniyar Munaya, Kaine farincikin Munaya, zanta k’aunarka har randa nufashina zaibar gangar jikina, nakumayi fatan ganina a cikin matanka dake aljanna Muhammad Sameer”.
Kasa magana Galadima yayi, sai bakinsa ke motsi alamar buk’ar firta wani Abu amma yakasa, idonsa yacika taf da kwalla, lallai hikimar zancema baiwace ga mace tagari, dashi kawai zata iya mallakar mijita babu boka babu Malam, dan gashi Munaya tasamu dukkan nasarori, ya rungumeni tsam a jikinsa tareda d’ora bakinsa saman la66ana, hawayen dayake rik’ewa suka gangaro saman fuskata. Banyi yunk’urin ko motsawa ba nabashi wuk’a da nama yayi yanda yakeso ni halalinsace……….??????

 

Hummmm, lallai matar kwarai rabin addini, ya ALLAH kabamu damar zama matan kwarai ga mazajenmu??????.

***

Bayan shud’ewar wani lokaci muka dawo daga duniyar da muka tafi, kunya duk sai ta kamani, nakasa had’a ido dashi.
Galadima ya murmusa yana kama hannuna zuwa hanyar bayi, banida za6in daya wuce na bisa kawai. Yauma dai tare mukayi wankan, nad’an sake dashi fiyeda d’azun da safe. Muka fito na taimaka masa da shafa mai, yasaka kaya marasa nauyi. Nima da taimakonsa na kimtsa sannan na sauka nemo masa abinda zaici dukda magrib ta gabato. Babu kowa a falon sai Khaleel dake homework. Sannu namasa shikuma ya gaisheni, nace, “Ina Samha my boy?”.
Yace, “Aunty yanzu aunty Dhibiya tazo suka fita”.
Agogon falon na kalla da mamakin fita a yanzun? Halan batasan Uncle d’inta ya dawoba?.
Bance komaiba na wuce kitchen.
Da taimakon kuku na shirya masa Abu mara nauyi, na had’o saman tire ina fitowa. Samha data shigo tad’an kalleni a firgice, nima kallon mamaki nake mata da tuhuma.
Nace, “Daga ina haka?”.
Kame-kame tafara na lalubo amsar dazata bani, wadda alamunta ke nuna k’aryace kawai zata fad’a.
Girgiza kai nayi kawai nai gaba abina ina fad’in “Zanso sanin mike tsakaninki da Dhibya Samha? wannan abotar taku k’arfinta yafara tsoratani”.
Banjira amsarta ba na haye saman benen.
Gudun karya fahimci wani Abu na daidaita kaina tunkan na shiga, nasan inhar yasan raina ya6aci akan Samha ne sai taci k’aniyarta, nikam ba buk’atata ba kenan, nafison sanin tsakaninsu da k’awartata kafin na rabasu.
Tsaye na iskeshi rik’e da abin salla, na ajiye tiren saman table d’in gaban sofa sannan na kalli agogo. Yanda banyi magana ba shima baiyiba, na nufi bayi nayo alwala nima, tsaye na kuma iskeshi yana jirana.

Bayan mun idar da sallah na kallesa ina fad’in “Abinci yalla6ai”.
Harara ya zubamin da rankwashi, na dafe wajen ina kwa6e fuska zanyi kuka.
Yace, “Yalla6ai d’inan bazai bar bakinkiba ko?”.
Dariya namasa da gwalo inaja baya, “Yo ba sunanka baneba”.
“Da kika rad’amin ko? Zan kamakine ai”.
Sanin halinsa yasani fad’in, “Toyi hak’uri bazan sakeba”.
“Harkin karaya kenan?”.
“Ba doleba, kamun nakane ai bamai sauk’iba”.
Dariya sosai tabashi, amma ya had’iye abunsa kawai yayi murmushi yana cizar lips.
Munaya tace, “Wato a rayuwa duk d’an Adam zaka sameshi dawata d’abi’a data zame masa jiki”.
Kallona yayi da alamar tambaya, amma baice komaiba.
Mik’ewa nayi tsaye ina cire hijjab da fad’in, “Cizon lips yazama maka jiki, harya zama d’abi’ar dake yawan birgeni agareka”.
Lips d’in nasa ya ciza sannan ya saki wani k’asaitaccen murmushi da girgiza kai, Munaya kenan sarkin k’uruciya. Yafad’a a zuciyarsa yana mik’ewa shima.

Saman sofa ya zauna yana d’aukar system ya d’ora a cinyarsa, ganin haka saina sauke tiren Dana ajiye a saman table na tura masa gabansa, nasansa akwai son d’ora k’afa, abinka da jinin mulki.
Aiko saiya maida k’afafunsa duk biyu akai yana fad’in “thanks”.
Bance komaiba sai murmushi dana d’anyi, na zuba abincin ina zama kusa dashi, tunda ya d’auki lap-top d’inan hanyar zamewa cin abincin yake Neman k’irk’ira, kuma saiya cishi.
Nace, “to yanzu ya za’ayi? Ga abinci”.
Batareda ya kalleniba yace, “Kici da nawa kawai ya wadatar”.
Ni dariyama ya bani, amma na daure banyiba, “Nikam ina mamakin yanda kake k’in abinci saikace wani Khaleel”.
Murmusawa yayi hankalinsa nakan aikinsa. Yace, bazaki ganebane, nifa wlhy abinci takuramin yakeyi, shiyyasa ko sau d’aya nacisa a rana ya watar dani”.
Nace, “Nikam dai ban wadatuba, bud’e baki wannan bashida nauyi, nasandai gudun k’aton ciki kake kawai”.
Dariya ya sanya kawai.
Nima nad’an dara ina kai abincin bakinsa.
ALLAH yanzu saikaga mutun nata hora kansa da yunwa wai karyayi k’iba, shikuma ALLAH ba ruwansa, idan haka yayoka ko ruwane kawai abincinka sai kayita”.
Abincin ya shiga taunawa da murmushi saman fuskarsa hankalinsa nakan system d’in.

Haka nacigaba da bashi abincin da janye hankalinsa da hira, yayinda yake aikinsa da saurarena, idan na murmushine ya murmusa, Wanda zaiyi magana ya amsamin a tak’aice, Wanda tuni na fahimci al’adarsace tak’aita magana yabaka a dunk’ule kawai ka fassara sauran.
‘Dagowa yay fuska a marairaice, “My mata ki tausayamin hakanan cikina karya fashe”.
Dariya nayi da nuna masa plate d’in daya koma empty.
Ya waro idonsa waje yana shafa ciki, “Dan ALLAH da gaske kike dukni na cinye?”.
Nakuma tuntsurewa da dariyar danake dannewa, “Yo dawa kukaci? Wlhy duk kai kacinye harma d’an k’arawa nayi”.
“Chiii yarinyarnan kin gama dani, amma gama dariyar muguntar ai kanki zata k’are wlhy, ke zakiji nak’ara miki nauyi”.
Dukda na fahimci inda ya dosa saina shareshi ina cigaba da dariyata, nama mik’e daga kusa dashi.
“Humyim zaki gane kuranki ne”.
Yay maganar yana cije lips.

Da lokacin isha’i ma yayi shine ya jamana jam’i, ya kuma komawa kan aikinsa, ganin aikin ya d’auke dukkan hankalinsa saina d’auka wayarsa Na kira su Zuhuriyya y’an Niger, muka gaisa dad’an ta6a hirar zuminci cikeda nishad’i. Sannan Na kira aunty Salamah itama nasha labari.
Ganin harna gama wayoyina yana aikin still saina d’auka Novel d’insa d’aya nai zaman karatu.
Sai wajen 10 ya dafe kai yana sauke ajiyar zuciya.
Kallonsa nayi da tausayawa. Nace, “Ka huta haka nan mana my king”.
Huci yakuma furzarwa yana k’aramin tsaki, ya taso daga gaban tebir d’in ya dawo bakin gadon ya zauna.
Hannunsa Na kamo, Na kwanto kansa bisa cinyata inad’an shata goshinsa, idonsa a lumshe yace, “wlhy sonake naga na had’a kud’in jirgi da abubuwan buk’atar mu idan zamu wuce Nigeria, Dan Dr Erfan Fahad yamin albishir da k’arshen watannan insha ALLAH zai sallami Abie, gashi ina cikin matsalar kud’i Munaya, narasa yanda zanyi, bazai yuwu Na kwashe kud’in kasuwa Na narkarba kuma”.
Ajiyar zuciya Nima nayi cikin damuwa, ganin ya bud’e idonsa saina murmusa ina d’an matsa masa kafad’unsa. Nace “ga shawara to”.
“Ina saurarenki”. Yafad’a cikin maida hankali gareni tareda hard’e hannayensa a k’irji.
Yatsana d’aya Na d’ora saman girarsa ina kwantar da gashin a hankali, “My King mizai hana gifts d’in dana samu Na aure da haihuwar yarannan kayi amfani da kud’ad’en ciki, abinda ya kasance Na kud’i a siyar dashi Dan banga amfanin ajiyesuba ai”.
‘Dan Murmushin gefen baki yayi yana lumshe ido, sannan ya bud’e a kaina, “Munaya duk abinda aka baki ko yarana halalinkine, idan Na kar6a nazama mai handama kenan, ta wani faninma zaluncine, nine yakamata Na baki domin sauke wasu nauye-nauyenki Na y’an uwa da makamantansu, saikuma Na amsa Dan nine baba rodo sarkin babakere”.
Na 6ata fuska ina janye hannuna daga saman girarsa dukda dariyar da furucinsa Na k’arshe ya bani, “Shikenan tunda baka d’aukeni yanda Na d’aukeka ba, yanzu tsakani da ALLAH idan kabarni dasu mizanyi dasud’in? Ashe abuna ba naka baneba?”. Nai maganar cikin matso hawaye.
Da Sauri ya tashai zaune yana rik’oni amma saina kwace ina niyyar sauka ma gaba d’aya daga gadon. Gaba d’aya yasani a jikinsa yana fad’in, “Sorry tsaya muyi magana to kinji my sweetness, ya kikeso ayi yanzun?”.
Hawayen nakuma sharewa nace, “Ka kar6a kawai”.
Shiru yay yana kallona da nazarin maganar, saikuma yad’an numfasa yana gyara zama. Yace, “to ai naga suna Nigeria? ”.
“A’a suna nan, Dan dukna had’osu Na taho dasu wannan karon”.
“Ok babu damuwa, da safe zamuyi magana, shirya yara nakaisu wajen Momma dare nayi nafara jin barci”.
Naji dad’i daya amince zai kar6a, Dan haka Na rungumeshi ina dariya.
Bayana yad’an bubbuga kawai yana cewa “jeki shiryasu”.
‘Dagowa nayi ina kallonsa, “Amma my King zamuke takura mata itama ai, ka barsu kawai”.
“Babu wani takurawa, bazaki gane bane y’ammatana”.
Babu yanda Na iya, dan babu jayayya a tsakaninmu, shiryasu nayi Na shayar dasu kowanne yay d’if, ya d’auka biyu yakai yadawo ya d’auki d’ayan shima. Nikamdai wannan Abu ya girmeni, amma babu damar magana.

Ya dawo yana dariya da bani labarin gargad’in da momma tamasa akan wlhy mu tashi da wuri, kokuma da anyi sallar asuba yazo ya d’aukesu, Dan bazai yuwu ake barinsu da yunwaba.
Sai Na k’arajin duk kunya ta lullu6eni, amma shi ko’a kwalar rigarsa, saima wata tashar daya kamo.

A gurguje please??.

 

********

Washe gari ya koma Kashmir, yaso mu tafi tare amma Na nuna masa Momma yakamata ta fara zuwa, Dan tunda aka kai Abie babu Wanda yaje saishi kad’ai.
Daga baya dai sai muka tsaida shawara akan zaije yafara ganin halin da ake ciki a yanzu, da wannan shawarar yatafi.
Ba k’aramin abin mamaki Dr Erfan ya shiryama Galadima ba, shiyyasa gaba d’aya ya hanashi ganin Abie.
Da yamma lik’is Galadima ya isa Kashmir, saboda bai tafi da wuriba, kai tsaye asibiti ya nufa dukda yana tunanin mawuyacine ya samu Dr Erfan Fahad a can, saboda lokacin tashinsa aiki yayi, saidai idan wani muhimmin aiki ya tsaidashi ko Emergency ya riskeshi.
Ilai kuwa a harabar asibitin Galadima yaci karo da Dr Erfan Fahad ya fito zai wuce gida, sosai Dr Erfan Fahad yay mamakin ganin Galadima, Dan basuyi waya yana hanyaba. Ya bashi hannu sukayi musabaha da rungume juna, “wai my friend dama kana hanya?”.
Galadima ya murmusa da shafa kansa, “Kabari kawai, ya aikin?”.
“Alhmdllh”.
“To inaga kawai muwuce gida. Dan wlhy nagaji sosai, yau nayi aikin daya wuce kima”.
Galadima yay d’an jim alamar tunani.
Murmushi Dr Erfan Fahad yayi yana dafa kafad’ar Galadima, “Sameer nasan kana tsananin buk’atar son ganin Abie ko? Karka damu, kaidai muje gida kawai abokina”.
Galadima baice komaiba ya bisa suka wuce, Dr Erfan Fahad nata jansa da hira, amma shi iyakarsa murmushi ko eh da a’a.
Ko kad’an Dr Erfan Fahad bai damuba, danya fahimci halin Galadima Na rashin son hayaniya tsaf, dama tun a baya bashida yawan magana, Ashe halin Na nan bai canjaba, saima k’aruwa dayay.
Shikam Dr Erfan Fahad mutum ne faran-faran, ko jama’ar dake jiyya namasa wannan shaidar ta yawan tsokana.
Ahaka dai suka isa gida, shidai Dr Erfan Fahad yanata murmushinsa.
A k’ofar falo ya tsaida Galadima, tareda fidda handkerchief a aljihunsa yace Galadima ya rufe idonsa.
Da mamaki Galadima ke kallonsa, amma yagaza furta komai.
Dr Erfan Fahad ya jinjina masa kai da had’e hannayensa alamar rok’o.
Ruf Galadima ya rife idonsa, Dr Erfan Fahad ya saka handkerchief d’insa ya d’aure masa ido, sannan ya kama hannunsa suka shiga ciki.
A tsakkiyar falon ya tsaidashi, ahankali yace, “my friend are you ready?”.
Cikin sauke numfashi Galadima ya d’aga masa kai.
Dr Erfan Fahad ya murmusa yana kwance masa handkerchief d’in sannan yace, “Bud’e idonka”.
A hankali Galadima ya shiga bud’e idanu, harya bud’esu gaba d’aya akan k’yak’yk’yawan dattijo zaune bisa kujera, fuskarsa ta k’awatu da murmushi, yasha gyaran fuska mai k’ayatarwa, sai gashi kad’an mai adon furfura da aka bari ya zagaye fuskarsa.
Wata zabura Galadima yay mai kama da firgita, Dr Erfan Fahad yay saurin tarosa, Dan kad’an yarage ya zube a k’asa.
Cikin rawar baki data jiki yake kallon dattijon, dak’yar ya iya fusgo numfashi da magana mai cike da in’ina daga bakinsa “A..b..ie k..ai.ne?”.
Abie ya share hawayen da shima suke ziraro masa, cikin tsantsar so da k’aunar d’an nasa yabashi amsa da fad’in “Tabbas nine Muhammad Sameer sanyin idaniya, Abie d’inka ne zaune yau agabanka, Wanda ya tashi cike da hukuncin Ubangiji gagara misali”.
Galadima ya maida kallonsa ga Dr Erfan Fahad.
Murmushi Dr Erfan Fahad yayi, “Karkayi kokwanto da ikon ALLAH Sameer, shike kwantar da Wanda yaso, Yakuma tasheshi a lokacin da yaso, dama ba’a yankema rayuwa hukunci, mai jiyya saiyayi rayuwa mai tsayi amma mai lafiya a wayi gari yazama gawa, ciwo bashi bane mutuwa, kwanaki 10 kacal Na d’auka ina treatment d’in Abie ga66ansa suka fara aiki, a sauran sati uku danayi tare dashi muna koya masa yanda zaiyi tafiyane, da zama, d’aukar Abu, da sauransu, Dan duk ga66ansa sun manta, kamar yanda ka sanarmin addu’ar da kukaita masa lallai itace babban magani daya zama mai tasiri a garesa, domin nikam abinda ba’a rasaba Na k’arasa, duk Wanda yabar addu’a lallai dole matsala tazama ma’abociyar rayuwarsa, a yanzu haka ina mai tabbatar maka Abie zai iya tafiya dayima kansa wasu abubuwa, amma bamasu yawaba, tafiyarma bamai tsaho ba, Dan yawanyin ne zai bama ga66ansa kwari da sabo, shekara 26 mutun Na kwance sai na’urori ke sarrafashi ba k’aramin Abu bane Sameer, Dan dolene akira Abie d’an baiwa, masu irin nasarorinsa kad’anne a cikin al’umma wlhy, kaje ga Abie, domin kuna buk’atar juna”.
Tamkar Dr Erfan Fahad yama Galadima allura ne, cikeda sasaarfa ya k’arasa ga Abie, a gabansa ya zube yana sakin wani kuka maiban tausayi tamkar mace”.
Abie ya sakko daga kujerar ya rungume jarumin d’ansa shima yana hawaye, sun dad’e a haka, jisuke tamkar karsu saki juna, a tunaninsu Kodai mafarki sukeyi, suna tsoron rabuwa su farka suga ba haka baneba.
Shi kansa Dr Erfan Fahad hawayen tausayinsu yake sharewa.

Ni kaina masu karatu wannan lamari yasani hawaye Na gaske??, da zaka k’iyasta hakan a kanka wane farinciki kake hangowa yayinda waraka ta riskeka?.??

Wad’annan bayin ALLAH yau lallai suna cikin tsantsar farin ciki, ko kad’an Galadima ya kasa gusawa daga jikin Abie, Yakuma k’i kiran kowa, burinsa shima yabasu mamaki tamkar yanda Dr Erfan Fahad yabashi. A yau yay niyyar su juya amma Dr Erfan Fahad ya hana hakan saidai gobe, Dan dare yayi kam a yau.
A gado d’aya Galadima da Abie suka kwana, dukda sunma cinye rabin daren da fira??.

****

Hankalin Munaya duk a tashe yake, saboda tanata kiran Galadima yak’iyin picking, tun tana daurewa harta gaza tafara kuka da shiga tsantsar tashin hankali.
Momma Ce ta lura da canjawarta, ta tambayeta lafiya?.
Kasa magana tayi saboda kunya, saida Momma ta kuma maimaitawa sannan tace, “Momma inata kiran Number Abbansu ne yak’i yin picking tun d’azun”.
Ita kanta Momma ta kirashi baiyi picking ba, amma ta d’auka ko wani uzirine yasha kansa, sai yanzumefa hankalinta ya fara tashi itama, waya ta d’auka tashiga kiransa amma babu amsa, kusan kira 10. Cikin firgici ta kalli Munaya da aunty Mimi da itama take kan gwada kiran nasa, amma itama ba’ayi picking.
“Kinga Munaya tura masa massage mu gani”.
Jiki a sanyaye Munaya ta tura massege, amma kusan 30minutes babu reply.
Hankalinsu fa yakai k’ololuwar tashi, amma sun rasa mafita.

***

Shikam Galadima baima San sunaiba, wayarma kanta baisan inane ya jefar da itaba, gabaki d’aya hankalinsa ya tattarane ga Abie, harkuma suka kwanta barci bai nemi wayarba.

*****

Yau kam inhar wani yay barci a cikinsu to bana kwanciyar hankali baneba, dan kowa damuwa tamasa katutu, dai-dai da Hadiman gidan suma duk a damuwa suke, sai dai tamkar yanda suka saba yauma sun mik’a lamarinsu ga Ubangijin talikai.

Washe gari

Tunda safe Momma ta nemi Number Dr Akash da Dr Ajey akan rashin jin Galadima, duk sun amsa mata da zasu bincika.

Can kuma su Galadima sun wayi garine da shirin dawowa New Dhalhi, cikin tsantsar farin ciki irin Wanda misaltashi ma 6ata lokacine……………..???

 

 

 

ALLAH ya gafartama iyayenmu??????
[7:09 PM, 8/21/2019] +234 813 508 4146: Typing??

https://2gnblog.blogspot.com/

??HASKE WRITERS ASSO….

?RAINA KAMA…!!?
(Kaga gayya)

Bilyn Abdull ce????

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply