Hausa Novels Raina Kama Book 3 Hausa Novel

Raina Kama Book 3 Page 21


Raina Kama Book 3 Page 21
Viral

BOOK 3 ????2?0?

……………..Galadima ganima yake kamar Sarkin mota baya Sauri, amma baiyi maganaba, zuciyarsa tamafi motar gudu, dan bugawa take da sauri-sauri tamkar zata fito.
Suna isowa bai saurari an bud’e masaba ya bud’e da kansa yay cikin asibitin, dayake k’aramin asibitin ne, na kud’i su Ahmad suka kaisu, da sauri Nurses d’in dake reception suka masa sannu, tare da gaisheshi, dan 6atancin da aka musu Shida sh Munaya a wancan lokacin yakuma sakawa wad’anda basu sanshiba ma suka sanshi, ga kuma abinda ya faru a kwanakinnan.
Uffan baice da suba yay gaba abinshi, cikin takunnan nasa Na k’asaita da izza, Wanda a yanzu yak’ara armashi da 6acin rai.
Su Ahmad da suka hango tahowarsa duk suka mik’e a tare suma suka nufosa, kallon mamaki yake binsu dashi, suma duksun lura da hakan.
Gebiral yace, “Uncle!”.
Kallonsa Galadima yayi idonsa sakaye cikin eyeglasses daya 6oye jajayen idonsa, kafin wani ya sake rmagana a cikinsu doctor ya iso wajen, duk hankalin su suka maida ga doctor d’in suna tambayar ya jikin Aunty?.
Doctor yace, “ku kwantar da hankalinku, insha ALLAH komai zai zama normal, Ranka ya dad’e barka da zuwa”.
Hannu kawai Galadima ya iya d’aga masa, a lokacinne suma su Abba Hayatudden suka k’araso wajen.
A hankali Galadima ya bud’e baki yace, “Ina matata da d’an uwana?”.
Cikin girmamawa Doctor yace, “Ranka ya dad’e inason magana dakai idan babu damuwa”.
Kamar Galadima bazaiyi maganaba saikuma ya gyara tsayuwa yana fad’in “Inason ganinsu tukunna”.
Doctor yay jimm baice komaiba.
Hakanne ya d’arsa tashin hankali a zukatan kowa Na wajen, Galadima ya yunk’uro zaiyi magana doctor yay saurin taresa ta hanyar fad’in “Amma ranka ya dad’e namijin kawai, dan gaskiya ita ba’ason ayi wani kwakwkwaran motsi a kusa da itane”.
Kowa Na wajen ajiyar zuciya ya sauke, danjin sunada rai, Galadima daya kasa koda motsi doctor ya kuma kalla, zaiyi magana ya d’aga masa hannu alamar baison jin komai.
Abba Hayatudden da Baffi da sukasan halinsa idan yana cikin damuwa suka kalli doctor, baffi yace, “doctor yakamata ko shi kad’aine ya ganta, mu saimu duba Nuridden d’in”.
A sanyaye doctor ya gyad’a kai, dan inda sonsamune babu mai shigar.
Nurse ya had’a su da ita takaisu inda Nuren yake, amma kar ayi hayaniyar dazai farka, dan ana buk’atar yasamu barci sosai.
Doctor kuma yayma Galadima jagora da kansa, amma a k’ofar d’akin suka cire takalmansu, dagasu sai sock’s d’in k’afarsu suka shiga.
‘Dakine madaidaicine da gad’o d’aya, asibitin sunada Kayan aiki babu laifi, tamkar an zarema Galadima lakar jiki haka yake takawa cikin sand’a, doctor ya nuna masa kujera guda d’aya dake kusa da gadon, idonsa a kanta tunda suka shigo, harya zauba yakasa janyewa, tana kwance sam6al a gadon tamkar wata gawa, kanta nad’e da bandeji alamar taji ciwo akan, dan har fuskarta tanuna saboda kumburi da tayi, alik’a mata oxygen a hanci Wanda da alamar shike taimakawa numfaahinta fita, ya maida kallonsa ga damtsen hannunta da shima yake anad’e, sannan kuma tafin hannunta ma haka, wasu hawaye masu zafi suka gangaro tacikin eyeglasses d’in idonsa daya hana ganin tahowarsu tun daga cikin idon.
Ya kalli doctor da shima yake tsaye kansa duk’e a k’asa alamun damuwa, baice komaiba ya mik’e ya fito abinsa, doctor ya biyoshi a baya shima da hanzari.
Da hannu yamasa alamar ya kaisa inda Nuren yake.
Nanma shine yamasa jagora, duk inda suka gitta idanun mutane akansa, oho baimasan sunayiba, abinda ya dameshi shine gabansa.
Su Abba Hayatudden suna d’akin har yanzu, shigowarsu Galadima ya sakasu juyowa suna kallonsa gaba d’aya, ya k’araso gaban gadon idonsa akan Nuren dake barci shima, saidai shi babu bandeji ko d’aya a jikinsa, dan baiji rauniba, dukansa da sukayi a kai ne ya sakashi suma, anama zuwa asibitin babu dad’ewa ya farfad’o, shine sukai masa allurar barci da saka masa k’arin ruwa danya huta, sanda zai farka ya farka da k’arfi a jikinsa..
Galadima ya durk’usa a gaban gadon ya kamo hannun Nuren cikin nasa, yana k’aunar Nuren sosai har cikin ransa, danshi mutumne simple, idan yamaka wani abun bazaka ta6a cewa shi jinin sarauta baneba, ko kad’an bashida damuwa a rayuwarsa, tunba yanzuba Nuren yake bama rayuwarsa gudunmawa, baita6a k’osawa ko gundura da halinsaba, balle yace masa bazaiyiba, saidai inhar abin baida tsarine zai bashi shawaran a canja kokuma ayi haka ko haka……….
Wayarsa datai ring ce ta katse tunaninsa, yad’an karkata yana cirota a aljihun wandon yadinsa, ring d’in daya sakama papi shi kad’aine ya sakashi fahimtar waye, ya mik’e daga gaban gadon yana picking call d’in, saida ya fice a d’akin gaba d’aya sannan ya amsa sallamar da papi yamasa cikeda girmamawa da tsantsar damuwa.
Daga can ajiyar zuciya papi yayi, dan baiyi zaton samun Galadima cikin k’oshin lafiya hakaba, cikin tausasa Murya papi yace, “Muhammad kana inane?”.
Shiru galadima yayi, kamar bazai iya maganaba, saikuma ya bud’e baki da k’yar yace, “papi asibiti”.
“Asibiti kuma? Wanene babu lafiya?”.
Kasa danne kukan daya taho masa yayi, ya fice daga cikin asibitin da sauri, mota ya bud’e ya shiga, ya kife kansa a sitiyari ya fashema papi da kuka mai tsima rai da 6argon jiki, gaba d’aya jikin papi yay sanyi lakwas, saima ya kasa magana shima, yay shiru kawai yana sauraren jarumin jikansa mai yawan hak’uri da juriya akan abu, saida yay kusan mintuna biyu yanayi, papi ya tabbatar nauyin da zuciyar galadima tayi ta ragu sai yay gyaran murya, cikin tausasa harshe yace, “Muhammad Sameer mike faruwane? Kokuwa kukan farin cikin cikar burine?”.
Da k’yar Galadima ya iya bud’e baki yace, “papi yanzunan duk abinda suka aikata a gareni tsawon shekaru bai ishesuba? Saisunyi yunk’urin kashemin d’an uwana da matata? Papi minayi musu da zaifi haka? Miye laifin mahaifina danyak’i goyama k’arya da cin amana baya? Miye laifinsa danya zama shugaba? Bayan hakan ba shirinsa bane tsarin ALLAH ne? Miyasa suka manta babu abinda ke dawwama sai ALLAH, papi inhar matata ko d’an uwana suka rasa ransu wlhy bazan hak’uraba, saina kashesu da hannuna nima s……..”
Dakatar dashi papi yay ta hanyar kiran sunansa.
Galadima ya amsa masa da k’yar.
“Kayi hak’uri Muhammad kaji, ALLAH yana tare da masu hak’uri, Hayatudden ya sanarmin komai, ALLAH yabasu lafiya, ba shari’ar duniya bace kawai shari’a, akwai babba wadda babban alk’ali zaima kowa, koba komai ALLAH ya kunyatasu tun a duniya, kowa yasan misuka aikata, kuma ka dak’ilesu suda masu burin aikata irin nasu, ka ringa tunawa akwai tonon asirin dayafi wannan, harma abinda yafi wannan da suka aikata akwai babbar kotu mai cikeda d’unbin jama’a da babban alk’ali a gaba, banason kabar wannan abin yayma zuciyarka tasiri haryakai ga kadaka k’asa, sannan karna kumajin kayi kuka, ka kwantar da hankalinka muci gaba da musu addu’a, insha ALLAH gobe zan shigo garin”.
Gyad’a kai Galadima yayi tamkar yana gabansa, papi yakuma kwantar masa da hankali da nasiha mai ratsa jiki, saida ya tabbatar hankalinsa ya kwanta sannan ya barsa….

Ya jingina da kujerar yanamai lumshe idanu, wata nutsuwa ta musamman Na ratsa jinin jikinsa da zuciyarsa, knocking glass d’in da akayi ya sakashi bud’e idanu a hankali, ganin sarkin motane saiya sauke glass d’in k’asa, cikin girmamawa sarkin mota ya mik’o masa gorar ruwa.
Bai musaba ya kar6a yana gyad’a masa kai alamar ya gode.
Sosai yasha ruwan kuwa, wata nutsuwa takuma saukar masa, ya kuma d’aukar kamar 5minutes ya fito daga motar, ya koma cikin asibitin, yanson ganawa da doctor d’in, idan yaji bai gamsu da aikinsaba dolene yasan mai yuwuwa.

Yana shigowa su Ahmad suka k’araso gareshi suna gaidashi da jajanta masa.
Cikin k’arfin hali yace, “baku tafi gida bane?”.
Sarkin mota dake tsaye kusa dasu yace, “Ranka ya dad’e ai Ahmad shine ya taimakeni nakawo camera d’in kotu d’azun”.
Da mamaki Galadima ya kalli Ahmad yana nunashi da d’an yatsa alamar kaid’in?.
Murmushi Ahmad yayi yana gyara tsayuwa. yace, “Uncle bayan fitowa daga kotune za’a hutunnan sai naji wani yaron su Abbana yana waya akan atare su Aunty a kar6a Camera d’in, dan basa buk’atar ta k’araso Court d’in, to hakan danaji shine Na k’arasa garesa Na bigi cikinsa akan zancen”.
“nake cemasa zamuje ni da su Ahakam muma a kwato Camera d’in damu, so hakan dayaji saiya d’auka da gaske tare nake dasu, shine yabani key d’in mashin. Ina ajiye driver d’inka, sai mukazo asibiti ni da Yassar muka sanarma da Uncle d’ina, shine ya bimu da Ambulance har wajen da abun ya faru muka d’akkosu”.
Galadima ya kamo hannun Ahmad ya rungumesa, yayma su Yassar dake kallonsu alamar suma suzo, cike da farin ciki suma duk sukazo jikinsa.

 

__________
https://2gnblog.blogspot.com/

Hankalin mai martaba a matuk’ar tashe yake, jin wai dan kawai yayi mulki wasu suka bada gudunmawa domin durk’usar da d’an uwansa, “hazbinallahu wa ni’imal wakil” wannan wace iriyar masiface hakan?.
Sai safa da marwa yakeyi a bedroom d’insa, idanunsa Na kwarar da hawayen tausayin d’an uwansa da Galadima, ALLAH Sarki mahaifiyarsa, yadad’e yana zarginta akan ciwon d’an uwansa, Ashe babu hannunta a ciki, son zuciyar mahaifinta ne, Wanda a yanzu haka tsufa ya kamashi sosai. Waya ya d’auka ya kira Abba hayatuddeen danyaji wane hali d’an d’an uwansa yake cikine? Dan yayi tsumayen shigowarsu masarautar amma yaji shiru.
Bugu biyu Abba Hayatudden ya d’aga. Mai martaba ya tambayeshi suna inane?.
Abba hayatudden ya amsa masa da vewar gasu a cikin asibiti, Dan mutanen su Alhaji Mansur sun saka an tare matar galadima a hanya itada Nuridden yayin kawo Camera Court.
Kasa magana mai martaba yayi, saboda jin kuma wani sabon zaluncin, Wanda suka aikata baya baima ishesuba kenan.
Abba Hayatudden ma bai kuma cewa komaiba saboda yasan ran yayan nasa ya 6aci.

Mama Fulani kanta yau cikin damuwa take, bata ta6a tunanin mahaifinta zai iya aikata hakanba, dukda tsantsar son datake da burin y’ay’anta suyi mulki bazataso duk’usar da Saifudden akan hakanba, shekaru 26 bawan ALLAH Na kwance yana jiyya tamkar gawa, banbancinsa da gawar fitar numfashi, wannan wane irin son zuciyane su jinin sarauta sukeyi? Shikenan saboda sarauta sai aita halaka juna? “Ni Marawuyya wannan wane irin burine mai cutar da imani…….”

Lallai zato zunubine koda ya zama gaskiya??, kiyi hak’uri mama Fulani munata zarginki Ashe ba haka bane????????.

 

………………………..?

A gidansu Munaya ma hankalinsu a matuk’ar tashe yake, gasu Abdurraheem nata kuka, dan tunda Munaya tabar gidan suke kuka, kukansu ya tada hankalin Munubiya dasu Inna sosai, lokacin da aka harbi Munaya bak’aramar fad’uwa gaban Munubiya tayiba, ta mik’e a zabure tana dafe k’irji, number Munaya tashiga nema, dan taji a jikinta wani mummunan abu ya faru da y’ar uwarta.

Lokacin da labarin abinda ya faru da Munayar ya iso garesu mafi yawan jama’ar gidan saida suka koka, Dady kuma ya hana kowa zuwa asibitin, saisu mazan kawai sukai shirin zuwa, gashi basusan wane asibitin bane.

__________

Iyalan su waziri hankalinsu a matuk’ar tashe yake, hakama su Alhaji Sageer, ga duniya tanata ALLAH wadai dasu, gaba d’aya yau kowacce kafar yad’a labarai da social media maganar kenan, su kansu sauran manyan kowa ya shiga hankalinsa, dan lamarin yayi matuk’ar girgozasu, suna yabama basirar Galadima matuk’a, gashi yabi ta hanyar da babu Wanda yata6a zaton zata 6ille masa yayi nasara, inhar za’a iya samun irinsa a yau, to lallai wataran za’a samo Wanda ya fisa ma.

………………..?

Yanda masarautar su Galadima take a harmutse gameda wannan lamari haka tasu papi ma ta gama harmutsewa, dan lamarin ba’a cewa komai, cin amanar da waziransu sukayi yayi matuk’ar girgiza masarautun, bakajin komai sai gutsiri tsomar bayi da dogarai, harma da manyan gidan ba’a barsu a bayaba.
Tashin hankalin da papi da inno suke ciki ba’a magana, ga Sauban ya tasasu gaba yanata kukan son zuwa yaga halin da Munaya da Nuren suke ciki, harma da yayansa.

Dukda an hana fad’ama Su Momma amma saida labarin yakai musu, aranar aka nemama Aunty Mimi ticket d’in tahowa Nigeria, Samha nata kuka itada Khaleel zasu biyota, amma bata sauraresuba, dan hankalinta a matuk’ar tashe yake.

……………………….?

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply