Hausa Novels Raina Kama Book 3 Hausa Novel

Raina Kama Book 3 Page 27


Raina Kama Book 3 Page 27
Viral

BOOK 3 ????2?7?

………………..Koda muka fito daga d’akin momma tamkar kwai ya fashemin a ciki haka nake tafiya, yana gaba ina binsa a baya, yayinda yafara taka steps d’in saiya juyo yad’an kalleni, k’asa nayi da kaina, yayi wani miskilin murmushi mai cike da ma’anoni, oho bansan yanaiba.
A step d’in k’arshe ya tsaya yana nunamin hanya wai Na wuce, ra6awa nayi ta gefensa na shige, yanzu kam ina a gaba yana bina a baya buka shiga bedroom d’in, yana nan yanda Na sanshi cikin k’amshi da tsafta, Na zauna a saman sofa ina sauke numfashi.
Tsaye yay kawai yana kallona, nikuma nakasa d’aga nawa idon Na kallesa, saima naji Na takura kallon dayakemin d’in. Kusan mintuna biyu sannan ya zauna a teble d’in dake gaban sofa d’in, ya kamo hannayena danake wasa da gefen siririn gyalen kaina. Cikin wata tattausar muryarsa mai cikeda nutsuwa da tarin k’asaita yace, “My Mata”.
Kasa d’ago idanu nayi Na kallesa, saida Na amsa a sanyaye.
Yad’an murmusa tareda saka hannunsa a ha6ata ya d’ago face d’ina. Kallo d’aya namasa Na risinar da idanuna, murmushi yayi mai sauti, yakuma sanyaya murya tamkar mai rad’a yana fad’in “Kin huce?”.
Kamar bazance komaiba dai saina d’aga masa kai siraren hawaye na ziraromin a kumatu.
Baice komaiba sai zubamin ido da yayi kusan seconds 30, ya sauke 6oyayyar ajiyar zuciya yana saka hannayensa biyu ya tallafe fuskata a cikin tafin hannun, ya gogemin hawayen da babban d’anyatsansa guda biyu.
“A d’an kalleni mana my Queen, a kuma min murmushi ko kad’an na tabbabatar an huce d’in”. Yay maganar yana Raba idanu akan fuskarta.
Yanda ya marairaice sai bansan lokacin da murmuahin ya kufceminba ma.
Shima murmusawa yayi da d’an jan hancina, “Haba kokefa my heartbeat”.
Hannu na saka na kare fuskata saboda naji kunya.
Yawani lumshe idanu da sakin murmushin gefen baki, tareda maida kallonsa ga k’aramin agogon dake bisa dirowan gefen gadon. Time yaja Sosa, kallonsa ya maida ga Munaya data kasa kallonsa. “tashi kiyi shirin barci mu kwanta, ga dare na Neman rabawa”.
Kallonsa nad’an sata ina janye idona. Nace, “To yaranfa?”.
Bai amsaminba saida ya mik’e tsaye, “karki wani damu kanki, tunda kikaga Momma bata bamuba aikinsan ranar ta musamman Ce yau”.
Ban sake maganaba danjin ya kamo wata tashar, na mik’e tsaye zuwa wardrobe na d’auka kayan barci.
Duk abinda take idonsa a kanta, yana zaune a bakin gado yana binta da kallo.
Ina juyowa muka had’a ido, nai azamar janye nawa, shikuma ya jehomin tambaya.
“Wad’annan kayanfa?”.
Kallon kayan nayi sannan Na kallesa da mamakin tambayar tasa, idonsa a kaina Dan haka Na janye nawa.
Nace, “Zan sakane”.
Baicemin k’alaba, sai mik’ewa da yay ya tako gareni cikeda izza da k’asaita, saina samu kaina da fad’uwar gaba, jinake tamkar nama zura da gudu. Kayan ya kar6a yana matsowa jikina, nad’anja baya amma saiya taro k’uguna da hannunsa yana kallon fuskata, cikin magana rad’a-rad’a daf da fuskata yace, “basu nake buk’atar ki sakaba yau, ke kad’anki nakeson gani babu wani shamaki a tsakaninmu”.
Da mamaki na kallesa saiya d’agamin gira, nai azamar janye idona ina marairaice fuska. “ALLAH nidai bazan iyaba yalla6ai”.
Kuma rank’wafowa yay kaina yana fad’in “Zaki iya my Queen, inhar da gaske kina son farin cikin mijinki, ni haka nake buk’atar ganin matata aduk lokacin kwanciya barci, ni kad’aina na isheki riga da bargo OK?”.
Yanda ya k’are maganar saida tsigar jikina ta tashi, babu shiri na d’aga masa kai alamar amsawa, dan inhar nabari muka cigaba da kasancewa a haka wlhy za’a iya samun matsala.
Harna fara tafiya ya rik’o hannuna, cak na tsaya batareda na juyoba. Yace, “nazo na tayaki wankan?”.
Ai babu shiri na juyo ina kallonsa cikin waro idanu, saiya kashemin ido d’aya yana cizon lips. Zare hannuna nayi nai gaba da hanzari, saida naga na rufe k’ofar bayin na jingina sannan na sauke ajiyar zuciya, lallai naga takaina da Galadima, dama haka yake? Sumi-sumi dashi, idan ka gansa saika d’auka bazai iya ko kallon macenba, amma humm.

Shima tana shigewa ya murmusa yana shafa sajensa zuwa gemu, takawa yay zuwa gaban gadon ya zauna, zuciyarsa na kuma tsunduma a k’aunar matarsa da ayyukanta, waya ya d’auka yana danne-danne, kusan wasu mintuna sannan ya mik’e yana ajiye wayar, kayan jikinsa ya cire, dagashi sai boxer ya haye gadon tareda jan bargo ya lullu6e jikinsa yana kwanciya, luf yayi tamkar mai barci.

Sosai na nutsu na gyara kowane lungu da sak’o na jikina, nasha turarrurukansa dake bathroom d’in, kunyar fita nakeyi da towel wlhy, Dan haka naja rigar wankansa na saka, ahankali na bud’e k’ofar, saida na fara lek’a kaina na hangoshi kwance akan gado da alama ma yayi barci. Ajiyar zuciya na sauke kafin na ida fita cikin sand’a.
Duk abinda takeyi Galadima na kallonta, ya had’iye dariyar dake taso masa da k’yar yana kuma yin luf.
Cikin tafiyar sand’ar tazo har gaban madubi, bai motsaba harta gama shafe-shafen turarenta da lips gloss, ta tako a hankali gaban gadon zata d’auke wayarsa data kusa fad’owa k’asa, wadda ya ajiye dama matsayin tarko, yasan inhar tagani bazata wuce ta bartaba saitayi yunk’urin d’aukewa.
Caraf kuwa ya damk’e hannunta, gabanane ya fad’i, ina k’ok’arin ja da baya ya kamo igiyar rigar wankan danaima d’aurin zarge, aikam lokaci d’aya ta warware, nai saurin rik’ewa Dan karta bud’e, amma ina saiya jawo igiyar ya fisgoni na fad’o jikinsa, bargon ya d’aga ya turani ciki yana murmushi mai sauti.
Ya zare wayarsa dake cikin hannuna yana fad’in, “Dukfa wayon amarya…..”
Shiru nayi nakasa magana danni tsoronsa ma kuma mamayeni yakeyi, ban ankaraba naji yana zare bathrobo d’in.
Cikin marairaicewa nace, “please yalla6ai kayi hak’uri kabarni da rigarnan akwai sanyi fa……”
Yatsansa d’aya ya d’ora saman la66ana, yaymin alamar nayi shiru, banida za6in daya wuce bin umarninsa.
Yace, “Nifa ba komai zanyiba, bashina da akaci za’a biyani, sanyi kuma nine bargonki ai”.
“Ni yaushe naci bashinka?”. Nai maganar a raunane”.
“Uhyim, in maye yaci ya manta ai maid’a baya mantawa, kedai kawai ki mik’a wuya, wahalar da aka bani yau duk saina fanshe kayana”.
Maganar danayi yunk’urinyi bansami lasisin kammalata ba ai, sai a cikin b…..??

(??ba ruwana nayi nan?????).

 

********

Yaudai kam Na tabbatar nashiga hannun manya, babu ga6ata da bata ciwo, nayi ligif saboda jikagata, baiyi k’aryaba kam, ya fanshe haushinsa harda gyara, da asubahi saida taimakon ruwan zafi nasami k’arfin jikina, Dan saida nagasa jikin, ga6o6ina suka d’an mik’e, bai fita masallaci ba, shiya jamu jam’i.
Sosai barci ya d’inga cin idanuna, muna idar da sallar Na zame a wajen Na kwanta, baice dani komaiba, saima Qur’an daya d’auka yafara karatu cikeda nutsuwa da kwarewa, tun ina saurarensa sama-sama har barci mai nauyi yay a won gaba dani.

Bai dad’e yana karatunba ya ajiye Qur’an d’in, Dan shima barcinne taf idonsa, kallon Munaya dake k’udundune cikin hijjaf yayi, yad’an murmusa yana shafa fuskarta, shikansa yasan jiya ya wahal da ita, amma soyayyartace duk ta jawo hakan, ya duk’a yana sumbatar goshinta da kumatunta, mik’ewa yay ya cire jallabiyar jikinsa sannan ya dawo inda take, itama cikin dabara ya cire mata hijjab d’in sannan ya d’auketa cak zuwa gadon.
Tad’an bud’e ido ta kallesa ta maida ta lumshe. Murmushi yay da sake sumbatar la66anta sanan yaja musu bargo, ya rungume yalla6iyarsa suka sake komawa duniyar barci.??????

 

?????

Tun Momma Na zuba idon sakkowarsu har abin yafara bata mamaki, gasu Abdurrahman sun farka tun d’azun, sai faman banka musu ruwan zam-zam mai had’eda Zuma take dasunyi kuka, da alama yunwa sukeji, amma takula iyayen nasuma sun manta dasu.
Aunty Mimi dai nata k’umshe dariya, har sukayi breakfast babu su munaya babu labarinsu, yaranma sun kuma komawa barcin dole.

Barcin yaran baiyi wani nisaba suka kuma farkawa da kuka, Dan yunwa ta hanasu barcinma.
Momma tace Samha tahau saman taga idan sun tashi.
Da to ta amsa tana hawa saman. Amma saita iske ko ina tsitt, babu alamar motsin mutum. Dawowa tayi ta sanarma Momma basu tashiba, ga Abdurraheem harwata shid’ewa yake saboda kuka, shi dama baida jimirin yunwa, sauran y’an uwansa sunfiahi hak’iri, ga matsalar ciwonsa da ba’aso ya yawaita kuka.
Babu shiri Momma ta jawo waya, zata kira Munaya saita tuna ai wayartama Na d’akinta, Dan haka ta maida akalar kiran ga Galadima.

Cikin barci yaji wayarsa Na ring, da k’yar ya iya mik’a hannu ya d’auka yana guntun tsaki, shi baima San a Yaya yay picking call d’inba, yadai saka a kunne kawai cikin yanayin barci yace, “waye?”.
Mamaki ya kama Momma, wato bama su tashiba?. Tace, “Kabarmin yarinyata tazo ta shayar da yara kaji malam”.
Babu shiri ya watsakke, saidai kafin yace wani Abu wayar ta yanke, kansa ya dafe danjin Momma Ce Ashe, ya kalli Munaya dake barcinta har yanzu, harga ALLAH tana buk’atar hutu, baison tashinta, saiyaji inama yabari yaran sunashan madara tun farko, aikam yanzu dolene ya nemota, Dan can zasu dinga kwana wajen Momma.

??yanzu kuma.

Aunty Mimi tace, “Momma kibata kawai takaisu, Dan wad’annan sakkowarsu aikice kam yau, yarannan kuma yinwa sukeji, ai maganinsa ma, bashine ya hana abasu madara ba, ai da yanzu sai a basu susha su k’oshi”.
Momma tai kwafa tana fad’in, “Ai dolensa ya nemota yanzu, Dan bazan iya wannan shelarba kullum nikam, indai yaran nada abinda zasuci sukam su shekara basu fitoba ina ruwan wani, yunwama ta ishesu”.
Aunty Mimi dai da jakadiya dariya suketa sha.
Samha ta d’auki Abdurraheem ta Goya, sannan ta rike Amaturrahman da Abdurrahman a hannu tahau saman.
Knocking tamusu dukda tanajin tsoron fad’an Uncle Sam, amma yazatayi dana Momma kuma.
Tasowa Galadima yayi da k’yar, ya d’auka jallabiya ya saka sannan yazo ya bud’e k’ofar.
Rissinawa Samha tayi ta gaisheshi, ya amsa fuska babu walwa, itadai duk a d’arare take, kar6ar biyun yayi yafara zuwa ya kwantar sannan yadawo ya kar6a d’ayan. Gudu-gudu sauri-sauri Samha ta sauka tana murnar an rabu lafiya??.

Kukan Amaturrahman ya sanya Munaya farkawa, tayi mik’a addu’a d’auke a bakinta ta bud’e ido.
Da Galadima ta fara tozali, ya sakarmata wani sassanyan Murmushi yana wani lumshe ido.
Itama murtani ta mayar masa da sinne kai saboda kunya.
Yace, “Ayi hak’u atashi yunwa mukeji”.
Munaya tad’an 6ata fuska tana kuma jan bargo, “ALLAH barcin nan bai isheniba nidai”.
“Haba my Queen yi hak’uri please ”.
Kamar Munaya bazata tashiba, tadai daure ta tashi zaune tana yamutse fuska, sauka tayi ta shiga bayi tayo brush sannan tadawo.
Ya d’ora mata Abdurraheem daya kafa sabon kuka a cinya.
“Wlhy rigimarka tayi yawa Abdurraheem, ko kad’an bakada hak’uri”.
Galadima yayi Murmushi kawai amma baice komaiba, sai ido daya zuba mata itada yaron.
‘Dai-d’ai taringa shayar dasu, yayinda Galadima ke can gefe saman kujera yana waya da latsa lap-top, da alama kiran mai muhimmancine.
Nidai nagama shayar dasu natashi, duk saman sofa Na maidasu Na gyara gadon tsaf, harna kammala bai gamaba, koda nazo shara da Morphing ma yanata wayarsa, nagama kimtsa d’akin fes na shiga bathroom shima Na tsaftace sannan nakoma falon, dukda babu datti shima saida Na kuma gyarawa, ina jiyo hirarsu Momma a k’asa amma banyi yunk’urin saukaba, danni yau bammasan ya za’ayi Na sauka k’asaba, kunyar kowa nakeji wlhy.

A tsaye Na iskeshi yana k’ok’arin d’aura towel idonsa akan yaransa daketa kalle-kalle.
Muka had’a ido ya d’agemin gira da fad’in “zanyi wanka”.
Da to Na amsa masa na shige bayin danna had’a masa ruwan wankan.
Ko kad’an banji shigowarsa ba, saida na d’ago da nufin fita naci karo da mutum, baya nayi zan fad’i yay saurin taroni na dawo jikinsa.
“Nikam kabani tsoro”. Nai maganar a shagwa6e.
“Sorry”. Shima ya fad’a yana k’ok’arin saka idonsa cikin nawa amma nak’i.
Nace, “Ga ruwan, bara naje karsuyi kuka”..
Hannu yasa ya rufe k’ofar yana jana cikin bayin sosai, “Bawani kuka da zasuyi, yau duk zame-zamenki tare zamuyi wanka Matar Sameer”.
Cikin waro ido nace, “Tarefa?”.
Saukar ruwa naji ajikina. Yace, “ga tabbaci ma”.
Inaji ina gani doledai akayi wankannan, Wanda shiriritar da muka tsaya tajamu tsawon lokaci.

Aunty Mimi ta had’a breakfast a babban tire tabama Samha takai musu, taita knocking ba’a bud’eba, saita d’an tura k’ofar ta lek’a, babu kowa a d’akin sai yara a kan gado, saikuma ta jiyo motsin ruwa a bathroom, hakanne yasata fahimtar wanka suke kenan, d’aukar tiren tayi ta shige cikin ta ajiye, a ranta tana fad’in soyyaya ruwan Zuma, duk d’aurewar Uncle Sam da k’asaitar nan tasa Ashe zai iya soyayya, Ashe mu aka raina aita mana mazurai da harara.??

Bayan mun gama shiriritarmu muka fito fuskar kowannen mu d’auke da farincikin kasancewa da juna, yaran duk sunyi barci, ya zauna gaban mirror yana fad’in “Kashmir fa zamu wuce yanzunan”.
Da mamaki na kallesa ina fad’in, “Kashmir fa?”.
Hannuna ya kamo ya d’orani saman cinyarsa, yawani k’ank’ance idanu yana kallona, “To bakece kika Sani dawowar doleba my Queen, tunda nasamu kin sauka ai saimu koma tare”.
Hannuna na d’ora saman kwantaccen sajensa dake jik’e da laimar ruwa ina fad’in “Kai dai ka koma abinka, ALLAH inajin kunyarsu Momma”.
Murmushi yayi ya kama hannuna yad’an ciza.
Kukan shagwa6a na sanya masa ina yarfe hannun.
“O, my Heartbeat ingani yayi jini?”.
“Ai saina rama”. Na fad’a ina lalubo nasa hannun nima.
Dariya ya sanya da k’ok’arin 6oyewa, kad’an garage mu fad’i daga saman stool d’in, Dan yamana kad’an. yakuma cizona a kunne kad’an.
Kukan shagwa6a na kuma sanya masa da fad’in bazan yardaba.
Biyemin yay mukai tayi yana dariya da zagaye sofa akan saina kamashi na rama, amma yak’i tsayawa, gashi dagamu sai towel, saida ya tabbatar nayi laushi sannan ya fad’a saman Sofa yana dariya da sauke numfashi, jawoni yay na fad’o jikinsa nima ya rungumeni.
“Sorry Yalla6iyana bazan sakeba kinji, inga kunnen shima koya huda”.
Na turo baki gaba da mik’a masa kunen, “Bagashi harda jiniba”.
Nanma dariya ya sanya, “Yaushe kika koyi sharri kuma?, saikace wani mai hak’orin zaki”.
Dariya nayi inad’an dukan k’irjinsa kad’an. Nace, “wama yasani ko irinsa gareka, ALLAH akwai zafi”.
“Rakinki yayi yawa my Queen, nidai tashi kibani abinci naci, fita zanyi Akash na jirana, kinsan d’an matsalarnan bikinsa yataho”.
“A lallai kace munada shan shagali”.
Hancina yaja cikin tsokana yace, “idan baki fara laulayiba sannan ko?”.
“Laulayi kuma? Nami?”.
“Na abin cikin kwan mana, kina tunanin banyi ajiya bane jiya?”.
Sauka nayi daga jikinsa ina fad’in “Ka rufan asiri my King, ina zani da wad’annan ma dake gabana?”.
“Duk ki had’a mana babie na”.
ALLAH ya kiyaye na fad’a a zuciyata, a fili kam bance uffanba.
Tsaf muka shirya kanmu, sannan mukayi breakfast a makare.
Yayi k’yau cikin fararen suit, sai zabga k’amshi yakeyi, nikam sket da Riga na lass na sanya, kusa dani ya zauna, ya sanyani jikinsa yay mana photo, sannan ya sumbaci la66ana.
Nad’an murmusa da maida masa murtani, cikin lumshe ido yace, “Thanks my Everything”.
Far nayi da idanu cikin kissa nace, “ALLAH ya tsaremin kai”.
“Amin” ya fad’a yana mik’ewa. Ya matsa ga yaransa dake barci duk ya sumbaci kumatunsu sannan muka fito..
Iya falon saman na tsaya ina masa adawo lafina.
Harya fara taka steps d’in ya tsaya, juyowa yay yana kallona, “Wai kina nufin iya nan zaki tsaya?”..
“Nidai wlhy kunyar su Momma nakeji”.
Dariya tabashi, amma sai baiyiba, yay murmushi yana cigaba da sauka abinsa.

Shi kansa dai daya sakko k’asan sai kunya ta kamashi, ganin Momma da Aunty Mimi duk suna falon, saiya samu kansa dak’in yarda su had’a ido.
Aunty Mimi Ce kawai tayi k’aramar dariya, amma Momma yitai tamkarma batasan inda ya dosaba, saima ta shiga yaba kwalliyarsa da tambayarsa sai ina kuma?.
Ganin Momma ta share shima saiya fuske yay mata tamkar yanda ya saba, yasamu ya fice abinsa.

 

*****

Ni dai kam nakasa sauka kasa, ganin kad’aici da kewar Galadima zata fara addabata saina d’auki waya na kira innarmu, hayaniyar danaji a gidan yasani tambayar mike faruwa?.
Innarmu tace, “To sarkin son gulma basai kinjiba, ya kuke?”.
Dariya nayi, nace, “Kai innarmu Dan ALLAH kid’an gumtsamin”.
“O ni Ai’sha ALLAH ya shiryeki Munaya, wato dai bazaki canjaba kekam?”.
Nanma dariyar nayi harda k’yalk’yatawa, “Kai Innarmu na canja mana, kinsan gidan namune sai a slow, nasan dai yanzu duk kin wuce da iskancinsu d’innan?”.
Itama dariya tayi daga can. Tace, “Ai tsakanina da kowa yanzu sai girmamawa, ni dariyama suke bani, Safara’u ce wai mijinta zai k’ara aure, shinefa inaga ta tada hankalinta taita zuba masa rashin kunya ya shashshek’a mata mari, to jiya dai a gida ta kwana, kinsansu da gutsiri tsomar tsiya, wai Jamila tashiga gaida Hadiza ta iske suna gulma itada Mero, shine taje tasanarma uwar tasu, wannan yakawo wanan fad’an da kikeji, Maman safara’u babu hak’uri tafito tanata zaginsu da fad’in ai ko auren Safara’u mutuwa yayi ba kanta farauba, tunda ga Siyama da Zarah nan a gida tun kafin ita. Shinefa suka kaure fad’a da cin zarafin juna”.
“Tofa, ALLAH ya k’yauta to, tosu su mom indai banda take laifinka ka hango na wani ai baikamata su zauna yida waniba ganasu y’ay’an zaune, anriga an koyama yaran gidanan d’aukar gulma wlhy, yanzu kamar jamila tasan ta d’auki zance takaima mamansu, to su Abba duk basa nan innarmu?”.
“Wlhy suna nan, kuma duk sunajinsu, shiyyasama danaje nabad’a hak’uri sau d’aya naga sunk’i saurarena nai dawowata d’aki, Aryaan na kwance yana fama da zazza6i gara Nazo natattali yarona yafimin”.
“hhh innarmu kinaji da autaras d’innan nakifa, ALLAH yabashi lafiya, sukuma ALLAH ya dai-daita komai. Hajiya Innaro fa?”.
“Tana gidanta mana, bama tajin dad’i kwana biyunnan wlhy, tana fama da ciwon k’afa, ki kirata ki gaisheta, dan jiya gwaggonku Safiyya ma tazo itama”.
“To su Innaro kodai gangarawa za’ayine? ALLAH yabata lafiya”.
“Ja’ira saidai tsohonki ya gangara, amindai to, ai dama sauk’i”.
Dariya nayi kawai.
Daganan muka cigaba da hirarmu wadda ta shafemu, nan ma innarmu ke sanarmin Aunty Salamah tazo gidan ansaka aurenta.
Cikin tsantsar farin ciki nace, “Innarmu dan ALLAH da gaske?”.
“To Munaya ana wasa da maganar aurene? Nasanma zata kiraki ai”.
Farin cikine sosai ya mamaye zuciyata, nace, “ALLAH sarki Aunty Salamah komai nada lokaci, anata surutun ta tsufa agida batayi aureba, gashi ALLAH yakawo iyakar, lallai aure da Haihuwa duk lokacine dasu, duk saurin mutum saiya jira ALLAH, ALLAH yabama sauran y’an matanmu mazajen aure nagari masu addini da nagarta, suma mazan haka”.
“Amin dai Munaya”. Inna ta amsa itama cikin farin ciki..
Nace, “Innarmu zancen Ayusher fa itama?”.
“Itama kwanannan sukace min zasuzo akan maganar, dan kawu Mani ma munyi waya dashi d’azunnan, tsohuwar nan ce tarasu mai ciwon hannun nan, shinema ya dakatar dasu”.
“ALLAH sarki Innarmu, badai wadda tabama yara maganin ciwon kai ba?”.
“Aiko dai ita, ashe kin ganeta, ALLAH ya d’auke kayansa shekaran jiya wlhy, Abbanku ma zasuje gaisuwa su dukansu harda Baba mai kanwa ”.
“Wayyo, to ALLAH ya gafarta mata, amma shi baba mai kanwa ina yaga k’arfin wannan doguwar tafiyar innarmu?”.
“Ai ba’anan takeba Munaya, dayake ALLAH yabashi lafiya, yace insha ALLAH saiyaje yaga tushena”.
“ALLAH Sarki baba mai kanwa, ALLAH yak’ara lafiya da tsawon kwana”.
Inna ta amsa da amin.
Munsha hira sannan mukai sallama.

Itama Innaro na kirata namata ya jiki, daganan muka gaisa da gwaggo Safiyya da aunty Habiba.
Na kuma kira Munubiya, sosai mukasha hira, take kuma bani labarin auren Aunty Salamah dayazo kamar ha6o. Tace, “Alhajinan dai dayayta naci wanda muke cema Cingom Alhaji dai shine mijin”.
“Oni rayuwa, Sweetheart kinga hikimar Ubangiji ko, idan yazo muyita masa iskanci har ita aunty salamah d’in Ashe dai shine mijin, gaskiya ya cancanci ta auresa, wajen shekaru biyarfa bawan ALLAH nan baita6a gajiyawaba”.
“Wlhy kuwa Sweetheart, son gaskiya kenan ai, ga Ayusher nan anata soyewa itada Hamma Youseeff, duk wannan shan k’amshin nasa ya mace mata, Yaa Fadeel ma in fad’a miki shida Badeerah Ashe sun k’ulle”.
“Dan ALLAH da gaske ko wasa?”.
Cikin Dariya Munu tace, “Wlhy kuwa, waike bak’ya waya da kowama kenan?”.
“Wlhy ba haka bane kemakinsan d’an tsakaninan damuwar data hanani sukuni, amma yau dolene na kirasu nasha kanu, shegiya Ayusher bara itama na kirata, dukda kud’ina sun kusa k’arewa, a gaidamin da Sweetness babies d’ina da Yaa Marwan inya dawo”.
“Zasuji insh ALLAH, asha amarci lafiya, aidai kulamin da yara kar soyayya tasa abarminsu su rame”.
Kafim nayi magana ta yanke kiran.
Dariya kawai nayi ina girgiza kai, alokacinne Samha ta shigo.
“Ah lallai aunty gimbiya yau Uncle Sam ya 6oye mana ke, Momma Ce tace yau bazaki sakko bane?”.
“Dan ALLAH da gaske?”. Nai maganar cikin waro idanu.
Dariya ta sanya, “Wlhy kuwa da gaske nake”.
“Ni munaya naga idi, ALLAH kunya nakeji”.
“Kam kunyafa aunty gimbiya, to miye najin kunyar? Wlhy ALLAH yabani miji irin Uncle Sam a gabanki zan mak’alk’ale abina”.
Duka nakai mata ta kauce tana dariya.

******

Cikeda jin kunyar su Momma na sakko k’asan, amma saisukayi tamkar basusan minike mawaba, tun ina sunne-sunnen kai hardai na warware nasaki jikina kamar yanda nasaba.
Momma da Aunty Mimi sunji dad’in haka, a zukatansu suna mana addu’ar d’orewar zaman lafiya nahar Abadan……………..???

 

Inaga sai Monday zakujini, kuyi fatan nama kammala gaba d’aya????????

 

 

 

ALLAH ya gafartama iyayenmu??????

 

?RAINA KAMA…!!?
(Kaga gayya)

Bilyn Abdull ce????

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply