Hausa Novels Raina Kama Book 3 Hausa Novel

Raina Kama Book 3 Page 23


Raina Kama Book 3 Page 23
Viral

BOOK 3 ????2?3?

……………..Mud’in mun kasance wasu yankin ahali daga wannan masarauta, sai dai nasan al’ada da ak’idar masarautar ta jima da shafemu daga kasantuwar tsatsonta.
Iftila’in al’ada Nak’in kar6ar d’iya mace a matsayin y’ar farko ga Sarki mai mulki shine silar barin iyayenmu damu kanmu, sarakuna da yawa sun shud’e labarinsu ya shafe tamkar yanda Na Sarki Madou Amadi yazama shud’ad’d’e” inna ta share hawayenta, sannan tacigaba da fad’in, “Lokacin da mahaifinmu yake bisa karagar Mulki da k’arfin iko sai ALLAH ya azurtashi da haihuwa ta a matsayin d’iyarsa ta fari. Haihuwata ta girgiza k’arfin mulkinsa matuk’a, Dan Al’adar masarautar shine tilas d’an Sarki Na farko ya kasance d’a namiji, acewarsu d’iya mace rusa masarauta takeyi da tsiyatata, dan ita bata mulki, kamar yanda ake korar duk wani Sarki da matarsa ta haifi y’a mace a haihuwar farko ga mahaifinmu sai bai yuwuba, saboda k’arfin iko da ALLAH ya bashi, anbuga-anbuga yak’i sauka, danshi burinsa ya canja wannan al’adar masarautar, har ALLAH yasa Na cika shekaru 7 a duniya. A tsakaninnan bayyana harmutsi da hayaniyar da taita faruwa 6ata lokacine, Dan mahaifinmu Sam yak’i sauka daga Matsin da suke masa. cikin amincin ALLAH sai kuma ga cikin Rabi’a babu zato, har wannan lokacin babu wani kwanciyar hankali a masarauta, saidai bayyanuwar cikinta yasa akace za’a dakata aga mizata haifa, idan d’a namijine shikenan. Saidai kash, daga lokacinda Rabi’a ta canyara kukan isowa duniya sai masarauta tayi tsitt, Dan kuwa dai kowa yaji macece. Dandanan fa aka tada Sabin bore akan dolenefa sarki ya ajiye a wannan karon, amma mahaifinmu saiya k’i a wannan karonma, danshi burinsa ya canja wannan mummunar al’adar kowa ya fahimci itama d’iya mace tanada tata darajar fa, kufa namijin bai fitaba, domin itama ALLAH ya haliccetane danta bauta masa tamkar namijin, dukansu kuma idan sunk’ibin ALLAH wuta zai sasu, idan sun bishi Aljanna zai kaisu, amma Sam sai suka bijirema dukkan tunatarwarsa, masuma goya masa baya suma sai suka daina, watan Rabi’a 1 kacal a duniya akai mana korar kare daga wannan masarauta dama yankin baki d’ayansa, muna kuka muda mahaifinmu haka muka tafi, mukabar ahalinmu, yankinmu , al’ummarmu. Saboda mummunanr Ak’ida, saidai kuma babu inda muka Sani, Dan haka iyayenmu suka yada zango awani k’aramin k’auye dagacan bakin gari, anan muka rayu tsawon wasu shekaru dahar nakai girman zama minzalin budurwa, itama Rabi’a ta girma, rana tsaka saiga tawagar masarauta wai ankai mata bayanin mahaifinmu baibar wannan yankiba, halan akwai abinda yake shiryawa? Dan bazai yuwu ayi sarki biyu cikin nahiya d’aya ba, sarkin ma da aka d’ora bayan korarmu shima matarsa mace ta haifa, tuni sun korashi, Na yanzunma kuma hakance ta faru, dalilin korarsane ma sukaji labarin mahaifinmu yana a wannan waje tare damu. Korar cin zarafi da akai mana a wannan lokacin tamafi Na farko, Dan alokacin munada wayo muma, munsan zafi munsan d’aci, a wannan karon bama Nahiyarmu ba, k’asar gaba d’aya muka bari, tafiya ta tsawon wattani da yada zango ce takaimu Nigeria, a wahalce a jigace, inda muka samu mafaka a tashar da suke lodin motocin da suke zuwa kasuwanni, makonmu uku a wajen, Dan bamu rasa abincin dazamu ciba iftila’in rayuwa da k’addara ta fad’amin, Wanda muka wayi gari da rashin mai taimakonmu sai wani bawan ALLAH (Malam fharuku kakansu Munaya??)”
Inna taci gaba da bada labarin k’yautatawar dasu Innaro sukai musu, har mutuwar iyayensu da aurenta da Abba, Dana mama Rabi’a, da zuri’ar da suka samu harda jikoki, ko kad’an bata fad’i muzanwa ko cin fuska da Innaro taita musuba sai alkairin mijinta da y’ay’anta.
Nanfa kowa ya shiga matse hawayen tausaya musu, hardamu, Dan munji abinda koda wasa bamu ta6a saniba balle tunanin kasantuwarsa, Dama iyayenmu jinin sarautane mai girma irin haka? Amma kullum suka kasance cikin shanye k’ask’anci da gorin talauci Dana ahali, lallai wannan banzar al’ada batada wani abin birgewa.
Shikansa sarkin saidai yay hawayen tausayinsu inna, Yakuma buk’aci su matso garesa, hakama tsohuwarnan rungumesu tayi tana kuka.

Innaro dai anyi zugudim tana kallon ikon ALLAH, Wanda ya girma ya d’aukaka, kunya da d’unbin nadamar Dana Sani sun dabaibayeta tagaza koda kwakwkwaran motsi balle d’aga ido ta kalli su inna, yanzu nan dukkan cin kashi dacin zarafin dataitama su Ai’sha musammanma ita shine zata lullu6e bak’in mugun halinta ta wanketa da alkairin mijinta Dana y’ay’anta? Wace irin k’yak’yk’awar zuciyace da wannan baiwa haka?.

Munsha kukan tausayin su innarmu, sannan munyi murna matuk’a da tarbar da akai musu damu kanmu, Su Abdurraheem dasu Aiyaan, da Aryaan, Ahmad, dake k’anan duk an janyesu, kowa yana d’aukarsu cikeda tsantsar so da k’auna. Saida akad’an lafa sannan Sarki yay bayani cikin nutsuwa da dattako.
“Lale marhabin agareku y’an uwana, kun kafa tarihin da tilasne a yaba muku, Dan babu wasu da suka sake waiwayen wannan masarauta bayan korar da akaimusu, sun tafi ba’a kuma jin labarinsuba ko inda suke. Bak’aramin durk’usar da wannan masarauta waccan Mummunar Al’ada tayiba, mun rasa ahalinmu masu d’inbin yawa, masarauta dake cikeda dangi yau takoma sai tsirarune a cikinta, kunganmu nan dudu iyakarmu kenan muka rage, wasu sarautunma sai hannun jama’ar gari da bayi ta koma, saboda babu masu rik’ewar, haihuwa itace yad’o, mukuma mun nisanta kanmu da wannan yad’on, masarautar nan ta dad’e tana korar ahalinta saboda haihuwar y’ay’a mata, ALLAH kuma yayta jarabtarmu da samunsu a matsayin y’ay’a, bayan shud’ewar marigayi Sarki Madou Amadi sarakuna kusan 20 sun shud’e a dalilin hakan, bamusan duniyar da sukeba, saida mahaifina yahau ya tsaida wannan al’adar gaba d’ayanta, saboda ganin wataran lallai sai kowa dake cikin ahalinmu ya k’are inhar wannan al’adar tacigaba da wakana, muna baku hak’uri, muna kuma Baku hak’uri, a yanzu wannan masarautar ba ita bace waccan da kukasani, mace Nada daraja sosai a yanzu, tanada kima da k’arfin fad’a aji, muna fata bazaku sake nisantarmu ba, zakuzo mu had’a k’arfi da k’arfe wajen kuma samun yad’uwar wannan masarauta ”.
Innarmu da mama Rabi’a Na hawaye suka amsa masa da insha ALLAH.

Zayyana muku farincikin daya cigaba da gudana 6ata lokacine, mun shige cikin dangin mahaifanmu munata warkajami, kulawa ake bamu ta musamman da birgewa, aranar aka canja mana masauki Na musamman dayafi wancan k’awatuwa da komai, aka zuba mana hadimai masu hidima, su Abba kam ko ganinsuma bakayi, gagarumin biki Na musamman aka shiga shiryawa Na murnar dawowar su innarmu. Kai lallai munashan kallo, kukadai najin dad’i da farinciki mun shashi, INA y’an gidanmu? Suzo suga abin al’ajabi daban mamaki, innaro dai baki ya mutu murus, saima dukta tsangwami kanta a cikinmu, aiko mukaita zuba mata habaici muma, Dan ganin su innarmu yama gagareta gaba d’aya, sun shige cikin y’an uwansu tamkar dama ciki suka taso, duk wannan hidima batasani mantawa da kewar mijinaba, musamman da Saurayin jiya yafara takurani da kallon tsiya har a ranar, nikuma ban daina antaya masa hararaba, saida nagaji nake sanarma su Munubiya, suma sukace ai duk hakan yake musu, itadai Munubiya tasamu tayi maganinsa ta hanyar mak’alk’alema mijinta, dukda kuma suna tare da Yaa Marwan d’in duk inda yasa k’afa, hasalima Yaa marwan ya koma sashensa gaba d’aya. Daganan tasamu lafiya, saiya koma kanmu ni da Ayusher, dukda wani lokacin yakan Gaza banbantamu ni da Munubiya, inhar baya ganta tare da yaa Marwan bane, itakuma Ayusher ta fini jiki, musamman ma ramar danayi ta jiyyar Dana sha, ita kanta Munubiya tafini jiki a yanzu. Gashi su Abdurrahman sun gagareni d’auka balle nima Na fahimtar dashi inada aure, inkin gansu a wajena shayar dasu zanyi, tokuma bazan iya hakan agabansa ba.

Wannan saurayi dai d’ane ga Sarki, Dan shine magajin masarautar ma yanzu.
_________

Muna zaune awata rumfar Bunu a washe garin da muka cika kwanaki buyu a masarautar, ranarda za’a gudanar da bikin dawowar su innarmu, zaune muke da wasu y’anmata kusan 8 masu kama damu, duk kuma bazasu wuce sa’annninmu ba, saidai wane ya girmi wane da wata 1 ko biyu, hira muke cikin so da k’auna juna, da d’okin kasantuwarmu ahali d’aya.
Suna bamu labarin yanda bikin al’adunsu ke gudana irinsu bikin sallah dana aure, muma muna basu namu, saidai maganar gaskiya ni hankalina ya rabune gida biyu, rabi garesu rabi ga Galadima.
Munubiya ce ta lura da hakan, ta d’an ta6ani Na juyo Na kalleta.
“Sweetheart mike faruwane wai?”.
Cikin marairaicewa nace, “Munu Galadima mana, yakamata yajini koda a wayane, kinga anama mahaifinsa Magani, baikamata ace koyaya bana bibiyar lamarin Yaya lafiyarsaba, karyaga kamar ban damubama”.
Cikin gamsuwa tace, “zancenki gaskiyane, shiyyasa kike burgeni wajen hangen nesa, inaga yakamata mu nemi sim card mu saya”.
Naji dad’in shawararta, Dan haka muka tambayi y’an matan.
‘Daya a cikinsu mai suna Badeera tace, “yanzunan kunason yin amfani da waya shine bazaku kar6i namuba? Amma bamuji dad’iba gaskiya, Ashe bamu zama d’ayanba kenan?”.
Hak’uri muka basu, Maryamu ta d’oramin wayarta a jiki tana fad’in gashi kiyi kiran duk Wanda zaki kira, bara a sanarma Yareema issifa yasa akawo muku.

(Nayi amfani da namune saboda wasu dalilai, yarenmu ba d’ayaba Dan haka abubuwan da suke fad’a bazai zama d’aya da namuba, to amma Raina kama anginashine bisa wani bigire daban, zanyi amfani da iya abinda Na sani, Dan ban zurfafa bincikeba gaskiya, ALLAH yasa zaku fahimceni??????).

Da mamaki nace, “waye hakan?”.
Cikin dariya sukace magajin wannan masarautar mana, Wanda kike k’orafin ya dameku da kallo”.
Baki nad’an ta6e cikin mamaki, nace, “To wai Issifa sunane?”.
Nanma dariyar sukayi, Dijahma tace Youseefa kenan fa.
Nace, “tab, sunayenku kukam wasu iri wlhy, nidai bara kuga naje Na nemo mijina”.
Dariya duk suka sanyamin.
Natashi zuwa cikin masaukinmu. d’akinmu Na shiga, Na lalubo wayata a handbag wadda tunda mukazo suka zama marasa amfani agaremu.

 

**********

A 6angaren Galadima kam suma Alhmdllh, Abie yanata samun kulawa ta musamman ga Dr Erfan Fahad, Dan da iya k’yautatawar yakema Abie abu, kodan sanayyar dake tsakaninsa da Galadima wadda saidaga baya ya tuna wanene Erfan Fahad d’in, sunyi karatun addni wajen malami d’aya a time d’in bazasu wuci shekaru 9 ba, har lokacin da suka kai 17years shi Erfan Fahad iyayensa suka d’aukesa daga wajen Sheaik Mu’azzam Abdul-aziz, saboda zasu koma Kashmir a lokacin, dama aikine yakawo mahaifinsa India, tundaga nan basu sake had’uwa ba sai yanzun, lokacinda Sheaik Mu’azzam Abdul-aziz ya rasu shi Dr Erfan Fahad yazo gaisuwa, amma basu had’u da Galadima ba, a sanann shikuma yana k’asarJapan karatun shekara 2 daya kaisa, saida ya dawonema yakejin rasuwar malamin nasu, gaisuwa kawai yaje yayma iyalansa yaymusu alk’airi mai yawa.
A kullum Dr Erfan Fahad da Galadima cikin hirar tuna baya suke, balle da Dr Erfan Fahad ya d’ebo masa wasu hotunansu suka gani, nanfa suka kuma rikicewa da labari, suna hirar sauran abokansu da rashinjin da sukayi a makarantar.

Rabonsa da jin Munaya tun randa suka tafi, suna gab da shiga Niger sukayi waya, daga nan basu sake ba, sosai yake kewarta, duk ya damu, kwana biyu kawai dabai jitaba, har Dr Erfan Fahad saida ya fahimci yana cikin damuwa, Dan Dr Akash da Dr Ajay sun koma India kan aikinsu.
Amma Galadima yace masa babu komai, Dr Erfan Fahad bai yardaba, Dan haka ya damesa da tambaya, doledai Galadima ya sanar masa.
Aiko ya tasashi gaba da tsokanar wai yace dai soyayya kecin zuciyarsa ba wani abuba, to yarage damuwa, yasan itama laila d’in nacan cikin damuwar rashinsa.
Murmushi kawai Galadima yayi, Dan yafara sabawa da yawan tsokana irinta Dr Erfan Fahad, akoda yaushe yanzu suna tare, idan kin gansu ba tareba to yashiga aikine, yakanbar Galadima a Office, Dan har yanzu ba’a shiga wajen Abie, awata na’ura suka sakashi dake taimakama ga66ansa motsawa a hankali, saboda allurar da ake masa duk bayan awanni 12, a koda yaushe saidai Galadima ya lek’ashi ta Window idonsa yakan cika da hawaye, Dan lallai ALLAH ne kawai zaima Abie hisabi dasu Alhaji Lawan tanderu bawai Alk’alin duniyaba.
Su Momma sunso zuwa amma Galadima ya dakatar dasu, Dan bayason suzo su d’orama Dr Erfan Fahad nauyi, shikuma maganar gaskiya a tsakaninnan aljihunsa yayi k’asa, damma akwai madogara Na business kala-kala da koyaya asiri zai rufu.

Yauma suna asibitin, Dr Erfan Fahad ya shiga wani aiki, Galadima ne kawai zaune a office d’in cikin k’ananun kaya, yana zaune a kujerun dake cikin office d’in daga can gefe, k’afarsa hard’e bisa teble d’in tsakkiyar kujerun, ya d’ora laptop yanata aikin Company daya zamana saita nan, harma Na Hukumarsu dake nan Nigeria, wato (DSS). Idonsa Na saye cikin medical eyeglasses mai haske, sosai yayi zurfi a aikin, alokacinne kiran Munaya ya shigo wayarsa, amma yay burus yacigaba da aikin tamkarma baijiba harta yanke, kuma kira Munaya tayi, nanma yak’i d’auka.
Bata gajiba tacigaba da damunsa, cikeda jin haushi ya kalli wayar yana jan tsaki, mamaki ya kamashi ganin Number d’in dabai saniba, baima ta6a ganiba, yanzunma harta yanke bai d’aukaba.
Idon Munaya harya fara tara kwalla.
Cikeda Damuwa takuma kira, shikuma ya d’auka cikeda k’uluwar an dameshi.
Kawai saita sakar masa kuka.
Kasa motsawa yayi, Ya kuma kasa magana, Munaya tace, “Ni zakama wulak’anci ko? Shikenan sai anjima”.
Zaiyi magana k’itt ta yanke wayar. Kansa ya dafe yana fad’in “O ALLAH my mata bansan ke baceba”. Kiranta yayi amma tak’i d’auka harta tsinke, saida yakuma kira sannan ta d’aga, itama tana gab da katsewar, harma ya fidda ran bazata d’agaba.
“Shikenan kin rama ko?”. Ya fad’a a hankali cikin taushin murya da nuna kulawa a gareta.
Munaya ta d’an tura baki kamar tana ganinsa, amma batace komaiba.
Ya murmusa yana ajiye lap-top d’in ya sauke k’afafunsa. “Kinga bara Na kiraki video call, gara naga dai ma ya kika koma”.
Bai jira cewata ba ya yanke wayar.
Dad’i sosai ya kamani da jin k’arin k’aunarsa, Wanda ban ta6a tunanin kalloma zan isheshiba shine yake damuwa idan Na damu……….
Kiran ya katsemin tunani, Na d’aga amma saina saka hannuna Na kare idona, bakina da rabin hancina kawai yake gani.
“Haba my mata please mana, ko saina miki kukane?”.
bakina nad’an motsa da turashi gaba kad’an alamar eh.
“Humm kinga duk randa Na kama bakinnan zai min bayani dalla-dallane”.
Cire hannuna nai babu shiri ina kallonsa, ya kashemin ido d’aya.
Nai k’asa da idona ina fad’in, “ALLAH ya shiryaka, nidai babu ruwana”.
K’asaitaccen murmushinsa yayi yana gyara zamansa, “Anya kina missing d’ina kuwa?”.
Fuska Na marairaice masa kalar tausayi, nace, “sosaima kuwa”.
“uhmyim to inga idon”.
d’an kwalina naja Na rufe fusakata ina dariya.
Yace, “Nifa wannan kunyar a ringa ajiyemin ita gefe sai ina buk’atarta, ina my children’s?”.
“Nayi k’yautarsu”. Nayi maganar ina bud’e fuska.
“Dakin birgeni, kinga danazo tun anan saina tanajin wasu abin cikin kwan”.
Share zancen nai kamar ban fahimtaba, nace, “yaushene zakazo to?”.
“Kina missing d’inane?”.
“Sosaima ALLAH kuwa”.
Dad’i ya kamashi, cikin lumshe idanu yace, “ina tafe soon, sai kunyi kwana 5 sannan zazo nayi kwana 1 mu dawo Nigeria ki tattaro kayanki miyo gaba”.
“To ALLAH ya kaimu, ya jikin Abiena?”.
“Abienki nata samun kulawa Alhmdllh, muna kuma hango nasara sosai, Dan Abokina yasan aikinsa sosai ”.
“Alhmdllh, ALLAH yasa iyakar wahalarce tazo, muma muga Abie d’inmu Na tafiya da k’afafunsa, yadawo k’asarsa ta haihuwa inda mak’iya basa son zamansa, bak’inciki dukya kashe shegu”.
“ALLAH ya tabbatar my Queen, guntsamin mana, Yaya kuka iske Niger d’in?”.
Cikin tsumud’i nace, “karkad’e kunnenka kasha labari yalla6ai”.
“Na karkad’e da k’yau yalla6iya”.
Cikin Nutsuwa Munaya ta shiga zayyane masa komai, tun yana al’ajabi yakoma mamaki, Yakoma tausayi, ya koma murna da nuna tsantsar farinciki.
Yace, “ALLAH Sarki innarmu, Ashe ita jinin girmace, shiyyasa ta kasance mai dattako, lallai yanzu Na fahimci ina kika kwaso halinnan naki, dama nadad’e ina tunanin anya baki shafi jinin masu sarauta ba, jan ajinki da son girma yayi yawa”.
“kai ba’ace naka yayi yawaba sai nawa?”.
Murmusa yay yana shafa girarsa d’aya. Yace, “toni minayi kuma?”.
“Ai idan zan lissafo maka sai kud’inka sun k’are ban gamaba”.
“Sheri dai zakimin kawai yalla6iya, inasu Abdurrahman wai?”.
“Tab ai wad’annan inba yunwa sukejiba ganin su wahala yakemin ni kaina, ai saikazo kawai kadai sha mamaki, duk yanda zan musalta maka a yanzu hasashe kawai zakayi”.
“Ina tafe insha ALLAH, koma Dan Na d’akko matata Na gudo, amma yanzu kam dole saina nema izinin shigowa”.
“Meyasa?”.
“Kinta6a ganin jinin mulki yashiga wata masarauta bada neman izini ba? Hakan tilas ne, yak’e-yak’en dake faruwa a masarautu yakawo wannan sharad’in, zuwa yanzu kuma yazama babbar Al’ada mai k’yau”.
“Lallai, to yanzu tayaya zaka nemi izinin?”.
“Zaki gani bari lokaci dai yayi. Yanzu mizan samu Na rage zafi?”.
Cikin salon narkar dashi Munaya ta juya idanu tana fad’in “Mikakeso?”.
“Gaba d’ayanki wlhy”. Ya fad’a cikin marairaicewa.
“Indai nice dama takace ai Muhammad Sameer”.
Lumshe idanunsa yayi yana cije lips, yaune ranar farko daya ta6ajin sunansa a bakinta, “Please sake fad’a naji”.
“Mid’in?”. ‘Nafad’a cikin d’an waro idanu’.
Ya wani marairaicemin kamar k’aramin yaro, yana k’ank’ance idanunsa da suka sauya kala. Yace, “Sunana”.
Yanda yay maganar cikin sanyi da kasala saida tsigar jikina ta tashi, kamar yanda ya buk’ata nakuma maimaita masa a kasalance.
“My Queen ina k’aunarki da yawa, zan tabbatar miki hakan randa kika dawo gareni, jinake duk duniya nafi sauran maza morewa da samun nutsatstsiyar mace mai tarin baiwa da tarbiyya, Har abada Na mallaka miki Muhammad Sameer da komai nashi, ki yi yanda kikeso dani my Heartbeat”.
Kwallan farin ciki ya cikamin ido. Nace, “My king tukwiycin wannan k’yauta sai ina kusa dakai, Dan tsadarta yakai tsada, tukwiycinta mai girman darajane, kuma zan mik’ashine gamai daraja, dolene yakasance a waje mai daraja, ba Kaine kaima sauran maza zarraba, nice, ni Munaya ninaima sauran mata fintinkau wajen yin dace da samunka a matsayin miji, Uban y’ay’ana, Masoyina, cikon farincikina, I love you so more irin wadda bata k’arewa d’innan har a Aljanna….”
“Na gode Uwargidana a Duniya da Aljanna, kece shugabar Matan Muhammad Sameer anan duniya, kuma kece a Aljanna insha ALLAH, ALLAH yayi miki albarka wadda bata yankewa keda gudan jinina”.
Hannuna naima kisses uku Na hura masa.
Ya wani lumshe idanu yana dafe k’irjinsa alamar sak’ona ya isa.
Wata dariya mai ida kashe jiki murus nayi masa, aiko saiya zame ya kwanta kawai cikin kujerar yana kifa wayar a k’irjinsa ya lumshe ido.
Nakuma bashi wani kiss d’in mai k’arar sauti, babu shiri ya d’auki wayar da Sauri saidai kitt Na yanke kiran ina dariya.
Nima zubewa nayi a gadon k’irjinna Na dukan goma-goma, dayasan tsiyar da Na shirya masa dabai yarda dani hakaba????.
Dariya kawai da tafi naji akaina, nai saurin bud’e ido, sainaga Ayusher, Munubiya, da Feena akaina. Hararsu nayi ina juya fuska can gefe da fad’in, “y’an sa ido, Uwarmiye aka biyoni?”.
Ayusher tace, “Yo k’arshen munafurci da cika baki mukazo gani, yaudai munga abinda ake 6oye mana da cika baki”. Suka kwashe da dariya suna tafawa.
Banza namusu.
Feena tace, “Aini wlhy dama tun a asibiti nace muku gayunnanfa sun d’inke, wuya tayi wuya SIRRIN ZUCIYA ya fito fili, sun gama cika bakin da jan ajin, shi k’asaita da mulki, ita jan aji, Ashe harda Mulkin bamu saniba. Kai kusamana wak’a muyi murnan K’ulluwar k’auna”.
Ayusher ta saka wak’a a waya suka ko dage suna tik’ar rawa..
Dariya suka bani wlhy, nace, “y’an iska kwadaiji da munafurcinku wlhy, nan gani nan bari dai Munafuncin su innaro”..
Aiko mi zamuyi inba dariyaba gaba d’ayanmu, nikaina Innaro d’ince kawai tazomin abaki ban shiryaba.

**********

Washe gari aka gudanar da bikin tarbarmu, Wanda yay matuk’ar k’ayatar damu da sakamu farinciki, munga al’adun daba namuba, su innarmu ansha shiga ta alfarma suda su Abba, Saiga su Abbanmu da sarauta, wai tunda sune mazajensu innarmu anbasu wata sarauta domin girmamawa agaresu, hakama Yaa Marwan, dad’i tamkar zai kashemu, aiko munsha hotuna da nuniya wajen jama’a.
Gashi ni banda ma sakewa, saboda yanzu banason hayaniya mai tsanani kusa dani, da za’ayi kid’a ma sai wajen nabari tilas, dama hayaniyar mutane da surutai harta fara sakani ciwon kai.
Da Galadima ya kirama sai Munubiya ce ta kar6a, ta sanar masa halin danake ciki, duk saiya rikice, yaringa rok’on Munubiya ta kula masa dani sosai.

******

Kwanakinmu 7 da zuwa cif mukaga anata hidimomi a masarautar, kasa shiru mukai saida muka tambayi dalili, su Badeera suka sanar masa wai wani d’an Sarki ne zaizo dana k’asarmu ta Nigeria.
Mamaki ya kamani, to wanene wannan? Dan nidai ko a jiya munyi waya da gadima kuma baicemin zaizoba, hasalima yana India, tunanin bashi bane ya sakani kauda zancen araina muka cigaba da hidimominmu.
Yanzu kam a masarautar babu inda bamu saniba, Dan kulum su Badeera cikin zagayawa damu suke, har cikin gari saida muka fita sau wajen uku, gaskiya Agadaz tanada abubuwan k’ayatarwa da Tarihi, hotuna kam ai yinsu muke tamkar babu gobe.

Su Hajiya Innaro dai kam an nutsu, ni harma tausayi tafara bani wlhy, Dan haka muka rage iskancin da muke mata, yanda ake bata kulawa da girmamata kawai a masarautar ya isheta kunyar abinda ta aikata, (lallai babu Abu mafi dad’i irin ka sakama mai jifanka da sharri da tarin alkairi) wlhy har Abadan bazai sake sukuniba a gabanka saboda d’unbin kunya da nadama dazata addabi zuciyarsa, Dan kullum zai kasance cikin tsarguwa da tsangwamar kansane. Kunga dai yanda innaro ta kasance a yau.????????

Sai wajen la’asar sakaliya labari yazo mana wai d’an Sarki nan ya iso, bushe-bushen algaitu irin nasu kawai dake tashi ya tabbatar mana da lallai yazo d’in.
Cikin mu babu Wanda ya maida hankali akan lamarin, danni kwance ma nake Na kifa Absurraheem saman cikina yana barci, Feena da Deejahma suna gefena zauna suna kallon hotunan da mukayo ayawon jiya da muka fita, su Munubiya kam Na tsakar d’akin suna hira da sauran y’ammatan, Ayusher nama Zuhuriyya kitso, Wanda anayi yana warwarewa saboda gashin akwai santsi, sai wata dabara sukeyi a k’arshen kitson.
Bayan sallar isha’i saiga mama Rabi’a ta shigo d’akin da muke, duk muka gaidata, fuskarta d’auke da Murmushi ta kalleni ina canjama Amaturrahman kayan barci dan an musu wanka. “Munaya ta shi kiyi wanka yanzunan”.
Da mamaki nace, “wanka kuma mama? Lafiya kuwa?”.
“Lafiya lau, kedai ta shi kiyi, bama Maryamu ta k’arasa shirya Amaturrahman d’in”.
Nidai duk al’ajabi ya kasheni, ganin duk yawan y’ammatan dake d’akin ba’ace kowa yatashi yay wankaba saini, suma dai Kansu kallon mamaki sukemin ni da mama Rabi’a d’in. Hannuna ta kama muka fice zuwa wani d’akin.

Cikin bayin gidan d’aya ta had’amin ruwan wanka, dama tunda mukazo komai yimanashi akeyi. Mama Rabi’a tacemin “Kinutsu kiyi wanka mai k’yau wlhy, inba hakaba dakaina zan canja miki wani”.
Mamaki kuma kasheni yayi, nadai nutsu nayi wankan fiyema da yanda take buk’ata, ga ruwa nata tashin mayataccen k’amshi, dan wannan masarauta sunsan sirrin k’amshi kam, akwanaki 7 d’inan har turare yafara zaunawa a jikinmu saboda bala’in yawan amfani dashi, motsi kad’an sai ahau tiraraki da turarurruka iri-iri.
Nafito Na iske Ayusher Na jirana wai zatamin kwalliya, zanyi gardama saiga mama Rabi’a ta shigi, dole Na zauna akamin simple, nikaina nasan nayi k’yau, kayan da aka bani Na sanya saida Na kallesu Na sake kallo, dan lafayarsuce ta buzaye datasha wani d’inki mai k’ayatarwa, aka d’oramin bak’ar alk’yabba tamkar ta larabawa, tasha golden d’in aiki daga sama har k’asa, a bud’e take dawasu igiyoyi biyu, can sama dakuma tsakkiya. Nidai narasa bakin magana, dan turarema har neman hawarmin kai ya fara, kai nidai a raina nafara tunanin ko tsafi za’ayi danine. Sai gulma muke da idanu ni da Ayusher, dan babu damar yi a fili ga mama Rabi’a a d’akin.
Hannuna ta kama muka fito, aka had’ani da bayi uku nabin bayana, sai ta hud’un a gabana tana mana jagora, masarautar tayi tsit babu yawan hayaniya, saboda d’an Karen sanyi da ake zubawa, kowa ya shige ciki sai d’ai-d’aiku dake kai kawo.
Wani sashe dakecan gefe shima mai k’yau muka Isa, munsha zuwa ta wajen amma bamu ta6a shiga cikiba, Baiwar tayi sallama, dukda ba’a amsaba ta shiga, mukuma muka cigaba dabin bayanta.
K’aton falone mai tarin k’awa da tsari, Wanda ke tabbatar maka a gidan sarauta kake, ganinai duksun durk’ushe k’asa, Na bisu da kallon mamaki sannan Na kalli inda suke fuskanta……………….???

 

 

ALLAH ya gafartama iyayenmu??????

 

 

??HASKE WRITERS ASSO….

?RAINA KAMA…!!?
(Kaga gayya)

Bilyn Abdull ce????

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply