Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 30


Raina Kama Book 2 Page 30
Viral

Book 2~ ????3?0?

…………….Galadima daskarewa yay a zaune, gaba d’aya magudanar jininsa tana neman Gaza aiki, saboda jininsa a daskare yake, dai-dai da bugun zuciyarsa salon datake bugunta da banne a yanzu, lallai masu kiran mata masu k’arancin *TUNANI* a zahiri sune masu k’arancin tunanin, lallai mata suna suka Tara, akwai mata akwai mata maza, juye-juye yay tayi a gadon ya kasa ta6ukama kansa komai, barci ya k’auracema idonsa, d’aya bayan d’aya Brain nasa ke markad’a maganganun Munaya dalla-dalla, wani murmushi yasaki yayinda yakai hannunsa yana shafo kwantaccen sajensa zuwa gemu, dukkanin bincikensa akan dai-dai yake, saidai rashin tsoron Munaya da kaifin basirarta ya matuk’ar k’ayatar dashi, ya tashi zaune yana jawo laptop ya kunna, saiga su Munaya sun bayyana a itada yara da Samha a kan gado, saidai yanda ya lura ba barci takeba itama, Dan tana d’an girgiza k’afarta daga kwancen. tsayin wasu mintuna ya kashe tareda mik’ewa ya d’auro alwala, abin salla ya shimfid’a ya fara gabatar da nafila kamar yanda ya saba inhar yanada lafiya.

********************

Yau likitocin Abie dasu Momma suna cikin farin ciki, saboda k’afarsa ta dama sun wayi gari tana motsawa, bayan gwaje-gwaje suna tabbatar da canjin da aka kuma samu a dukkan halittun ga66ansa, yau daga shi har Momma harda kuka, tako rungumeshi cikin tsantsar farin ciki da godiyar ALLAH, jakadiya sai fita tayi jiki na rawa…..

Galadima na tsaka da salla kira ya shigo wayarsa, koda ya idar saiya share, har yana masifa a ransa wane ke kiransa a wannan time d’in bayan yasan shi mai iyaline (?? kaga mai iyali??????).
Ganin dai baza’a barsa yaji da abinda ya damesa ba saiya d’auka a masife da nufin kashewa, kad’an ya rage ya aikata hakan sai yaga Ashe Momma ce, mugun zaro idanu yayi, jikinsa na rawa
yay picking video call d’in, Momma ce ta bayyana tana sharar kwalla, har taune harshe yake wajen fad’in “Momma mike faruwa ne?”.
Ganin ya rikice saita hau dariya da share kwalla tana masa bayani, ta matsa kusada Abie ta had’asu, yaukam dai Galadima harda k’ananun hawaye yayi Dan dad’i, gashi yau yaji muryar Abie d’insa tafito sosai ba laifi. Sunja lokaci suna waya, har kud’in wayar Momma ya k’are sannam suka hak’ura, baibi kiranba yacigaba da mik’a godiyarsa ga ALLAH. ranar dai zumbur akan abin sallah yayisa, sallar asubahi ma a d’aki yayi sannan ya samu ya kwanta, barci mai nauyi kuwa ya kwashesa.

Da shirye-shirye Munaya ta tashi, dukkan abinda zasu buk’ata tagama tanadar musu itada yara, Samha dai tayi tagumi tamkar zatayi kuka.
Bayan anma yara wanka Munaya ma tayi sai ta zauna yin break fast, suna d’an hira jefi-jefi da laraba dake ma y’an uku shiri cikin wasu kayan sanyi masu laushi.
A kullum Munaya kan tsarkake sunan Ubangiji idan ta kalli yaranta, takanyi mamakin anya kuwa daga jikinta suka fito? idan ta tuna a yanda mahaifinsu ya Samar dasu takanyi murmushi da cizar lips (copy copy????).
Duk abinda takeyi laraba na lura da ita, Munaya na birgeta sosai, Dan idan tana wani abun takanyi tunani kodai Munaya jinin sarautace? Dan salonta da takunta tana kamada na mashahuran y’ay’an sarakuna masu aji da Jan aji, cikin hikima irin tasu ta manya tace, “Ranki ya dad’e ko Baban y’an uku yatashi? Naga bakije dubashiba, gashi tun d’azun naga ankawo Karin kumallo, kuma since shima sunkai NASA amma baya falo.
Munaya tad’an Sosa k’eya tana murmushi, tace, “eh iya, ban saniba koya tashi, amma bara na lek’a na ganni”.
“yauwa ko kefa ranki ya dad’e”.
d’aukar k’aramin mayafi tai ta fita, sanye take cikin sket da riga na wani yadi mai kama da boyal Orange color, an masa kwalliyar surfani kad’an da stones da milk . Sai mayafinta siriri ya kasance milk shima, tayi k’yau sosai gashi tasha d’aurin zarah buhari??.

Tunda ta fito daga bedroom d’inta idon Galadima a kanta, fitowarsa kenan daga wanka sanye da bathrobe da k’aramin towel a hannu yana tsane ruwan kansa zuwa fuska da wuya, daina tsane ruwan yayi yatsaya kallonta ta cikin Computer d’in, harta shigo falonsa, tad’anyi kalle-kalle da lakatar center table d’in falon da d’an yatsa, da alama tana duba ko da dattine, idonsa yad’an lumshe yana lasar lips, yabar gaban Computer d’in zuwa ga mirror, zamansa babu dad’ewa tayi knocking k’ofar tare da sallama, kamar bayaso ya amsa mata, ko kad’an bata wani jisaba, Dan haka ta harari k’ofar sannan ta bud’e ta shigo.
Ko motsi baiyiba daga inda yake, saima cigaba da shafa mansa dayayi, itama batareda ta kallesa ba ta wuce zuwa ga bed d’insa tana fad’in “yalla6ai barka da asuba”.
Yanda tayi wani masifar basar dashi saiya d’an waigo ya kalleta, sa6anin da da yake kallonta ta cikin mirror. Zanin gadon ta cire hankalinta kwance, ta wuce ga wardrobe nashi ta d’akko wani tazo tana k’ok’arin shinfid’awa.
Mik’ewa yay ya tako gareta.
Jinsa akwai nayi a kaina, amma ban lura da sanda yabaro gaban mirror d’inba, k’amshin sabulun dayay wanka dashi da man days shafa duksun addabi hancina, na d’ago gaba d’aya na ina gyara mayafina domin ya rufemin k’irji da k’yau, saboda kayan babu laifi sun kamani, wajen yakuma cika sakamakon shayarwa. Dab dani yake a she, koda na mik’e sainayi kamar zan fad’a masa a jiki, nadai samu nad’an jaa baya ina tunzura baki, taku d’aya yayi yakuma matsoni, na matsa nima, shima ya matso, hardai muka kai k’arshen bango, kad’an ya rage na yandda Prime dake saman drowan gefen gadon, Wanda hoton Y’an uku ne yasa akayi ya ajiyeshi a wajen, na kalla ina gyara masa zama cikin d’an rankwafawa kad’an, hakkane yabama gyalen damar kuma zamewa, batareda na luraba na tsaya sosai, nad’an 6ata fusaka ina fad’in “yalla6ai lafiya kuwa?”.
Luuu yay da idanu saikuma ya bud’e a kaina yana cizar lips, ganin ya tsurama waje d’aya ido a jikina saina kalli wajen, baki na bud’e nakama gyalen zan rufe k’irjina da sauri ina tura baki.
Caraf ya rik’e hannun, zan saka d’ayanma shima ya rik’esa, sosai na had’e fuska idona na tara kwalla, kuma matsoni yayi sosai, ya rankwafo da kansa saitin k’irjina, rufe idona nayi ina k’ank’amesu sosai saboda tsoron mizaiyine haka?………
Bankai k’arshen tunanina ba naji saukar iska a wajen, a hankali na bud’e idona, sainaga Ashe gyalen yake hurawa da iskar bakinsa danya bud’e sosai, kunya ta kamani, dan rabin k’irjin duk abid’e yake, wuyan rigar ya cika girma.
Wata muguwar girgiza nayi, had’eda shock a lokaci d’aya, saboda saukar nutsatstsiyar Sumbata danaji a wajen, babu shiri na maida idona na lumshe ina sauke ajiyar zuciya cikin shashsheka da nima bansan nayiba.
Hakan ba k’aramin yamutsa jinin Galadima yayiba, ya d’ago yana matsoni jikinsa sosai da maida hannuna duka baya ya rik’e da hannu d’aya, na manne da jikinsa sosai. K’asa nayi da kaina saboda wata matsananciyar kunya data ratsani da mamakinsa, murmushi ya saki, Wanda tundaga zuciyarsa ya taho, Dan naji alamar hakan ta k’irjinsa, ya wani kuma maida muryarsa very slowly cikeda k’asaita yace, “yalla6iya dama kinada lafiya haka?”.
Bansan na d’ago kai da idoba na kallesa, baki bud’e nace, “kamarya? Dama nace maka banida lafiya ne? ni kabarni nayi aikina inada abunyi”. ta k’are maganar da kauda kai gefe tana tura baki.
Gira d’aya ya d’age sama, cikin ta6e baki yasa yatsu biyu ya maido fuskata Inda take, yace, “kin tabbatar kinada lafiya?”. Yay maganar yana d’aura yatsansa kan la66ana da zagayasu a hankali.
Yanzunma tilas na lumshe ido, jikina harya fara tauma, zuciyata kam sai fat-fat take tamkar zata faso k’irji ta fito.
Gangaro da yatsansa yafarayi daga saman bakina zuwa wuyana har yazo k’irijina.
Bansan nafara kamo addu’a inayiba azuciyata, gashi na kasa bud’e idanu, muryata na rawa nace, “please yalla6ai k…ka…kabari”.. Uffan bai ceba, idonsa akan fuskarta yana murmushi da taunar lips, kuma bai bar abinda yakeba har saida ya dire saitin da zuciyata take, yace “ita wannan miyasata fargaba?”.
Bud’e ido nayi a hankali dan naga miyake nufi? Na kallesa, ya nunamin k’irjina da ido, a d’arare na kalla inda yatsan nasa yake, na had’iye wani yawu dak’yar ina fad’in “babu komaifa, kaga yara zasu iya kuka ina nan fa”.
“Uhmyim” yafad’a yana d’auke yatsansa daga saman k’irjina yana maidawa kan k’uguna, ya tura hannunsa cikin rigata cikeda wani salo, hannuna nafara yunk’urin kwacewa, saiya tsaya kawai yana kallona, saida nayi harna jigata kafin yayi wani munafikin murmushi, ya matso da k’uguna da k’arfi ya had’e da jikinsa, saida naji zafi na yamutsa fuska da cewa “Uhchhh! Yalla6ai ciwo”.
“Da gaske?”. ‘yay maganar cikin matso da fuskarsa dab da tawa tamkar zai had’e bakinmu, idonsa cikin nawa yace, “kinsan mizan baki?”.
Kaina Na girgiza masa kamar wata sokuwa.
Hannunsa Yakuma turawa cikin rigata har zuwa gadon bayana, a hankali yace, “k’yauta”.
“K’yauta kuma? Tami to?”.
K’ala baice daniba ya juyani ta hanyar murza k’uguna ya maidani saitin gadon yana lankwasani a hankali, yayinda shikuma yake biyoni idonsa kan lips d’ina danake motsawa amma maganar ta gaza fita.
Muna gab da kaiwa gadon ya saki hannayena ya tallafe bayana da hannunsa, d’ayan kuma yana rik’e da k’uguna har yanzun, ahaka muka fad’a saman gadon, saidai bai sakemin nauyinsaba sosai, koda ya fad’o jikina banji zafi mai tsananiba, yay min runfa da faffad’an k’irjinsa yana matso da face nashi daf da tawa. cikin wata iriyar murya mai sanyi da k’asaita yace, “bud’e ido ki gani”.
Ban musaba na bud’esu, sai cikin mayun nasa da har yau launinsu yakeda sirkin jaa, duk yanda naso fiddawa na kasa, dan ya hanani wannan damar, saima wasu abubuwa danaga tamkar yana zubawa cikin idona, batareda na fargaba na shagala nima nabar yunk’urin janye nawa. Munkai tsawon mintuna a haka, saida ya tabbatar nagama zuwa hannunsa sannan ya d’ora tattausan lips d’insa akan nawa ya fara sarrafasu cikin tsantsar nuna yana tare da kewa da bege.
Ni munaya naga ta kaina, bansan ya akayi galadima yaci galabar samun kainaba, lallai shid’in yanada wani baiwar iya sarrafa mace a yanda yaso, ya mantar dake wacece ke balle daga ina kika fito, yakan basar tamkarma baisan micece wata soyayya ba, duk kuma randa kikazo hannunsa zaki tabbatar yacika namiji, Dan asalin jinin Malam bahaushen Na yawo ajikinsa, dukda kasancewar wayayye kuma bai girma cikin k’abilarsa ba, yakan maida hankali a harkokinsa, randa kuma soyayyar ta motso yabata muhimmanci Na ban mamaki (Matan hausawa konayi k’ayya ba hakan mazan hausawa sukeba???) (Shiyyasa Muke cewa basu iya soyayya ba?????????).
Sosai na shiga bashi dukkan goyon baya harda saka hannayena na zagaye bayansa dasu………..

??yaukuma su Oga Galadima an tina da sadaki??????.

Tafiya tafara nisan da naji yana neman sakin layi, a kasalance na rik’e hannunsa dake yawo a jikina, sannan na fara k’ok’arin janye fuskata daya koma bama kisses tako ina, sai gwama numfaahi yake yana sakin tagwayen ajiyar zuciya. ganin bazai bariba nasakar masa siririn kuka, ina fad’in, “yalla6ai jegofa m….mu…mukeyi”.
Sai a lokacinne ya tsaya cak, amma yak’i d’agani, juyo da fuskata nayi na kallesa, ya sake sark’e idonsa da nawa, idanunsa sunkuma rinewa launin jaa sosai, wani murmushin takaici ya sakarmin, cikin magana da k’yar yace, “kina kukane danna mori sadakina?”..
Wannan magana tasa tamun nauyi, Dan haka na gagara bashi amsa, sai janye idona da nayi hawaye masu d’umi suka gangaro ta gefen kunnena.
Gefena ya koma ya kwanta yana cizar lips da lumshe ido, yayinda hannunsa ke shafa kaina saboda tuni d’an kwalin ya zame. A haka yafara magana a hankali, “toke yanzu Yaya kenan? naga alamar auren Contract yakusa k’arewa, gashi ko rabin sadakina ban Moraba, zaki dawomin da kayanane ko yaya?”.
Kai wannan Bawa ya shahara a fagen rainin wayo, nafad’a a zuciyata, a fili kuma sai nace, “nima sai’a biyani d’aukar ciki da nak’uda, da shayarwa ai, tunda babusu a yarjejeniyar auren”.
Yanda nayi maganar ina yamutse fusaka da murgud’a baki saiya shagala da kallon la66anta, hannu yasaka ya tallafo fuskarta yajuyo da ita sosai inda tashi take, dukda idonta a rufe suke, “kifad’i ko nawane sai a biyaki ai, nikuma ba kud’in Dana bayar nake buk’ata ba”.
Na bud’e ido baki bud’e, “to mi kake buk’ata? Naga kud’i ka bada kuma kud’i ya kamata a baka”.
Cikin ta6e baki yace, “farashina ya wuce haka”.
Nina bakin na ta6e nace, “Niba arhar banza bace”. Nayi maganar ina yunk’urawa da tashi zaune, da kallo ya bini, saida na ziro k’afafuna k’asa sannan nakuma fad’in “mun gama sahirinmu”.
Shiru yamin tamkar bazai tankaba, harma na juyo na kallesa, idonsa a rufe suke yayi filo da hannayensa, d’auke idona nayi ina gyara rigata.
Yace, “zuwa ina kenan?”.
Nace, “gidanmu”.
Tashi yay ya sauka daga gadon duka yana nufar wardrobe, saida ya bud’e yana kallon kayansa sannan yace, “mizai hana kibari ki k’arasa aikinki kawai saiki tafi gaba d’aya”.
Na murmusa ina mik’ewa tsaye nima, na koma jikin mirror na jingina ina hard’e hannayena a k’irji, idona akansa nace, “aini nagama aikina, Dan nabaka dukkan sirrin dake raina”.
Yana ciro wasu bak’ak’en wando da Riga yace, “zadai ki gamane yarinya, Abin cikin kwan bazasu gusa a kusa daniba”.
“Humm” nafad’a cikin takaici, nace, “mizai hana ka yanke dukkan alak’a, Dan nima iyayena na buk’atar ganina a kusa dasu”.
Murmushi yayi yana juyowa hannunsa d’auke da kayan daya za6o, kallo d’aya yamin ya janye ido, “mikikeci na baka na zuba babie, indai an gama yak’in ai zata yanke”.
“nikuma bana buk’atar ganin k’arshen, in ank’i cikin sauk’i zan bud’e komai kowa ya sani”.
Murmushi yay mai sauti, har fararen hak’oransa na bayyana, ya kwance igiyar rigar wankar babu kunya ko shakkar ganina, kauda idona nayi daga inda yake, yafara saka kayansa, cikeda izza yace, “wace k’arfin gwiwa gareki na samun wannan damar?”.
“Court, tabbas zan maka ka a Court, sai a kar6a min ai”.
“kinada abin dariya kwarai da gaske, a mutum dubbunai dasuka shaida na biya sadaki sannan na d’auka, mutum d’ayane yasan sirrin ba haka bane, bayan wannan hujjar kinada watane?”.
Dariya nayi irinta tsantsar rainin hankali, harya d’ago daga d’aura belt d’in da yakeyi ya kalleni sannan ya janye, zama nayi a stool mirror, na d’ora k’afa d’aya kan d’aya ina girgizawa, “yalla6ai kenan, a tunaninka zaka iya cin bulus ne?”.
Murmushi kawai yayi bai sake tankawa ba, Dan ya kula ciwon kai take Neman saka masa, ya zauna bakin gadon yana saka sock’s da takalmi, yayinda Munaya taketa cika da batsewar sharetan da yayi. rigar jacket d’insa milk color ya d’ora bisa bak’ak’en kayan, komai nasa ya kasance bak’i, jacket d’ince kawai milk, ya matsa gaban mirror kusada ita yana gyara sajensa da fesa mayen turarensa. Saida ya gama dukkan uzirinsa kafin yazo gabana ya tsaya hannayesa duka zube a cikin aljihu.
Dan k’yau yayi k’yau kam, amma saina kauda kai gefe ina ta6e baki, irin bakayi d’innanba.
Shima bakin ya ta6e yana rankwafowa kaina har inajin hucin numfaahinsa, “karki damu mai yabawar tana nan tafe lokaci kusa, matar Sameer sarauniyarsa kinji yalla6iya”.
Cikin azama na mik’e, yay saurin ja da baya, Dan daya tsaya saina buga masa kaina wlhy.
Hanyar fita na nufa ina fad’in “idan kana buk’atar y’ay’anka zaka iya bina gidanmu ka kar6o abinka”.
Da kallo yabi bayanta kawai yana ta6e baki, akan la66ansa yace “iya tsiwa”.

Agogonsa ya d’auka bak’i ya d’aura, sannan yazuba wayoyinsa a aljihu tareda saka eyeglasses mai duhu a idonsa, ya 6oye tsananin jaa da sukayi, a falo ya iske tea a cup an had’a yanata turiri, zama yay yana lumshe idanu, yakan rasa Munaya wace irin macece ita? So salon nata akwai tsagwaron k’ayatarwa, Crossing k’afarsa yayi yana shan tea d’in a hankali, yasha kusan rabin cup ya ajiye yana mik’ewa da kallon agogonsa yanajan k’aramin tsaki.
sashen Munaya ya nufa, bayin daketa gyare-gyare suka zube suna gaidashi, hannu ya d’aga musu kawai batare da yace k’ala ba, cikin takunnan nasa na k’asaita da izza yake tafiya, bayinnan sai satar kallonsa suke, da sallama ciki-ciki ya shigo d’aki, Laraba tai saurin risinawa tana gaisheni, ya amsa batareda yako kalleta ba, ficewa tayi da hanzarinta, Samha ma ta gaidashi.
Zama yay a bakin gadon idonsa akan akwatina da Munaya ta had’a, ya janye ya maida kan yaran yana fad’in “ku shirya gobe zaku koma?”.
Cikin d’oki Samha tace, “Uncle Sam harda Aunty gimbiya?”..
Cire glasses d’insa yayi ya maka mata wani kallon daya saka hanjin cikinta mitsawa, yace “tare kuka zone?”.
Da k’yar ta had’iye yawu tana girgiza masa kai.
Da yatsa ya nuna mata k’ofar fita, jiki na rawa ta ajiye Amaturrahman tafice tana tuttura baki da share kwallan shagwa6a.
Ya lumahe ido yana jan tsaki, Munaya dai na zaune tana had’a wasu y’an kaya da suka rage a k’aramar bag, ko kallo basu isheta ba.
Rankwafawa yay duk ya sumbaci kumatun yaran, sannan ya kalleta fuska babu alamun yasan dariya yace, “wannan kayanfa?”.
Duk da na tsorata da yanayinsa, hakan bai hanani dakewa ba, cike da jan aji nace, “Na tafiya”.
Uffan baice daniba ya mik’e, kansa tsaye ya nufi k’ofa, nikuma nabisa da kallo harya fice.
Wasu hawaye danake rik’ewa tun lokacin dana baro d’akinsa suka samu damar zirarowa, hannu nasaka na sharesu ina zuge zip d’in bag d’in.

Waya na d’auka na kira Momma, na gaisheta cikeda ladabi, albishird’in cigaban jikin Abie da aka samu ta sanarmin, tsantsar farinciki ya sake kamani, nace insha ALLAH su Samha ma zasu taho da wasu magungunan. godiya tamin da sake sakamin albarka, ta tambayeni ya mukayi dashi?.
Na sanar mata yace baza’a jemai ko ina da yaraba.
Murmushi tayi mai sauti har ina jiyota. “karki damu d’iyata. Da Kansa ma zai kaiku”.
Na amsa mata da to kawai, Dan banga alamar Galadima zai tankwaru ta cikin sauk’iba akan tafiya wanka d’innan.

***********

Tunda ya fito hadimansa keta kwasar gaisuwa damasa Yaya jiki, hannu kawai yake iya d’aga musu fuskarsa babu walwala, sarkin mota da dogaran dakan bisa yayin fita suka taso da hanzarinsu, bud’e masa mota akayi ya shiga.
Saida Sarkin Mota ya tada motar sannan yace, “ranka ya dad’e ina muka nufa?”.
Banza ya masa kamar bazai tankaba, sai zuwa can yad’an nisa yana bud’e ido, “mu fara Shiga wajen mai martaba”.
“Angama ranka ya dad’e”. Sarkin mota ya fad’a cikeda girmamawa.
Bai fita a motarba, sarkin mota ne yafita domin nema masa iso, amma sai jakadiya tace, “ai takawa tunda safe suka fita shida su Masu da baraya.
Sarkin mota yazo ya sanarma Galadima, baice komaiba sai kansa daya jinjina kawai.

Daga nan basu zame ko inaba sai gidanda su Muftahu suka kai yarannan. Muftahu da kansa ya bud’e musu k’ofa suka shiga, aka bud’ema Galadima ya fito, tafiya yake a nutse cikeda k’asaitar masu mulki da tashen k’uruciya, Muftahu ya tako a hanzarce garesa, hannu yabasa sukayi musabaha, sannan suka cigaba da tafiya cikin gidan a jere, fuskarnan babu walwala yace, “ya kuke ciki dasu?”..
Muftahu yad’an nisa yana bud’e masa k’ofar shiga falon dansun k’araso, “Ranka ya dad’e bamu tambayesu komaiba, Dan wannan ba Hurumin mu baneba ai”.
Galadima baice komaiba, ya zauna kujera mai zaman mutum d’aga yana d’ora k’afa d’aya kan d’aya.
Muftahu bai zauna ba saida ya d’akko glass cup da kwalin Hollandia ya ajiye gaban Galadima.
Galadima dake danna waya yad’an d’ago ido ya kallesa ta cikin glasses, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru ya maida kansa ga wayar.
Girgiza kai kawai Muftahu yayi, Dan yasan magana yakesonyi amma yaza6i yayi shiru daya bud’e bakin. yana tausayama Munaya wlhy, “Ranka ya dad’e su zone?”. dan yasan bai wuce abinda yake son cewa kenanba.
Ilai kuwa sai Galadima ya jinjina kai yana nuna yatsansa d’aya alamar mutum 1 yakeso.
Nanma dai Muftahu kan ya girgiza kawai sannan ya mik’e. Mintuna uku kacal saigashi da mutum d’aya a cikinsu. har yanzu kuma idon Galadima nakan phone nashi.
Saurayi da bazai wuce shekaru 30 zuwa sama a duniya ya durk’usa gaban Galadima kamar yanda Muftahu ya umarcesa, kwarjinin Galadima da cikar haibarsa da tsare gida duksun rikita gayen, bakinsa na rawa yace, “barka da safiya ranka ya dad’e”.
K’ala baice dashiba, kusan mintuna biyu ya ajiye wayar yamasa kallon tsaf sannan ya janye idonsa, kansa ya jingina da kujera ya lumshe idanu, hannayensa duk suna bisa hannun kujerar, cikin maganar nan tasa mai kama da anmasa dole yace, “wanene kai? miya kaika gangancin shiga hurumina?”.
Ba k’aramin tsuma da birkita muryar Galadima ta saka guy d’inba, haka kawai sautin muryar Galadima dabata da r a cikin kalami ya rikita guy d’in, murya na rawa yace, “Ranka ya dad’e sunana Shazali, kuma wlhy bansan komaiba, nidai kawai anzo an bamu aikine”.
Halbi Muftahu yakai masa yana fad’in “k’arya kakeyi”.
“Wlhy da gaske nakeyi”. Shazali yafad’a cikin mak’yark’yata.
d’agowa Galadima yayi zaune sosai, yace, “kozan iya sanin wanene yabaku aikin?”.
“Bansan sunanta ba Ranka ya dad’e, amma zan iya ganeta”.
Kallon Muftahu Galadima yayi, Muftahu daya san abinda yake nufi ya jawo laptop yana ajiyewa gaban Galadima.
Zama ya gyara, cikin kwarewa yafara sarrafa System d’in yana cizar lips kad’an-kad’an, wannan salo na yarima yana burge Shazali, aransa yana jinjina mulki mai dad’i kenan, haka kawai k’aunar Galadima ta shigesa, kuma yayi alk’awarin taimakonsa cikin sauk’i insha ALLAH…….
Tunaninsa ya katse lokacin da Galadima ya turo masa laptop d’in.
Kallonsa yad’anyi Dan baisan mizaiyi da itaba. d’auke kai Galadima yayi alamar bazai yi magana ba.
Muftahu yace, “ka duba idan akwaita anan”.
Laptop d’in Shazali ya ida jawowa gabansa, hotunane suka bayyana da yawa. Muftahu yamatso yana masa zooming nasu one by one.
Nuren yafito daga wani d’aki yana mik’a, da mamaki yake kallon Galadima dashima shi yake kallo, “brother kaine?”.
Kai Galadima ya girgiza masa alamar a’a.
Nuren ya murmusa yana tahowa cikin falon, hannu yabama Galadima sukayi musabaha, yana tambayarsa yaya jiki?.
Akan la66a ya amsa da “Alhmdllh”.
Nuren yace, “ina yarana?”.
Da hannu yamasa nuni da lfy.
Kular da Nuren yayi yau k’asaitar a kusa take saiya barsa ya mik’e, Coffee ya had’o yadawo ya zauna yana kallon abinda su Muftahu sukeji.
Shikam Galadima yayi shiru yana tunano yanayinsu da Munaya na d’azun, yana da buk’ata mai tsanani, saidai yakan danne saboda jarumta, musamman idan ya tuna matsayin auren nasu, ko a baya saboda yanayin data shigane ya sakashi yin yadda yaso da ita, Dan hak’k’insa ne ya taimaketa a lokacin kodan buk’atar tazame mata lalurar cikinsa, yanzu kam dolene yanemo mafita ko matar aur……….
Tunaninsa ya katse lokacin da Shazali ke fad’in “itace wannan yalla6ai”.
Daga Muftahu har Nuren kallon picture d’in suka tsaya yi, sannan duk suka kalli Galadima da shima idonsa ke Kansu.
Nuren ya d’auki laptop d’in ya mik’a masa, shiru Galadima yay yana kallon hoton, Matar Abie ce ta biyu, wadda yata6a gani a wayar Harun, yay wani miskilin murmushi yana yana kallon Shazali, saikuma ya janye idonsa batare da yace uffanba.
Shazali ya gyara zama yana fad’in “bayan ita kuma sai aka had’amu da wannan matan daga masarauta, sukuma sunce Uwar gidan sarkice ta sakasu”.
Nuren yace, “uwargidan Sarki kuma? to tayaya tasan kud’in ga abinda zakuyi?”.
“wlhy ban saniba nima ranka ya dad’e, abinda na Sani kawai a ranar wlimar kafin mu shigo hall d’in aka taremu a hanya, shine wani dogari ya shigo motarmu, da farko mun taso masa harda fiddo wuk’ak’e, saishi kuma ya nuna mana bindiga, hakanne ya sakamu nutsuwa, yace, yasan abinda zamujeyi ai, dan haka idan munason mu tsira da ranmu mu sauraresa da k’yau, shima aiki zai bamu. Zai had’amu da bayi biyu mata dazasu taimakemu mu sace yaran, bayan mun gama akwai kaso mai tsoka, sannan zai fad’a mana wani sirri, mahaifin yaran yayi shirin canjasu da y’ay’an babyn roba dan haka karmu sake mu d’auki yaran da za’a bama wasu yara, mu d’auki na cikin gado daza’a sakasu a wajen taron, sune zasu zamo na gaskiya, mak’udan kud’in daya bamune suka samu amincewa da gaggawa, Yakuma sanar mana aikin uwargidan sarkine, idan har mukayi kuskuren wani yasani dagamu har ahalinmu sai sun shafe labarinmu a doron k’asa”.
Daga Muftahu har Nuren kallon Galadima suke da mamakin Brain nashi, hakan suka shirya, amma daga baya sai sukaga ya canja yabada yaran da gaske, sunyi mamaki sosai, amma bai basu fuskar tambayarsa ba a time d’in.
Yay musu alamar miye suke wani kallonsa.
Salute d’insa sukayi su duka, ya kauda kansa kawai yana ta6e baki.
Sun kuma tabbatar da akwai sirrika da yawa da Galadima ya Sani, akwai yana basarwane saboda jiran lokaci.
Da hannu yamasu Nunin Shazali yatashi yaje.

Bayan tafiyar Shazali ya kallesu yana sauke ajiyar zuciya da gyara zamansa, ya d’auki kwalin hollandia yazuba a cup, Muftahu da Nuren dai na kallonsa, saida yafara sha da kallon agogon hannunsa sannan yace, “Zanje India gobe idan ALLAH ya kaimu, akwai ayyukan dazan tattara na kwanaki uku, sannan na d’auki Hutu a wajen aiki, dukda muna shirye-shiryen fidda kaya na shekara mai zuwa, a Daren yau Harun zaisan matsayinsa, Dan tuni nagama da matsalarsa dama, wannan ranar nake jira, so Nuren ka bincikamin inda matarnan take zaune a yanzu, Dan ina dawowa zan shiga aikine sosai, matsalar Harun da ita da Sarauniya kowanne akwai manufa, su nasu wasan yarane a wajena. Erfan shine yajema Munaya a matsayin Fu’aad, yanzu na fahimci sune suka saka aka buga waccan jaridar, amma da saka hannun wasu a gefe……..”
Muftahu yay saurin cewa “yi hak’uri ranka ya dad’e zan katseka, sai yanzu wani Abu yazomin a rai, wato ranar salla a filin idi, kasan Erfaan yana tare damu, anya kuwa ba a wannan time d’in ya ganku kaida gimbiya ba, lokacin da kukayi karo, wata k’il shikuma yayi tunanin alak’a Ce a tsakaninku?”.
Murmushi Galadima yayi yana lumshe ido, “ni kaina ina tunanin haka, saidai akwai wani Abu bayan wanna, dan haka sarakuna uku sun shigo cikin aikina”.
Da mamaki Muftahu da Nuren sukace sarakuna kuma?.
K’ala baice da suba ya mik’e tsaye, ya kalli agogon dake tsintsiyar hannunsa sannan ya kallesu, “gobe da safe Alhaji Shehu Darma zaije taron k’arama juna sani a jihar Katsina, lallai bana buk’atar yama k’arasa”.
Kusan a tare sukace Alhaji Shehu Darma kuma?.
Ficewarsa yayi batareda yabasu amsaba balle su sami k’arin bayani. baki bud’e Nuren da Muftahu suka kalli juna, Muftahu yace, “shikuma miye nasa to?”.
Cikin jimami Nuren yace, “nima abinda nake son Sani kenan, mutumin da tunda mijin aunty Mimi ya rasu yake fad’i tashi a kanta da yaranta, danma tak’i amincewa ne da aurenta zaiyi, anya kuwa shi yake nufi kodai wanine mai irin sunansa?”.
Jiki a sanyaye Muftahu ya yarfar da hannu alamar bai saniba shima. danshi lamarin Galadima yafara bashi tsoro, mutum kamar wani tsohon aljani.

Shikam koda yabar wajensu wani office yace Sarkin mota ya kaisa, yakai tsawon lokacin a wajen tareda wani mutum dabazai gaza shekaru 56 ba a duniya, bansan mi suka tattauna ba, dan ba’a bani damar jinba.
A wajen yay sallar azhur har la’asar sannan yayo masa rakkiya wajen Motocinsa, saida yaga fitarsu sannan yakoma Office d’in.

Daga nan masarauta suka nufa, dan Galadima a matuk’ar gajiye yake,
Ya iske sashensa fes an gyara, ko ina yana tashin k’amshi tamkar yadda yake buk’ata, kayansa yacire ya watso ruwa, bai nemi kowa baya ya zauna a falo yana aiki a System, dukda yaga abincin da aka ajiye masa baiko bud’eba balle tunanin cinsa, Yakuma san Aunty Mimi ce zata saka a kawo.
Yana tsaka da aikin Sauban ya shigo, bai kallesaba koda ya gaidashi, yadai Amsa.
Sauban yace, “yaa Sam tafiyar safe zamuyine goben?”..
Ido Galadima yad’an d’ago ya kallesa, ya maida kansa ga laptop d’in yana fad’in, “Kwana 3 zamuyi ni da kai mu dawo, komanka na gameda bautar k’asa yagama kammaluwa”.
Kamar Sauban zai sanya kuka yace, “Amma Yaa Sam su Momma sai abarsu babu kowa?”.
“kafin ka girma dawa suke zaune?, Sauban ka kiyayeni, karka bari na fusata akanka, tashi bani waje”.
Sauban ya mik’e zuciyarsa na zafi, harzai fita Galadima yace, “zonan”.
Dawowa yay yana mirgina kai, batareda Galadima ya kallesa ba yace, kar6a wannan, kaje ka sakashi jikin rigar Abdurrahman ko Amaturrahman ka d’auki Wanda ka samawa d’in kaje sashen Ummu Amaan (gimbiya Zulfa) dashi”.
Sauban baice komaiba ya kar6a abinda yabashi mai kama da ma6alli ya fita, ya iske Munaya na barci, yaran kuma na tare da Khaleel dake ta fama jagwalgwalasu, Abdurrahman ya d’auka ya sakamawa ya nad’eshi a showal ya fita……

Nikam wannan gangancin na Galadima ya isheni??????.

Bansake jin miya faruba dan banbi Sauban ba nikam, ina tsoron ganin abinda zai hanani barci??.

__________________________

Misalin 8:30 na dare Galadima ke shiri bayan ya dawo daga sallar isha’i, yagama tsaf cikin k’ananun kaya da jacket d’insa wadda takai masa har gwiwa, ya saka safa har a hannunsa, cikin takunnan nasa na gwarzantaka ya fito, sashen Munaya ya nufa, sukaci karo a k’ofar d’aki zata fito a rikice, sauri tareta yayi ta fad’o jikinsa saboda kad’an yarage ta fad’i, k’amshin turarensa ya sakata shaida shine, ta share hawayenta tana kallonsa a rikice, shima kallonta yakeyi, Muryarta na rawa saboda kuka tace, “yalla6ai Abdurrahman sai kuka yakeyi, jikinsa ya d’auki zafi”.
Baice komaiba ya kama hannunta suka koma cikin d’akin, laraba da aunty Mimi na zaune, aunty Mimi tana zarema Abdurrahman kayan jikinsa za’a watsa masa ruwan d’umi kozaiyi shiru.
Zama yayi ya kar6e sa daga hannun Aunty mimi, ya fiddo wani kwali k’arami daga aljihun jacket d’insa ya bud’e, k’aramar kwalbar dake cikeda magani ya fiddo, ya d’iba maganin cikin tsinken da ake bama yara magani ya zubama yaran a bak’i, dak’yar ya shanyeshi.
Sudai sunyi jugum-jugum suna kallonsa.
Yunk’urin amai da yaron keyi yasaka Galadima d’agashi daga jikinsa dan kar yay masa, baimayi amanba, hakanne yasaka Galadima sauke ajiyar zuciya ya mannashi da k’irjinsa yana hura cikin kunnen yaron a hankali.
Tun yana kukan kad’an-kad’an ya koma ajiyar zuciya, sai gashi yayi barci. Kwantar dashi yayi kusada y’an uwansa ya lullu6esa.
Ya kalli aunty Mimi yana mik’ewa, “insha ALLAH zai sauka zaza6in”..
Yanda Aunty Mimi kebinsa da kallon tuhuma saiya janye idonsa yakama hanyar fita, da sauri tamik’e tabi bayansa a fusace. Dan Sauban ya sanar mata Galadima ya sashi kai yaron sashen mai martaba d’azun.
“Dakata Sameer”.
Cak ya tsaya yanajan hular rigar bisa kansa, amma bai juyoba.
“Sameer wai mike damun kankane haka? da zaka ringa wasa da rayuwar yaranka da kanka?”.
Lips d’insa ya ciza, ya juyo yana kallonta, amma ita bata ganin idanunsa saboda hular ta rufe, murmushin takaici yayi, yace, “Ni ba wasa da rayuwarsu nakeba aunty Mimi, komai kikaga nayi nasan abinda nakeyi, zuwa nangaba kad’an kuma zaku fahimci komai”.
“ALLAH yasa to, amma ni yanzu na zone muyi maganar komawar Munaya gida kafin mu wuce goben, tunda jirgin rana zamubi”.
Agogon hannunsa ya kalla, yace, “yanzu kam inada uzirin fita?”.
“fita? Inakuma zakaje a wannan daren?”.
Batareda ya tanka mataba yajuya yakama hanyar fita, saida yaje bakin k’ofa sannan yace, “Farauta”. yay ficewarsa.

Kasa motsi aunty Mimi tayi a wajen, sai maimaita Sunan Galadima kawai takeyi akan la66anta.

******

Tacan baya yabi shikam, hanyar akwai k’arancin mutane sosai, yana zuwa ta wani waje yagamu da wani Wanda ke sanye da irin kayan hadiman masarautar, rissinawa yay yabashi keys d’in mota. ya kar6a batareda sunma juna maganaba ya wuce.
Can sashen su Harun naga ya nufa, dukda tazarar dake tsakaninsu baiji tafiyarba, motar dake fake a wajen ya bud’e ya shiga ya zauna, zamansa da mintuna uku Harun yafito ad’an hanzarce, motar yabud’e seat d’in baya ya shiga ya zauna, cikin bada Umarni yace, lawandi muje, kasan d’an bala’innan yanada securitys dake kaimasa rahoto”.
Murmuahin gefen baki Galadima yayi yatada motar yafice daga masarautar…………….???

 

“Hummmm! Reader’s harna sauke numfashi, babbar magana, yau dai ga Galadima ga Harun, sauran abinda zai faru kuma sai a buk 3 na raina kama”.
Miya faru da Abdurrahman lokacin da Sauban ya kaisa sashen gimbiya zulfah ne??? Yaya batun kama SD?, wad’anne sarakuna ne Galadima yake zargi? Kodai dama can Galadima yasan wanene Harun yabashi damane kawai???, Yaya batun warkewar Abie da Auren Contract tsakanin Galadima da Munaya?, mi suke shiryawa itada Momma da suka damu da zuwanta wankan gida? Ko Galadima zai amince?”.

Yaya batun gano asalin innarsu Munaya? Da ita Munayar ta d’auki alwashi?.

Tofa wannan amsar dai duk zatazo a littafi na 3 kuma na k’arshe da izinin ubangiji, dukkan wasu tambayoyinku amsarku na cikinsa, zan had’a muku da albishirin zan dingayi a weekend rana 1, kodai asabar ko lahadi, kowacce rana nasamu dama aciki, dan buk 3 inason kammalashi ne a gaggauce saboda uzirin danake dashi insha ALLAH.

Ngd sosai da had’in kan da kuke bani, muje zuwa my guys???????????????????????????????????????????????.

Barkanku da juma’a????.

Musha weekend lafiya????????????????????

 

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
*_typing??_*

?? *_HASKE WRITERS ASSO….._*

*_?RAINA KAMA…..!!?_*
_(Kaga gayya)_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*
_________________________

*_Kai jama’a yau dai kun Sani typing dole saboda munafurcin y’an bani Na iya, wannan karon kuma kurasa k’ullin da zakuyi sai akan Uwa da ‘Diya?, nikam yau koda mamana (mamu gee) kwaikwayar RAINA KAMA tayi to wlhy birgeni zatayi, ai baiwace ma wani yayi Abu kabishi daki-daki kana kwaikwayo. Irin wannan shirmen naku baya cikin kan Bily, ba mamu gee ba koda watace aka jingina da hakan bazanji komaiba wlhy, sannanma nifa abinda yabani mamaki a writeup d’in da mamana tayi bata ambaci sunan RAINA KAMA ba aciki ko wani littafi daban, to tayaya y’an bani Na iya da tsugunne-tsugunne su anasu writeup d’in suka saka sunan RAINA KAMA? (Wlhy halin wasu daga cikin writers namu ko kad’an bashida k’yau, neman sunane kokuwa son asanine niban saniba??????)._*
_Reader’s kuma da naku, sometimes bakunanku basuda linzami, irin wannan abubuwan kune ke fara tsirarsu saisuzo kuma su buwayeku, Ku ke karanta RAINA KAMA DA TARAYYA Ku kusan banbancin abinda ke cikin kowanne, amma dayake Ku irin wannan dama shine farin cikinku saikuyita k’irk’irar abinda dolene daga k’arshe saiya zama rikici, to nikam zan sanar muku, awanan karon sai had’in naku baiyiba, Dan MAMU GEE DA BILYN ABDUL duk Abu d’ayane, daga tarayya har Raina kama buks d’inmu ne, mu muke rubuta abunmu, babu wata munafukar writer ko reader da mukayi shawara da ita kafin mu d’aura alk’alaminmu a takarda, masu had’a husuma kuma sai kusha fetur Ku had’iyi ashana kuyi bombing d’in kanku, ina dai shikenan ko?????_.
*Daga k’arshe inamai muku nasiha da kuji tsoron ALLAH, wlhy bashin naira 10 kacal yana hana bawa kwanciyar kabari, karo tsakanin rago da rago kawai akwai hisabi tsakaninsu, aranar kiyama bayan an tsaya hisabi duk Wanda kasani koya sanka saika Ganshi kakuma ganeshi, bawai kaitsaye za tantanceka akaika wuta ko aljanna ba, wlhy sai an tsidaka, ancire hak’in mutane a kanka, ka zagi wane babu hak’k’insa, ka harari wane, kama wane zind’e, ka cinye kud’in wane, ka had’a fad’a tsakanin wane, ka 6ata sunan wane, ka cuci makwafcin, ka…ka…ka…da yawan gaske, duk wani cin amana ko zalunci dakama wani inhar bai yafe makaba a wannan ranar sai an cire masa hak’insa a cikin ayyukanka, (Dan sune kad’ai guzirinka) komai tarin aikin alkairin daka tara inhar kanada irin wad’annan bashishshikan d’aya bayan d’aya sai an zaresu daga gareka, koda dabba da kafiri ka zalunta kuwa, idan dama bakada komai, sai ayita kwashe nasu zunubai ana lafta maka, sai angama tas, kabiya an biyaka saikuma a gwada ayyukanka a kan mizani, miyarage kuma? Saika koma gefe jiran sakamako. Wlhy y’an uwa babu babban tashin hankali irin kar6ar sakamako, a wannan lokacin uba baya gane d’ansa, y’a bata gane uwarta, miji baya gane matarsa saboda tsantsar tashin hankalin da ake ciki, da wane hannu xaka amsa, ina ne zaizama mazauni Na dindindin, duk baka saniba, haba y’ar uwata, kinada wannan babban aiki a gabanki amma kika shagala wajen had’a husuma irin ta social media wadda bansanki ba, baki sanniba, maybe ma har Abadan bazamu ta6a sanin junanmu ba, muji tsoron ALLAH wlhy, yakamata irin wannan abubuwan su tsaya hakanan, daga ni har mamana badan Neman suna mukeba, domin Isar da sak’o mukeyi a cikin tarayya da raina kama, burinmu kuma ko mutum d’aya ya amfanu da manufarmu ya wadatar, bawai tarin masu karantawa ba, ni miyasa babu Wanda yata6a tarata yacemin tarayya copy d’in raina kama ne? to Ku kama kanku please, kodan tsoron ALLAH.*

_My Sweet mah-mah mamu gee wannan page d’in sadaukarwane a gareki, kiyi yadda kikeso dashi nabaki, ALLAH yabarmu tare, I love you irin trillions d’innan, kisamun albarka nakuma zama gagara badau????._

Bilyn Abdull & Mamu gee RAINA KAMA ne mu, sannan munyi TARAYYA NE akan Isar da sak’o mai muhimmanci, mabiyanmu Na gaskiya a KAFTA kawai?????????????????????.

HARUN da GALADIMA kuma Ku KAFTA naku wasan???????????????????????.

_

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply