Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 6


Raina Kama Book 2 Page 6
Viral

~Book 2~ ????6?
https://2gnblog.blogspot.com/

…………Har ya fita ya dawo, laptop da wasu takardu ya d’auka a falonsa ya fita, zai zauna a falonta saikuma wata dabara ta fad’o masa, bedroom d’inta ya nufa yana wani ciccijewa (kaida zaka karoro, miye na fuska to yalla6ai?????).
Munaya Na tsaye tana ninke hijjab d’in data rama sallolin dasuka risketa a hanya sai kawai shigowarsa tagani da sallama ciki-ciki. k’ok’arin warware hijjabin tafarayi tana masifa ita kad’ai a zuciya, haka kawai aita shigoma mutum d’aki babu izini, wannan wane irin rayuwane.
https://2gnblog.blogspot.com/
Shikam Galadima kallo d’aya yamata ya d’auke kansa, Dan daga ita sai zani d’aurin k’irji. Laptop d’in hannunsa da takardu ya ajiye a bakin gadon, sannan shima ya zauna, batare da ya kuma kalllon Munaya ba yace, “kinajin yunwa ne?”.
Ba yunwar takeji ba, amma dan Neman magana kawai tace “eh”.
Kallonta ya sakeyi, bata yarda sun had’a idoba, yace “Saidai kisha fresh milk kuwa, dan bani da abinci”.
Manyan idanunta ta waro masa waje, kamar wadda akace tasha wuta, cikin dafe k’irji tace “yalla6ai fresh milk?”.
Da mamaki ya kalleta, danshi bai fahimci ma’anar razanar tataba, yace, “uhmmm”….
“Na yafe wlhy”.
Tafad’a da saurinta.
“To mine nawani birkicewa haka? fresh milk d’in wani abune dashi?”.
“Humm”. Munaya tafad’a tana ta6e baki, tace “yalla6ai nikam idan kaga nasha fresh milk d’in data fito daga d’akinka saidai idan bana a hayyacina”.
Da tsantsar mamakin furucinta yake kallonta, da yake basuda nisa saiya mik’a hannu ya rik’o nata, zatayi magana ya fizgota ta zauna kusadashi, kad’an ya rage ta hau masa laptop, amma yay saurin janyewa da d’ayan hannunsa.
“wash hannuna”. Munaya tafad’a tana matse baki.
Banza yamata, yakuma matsa hannun da mugunta. tasaki k’aramar k’ara tana fad’awa gefen kafad’arsa.
Ya d’an kalleta ya janye yana ta6e baki “ban fahimci zancenki daga nesa ba, maimaitamin”..
Cikin tunzuro masa baki tace, “yoni babu abinda nake nufi fa, nidai bazan sha fresh milk d’in data fito daga d’akinka ba wlhy. haka kawai aje asakama mutum abinda zai halakashi”. ‘k’asa-k’asa ta k’arasa maganar, amma yajita sarai’.
Shifa saima yanzu yagane inda zancenta ya nufa, wani miskilin murmushi yasaki yana danne dariyarsa datake shirin kufcewa, amma dukda haka saida taji sautin fitar murmushin nasa.
Munaya dake satar kallonsa idonta harya cika da kwalla, a zuciyarta tace mugu d’an masa, dole fa kamin dariya.
Saida yayi dariyarsa a zuciya ya gama ya kalleta, itakuma saiwani mar-mar takeyi da idanu wai zatayi kuka.
Murmushi ya kumayi, sannan yace, “wannan bakin dakike tunzuromin ko, hummm…..”. ‘yak’are maganar da cije lips nashi’.
Yunk’urawa tayi zata mik’e, tace, “yalla6ai ni wlhy barci nakeji fa”.
Dawo da ita yayi ta fad’o jikinsa shima yana fad’in “nikuma gadinki zanyi ko? yalla6iya!”.
Tace “wayyo innarmu kice ya fitarmin a d’aki please”.
“ko waya zan baki ki kiratane”. ‘yay maganar cikin d’age gira d’aya’.
Munaya tai saurin janye idanunta daga Kansa ga k’amshin turarensa ya gallabeta, barci takeji, amma takula mugunnan soyake ya hanata ma.
Kamar zatayi kuka tace, “yalla6ai wai mikazo nemane please? Wlhy barci na keson yi?”.
Shiru yamata, saida ya mula dan kansa sannan yace “jikina fa”. ‘yay maganar yana kallon k’ugunta’.
Da sauri Munaya ta sauka daga jikinsa tana k’unk’uni da tura baki.
Medical glasses d’insa ya d’auka ya saka, tareda cigaba da aikinsa a laptop, a zuciyarsa yana fad’in yarinyarnan akwai ruwan tsiwa, amma duk randa Na kama bakin tsiwarcan sai yamin bayani dalla-dalla kuwa.

Ganin ya shareni ya cigaba da sabgarsa a System, nima sai ban kuma bi ta kansa ba Na d’auki kayan barcina nashiga bayi domin Na sanya. Sai dai zuciyata cike take da fargabar miya kawoshi d’akina?. haka na fito kamar wata munafuka ina lallak’ewa jikin bango.
Duk yana kallona ta gefen idanu, amma yay kamar baima San dani a d’akinba.
Sai zuwa can ya d’ago yana kallona, yana wasa da pen d’in hannunsa kan la66ansa, “idan bak’yajin barci zokimin wani d’an aiki nan”.
Saida gabana ya fad’i, a raina nace aikin mi kuma?, a fili saina aro jarumta na yafama kaina, Dan nakula tsoron daya fara gani a idona ne yake neman fara rainani da samin fargaba (??ho munayan shagali).
Takowa nayi inda yake, ina niyar zama bakin gadon sai ya nunamin tsakiyar gadon, shima laptop d’in ya tura sosai kan gadon ya haye tsakkiya yana gyara zamansa. kuma had’e fuska nayi ina wani dojewa na hau nima na zauna, cigaba yayi da danna laptop d’in, kusan mintuna 3 ya jehomin tambaya.
“shin kinsan minene aikin Abba?”.
Da mamaki na kallesa, nace “wai Abbana kake magana?”.
“uhmm”. ‘yafad’a batare da ya d’agoba’.
Shiru nayi alamar tunani, harya d’ago ya kalleni bance komaiba, maida kansa yayi ga laptop d’in yacigaba da aikinsa, zuwa can nace, “ma’aikacin gwamnati ne kawai tawani fanin kuma aikinsa yanada Nasaba da jarida”.
Tunda nafara magana ya tsuramin idanu, bakina kawai yake kallo yana taune lips nashi, saida nakai aya sannan yace, “jarida?”.
Nace, “eh, wani abune ya faru?”.
Kansa ya girgizamin, “innalillahi” yashiga maimaitawa a zuciyarsa, baya fatan zarginsa yazama gaskiya, cikin dakiya yakuma cemin “kokin san abokansa? ina nufin cikin manyan mutane haka?”.
“eh to, akwai senator halluru garba, sai kuma wani anacemasa Alhaji Mamman k’afur, last year yafito takarar shugaban k’asa……”
Caraf ya kama hannuna, “kina nufin Alhaji Mamman k’afur abokin Abban kune?”.
Ni tsoroma yabani, yanda yay maganar cikin rawar jiki, na jinjina masa kaina a hankali.
Gani nai ya taune lips nashi da masifar k’arfi, ya kaima iska naushi. da sauri na matsa baya Dan karya nausheni, ganin kamar na tsorata sai yay murmushi, cikin k’asaitacciyar muryar nan tasa yace “my Friend! Yanzu ne zamu fara aiki tare da gaske ni da ke”.
“kamar ya yalla6ai? wane irin aiki kuma?”.
Murmushin takaici yayi, ya kalleni ido cikin ido, kasa jurewa nayi nai k’asa da nawa. shima lumshe nasa yayi yana fad’in “zaki gani”. daga haka ya janye laptop d’in gefe ya zame ya kwanta.
Binsa nayi da kallo tamkar wata sokuwa, gaba d’aya ya kulle magudanar tunanina da wadda ke kaima kwakwalwata sakonni.
Medical glasses d’in idonsa ya cire ya ajiye, sai kuma ya juyo gareni, hannunsa d’aya ya mik’amin yanamin alamar nazo gareshi.
Idanu na d’an zaro, sai kuma na nok’e kafad’a alamar nak’i din.
Wani murmushin da bako yaushe yakeyinsaba ya sakarmin, ya juyamin baya yay kwanciyarsa. bai sake juyowa gareniba har kusan 6minutes. nagaji da kallonsa da nazarin murmushinsa da tambayoyinsa na janye idanuna, waishi guy d’innan mike damunsa ne? gaba d’aya ya canjamin daga saukarmu zuwa yanzun, dubana nakai ga agogon d’akin. 3:27am, “ya salam” na fad’a a hankali, muna Neman kwana a zaune. can k’arshen gadon na koma na kwanta, zuciyata cike da tsoron ALLAH yasa bawani Abu ya shiryaminba, babu dad’ewa barci 6arawo ya saceni.

Numfashina dake sauka a hankali yasaka Galadima gane nayi barci, juyowa yay yana kallona, yayinda zuciyarsa keta cud’a amsoshin dana basa yanzun, tabbas mahaifin yarinyarnan akwai abinda yasani, kwarai da gaske zaiyi amfani da ita wajen gano ko wanene mahaifinta?, minene alak’arsa da case d’ina?, sannan minene alak’ar Muftahu da ita?, Dan tabbas akwai manufar sako yarinyar acikin wannan tak’addamar, kuma Muftahu dashi aka shirya komai. yasaki wani murmushin mugunta tareda nuna kansa, a fili yace _MAK’IYAN MAHAIFINA SAINA ZAME MUKU_ *RAINA KAMA KAGA GAYYA* tabbas lokaci yayi dazakuga wannan *Gayyar*.

Tofa masu karatu, ana zaton wuta a mak’era??, mikuna yasako Abban munaya a rikicin masarauta? Kodai ba masarautar kawai bace keda alhakin ciwon tsohon Sarki Saifudden Abubakar???, shin tsakanin Galadima da Munaya & munubiya, innarsu Munaya. Wanene RAINA KAMA…… d’in???.

Kumuje zuwa kudai my Guy’s??, duk nisan jifa????, k’asa zai fad’o??????

?___________________________?

Bayan shigewar su Galadima Muftahu ya fito daga mota shima yana murmushin dashi kad’aine yasan fassararsa, jiyay kawai handkerchief ya rufe masa fuska, yay saurin cirewa yana waige-waige dan dunba wanene ya jeho masa, wayam babu alamar mutum a wajen, bai gama dube-duben ba yay luuu zai fad’i, saigashi a hannun mutum, idanunsa sunriga sunyi nauyi, dishi-dishi yake kallon Wanda ya tareshi d’in, dama gashi ya rufe rabin fuskarsa ba’a gani, wasu samarine su biyu sukazo suka kama Muftahu tareda wancan suka danna a mota, tun yanajinsu sama-sama har idonsa da jinsa suka rufe baki d’aya.

????tofa suwaye?.

?__________?_________?

Tun kusan around 8pm Nuren yake k’ofar wajen, a dukkan bayanan daya samu daga majiya mai k’arfi yarinyar Minister ta shigo gari yau, kuma zatazo shan ice-cream wajen, wayarsa ya d’auka yay wasu ‘yan danne-danne, murmushi yayi ya maida wayar ya ajiye tareda dasama k’ofar wajen idanu, dolene kafin tashiga ciki zai saceta, dan bincikrnsa ya nuna masa cctv camera d’aya ce a cikin wajen kawai, a waje babu, dan haka bama ya buk’atar ta Shiga, murmushi yayi saboda ganin motar da driver d’inta yamasa kwatancen zasuzo aciki, saida driver n yaga motar Nuren sannan yazo kusada ita yay parking, bud’e murfin gefen mai zaman banza Nuren yayi, hakan kuma yay dai-dai da fitowar zankad’ed’iyar budurwa daga motar datai parking kusada ta Nuren d’in, murfin ne ya daki gefen hannunta kad’an.
A fusace ta kalli motar Nuren, shikuma yay mata murmushi, wani haushine ya kamata, banda rainin wayo ya bigeta amma yamata murmushi saboda wulak’anci, yau saitaga wanene ubansa a garinnan?. da k’arfi tabuga saman motar tana lek’a kanta ciki, “kai wawa bakaga abinda kayi bane?”.
Maimakon ya bata amsa saiya jefa mata handkerchief d’insa saman fuskarta, janyewa tayi da sauri zatayi magana kanta ya sara mata, da lalube ta dafa kujerar motar ta shiga ta zauna, sai faman lumshe idanu takeyi. murmushi Nuren yayi, ya taimaka mata ta ida shigowa Sannan ya rufe motar, komai akan idon driver n ta ya faru, bashida damar hanawa, dan Nuren yasashi a tsaka mai wuyane. Agaban idonsa Nuren yaja motarsa yabar wajen yana murmushin samun nasarar tafiyar plan d’insa yanda ya tsara. a wannan daren yanufi gidan Galadima dake can bayan gari inda aka ta6a kai Munaya.

??humm yau ‘yar kidnapping akeyi kawai????.

————(((?)))————–

Galadima yariga Munaya farkawa, dama bawani isashshen barci yayiba, tunani da damuwa suka taru suka hana idonsa rintsawa sai gabannin Asuba. Ana kiran sallar farko kuma yana farkawa, tashi yay zaune dafe da kansa, kusan mintuna biyu ya juya yana kallon munaya data juyo tana fuskantar inda yake yanzun, da gani kasan barcin bamai dad’i takeyiba, dan sai yamutse fuska takeyi a cikin barci. matsawa yayi kad’an ya d’ora yatsunsa biyu gefen fuskarta, sai yaji zafi jikinta, ya janye yana mamakin wai mike damun yarinyar nan kwana biyu haka? dolene yau yasata taga doctor idan sunje ganin Abba. gabansa yad’an fad’i daya tuna har yanzu itafa batasan komai ba, shi baima San ta yadda zai sanar mata abbanta yana cikin mawuyacin hali ba, ya dafe kansa yana ambatar sunayen ALLAH kozaiji sassauci a ransa. Da k’yar ya samu ya mik’e domin yin rakata ainul’fijir kafin akira assalatu.

Bayan ya idar ya tadani, da k’yar na iya tashi dafe da kai, dan barcin bai isheniba, muryarsa da alamun shima rashin isashshen barcin yace, “time d’in salla yayi”.
Idona dake bud’ewa da lumshewa Na kad’a masa alamar amsawa, yay saurin janye nasa saboda wata fad’uwar gaba da tsirgawar wani Abu dayaji lokaci guda tun daga Kansa zuwa yatsan k’afarsa, bai sake magana ba yafice. nikuma nakoma Na sake kwanciyata.

‘Dakinsa ya shiga ya tada Sauban dansu tafi massalaci.
Babu dad’ewa Sauban ya kammala alwala yafito ya iskeshi a falo yana jiransa, harara ya antayama Sauban, shikuma ya kauda kai gefe yana had’iye dariya (yo daga taimako saiya zama laifi?).

Sarki yayi mamakin ganin Sauban, dan yaron bawani zuwa k’asar yakeba saida dalili mai k’arfi, bayan yagama k’ar6ar gaisuwa wajen jama’arsa Galadima da Sauban sukabishi zuwa sashensa.
Kasa 6oye mamakinsa yayi, ya kamo hannun Sauban d’in dake d’ayan 6arinsa zaune kamar yanda Galadima yake, “yarona ne yau ak’asarsa ba biki ba ba bikin salla ba?”.
Dariya Sauban yayi, yace “Abba nazo gaidakune kawai”.
Sarki ya Murmusa yana kallon Galadima, “Galadima kodai akwai abinda ke faruwane kuke 6oyemin?”.
Galadima ya d’ago kansa cikin damuwa yace “babu abinda muke 6oyewa ranka ya dad’e. Mahaifin Munaaya ne yay Accident shine suka taho da Sauban d’in”.
“mu bamuda muhimmancin da zamu Sani kenan ko?”.
“ALLAH ya huci zuciyarka ba haka nake nufiba, bayan barina wajenka jiya nima aka sanarmin, lokacin dana shigo kuma dare yayi”.
Ajiyar zuciya mai martaba ya sauke, yace “ALLAH yabashi lafiya, zuwa anjima sai su waziri suje dubashi ai, tana ina ne ita d’iyar tawa?”.
“tana nan cikin masarauta”.
Jin jina kai kawai Sarki yay bai kuma cewa komaiba, sai zuwa can yacigaba dayima Sauban tanbaya akan jikin Abie, shikuma yana bashi amsa. Galadima dai Na jinsu bai saka bakiba.

*************

Saida gari yafara haske ALLAH yabani ikon tashi, dan zazza6in kuma ya sauka, yanzu kuma haka yakemin, da dare yayi zan fara zazza6i, lokacin da gari zai waye saikiji ya sauka. Sai dai ciwon jiki.
Saida nayi wanka da ruwa mai zafi sannan nayo alwala, sallar asubahi data kwacemin nayi, Na jawo handbag d’ina danazo da ita Na d’akko wayata, sim card d’ina Na 9ja Na d’akko shima Na saka akan wayar, massage suka turomin Na adadin awannin da suka bani sim card d’in zai d’auka kafin ya cigaba da aiki. ganin haka saina ajiye wayar natashi domin gyara d’akin, ina cikin kakka6e gado idona yakai bisa wayar Galadima. dad’ine ya kamani, koba komai nakira wani d’an gidanmu Na sanar dasu nazo 9ja.
Wayar Na d’auka Na saka number Abbana, dan yanzu nafi kwad’aituwa dajin muryarsa fiye da kowa, kodan mafarkai marasa dad’i danakeyi a kansa, Mtn d’insa nafara kira amma a kashe, saina kira glo d’in, shima switch up, ban kawo komai a rainaba na maida kiran kan innarmu, bugu biyu aka d’aga, wani dad’ine ya kamani, cikeda d’oki nace “innarmu I miss you”.
Aiyaan daya d’aga wayar yay dariya, aunty ba inna baceba. Nine, Nima Na iya waya yanzun”.
Dukda naji dad’in jin muryar d’an uwana, hakan bai hana zuciyata shiga fargaba ba, nace “Aiyaan Kaine? ina innarmu d’in?”.
“Tana wanka ne zamuje asibiti wajen Abba”.
Da sauri Na dafe k’irji, nace “Asibiti kuma? miya sami Abban?”.
“Lah Aunty baki saniba? Ai accident yayi fa, kuma innarmu nata kuka, hakama innaro dasu daddy”.
“Aiyaan!!…” nafad’a da k’arfi, kafin nace wani Abu naji an rik’emin hannu ta bayana an zare wayar daga kunnena.
Kuma rikicewa nayi, Na juyo da hanzari, cikin kuka naketa fad’in “abbana! Abba da gaske Aiyaan yake yi? Yalla6ai da gaske Abbana yayi accident?”.
Wani tausayina yaji ya tsargashi, ya dafa kafad’una, cikin sigar lallashi yace “cool down mana my friend”.
“to ka fad’amin da gaskene Abbana yayi accident d’in?”.
Rasa mizaice min yayi, sai bin fusakata da idanu yakeyi, ya cije lips nashi yana fad’in “inhar kinason na kaiki ki gansa toki nutsu”.
Share hawayena nayi da sauri nace, “to na nutsu muje”.
Yaja hancina, a hankali ya furta, “good girl”. Sai ya juya kuma ya fita.
Binsa nayi da kallo hawaye na zuba a kumatuna, kenan da gaske Aiyaan yakeyi Abba yayi Accident d’in, “hasbinallahu wa’ni’imal wakil”. Na dafe kaina tareda zama a bakin gadon nacigaba da raira kukana.

Shikam yana fita ya dunk’ule hannunsa yana cije lips, yama akayi yabar wayarsa harta d’auka tayi kira dashi, ko kad’an baiso hakaba. Baiso tajiba kai tsaye.

Saida naci kukana na gode ALLAH sannan natashi na hau shiryawa, atamfa na saka zani da riga, bawata kwalliya nayi ba, na shafa fauda kawai da lips gloss, turarema kad’an na shafa. ina cikin Neman mayafi ya shigo, kamshin turarensa yasani juyowa na kallesa, sanye yake cikin oxblood d’in shadda, hularsa takalmi agogo duk black, link d’in hannun rigarsa yake sakawa, sai alk’yabba pink da ratsin milk a hannunsa.
d’auke kaina nayi naci gaba da neman gyalena a cikin kayan lefena.
Baimin magana ba ya tako har inda nake, hannu yasaka a kafad’una ya d’agoni, fuskarsa babu walwala ko kad’an, idonsa akan fuskata, kusancin damukai da juna sosai yasaka numfashinsa ke sauka akan fuskar tawa, janye idona nayi na maida kan design d’in gaban rigarsa, yayinda shikuma ya warware alk’yabbar hannunsa mai k’yau ya sakamin, d’agowa nai muka k’ara had’a idanu, ya jinjina min kansa kawai.
Jinai tamkar in fasa ihu, banason saka alk’yabba d’in nan nidai, dan nauyi sukemin, garama wannan batada nauyi gaskiya, dan tamkar riga After dress take, saidai suffar alk’yabba aka mata, kuma tanada kaurin dabaza’a ga jikin mutumba.
Hannunsa yakuma d’orawa akan kafad’una ya d’ago hular alk’yabbar dake kwance a baya ya sakamin, ni kaina koba’a fad’aba nasan nayi k’yau, yanzunma baice uffanba ya juya ya fita yana nunamin agogon hannunsa alamar time yana tafiya.
Handbag d’ita na d’auka da wayata nabi bayansa, dauriya kawai nakeyi na hana kuka tasirin zubowa.
A falo na iskeshi shida Sauban dake zaune a kujera shima cikin manyan kaya, dayake ba sakawa yakeba sainaga ya canjamin, ya kalleni cikin halinsa na tsokana yana fad’in “kaga sarauniya gagara badau ta gobe, takawarki lafiya 6auna mai tafiyar k’asaita…….”.
Harar da Galadima ya zuba masa ce ta sakashi gimtse bakinsa yana had’iye dariya.
Nidai banma tankaba, dan yau zuciyata babu dad’i.
Galadima ne yay gaba mukabi bayansa, tunda muka fito hadimansa suke zubewa gaishemu, Sauban kawai ke amsa musu, shikam Galadima saidai d’aga hannu, Niko ko kallonsuma banayi. Hakan yasa suka fahimci har yanzu akwai matsala kenan, dansu bama Susan munzo nida Sauban ba.

Muna k’ok’arin shiga mota Harun ya iso wajen, gaidashi Sauban yayi, nima na gaidashi, ganin ni da Galadima kowa fuska a tamke sai abin yabashi mamaki, hannun Galadima ya kama suka koma gefe.
Nikuma da Sauban muka shiga mota.

“Sameer babu fad’a miya kawo gaba?”.
Murmushi Galadima yayi, ya cije lips nashi kad’an yana kallon Harun, “bazaka ganeba Harun, na iske abinda ya dagula lissafinane kawai, naga kiranka jiya, amma ina cikin rud’ani a time d’in shiyyasa ban d’agaba”.
“rud’ani? mike faruwa ne?”.
“mahaifin munaya ne yay Accident, a time d’in ina hospital wajensa”.
“ya salam, ya jikin nasa to?”.
“Alhmdllh, zamuje canne bayan mun gaida jama’ar gidan”.
“ok bara na k’arasa abinda zanyi kafin Ku fito saimuje”.
Kai kawai Galadima ya jinjina masa.

Bud’e masa gefena akayi ya shigo, yad’an kalleni, kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru.
Sashen mama Fulani muka fara Isa, amma sai aka sanar mana tasha maganin mura ta kwanta, daga nan muka nufi sashen matan Sarki, inda yafi ko ina k’awa da ado a gidan kenan.
Mun sami tarba ta musamman ga Uwar gidansa, nidai matarnan tana k’aunata na lura, kuma tafi sakarma Galadima fiye da kowa a Matan sarki, tanada kirki sosai, haka taita jan Sauban a jikinta, nakula suma sunfi sakewa da ita.
Sosai ta nuna damuwarta akan Accident d’in mahaifina da Galadima ya sanar mata, taita jinjina maganar tana lallashina da jerama Abba addu’ar tashi cikin k’oshin lafiya.
Tasa aka kawo mana break fast wai saimun karya anan, Sauban ne kawai yaci, amma Galadima cewa yay ya k’oshi, nima nace bazan iya ciba. dan burina kawai naga mahaifina, gaisuwarma duk akan k’aya nake.
Shima Sauban d’in bai wani ci abun kirkiba yace ya k’oshi, mun fito muka shiga sauran sassan, amma ba ko inaba.

Sauban da harun sun tafi a mota d’aya, nikuma ni da Galadima. Sai motar dogaran Galadima guda biyu, sai kuma kuyangi hud’u da Uwargidan sarki gimbiya Zulfah tahad’oni dasu, wai kafin mu dawo nima a turamin bayina da zasu ke kula dani, ni dai da to kawai na amsa, Galadima kam baima ce uffanba.
Babu mai magana a cikinmu daga ni harshi, sai saukar ajiyar zuciyata da share kwalla time to time danakeyi.

……………………………………..

Innarmu na fitowa daga bayi Aiyaan ya sanar mata na kira, da mamaki tace masa kodai Munubiya ce?”.
“wlhy Innarmu aunty Munaya ce, kuma batasan Abba bashida lafiya ba”.
“ka sanar mata ne?”. tafad’a a rikice.
“eh innarmu na sanar mata, kumafa naji tana kuka”.
“innalillahi Aiyaan wayace ka sanar mata? da wace Number ta kira?”. Tayi maganar tamkar zata make Aiyaan.
Runtse idanu yayi yana k’ank’ame jiki saboda tsoro. innarmu dukta rikice, tasan su Munaya da shiga Rud’ani akan Abu, yanzu haka tana cikin damuwar Munubiya itama, dan jikinta yakuma janga6ewa, ga laulayi ga wannan damuwar Abban.
K’ok’arin kiran Number tashigayi danta kwantarmin da hankaki amma sai tak’i shiga.
Har suka gama shirin asibiti wayar bata shigaba.
Koda suna mota taita gwadawa.

A asibitin suka had’u da mama Rabi’a suma sunje, ganin innarmu a cikin damuwa yasata k’ok’arin fara kwantarma ‘Yar uwarta da hankali.
Innarmu ta sanar mata kato6arar da Aiyaan yayi.
“to Yaya ko su Munaya sunzo k’asarne?”.
Anya kuwa Rabi’a, naga jiya mijinta na nan amma baiyi maganar zata zoba”.
“ito da wannan dan wanann, amma ai bama fidda raiba”.
“hakane”. cewar innarmu.

Babu dad’ewa da zuwansu saiga gwaggon Haleematu da matan k’annen ta sunzo duba Abba, (dayake har yau bata dawoba ita). k’in gaisawa tayi da innarmu da mamansu yaa hameed, innarmu bata damuba, amma mamansu yaa hameed saida taja tsuka, babu dai Wanda ya tanka. Sukuma suka shiga suka ga Abban, dayake yau ana barin na jikinsa zuwa su duba shi.
Koda suka fito harda kuka takeyi, matan k’aninta suka tafi amma ita saita zauna, kaf ‘yan gidanmu babu Wanda yace mata danmi, kowama tasa ta isheshi aransa.

?????

Tunda motocinmj suka shigo harabar asibitin sai kallo ya koma sama, ‘yan gidanmu dakeda yak’in Galadima ne kowa tsumayen fitowarsa yakeyi, sauran jama’a kuma da ‘yan dubiya son ganin wad’anda zasu fito sukeyi.
Sai da aka bud’e mana sannan muka fito, suma su Harun duk sun fito.
Su yaa Hameed suka taho garemu sunama Galadima sannu da zuwa, cikeda kulawa yake amsa musu.
Kowannensu fuskarsa ta nuna farin cikin ganina, yayinda nikuma naketa faman zirar da hawaye.
Cikin d’okin ganina Fauziyya tazo ta kama hannuna itada Safara’u, saina rungumesu na fashe da kuka, kukana ya karyar musu da zuciya suma suka fara, sauran ‘yan uwanama duk suka taso gareni, dama duk sun zo, ni kad’aice wadda nake nesa.
Saida baba k’arami yamana magana sannan suka sakeni, na matsa ina sharar kwalla na gaida iyayena, Munubiya ce kawai ban ganiba, ina share hawaye na tambayi tana ina?.
Aunty khalisat tace “sunje ganin doctor itada yaa marwan, dan batajin dad’i itama”.
Kaina kawai na jinjina, na k’arasa gabansu innarmu na durk’usa ina gaishesu, duk sun amsamin cikeda kulawa, da tambayata ya hanya?, nace “Alhmdllh”.
Matan gidanmu kowacce kallona take da mamakin canjawata a cikin wata 1 kacal. Na katse musu tunani da tambayar d’akin da Abba yake.
Aunty Ramlah ce taja hannuna muka shiga corridor d’in dazai sadamu da d’akin da Galadima yasa aka canjama Abba.
A ciki na iske Galadima da Harun da Sauban, sai doctor da yaa Shafi’u yaa Hameed.
Takun takalmanmu yasakasu juyowa suka kallemu, na zare hannuna daga na aunty ramlah ina toshe baki saboda kukan dake Neman kufcenin, taka wa nayi gaban gadon da Abba yake, na durk’ushe ina sakin kuka mai tsuma rai da zuciyar mai saurarona, tare da kife kaina jikin gadon.
Kukana babu zuciyar Wanda bai karya ba, Galadima ya tako a hankali inda nake, hannayensa biyu ya saka ya kamoni na mik’e tsaye, fad’awa nayi saman k’irjinsa na kuma sakin wani sabon kukan.
Bashida za6in daya wuce kar6ata, dan haka shima saiya saka hannayensa ya zagaye bayana dasu, ya d’ora ha6arsa saman kaina yana lumshe idanu da cije lips. kad’an-kad’an yake buga bayana alamar lallashi.
d’ai-d’ai su yaa Hameed suka zare jikinsu suka fice daga d’akin, aka barmu mu kad’ai sai Aunty Ramlah da muka birgeta, itama ganin sun fita saita fice taja mana k’ofar.

Munkai tsawon lokaci ahaka, saida na tsagaita da kukan sannan Galadima ya d’ago kaina daga jikinsa, hannunsa yasa yana gogemin hawayen fuskata, amma ya gaza cewa komai. sai girgiza min kai kawai yakeyi.
Ajiyar zuciya kawai nake saukewa a jere, da hannu ya nunamin hanyar fita.
Banyi musuba nabud’e k’ofar muka fito, ina gaba yana bina a baya. tafiya nake a hankali saboda juwar dake Neman fara hajijiya dani, burina kawai nakai inda ‘yan gidanmu suke zaune akan kujeru nima na samu na zauna.
Muna gab da k’arasawa wajen na dafe kaina, sai nayi baya luuuuuu.
Da sauri Galadima dake bayanta ya tareta ta fad’o jikinsa, gaba d’aya ‘yan gidanmu da mutanen wajen suka mik’e tsaye cikin ambaton sunan ALLAH.
sosai Galadima ya tallafota jikinsa, yayinda wasu Nurses biyu suka iso da gudu domin kar6ar Munayar.
Amma saiya hanasu yana daka musu tsawa da ambatar su kira Doctor.
Basu ba kowama a wajen saida tsawarsa ta rikitashi………………..???

*_Comments d’inku shike k’aramin k’arfin guywar rububutun nan wlhy, amma da tuni na ajiye saina samu lafiya??????, amma yanda kuke k’ok’arin Comments sai bana iya barinku banyiba??, ina godiya kwarai da gaske, I love you all???????????????????_*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu??????_*
*_Typing??_*

*_Haske writer’s asso…._*??

*_?RAINA KAMA……?_*
_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull Ce_*????

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply