Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 8


Raina Kama Book 2 Page 8
Viral

Book 2~ ????8?

………Tunda aka bud’e mana muka fito hadimansa sukayo caa akan mu, kowanne k’ok’arin nuna farincikin sa yake ga Galadima.
Casuke ALLAH dai ya infanta mana, ranki ya dad’e ALLAH ya saukeki lafiya.
Cikin tsantsar farinciki yake amsa musu, murmushi yak’i barin fuskarsa.
Nikam zuciyata Ce ta shiga tsitstsinkewa, idan har Na fahimci inda zancensu ya nufa cikine dani kokuma wani keda cikin? Galadima Na kalla, amma saiyamin wani miskilin murmushi yana kauda idonsa, alk’yabbar jikinace kawai taima mutane katanga da ganin zufar data gama jik’emin jiki.
Tun a falon farko Na dakatar da kuyangin da damuke tare, handbag d’ita Na kar6a nace suje nagode. cikeda girmamawa suka amsamin suka fita suna min addu’ar k’ara samun lafiya. suna fita na juyo ga Galadima, amma tuni ya shige d’akinsa. handbag d’in Na dungurar saman kujera nabi bayansa, hankalina bazai ta6a kwanciya ba sainaji gaskiyar lamarinnan.
Na iske babu kowa a falonsa, Dan haka nashiga bedroom d’insa, ranar farko kenan dazan fara shiga bedroom d’in. babu kowa nanma, sai motsin ruwa dana jiyo a bathroom.
Waige-waige nafarayi ina k’arema d’akin kallo, komai ya birgeni a d’akin, sai k’amshin mayen turarensa da ya mannema d’akin. karaf idona ya sauka ga takarda kusada kayan daya cire, mik’ewa nayi Na d’akkota, Na dawo Na zauna. cikin nutsuwata nafara karantawa, nai mugun waro idanu ina fad’in “wlhy impossible, abindama bazai ta6a yuwuwaba kenan” sai kuma Na fashe da kuka.
Dai-dai lokacin Galadima ya fito daga bathroom, sanye yake da rigar wanka fara, ahankali ya ringa takowa idonsa a kaina, sai dai fuskarsa a d’aure take tamkar bashine cikin walwala ba a asibiti.
Bai k’araso inda nakeba ya tsaya a tsakkiyar d’akin ya cigaba da goge ruwan kansa zuwa fuska hankalinsa kwance. a harzuk’e nayo Kansa ina cigaba da kukana, naja birki a gabansa, da d’anyatsa Na nuna masa takardar, har yanzu kuma kukan nakeyi, nace “wannan cikin a jikin wa ake nufin yake?”.
d’auke fuskarsa yayi daga kallona yana wani lumshe idanu, batare daya bani amsa ba ya taka zuwa wajen mirror, cikeda izza yace “sunanwa kika gani a jikin takardar?”.
Da sauri Na ruk’o bathtub d’in jikinsa, cak ya tsaya, murmushin gefen baki yayi, saikuma ya kuma d’aure fuska sannan ya juyo yana fuskanta ta, inda Na rik’e ya kalla yana fad’in “kona kwance miki igiyar ne?”.
Sakin rigar nai da sauri ina share kwalla, cike da tsiwa nace “aini ba ‘Yar iska bace ba”.
Shikuma cikin gatse yace, “amma kikayi ciki?”.
Hannu na aza akaina nakuma fashewa da kuka, “wlhy koma mi za’ayi sai dai ayi bazan haifi wannan cikinba, aiba haka mukayi da kaiba, kawai daga auren Contract sai aganni da ciki? ka tabbatar saina zubar dashi yau d’innan, dan bazanje gidan miji da agola ba, ba kuma zan haifi d’ana Na bari gidan wani ba matar uba ta kashemin”.
Da k’yar ya iya danne dariyar dake k’ok’arin kufce masa, yay saurin cafko hannuna saboda zaburar danayi xan fita.
“k yi ahankali karkimin asarar abin cikin kwan fa”.
Wani bak’in cikine ya turnuk’omin, Na harzuk’o masa da masifa amma saiya wani tsare gida, dolena Na had’iye maganar nacigaba da kukana.
Shikuma ya watsa mini harara yana jan tagwayen tsaki, sannan yaja da baya yakoma bakin gadonsa ya zauna.
Durk’ushewa nayi saman carpet d’in gaban gadon Na fashe da kuka mai tsuma rai ina rok’onsa. “dan girman ALLAH ka kaini a zubda cikinnan, kafa tuna da Girman alk’awari, a auren yarjejeniyarmu babu wannan, aikin had’in guywa ka nemeni muyi, kaifa ka tabbatarmin da zaka kasance mai cika alk’awari aranda Na kwana biyu a masarautarnan, miyasa yanzu zaka kasa cikawa? kacemin a matsayin kuskure abinda yafaru ranar ya faru, dukda zuciyata Na cike da bak’in cikin faruwar tasa haka Na hak’ura Na danne Na yarda dakai, ka taimakeni mu rabu cikin salama batareda d’ayanmu ya cutuba, karka k’ask’antar da rayuwata saboda kana ganina mace kuma talaka wadda take k’ark’ashin mulkinka, kamin adalci Dan girman ALLAH Muhammad Sameer”.

Tunda munaya tafara magana Galadima ya tsaya daga k’ok’arin fara shafa man da yakeyi, idanunsa ya tsura mata, dukkan maganarta ta shigesa, dukda yana k’aunar cikin dake jikinta shima baiso gudan jininsa yazo ta wannan hanyar da babu soyayya tsakaninsa da mahaifiyar d’ansa ba, sai dai wayonsa ko dabararsa bazai ta6a canja k’addararsu ba shi da ita. da k’arfi ya cije lips nashi tamkar zai hudasu da hak’ori.
Ya mik’e tsaye yana mai fidda huci mai zafi, takawa yay zuwa jikin window n d’akin, ya zuge labilan yana kallon waje, bayi keta kaikawonsu hankali kwance, dukda kasancewar rana ta take. ya maida labilan ya rufe Yakoma takowa tsakkiyar d’akin yana fad’in “tabbas ni Muhammad Sameer mai cika alk’awarine, kuma dukkan alk’awarin Dana d’auka miki ina k’ok’arin cikasu, sai dai nayi kuskure d’aya a cikin AUREN YARJEJENIYA, Na manta da babbar rahamar da ubangiji yake shinfid’awa ga dukkan wasu ma’aurata dazasu iya killace Kansu a matsugunni d’aya, Na manta da ko babu aure tsakanin mace da namiji inhar zasu kasance waje d’aya shaid’an yakan iya zama Na ukunsu ya sakasu aikata sa6o, balle mu da Muke ganin akwai igiyar aure a tsakaninmu, gaskiya kika fad’a, munyi yarjejeniyar aure domin gano mak’iyanmu bata zama Abu d’aya ba, amma kuma sai bamu d’auki matakan dazamu nisanta kawunanmu ba, daga ni har ke bamu Isa hana ubangiji ikonsa ba akanmu, tabbas ALLAH shidane bada gangan Na kusancekiba a wancan lokacin, sannan bansan ciki ya shiga jikinki ba, to mizaisa kizo ki titsiyeni kina min bore akan zubda shi. Bara kiji Na tabbatar miki yarinya, koda ace ta hanyar aikata zina Na Samar da wannan cikin inason abuna, kuma baza a zubarmin ba, ballantana sadaki Na biya d’unbin mutane suka shaida ke matata ce, mu uku kad’ai mukasan da wani Auren Contract. Dan haka kima nutsu idan zaki nutsu, kamar yanda kikace Duk abinda za’ayi saikin zubar da ciki ko? to Nima duk abinda zai faru saidai ya faru, babu ubanda ya Isa yasaka a zubar da cikinnan, sai dai idan Wanda yabani ne ya kar6a banida ikon hana wannan, idan kin gadama kici gaba da duk abinda kikeso har k’udirin zubda cikin, ni kuma Muhammad Sameer ina mai miki rantsuwa da ALLAH saina nuna miki ainahin color d’ina”. ‘ya k’are maganar da buga yatsunsa biyu suka bada sautin d’ass! d’ass!! A saitin fuskarta’.
Fita munaya tayi da gudu daga bathroom d’in tana kuka, ahaka ta isa bedroom d’inta ta fad’a saman gado.
Shi kuma tana fita yaja wani wawan tsaki ya fad’a kan gado yana dafe kansa dake sara masa. ga wata yunwa dake cinsa, shi saima yanzu ya tuna ko breakfast basuyiba suka fita, tsaki kawai yaja yana jawo wayarsa. number Nuren ya kira, bugu biyu ya d’aga yana tsokanarsa da fad’in “ho angon k’arni”. Galadima ya danne 6acin ransa, dan baya buk’atar kowa yasan wannan matsalar data kunne kai tsakaninsa da Munaya, muryarsa a sake yace “kun gama ne?”.
“eh mun kammala, saidai kuma baka fad’i dawa-dawa za’ama visa ba cikin ‘yan gidan nasu?”.
Ya cije lips nashi yana gyara kwanciya, “tokai dawa yaka mata kake ganin zasu tafi?”.
“eh, indai tanine gaskiya yakamata ace cikin k’annensa d’aya yaje, sai kuma mummynsu gimbiyarmu itama, tunda kaga itace first wife nashi”.
“Okay hakan yayi, zuwa dare sai muje gidan muji yanda zasuyi, nasan kai dai bazaka shigo nanba, please kabama Sauban Abinci ya shigo mana dashi, dan ko breakfast My mata batayi ba”.
“kai brother amma wannan sakacine ai, gashi ba ita kad’aiba?”.
“wlhy Na mantane, saboda kaga ai yanayin da take tun barinmu gidan, inaga zanma inno magana a bamu mai abinci kawai”.
“hakan zaifi kam, bara Na bashi ya taho yanzu kawai, amma zuwa anjima fa saika fito mun had’u”.
“okay babu damuwa”.

Yana yanke wayar kiran papi Na shigowa, fuskarsa d’auke da murmushi yay picking. cike da girmamawa yace “ran papinmu ya dad’e tare da k’yak’yk’yawan aminci”.
“tunda kamin laifi fa ai dole ka faramin da dad’in baki”.
Murmushi Galadima yayi har sarki Abdul’fatah na jiyo sautinsa, yace “a gafarceni ranka ya dad’e. ina fatan kuna cikin k’oshin lafiya kaida inno da dukkan ahalin masarautarka?”.
“Alhmdllh Muhammadu. sai kuma wasu k’yawawan albishir suka riskemu a wannan rana. to ALLAH ya inganta, ya sauketa lafiya, shi kuma mahaifinka ALLAH yaci gaba da d’orar da lafiyarsa”.
“Amin ya rabbi ranka ya dad’e ”.
“Muhammad mikuma ya faru da sirikinka haka mara dad’in ji?”.
“humm, ranka ya dad’e bansan miya sakoshi cikiba shi kuma?”.
Murmushi mai sauti papi yayi, ya gyara zamansa akan kilisarsa, cikin nuna kulawa yace, “akwai abinda bamu saniba ne kawai, amma a fiddashi daga k’asar kafin mu fara wani yunk’uri”.
Kamar Galadima na gabansa yashiga jinjina kansa, “to insha ALLAH zuwa gobe da daddare idan ALLAH ya kaimu zasu wuce”.
“hakan yayi, aci gaba da hak’uri dai kaji Muhammad, hak’uri jarine, jarabawa kuma tsanice ta zuwa wajen nasara, ALLAH yayi muku albarka”.
“amin ranka ya dad’e, nagode sosai”.
“yaushe zaku shigo?”.
Murmushi Galadima yayi, hakan yana nufin kakansa nason ganinsa kenan, a ladabce yace “dasun tafi insha ALLAH ”.
“ALLAH ya kawoku lafiya”.

Tunda suka katse wayar saiyayta sauke ajiyar zuciya, koba komai ya sami nutsuwa akan wayar dasukai da papi. tashi yay ya k’arasa shafa man, sannan yasaka kayan da bazasu takurashi ba.
Falonsa ya fito, abinda ake nunawa a tv ya d’auki hankalinsa sosai, ana cigiyar d’iyar Minister Ce, wai an nemeta an rasa tun a daren jiya. Akan la66ansa ya furta “Nuren!” Sai kuma yayi murmushi kawai ya kwanta saman doguwar kujera.
A haka Sauban ya shigo ya sameshi da sallama, sai bayi buyu dake binsa a baya d’auke da ledoji.
Galadima ya bud’e idanunsa yana kallonsu amma bai tashiba, bayan bayin sun ajiye suka zube sunama Galadima barka da hutawa, murmushi kawai ya musu ya d’aga musu hannu.
Sauban yabasu izinin tafiya.
Zama Sauban yayi a kujerar dake kallon Galadima, “kai yau ina cikin nishad’i wlhy yaa Sam…”
Kallonsa Galadima yayi yana d’an murmushi, amma baice komaiba.
Sauban yace “yaa Sam… Aunty gimbiya fa?”..
Galadima yace “barci takeyi”.
“tofa Unborn babynmu yazo da sabon salo kenan”.
Hararsa Galadima yayi, ya mik’e yana dariya ya shige bedroom.
Galadima ya girgiza kai kawai yana tashi zaune. ledojin ya duba dan ganin mi suka sayo?.
Abinda yasan zata iya ci ya d’auka ya fita.
Saida ya d’anyi jimm a k’ofar d’akin sannan ya shiga da sallama, har yanzu tana a kwance tana kuka, lips d’insa ya d’an cija sannan ya ajiye abin hannunsa saman table d’in dake gaban gadon, idanu ya tsura ma bayanta nawasu ‘yan seconds, ko alk’yabbar bata cireba, zama yayi a bakin gadon kusada ita, amma ya juya mata baya.
Tun daga shigowarsa har zamansa tana jinsa, amma ko motsi batayiba, kusan mintuna 3 suna zaune a haka, ganin batada niyyar tashi ko kulashi ya sakashi juyawa yana kallonta, gyaran murya yayi sannan yace, “tashi kici abinci”.
Shiru tayi ta shareshi, ko motsima bata yiba.
Tsawa ya daka mata, babu shiri ta tashi zaune, jikinta sai rawa yakeyi, tunba yanzuba munaya akwai tsoron tsawa, bata barin saita kwana amma batason amata tsawa. Shi kansa yayi mamakin tsoratar tata, ya watsa mata harara yana kwafa, sai kuma yaja tsaki, alk’yabbar yacire mata, sai hawaye take zirarwa, bai kuma cemata uffanba ya bud’e abincin ya ajiye a gabanta, kafeta kawai yayi da idanu, hakan saiya tasirantar da tsoronsa a zuciyarta, dan haka tafara cin abincin, tanayi dai hawaye na zurara, cikin nata bamai tsurfa baneba, komai ci take hankali kwance, sai dai laulayi na ciwo.
Dolenta ta saki jiki taci abincin, danya kafeta da idanu ga fuska cid’in-cid’in, duk jarumtarka dolene kaji shakkarsa.
Kallo d’aga tamasa ta janye idonta, shi kuma ya harareta yana fad’in “kin k’oshi ne?”.
Kanta ta jinjina masa tana matso kwalla. baice komaiba ya sauke sauran abincin k’asa, sannan yace “sauka kije kiyi wanka”.
Baki ta bud’e zatayi magana ya dalla mata harara. sauka tayi tana k’unk’uni akan la66a. yana kallon motsin la66an nata, sai dai bayajin mi take fad’a.

Yau kam Alhmdllh taji dad’in jikinta, ko k’arin ruwan da aka saka matane yasakata jin kwarin oho, ruwa mai d’an d’umi ta tara tayi wankan, tanayi tana hawaye, itafa ko mi zaiyi ba masifaba bazata bar cikinnan ba, babu yanda za’ayi ta reni ciki ta haifeshi sannan yazo daga baya ya saketa, bazata d’auki wannan rainin hankalinba, su maza a kullum d’aukar mace suke mai k’arancin tunani, kowane yayin rashin mutuncinsu suka kwaso saiya k’are akan mata, wlhy akan cikinnan tata d’aga masa hankali kenan harsai ya amince an zubar dashi sannan, kuma ana zubarwa zata k’ara gaba, mahaifinsa kam kobasa tare insha ALLAH zata cigaba da masa addu’oi ana aika masa.

Jin shiru tak’i fitowa ya sakashi mik’ewa, bai wani kwankwasa ba ya bud’e k’ofar bathroom d’in kawai, danshi zatonsa ba wankan takeba ta tsaya kukane.
A birkice munaya ta kalli k’ofar, ganin Galadima tsaye yana kallonta ta fasa k’ara, yay hanzarin ida shiga bayin ya rufe bakinta da tafin hannunsa dankar ta tara masa jama’a.
Juyawa tayi ta ruk’unk’umesa, tare da saka hannayenta ta zagaye bayansa ta manne k’irjinta da nasa, ita duk bata son yaga jikinta ne????.
Shima fuskantar hakan da yayi ya sakashi sakin murmushi, saiya saka hannunsa biyu ya zagaye bayanta ya manneta sosai a jikin nasa.
Shiru sukayi nawasu seconds, tana sauke ajiyar zuciya shima yana saukewa, saboda yanason ganin yanda zatayi saiya fara k’ok’arin janye jikinsa itama zai janye ta.
K’ank’ameshi tayi ta fashe da kuka, jiyay tamkar ya kwashe da dariya, amma saiya daure, cikin dakiya yace, “malama sakeni mana? konaci bashinki ne wai?”.
Cikin dasashshiyar muryarta datasha kuka tace, “to kabani zanina da hijjab na saka”.
“to kin k’udunduneni ta ina zan iya baki wani zani? sakeni saina baki”.
Kafad’a ta nok’e alamar tak’i.
Murmushi Galadima yayi, ya shafa bayanta cikin murya k’asa-k’asa yace, “idan an hanani ganin can ai gashi ina kallon nan”.
Da sauri tayi wata wulk’itawa ta koma bayansa ta 6uya.
Kansa ya dafe yana fad’in “yau Sameer kaga ta kanka, ranar farin cikinka sai saka maka ciwon kai da zafin kai akeyi, wai ke yalla6iya mikike 6oyemin daban saniba ne?”.
Baki ta murgud’a masa tana fari da idanu, dayake ba ganinta yakeba baisan hidimar datakeyi ba.
K’ok’arin juyo da ita ya farayi amma tabi ta kanannad’e shi, rasa yanda zai mata yayi. yakula yarinyarnan ‘Yar daruce kawai. zaninta ya jawo ya mik’a mata, saida ta tabbatar ta d’aura sannan ta sakeshi, yana juyowa ta juya masa baya ita kuma.
Baice komaiba ya ta6e baki ya fice daga bathroom d’in.
Harar bayansa tayi ta na fad’in “ALLAH ya isana”.

Nace Humm.??

Fita yay daga d’akin gaba d’aya, tunda dai yasamu taci abincin, harya kai k’ofarsa ya tuna batasha maganinta ba, dawowa yayi da baya.
Ita kuma motsin fitarsa dataji yabata kwarin guywar fitowa.
Shigowarsa tasata kwakumar hijjab ta saka, bakinsa ya ta6e ya wuce wajen handbag d’inta batare daya kalleta ba.
Magungunan ya fido, ya zauna bakin gadon, “kizo kisha magani”. ya fad’a cikin k’asaitarsa.
6ata fuska tayi, tace “babu amfanin tattalin abinda za’a zubar ai”.
Lips d’insa ya cije, sai kuma ya ajiye drugs d’in yana kallonta, mik’ewa yayi ya taka inda take, a bayanta ya tsaya, fisgota yayi ta fad’o saman k’irjinsa, saida ta rumtse ido dan zafin dataji, ya matso da fuskarsa daf da tata, a wani yanayin data kasa fassarawa yace “adadin nawa kike buk’atar na biyaki danki barsa?”.
Rik’esa nayi da k’yau gudun karna fad’i, na janye idona dake cike da kwalla daga cikin nasa, “Bana buk’atar ko sisinka yalla6ai, cikinne kawai bana buk’ata, kuma bazan raineshi ba balle nakai ga haifeshi”.
Wani murmushi mugunta yayi, sanan ya sakeni tamkar zai hankad’ani, mikuma ya tuna oho masa, saiya kuma damk’e hannuna, muryarsa a kausashe yace “wlhy idan kinga baki haifi cikin nanba to sai dai idan wanine a cikinmu numfashinsa yabar gangar jikinsa, sai kuma idan ubangiji ya kaddara Shiba mai Shak’ar iskar duniya bane, dan bani da hakk’in kowa, ubangiji kuma bazai barki ki shiga nawa ba”.
yana gama fad’ar haka ya saki hannuna yafice daga d’akin baki d’aya.

Yariga yasan zai fuskanci abindama yafi haka daga munaya, shiyyasa bai zafafama zuciyarsa akan wannan rikicin nata ba, shi babbanma burinsa yanzu Abbanta yabar k’asar nan, danya samu damar gudanar da aikinsa yanda ya kama ta.
Da wannan tunanin ya dawo d’akinsa, ya iske Sauban kwance wai zaiyi barci, hararsa yayi yana fad’in “ kama tashi, time d’in zuhur yayi.

Yana fita na raka bayansa da harara ina murgid’a baki, “oho dai, koma mizaka fad’a ka fad’a, nima ai bani tare da hak’k’in kowan, ALLAH kuma bazai baka damar danne nawaba, sokake nazama shashar mace ko? munyi auren contract batare da sanin iyayena ko naka ba, kazo kamin ciki na haifa maka ka sakeni na koma gidanmu, katashi da riba biyu kenan, nikuma babu ko d’aya sai bak’incikin danakema iyayena tanadi da kaina, Galadima ko a matanma ai _AKWAI BANBANCI?_ wlhy.

gaskiyane Munaya, rik’e darajarki shine ‘yancinki??????.

*******

Bayan sun fito massalaci sukejin labarin wai an rasa inda Muftahu yake, a safiyar yau aka samu motarsa a bud’e, sai kuma agogonsa da takalminsa d’aya a k’asa alamar da k’arfin tsiya aka saceshi.
Hakan yasaka aka kama dogaran dake tsaron k’ofa ta uku, dan anga alamun tanan aka fita dashi.
Dukda Galadima najin haushinsa saida hankalinsa ya tashi, dan haka suna shigowa ya d’au waya ya kira Nuren.
Nuren na d’aga wayar Galadima yace, “Nuren Muftahu, kaine ko?”.
“Muftahu kuma? nine naimi?”.
“A daren jiya an rasa Wanda ya bar masarauta dashi”.
“humm brother, dukda muna ganin Muftahu cikin masu mana zagon k’asa banta6a tunanin saina d’aukeshi zan gane hakaba, wlhy bani bane”.
“ya salam”. ‘galadima ya fad’a cikin dafe kai da cije lips, wayar ya yanke ya Shiga safa da marwa, yarasa wazai hararo.
Yana cikin wannan halin saiga harun shima a rikice, kowa yasan su ukunnan abokan junane, kuma akwai shak’uwa tsakaninsu, matawalle ne dama bai cika shiga cikinsu ba, saboda mama Fulani Na hanashi tun yana yaro, a cewarta shine d’an Sarki mai mulki, kuma shine mai jiran gado, darajarsa datasu Galadima ba dai-dai takeba, wannan hud’ubar ce tamasa tasiri sosai, amma yanason ‘yan uwansa har zuciyarsa.
“galadima shin kaji kuwa mike faruwa a masarautarnan?”.
Cikin damuwa Galadima yace, “Harun su waye da wannan aikin?”.
“kowa abinda yake tambaya kenan Sameer, Muftahu bashida wani abokin fad’a”.
Hankalin Galadima kuma tashi yayi, shi duk damuwarsa karda a cutar da Muftahu ta dalilinsa, tunda ya kula duk wani makusancinsu shine abin harin mak’iyansa. shifa baima yarda ba Nuren bane da wannan aikin, dan yasan halinsa sarai, dolene kuwa yafita wajensa yanzunnan.
Harun yace bara yaje, suna son akai report gidan radio da television.
Jin jina kai Galadima kawai yayi, shima ya shige ciki danya shirya.

Tun safe an sanarda jami’an tsaro 6atan Muftahu n, kuma suna a kan aikinsu.

???

Yunwar da yakeji tasashi bayan yayi shiri ya samu fresh milk yasha kawai, sannan yafito, d’akin Munaya ya lek’a, saiya isketa baje a gado tana shak’ar barci, baiyi yunk’urin tashinta ba yafito.
Har dogaransa sun taso yace suyi zamansu su huta, zai fita shida Sauban, cikin damuwa sarkin mota yace, “kayi hak’uri ranka ya dad’e, koda nine kawai mu fita, Mai martaba ya sanar yau a fada kar’a sake barin wani d’an gidannan yafita wani waje shi kad’ai”.
Kallonsa Galadima yayi, kamar zaiyi magana saikuma yafasa ya bud’e mortar da kansa ya shiga, batare da ya jira an bud’e masa ba.
Da hannu sarkin mota yayma sauran dogaran nuni da su biyosu a baya idan sun tafi.

A wani waje suka had’u da Nuren, Nuren ya fito daga motarsa yadawo inda Galadima yake, sai sarkin mota yafita yabasu waje kawai.
Galadima yace “please idan kaine ka sakeshi”.
Da mamaki Nuren yace, “wai Muftahu n dai? am telling you banida alak’a da d’aukarsa. yarinyar Minister ce kawai a hannuna”.
“innalillahi, wlhy Nuren inajin tsoro, karsuje su cutar dashi”.
“Sameer! nifa ina zargin kawai ya had’a baki da wasune suka kamashi dan yayi wasa da hankalinmu”.
Idanu Galadima ya tsurama Nuren tamkar yana hango gaskiyar maganarsa, ya saki wani guntun murmushi, sannan ya gyara zamansa yana fad’in “well, koma minene dai zai fito ai”.

Nuren yace “ni kaga dama kabar zancen wani Muftahu n banza can, way note mu wuce gidan sirikanka kozamu samu wasu evidence daga canma akan Accident d’innan”.
Agogon hannunsa ya kalla, sannan ya kalli Nuren d’in alamar suje.

Anan Nuren yabar motarsa suka tafi ata Galadima, saida suka fara tafiya Galadima ya lura da mototin dogaransa a bayansu.
d’an murmushi yayi yana kallon Sarkin mota, yace “sarkin mota an karya min doka kenan?”.
Sarkin mota daya fahimci Galadima yagane dogarai Na binsu sai yayi ‘yar dariya, yace “ka gafarceni ranka ya dad’e, bazai yuwu mu barka ka fita kai kad’aiba ai, dan fitarka babu kowa tafi ta kowa had’ari a masarautarnan, mai martaba ma nasan saboda kaine ya saka dokar ai”.
Galadima baice komaiba sai murmushi dayayi, Nuren ma murmushin yayi, sannan yace “amma kamar bayan motar dogaranka akwai wata bak’ar mota Na bin tasu?”.
Galadima ya juya shima, tabbas anabin motar dogaran a baya, “sarkin mota su wucemu, karsu tsaya”.
“To ranka ya dad’e”.
Bayan sarkin mota ya sanar musu suka wuce su Galadima, motarma ta wuce, da kallo Nuren da Galadima suka bita, Nuren yay hanzarin d’aukar motar hoto a wayarsa. “humm da alama suna zaton kana d’aya daga cikin motocin canne”.
Murmushi Galadima yayi, a k’asaitarsa yace, “kokuma suna son wasa da hankalinmu ba”.
Da mamaki Nuren yace “kamar ya?”.
Murmusawa Galadima ya kuma yi, ya kwantar da kansa jikin seat yana lumshe idanu, “Nuriddeen! Sameer ya wuce tunanin dukkan mai tunani, kai tsaye ba’a gane manufar zuciya, kwanji ko dama basu ke nuna k’arfin ikon mai ikoba, nazarin komai daki-daki da iya sarrafa duniya a yanda tazo shike nuna k’arfin gwarzan taka, mazantaka ba’a shaidata a fuskar namiji, duk lokacinda kai gamo da nama, kud’i, mata bisa hanya, karkayi rawarkan d’auka ko murnar ALLAH ne ya baka, zata iya yuwuwa tarko aka d’ana maka, shi k’yawu had’arine, 6oyeshi kuma nagartace, maiyi baya fad’an zaiyi, sai dai aga aikinsa a k’asa, tasowar iskar hadari bashi ke nufin ruwan zai zuba ba, watak’il sunan wannan iskar gyara kayanka. Dalili da dalilai basa ta6a saka zuciyar Wanda yake nema ta raunana, time d’in da zan nunama mak’iyan mahaifina d’an zaki ya girma yayi, sun durk’usar da shi a k’asa batareda tunaninsu yabasu ya haifi Raina kama ba, Su cigaba da raina aikin Muhammad Sameer daga k’arshe kuma saisuga gayya, tafiyar hawainiya bashike nufin gazawar kuzarinta bane, lokuta da dama hanzari kan katse igiyar cikar buri, a sannu kowa zai fahimci wanene *_RAINA KAMA….._*????
https://2gnblog.blogspot.com/
Ba Nuren ba hatta da sarkin mota maganganun Galadima ya shigeshi, tabbas mutane dayawa sunama Galadima kallon mutum mai yawan sakaci da rashin ho66asa, koshi yana d’aya daga ciki, amma wannan zantukan nasa sai suka sakasu a rud’ani, kenan akwai abinda sud’in basu saniba………..
Dole tunaninsu ya katse saboda isowarsu gidansu Munaya.

Fita sarkin mota yayi yanema musu iso, babu dad’ewa saiga baba k’arami ya fito, sarkin mota ya bud’ema Galadima, yayinda Nuren ya bud’e da kansa, zuciyarsa sai jujjuya hannunka mai sandar Galadima yakeyi.
Dukda baba k’arami yayi mamakin zuwan Galadima haka ya danne, yaymusu k’ar6a ta girma, sannan suka shiga cikin gidan.
Gidan tsitt tamkar babu mutane, saikace ba gidannan bane mai kama Dana ‘yan dambe??, (yo kowa Na tsoron a korashi gidansu????).
A falon daddy aka musu masauki, dan danan aka cika musu gaba da kayayyaki, baba k’arami ya fita domin basu damar cin wani Abu.
Babu abinda suka ta6a, dukda kuma Galadima ma yunwa yakeji, a haka daddy da baba k’arami suka dawo.
Daddy yace “anya kuwa wannan d’an namu yana d’aukar gidannan matsayin nasu?”.
Murmushi Galadima da Nuren sukayi, Galadima yace “sosaima daddy”.
Baba k’arami yace “ta INA zamu amince da haka kuwa, bayan inada tabbacin ko ruwan gidannan Baka ta6a sha ba”.
Kunya Ce ta kama Galadima, sai kuma yaga bai k’yautaba, ya rissinar da kai yana fad’in “amin afuwa zan gyara”.
Mik’ewa baba k’arami da daddy suka kumayi, “to mun bada dama ta biyu”. cewar Dady yana dariya.
Bayan fitarsu Nuren ya bud’e kulolin shima yana dariyar, danbun shinkafane daya samu nutsuwa ta musamman, sai k’amshi mai dad’i yakeyi, daga Galadima har nuren saida kwad’ayin cin abincin yazo musu.
Kallon Galadima Nuren yayi yana d’aga gira, Galadima yay murmusa tareda fad’in “kadaiji kunya”.
“kaima jinta zakayi yanzu, dan nasan ci zakayi”.

Yau dai kam Galadima yaci abincin gidansu Munaya, kuma gashi girkin innarsu, babu kunya sukaita zuba Santi shida Nuren sunama juna dariya, Galadima harda su6utar baki yana fad’in “amma my mata muguwace, bata ta6amin irin wannan ba”.??
Mi Nuren zaiyi inba dariya ba??, su Galadima anji dad’i har kwalwar kai Baki ya bud’e????.

Saida suka mammala tsaf sannan su baba k’arami suka dawo, sunji dad’i dasuka iske sunci.
Daga nan sukayi gaisuwa, su baba k’arami suka d’ora da godiyar d’awainiyar Abba da Galadima ya d’auke musu.
Murmushi kawai Galadima yayi.
Nuren ya gyara zama, a ladabce yamusu bayanin son fidda Abba da Galadima kesonyi, dan likitoci sunce ana buk’atar kulawa saboda karayar hak’ark’arinsa data k’ugu, “to yanzu haka dai angama setting d’in komai gameda tafiyarsa, har asibitin daza’a kaisa, visa d’insa da komai, sai dai anason tafiya da mutum biyu a cikinsu, mi kuka gani akan Wanda za’aje da shid’in?”.
Daddy da baba k’arami suka kalli juna, summa rasa wane irin farin ciki zasu nuna dan Galadima yasan sunji dad’i? sunta jero masa k’yawawan addu’oi, kafin daddy yace “ai kawai sai atafi da jafaru da Ai’sha, dan bai kamata mutafi mu duka ba gida babu kowa, dukda akwai su Anas, gakuma su Hameed zasuke zagayowa, amma hakan yafi dai.
Duk sun gamsu da hakan, dan haka suka buk’aci passport d’in baba k’arami da inna, ita inna babu, sai sunje an mata, amma baba k’arami an samu.
Sun bari akan zuwa anjima za’azo akai inna tayo.
Daga nan Galadima ya buk’aci number da aka kira aka sanar musu da accident d’in Abba.
Daddy yace Ai’sha aka kira, saidai akawo wayar tata. Kiranta yay yace tabama cikin su Aryaan ya kawo wayarta.
Babu dad’ewa saiga Aryaan d’in da ita, yanda yaron ya gaishesu saida abin ya birge Galadima, ya yarda yaran gidan akwai tarbiyya babu laifi kam.
Galadima yace, “amma Dady ko numbers nawa Abba ke amfani dasu?”.
baba k’arami ya bashi amsa da cewar “uku ne”.
Nuren yace “kozamu samesu dukansu?”.
Dukda baba k’arami da daddy sunshiga mamaki, dansu zukatansu basu kawo musu akwai wani Abu a k’asa ba, sun d’auka kawai Abba yayi Accident ne dai.
Baba k’arami yabasu Numbers d’in duka.
Bawani bincike Galadima yayi a wayar innarsu Munaya ba, wani Abu kawai ya saka (Wanda Nima ban saniba??) yabama Dady wayar yana fad’in “zata bar wayar anan dan a can bazatayi aikiba, kuma gashi muna buk’atar wayar, dan haka daddy saika rik’e a hannunka tunda kai kana gida”.
Dady ya amsa da to, duk su Galadima sun kuma sakasu a duhu.
Sallama sukai musu suna fito domin tafiya.
Harsun Shiga mota saiga Aiyaan da gud’u d’auke da wata Leda.
Sarkin mota ya tareshi yana fad’in yaro miya farune?”.
“Auntynmu za’a kaimawa inji innarmu”.
Galadima yayma sarkin mota nuni da yabar Aiyaan d’in ya k’araso.
Bud’e murfin Galadima yayi, Aiyaan ya k’arso, Galadima ya kamo hannun Aiyaan yana murmushi, “my friend ya akayi?”.
‘Uncle innarmu ce tace akaima Auntynmu dan ALLAH”.
murmushi Galadima yakumayi, sannan ya kar6i ledan yana fad’in “ita kad’ai banda ni?”.
Aiyaan yad’an zaro ido waje, sai kuma yace “to bara naje Na fad’am innarmu kaima ta baka naka”.
Da sauri Galadima ya kamo hannunsa dan yana neman tsillawa da gudune, “kaga dakata, idan naje saimu raba wannan da ita, yanzu dai ka fad’ama innarmu ta shiryaka gobe zan aiko a d’aukeka kazo ka zauna damu tunda kuna hutu ”.
Cikin murna Aiyaan yace, “wajen auntymu?”.
Galadima ya jinjina masa kai.
“to amma kuma Aryaan fa?”.
Cikin mamaki Galadima yace, “wanene Aryaan d’in?”.
“lah baka San mu 2wins bane ba?”.
“da gaske?”.
“ALLAH kuwa”.
“to shikenan, kacema innarmu ta shiryaku Ku duka biyun zakujema Aunty hutu”.
Cikeda murna Aiyaan ya shek’a da gudu gida danya kai labari.
Galadima yay murmushi yana rufe k’ofar motar, Nuren ma murmushi yakeyi, a fili yace, “yara sunyi wlhy”.
Galadima ya kalleshi, cikin d’age gira sama yace, “kayi aure”.
Sosai Nuren yay dariya.

******
A inda suka d’auki Nuren anan suka ajiyeshi, su kuma suka koma masarauta, sun iske tuni dogaran sun dawo abinsu.
d’akinsa ya Shiga, ya iske Sauban nata barcinsa.
Bai tadashiba, yadawo falo ya zauna.

_____________________________

Da daddare Galadima Na falonsa zaune yana aiki a system akayi knocking d’in k’ofa, izinin shigowa ya bada, sarkin mota ya shigo hannunsa d’auke da leda.
Galadima dake aikinsa bai d’agoba, a haka ya amsa gaisuwar sarkin mota.
Sarkin mota yace “ranka ya dad’e kayi mantuwane a mota ”.
d’agowa Galadima yayi ya kallesa, ganin ledar da Aiyaan ya kawo yatuna masa sak’on munaya, nuni yama sarkin mota daya ajiye.
Sarkin mota ya ajiye yana masa saida safe.
Nanma bai tankaba, kansa kawai ya jinjina masa.
Bayan fitar sarkin mota ya mik’e d’auke da laptop d’insa da ledar, dama tunda ya shigo baima lek’a ta ba, dan Sauban yace yakai mata abinci, kuma tun d’azu suna tare suna hira. Hakan yasa yagane shine ta raina kenan. wannan haushin ya hanashi Neman inda take.

A bakin gado ya isketa zaune tagama waya da Munubiya, k’in d’agowa tayi ta kallesa, tadai amsa masa sallama.
Shima bai kula taba ya zauna bakin gadon d’an nesa da ita.
Shiru kowa yayi suka share juna, haushi ya turnuk’e Galadima, lokaci yayi dazai daina d’agama yarinyar nan k’afa, yakamata su goga raini shi da ita. ta gefen ido ya saci kallonta, sai wani cika da batsewa takeyi, ya cije lips nashi.
“k baki iya gaisuwa bane?”.
Saida takuma tura bakin sannan tace “ina yini” tana mik’ewa da nufin bar masa d’akin, tana k’unk’uni
Bai amsata, sai mik’ewa da yayi shima, matsawa tashiga yi baya yana binta, fuskarsa a matuk’ar d’aure, da jikin bango ta manne, shikuma ya mata runfa, hannunsa d’aya a dogare da bangon yayinda yasaka d’aya ya rik’o hannunta ya matsa da k’arfi, zatai magana ya jawota tafad’o jikinsa, ya manne bakinsa kan nata, duk yanda taso kwatar kanta hakan ya gagara, dan ya kama hannuwanta biyu ya murd’esu ta baya yanda ta kasa koda motsi. A haka ya wulk’itata takoma saman gadon, shima yabi bayanta.
Ya d’ora hannunsa kan bakinta dan karta ishesa da tsiwa, idonsa ya saka cikin nata ya hanata kata6us, cikin tsare gida yace “dolene yau Na kora miki warning na musamman danki ringa banbance inda zakiyi tsiwa”.
Bai bata damar dazata fad’i nata ba yashiga aikata yanda yakeso da ita??????……………..???

Kutttt Galadima auren Contract nefa????, ba ruwana kaida masoyan Munaya aradu???????????????????????????????????????.

i miss you wujiga-wujiga my sweet fans??????????.

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
*_Typing??_*

*_Haske writer’s asso…._*??

*_?RAINA KAMA……?_*
_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull Ce_*????

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply