Hausa Novels Raina Kama Book 3 Hausa Novel

Raina Kama Book 3 Page 15


Raina Kama Book 3 Page 15
Viral

BOOK 3 ????1?5?

……………..Duk da Munaya a rikice take haka tayi jarumtar danne zuciyarta, cikin hikima ta dinga bin jama’ar gidan d’ai-d’ai tana tambayar wad’anda tasan Abba zai iya kira kai tsaye, amma kowa yakance tun daren jiya basuyi wayaba, hankalinta a tashe ta sulale gidan innaro ba’a saniba, itama dai tace tun bayan sallar asuba bai sake kiranta ba. Munaya tafito jikinta sai rawa yake, kiran Galadima tayi, lokacin yana waya, tamkar zata fasa kuka ta cire wayar daga kunnen ta, tana niyyar sake kiranshi saigashi ya kirata.
Da sauri ta d’aga.
Yace, “yauwa Yayi waya da wani?”.
Muryarta na zuga alamar tahowar kuka tace, “A’a, innaro kawai ya kira bayan sallar asubahi, amma yau koda su innarmu baiyi wayaba”. ta k’are maganar hawaye na gangarowa a kumatunta.
Galadima ya furzar da huci daga can, a hankali yace, “Munaya”.
Muryarta na zuga ta amsa tana share hawayen da bakin hijjab.
Had’iye abinda ya tsaya masa a mak’oshi yayi da k’yar, muryarsa takuma komawa can k’asan mak’oshi, cikin sigar lallashin da Munaya bata ta6a sanin galadima ya iyaba yace, “insha ALLAH babu abinda zai faru da Abba, kiyi mana addu’a, sanan karki sanarma kowa wani Abu har inna, wayarki tazama kusa dake, Dan zan dunga kiranki idan buk’atar hakan ta taso”.
Munaya takuma goge hawayen dasuka gaza tsayawa, cikin had’iye kukan tace, “ALLAH yabaku nasara, ya tsareku da tsarewarsa”.
“Amin ngd”. Galadima ya fad’a yana yanke wayar.
A bakin fanfo Munaya ta tsaya ta wanke fuskarta, akuma lokacinne Zarah da Siyama suka shigo kusan lokaci d’aya.
d’agowa nayi Na kallesu ina k’ak’aro murmushin da musu sannu da zuwa. Saidai ayanda suka amsamin cikin sanyin jiki saina tsorata, nabaro bakin fanfon da hanzari zuwa garesu ina fad’in “Kai lafiyarku kuwa?”.
Duk d’insu murmushi suka k’ak’alo, Siyama tace, “babu komai fa sis…”.
Dukda ban yardaba haka nayi murmushi, sannan Na kar6i yaransu duk biyu Na rik’e ina yaba Girman da sukayi, saikace tagwaye.
Daga Siyama har Zarah basuce dani Uffanba duk suka shige, kowa tanufi d’akin Uwarta. Duk binsu nayi da kallo, saida suka shige Na sauke ajiyar ziciya nima Na nufi sashenmu Ina tunanin mike faruwa? Dan alamu sun nuna akwai dai wani Abu a k’asa.
Saidai bankai ga Shiga d’akinmu ba mamansu Yaa hameed ta tareni ta kar6i yarinyar Zarah. Ban musaba Na bata tundai ALLAH yasa Nima Na Haifa balle ace, na shige falonmu da d’an Siyama nima.

Bayan Galadima sun gama waya da Munaya, number da daddy ya turo masa ya duba, ganin wadda yake da itace saiya gwada kira, switch up, ya ciza lips yana kallonsu Nuren da suma duk suka zuba masa idanu.
Muftahu yace, “Ranka ya dad’e mu sanarda y’an sanda mana?”.
Murmuahi takaici Galadima tayi, ya girgiza kansa yana fad’in “Hakan zai 6ata aikinmu, duk indama yake a safiyar yaune suka sameshi, akwai zoben dake hannunsa zamu iya bibiyarsa tanan, saidai matsalar d’aya dole sai wayarsa Na aiki, gashi number sa kuma switch up”.
Nuren yace, “to mizai hana mu bincika kozamu samu daga inda Number tabar aiki”.
Da sauri Galadima yace, “yes, yes Nuren, shawara mai k’yau…..”
Shiru yay yakasa k’arasawa, saboda tuno da matsalar da Computers nasu suke ciki kuma, ya dafe kansa.
Daga Muftahu har Nuren duksun fahimceshi, zuwacan kuma miya tuna saiya mik’e da hanzari zuwa cikin d’akin, babu dad’ewa yafito dawani k’aramin abu a hannunsa, lap-top yajawo ya manna a jiki, ya had’a da waya ya Shiga sarrafata cike da kwarewa.
Zuwa can yad’ago yana kallon su Muftahu da tura musu lap-top d’in gabansu, yana sanar dasu titin da wayarsa ta daina aiki.
Cikin takaici yace, “Sunriga da sun tsara komai, mubarma tunanin plan A, muje zuwa plan B kawai”.
Cikin mamaki duk suka kallesa alamar miye plan B d’i?.
Lips d’insa yad’an ciza yana d’age gira d’aya da buga yatsan saman bakinsa, Yace “maida hankalinmu a nemansa shine target d’insu Na farko wajen janye ra’ayinmu, plan d’inmu mukuma anan shine bazasu ta6a kasheshi ba inhar bai basu Camera d’inba, a yanda Na lura kuma yanada taurin kai shima, bazai ta6a basuba ko fad’a musu inda take. Sunada damar yin amfani da surukan senator halluru wajen turasu gida su nema musu camera d’in, kodai ta hanyar musu barazana da mutuwa, kokuma akan aurensu, ko kashe mahaifinsu, kodai wani Abu daban, shiyyasa dolene mumaida matsalarsa cikin plan B d’in”.
Duksun gamsu, dukda sufa har yanzu yak’i sanar musu miyake shiryawa a plan B d’in.
Cikin damuwa Nuren yace, “Amma nasan zasu wahalar dashi”.
Galadima baice komaiba dan shikad’ai yasan azabar da zuciyarsa kemasa, bayason ya nuna karayarsane saboda karsuma su Muftahu su karaya, sannan koda sanyin jiki yanemi tasiri gareshi sai kalaman Munaya su masa allura, inhar yarinya k’arama kamarta zata iya tasirantuwa da abinda ta fad’a, mizai hana shima ya samu jarumta cikin tagomashin fik’irarta.
Mik’ewa yay tsaye yana tattara kayansa da fad’in “Bara Na wuce, sai kunji yadda zata kaya kawai”.

Basu barshi yatafi shikad’aiba, saida sukai masa rakkiya har masarauta, koda ya shige sashensa saiya kulle kansa, domin yin shiri.

Hummm,??????shirya da k’yau Galadiman mu.

 

???????????

Abinda ya faru da Abba shine, bayan yagama kammala shirinsa domin baro inda sukaje shida S… halluru daya jashi domin masa rakkiyar tafiyar kwanaki biyu kacal.
Lafiya lau suka shiga mota zasu taho, amma sai shi S… Halluru ya dakata da cewar Abba yayo gaba, shi anmasa kiran gaggawa, bai kuma kamata ace ya tsaidashiba shi, tunda ya sanarma iyalansa yau zai dawo.
Da farko Abba kamar zaice suzauna kawai harya gama, saikuma tunanin yariga da ya sanarma su innaro zai dawo ya fad’o masa, shiyyasa kawai yataho, basuyi wani nisa da tafiya ba driver ya tsaya wai motar Na d’aukar zafi, ALLAH Sarki Abba, sai shima ya fita domin taimaka masa, suna tsaka da duba motarne garadan samari hud’u suka fito daga ma6oyarsu sukai ma Abba d’aukar amarya. Duk yanda yaso kare kansa ya gaza.
Driver da dama duk cikin shiri yayi haka saiya hau tsallen k’arya cikin pretending yana ihun azo a taimakesu, (??????bayan yasan baza’a samu kowaba a wajen tunda jejine?).

Abba mutumne mai dagiya akan ra’ayinsa, hakan yasa duk yanda sukaso yabasu had’inkai akan zancen Camera yak’i, yama dage shi baisan Cameran da ake magana a kaiba, kuma dayaso basun tun lokacin da ake bibiyarsa da dukiya mai tsoka daya bada, amma basuda kud’in dayakai darajar camera d’in, sannan inda zai bada kodan barazana da rayuwarsa da sukasa aikaitayi tunba yanzuba daya bada, amma yasan ruhinsa Na hannun Wanda ya halicceshi, shine kuma mai kar6a aduk lokacin da yaso, inma sun kasheshi dama kwanansa ya k’arene, Dan haka subar wahalar da Kansu kawaima.
Wannan maganar Ce ta fusatasu, wani ya daki Abba a baki harya fashe, dukda yaji zafi saiyayi murmuahi kawai yana kauda kai gefe.
Wanda sukasa yamusu aikin lalata documents d’in Galadima Na cikin Computers ne ya ankarar dasu zoben hannun Abba akwai wata kimiya a cikinsa, wannan ne ya sakasu cire zoben daga yatsansa, shi Abba saima yanzune yasan manufar zoben, yay murmushi, Dan hakan ya tabbatar masa cewar Galadima yasan wani Abu game dashi.
Duk yanda suka ringa k’ok’arin yima Galadima mugunta a sirrinsa Na Computer Abba Na kallonsu, hankalinsa kuma a tashe yake, amma jarumin namijineshi mai iya sarrafa kai aduk yanayin daya kasance, ko’a fuska bai nuna musu yana tare da damuwar abinda sukeyinba, saida Galadima ya kashe komai nasune Abba ya sauke 6oyayyar ajiyar zuciya, dukda yasan hakan ba shine nasaraba.
Wanda suka saka aiki mai suna William yashiga rud’anin abinda Galadima yayi, Dan da farko yanata cika baki babu wani d’an African daya isa ja dashi a fannin ilimin Computer, bak’ak’en fatar ai a wajen su suke koyan komai, ta Yaya kuma zasu fisu Sani?.
wad’annan kalamai nasa sun Sosa zuciyar Abba da sakashi cikin takaici, shiyyasa yayta jerama Galadima addu’ar samun nasara a zuciya.
Yayinda sukuma wad’anda akema aiki suke kuma hurama William kai da kwanzartashi (ko kishin Kansu basayi??, a zageku da kuma k’ask’antar daku kuna yabon mai ganinku marasa daraja??????, wata dai bahaguwar rayuwa sai bak’in fata????.

Dak’ilesu da Galadima yayi ta hanyar kashe komai ya fusatasu suda William d’in, suna kuma kunna Computers d’in komai naciki ya goge, wannan Abu ya rikita William matuk’a, gashidai yagama proud d’in shi kwarone kuma bak’in fata d’an Africa ya masa kwaf d’aya, dukkan fushinsu saiya dawo kan Abba.
Ana cikin haka saiga Alhaji halluru da sauran tawagar y’an group d’in, wad’anda sai yanzune suka samu k’arasowa, da farko Abba ya zata Alhaji Halluru taimakonsa yazoyi, saida yaji suna masa izgilanci sannan ya fahimci komai, cikin tsantsar mamaki yace, “Alhaji Halliru da kanka?”.
Ta6e baki Alhaji Halluru yayi, yace, “zaka bani takarar Governor ne?”.
Abba yay murmushin takaici yana fad’in “Tir da kai Halluru, wannan ai jahilcine, ALLAH shikad’aine ke bada mulki ga Wanda yaso, akuma lokacin dayaso,, yanzu kana nufin duk shekarun daka d’auka a jikina kai dama da manufa kake tare dani?”.
Alhaji Halluru ya kuma ta6e baki yana murmushin mugunta, yace, “Alhaji Auwal kenan, ai bama zaka tabbatar da hakanba sai y’ay’anka da kansu sun d’akko min camera sun kawo, sannan mukuma kasheka a gabansu babu yanda zasuyi, yanzu haka suna gida, zuwa anjima kad’an kuma camera zatazo garemu”.
Zufa ta fara karyoma Abba a dukkan sassan jikinsa, danjin za’ayi amfani da gudan jininsa wajen tarwatsa abinda yad’au shekaru yana rik’ewa amana, k’ala baice da Alhaji Halluru ba, su kuma sai kiraye-kirayen waya suke Na had’ama Galadima tarko.??????
Abba ba tausayin kansa yakejiba, tausayin Galadima yakeji matuk’ar tik’ewa, Dan ganin rai kusan 15 kowa k’iyayyarsa akansa take da muguntarsa…

 

??????????

Tunda Galadima ya shigo bai zaunaba, saida yagama had’a komai dazai buk’ata, yabama sarkin mota yakai cikin motar dazaiyi amfani da ita, alwala yay yafita salla massalacin masarautar, bai yarda sun had’u da Sarki ba, yay fitowarsa, koda ya dawo saiyasha magani ya kwanta, kaikace bashida wata matsalane, babu dad’ewa kuwa barci yay gaba dashi.
Bai tashiba saida aka kira sallar la’asar, nanma massalacin yaje, bayan ya dawo yay kiran Momma ta video call, duk suna asibitin hardasu Samha, d’aya bayan d’aya ya gaisa da kowa, Samha harda kukanta tanason zuwa Nigeria, ita missing nasu takeyi sosai. Galadima yace a’a ba yanzu ba, tashi tai tabar gaban lap-top d’in tana kuka, Galadima ya girgiza kai kawai.
Yasha hirarsa da Abie sosai, saboda Alhamdullah jikinsa saidai godiyar ALLAH, dama ciwo keshiga farat d’aya, sauk’i kam sai a hankaki. Addu’a kuma takobin muminice ako yaushe.
Bayan ya gama waya dasu Momma Sir Isa ya kirashi, ya tabbatar masa da komaifa is done, Dan ansami kowanne acikinsu, yanzu haka wasu sunma iso.
Galadima yay murmushi yana shafa fuskarsa. Yace, “Nama canja shawara, zamu canja gidan da zamu ajiyesu da, yanzu akwai wani gida annan kusada plaza d’ina, nagama magana da Saleem komai yayi ready, Ameer duk yakaisu can, insha ALLAH ana idar da sallar Isha’i zan fito”.
Sir Isa yace, hakan yayi, dan acikin yaran nasuma za’a iya samun munafukai, tunda duk sunsan gidan daza’a ajiyesun, yanzu kuwa shi Ameer kad’ai zaisan da wannan.

Galadima ya kira Munaya, dama tun d’azun kiran nashi take jira, ta d’aga tana shigewa cikin bayin d’akinsu Dan kar wani yaji.
Galadima yace, “haryanzu kukan?”.
“a’a” ta fad’a cikin share hawaye.
Yad’an murmusa kawai yana fad’in, “Akwai bak’in da sukazo gidanku?”.
“A’a babu Wanda yazo, sai Siyama da Zarah”.
Galadima yay murmushin gefen baki yana cigaba da danna lap-top, hasashensa yazama gaskiya kenan, gyaran murya yad’anyi kad’an yana fad’in, “kina jina?”.
Munaya tace, “eh”.
“Ki saka ido akan d’akin Abba, motsin kowa yazama akan idonki koda cikin matansane, ko yayyenki maza, Dan za’a iya yin amfani da kowa, inda da dama ma key d’in d’akin yazama a hannunki”.
Munaya tayi d’an jimm alamar tunani, zuwa can tace, “babu damuwa, zan gwada hakan insha ALLAH, amma kunji labarin Abban?”.
“Karki damu, insha ALLAH Abba zai dawo gida, addu’a muke buk’ata”.
Munaya ta jinjina masa kai tamkar tana ganinsa, ta share hawayenta dake zubowa.

Yana yanke wayar nafito, cikin dabara nashiga d’akin innarmu, key d’in d’akin Abba Na d’akko, dukda nasan kowama yana dashi cikin matansa, fitowa nayi naje cikin dabara da sauri-sauri Na saka key d’in cikin k’ofa d’in, cikin addu’ar Neman nasarar kozai karye a ciki, amma ko gezo baiyiba, hannuna sai azabar zogi yake, danma nayi amfani da wani abin sarrafa k’arfene, cirewa nayi nakoma ciki kozan samo wani k’aramin k’arfe dazai iya Shiga, saida nasha wahala nanma sosai kafin Na samo, gashi duk a tsorace nake kar wani ya fahimci abinda nakeyi, cikin kafar makullin Na turashi, Alhmdllh nasamu ya shige, nagwada saka key amma yak’i Shiga, nasan babu yanda za’ayi wani key ya sake shiga wajen harsai mai gyara yazo, tunda kuma Abba bayanan ai babu buk’atar hakan, Dan duk wanda zai buk’aci shiga yanzu lallai akwai manufa. Dukda haka saida nasamo kwad’o nakuma sakawa sannan hankalina yad’an kwanta.

**********

9:00pm

Fitowarsa kenan daga wanka baiko tsaya shafa mai ba ya hau shiri cikin wandon da riga k’ananu, fuskarnan babu alamar walwala tattare dashi, komai yana yinsane cikin karsashin fushi da damuwa, ya kammala tsaf yad’an saka turare.
A k’ofar sashensa ya iske Nuren yana jiransa, sauran Hadeemansa dabasuyi barciba suka shiga masa barka da fitowa, kansa kawai ya d’aga musu, d’aya daga ciki ya bud’e masa bayan motar, amma sai bai shigaba ya d’aga masa hannu ya bud’e gaba da kansa ya Shiga, Nuren yay murmushi kawai, yasan yau mazan a wuya suke.
Shiga yay shima mazaunin driver yaja suka fice.

Gidane matsakaici sabo, dagani ko dad’ewa da gama gininsa ba’ayiba, saidai anzuba komai Na amfanin gida, ahaka suke buk’atar badashi haya. Dan haka da saleem yanemi hayar suka bashi kai tsaye.
Suna isowa Muftahu ma ya iso d’auke da su Harun, Alhj Darma, Farhat d’iyar Minister sai mal. Saminu driver Alhaji balala, kusan shima yana hannunsu har yanzun.
Ameer ya mik’e da Sauri yana salute d’in Galadima, hararsa yayi, Ameer yay murmushi yana yin k’asa da kansa. Cikin girmamawa yace, “Ranka ya dad’e wad’annan sune phones d’in yaran da tarkacen kayamsu”.
Jinjina kai Galadima yayi, hannunsa duk biyu goye a bayansa yana zagaya table d’in da aka zube wayoyi, da lap-tops, iPad’s dukna wad’anda aka kawo d’in, ya kalli Ameer cikeda k’asaitarnan tasa yace, “Suna INA?”.
“Duk suna sama ranka ya dad’e, Dan inaga yakamata kazauna acan, danka ke ganin motsin kowa daga waje, dukda ansaka cctv a ko ina na wajen”.
Galadima ya kad’a kai alamar gamsuwa da bayanin Ameer.
Cikin takunsa na izza da lafiya ya nufi saman benen dake gidan, Muftahu da Nuren suka kalli Ameer cikin neman k’arin bayani, murmushi yamusu, yana tattare wayoyin yabi bayan Galadima dasu.
A k’aramin falon k’asan ya iskeshi tsaye yanabin komai da kallo, Ameer yace, “ranka ya dad’e yazamuyi da wad’annan phones d’in nasu?”.
Galadima yad’an ciza lips yana kallon Ameer, yace, “inasu Nuren d’in?”.
“Suna k’asa”.
Galadima baice komaiba, hakan da yayi ya saka Ameer fahimta su shigo kenan, saiya ajiye abin hannunsa ya sauka k’asan Dan kiransu.
Saleem yafito daga wani d’aki ya taso k’eyar wani matashin Saurayi k’yak’yk’yawa, daka gansa kasan hutu yagama ratsashi, kallo d’aya Galadima yamasa ya d’auke kansa, Saleem yaja kujerar dining d’aya ya zaunar dashi, sannan yasaka igiyar daya d’auka ya d’auresa jikin kujerar, saurayin sai zaginsa yakeyi, amma Saleem ko kulashi baiyiba, saida yagama tsaf sannan ya kalli Galadima, wata alama yamasa da ido.
Sai kawai naga Saleem ya d’auke saurayi da wani shegen mari, Wanda yasaka su Nuren dake shigowa jan birki suna kallon Saleem, bakin saurayi bai mutuba, Dan haka Saleem yakuma zuba masa wani har hancinsa Na fashewa, azaba ta sakashi kama bakinsa yay shiru yana huci da had’iye hawaye.
Galadima ya ta6e baki yana d’age kafad’a. Alamar sudai suka sani.
Haka Saleem yayta fiddosu d’aya bayan d’aya harsu 7, maza 5 mata 2, sai Farhat cikon ta takwas, amma su matan babu wacce aka d’aure, mazanma idan har bakayi gardama ba ba’a ta6asu.
Saleem yagama jerasu reras gaban Galadima daya d’ora k’afa d’aya kan d’aya cikin kujera yana danna lap-top hankali kwance.
Muftahu da Nuren dai sunyi mutuwar zaune, basu ta6a tunanin Galadima zaibi wannan hanyarba, gashi yak’i basu wata fuska dazasu masa magana ko tambaya.
Saleem da Ameer suka kamo Harun shima aka d’aureshi a gefe ba cikin yaranba, shi baima cikin hayyacinsa, Dan su Nuren saida suka shak’a masa Abu, Alhj Darma da m. Saminu ne kawai ba’a d’aureba, suma dai aka kawosu gabansa aka zube.
Galadima ya d’ago yana kallon su Muftahu dasuka Gaza barin kallonsa, cikin ta6e baki yace, “kallonfa?”.
Ajiyar zuciya suka saki a tare, Nuren yace, “Brother mufa bamu fahimtaba”.
Lips yad’an ciza yana ta6e baki da fad’in “Duk wannan dalla-dalla d’in da akai muku?”.
Shiru sukayi Dan inhar a fahimtarsuce dai yau sunzama Kidnappers Na gaskiya kenan????.
Galadima yace, “Well, Ku ajiye zancen fahimta gefe, kuduba phones d’in su Wanda babu charge a saka, Dan zuwa safiya duk za a fara aiki dasu, daganan mai buk’atar barci yaje ya kwanta kawai, sauran aiki sai safiyar gobe”.
Babu Wanda ya iya cewa komai, dan sunsan dai Galadima bazai sakasu a had’ariba saboda son zuciya, Ameer ya fidda Chargers suka saka dukkan wayoyi ajikin caji, Dan akwai wuta.

A wannan daren Galadima ya tura sak’o ga dukkan iyayen yaran, lokacin duk sunbar wajen Abba sun koma gida, anbarsa da garadan samarinnan akan sai washe gari, Dan sun tsarama su Zarah duk yanda zasuyi.

Babbar magana, Alhaji Mansur habibu Uba yana shirin kwanciya barci wayarsa tayi tsuwar shigowar sak’o, sharewa yayi, hakan kuma saiya saka matarsa a zargi, tatashi zata d’auki wayar ya hana, saita kuma tsarguwa, a zarginta wata shegiyarce ta turo masa, ganin ta fusata saiya bud’e sak’on.
Babu shiri ya dirgo daga gadon a tsorace yana tambayarta ina nerh-nerh take?.
Da mamaki race, “batace ta sanar maka zataje wajen Rahma ta kwanaba?”.
A rikice yace, “Rahmar ubanwa, maza kiramin ita yanzunnan su Abubakar suje su d’akkota”..
Bata fahimci inda ya dosaba, amma rikicewarsa saiya sakata d’aukar waya ta kira nerh-nerh d’iyarsu, wayar na Shiga amma ank’i d’agawa, cikin tsantsar tashin hankali ta sanar masa, ya daka mata tsawa yana fad’i “ki kira Rahma d’in ko wani d’an gidansu mana!!”.
Maida akalar kiran tayi kan Rahma, itama dai ank’i a d’aga, bataso kiran Hajiya yalwa ba, dan atunaninta kota kwanta, amma dole ta kiratan.
Hajiya yalwa Na zaune kusada mijinta Alhaji Abdul-Naseer Nafi’u kiran ya shigo, tayi mamakin Kiran, Dan hajia Marya bata kiranta a irin wannan time d’in, saitayi tunanin ko takasa hak’urine da rashin nerh-nerh abinka ga auta. Cikin raha tayi picking tana nunama mijinta wayar da baki, yay y’ar dariyarsu ta manya yana kuma kishingid’a da zubama matar tashi idanu.
Tambayar da Hajiya Marya tama hajiya yalwa ce ta rikitata, ta mik’e zumbur tana fad’in “bara Na duba to, Dan wajen 3pm suncemin zasuje zaga gari, amma 7 zasu dawo gida, to wlhy bak’i mukayi suka d’auke hankalina nikuma ban nemi ganinsuba, tunda ina tunanin sundawo suna sashen Rahma”.
Duk kiranda Alhaji Abdul-Naseer kema hajiya yalwa batajishiba, hakan ya sakashi biyota.
Kusan atare suka iso sashen Rahma d’iyarsu, y’an aikinta guda biyu Na zaune a falonta sunata gyangyad’i, kai kace sashen wata mai aurene ba budurwa y’ar 17years ba, Dan itace autarsu suma.
Hajiya yalwa ta dakama masu aikin tsawa tana tambayarsu ina su Rahma?.
A rikice sukace suma dawowarta suke jira tun d’azun (Dan sunsan inhar ta iske sunyi barci zasu yabama aya zak’inta, maybe ma yazama sanadin barin aikinsu).
Alhaji Abdul-Naseer yana k’ok’arin gwada kiran Rahma shima irin sak’on Alhaji Mansur ya shigo masa.
Ai sai suka kuma rikicewa, Ashe sak’o dukya jema sauran abokansu, dan dannan suka Shiga kiran juna kowa yana tabbatarwa d’an uwansa Galadima ya d’auke masa d’a ko y’a.
A wannan Daren suka sanarma police, gidajennan 11 babu Wanda ya rintsa barci, dukda yaran 8 ne a hannun Galadima, biyu basuda sauran yara a gabansu, duk sunyi aure, Galadima kuma yakafa musu nasu tarkon ne daban, biyu kuma a ciki bamasu ta6a haihuwa ba, biyar sun mutu yace bashida matsala da matacce, shi wannan saisunje babbar Court ALLAH zaimusu nasu hisabin. Sauran yaransu irinsu Alh halliru kuma yace nasu mai sauk’ine tunda manyansa suna hannunsa.
Tun a wannan daren manyan police suka Shiga Neman ina Galadima yake, tunda kai tsaye yasaka sunansa a sak’on messages d’in daya turama iyayen yaran.

Galadima yarigada ya tsara komai yanda ya dace, duk wata waya dazata fita a wayarsu saiya ganta yakumayi recoding d’in maganar, wannan yasa duk abinda suka fad’ama police yaji, murmushi kawai yaytayi, yayinda su Nuren sudai hankalinsu bai wani kwantaba, dukda sunji dad’in rikicewar da mak’iyar Galadima sukayi.
Abinka ga manya, tun a labaran 12am Na daren ranar aka fara saka maganar, labari yafara shiga kunnuwan wad’anda basuyi barciba.
Ciki kuwa harda y’an masarautar gagara badau.
Hankalin mai martaba ya tashi, a Daren ya aika jakadiya data rako matarsa turakarsa kiran Galadima, danya kira wayarsa switch up.
Lokacin da jakadiya taje sark’in k’ofa ya tabbatar mata Galadima ya fita tun farkon dare.
Komawa jakadiya tayi ta sanarma mai martaba, aiko yakuma shiga tashin hankali, minene haka Sameer dayake kallo mai nutsuwa da hankali ya aikata?.
Yana cikin wannan damuwa Waziri ya kirashi, ya tabbatarmasa Sameer ya turo masa sak’o shima Harun yana hannunsa.
Zuface ta shiga jik’a mai martaba, yanzunan duk jajen da akeyi Na 6atan Harun d’an waziri dama Sameer yasani amma yay kunnen uwar shegu da kowa, hazbinallahu wa ni’imal wakil, shikam baya fata wannan mummunan labarin yaje kunnen ‘Dan uwansa dake kwance cikin halin matsananciyar jiyya (kunsanfa har yanzu babu Wanda yasan samun sauk’i da Abie yakeyi, bayan ahalinsa dasu papi) a gagara badau babu Wanda yasani.

Su Galadima duk suna ganin abinda ke faruwa a TV suma, amma ko’a kwalar rigarsa, damuwa d’aya kecin ransa halinda Abban Munaya ya tsinci kansa a ciki, amma sauran matsalolin dama dukya dad’e da shirya abinsa, komi zai biyo baya dama zuciyarsa ta shirya d’auka.
Yau dai kam kusan a zaune suka kwana, abin tausayi saiga Galadima da kwannan kujera, aiko yasha wahala, Dan tashi yayi jikinsa Na matuk’ar masa ciwo, d’akin da aka saka masa kayansa yashiga, yasamu yay wanka sannan yayo alwala sukayi salla a jam’i, Dan har yaran duk kwancesu akayi, wad’anda kuma basayi suna zaune daga gefe.
Galadima yace Ameer yaje da y’ammatan su had’a musu breakfast, cikin cika umarni yatasasu gaba suka fice, saidai kuma Farhat ce kawai ta iya girkin a cikinsu, gashi tanada Asthma, bakomai take iya sakewa wajen yiba, haka dai Ameer ya saka Nerh-nerh da Rahma suka taimaka mata da Abu mai sauk’i, dayake a tsorace suke, komai aka saka su yi sukeyi, sunga zuk’ek’iyar bindiga ahannun Ameer yo????.

Koda aka kawo abincin dukda tashin k’amshi da yakeyi Galadima cayay bazai ciba, sudai su Muftahu kam ci sukayi, shikuwa yak’are dacin cake da tea, Wanda dama da kayayyakinsa yazo caf (Galadima fa da shirin zama yazo?? fans).

Tun’a daren jiya gidan da su Galadima suke aka zagayeshi da y’an sanda, yasan kuma da hakan Dan CCTV Na nuna masa komai, amma saiyayi tamkar baima San da zuwansuba.
Harun dai yak’i ci shima, hasalima sai yankama Galadima magana yake, wai inhar ya isa shid’in shegene ya kwanceshi mana, Ashe shid’in matsoracine ma, Dan ba’a sake d’aure kowaba bayan sunyi salla saishi Harun d’in daya nemi yin gardamar k’in nutsuwa waje d’aya.
Ko inda yake Galadima bai kallaba.

Nuren yay gyaran murya, duk suka maida attentions d’insu garesa. Yace, “inhar kun shirya bamu had’inkai kowa zai fita a gidannan lafiya babu ko kwarzane a jikinsa, Dan bamuda matsala daku, da iyayenku mukeyi, Wanda yaza6i kuma tafiya barzahu babu shiri saiya nuna jarumtarsa ko rashin kunya, wannan wawanma ya isheku izna”. Yay maganar yana nuna Harun daketa bige-bige yana kumfar baki masifa.
Duk suka amsa da zasu bada had’inkai.
Yau dai Darma kam shima yashiga hankalinsa, Dan yaga lamarin yafi k’arfinsa.
Galadima ya d’auki k’aramar wata waya dake kusa dashi yafara dannawa yana shan tea d’insa hankali kwance, yayinda k’afarsa ke hard’e d’aya kan d’aya.
Munaya ya kira, wadda itama batayi isashen barciba, gashi suna a yanayin rashin tsarki balle ta duk’ufa gayama ubangiji itama, amma dukda hakan bata fasaba, zuwa dare kuma kowa ya ankara da rashin dawowar Abba akwai matsala, dan around 7:30pm Baba k’arami ya dawo gida, babu dad’ewa kuma saiga Dady shima, dawowarsu yasaka kowa Sanin mi ake ciki, innaro ce kawai aka hana kowa ya sanar mata.
Babu Wanda yay barcin kwanciyar hankali a gidan su Munaya, saidai yaran k’anana dabasu San dawan garinba, irinsu Inna ma ai akan sallaya suka kwana suna gayama ALLAH kukansu??.
Basuda wuta a daren jiya, shiyyasa basuga abinda yake faruwaba, rashin kwanciyar hankali ya hana a kunna musu gen…, Gasu Abdurraheem kwana sukayi kuka.??????
Cikin sanyin jiki Munaya ta d’aga kiran, muryarta ta dushe saboda kuka, ahaka ta gaisheshi.
Ya amsa a sanyaye shima yana tambayar yaranshi, tace, barci sukeyi.
Cikin lumshe ido yace, “karki damu daduk abinda zaki gani, sannan karki kirani, dan duk kiran dazakiyi nasan baizama lallai nikad’aine zan jishiba, zan dinga kiranki dakaina insha ALLAH. Please take care of yourself”. Kitt ya yanke wayar batare da yajira cewarta ba.
Kanta ta cusa cikin k’afafu ta fashe da kuka, yayinda Munubiya ma ke gefenta tana nata da shayar da Ameen daya tashi barci.

Galadima kuwa yana yanke wayar ya mik’e cikin takun izza da k’asaita ya k’arasa gaban Harun da bakinsa yakasa yin shiru.
Izzarsa da k’asaitarsa Na burge matasan samarin nan, hakan yasa duk suka bishi da idanu har y’ammatan, ga fuska a cakud’e babu alamar yasan minenema dariya.
Gaban Harun ya tsaya hannayensa duka a cikin aljihun wandonsa, babu Wanda yakula da lokacinda Galadima yaciro hannunsa d’aya a aljihu, saidai k’arar mazgar Harun dayayi abaki sukaji kawai, kafin Harun ya farfad’o Galadima yakuma k’ara masa ta d’ayan gefen.
Sannan ya d’an risuno yanama bakinsa alamar zip da yatsunsa biyu??, Harun yamasa shiru kenan??.

Kutt, gaskiyafa Harun ya mazgu babu k’arya????.

Amma d’an bala’in naku bakinsa bai mutuba, bayan ya farfad’o daga azabar dukan saiya cigaba da magana cikin haki da huci.
Sharesa Galadima yayi yakoma ya zauna dan fuskantar abinda ke a gabansa, a fusace ya d’auki k’aramar bindigar daya fiddo yanzu yafara Harbin inda Harun yake, ta saitin k’afafunsa. Rikicewa kowa yayi, Harun yashiga mutsu-mutsu da k’afafu yanasan d’agewa Dan kar Harbin ya sameshi.

K’aramin d’an iska Ashe kanajin tsoron mutuwa???.

Wannan harbi ya kid’ima police d’in dake a wajen gidan, akuma dai-dai lokacinne manyansu suna iso suma, kuma duk sunji harbin………….???

Humm babbar magana, komiye shirin Galadima Na zama kidnapper?.??????
Wane ahiri kuma su Zarah sukazo dashi gida?????.
Sannan wane shiri Galadima yake akan ku6tar Abba? tunda yace plan B???.

Ina baba mai kanwa? Wane taimako zaibamu shima??.

 

Kumuje zuwa my guys karku k’osa dai, sannu-sannu bata hana zuwa, saidai a dad’e ba’a zoba????.

 

 

 

ALLAH ya gafartama mahaifanmu??????
Typing??

 

??HASKE WRITERS ASSO….

?RAINA KAMA…!!?
(Kaga gayya)

Bilyn Abdull ce????

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply