Hausa Novels Raina Kama Book 3 Hausa Novel

Raina Kama Book 3 Page 17


Raina Kama Book 3 Page 17
Viral

BOOK 3 ????1?7?

……………….Abin surutu lallai ya samu, mak’iyan Galadima kuwa duk sun kasance a tsorace, Dan ba kowane ya fahimci inda shirinsa ya dosaba, hakama a cikin masoyan nasa, wasu suna ganin daidainsa wasu kuskurensa, kowa da irin fahimtar dai da yayma lamarin.

Yauma dai haka suka kwana zagaye da police.
Amma su IG duk sun tafi, d.p.o ne kawai tare da tawagarsa, kamar kuma yanda ya buk’ata sunakan tattara case d’in zuwa Court.

6angaren su Baffi kuwa lauyan Abie dukkan shirye-shiryen shiga Court suma suna akanyi. Dan dukkan shirin Galadima yasan dashi tsaf, hakan yasa koda yagani baiyi mamakiba, kisan Ahmad daine da akace yayi yabashi mamaki, dukda zuciyarsa bata aminta Galadima zai iya kashe yaro ko d’ayaba. Amma lallai hakan ya sakashi a rud’ani, harma ya kira sir Isa sukayi maganar. Sir Isa yace shima yagani a labarai amma gaskiya bai yardaba, akwai dai abinda duk basu saniba, Dan Galadima bazai aikata hakanba.
Da wannan maganar ne Baffi yad’an samu Nutsuwa yacigaba da tattara bayannsa daduk abinda zasu kafa hujja dashi a court.

Duk abinda ke faruwa Momma tasan komai. Dan Galadima ya sanar mata, baya kuma 6oye mata dukkan shirinsa akan wannan case d’in dama, amma sai tayi lup tamkar batasan anaiba, koda labari yazo musu saita taya su Aunty Mimi rud’ewar itama, harda pretending d’in kukanta tana Neman number Galadima, amma sai tak’i wucewa.
Daga Baffi har mai martaba babu Wanda ya kirata akan batun, duk a nufinsu Na 6oyemata kar hankalinta ya tashi balle Na mahaifinsa dake kwance yana fama da kansa.
Amma saiga kira daga mama Fulani, tafad’ama Momma maganar daduk yazo bakinta ta 6atanci akan Galadima, itadai momma cikanki batace da itaba, har tayi ta gama ta yanke wayar.
Saiga gimbiya Zulfah ma ta kira Momma, itakam ai harda kukan makirci irinna y’an duniya. Itama dai tayi kid’anta tayi rawarta Momma Na saurarenta.
Koda ta Yanke wayar saita kira munaya. Taita kwantar mata da hankali da lallashinta akan ta kwantar da hankalinta. Insha ALLAH komai zaizo k’arshe, kowace rayuwa takan tafine da jarabawa. Babu wani rai dazai rayu cikin farinciki da samun yanda yakeso 100%, dolene kowacce rayuwa akwai NATA k’alubale, nakowa kuma akwai ta hanyar dayake fuskantar nashi.
Sosai Munaya ta gamsu da nasihar momma hakannema yad’an samu mata nutsuwa tad’an rintsa a wannan dare.

……………………………?

WASHE GARI

Nasara ta farko da aka wayi GARI da ita shine farfad’owar Abba cikin hankalinsa, saidai har lokacin baya sanin Wanda yake a tare dashi, hakanne yasaka likitocin fad’in a k’ara masa lokaci yasamu isashen hutu.
Ahalinsa sunsamu Kansu a farinciki ainun, hakama masoyansa, shikansa Galadima Yakuma samun kwarin gwiwa da karsashi akan aikinsa.

An kuma shigar da case d’in Court kamar yanda Galadima ya buk’ata, abinka da lamarin manya har antsaida washe gari a matsayin ranar da za’a zauna Court d’in.

Yinin ranar zubur Galadima baiyi magana da police ko d’ayaba, koda sun buk’aci magana dashi saiya had’asu da Muftahu ko Nuren. Daga k’arshe dai dolensu suna k’yaleshi.

????????

?RANAR SHIGA COURT?

Yau ta kasance ranar zaman court, shari’ar su Galadima Ce kuma farko da za’a fara saurara a court d’in, lallai wannan shari’a ta manyace, Dan court d’in ta cika da manyan k’asa wad’anda sunfi kud’i wahalar gani, amma yau gasu available, y’an jaridar ma manya-manya aka bari, k’ananun suna awaje sunyi tururuwa domin rajin nemawa d’an uwansu hak’insa wato Alhaji Auwal fharuk dayake a asibiti har yanzu cikin halin ni y’asu.
Mukuwa talakawan gari y’an jiran jin yazata kaya mu sai dai gani a tv?.

Yo Wayaba asibi laya ubanta ba malam ba??, ai ko babama da babansa aradu??.

Court d’in tayi tsit babu abinda kakeji sai gudun fankoki da tarin manya jefi-jefi, dan babu alamun fara’a a fuskar kowa.
Daga masarauta dai k’anin mai martaba ne yazo wato Garkuwa Hayatudden Abubakar, sai wasu daga tawagar y’an majalissar Sarki, harda waziri dayazo bisa tirsasawar mai martaba.
Daga masarautar su Papi kuwa yarima mai jiran gado mahaifin su Nuren wato Wambai Abubakar Abdul-fatah Wanda yagaji sunan kakansu Galadima marigayi Abubakar kenan. Saikuma wasu daga jiga-jigan masarautar suma.

Fitowar alk’alin alk’alai Othman Ibraheem gwannu tasaka dukkan jama’ar Court d’in mik’ewa domin girmamawa a garesa, (dan shima Alk’ali baba uban su babane shima????).
Saida ya zauna sannan yabada izinin kowa ya zauna, Court d’in tayi tsit kowa ya Zubama alk’ali dake karanta takardar k’arar hankali kwance ido, kusan mintuna 3 ya d’ago yanabin Court d’in da jama’ar cikinta da kallo ta cikin eyeglasses nashi daya jawo k’asan ido, d’auke idonsa ya ya maida ga Lauyoyi dake zaune suna jiran kule, suce cas.
Gyaran murya yayi yana maida idonsa ga takardar da fad’in “Ina wad’anda suke k’arar da kuma wad’anda akai k’ara? Idan kuma Lauyoyine to na masu k’ara da wad’anda ake k’ara suna inane?”.
A tare Baffi suka mik’e shida abokan aikinsa su uku, cikin girmamawa ga alk’ali ya risinar dakai yana mik’a gaisuwa da fad’in “yamai girma mai shari’a sunana Barrister Usman Audu Tsanyawa, nine lauya mai kare Wanda yake k’ara, tare dani akwai Yohan Emanuel, da Bilkisa Ibraheem Musa (kutu melesi su bilyn Abdul anzama lauyoyin novel????????????).
Bilkisu da yohan suka risina alamar girmamawa.
Alk’ali ya jinjina kai alamar gamsuwa, su Baffi suka zaune, lauyan wad’anda ake k’ara shima ya mik’e, ya rissina tamkar yanda Baffi yayi, sannan yace, “ya mai girma mai shari’a sunana Barrister Adam Sadiq Adam, nine lauya mai kare wad’anda ake k’ara, tare dani akwai Barrister Aliyu Sa’adu yaro”.
Barrister Aliyu ma ya mik’a gaisuwa ga alk’ali sannan suka zauna.
Alk’ali yabama Baffi damar tashi domin yin magana.

ALLAH Sarki dattijon kwarai kenan, masu wahalar samu cikin k’asa a halin yanzu, ya gyara hularsu ta lauyeyi dake Kansa, tare da farin eyeglasses d’insa dan rayuwa taja, ijiya duk sun raunana, ya kalli jama’ar cikin Court d’in sannan ya dawo da kallonsa ga alk’ali, yace, “yamai girma mai shari’a! Kamar yanda kowa yasani Muhammad Sameer Saifuddin Abubakar (Galadima) shine yake Neman son sanin miya saka wad’annan mutanen 11 yin gamayya wajen kama surukinsa harsu wahal dashi? Bayan kuma shikeda alak’a dasu bawai surukinsa ba?”.
Kai Alk’ali ya jinjina, cikin sauke numfashi yace, “Lauyan wanda ake k’ara gareka”.
Barrister Adam Sadiq Adam ya mik’e shima yana fitowa fili, yayinda Baffi Yakoma ma zauninsa ya zauna, Brr Adam Sadiq Adam yace, “yamai girma mai shari’a wace irin tambayace ke fitowa daga bakin lauyan mai k’ara? Ai sune yakamata ayima tambayar minene dalilin shi Galadima Na kama yaran wad’annan mutane 11 yayi Garkuwa dasu yau tsawon kwana biyu? harma da kisan wani a cikin su………
A hanzarce Baffi ya d’aga hannu sama yana mik’e da fad’in “yamai shari’a tambaya akaima lauyan mai k’ara, amsa kuma yakamata ya bamu baya sakko tashi tambayarba”.
Hannu Alk’ali ya d’agama Brr Adam Sadiq Adam, yace, “Brr Adam ka gyara, amsa muke buk’ata, kanada dama kaima kayi taka tambayar daga baya”.
Brr Adam Sadiq Adam ya risinar dakai alamun ban hak’uri sannan ya gyara tsayuwarsa yana fad’in “Yamai girma mai shari’a akwai abinda ke hannun Alhaji Auwal Fharuk Wanda mallakin su wad’annan mutane 11 ne, shine sukeda buk’atar kar6a”.
Baffi yamik’e yana fad’in “yamai girma mai shari’a ko zamu iya sanin minene wannan Abu da suke tuhumar Alhaji Auwal Fharuk akansa, dahar suka kasa mik’ashi ga sharia domin kar6a har sai sunbi ta hanyar nuna k’arfin ikonsu?”.
Brr Adam Sadiq Adam yay shiru yakasa cewa uffan, dan ganin tun a tashin farko yana shirin zurmawa.
Ganin yak’i cewa komai Baffi ya kuma cewa “ya mai girma mai shari’a idan baza’a samu amsaba ina buk’atar d’aya daga cikin y’an wad’annan tawaga domin ya amsamin tambayata idan shi Barrister bai saniba”.
Alk’ali ya jinjina kai yana bada Umarnin tasowar d’aya daga cikin su Alhaji Mansur.

Dukfa abinnan dake faruwa Galadima yana kallon komai kai tsaye ta Computer, danshi baizo Court d’inba, babu damar hakan, yana fitowa a gidan police kamashi zasuyi, wannan yasa tukan zaman Shari’a Alk’ali yabada wannan damar ta had’a video call d’in da Galadima zai iya ganin komai da za’ayi kamar yanda IG ya buk’ata bisa umarnin shi Galadima d’in, kamar yanda ya shard’anta ko amasa hakan koya jeho gawar yaro d’aya ko yarinya. Hakan yasa sukai masa babu gardama.

Alhaji Abdul-Naseer dake farkone ya taso, ya shiga inda aka tanada domin buk’atar hakan, ya fad’i sunansa da matsayinsa, sannan Alk’ali yabama Baffi damar masa tambayar.
Baffi ya k’arasa jikin katakon d’aya shiga tsakaninsa da Alhaji Abdul-Naseer, idonsa a kansa yace, “Alhaji Abdul-Naseer, nasan kana d’aya daga cikin y’an wad’annan tawaga, shin kozaka iya amsa mana tambayar da lauyanku ya kasa?”.
Murmushin Alhaji Abdul-Naseer yayi, cikin kwarin gwiwa yace, “Brr Usman, a ganina wannan sirrinmu ne, koma mi muke buk’ata a hannun Alhaji Auwal Fharuk mukeda alak’a dashi ai ba kowaba ko?”.
Baffi yashiga jinjina kai yana murmushi, yayi taku d’aya biyu saikuma ya juyo ga Alhaji Abdul-Naseer, yace, “lallai wannan gaskiyane Alhaji Abdul saidai kuma dalilin sanin Court yanada alak’a da samo Alhaji Auwal Fharuk a hannunku, wanda ta silar kama y’ay’anku da surukinsa yayine kowa yasan hakan, saikuma gashi shi wannan bawan ALLAH Alhaji Auwal Fharuk a jiya daya farfad’o dukda baya cikin hayyacinsa, amma yana ambatar sunan Alhaji Halluru da jaddada lallai koda zaku kasheshi bazai bada wannan camera ba, domin shekarunma da kuka d’auka kuna ma rayuwarsa barazana bai bakuba balle kuma yanzu da lokacin Isar da ita ga Wanda akace ya Isar yayi, kenan Alhaji Auwal Fharuk k’arya yayi?”.
Da sauri Brr Adam Sadiq Adam ya mik’e yana fad’in “ya mai shari’a wannan ai tamkar titsiyene Brr kema Wanda ake zargi, dan babu yanda za’ai la’akari da mutumin da baya cikin hankalinsa kamar yanda ya fad’a…..”.
Shima Baffi azamar dakatar dashi yayi, yace, “yamai girma mai shari’a Barrister Adam bashida hurumin yanke hukunci akan yanayin Alhaji Auwal, sai ya bari bayanin likitoci ya tabatar mana hakan”.
Alk’ali yay gyaran Murya da buk’atar ganin likitan dake kula da Alhaji Auwal Fharuk (Abba).

Cikin mintuna 3 saiga doctor ya shigo.
An sakashi d’ayan wajen, ya fad’i sunansa da aikinsa, sannan Alk’ali yace, “kaine likitan da ke duba lafiyar Alhaji Auwal Fharuk? ”.
“eh nine yamai shari’a”.
Alk’ali yace, “kozamu iya sanin wani Abu dangane da jikin Alhaji Auwal Fharuk? ”.
“kwarai kuwa ya mai shari’a, an kawo mana Alhaji Auwal Fharuk cikin hali irinna suma, amma babu wani alamar duka ko harbi a jikinsa, saidai bincikenmu ya nuna an shak’a masa wani Abu. Daya saka numfashinsa Nisan zango, sai ajiyane bisa hukuncin ubangiji ya farfad’o, wad’annan kalamai sune abinda ya farka dasu a bakinsa, kuma kwakwalwarsa ras take, abinda aka shak’a masanne kawai bai sakesaba har yanzun, danma yanada jini mai k’arfine”.
Cikin wad’anda suke zaune ma’aikatan Court d’in d’aya yaje ya kar6i wayar doctor da yay recording ya kaima alk’ali.
Alk’ali ya kunna recording ya saurara, ya ajiye wayar gefe da sallamar doctor cikeda gamsuwar abinda yaji. Sannan shima yabada Umarnin sanin ita camera ta micece?.
Baffi yakuma mik’ewa tsaye yana gyara k’atuwar rigarsa, yace, “ya mai shari’a, ita wannan Camera da wad’annan gamayyar mutane suke farautar rayuwar Alhaji Auwal Fharuk a kanta tanada alak’a da Muhammad Sameer Saifuddin Galadima ne, itace kuma musabbabin d’aukar yaran wad’annan mutane 11 dayayi yake tsare dasu a gida mai labba 67 dake anguwar tudun na ALLAH a tsakiyar binni, damin camera dai k’unshe take da abinda ya faru da tsohon Sarki dake jiyya a India, wato Mai martaba Saifuddin Abubakar tsawon shekaru 26 kenan ba’asan wad’anda suka aikata masa abinda ya kaisa da jiyyarba”.

Turk’ashi, kallon kallo kenan, to lallai shine aka shigayi a wannan Court, nanfa k’ananun magana suka fara tashi tsakanin manya, Court ta harmutse da hayaniya babu maijin zancen wani, saida alk’ali ya tsawatar sannan akayi tsit.

Inda kuma a gefe tsantsar rud’ani da rikita ta mamaye su Alhaji Balala, ko kad’an basuyi zaton shigowar wannan maganar da wuri ba cikin shari’ar, shima kansa lauyansu haka, tunda wawantar dasu Galadima yayi akan Shari’ar ta shafi d’aukar Alhaji Auwal Fharuk ne da farko.
Alk’ali da shima kansa ya shiga wani yanayi ya buk’aci ganin Muhammad Sameer a Court.
Baffi ya kuma mik’ewa yana fad’in “ya mai shari’a, ai Muhammad Sameer Saifuddin Galadima bashida ikon zuwa court a yanzu, domin kuwa yana can tsare da yaran wad’annan mutane 11 ne, kuma yana fitowa y’an sanda zasuyi ram da shine a matsayin mai laifi babbama kuwa, dan yanzu akwai laifin garkuwa da yara d’in a kansa, saidai munada hanya sassauk’a ta had’a wannan adalar kotu da Galadima kai tsaye”.
Alk’ali ya bada damar hakan.
Dandanan kuwa aka had’a Galadima da kotu, Wanda dama shi tuni yana ganin duk abinda sukeyi, sunedai basa ganinsa.
Galadima dake zaune a falon gidan da yake tsare dasu harun ya mik’e tsaye domin girmamawa ga alk’ali, sannan ya gabatar da sunansa kamar haka, “ya mai shari’a sunana Muhammad Sameer Saifuddin Abubakar, ma’aikaci a hukumar bincike ta DSS”.
Wani sabon kallon kallon aka koma, Wanda yaja hankalin mutane fiyema dana d’azun, hattada y’an masarautar gagara badau basusan da wannan aiki Na Galadima ba.

Alk’ali ya kuma tsawatarwa, sannan ya maida hankalinsa ga Galadima yana fad’in “To Muhammad Sameer minene alak’arka da iyayen yaran dakake rik’e dasu, danmu ka rikita mana tunani, da farko kallon Criminal muke maka, saikuma gashi sunanka yafito a d’aya daga cikin manyan hukumominmu Na tsaro masu muhimmanci?”.
Murmushi Galadima yayi yana gyara tsayuwa, ya hard’e hannayensa a k’irji yana sauke numfashi da cije lips, yace, “ya mai shari’a wannan labarine mai tsawo, amma tabbas abinda lauyana ya fad’a shine gaskiyar zance, Camera dake hannun Alhaji Auwal Fharuk itace babbar alak’ar dake tsakanina dasu, wadda nad’au tsawon shekaru akan nemanta, sai a shekararnan ne cikin watanni shida nasamu labarin inda take dukda banida tabbacin ita d’ince, bansan mike cikin camera d’inba, amma su Alhaji Balala duk sun Sani, tunda har suka iya salwantar da rayuka da yawa akanta, shi kansa Wanda suka hara a yanzu ALLAH ne kawai yasaka yanada tsawon rai, amma da tuni sun kasheshin, ni kaina rayuwata tasha hare-hare iri-iri harda jariran yarana da aka sace kwanaki 7 kacal da zuwansu duniya”.
Alk’ali da yay shiru yana sauraren Galadima yaja dogon numfashi yana ta faman jinjina kai tamkar k’adangare yaga abinci mai manja????.
Yace, “lallai wannan Court tana buk’atar jin cikakken bayani daga Muhammad Sameer Saifuddin, dan haka ta d’aga wannan k’ara zuwa nan da kwanaki uku masu zuwa, kotu tana bama y’an sanda Umarnin subar Muhammad Sameer Saifuddin ya fito daga wannan gida a ranar da Court zatayi zama Na gaba batare da koda masa hararaba, sannan kuma kotu ta bada Umarnin a cigaba da tsare su wad’annan mutane guda 11, likitoci kuma su cigaba da bama Alhaji Auwal Fharuk kulawa ta musamman dan shima kotu Na buk’atar ganinsa a zama Na gaba saboda son sanin mike cikin camera d’in”. Alk’ali ya buga gudumarsa yana mik’ewa.
Gaba d’aya kowa ya mik’e har alk’ali ya shige.

Galadima yay wani k’asaitaccen murmushi yana zaunawa cikin kujera bayan shigewar alk’ali.
Muftahu, Nuren, dasu Harun dake zaune gefe suma suna kallon komai tun farkon Shari’ar duk sunyi mutuwar zaune tun lokacin da Galadima yafad’i kasancewarsa cikin hukumar C.I.D.
Ameer ne kawai yay murmushi yana k’amewa da salute d’in Galadima.
Shima baki sake su Nuren suka bishi da kallo suna nunashi alamar dama yasani shi?.
Murmushi yay musu har hak’oransa Na bayyana ya had’e hannayensa waje d’aya alamar tuba a garesu.

?……………………………….?

Yau kam Galadima wani farin ciki Na musamman ya tsinci kansa a ciki, ya shige d’akin da yake matsayin nasa a yanzu ya fad’a gadon yana rungume filo idonsa Na zirar da hawaye, ko a haka aka tsaya lallai yaci nasara, dan ya nunama su Alhaji Abdul-Naseer d’an zaki ya girma.
Wayarsa dake saman gadon a can gefe yasa hannu ya janyo, ya kunnata, massages ne sukaita shigowa a jere-jere kamar jira, bai bud’e ko wanneba ya shiga binciko number Munaya, ya dad’e yana kallon Number amma ya kasa dialing, yaja wasu seconds kafin yatsansa ya sauka akan number ya danna kawai.

Munaya Na zaune a falo tare da su Ayusher da kullum sai sunzo, d’an kunne ne ya shige cikin jikin Amaturrahman yanata cin jikinta basu saniba, sai yau da an ta6a fuskarta koyaya saita fashe da kuka, Munaya tarasa mike damun yarinya, dukta rikice ita kanta, saida laraba tace ta bata nono, tana kwantar da ita ta wajen kunnen sai takuma d’ad’ewa da kukan da Munaya ke jinsa har cikin jini, d’agota tayi tana duba wajen, Laraba tace, “Anya ba kunenta ke ciwoba?”.
Munubiya dake kusada Munaya ta amshi Amaturrahman ta kifata a cinyarta tana dubawa, sai taga d’an kunne ne ya shige Ashe duk bayan kunnen yayi ruwa, tsoro ya kama Munubiya, cikin zaro ido waje tace, “innalillahi, d’an kunne natacin kunen yarinya bamu saniba”. Da an fara k’ok’arin ciremata saita kuma fashewa da kuka tana mimmik’ewa, gwaggo safiya data shigo yanzu saboda jiya ta iso akan abinda ya faru da Abba, ta k’araso cikin falon tana fad’in “mike faruwane?”.
Bayani feena tai mata, gwaggo safiyya ta kar6i Amaturrahman tana cewar asamo mata ruwan d’umi da k’aramin handkerchief.
Ana cikin hakane Galadima yayi kiran Munaya, tashitai tabar wajen tana had’iye kukan dake shirin taho mata saboda tausayin yarinyar.
‘Dakinsu ta shiga, ta fad’a saman gadonsu ta kwanta tana amsa wayar.
A hankali Galadima ya sauke ajiyar zuciya yana gyara kwanciya. Murya can k’asan mak’oshi yace, “babu fad’a miya kawo gaba yalla6iya?”.
Murmushi Munaya tayi tana share hawayenta. Tace, “Kodai Kaine za’aima wannan tambayar?”.
Jimm yayi saboda jin muryarta ba ayanda yasaniba. yace, “mike faruwa kike kuka?”.
Mamaki ya kama Munaya, ta Yayama ya gane kukan take, cikin k’ok’arin kare kai tace, “ba kuka nakeba yalla6ai, ina yini”.
bai amsa gaisuwarta ba yace, “kina wasa da sanin danai miki ko?”. Yay maganar cikin d’an kausasa murya.
Munaya sai bataji dad’iba, tace “kayi hak’uri, dama Amaturrahman ce d’an kunne ya shigema a jiki taketa kuka, amma gashi can suna cire mata d’an kunnen”.
Babu shiri Galadima ya tashi zaune yana fad’in “k ya akayi har d’an kunne ya ringa cin jikinta baki saniba? Anya kuwa kinason yarannan Munaya?”.
Wani haushine ya kamata, tama rasa mizata Ce masa.
Shima bai jira amsartaba yace, “maza ki tashi kuje asibiti a dubamin yarinya, karkuce zakuyi gangancin cire mata a gida wata matsalar ta biyo baya”.
“Uhumm”. Kawai Munaya tace ta yanke wayar.
Ta jefar da wayar gefe tana hawaye, shi kawai yaransane damuwarsa, harma zaice yafita sonsune dazai dinga jifanta da bata sonsu kulum-kullum, itafa wannan Abu yafara kaita bango wlhy.

A can kuwa shima Galadima duk sai yaji ya damu, jiyake tamkar yay tsuntsuwa yafita yakai yarinyarsa asibiti da kansa, amma babu damar hakan.
Ya dad’e jikin window tsaye yana kallon mutane daketa zirga-zirga a anguwa da police d’in dake zagaye da gidan har yanzu.

Fita munaya tayi dan ganin ko ancire?, ta iske an cire ana gasa kunnen, Amaturrahman taci kuka harta koma ajiyar zuciya, Gwaggo Safiyya tace, “zoki zauna kibata tasha sai’a k’arasa gasawar”.
Zuwa Munaya tayi ta zauna tana kar6ar Amaturrahman.
K’in k’ar6ar nono tayi, sai ajiyar zuciya taketayi, Laraba tace, “yaranan zuciya irinta Magajin gari suke da ita, yanzu inba sa’a ba bazatashaba”.
Dariya su Ayusher sukayi.
Dak’yar dai Munaya ta turama Amaturrahman nono abaki ta kar6a. Akad’an kuma gasa kunnen dayay uwar huda naman wajen yafita sosai, k’ofar tazama babba.
Munaya dake kallonta tasaka hannu tana goge mata zufar data taru mata a goshi, saikace wata babba.

Galadima yanata kiran Munaya yaji kosun tafi asibitin amma bata d’agaba, dayake ta bar wayar a d’akinsu.
Saida Ayusher taje d’akin ta gano, ta d’akko da sauri ta kawo mata tana saka mata a kunne.
Maganarsa kawai munaya taji yana fad’an ina ta ajiye wayar.
Ajiyar zuciya ta sauke tabashi hak’uri kawai, dan bata buk’atar jan maganar.
Yace, “kunje asibitin?”.
Munaya tace, “An cire mata ai, babu wata matsala tunda bai ta6a cikiba”.
Ca yay ta d’auka hoton wajen ta turo masa yagani, kamar tace bazatayiba sai kawai ta cire wayar ta katse kiran, hoton wajen ta d’auka ta tura masa”.

Tausayin yarinya ya kamashi ganin yanda wajen yay cinye sosai, Yakuma kiran Munaya yana jaddada mata karta sake akuma sakamata wani d’an kunne.
To kawai ta amsa masa dashi dan a zauna lafiya.

 

…………………………?

Tun daga ranar Munaya bata sake jin Galadima ba, saboda yayi busy da yawa akan shirye-shiryen shari’ar dake gabansu, dan fatanshi wannan zaman yazama zama Na k’arshe insha ALLAH.

Alhmdllh jikin Abba anata samun haske sosai, dan sauk’i yana samuwa iya gwargwadon iko.

RANAR DA ZA’A KOMA KOTU…………….???

 

Hummm??

ALLAH ya gafartama iyayenmu??????

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply