Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 4


Raina Kama Book 2 Page 4
Viral

Sosai hadimansa sukayi farincikin ganinsa, kamar yanda shima yay farin cikin ganin Nasu, sud’in mutanene masu muhimmanci a rayuwarsa, sunzama wasu 6angare na duniyarsa.
Kwance yake a bayan motar idonsa a lumshe, ya saki guntun murmushi saboda tinano yanda zata k’are masa a wajen Momma, koda wasa bai sanar mata Nigeria zai zoba, yayi hakane kuma dan kartayi yunk’urin dakatar dashi ma. jin alamar motar ta tsaya ya bud’e lumsassun idanunsa tareda furzo k’aramar iska, duk da isowar dare yayi hakan baisa sauran hadimansa sun kwanta ba, ya iskesu zazzune a k’ofar sashensa suna jiran isowarsa.
Dogarin daya bud’e masa k’ofar yafara k’ok’arin d’aukar briefcase d’insa domin shigar masa.
Shima ziro k’afarsa d’aya yayi ta inda aka bud’e masan, ya zuk’i iskar masarautarsa tareda fesota tabaki yana lumshe idanunsa, ko ina kwanyar yake da hasken lantarki tamkar rana, duk lokacin daya zo cikin masarautarsa, mahaifarsa, yakan tsinci kansa cikin tunano abubuwa masu d’aci da rad’ad’i a zuciyarsa, yakanji inama ace shid’in ba kowa baneba, inama ace shid’in talakane fitik mai tarin kwanciyar hankali, da za’ace yaza6i rayuwar dazaiyi, da zai za6ama kansa zama talakane, dan babu Wanda yakai talaka kwanciyar hankali inhar yanada k’yak’yk’yawar zuciya da wadatar zuci, amma babu komai a cikin dukiya da mulki sai damuwa darashin kwanciyar hankali, kai kenan kullum cikin rashin nutsuwa, idan kayi wasama ibadar da ubangiji ya halicceka dominta bazakayiba, ya had’iye wani Abu mai d’acin gaske a mak’oshinsa. sannan yashiga k’ak’aro murmushin dole ga sauran hadimansa dake gida basuje tarbarsaba. daka kallesu kasan suna cikin tsantsar farincikin ganinsa, dan sunyi kewarsa, shima hakance agaresa. bayan sun gama gaggaisawa ya tambayesu lafiyarsu sannan yashige ciki.
Ko ina k’al yake tamkar yanda yake buk’atar ganinsa, (hadimansa nada k’ok’arin tsaftace sashensa koda baya k’asar).
Zama yay bisa kujera yana fad’in “ya ALLAH! Alhmdllh”.
Dogarin daya shigo masa da jakka yakuma masa sannu da zuwa sannan yafice.
Yakai mintuna 5 a wajen zaune, sai k’ullawa da kwancewa kawai yakeyi, ga gajiyar zaman jirgi na nuk’urk’usarsa data rashin isashen barci dabasa samu shida Munaya. da k’yar dai yamik’e zuwa bedroom d’in, komai need sai k’amshin mayen turarensa da air fresheners mai sanyin dad’i ke tashi, ya ajiye jikkarsa a kan gadon sannan yafara zame kayansa danya samu ya watsa ruwa.

Ya d’an jima a bayin sannan ya fito d’aure da towel, yana tsane fuskarsa zuwa kai dawani. wardrobe yabud’e ya d’akko boxes kawai yasaka, sannan ya saka jallabiya, sallolin da suka riskesa a hanya ya rama, yana idarwa yacire jallabiyar, matsawa yay jikin mirror ya fesa turare kad’an ya hau gadonsa da yay missing. harya kwanta yatashi zaune, briefcase d’in dayazo da ita ya bud’e, ya Ciro wayoyinsa tareda layinkansa na Nigeria duk ya saka, sannan ya ijiye wayoyin, insha ALLAH zuwa lokacin da zai tashi yana fata komai ya dai-daita.
Addu’ar barci yayi ya gyara kwanciya, amma sai barci yace bai gadaba, tunanin ahalinsa daya baro wata k’asa ya dabaibaye zuciyarsa, wata kewarsu ke tsikarar zuciyarsa, yanzu yasan Abie yayi barci, hakama Momma watak’il ta kwanta, dan macece mai yawan k’iyamull laili, duk da a asibiti takan kwana hakan baya hanata kusanta kanta ga mahaliccinta, Aunty Mimi da Samha ma yasan sunyu barci, Sauban ne dai dakamar wahala ace ya kwanta, ya juya kwanciyar sa yana murmushi, zuciyarsa tace “to matar contract fa?”. ya d’age kafad’a da ta6e bakinsa kad’an, saikuma yasaki k’aramar dariya, daren jiyane kawai ya fad’o masa a rai, yau kuma koyaya ta yini ta kwana? (danba time d’inmu d’aya da India ba), a fili yace, “ALLAH yasa yau dai babu zazza6in, my Friend kin cika taurin kai, dakin yarda nakaiki asibiti zanfi samun nutsuwa, oh god??????”. ‘ya k’are maganar da dafe kai’.
Shima yajima baiyi barciba, sai can dare yaja da nisa sannan ya saceshi.

Da asubahi da k’yar ya iya tashi, alwala yay yafita massalaci, bayan an idar da salla yafito suka had’u da Sarki da jama’a keta zubewa suna kwasar gaisuwa.
Sarki yayi mamakin ganinsa, dan har saida fuskarsa ta nuna hakan, murmushi kawai Galadima yayi yana rissinar da kansa k’asa.
Sarki baice masa komaiba yanufi sashensa, sai Galadima yabi bayansa, dogarai kuma suka take musu baya, bayan sun gaida Galadima d’in.

A hamshak’in falon mai martaba na farko suka yada zango, Sarki na zaune bisa kujera mai zaman mutum biyu, Galadima na k’asa kusada k’afafunsa. Kukun Sarki ne suka shigo shida jakadiyya bayan sunyi sallama..
K’aramin tire suka ajiye dake d’auke da butar shayi, sai mug da wani k’aramin bowl mai k’yau anzuba sukari, sai jug k’arami shima an zuba tataccen lemon tsami, saikuma Zuma shima a k’aramin bowl.
Kuku da jakadiyya suka zube gaban mai martaba suna kwasar gaisuwa, sannan suka gaida Galadima shima da masa barka da zuwa.
Cikeda kulawa ya masa musu, har kuku ya durk’usa zai had’ama mai martaba shayin Galadima ya dakatar dashi, tareda masa nuni dayaje abinsa.
Kuku ya rissinar da kai alamar girmamawa sannan suka fice shida jakadiyya suka basu waje.
Galadima ya had’ama Mai martaba shayi da ruwan lemon tsami kamar yanda yasan yana sha a kowacce Safiya, (ada mahaifinsa yasani da wannan al’adar, dan awajensa Sarki jalaludden ya koya). cikeda girmamawa ya mik’ama mai martaba mug d’in, kar6a yayi yana masa murmushi, sannan yace “kaifa?”.
Girgiza kai Galadima yayi, yace “a’a Abba, wannan sai ku”.
Mai martaba yay murmushinsu na manya sannan yace “Saukar yaushe Sameer?”.
Galadima yad’an shafa wuyansa, cikin tsantseni yace, “da daddare Abbah, wani business ne ya kawoni, inaga insha ALLAH zamu bud’e company anan Nigeria saboda muma matasanmu su Mora daga guminmu”.
Murmushi mai martaba yayi, ya kur6i shayinsa sannan yace “tunani mai k’yau yarona, ALLAH yasaka hannu a lamarin. ya jikin d’an uwana dasu auntyna Zeenah?”.
“jikin Abie Alhmdllh Abba, dan bayan tahowarku sauk’i yakuma samuwa gaskiya, Momma kam suma lafiyarsu lau”.
“to Masha ALLAH, tareda iyalin naka kazo kenan?”.
“a’a Abba, ni kad’ai nazo, saina kammala abinda nazoyi itama idan zan dawo zamu dawo tare”.
“to ALLAH ya tabbatar”.
“Amin Abba, bara naje nad’an kimtsa mu gaisa da jama’a, dan zan d’an fita”.
“ok, ALLAH yayi Albarka”.
“amin Abba, a huta lafiya”.
Hannu kawai mai martaba ya d’aga masa, Galadima kuma yafita.

Babu inda ya Shiga, ya koma sashensa domin yayi shiri. saida ya had’a coffee da kansa kamar yanda ya saba idan yazo k’asar, ya zauna yasha danba abincin kowa yakeci a masarautarba, ko Ummu hasheem bayacin abincinta kota kawo, duk da kuma kulawa datake nuna masa fiye da kowa a gidan, gimbiya zulfah uwargidan sarkima tanada k’ok’arin aika masa abincin inhar yazo, amma ko kallon kulolin ma bayayi, saidai bayinsa su cinye.

Yafito wanka yana tsane jikinsa wayarsa tayi k’ara alamar shigowar sak’o, wayar ya d’auka danya duba ko company ne, dan yana fatan ace komai ya daidaita ne, yanason kiran su Momma yaji Yaya jikin mahaifinsa.
Ganin number ce sai abin yabashi mamaki, bud’e sak’on yayi kawai azatonsa ko Nuren ne.

_Gargad’i!! tabbas sirikinka ya tsira a wanan karon, amma ka tabbatar masa next time bazamu barsaba, saimun raba ruhinsa da gangar jikinsa!!!!………………_???

*_ALLAH ya gafartama mahaifanmu?????????_*
*_Typing??_*

*_Haske writer’s asso…._*??

*_?RAINA KAMA……?_*
_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull Ce_*????

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply