Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 5


Raina Kama Book 2 Page 5
Viral

Book 2~ ????5?

…………..Bayan an idar da salla Galadima yace wanne office yakamata su fara zuwa?, mtn ko glo?.
Shiru Nuren yay yana tunani, zuwa can ya kalli Galadima “Sameer mizai hana mubari sai zuwa gobe, kasamu kaje kad’an kwanta ka huta, kaga yanda idonka yay jazur kuwa, ga jijiyan dukta tashi”.
Lumshe idanu Galadima yayi yana furzar da huci mai zafi a bakinsa, “Nuren muje kawai, kona kwanta bazan samu nutsuwa ba, kaga fa yanda suka jigata bawan ALLAHn nan”.
“hakane, amma karka damu muje kai dai kawai”.
Galadima bai musaba, suka jera shida Nuren zuwa wajen mota, bayan anbud’e musu sun shiga sai Nuren yacema Sarkin mota suje hotel d’in daya sauka.
Galadima yanajinsu amma baice uffanba, yayi shiru kawai yana kallon jama’a ta glass.
Koda suka isa hotel d’in sai Nuren yace su sarkin mota suje abinsu, zuwa anjima zai kirasu su maida Galadima d’in gida.
Cikin girmamawa sarkin mota ya amsa da to, yamusu sallama suka tafi.

Koda suka isa d’akin da Nuren ya sauka Galadima cire rigar shaddar yayi ya kwanta dagashi sai dogon wandon da vest, kwanciyar mintuna 5 kacal barci yay gaba dashi. Sosai tausayinsa yakama Nuren, yanason d’an ‘yar uwar mahaifinsa sosai, (Nuriddeen d’ane ga Abubakar yayan Momma, babban d’an Sarki Abdul’fatah daya gaji sunan Sarki Abubakar kakansu Galadima, mahaifin Nuren ayanzu haka shine mai jiran gado a masarautar su momma, Nuren d’ansane na biyu, akwai yayansa Ballo, shid’in sa’an Galadima ne, kusanma tare akayi goyonsu, amma Galadima ya girmesa da watanni 7 a duniya, kunga d’an uwansane na jini kenan, ta 6angaren mahaifiya????).

Galadima ya jima yana barci, dan kiran sallar la’asarne ya tadashi ma, wanka yasake yi, ya kar6i kayan Nuren ya sanya, k’ananun kayane amma sun masa k’yau sosai, Nuren nata tsokanarsa, wai kayan sun masa k’yau, inhar Munaya ta gansa bazata ganeshi ba.
Harara ya zubama Nuren, sannan yanemi hanyar fita, “malam idan kagama surutun saika taho muje”.
“sorry sarkin gagara badau mai jiran gado”.
tsaki Galadima yayi kawai yafice abinsa, shifa haushin mai jiran gado d’innan yakeji idan aka ambata masa, sadai nemi mai jiran gadonsu amma bashiba, mtsoww!!.

Wata mota dake fake a harabar hotel d’in suka nufa, Nuren ya zauna a mazaunin driver, yayinda Galadima ya zauna gefensa.
A hankali Nuren ke tuk’in suna ‘yar hirarsu jefi-jefi, dayake kowanne akwai nutsuwa basuda yawan hayaniya, dan shima Nuren d’in bashida surutu.
Tafiya mai d’an nisa ta kaisu wani k’auye, bawani babban gari baneba can. Galadima ya kalli Nuren yana hararsa, “wai Nuren bazaka saida gidannan ba dai ko?”.
Murmushi Nuren yayi, yad’an gyara zamansa yana kallon Galadima, saikuma ya maida ga hanya. “brother kenan, ai yanzu ba abinda kuke tunanin nake aikatawa ba a gidan, wlhy babu ruwana da ‘yar kowa yanzun”.
“Humm Nuridden! nasan inhar kana tareda Muzaffar bazaka ta6a daina neman mataba, nidai bazan gaji da gaya maka gaskiya ba, inhar aure kakeso kawai kayi aure, bazaka gane llar zina ba saika auri yarinyar da wani yagama Sani, saika haifi yara kuma, Nuren! Ba cika baki nakeba, bakuma nafi k’arfin ALLAH ya jarabceniba, amma dana aikata zina ka ganni nan gamma a d’auramin aure da mata hud’u a rana d’aya, please and please d’an uwana, ka canja tun Kannada damar hakan, dukkanin ahalinmu basa son wannan d’abi’ar taka wlhy”.
Nuren ya jinjina masa kai yana cije la66a, “na gode d’an uwana, insha ALLAH nabari har abada, kuma kwannan zakaji maganar aurena ta tashi, wlhy tun wancan lokacin da abunnan yafaru ban sake mu’amulla da kowacce maceba, idan najima zan takura saina fara azumi”.
“tom ALLAH yacigaba da gadinmu muda zuciyoyinmu, amma Auren shine tafi cancanta dakai, dan wani lokacin da mutum yakai azumin ma zakaga komai yadawo, kaga Auren shine cikakkiyar mafita kawai”.
“gaskiyane wlhy, ALLAH dai ya k’ara shiryamu”. ‘Nuren yafad’a yana horn a k’ofar gate d’in katafaren gidan gonarsa dayake kiwo’.
An bud’e musu gate d’in suka shiga, ma’aikatan sai murnar ganinsa sukeyi, tsayawa yay da motar batare da sun fitoba, sukaita zuwa gaishesu, bawani Sanin Galadima sukayi sosaiba, tunda bawani zuwa wajen ya keyiba, Nuren zai fad’a musu wanene, amma Galadima yamasa nuni da karya fad’a, hakkane yasakashi 6ame bakinsa.

******************************

Ran mama Fulani a 6ace yake kallon manyan jikokin nata maza guda uku tayi, cikin isarta da k’asaitarta tafara kiran sunayensu, “Talba! Wanbai! Matawalle!, kunsan dalilina Na taraku anan kuwa?”.
A tare suka girgiza mata kai kawai.
Takuma gyara zamanta cikin tsantsar mulki da izza, tace, “nakula mahaifinku har zuwa yanzu baison ciwonku ba, shi dole yanaso ace masa adalin Sarki, shiyyasa kullum yake fifita d’an wani bisa Ku da ALLAH ya bashi, Matawalle shekarunka dana Galadima kusan d’ayane, amma mahaifinku nagani Galadima yay aure bai ta6a nuna damuwarsa akan kai kayiba balle sauran ‘yan uwanka, to yanzu matar Galadima cikine da ita, kuma tabbas ta haifi namiji kuda sarautar gagara badau saidai kallo”.
A razane Talba da wambai suka zaro idanu waje a zabure, matawalle kuwa murmushi kawai yayi yana girgiza kai da mamakin wannan kakar tasu mai shegen son kanta.
Wambai yace, “haba Granny miyasa kike fad’ar wannan maganar, yakamata bakinki ya fad’i alkairi mana, shi dan uban cikin basai mun bari an haifesa ba, koshi uban cikin dayake tak’ama yana jiran gado bai isa yayi mulkiba balle cikin da babu tabbas d’in haifosa, ni wlhy kinma 6atamin rai”.
Talba yaja tsuka shima yana harare-harare, “Granny ya akayi kikasan tanama da cikin to? wannan sarkin girman kai d’inne zai iyama mace ciki?”.
Harara mama Fulani ta zubama Talba, “to uban matanbaya, azatonka zai zuba mata idone yana kallonta kamar hoto ko television a gida? ince kwana nan 4 kenan dabaro inda suke”.
Wambai yace “amma shine bakiyi maganarba sai yau Granny?”.
“to ubana koyamin yanda zanyi”.
“ALLAH yabaki hak’uri”. ‘cewar wambai yana k’unk’uni k’asa-k’asa’.
Matawalle dabaice uffanba tunda aka fara maganar yay guntun murmushi, muryarsa a tausashe yace, “Ranki ya dad’e ni banga amfanin wannan maganarba, ALLAH shine ya azurta Galadima da samun ciki a jikin matarsa, wannan kuma abun farin cikinmu ne amatsayinmu Na ‘yan uwansa, shi dai mulki Na ALLAH ne, shike badawa ga Wanda yaso akuma lokacin da yaso, bamuda tabbacin tsawancin ran ganin gobenmu ma balle maganar gadar sarautar cikinma daba’a San miza a haifaba, please musama zukatanmu sallama kodan mutuwa, nifa banga wani dalili dazamu ke saka kammu a wahala akan mulkin da ubangijine kawai madawwami a mulkinsa, nikam kunga tafiyata, ki gafarceni inada uzuri”.
Tunda matawalle yafara maganar Mama Fulani da Talba da wambai ido suka zuba masa, harya fice ba’a samu mai iya tanka masaba. haka yake shi, babu ruwansa da bak’in mugun abun masarautar, da zuciya d’aya yakeson d’an uwansa, shi bama wani zaman k’asar ma yakeba sosai.
Wani wawan tsaki Talba yaja, yabi bayan Matawalle da harara yana fad’in “lusari kawai, inkai bakason sarautar mu ai munaso, shifa wannan ko sarautar ya gada wlhy lusarin Sarki mai lasisi za’ayi anan, duk wannan wahalar akansa akeyinta danya zama magajin Abba amma shashashan nan baya gani”.
“mtsoww!! bar banza d’an uwa, idan zai bamu matsala kai basai ka zama magajin Abban ba, nifa harma tunani nake, anya matawalle jinin gidannan ne?……….”
“kai ya isa haka, banason rashin tauna magana, Ku k’yalesa zaima dawo hanyane, miye mafita yanzun?”.
“mafita d’ayace Granny a 6arar da shegen cikin kawai, kuma ma ai Galadiman yazo jiya”.
Da sauri mama Fulani ta tashi zaune daga kishin gid’ar datayi, “wambai kana nufin Sameer na a masarautar nan?”.
“kwarai ma kuwa, da safe nagansa zaishiga mota a k’ofar sashensa, yanata faman d’aurema mutane wannan shegiyar fuskar tashi da yakejin tafi ta kowa k’yawun gani”.
Wani k’asaitaccen murmushi mama Fulani tayi tana fad’in “lallai yaronnan ya isa, kuje kawai, bayan nagama tsara komai zan nemeku”.
atare suka mik’e suna fad’in “ahuta lafiya ranki ya dad’e sarauniyar gagara badau”.
Murmushi tama jikokin nata tana gyad’a musu kai.

____((____(((?)))____))____

Galadima da Nuren sun shiga ainahin matsakaicin gidan Nuren dake a gidan gonarsa Na kiwo, sosai ya tsara cikin gidan, dan ananne yake holewa da ‘yammatansa a watannin baya, sai dai yanzu kam alhmdllh yabari gaskiya, dan sai lokaci-lokaci yake d’an ta6awa, fatansa ma yabari gaba d’aya, dama ta silar abokai ya koya??????.
Galadima ya zauna saman kujerar guda d’aya yana sauke numfashi, har yanzu zuciyarsa tak’i nutsuwa waje d’aya, halin da yaga Abban Munaya ya dank’are masa zuciya.
Cikin ma’aikatan wajen yay sallama daga waje, Nuren yabashi izinin shigowa, kayan marmarine yahad’o ya kawo musu bayan ya tsaftacesu, a saman center table d’in ya ajiye, sannan yakona yaciro musu ruwa a freight d’in dake falon da cups Na glass.
Bayan fitarsa Galadima ya kalli Nuren d’in, “Brother wai miyasa ka kawoni nan ne?”.
“cinikin kanka nayi”. ‘cewar Nuren yana harar Galadima’.
“Wani k’asaitaccen murmushi Galadima ya saki, yakai hannu yana shafa sajensa zuwa gemu, cikin d’age kafad’a da la6e baki yace “baka kai girman saida kainaba yaro”.
“uyim! Haka kace ko?”. ‘cewar Nuren yana kallon galadima’.
“kaima kasan hakanne ai”.
Mik’ewa Nuren yayi yashiga wani d’aki yana dariya, mintuna 4kacal saigashi tare da wani dattijo.
Galadima da yake kishingid’e yad’ago ido yana kallon Nuren da dattijon, amma baice komaiba yacigaba da latsa wayarsa hankali kwance.
Dattijo direban Alhaji balala ya zube k’asa yana kwasar gaisuwa ga Galadima.
Galadima shi mutumne mai mutunta Wanda ya girmesa, dan haka Yakuma d’ago kai yana kallon dattijon, fuskarsa ba’a d’aureba ba’a sakeba, cikin muryarnan tasa ta isar masu mulki da k’asaita yace “no baba zauna da k’yau, kabar durk’usamin banaso”.
Dattijo yace, “ai girmanka ne ranka ya dad’e”.
Murmushi kawai Galadima yayi, ya ajiye wayar hannunsa yatashi zaune sosai, ruwa ya d’auka ya zuba a cup sannan ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya yana kallon dattijo.
“bawan ALLAH minene sunanka?”.
Jikin dattijo Na rawa yace “Barau ranka ya dad’e”.
“humyim baba barau, koka sanni?”.
“sosaima ranka ya dad’e, wanene zaice bai sankaba a wannan nahiyar”.
Galadima ya wani lumshe idanu yana cije lips nashi, ya bud’e idanun akan Mal barau da duk yake a tsure, sosai kwarjinin Galadima da cikar haibarsa suka rikita dukkan tunaninsa da kwarin guywarsa.
Galadima ya katse masa tunani da fad’in, “Baba barau nasan akwai tambayoyi taf bakinka a gareni, saidai bazan baka amsar ko guda d’ayaba, zan baka dama da sharad’i, Na farko shine kanada damar fad’amin gaskiyar abinda kasani idan Na tambayeka, nikuma nabarka ka tafi salin alin, Na biyu inada sharad’in ka d’aukarmin alk’awarin komai zai fito abakinka ya zamto gaskiyar abinda Na tambayeka, idan kamin k’arya koka yaudareni kuma…. Humm”. ‘yak’are maganar da cije lips nashi batare da ya k’arasaba’.
Hakan yasaka jinin Malam barau rawa, yana karkarwa yace, “insha ALLAHU ranka ya dad’e zaka sameni yanda duk kake buk’ata”.
Nuren yace, “good daka fahimci hakan”.

Galadima bai sake cewa komaiba yacigaba da latsa wayarsa.

Nuren ya kalli Malam barau yace, “malam barau kasan wanene tsohon Sarki?”.
“eh kwarai ranka ya dad’e Na sanshi, shine yake jinya a India yanzu haka aiko”.
“shin minene alak’ar uban gidanka da tsohon Sarki?”.
A rikice Malam barau yace “ranka ya dad’e miyasa zakamin wannan tambayar? Ku gafarceni, kuyi wata amma ba wannanan ba dan ALLAH”.
Galadima ya d’ago idanu ya zubama Malam barau su, jiyay zuciyarsa tana Neman fara hasala, har zaiyi maganar sai kuma miya tuna yay shiru ya had’iyeta, maida kansa yayi yacigaba da latsa wayarsa.
Nuren ya bud’e k’aramar drowa dake jikin center table d’in falon, saiga bindiga ‘Yar k’arama ta bayyana, Malam barau ya waro idanu waje yana kallon yanda Nuren ke d’ura Bullets a cikin bindigar.
Galadima duk yana kallon Nuren ta gefen ido amma baice masa uffanba, saida Nuren ya gama sannan ya tashi ya koma kujerar kusada Malam barau, cikin d’aure face yace, “nasan dai tsoron mutuwa ko rasa aiki zai hanaka bamu amsar tambayarmu, to tabbas in baka fad’anba zan fasa kwalwar kanka da wannan gun d’in, kuma ko k’arar fitar bullet d’inta baza’ajiba ballema asan an kasheka, akuma cikin falonnan zan binne gawarka wlhy!!”.
Jikin Malam barau Na 6ari yarik’e wandonsa, dan har fitsari yafara fito masa kad’an, yace, “ranka ya dad’e mi kuke son sanine?”.

Galadima dake latsa wayarsa hankali kwance, batareda ya d’agoba yace, 20 ga watan Yuli miya faru a masarautar gagara badau”.
“ranka ya dad’e wlhy bansan komaiba, amma tabbas ogana yafito ransa a 6ace daga wajen meeting d’in dasukayi da Sarki shida abokansa. daga hakan bansan komaiba wlhy kaji Na rantse maka”.
Idanu Galadima ya d’ago ya zubama Malam barau, yace, “malam Saminu kafadda!. koba shine ainahin sunanka ba? Na sanar da kai karkamin k’arya, dan tunkan nakawoka nan nasan komai daya shafeka, amma a tashin farko kamin k’aryar sunanka Malam barau, humm abin dariya, inason mutum mai gardama dason ku6tar da kai. Malam Saminu shiga tarkon Muhammad Sameer ba abune mai sauk’iba, ina aiki da kwakwalwa, kamar yanda gangar jiki take aiki da zuciya, karka yarda a maganarka ta gaba k’arya ta shigo, idan hakan ta kasance saina binneka da ranka, wannan tabbatacciyar maganar Muhammad Sameer Saifuddeen ce”. ‘ya k’are maganar da mik’ewa tsaye yana had’a yatsunsa biyu ya buga a saitin fuskar Malam Saminu, suka bada sautin d’as! d’ass!, sannan ya ra6a ta gefensa yafice’.

Nuren ya girgiza kansa, “dattijo kayi kuskure kwarai da gaske, Galadima ya wuce dukkan tunaninka, tashi mu koma inda ka fito, a yanzu kam bazai ta6a saurarenka ba sai kuma wani karon”.
Hawaye Malam Saminu yafarayi yana bama Nuren hak’uri, “yalla6ai dan girman ALLAH ka kirashi, wlhy zan fad’a yanzu, wlhy nagaji da zaman kurkukunnan, nasan hankalin iyalaina da mai gidana a tashe take, ka taimakeni”.
K’ala Nuren baice masaba, ya dannashi a d’akin ya maida ya kulle sannan yabi bayan Galadima.

?):(?):(?):(?)(?):(?):(?):(?):(?

Tunda suka tafi babu Wanda yay maganar, saida suka shigo cikin gari sosai.
Nuren yace, “dattijonnan nakula zaiyi taurin kai gaskiya”.
Murmushi Galadima yayi yana kuma lafewa cikin seat, idonsa a lumshe batareda ya bud’eba yace, “mu wuce asibiti”.
Amsawa da to kawai Nuren yayi.

Sun isa asibiti suka iske duk ‘yan gidanmu suna nan, saisu Munubiya da Dady yace su tafi gidajensu hakanan, tundama ba bari ake aga Abban ba basuga amfanin zaman nasuba, gashi mafi yawansu duk da tsohon ciki, sai kuma Munubiya da Fauziyya da Haleematu dake fama da laulayi.
Haka ba dan sun soba kowacce takama hanyar gidanta, wadda mijinta kuma yace ta jirasa ta zauna jiransa.
Suma su innarmu Yaa Anas ya kwashesu ya maida gida.

Lokacin da su Galadima suka shigo asibitin mafi yawansu duk sun wuce, sai mazan kawaine a asibitin.
Dan haka Galadima yasamu gaisawa da Munubiya dake jiran yaa marwan yazo d’aukarta.
Munubiya ta tambayi ‘Yar uwarta fa?, gaban Galadima yafad’i, danshi yama manta su Munaya suna hanya, guntun murmushi yayma Munubiya yace insha ALLAH suna hanya itama, maybe su iso cikin darene kokuma da asuba”.
“ALLAH ya kawosu lafiya”. ‘cewar Munubiya tana sharar hawaye’.

Tabama Galadima tausayi sosai, haka ya k’arasa wajen doctor domin kumajin ko ansamu wani cigaba a jikin abban..
Doctor yamasa bayanin duk an gyara karayar jikin Abba, hakama sauran ciwukan suna samun kulawa, kuma bugun zuciyarsa ta daidaita bakamar jiya zuwa safiyar yauba.
Galadima ya jinjina kai, tareda sake jaddadama doctor gargad’in kulawa da Abba d’in sosai.
Yad’an jima a asibitin sannan su sarkin mota sukazo d’aukarsa, Nuren kuma daga nan hotel d’in daya sauka yanufa. ya sauka hotel ne saboda basa buk’atar wani a masarautar su Galadima yasan da Nuren d’in.

___________________________

Wajen misalin 2:30 na dare su Munaya suka sauka, Sauban yayta wayge-wayge ko an zo d’aukarsu, amma baiga alamun wani mai alak’a da masarautaba, ya kalli Munaya yana dariyar tsokana, “Aunty gimbiya Honey d’inki ya manta damu, bai aiko d’aukarmu ba, kuma inatsoron mu shiga motar haya azo a kwamushemu, kinsan yanzun kasuwancin kidnapping shine keda tsada a 9ja”.
Duk da Munaya tana tare da damuwa hakan bai hanata yin dariyaba, tace, “kai yaa Sauban bakada dama, ina zamu samu waya mu kirashi to?”.
Kafin Sauban yabata amsa sukaji magana a bayansu.
“to maganannu, saikuzo mu wuce, wannan surutun nakuma bayasa ayi kidnapping d’in naku ba”.
Gaba d’ayansu juyowa sukai suna kallonsa, Galadima ne sanye cikin wando fari 3quarter da riga t-shirt pink mai gajeren hannu. harya kwanta suka fad’o masa a rai, babu shiri yazari mukullan mota yafito, bai tada kowaba a dogaransa saboda kasada irin tasa ya fito zuwa airport, isowarsa baifi da 17minutes ba jirginsu Munaya ya sauka, tunda suka fara fitowa daga jirgin idonsu a kansa, har tsayuwarsu da waige-waigen dasukeyi na son ganin Wanda yazo d’aukarsu yana kallonsu. shagala yay da kallon Munaya, wadda sai a yanzune yaga k’ibar da Samha ke fad’in tayi, ta murje tayi 6ul-6ul da ita, har wani haske yaga ta k’ara masa, saboda hasken daya haske ko’ina a cikin airport d’in. yadad’e tsaye a bayansu, duk gulmarsa da Sauban yayi akan kunnensa ne.

Sauban ya k’araso da sauri ya rungume d’an uwansa, dukda jiyane kawai suka rabu saiyaji yayi kewarsa.
Galadima yad’an daki bayansa yana fad’in “k’aton banza, ka girma bakasan ka girma ba”.
d’agowa Sauban yayi daga jikin Galadima yana dariya, yayinda Munaya da Galadima suka had’a idanu, gira d’aya ya d’aga mata, itakuma tayi guntun murmushi tana kauda idonta gefe. (A ranta tace d’an duniya).
Juyawa yayi batare da yak’ara magana ba, Munaya da Sauban sukabi bayansa, Sauban ya shiga baya, badan Munaya tasoba tashiga gaba kusada Galadima da zaiyi driving nasu, wannan ne karon farko da zataga tuk’insa a k’asarsa.
Saida yatada motar suka fita daga airport d’in sannan a hankali kamar bataso tace, “yalla6ai mun sameku lafiya?”.
Juyowa yayi kad’an ya kalleta ya maida kansa ga titi, saida yaja numfashi sannan yace, “kunzo lafiya my Friend?”.
Kallonsa kawai tayi kad’an ta girgiza kai, a zuciyarta tace su Friend anji jiki, zanbika a hakan kodan samun yanda nakeso a kanka, danna cika alk’awarin danama mahaifiyarka insha ALLAH.
jin batace komaiba yakuma fad’in “ko gajiyar tafiyarce?”.
“kusan haka yalla6ai”.
Yace, “to sannu yalla6iya”.
Ba Munaya ba har Sauban saida yayi dariya da wannan suna, daganan motar ta d’auki shiru, har suka Isa masarautar.

Muftahu dake binsu abaya ya sauke ajiyar zuciya, sannan shima ya shigo masarautar, tunda Galadima ya fito daga sashensa akan idonsane, Dan haka yay saurin bin bayansa da mota shima Dan yaga inda zaije. (Humm Muftahu??).

Sosai Munaya kejin barci da farinciki, yau gata tadawo k’asarta ta haihuwa, sun shiga sashen komai need tagansa, sai k’amshi dake tashi kamar kullum.
d’akinta ta shige, Sauban da Galadima suka nufi nasa. Sauban ya zube a kujera yana kiran “wash!”.
Galadima ya d’an hararesa, “amma idan yawonkane aibaka gajiya”.
“yaya wlhy bazaka ganeba, nidai kawai bani wajen kwana na kwanta wlhy”.
“Saidai ka kwana anan falo kuwa, kafin da safe a gyara sashenku ka koma can”.
6ata fuska Sauban yayi, “haba Yaya da gatana na kwana saman kujera, kadai katafi d’akin Aunty gimbiya ka kwana gaskiya kabani gadonka”.
Galadima zaiyi magana Sauban yatashi da gudu ya shige bedroom d’insa ya saka key.
Da sauri Galadima yace, “zan 6ata maka rai fa Sauban”.
Ina, baima sauraresa ba, dafe kai Galadima yayi kawai, wlhy baisan lokacin da Sauban yafara rainashiba, kodan yaga tsawonsu kusan d’aya yanzu?. babu yanda ya iya dole yafita zuwa d’akin Munaya??……………..???

Ho Sauban aikinka yay k’yau??, su Galadima dole a tafi??, ba ruwana karya jini???????

Readers kuma kuyi dariya a hankali fa????.

Barkanku da juma’a????.

Musha weekend lafiya sisters??????????????????????????.

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply