Hausa Novels Raina Kama Book 3 Hausa Novel

Raina Kama Book 3 Page 22


Raina Kama Book 3 Page 22
Viral

Doctor da kansa ya fito yayma Galadima iso cikin office nashi, bayan sun zauna doctor ya kalli Galadima cikin alamun damuwa, yace, “ranka ya dad’e da farko dai ina mai baka hak’uri akan zaluncinsu mijin y’ar uwata, ALLAH yay maka babban samako da sayya agaresu”.
Murmuahi kawai Galadima yayi amma baice komaiba.
Doctor ya kuma gyara zama yana fad’in “Alhmdllh jikin namijin babu wata babbar matsala, yanzuma mun saka masa alurar barcine cikin ruwan danya huta sosai yasamu nutsuwa, daya farka Normal zaku gansa. Ita kuma akwai harbi da akai mata a hannu, amma Alhadullh mun samu nasarar cire harsashin, tafin hannunta kuma shima anji mata ciwo, dan yatsunta Na tsakkiyama duk sun samu karaya, amma shima an gyarashi, maganar gaskiya ranka ya dad’e bazan 6oye makaba, tasamu buguwa akai, dan ALLAH ne ya tak’aita batasamu wata babbar Matsala a brain ba, saidai ahalin yanzu dukkan wani motsi mai k’arar sauti bama buk’atarsa kusa da ita, insha ALLAH inhar za’a kiyaye cikin kwanaki kad’an komai zai iya dai-daita, takuma dawo normal kamarma komai bai faruba, zamu bata dukkan kulawar daya dace da izinin Ubangiji. daganan har kwanaki uku zuwa hud’u zata kasance a halin barci, dan hakanne kawai zai girmama nutsuwar da muke buk’atar ta samu d’in, kai kad’aine kuma zaka ringa shiga d’akin”.
Galadima ya lumshe idonsa tausayin Munaya da yaransu Na kuma mamaye jinin jikinsa da kowanne ga6a, da k’yar ya iya bud’e baki yace, “Doctor! Kana ganin zaku bata dukkan kulawa?. Sannan tanada yara jinjirai, yaya kenan za’ayi?”.
Insha ALLAH ALLAH ranka ya dad’e, dan munada kayan aiki a asibitin mu, dakuma kwararrun likitocin da zasu iya aiki a kowacce k’asa, maganar yara inaga inhar akwai mai kulawa dasu acigaba da basu madara har ALLAH yasa ta farfad’o, saboda mu yanzu matsalarmu kawai shine motsin dazai iya farkar da ita ko wanda zaiyi tasiri cikin brain nata”.
Gyad’a kai kawai Galadima yayi, yabama doctor hannu sukayi musabaha, daganan ya fito.

Kuma ficewa yayi daga cikin asibitin, Sarkin mota yay saurin biyo bayansa, da hannu yamasa alamar yashiga mota suje.
Dukda sarkin mota baisan inda suka nufaba haka ya amsa cikin girmamawa.
Saida suka fara tafiya ya sanar masa inda zasuje.
yana nufi gidansu Munaya dan yaga halin da yaransa suke ciki.

Munubiya da kanta ta fito masa dasu itada Ayusher, tausayin su ya kamashi matuk’a, musamman ma Munubiya, dan tayi wujiga-wujiga.
Cikin k’arfin hali yace, “kiyi hak’uri Sister, muyi musu addu’a ita kad’ai suke buk’ata a wajenmu, yanzu yaza’ayi dasu Amaturrahman? Dan nakula kamarma yunwa sukeji?”. ‘yay maganar yana kallon yaran da sukayi barcin wahala bayan sun gama shan kuka’.
Share hawaye Munubiya tayi. tace, “Yakamata a nemo musu madara, idan kuma Na shayar dasu to shikenan”.
Galadima ya jinjina kansa yana fad’in “Bamusan hikimar da ALLAH ya 6oyeba a gaba, karmuyi ganganci, bara kawai a nemo madarar, dan dolene su kwana anan, ita ba’ason mata hayaniya yanzun, maybe ma harnan da wasu kwanaki, saboda ta bugu a kanta, kuskuren kwakwkwaran motsi zai iya shafar brain nata”.
Munubiya takuma fashewa da kukan tausayin y’ar uwarta, hakama Ayusher, shi kansa Galadima dauriya kawai yakeyi, danma ya 6oye idanunsa cikin eyeglasses shiyyasa basa ganin nasa tsantsar damuwar.
Muftahu ya kira ya sanar masa a samoma su Abdurraheem Madarar da zasu ringa sha.

Daga nan gidan yabaro akan cewar Muftahu zai kawo, yakuma rok’esu akan Abdurraheem, dan ba’ason yacika yawan kuka.

 

A gurguje please????

_________

BAYAN KWANAKI UKU
https://2gnblog.blogspot.com/
A kwanaki ukunnan fad’ar tashin hankalin da bayin ALLAH suke ciki 6ata lokacine, musamman ma Galadima da har wata uwar rama yayi lokaci d’aya, hakama Munubiya da innarsu, Nuren dai ya farka tun washe garin faruwar lamarin, kuma jikinsa Alhmdllh yanata murmurewa, saidai tausayin d’an uwansa daya addabi ransa.
Ko abinci Galadima bayasonci, sai Aunty Mimi ta turkesa tana bashi abaki, shima baifi yay lauma biyarba yace ya k’oshi. tayi-tayi kuma ya kafe, garama idan tea ne, shima sai an had’a da lallashi, babu abinda ke addabar ransa irin damuwar Munaya da yaransa, sukansu duksun rame, danma suna samun tsantsar kulawane ta kowanne fanni.
Papi yazo ya dubasu, hakama su mom da iyayen su Nuren d’in da y’an uwansa, mai martaba ma da daddare yazo cikin 6adda kama ya dubasu.
Mama Fulani ma kullum saitazo, a matan Sarki gimbiya Zulfah Ce kawai batazoba, Dan kunyama ta hanata walwala gaba d’aya a masarautar, Mai martaba kuwa ya hanata hanyar ganinsa gaba d’aya itada y’ay’anta, sai matawalle kawai daya nuna damuwa akan abinda kakansu da mahaifiyarsu suka bada gudunmawa wajen aikatawa wan mahaifinsa, sanan yay ALLAH wadai akan son zuciyarsu, koda yaushe yana tare da Galadima da Muftahu a asibitin, da wata buk’ata ta taso kafin Galadima yayi shi yayita.

A koda yaushe Momma cikin kira take taji yaya jikinsu Munaya, koda wasa ba’a sanarma Abie komaiba, Dan ana ganin cigaba da haske game da jikinsa sosai, ba’a fatan wani abinda zai maido da hannun agogo baya game da ciwon nasa.
Addu’oi kam sosai aka duk’ufa yinsu game da Munaya, wadda har yanzu Galadima ne kawai keda alhakin shiga ya dubata, shima sau d’aya a rana kawai, yau dai duk ake saka ran farkowarta, Dan an dakata damata dukkan wata allura dake sakata barci, saidai kuma har dare babu wani bayani.
Zasu tayar da hankalinsu doctor yace suyi hak’uri, maybe zuwa dare ko safiyar gobe ta farka d’in, danba a sume takeba, barcine kawai da sune suka sakata ta hanyar mata allurar.
Badan hankalin nasu ya kwantaba sukai shirun, har lokacin barinsu asibitin yayi babu wani bayani game da farkawar tata.

Washe gari.

Duk dai yanda akaso farkawar Munaya a ranar sai a washe garine ALLAH ya amince da hakan, Alhmdllh anci nasarar farkawar tata yanda ake buk’ata, saidai ciwukan jikinta a halin yanzu.
Saida doctors suka gama dukkan kai kawonsu naganin komai ya ida daidaita sannan aka bama Galadima damar shiga.

Tamkar mai sand’a haka ya shiga d’akin, tana kwance amma idonta biyu, sai dai a lumshe suke, an kuma cire mata bandejin da aka zagaye mata fuska, sai kad’an aka bari inda ciwon yake.
Durk’usawa yay a gaban gadon, ya kamo hannunta Na haggu dakeda lafiya ya saka nashi ciki, a hankali ta bud’e idanunta saboda jin tattausan hannunsa cikin nata, ga k’amshin turarensa daya mamaye d’akin Wanda ya tabbatar mata da shid’inne, tana shak’a a hankali.
Idonta ta saka cikin nasa, kowanne yakasa koda kwakwkwaran motsi tsawon mintuna 2, a hankali Galadima ya bud’e baki tamkar mai rad’a ko gudun wani ya jisu yace, “Munaayaa I love you, I really love you, I love you more and more my Heartbeat..”
Lumshe idanu Munaya tayi, wasu hawaye suka gangaro daga cikin idanu zuwa gefen kunnuwanta, zuciyarta sai wani irin bugawa take da sauri-sauri, ta kuma damk’e hannunsa cikin nata tana maijin tsigar jikinta Na tashi, jininta sai yamutsawa yake a kowanne 6angare. Kuma bud’e idon tayi a kansa, suka sakarma juna lallausan murmushi ga hawaye Na zuba a idonta har yanzu, shima kwalla sun tarar masa a cikin ido sun saka idon wani k’yalli Na musamman daya kuma sakama munaya wata kasala da tsantsar k’aunarsa, ya lumshe idanunsa alamar tabbatar da abinda ya fad’a mata har cikin ransane ba iya fatar bakiba.
Itama hawayen ta kuma matsowa, ta bud’e baki da k’yar tana cigaba da kwararo hawaye. Tace, “i love you too yalla6ai, I love you so much…”. ‘takai k’arshen maganar wani kukan Na kwace mata.
Hannunta dake rik’e cikin nasa ya sumbata yanamai jin farin ciki, yace, “ki kasance dani Munaya, ki kasance dani har k’arshen rayuwata, ke Katanga tace, haskena ce, farinciki nace, duniyata ce, duk duniya kece mace ta farko bayan mahaifiyata da y’ar uwata danakema so Na musamman, please karki barni uwar y’ay’ana, karki gujeni komai rintsi, nima namiki alk’awarin kasantuwar mu tare har k’arshen numfashi, ki rayu dani, ki mutu dani bugun zuciyata, kamar yanda nima burina kenan a gareki tsawon lokaci”.
Lallai yau daba’a halin ciwo takeba har rawa sai tayi, Wanda bata ta6a tsammani ko tunanin zaisotaba shine yake furta wad’annan dad’ad’an kalamin agareta, shine yake rok’onta ta kasance dashi har k’arshen rayuwarsa?, shine yake kiranta katangarsa?, harskensa, bugun zuciyarsa? Koda a yau tabar duniya ta ribantu da nasarorin masu yawan da wahalar k’ididdiga wajen lissafi.
Galadima dake share mata hawaye da hannayensa ya duk’a ya manna mata kiss a goshi da saman la66a.
Ta kuma bud’e idonta da suke jajur akansa, murmushi suka kuma sakarma juna, ya girgiza mata kansa alamar tabar kukan, idanunta ta lumshe alamar amsawa.
Shikam ya tsura mata idanu ko k’yaftawa bayayi, y’ar ramar da tayi saiya k’ara mata k’yau da k’uruciya, ya shafa k’ananun kitson dake kanta ta kuma bud’e ido tana kallonsa.
Cikin d’age gira d’aya yace, “baki tambayi ina yaraba?”.
Lallausan murmushi ta kuma sakar masa, ta kwanto hannunsa dake sark’e da nata saitin bakinta ta sumbata, sannan ta d’orasa a saman k’irjinta.
Tausayinta ya kamashi sosai, domin jikinta akwai zafi har yanzu, ga abincinsu sunyi matuk’ar cika, Wanda zazza6in nata yanada nasaba da rashinsu gareta, dukda akwai Na zafin ciwo.
Hakan da tayi shima saiya fahimci mitake nufi, kuma duk’owa yay ya sumbaci goshinta, zaiyi magana doctor ya shigo.
Shiru Galadima yay ya juyo yana kallonsa, itama Munaya daga kwancen take kallon doctor ta k’asan ido.
Doctor dake gulma da zuciyarsa yana fad’in lallai ya yarda, duk sarautar Sarki a gaban matarsa bawane, matarce ke zama sarauniya….. (Ga naku Matan kwarai sarakin duniya??????????)
Galadima ya katse tunaninsa ta hanyar buga yatsunsa biyu suka bada sautin d’as-d’as.
Doctor ya dawo hayyacinsa a kunyace. Yace, “sorry ranka ya dad’e, dama Nurse zata goge mata jikine da kuma gasa mata, Dan tasamu sauk’in nauyin da yay mata”.
Murmusawa Galadima yay, ya zare hannunsa daga cikin Na Munaya yana mik’ewa tsaye, hannayensa ya hard’e a k’irji yana kallon doctor da fad’in “Doctor da raina zan bar wasu ganarmin sirrina? Ku kawo kayan buk’ata kawai”.
Doctor daya fahimci Inda zancen Galadima ya nufa saiya murmusa yana cewa “Afuwan ranka ya dad’e”.
Hannu kawai Galadima ya d’aga masa, ya juyo suka had’a ido da Munaya ya d’aga mata gira da cizar lips d’insa.
Baki ta tunzuro masa tana yamutse fuska.
Ya d’aga kafad’a da ta6e baki alamar bashida matsala????????.

Nurses biyu suka shigo da dukkan abinda ake buk’ata, Galadima Na tsaye ko kallon inda suke baiyiba, idonsa nakan matarsa k’yam, sukam sai satar kallonsa sukeyi, suka ajiye suna fad’in “Gashi Ranka ya dad’e”.
hannu kawai ya d’aga musu amma ko tari baiyiba.
Fita saukai cikin takaici, dan sunso yayi musu magana koda sau d’aya ne.

Takawa yay a hankali jikin k’ofar ya Mirza key, sannan ya dawo yana cire link d’in hannun rigar farar shaddarsa da tattarewa zuwa sama.
Suka had’a ido da Munaya tai azamar janyewa cike da kunya.
Murmushin gefen baki yayi yana zama bakin gadon kusa da k’ugumta.
Bottoms d’in jikin green d’in rigar asibitin yafara cirewa a hankali, itadai kunya ta hanata bud’e ido, gashi ya tsareta da idanu, Dan tanajin yanda idanunsa ke yawo cikin jininta, salon daya koma wajen cire bottoms d’in ya sakata dafe hannunsa da hannun haggunta, ta bud’e ido tana kwa6e fuska.
Gira ya d’aga mata, da wani mata salo da kwayar ido.
Babu shiri ta maida idonta ta rufe ruf, tsigar jikinta Na tashi.
A haka dai aka gama cire rigar, yaja bedsheet d’in da ake lullu6a mata a k’afafu ya rufa mata a jiki, sannan ya kuma gyara hannun rigarsa yana tsoma madaidaicin towel d’in cikin ruwan d’umin dake a boket, ya matsa dukda akwai d’an zafi ruwan haka yafara danna mata jiki dashi.
Tanajin zafi, amma kuma tanajin dad’in d’umin ruwan sosai, k’in yarda tayi su had’a ido har aka gama, ya d’auki wani d’an kwalba da mai ke ciki tamkar zaitun, karantawa yay yaga amfaninsa sannan ya zuba a tafin hannunsa yana murzawa, kumajin tattausan hannunsa daya had’u da sul6in mai tayi a k’afafunta, tad’an kuma bud’e ido tana kallonsa. Ganin ba ita yake kalloba saita shagala da kallonsa, babban mutum mai daraja jinin mulki yau shine ke mata hidima irin haka, itako badan kar ace tayi alfahari ba da cika baki da yawa da tace ta more fiye da kowacce mace (??nidai fa bandani, reader’s Ku kun yarda harda Ku??????)?.
Sosai tafara jin dad’in tausar, Dan da salon nutsuwa yake mata, tuni tafara lumshe idanu, hardai barcin yaci galaba a kanta. Sai dai saukar numfashinta yaji a hankali.
Ya kalleta yana murmushi da lumshe idanu, bai bartaba saida ya tabbatar barcin yayi nisa, cikin dabara ya canja mata rigar da suka sakko a kayan domin canji. Ya duk’o ya sumbaci goshinta da bakinta yanajan bedsheets d’in sosai ya kuma lullu6a mata.
Kayan ya maida gefe, ya koma saman kujerar dake gefem gadon ya zauna ya zuba mata idanu, kai kace yaune ya fara ganinta, ya dad’e a haka kafin ya d’auka wayarsa yana dannawa.
A haka Nurses d’in suka masa Knocking, izinin shigowa yabasu, amma sai suka murd’a k’ofar a rufe.
K’aramin tsaki yaja yana muk’ewa, shi yama manta ya rufe. Bud’ewa yay yadawo ya zauna yana d’ora k’afa d’aga kan d’aya da kuma d’aure fuska.
Tuni Nurses d’in suka shiga hankalinsu, cikin risinawa d’aya tamasa bayanin zasu canjama Munaya bandejin jikinta ne.
Batareda ya kallesuba yace, “kuyi a hankali, Dan barci takeyi, idan kuma kunsan zata iya farkawa kubarsa saita tashi ”.
Kallon juna suka, kowacce tad’an ta6e baki, d’ayar tace, “insha ALLAHU bazata tashiba ranka ya dad’e”.
Nanma Kansa kawai ya jinjina musu yacigaba da latsa wayarsa.
Haka sukai wannan aiki a gabansa Dan yak’i fita, data motsa ya zuba musu uwar harara mai rikita hanjin ciki.
Dolensu suka bita a sannu har suka samu kammalawa lafiya, kowacce ta fice a tsorace………….???

ALLAH ya gafartama iyayenmu??????

 

?RAINA KAMA…!!?
(Kaga gayya)

Bilyn Abdull ce????

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply