Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 7


Raina Kama Book 2 Page 7
Viral

~Book 2~ ????7?

…………….Gaba d’aya ya rikice ya rikita Nurses d’in da jama’ar wajen, cak ya d’auki Munaya, gadonma da aka kawo masa domin d’orata ko kallonsa bai yiba. Wani d’aki suka nuna masa ya shiga da ita.
Da sassarfa doctor dazai duba munayar ya iso, dan dogaran Galadima tasoshi gaba sukaje sukayo.
Kai tsaye Galadima yace baya buk’atar namiji mace yakeso ta duba masa matarsa.
Hak’uri doctor d’in ya bashi, sannan yakira wata likita mace mai suna doctor Farida.
Isowarta yasaka Galadima da yay bake-bake a k’ofar bata hanya ta shiga.
Duk yanda taso yabata waje tayi aikinta yak’i, gashi duk yabi yagama rikitata da tsawarsa.
Doctor d’in da Galadima ya hana ya duba Munaya ne ya matsa kusada su harun yana fad’in “dan ALLAH sir Ku lalla6a yalla6ai ya fito danta samu damar aikinta, wlhy dukya rikitata”.
Murmushi Nuren da isowarsa kenan asibitin aka masa bayani shima yayi, suma su harun duk murmushi sukayi.
Nuren ya kalli baba k’arami yana murmushi, “Abbanmu inharfa bakai kamasa magana ba bawai zai fito baneba”.
Shikansa baba k’arami murmushin yakeyi, koba komai hankalinsu Yakuma kwanciya da zaman ‘yarsu inda suke tunanin anfi k’arfinta.
Bayan doctor yabi zuwa d’akin, Galadima dake zaune, kan Munaya na bisa cinyarsa sai murza tafin hannunta yakeyi wai kozata farfad’o, yayinda doctor Farida ke k’ok’arin lik’a mata oxygen ita kuma”.
Shima baba k’arami da k’yar ya lalla6ashi ya fito.

Tsawon lokaci doctor Farida tana ciki bata fitoba. Galadima dukya damu, danma ankawo masa kujera ya zauna, amma sai jan tsuka yakeyi time to time.
Hankalin ‘yan gidansu Munaya ma duk a tashe yake, jiran fitowar doctor Farida kawai akeyi dan aji mike damun munayar.
Innarsu Munaya kam gefe ta koma tana sharar kwalla, itakam batasan yazata misalta wannan tsakaniba, miji da ‘ya’ya duk babu lafiya, Munubiya ma fa sunacan ana k’ara mata ruwa.
Fitowar doctor Farida yasaka kowa mik’ewa anason jin bayani, Galadima dai yana daga zaune ya zuba mata idanu shima. Doctor Farida tace su kwantar da hankalinsu ta farfad’o, amma tamata allurar barci, yanzu tanason ayo gwajin jinin Munayar data d’iba.
Galadima ya lumshe ido yana ambatar “Alhmdllh” akan la66ansa.
Sauban ne ya kar6a suka tafi shida Sarkin mota lab d’in.
Dr Farida ta kalli Galadima tana murmushi, “ranka ya dad’e zaka iya Shiga ka ganta yanzun”.
Nuren ya kalli Galadima ya jinjina masa kai alamar yaje.
Saida yaja wasu seconds sannan yamik’e cikin takun nan nasa na k’asaita da izza, duk idon jama’ar wajen akansa yake, yana birge kowa.
d’akin ya tura ya shiga, ya taka har gaban gadon da Munaya ke kwance, idanu ya tsura mata, tayi wani fayau da ita, ya jawo kujerar dake wajan ya zauna, har yanzu idonsa na kanta, cikin cije lips da lumshe idanu ya d’ora hannunsa bisa sumar kanta da d’ankwalinta ya zame ta fito, saikuma yasaka d’ayan hannunsa ya shafi kumatunta, a kan la66ansa ya furta “sorry my friend, ALLAH yana tare da masu hak’uri kinji”.
Daga haka bai sake cewa komaiba, ya janye hannunsa daga kanta ya mik’e ya fito.
A k’ofar d’akin ya iske Doctor Farida tsaye, kallonta yayi cikin maganarnar tasa mai kama da an masa tilas yace “zata iya kaiwa wane lokaci bata farkaba?”.
“Ranka ya dad’e inaga daganan zuwa kamar awa d’aya”.
Kansa ya jinjina mata, bai sake magana ba yanufi d’akin da Abba ke kwance. ya Tatar da doctor d’in dake kula da Abban a d’akin.
Da sauri doctor yabashi kujera ya zauna, k’afa d’aya kan d’aya ya d’ora ya Ciro waya a aljihu yana danne-danne. batare da ya kalli doctor ba yace, “kunyi gyaran karayar?”.
Doctor yace, “eh ranka ya dad’e duk an gyara, saidai na hak’ark’arinsa yaso kawo matsala, amma Alhmdllh komai ya dai-daita”.
“humyim, maganar bayanan danace a tattara minfa?”.
“shima komai ready ranka ya dad’e ”.
“o right, insha ALLAH zuwa jibi nakeson mu tafi, amma wai har yanzu bai ta6a farfad’owa bane?”.
“ai ba’a sume yakeba, allurar damuke masace kawai takesakasa yawan barci”.
d’ago ido Galadima yayi yana kallon doctor d’in, yace “amma danme ake masa?”.
“ itace ke taimaka masa wajen rage masa rad’ad’in ciwukan, dan maganar gaskiya yana cikin matsanancin ciwo”.
Cije lips Galadima yayi kawai, yace “ALLAH ya bashi lafiya”.
“amin ya rabbi”. ‘cewar doctor.

Daga haka suka fito shida doctor d’in.
Inda Harun yake Galadima ya nufa, “brother yau ba zakaje aikiba kenan?”.
Kallon agogon hannunsa Harun yayi, sannan ya kalli Galadima, “ka rikitamu ne ranka ya dad’e shiyyasa ban kula time ya tafi hakaba”.
Murmushi kawai Galadima yayi amma baice komaiba.
Harun yay musu sallama ya fita da nufin zuwa anjima idan yatashi aiki zai dawo.
Su yaa Hameed sukai masa godiya da fatan alkairi sannan yatafi.
Daddy ya kalli su yaa Hameed d’in yace ai kuma da tafiyar kukayi, karku makara wajen aiki”.
A ladabce suka amsa masa da to, suna shirin barin wajenne saiga motocin su waziri sun shigo, dole su yaa hameed suka dakata.
Waziri ne da matawalle, sai Garkuwa da baraya, sai kuma wasu manya-manyan ‘yan majisar Sarki. dogarai duksun kasa sun tsare, wasuma zato suke sarkinne yazo da kansa.
Su daddy ne suka musu iso har d’akin da Abba yake kwance, sosoi suka nuna tausayawarsu gareshi, sunja doguwar addu’ar samun lafiya da fatan alkairi ga Abba. Sannan suka Isar da sak’on Sarki.
Sun d’an jima a d’akin suka fito da nufin tafiya, a dai-dai time d’inne kuma doctor Farida ta iso gaban Galadima cikeda sassarfa. Bakinta a washe tamkar gonar auduga. Wani dogari Na k’ok’arin dakatar da ita Galadima ya d’aga masa hannu alamar ya barta tazo.
Cikin girmamawa doctor Farida tace “wannan asibiti da dukkan jama’ar cikinsa suna taya masarautar gagara badau murnar samun k’aruwa daga jikin gimbiya Munaya, insha ALLAH nanda watanni 7 dawasu satittika zata zama uwa, ma’ana tana d’auke da cikin wata 1 da sati uku”.
Atare dogarai suka d’auki kabbara, Galadima dake tsaye baki bud’e cikin tsantsar mamaki ya kafe doctor Farida da idanu, sai kawai yashiga zame agogon hannunsa mai masifar tsada da k’yau ya mik’ama doctor Farida.
Sauban yazo ya rungumesa, hakama matawalle.
‘Yan gidansu Munaya sai suka koma ‘yan kallo kawai, amma bakin kowa yakasa rufuwa.
Doctor Farida ta kalli Galadima cikin mamaki da al’ajabi, “ranka ya dad’e ni Na cancanci wannan agogon mai d’unbin tsada kuwa?”.
Wani murmushin Daba a cika gani Galadima yayiba ya saki, ya gyara tsayuwarsa yana fad’in “idan duk abinda na mallaka a duniya kike buk’ata zan baki shi, saboda wannan shine albishir Na farko da aka ta6amin Na farinciki a rayuwata, kifad’i dukkan abinda kike buk’ata inhar baifi k’arfina ba kafin nabar asibitinnan za’a kawo miki shi”.
Kanta ta shiga girgizawa, kafin ta d’aga agogon ga mutane su gani.
Mamaki ya cika kashe matan gidansu Munaya hassada da al’ajabi ya cika zukatansu, tunma ba’a haifi cikinba Galadima yake wannan rawar kan inaga an haifoshi?, Kansu bai kuma kwanceba saida sukaji waziri da baraya Na sanarda tasu k’yautar ga doctor Farida, hakama matawalle da Nuren.
Doctor Farida fa ta rikice, itakam yau taga farar rana, (??idan ta ALLAH ake niya kamata abama wad’annan k’yaututtuka ma??).

Nuren da matawalle suka hau rabon kud’i a asibitin, tamkar basu San ciwonsu ba.
Waziri kam d’akin da Munaya take kwance aka musu rakkiya, sun mata addu’a kafin su fito, kowa bakinsa a washe, wasukam ta cikin Na ciki kawai????.

Kafin kace mi labari yagama zagaye asibitin, gidan Sarki kam kafin su waziri su Isa labarin cikin Munaya yaje.

hakama Sauban ya kira su Momma ya guntsa musu, Momma saida tayi sujudar shukur.
Abie bakinsa yakasa rufuwa, kamar daga sama sukaji yace “ALLAH ya inganta”.
Dukda a hankali yayi maganar hakan bai hanasu ganin motsawar la66ansa ba, Khaleel dake kusa dashi yace “Lah Abie yayi magana Momma!!”.
ba momma ba hatta da jakadiya sakin kwanon hannunta tayi ta waigo tana kallon Abie. Aunty Mimi ta tura laptop d’in gabanta tafad’o, hakama Samha wuntsilowa tayi daga kujerar datake zaune tayo inda gadon Abie yake.
Gaba d’aya suka rufu akan abie, kowa yanason sanin gaskiyar batun Khaleel, murmushi Abie yamusu yana jinjina kai alamar gaskiyane, sannan a hankali yakuma furta “da gaske Khaleel yake”.
Ai yau babu kunya Momma ta rungume Abie a gabansu aunty Mimi ta fashe da kuka mai ban tausayi.
Aunty Mimi ta had’a momma da Abie d’in ta rungume itama.
Jikin Samha har 6ari yakeyi takira Number Galadima ta Nigeria.
Ya rako su waziri da zasu tafi kiran Samha ya shigo, bai d’auka ba, itakuma bata gaji da kira ba.
Saida su waziri suka wuce sannan yaciro wayar a aljihunsa cikeda haushin wanene mai nacinnan. yana dubawa yaga Samha Ce.
Murmushi yayi kawai sannan ya kirata da kansa, bugu d’aya Samha ta d’aga, kuka kawai ta fashe masa da shi, zuciyar Galadima tashiga tsitstsinkewa. tsawa ya daka mata yana tambayar lafiya?.
Share hawayenta tayi, murya Na rawa tace, “Uncle Sam wlhy Abie yayi magana, yanzun nan da Uncle Sauban ya kira yace aunty gimbiya nada ciki sai Abie yace ALLAH ya inganta”..
Galadima ya ciro wayar a kunnensa ya kuma kallon number, tunaninsa wasune kawai keson masa yawo da hankali, ganin dai da gaske number Samha d’in ce saiya maida a kunnen, cikin sanyi murya ya kira ainahin sunan Samha, “Zeenah! banason wasan banza kema kin sani”.
“wlhy Uncle ba wasa nakeba, ga Momma ma kaji awajenta”.
Kafin yace wani Abu yaji muryar Momma namasa sallama, yanayin muryarta yasakashi lumshe idanunsa. Momma tace, “Muh’d! Yau ranace dabazamu manta da itaba a tarihinmu, k’yautar abinda kud’i baya saya, ALLAH kuma yabama takawa damar magana, narasa yanda zan musalta farin cikina Muh’d”.
Wasu hawayene suka gangaro a kumatun Galadima, ga murmushi yak’i barin fuskarsa, cikin nutsatstsiyar muryarsa yace “Momma ko yanzu Ubangiji ya d’auki raina yagama min komai, Momma mizanyi duniya tasan ina cikin tsantsar farincikin da tunda nazo duniya ban ta6a riska ba?”.
Dariya momma tayi, tace “godiyar ALLAH ta wadatar da komai Muh’d, lallai yarona zai zama baba”.
Galadima yayi dariya yana goge hawayen fuskarsa, “Momma bama Abie wayarnan”.
Cikin tsokana tace, “nawa zaka biya? kasan mu yanzu komai Na kud’ine”.
Sosai yasaka dariya, har jerarrun hak’oransa Na bayyana. Dogaransa duk sun saki baki suna kallonsa, duk da bajin maganar da yake sukeba, tunda suke da shi basu ta6a ganin yana dariya makamanciyar wannan ba, Sauban kan ai hotuna yaketa masa bai saniba.
“shikenan Momma, inhar baki had’ani da Abie ba kema kuwa d’iyarki bazata dawo India ba ashe?”.
“a’a miyay zafi? indai takawa ne gashi”.
Nanma dariyar Galadima yayi, Abie da tun d’azu yaketa murmushi shima saboda a Hans free momma tasaka wayar duk sunaji, a hankali yace Daddyn Unborn!”.
Galadima baiji mi Abie ya fad’a ba, amma tabbas yana jiyo alamun motsi, da sauri yace, “Momma video call please ”.

Mota ya bud’e ya shiga, Sauban ma ya k’araso dan kuma taya d’an uwansa murnar k’aruwar daya samu. tunda aka bayyana maganar cikin Galadima bai samu Kansa ba, balle su ke6e.
Motar yashigo shima, ganin video call Galadima ya had’a dasu Momma saiya matso kusada shi sosai yana d’aga musu hannu.
Momma tace, “ho autana ina ka shige wai?”.
“momma ina zaki ganni nazama Abban Unborn”.
Dariya sosai suka sanya, Galadima ya rankwashi kansa.
Wayar aka saka kusada Abie sosai, a hankali yace, “lallai wad’annan iyaye akwai zumud’i dai”.
Basuji miya fad’aba. Amma sungane ta hanyar motsin la66ansa. cikin zaro ido Sauban yace “Abie!!”. Sai kawai ya rungume Galadima ya fashe da kukan farin ciki.

Humm masu karatu, nabama kowa damar k’iyasta wannan farin cikin a zuciyarsa shima????.

?*??*?*??*?*??*?

A lokacin da Galadima suke can suna waya dasu Momma Munaya ta farka, doctor Farida ta cire mata k’arin ruwan danya k’are.
Ta kalli doctor Farida tace “doctor Abbana fa? karki cemin dai Abbana ya mutu Dan ALLAH?”.
Hannunta doctor Farida ta rik’o, fuskarta d’auke da murmushi tace, “gimbiyarmu Abbanki nanan da ransa, insha ALLAH kuma zai tashi, kedai kici gaba da masa addu’a kinji”.
Kai Munaya ta jinjina mata, sannan tace, “to zanyi fitsari”.
Doctor Farida ta amsa da to, da kanta ta taimakama Munaya tashiga bayi, fitowa tayi tabata waje, saida ta gama sannan ta kuma taimaka mata ta fito.
“doctor ‘yan gidanmu fa?”.
Murmushi Dr Farida tayi, cikin tsokana tace, “Gimbiya Galadima yakamata ki fara tambaya ai”.
Murmushi Kawai Munaya tayi, amma batace komaiba, Dr Farida tace “to bara Na musu magana”.

Babu dad’ewa saiga ‘yan gidanmu nata shigowa, yanda kowanne fuskarsa ke a washe sai suka bani mamaki, nakasa hak’uri nace, “Abba ne ya tashi? kuke farin ciki haka?”.
“shima insha ALLAH zai tashi ‘Yar albarka”. Cewar innaro tana dariya.
Ni duk sun kuma d’auremin kai da addu’ar da sukeyi suna fad’in ALLAH ya inganta.
Mamansu Fauziyya tace minakeso akawo min naci.
Nace, “banajin yunwa mama, ni sonake ma Na kuma ganin Abba”..
“karki damu, Abba yana barci ne, kedai kisamu kici abinci babynmu yak’ara k’ato kafin ki haifo mana”.
Ban fahimci maganar ta Fiddausi ba, Dan naga awajen akwai masu ciki da yawa, aunty Ramlah, aunty Khaleesat, aunty Hauwa’u, Siyama, Zarah, aunty Raihana duk cikinsu ya tsufa, haihuwa yau ko gobe.
Na kalli innarmu dake tsaye batace komaiba, murmushi namata, itama saita mayarmin, nace, “wai har yanzu Munuhiya ba a cire mata ruwanba?”.
Mama Rabi’a tabani amsa da cewar “an cire, barci takeyi”.
Cikin marairaicewar murya nace “ALLAH sarki Sweetheart d’ina, ALLAH yabaki lafiya”.
Duk suka amsa da amin.
Doctor Farida tashigo tana sanar musu ga Galadima nan zai shigo.
‘Yar rige-rigen fita iyayena suka farayi, kowa yana jin nauyin suruki ya shigo ya iskeshi, ni dariyama suka bani, nayi murmushi ina komawa Na kwanta.
Saida suka fita kaf sannan nafara jiyo takun takalminsa.
Idanu Na lumshe kamar mai barci.
Tunda ya shigo idonsa Na kaina, yacigaba da takowa gaban gadon, duk tunaninsa barcin gaske nakeyi, maimakon ya zauna saiya dafa gadon ya rankwafo kaina, da sauri da sauri zuciyata tafara bugu saboda kusantoni da ya keyi, fuskarsa daf da tawa tamkar zai had’e bakinmu, mikuma ya tuna saiya janye ya maida saitin goshina ya manna min kisses guda biyu a goshi da saman hanci.
Cikeda mamaki Na waro manyan idanuna, kallon ido cikin ido mukaima juna, ya d’aga min gira d’aya.
Saurin kauda idanuna nayi gefe.
Shikuma yaja kujera ya zauna dab da fuskata yana murmushi.
Munja wasu seconds sannan yasaka hannunsa bisa kumatuna ya juyo da face d’ina inda yake, kin bud’e idona nayi Na kallesa, bai damuba yace “yalla6iya dama haka kike da saurin cafke Abu?”.
Babu shiri Na waro idanuna kansa, nace “yalla6ai mina cafke?”.
Idanunsa ya d’an jujjuya alamar tunani, saikuma ya kalleni, har yanzu hannunsa Na tallafe da fuskata, yace “uhuumm mima kika cafke? Na manta ma”. Ya k’are maganar da d’age kafad’a yana ta6e baki.
d’an hararsa nayi ina tura baki, mutuminnan ya iya rainin wayo.
Yanzunma murmushin yamin, saikuma ya d’ora hannunsa saman shafaffen cikina mai kama da babu ko kayan ciki balle kayi tunanin akwai mutum.
Da sauri Na rik’e hannunsa ina fad’in “ yalla6ai lafiya kuwa?”.
Cikin basarwa yace “itace ta kawo haka, bakimin murna ba”.
Nace, “Murna kuma? tami?”.
Cikin d’age gira d’aya yace “Muhammad Sameer Saifudden yazam pah-pah”.
d’auremin kai maganarsa tayi, Na yunk’ura a hankali zan tashi, mik’ewa yayi ya taimakamin Na zauna yana fad’in “yi da kula karkima jama’ar gari 6arna, dan akwai sarkinsu anan”.
Waige-waige Na farayi, nidai banga kowa ba bayan mu biyun dake zaune, saina d’auka da kansa yake, na d’an ta6e bakina kawai.
Shima saiya ta6e bakin yana komawa ya zauna. kusan mintuna biyu duk mukai shiru.
Zuwa can nace, “nikam dai na dawo normal, kace musu su sallameni kawai”.
Batare daya d’agoba yace “nafi buk’atar hakan, mi kikeso Sameer yamiki k’yauta da shi?”.
“k’yauta kuma? akanmi?”.
“Abie ya fara magana”.
Babu shiri na wuntsilo daga gadon ina fad’in da gaske?”.
Da sauri Galadima ya ruk’oni, jikinsa har rawa yakeyi, jina nai kawai bisa cinyarsa.
“yalla6ai!”. nafad’a cikin zaro idanu, sai kuma na hau waige-waigen kar wanifa ya ganmu.
Daf yamatso da fuskarsa kusada tawa, numfashin junanmu na sauka bisa fuskokinmu, na marairaice fuska tamkar zanyi kuka, yanda yasaka idonsa cikin nawa tsigar jikina dukta mimmik’e, jikina har tsuma yakeyi, amma tsabar muguntarsa yak’i ya janye, yakuma hanani damar da zan janye nawa.
A hankali tamkar mai rad’a, yace “ki kula, domin abin cikin kwan yafi kwan dad’i my friend ”. ‘ ya k’are maganar da d’age min gira sama’.
Lumshe idanuna nayi kozan sami sassaucin daina ganin abinda ke yawo a idanun Galadima.
hakan yabashi damar d’ora bakinsa akan nawa, shima ya lumshe nasa idanun.
Babu shiri na bud’e nawa saboda tsorata, ni Munaya mike damun wannan bawa yau? duk yanda naso kwatar kaina hakan ya gagara, dole na sallama yayi iya yinsa sannan ya sakeni.
Zumbur na mik’e daga jikinsa ina sharar kwallar takaici, shima saiya mik’e yana karkad’amin d’anyatsa, ya matso daf dani a hankali ya furta “k’yautar farko kenan”.
juyawa yay yafita yana murmushi da gyara zaman hular kansa.
Na bishi da kallo ina maimaita zancensa na k’arshe, “k’yautar farko? Kamar ya k’yautar farko? mi yake nufi to?”. ban kai ga samo amsarba doctor Farida ta shigo tana murmushi. “ginbiyarmu yalla6ai yace abaki sallama kuje gida ki huta gaba d’aya”.
Saboda Banason tafiyar, sai nace doctor jikina bai gama sakiba, ki Ce masa sai dare zaku sallameni kawai”.
‘Yar dariya tayi, ta nunamin Galadima dake bakin k’ofa tsaye ya hard’e hannaye a k’irji.
Baki na tunzuro gaba saboda borin kunya.
Shikuma ya janye idanunsa yana ta6e baki.

Doctor Farida ta bamu sallama, na d’auki alk’yabbata na saka, tareda d’aukar handbag d’ita, sai wani ciccin Magani nakeyi, shi da nakeyi danshi yawani share tamkar bai gane da shi nakeyi ba.
Jinai ya sak’alo hannunsa cikin nawa, na kalleshi da sauri, saiya kannemin ido d’aya.
Ja nayi na tsaya, shima saiya tsaya, ga mutane duk sun zubo mana idanu, kuma har ‘yan gidanmu. tamkar zan fasa ihu nace, “yalla6ai ni dai wlhy ka sakeni, kai bakajin kunyar su innarmu ma?”.
Yace “kai ALLAH dai ya shiryeka Sameer, yalla6iya Sameer najin kunyar su Innarmu fa, sai dai kuma yana gudun amasa gangancin abin cikin kwan ne”.
Kallonsa nayi, “ wai minene wannan abin cikin kwan daka ishi mutane da fad’a”.
Ya d’an d’ora hannunsa saman bakinsa alamar mamaki, “yamzu nan bakisan abin cikin kwan ba friend? Lallai news ya wuce dake, ina tayaki jaje kam”.
Kuma kullemin kai yayi a duhu.
Ita dai doctor Farida dake bayanmu sai kuma birgeta muke da bata dariyar salon namu.
Mutane kam dake kallonmu tunaninsu koda doctor Farida muke magana, Dan bazaka ta6a d’auka Galadima ya iya zaro magana hakaba. nikaina mamakin dama yana magana mai tsayi irin haka nakeyi, narasa miya d’abbak’a wannan farin cikin nasa na yau?, duk da bawai yanata dariya baneba, fuskarsa nanan yanda take babu walwala, sai dai yau akwai sakewa tattare dashi, kuma yakan yawaita murmushi bakamar ko yausheba.
Nidai nace, “dan ALLAH yalla6ai kayi hak’uri, wlhy bazan iya zuwa gabansu baba k’arami ahakaba”.
Baice komaiba ya saki hannuna, amma munci gaba da tafiya kafad’a da kafad’a dashi.
Wata kuyanga cikin kuyangin da uwargidan Sarki ta had’omu tai saurin tasowa ta kar6i bag d’in hannuna, ban musaba na mik’a mata, mutane sai gaishini sukeyi, nidai kunyama ta isheni, Dan wasu sun girmemin.
Mun Isa gaban ‘yan gidanmu, kowa ya taso yana k’ara min sannu da jiki, nidai sai ce musu make na samu sauk’i.
d’akin da Abba yake muka shiga, hawaye suka cikamin idanu, Galadima ya ruk’o min hannu, kallonsa nayi saiya girgiza min kai alamar kar nayi.
Bance komaiba na janye idanuna, sannan na k’arasa gaban gadon nafara tofa masa addu’oi, shima Galadima ya matso ya tayani, daganan fitowa mukayi, Galadima yakuma gargad’ar police d’in akan su kula sosai, inhar wata matsala ta biyo baya to suyi kuka da Kansu.
Cikin girmamawa suka amsa masa da insha ALLAH hakan bazata faruba ma.

Ni dai ina wajen ‘yan gidanmu, jinake kamar karna tafi wlhy, amma innaro tace kartaji karta gani, nabi mijina naje gida na huta, suma sauran ‘yan uwana duk gida zasu tafi hakanan, tunda dai iya k’ok’ari galadima tsaye yake akan komai na abban, dukkan kulawa yasaka ana bashi gwargwadon iko.
Nidai sai tunzura baki nake su Fiddausi namin dariya.

Muna haka Galadima ya k’araso wajen, cikin girmamawa yace yakamata suma ‘yan gidanmu suje gida hakanan su huta, insha ALLAH Abba zai samu kulawa tamkar suna nan.
Godiya suka shiga yimasa, innaro nata kwararamasa addu’oin gamawa da rayuwa lafiya, da samun afuwa shima ga mahaifinsa, ta k’are maganar da f’adin “ALLAH ya kawo mana kishiyata ko angona duniya lafiya”.
K’asaitaccen murmushi Galadima yayi, a kan la66ansa ya amsa da ammin Granny ”.

Daga nan wajen Munubiya muka nufa, suma ‘yan gidanmu suka shiga dansu k’ara ganin Abba su tafi.
Munubiya na kwance tana barci har yanzu ana k’ara mata ruwa, rungumeta nayi ina hawaye, yayinda Galadima da yaa Marwan suke gaisawa cikin mutunta juna, inajinsu sunama juna Congrat, amma ban fahimci na mineneba.
Nace “yaa marwan wai mike damun sweetheart ne haka ta rame?”.
Dariya yaa marwan yayi, yace “babynku ne”.
“lah yaa marwan kana nufin tanada cikine?”.
Kansa ya jinjina min.
Cikeda murna na kuma rungume munubiya ina fad’in “ashe na kusa zama mummy”.
Galadima ya kauda kai gefe yana murmushi kawai, shina yaa marwan sai k’aramar dariya yakeyi.

Da k’yar dai na hak’ura na baro asibitin nan badan nasoba, suma ‘yan gidanmu duk sun wuce gida.

*****************

A mota sai zun6ire-zun6iren baki nakeyi, saboda haushin banso rabuwa da ‘yan uwana ba yanzu, Galadima ya wani shareni.
shikam dukya gajine, bai cika wahalar zirga-zirga irin hakaba, gashi dama bawani isashshen barci yasamuba jiya.
Batare dana kalleshi ba nace “wai ina yaa Sauban ne?”.
Bai d’ago daga latsa wayar dayakeyiba ya bani amsa da “suna tare da Nuren”.
Da sauri na kalleshi danjin ya ambaci sunan Wanda nake son Sanin wanene shi?, cikin kwantar da murya nace “yalla6ai wai wanene Nuren? ”.
Tambayar tabashi mamaki, amma saiya share ya d’ago muka had’a ido, kowa ya janye cikin basarwa. bai bani amsarba har muka shiga cikin masarautar……………….???

Kuyi manage da wannan sister’s??.

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
*_Typing??_*

*_Haske writer’s asso…._*??

*_?RAINA KAMA……?_*
_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull Ce_*????

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply