Hausa Novels Raina Kama Book 3 Hausa Novel

Raina Kama Book 3 Page 18


Raina Kama Book 3 Page 18
Viral

BOOK 3 ????1?8?

……………..Yauma dai kotun ba’a cewa komai, wad’anda ma basuzo zaman farkoba yau sunzo, Dan su sir Isa duk suna wajen da muk’arabansa, hakama tawagarsu Tanderu, Dan suma lauyansu a cewarsa yau yazo da sabon shiri, ranarma an mamesa ne kawai.

Galadima yagama shirinsa tsaf cikin wani lallausan yadi sky blue dayasha d’inkin boda, Dan rigar iyakarta Rabin cinyarsa, kayan sunmasa k’yau matuk’a, danya fito ainahinsa Na jinin Hausa Fulani, ya Mirza hularsa sky blue itama, fuskarnan tayi fayau Dan hardasu gyaran fuska yayi abinsa, danma ya tabbatarma mak’iya yana cikin farinciki fiye da zatonsu, yana cikin saka sock’s Nuren ya lek’o yana fad’in “Brother ka hanzartafa mun makara”.
“umhum” kawai yace masa yacigaba da saka kayansa a tsanake kamar yanda yafara, danshi komai saurin dazaiyi akan Abu to anutse zaiyi abinnan, ganin haka sai kawai Nuren ya ida shigowa, ya durk’usa gabansa yana kama k’afar daya sakama sock’s d’in ya saka masa takalmi.
Baki Galadima ya tsa6e yana cewa, “kaifa shegen gaggawane dakai wlhy, ni bansan INA kuka kwaso halinnanba, haka Momma da Aunty Mimi suke, komai kunfison mutum yanayi kamar wani mazari”.
Nuren ya sanya dariya yana saka masa d’aya takalmin, yace, “to sokake muke Abu kamar marasa laka a jiki? Munaya dai kam tana fama…”
Hararsa yayi, hakanne ya hana Nuren k’arasawa, Galadima daya wani tsaresa da ido yace, “Tana fama da k’aniyarka”.
Nuren ya mik’e yana fad’in “oho maka dai, mu ka fito su sarkin mota tuni sukazo”.
Mik’ewa yay ya d’auki turarensa Na kullum a bag d’in daya had’o kaya ya fesa, k’amshin ya gauraye ko ina, waya d’aya ya zura a aljihu ya fito.
Su Ahakam duk shagala sukayi da kallonsa, a ransu suna matuk’ar yaba tsarinsa, komai nasa abin birgewane, kamar yanda ya saba haka yabasu hannu da kansa sukayi musabaha dukda suna nok’ewa alamar jin kunya da girmamawa a gareshi, shikam babu ruwansa, inhar bakasan halinsa bane dolene tashin farko ka jefeshi da kalmar girman kai.
Su Farhat ma suka gaisheshi cikin risinawa, wani miskilin murmushi yamusu yana d’aga musu hannu kawai, ya kalli Saleem tare da masa nuni yabama kowa kayansa.
Saleem ya amsa da cewar “ok boss”.
Bag d’in da wayoyinsu ke ciki ya d’akko, amma sai sukace sukam ya barsu, Dan inhar ba’a yanke hukunci ba zasu dawo su cigaba da zama dasu, Dan zama da Galadima akwai dad’i, kuma ko an yanke hukuncima masarauta zasu bishi.
Shi dariyama abin ya bashi, hakanne yasakashi bubbuga kafad’ar Yassar dake kusa dashi yana sakin murmushin da har hakwaransa ke bayyana, ya wucesu yana sauka daga benen cikin takunsa Na birgewa.
Suma duk binsa sukayi a baya, komai nasa Saleem ya tattaroshi, dan bazai sake dawowa gidanba koda ba’a yanke hukunci ba kuwa.
Harun dai anyi laushi matuk’a, dan maganarma yanzu ba iyayin mai k’arfi yakeba, saboda saiya gadama yakecin abinci, babu kuma mai sakashi dole yaci.
Cikar k’ofar gidan tabama Galadima mamaki matuk’a, yakuma d’aure fuska tamkar bai ta6a dariya ba, musamman yanda duk aka zubo masa ido, a Bayama an kallesa balle yanzu da yayi abun kallon, y’an sanda da dogaransa da suka zo d’aukarsa tun d’azun sai k’ok’arin hana y’an jarida dakeson zuwa ga Galadima sukeyi, amma suna k’ok’arin kutsowa.
Tsaye Galadima yayi ya zuba dukkan hannayensa a aljihu, saida yaga shigarsu Rahma mota dasu alhaji darma sannan yanufi inda sarkin mota ya bud’e masa, y’an jaridar daketa masa tambaya ko kallo basu isheshiba ya shige mota abinsa, yayinda Muftahu ya zauna gefensa, Nuren Na a gaba.
Mortar y’an sanda Na a gabansu da Bayansu, a haka akayi tafiyar.
Sauran y’an sandan da aka bari suka shiga gidan domin d’akko gawar Ahmad, amma sun bincika lungu da sak’o babuma alamar an cutar da wani, sai harbi guda d’aya daya shiga jikin bango, (shima Wanda Galadima yayine sanda ya tsoratasu da cewar ya kashe Ahmad), basu samu komaiba dazai nuna Galadima d’an ta’addane, sai suka fito suna kulle gidan, amma basu tafiba harsai kotu tabada damar hakan.

……………………….?

Sun Isa Court d’in, inda Galadima da Nuren da Muftahu ne kawai suka Shiga, yaran dasu Alhaji Darma an kaisu wani d’akine kusada wajen.

Takun takalman Galadima dake tafiya cikin tsantsar izza da nuna jinin mulki ya saka dukkan jama’ar kotun zuba masa idanu, shikam ya had’e fuska tamkar hadarin gabas Na tsakkiyar ogusta dabaya d’aga k’afar zubar ruwa, kallon kowa bayayi, gashi ya toshe idanu da Google eyeglasses d’insa da babu mai kallon kwayar idonsa.
A kujerar farko irin wadda su Alhaji Mamman ke zaune shima aka nuna masa shida Nuren da Muftahu.
Wani zama yayi dake tabbatarma da mak’iya shid’infa sarakine, gaba da baya kuma.
Hakan ya k’ona zuciyar su Alhaji balala matuk’a, amma babu yanda zasuyi.

Zaman Galadima babu jimawa saiga alk’ali ya fito, kowa ya mik’e domin girmamawa, saida ya zauna sannan duk aka zauna.
Kotun tayi shiru kowa ya zubama alk’ali idanu, yagama dube-duben ta kardun gabansa sannan ya d’ago ido yana kallon jama’a, yace, “Yau shari’ar zata tafine kai tsaye batare da shigar lauyoyi Na kowanne 6angare a tsakiyaba, Dan haka muna buk’atar Wanda yay k’ara, da wad’anda ake k’ara a gaban kotu”.
A hargitse su alhaji Sageer suke kallon kallo, hakama lauyansu dukya shiga rud’ani, saboda mugun shirin dayayo yau akumace ba haka za’ayiba.
Shikam Galadima wani mugun murmushi yayi yana kallonsu Alhaji mansur d’in damusu wata inkiya da yatsu biyu alamar a kafta, sannan ya mik’e.
Dole suma duk suka mik’e inda aka buk’aci ganinsu, dukda wajen yamusu kad’anma.

Alk’ali ya kalli galadima. Yace, “kaine Wanda kai k’ara, Dan haka munason jin shin minene mafarin wannan takun sak’a kai tsaye?”.
Murmushi galadima yayi, ya cire eyeglasses d’in idonsa ya saka cikin aljihu, tareda zaro handkerchief ya goge fuskarsa, yasa hannayensa biyu ya dafe katakon gabansa yana jifan waziri mahaifin Harun dawani mugun kallon daya hargitsa y’an cikinsa da tunaninsa, hakanne yasaka mutane kallon waziri suma, duk sai yaji ya muzanta.
Galadima ya ta6e baki yana janye idonsa dad’an cije lips, cikin k’asaitacciyar muryarsa yace, “ya mai shari’a labarina mai tsawone kwarai da gaske, sannan cike yake da abubuwan ban mamaki da takaici masu tarin hargitsi, duk da nasan kowa yasan sunana amma zan sake maimaitawa, sunana Muhammad Sameer Saifuddin Abubakar, gidan sarauta Na fito, mahaifina shine tsohon Sarki da k’addarar ciwo ta kwantar tsawon wasu shekaru, amma lallai da sanadi, wannan kuma sanadin shine Na d’auki tsawon shekaru tundaga tasowata har zuwa yau ina nema. tun daga lokacin dana mallaki hankalin kaina nasan minene matsalar mahaifina natashi da burin d’aukar fansa, sai dai kuma tayaya? Wannan shine yayta wahalar da Muhammad Sameer a tsawon shekaru”. Galadima ya k’are maganar idonsa Na ciko da hawaye, yay murmushin takaici yana jinjina kansa da had’iye hawayen.
Hakanne yasaka jikin wasu fara yin sanyi, musamman wad’anda suka k’ullaceshi da farko.
Galadima ya cigaba da fad’in, “Ban taso maraya ba, amma nayi rayuwa irinta marayun, ALLAH shine gatana saikuma mahaifiyata da kakana da suka tsaya tsayin daka wajen tsayamin nazama jarumi wajen sanin wahalhalun rayuwa Na yau da kullum, duk Sana’a mai wahala kad’ance banyitaba a k’asar daba tawaba, gakuma gefe ana gwagwarmayar Neman ilimi, ga burin son sanin suwaye suka durk’usarmin da mahaifi?, ban cutar da kaina wajen nutsuwa Na fahimci rayuwa ba, hakama nabama karatuna muhimmanci saboda k’aunarsa da nakeyi, duk da banida burin yin aiki a k’ark’ashin kowa, Alhamdllh yanzu haka inada Company Na had’aka da duk shekarar duniya yake fidda wayoyin Hannu da computers dakan zagaya cikin duniya, ina alfahar da samun cikar burina sosai, Na dad’e ina bulayin Neman hanyar bincike akan abinda yafaru da Abie na, alokacin mutum d’ayane zuwa biyu ke bani gudun mawa, wato lauyan mahaifina, baffina Barrister Usman Audu, sai kakana Sarki Abdul-fatah. Ganin inata wahala sanan babu wani haske a cikin lamarin sai suka bani shawarar mizai hana a nemamin aiki k’ark’ashin wata hukumar tsaro, da farko ban aminceba, Dan irin wad’annan ayyukan basa wani birgeni, hasalima haushin masu yinsa nakeyi, Dan sun gaza binciko Wanda ya cutarmin da Abie na. A tashin farko dana nuna banaso Papi da Baffi sun k’yaleni, basu sake min magana ba, sai wata rana kwatsam wani Abu yafaru anan Nigeria, wasu y’an ta’adda sukayi mummunar 6arna a sirrin gwamnati, k’ark’ashin hukumar DSS. wannan 6arna ta rikita Nigeria sosai a lokacin, shekaru 10 kenan inhar ban mantaba, a lokacin nagama bautar k’asata anan Nigeria ina shirin komawa india, bansan ya akayi sukasan nasan Computer ba, har masarauta akazo aka rok’i mai martaba akan Na taimakesu. Da farko kam naso bijirewa amma babu abinda iyayena zasuce nayishi banyiba inhar bai sa6a shari’a ba, nasanma bazasu sakani wannanba, bisa umarnin mai martaba Na amince da gwadawa idan zan iya, haka akaje dani headquarters d’insu, tun hawan Computers d’in danai a tashin farko Na gane da had’in kan waaunsu aka kwashi bayanan, sannan masu kula da Computers d’in sunada buk’atar k’arin ilimi ma gaba d’aya. Cikin sauk’i Na d’akko bayanan da aka d’auka Na dawo musu dashi, sannan nasaka musu securitys masu tsaurin gaske daba wani mahaluki dazai kuma musu irin wannan kutsen. Ni ban d’auki abinda nayi matsayin komaiba, amma agaresu sun girmamashi, sunkuma biyoni har gida da rok’on kasancewa a cikinsu amma nak’i Sam, nama tattara Na koma India, Ashe sunata bibiyata ta wajen kakana, to shima dama yana burin nayi aikin, Dan haka yabasu goyon baya, sannan yaje har India ya sameni da batun, ya nunamin ta wannan hanyarne kawai zan iya binciko abinda ya faru da mahaifina cikin sauk’i, hakama Baffi ya fad’amin a lokacin, Na zauna nayi nazari dakuma samun kwarin gwiwa daga Mahaifiyata. Rana d’aya sai nima naji yakamata Na amince, Dan haka Na amince, tundaga lokacin nashiga cikin hukumar CID nima, saidai ina musu aikine cikin sirri, a hukumarma ba kowa yasan daniba, tunda ni komai ta computer nake gudanar dashi. Sir Isa Maharazu shine ya taimaka min wajen binciko file Na binciken case d’in mahaifina, Wanda tun kusan shekaru 8 mai kula da case d’in ya rasu, Wanda kuma suke ta fannin y’an sanda suma sukayi shiru, daganan aka ajiye case d’in gefe kawai. Tun a file d’in nafara cin karo da sunayen wasu daga cikinsu Alhaji Lawan tanderu. Nasha mamaki kwarai da gaske amma sai banyi wani yunk’uriba, ina wata shida da aiki wani yaso min kutse a cikin Computer, ta silarsa nagano uban gidansa, har zuwa Kansu Marigayi Alhaji Labaran kachia. Tundagafa wannan lokacin saina tsananta bincike da kwakwalwa dakuma tannin aiki, bisa taimakon sir Isa, mun baza yara cikinsu Tanderu batare da sunsaniba, kullum kuma cikin bin diddigin motsinsu suke. Kwatsam sai Tanderu ya rasu sanadin had’in mota, babu jimawa shima Alhaji Labaran khacia ALLAH yamasa rasuwa sanadin rashin lafiya. daga nan saina d’an dakatama gaba d’aya da wani bincike Na koma gefa Na zuba musu ido kawai.
Saida Na d’auki kusan shekaru biyu ban sake wani yunk’uriba sai kwatsam muka wayi gari mijin Yayata Haneefa yayi had’arin Mota, saidai kuma a ranar ne aka turomin massage daya nuna accident d’in nashi akwai saka hannu a ciki, dayake bai rasuba a lokacin sai a asibiti bayan awanni uku da kaisa, Alhaji shehu Darma abokinsa ne Na kut da k’ut sannan d’an uwansa, Dan haka yana tare damu a wajen, saina matsanta akan tambayarsa kozai fad’amin akan miya faru dashi kafin had’arin? Bai iya cemin komaiba sai murmushin k’arfin hali da yayi yana kallon Alhaji shehu har numfashinsa ya k’are, wannan kallo ya tsayamin a rai sosai, Dan nagaza mantawa dashi, abinda Yakuma k’arfafa min zargin Alhaji shehu shine Aunty Mimi Na fita daga takaba sai Yace yanason aurenta, nine Na hana, nama tattarata gaba d’aya itada y’ay’anta Na maidasu india, dukda dangin mahaifin yaran sunso d’aukarsu suma. Dama can lokaci-lokaci Alhaji shehu yakanbi mijin Aunty Mimi suje duba Abie, dan haka ko bayan rasuwarsa bai daina zuwaba, abinda na fara fahimta shine Samha d’iyar marigayi tana tsoron Alhaji shehu, amma shi yana tsananin nuna mata kulawa dayin kaffa-kaffa da ita a gaban mutane. Wannan ma yasa na kuma saka ido a kansa, abinda Na fara karo dashi shine Alhaji shehu yana tursasa Samha ta hanyar mata barazana akan ta d’akko masa wasu sirrikana”. Galadima ya murmusa cikin takaici yana gyara tsayuwa da goge fuskarsa da handkerchief. Yaciga da fad’in,
“Tunda Na fahimci hakan saina jata a jikina, nakuma dinga ajiye mata dukkan abinda yasaka ta d’akko, itako data gani saita tura masa saboda tsoron barazanar da yake mata. Suma sauran Na cigaba da bibiyarsu suda ayyukansu, so banida matsala da sauran mugayen halayyarsu, nidai kawai wadda ta had’amu nakeson Sani, Dan Na gano sun gana da mahaifina ana gobe abinda ya sameshi zai sameshi, kuma yafito daga d’akin tattaunawar ransa a 6ace. Batanci da akaimin a shekara d’aya data wuce cikin jaridar manuniya shine mafarin yalwatur haske a matsalolina, dukda Na fahimci ankai tsawon shekaru ana bibiyar dukkan al’amurana, kuma inhar Nazo k’asarnan kullum cikin bibiyata ake, domin rufe bakin mak’iyana Na auri wadda sukaso sakawa a matsalar dabatajiba bata ganiba, wadda a yanzu Alhmdllh itace uwar y’ay’ana, nasan hakan ya girgizasu a lokacin kwarai da gaske, adalilin zama da ita nama fahimci abinda ban fahimtaba da farko, Dan da Duk zargina ko da itane aka had’a kai wajen Neman 6atamin suna, amma sainaga dukba haka baneba, ya mai shari’a Alhaji Auwal Fharuk sai shine surikina mahaifin matata, kuma anyi yink’urin kasheshi watanni kusan 7 da suka shige, saidai ALLAH ya k’addara yanada sauran kwanaki a gaba, bisa dalilin yun k’urin kisansa ne kuma Na fara karo da alak’ar case d’in mahaifina dashi, hakan kuma tafaru bisa sanadin matata, data dinga zak’ulomin wasu masu alak’a da mahaifinta kuma Na jikinsu tanderu, irinsu Mamman k’afur, Alhaji Halluru, saikuma daga baya ga SD, wato Alhaji shehu Darma, Wanda shine aka saka yake bibiyar Alhaji Auwal Fharuk yana masa barazana, satar yarana da akayi a ranar sunansu ta kawo bayyanar aminina d’an uwana cikin case d’in mahaifina daban ta6a tunanin kasantuwarsa a cikiba, wato Harun d’an gidan waziri, shine wazirin mahaifina shine kuma wazirin Sarki Na yanzu, ina cikin rud’anin Hakan saikuma ga Alhaji Rabilu ya bayyana a gareni shida Badi d’a ga mai dokuna a masarautarmu, Wanda tun ina k’arami Na sanshi, amma daga baya ya 6ata 6at. Bayanan wad’annan bayin ALLAH da bincikena Na had’a suka tabbatar min da zargina akan wad’annan mutanen, nasan abune mai wahalar gaske samunsu cikin sauk’i da fahimtata da duniya zatayi akan zargin danake musu, shiyyasa naza6i yin Garkuwa da yaransu bisa tursasasu tilas sufad’i abinda ke ransu da Wanda suka aikata. Dukkan Wanda ya shigo cikin labarin nan nawa akwaishi a wajennan, mijin yayatane kawai bayada rai sai mahaifan Badi, dakuma wasu daga cikinsu da sukabar duniya, Dan haka ina rok’on wannan kotu data nemo dukkan Wanda Na ambata domin jin ta bakinsa”.

Alk’ali ai yama kasa magana, sai kad’a kai kawai yake mamaki da al’ajabi Na cinsa, yayinda kotu tayi tsit kowa yana k’ullawa da kwancewa da tausayin Galadima, irinsu Alhaji Halluru kam ai cikine ya d’uri ruwa, sunsan dai tasu tagama k’arewa kam, Dan yau ranar bankad’a Ce da walle-walle.
Alk’ali yad’anyi rubuce-rubucensa sannan ya buk’aci ganin Badi da Alhaji Rabilu, Galadima kuma yaje ya zauna.
Alhaji Rabilu da Badi sun bayyana a gaban kotu, hakan ya kuma hargitsa hanjin cikin Waziri, yana mamakin dama Badi bai mutuba? Amma su hak’ilu sukazo sukace ya mutu a wancan lokacin, dan agabansu mai besfa ya kad’eshi, innalillahi ya shiga ambata a zuciyarsa, sai zufa ke jik’eshi, sauk’insa ma akwai malun-malun da rawani a jikinsa, Abba Hayatudden kallonsa kawai yake da tsantsar tsana da mamakinsa.
Duk yanda Badi da Alhaji Rabilu sukaima Galadima bayani haka suka maimaita a gaban kotu, wasu harda hawayen tausayinsu suke matsewa, Alk’ali yace, a kawo Alhaji Auwal Fharuk Dan Badi yaga idan shine yabama camera.
An kawo Abba, Wanda Alhmdllh jikinsa yayi sauk’i sosai, saidai abinda ba’a rasaba Na k’arfi, kallo d’aya Badi yayma Abba ya ganeshi Dan bai canja masaba sai canjin girma irinnan shekaru, hakama Abba ya gane Badi sarai Dan shima d’in bai canja masanba, aiko suka rungume juna kowa yana hawaye, Abba yana fad’in “Bawan ALLAH Dama baka mutuba a waccan ranar?”.
Shima Badi cikin kuka yace, “ban mutuba, sai daga baya ne Na farfad’o a wajen”.
Alk’ali ya ankarar dasu cewa a kotu suke, kotu kuma Na buk’ar jin bayani daga bakin Abba, ta Yaya Camera ta dawo hannunsa?.
Abba ya dai-daita tsayuwarsa sannan ya gabatar da kansa ga kotu, ya d’ora da fad’in “shekaru 22 kenan da suka shud’e wannan camera take a hannuna ranka ya dad’e, nakuma sametane ta hanyar kad’e wannan bawan ALLAH danayi da abin hawana a wancan lokacin, saboda ya shigo hanya yana matsanancin gudun dabansan mafariba sai yanzu danaji a ya fad’a a gaban kotu. bayan na bigeshi numfashinsa Na Nuna alamar bankwana da gangar jikinsa ya d’auki wannan camera yabani acikin akwati da sunan amana, yakuma ambatamin sunan wad’anda zanba kamar yanda yafad’a, daganan numfashinsa ya tsaya cak da aiki, ina cikin k’ok’arin taimakonsa saiga wasu mutane da gudu da makamai sun dosoni, tsoro naji, Dan inada tabbacin shima sune suka biyoshi, saboda son isar da amanar daya bani inaji ina gani badan nasoba Na tsallakesa Na gudu, Dan nasandai zasu iya kwatar abinda yabani d’in. tunda camera d’in nan ta dawo hannuna ban sake barci mai dad’iba, kullum burina da tunanina tayaya zan Isar da amanarta Na huta, tsawon shekaru ban ta6a fuskantar wani k’alubale akanta ba, Dan ko iyalina babu Wanda yasan da zamanta a hannuna, matata tasha tambayata idan taganni cikin damuwa amma banta6a fad’a mataba, kwatsam cikin laluben Wanda zan bamawa sai Marigayi Alhaji Abdul-hakeem Uba tsohon Governor d’inmu ya fad’omin, Dan ganin yana auren d’iyar tsohon Sarki wadda tana d’aya daga cikin wad’anda akace nabamawa, to lallai anan Alhaji shehu SD yasan Camera Na hannuna, Dan tabbas yaji zancen da mukayi da Alhaji Abdul-hakeem d’in ta hanyar la6ewa, aranar da mukayi zan bama Alhaji Abdul-hakeem camera ya damk’ata ga matarsa sai aka samu akasi wani aiki ya tasomin Na manta ban fito da camera ba, amma mun had’u da shi marigayi Alhaji Abdul-hakeem Na bashi hak’uri da sanar masa uzirina, shikuma SD a tunaninsu nabama Alhaji Abdul-Hakeem wannan camera, shine suka hari rayuwarsa da nufin kar6a kafin ya kaima matarsa, inaga daga baya da suka fahimci babu Camera d’in a hannunsa shine suka juyo kaina. Sunta matsama rayuwata da barazana iri-iri, kiran waya da sauransu, duk number da suka kirani da ita gobe bada ita zasu kirani ba, hakkane ya sakani ware sim card guda kawai dansu, babu Wanda ya sanni dashi, sai matata Dana saka number cikin wayarta batare da itama tasan hakanba, nayi hakanne saboda watarana koda ALLAH yabasu nasarar kasheni d’in. A lokacin da akaima yarana 6atanci da Galadima lallai hankalina ya tashi matuk’a, amma daga baya danayi nazari saina gano maybe su SD ne suka aikata hakan domin 6atamin suna, hukuncin ALLAH kuma saigashi mai martaba Sarki jalaludden da mai martaba Sarki Abdul-fatah sunzo nemawa d’ansu Galadima auren yarinyata da abin yafaru akanta, dukda a 6adda kama sukazomin ni sarai Na ganesu, amma ko y’an uwana ban sanarmawaba, abinda yabani k’arfin gwiwar aurar musu da yarinyata shine Isar da amanar hannuna cikin sauk’i, saikuma aminin mahaifina Baba mai kanwa yace nabasu, Dan shine kawai yasan da zaman Camera a hannuna, shima bani Na sanar masaba, bankuma San a ina yajiba. A randa za’akai y’ata gidan mijinta a ranar Na saka wannan camera da takarda cikin wani kwali Na sakashi a kayanta batare da tasaniba, bansaniba kota gani? Dan cikin gifts d’inta data samu a hannun abokan mijinta ranar dinner d’in auranta Na sakashi, nabama d’an uwantane Abdul-Hameed babban d’ana yabata batare da shima ya san minene a ciki ba. Hikimata anan idan tagani tabama mijinta batare da kace Na ceba. SD bashikad’ai ke bibiyar rayuwata ba, Dan akwai masu sakashi yazomin da farashin kud’i masu tsoka akan camera d’in amma nayi kunnen uwar shegu dasu, hakanne yasakasu k’ok’arin salwantar da rayuwata wai tunda Na hanasu camera, nasan sunajin tsorone saboda Na kusantu da Galadima a lokacin, zan kuma iya bashi camera d’in, saidai abinda basu ma saniba tuni Camera d’in tabar hannuna. Alhaji Halluru abokinane Dan school mate d’inane, ada babu wata alak’a mai k’arfin tsakanina dashi, amma daga baya sai yayta Jana a jikinsa, ban fahimci manufarsaba dagashi har Alhaji Mamman, Dan da zuciya d’aya ni nake zaune dasu. Sai wannan karon da suka tabbatarmin da zulwa jahainin fuskarsu, sannan suka tursasa y’ay’ana biyu Dana d’auka nabama y’ay’ana Alhaji Halluru aure saboda yarda wai su d’akko musu camera a d’akina kosu kashesu dani dakuma iyayensu mata, sun razanasu da cewar sun dasa bomb a gidana, agabana duk suka sanar musu a waya. Abinda yasa ban damuba nasan k’arya suke, sannan Camera d’inma bata gidan, duk k’ok’arin lalatama Galadima sirrika da sukayi agabana sukayishi, amma ALLAH baibasu nasaraba, jin asirinsu zai Toni ta hanyar Garkuwa da y’ay’ansu da Galadima yayi shine suka shak’amin abinda ban saniba, daganan ban kuma Sanin ina kaina yakeba sai a asibiti yamai shari’a”.
Wannan bayanima Na Abba ya girgiza zukata sosai. Dan har alk’ali kasa motsawa yayi, saidai yaja kusan mintuna biyu sannan ya sauke ajiyar zuciya mai k’arfi. Ya buk’aci a kawo masa camera nanda awa 2 kacal. Anbar lokacin a matsayin hutun kotu.

Babu Wanda yaso matsawa konan da can, kowa burinsa dai camera ta iso aga mita k’unsa.

Galadima ya kira Munaya, yace ta shirya ga Sarkin motanan zasuzo da Nuren su kaita masarauta ta duba cikin gifts d’inta Na Aure data samu Abba yace camera Na ciki.
Dayake a labarai an nuna takuma gani, sai kuka dama takeyi da mamakin miyasama bata duba gifts d’in auren nataba tun wancan lokacin? Koda yake bata dad’eba a Nigeria suka wuce India, itakam a dukkan zaman da suka d’an tayi idan sun dawo bata sake bi takan gifts d’inba, to kawai tace masa ya yanke wayar, Dan yanzu babban burinsa kawai a tabbatar camera d’in tana wajen nata.

Tana gama shiryawa sarkin mota yazo da Nuren dakuma police, bata d’auka yaro ko d’ayaba tafito suka tafi masarauta.

Sun iske masarautar tsit, tamkar anyi sharar mutane, kowa Na sashensa abinda ke faruwa yama zukatansu murus, hannu kawai take iya d’agama hadiman sashen nasu dake gaisheta, basu damuba, dansunsan tana cikin wani yanayine.
Sashen nasu yayi y’ar k’ura, saboda kwana uku babu kowa a ciki, Munaya kanta tsaye bedroom d’inta ta shige kawai, ta bud’e wardrobe nata tashiga fiddo gifts d’in aurenta data tara gefe, tareda Na haihuwar su Abdurraheem. d’ai-d’ai taita farkesu, idan taga bashi bane ko bud’awa batayi take jefawa saman gado, tasha wahala matuk’a kafin ta gano akwatin da idonta ya ta6a tozali dashi a d’akin Abba itada Munubiya, rungume akwatin tayi ta fashe da kuka maiban tausayi, ana haka kiran Galadima ya shigo wayarta, share hawayenta tayi ta d’aga.
A d’arare yace, “kin hanshi?”.
Cikin dariya da kuka ta amsa masa da eh ta gansa, shima murmusawa yayi, yace, “maza Ku tahoto, mintuna 46 suka rage a lokacin da alk’ali ya bada, sonake kawai a kammala shari’arnan a yau”.
Munaya ta amsa da “to gamunan……………..???

 

“insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu, koma mike cikin camera d’in dai zamu gani, nima Na k’osa nagani a wuce wajen????????”.

 

 

ALLAH ya gafartama iyayenmu??????

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply