Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 3


Raina Kama Book 2 Page 3
Viral

~Book 2~ ????3?

…………Shiru kawai yayi yana kallon fuskarta ta cikin d’an hasken mai kalar jaa, sai fuskar tabada wata kala data k’ara mata k’yau. yaune ranar farko dazaice yamata kallon k’urilla irin haka, yadad’e yana kallonta kafin ya janye idanunsa dake cike da barci. hannu ya mik’a ya kunna ainahin fitilar, haske ya gauraye d’akin, cikin dabara yafara yunk’urin janye jikinsa, amma tak’i yarda, saima farkawa datayi, tabud’e idanunta dasukai nauyin barci a hankali, kad’an take kallon face nashi, ta lumshe idon tasake bud’ewa.
“wannan d’aurin goronfa?”. ‘galadima yay maganar a hankali cikin muryar barci, yanabin hannun munaya da ta zagaye cikinsa da kallo’.
Sosai Munaya ta waro idonta yanzun, ganinta a jikinsa kwance, gashi tawani dabaibayesa saita sakeshi da sauri tana matsawa baya da waige-waigen inda take kwance. gabanta ne ya fad’i, dan ita harga ALLAH tama mance ta hau masa gado, tayi saurin rik’e kanta dake sara mata tana tashi zaune.
Shima saiya tashi yana binta da kallo, a mugun sanyin murya yace “bakida lafiya ne?”.
Hawaye suka wanke mata fuska, muryarta na rawa tace “kaina kamar zai tsage”.
Saida yaja 1minute kafin yad’an matso kad’an, yatsunsa biyu ya d’ora gefen wuyanta, saiyaji jikin zau da zafi, ya janye ya d’aura zuwa gefen kanta, jijiyar wajen sai motsi takeyi d’ass d’ass d’ass d’ass, alamaun kan namata ciwo sosai. hannun ya janye tareda sakkowa daga gadon gaba d’aya.
Ya zagayo 6ari da take, hannu yasa ya zame nata hannun data tallafe kanta dashi, ta tad’ago idanunta dake cike da barci, sunyi d’anja sun k’ara girma, idonsa a kanta, Dan haka ta janye nata ta maida k’asa tana cigaba da hawayenta.
Kad’an yad’an furzo iskar bakinsa, kafin a hankali yace “mike miki ciwo bayan kan?”.
Saida takuma matso wasu hawayen sannan tace, “duk jikina”.
“kin fad’ine?”.
Kanta kawai ta iya girgiza masa, ya cigaba da tsura mata idanu batare da yace komaiba, ganin tana hawaye duk sai yaji babu dad’i, koba komai itad’in Friend nashice ai, kamar yanda yafad’a tun farko. yad’an sauke ajiyar zuciya mai sauti kafin ya mik’e, bayi yashiga, mintuna kad’an yafito, tana a inda ya barta dafe da kanta, yace “taso kid’an watsa ruwa, ko jikin zai huce”.
d’agowa tayi ta kallesa, sai taga ya tsatstsareta da mayun idanun nan nasa, tayi saurin janye nata, amma takasa tashi. matsowa yayi kusada ita, ya mik’a mata hannunsa, alamar takama ta tashi, ta d’ago ta kallesa ya d’aga mata kansa yana mai lumshe idanunsa alamun tabbatarwa.
Hannunta ta saka a cikin nasa, ya had’e waje guda sannan ya taimaka mata ta tashi tsaye, kallo d’aya yamata ya kauda kai, dukda kayan nata masu kaurine saida yaji wani Abu daban, dansu fidda surarta sosai. Har wajen wankan yakaita, sannan yafito batare da ya ce uffanba. da kallo tabi bayansa, a ranta tana mamakin sauk’in kai irin nasa, ada kallon mutum mai girman kai take masa, amma tunda suka fara rayuwa a tare saita fara fahimtar ba haka baneba, kawai dai shi mutumne dabai cika hayaniya da surutu ba, shiyyasa inbaka gama saninsaba saika dunga masa kallon mai girman kai.
Koda ya fito saiya had’a mata tea, shi dama baya rabo dasu a d’akinsa, magani ya d’akko shima ya ajiye, yakoma bakin gadon ya zauna yana tsumayen fitowarta.
Kusan mituna 10 tagama watsama jikinta ruwan, lallai naji dad’i sosai, saidai kuma bazan iya maida kayan dana cireba, inajin kunyarsa, kuma jinsu nake sun d’auki zafi, towel naja Na d’aura, saidai bashida girma, bazan iya fita a haka dashiba Galadima yana d’akin, kad’an nabud’e k’ofar Na lek’oda kaina, yad’an juyama k’ofar bathroom d’in baya kad’an, a hankali cikin muryata mai nuna alamun banida lafiya nace “please yalla6ai ka taimakeni da hijjab”.
Waiwayowa yayi ya kalleni, alamun baijiba sosai, Na turo baki kad’an sannan nace “please yalla6ai hijjab”.
Baice komaiba ya mik’e, inda nake ajiye hijjab d’in yaje ya d’ako, yazo inda nake ya d’oramin akan hannuna dana mik’o, kallon ido cikin ido mukaima juna, kowa ya janye cikeda basarwa.

Bayan nasaka hijjab d’in nafito kamar wata muna fuka, sai k’asa nakeyi da idanu nakasa kallonsa, shima idonsa a lumshe ya jingina da fuskar gadon, wucewa nayi wajen akwatina Na d’akko wasu kayan barcin, bayi nakoma Na saka, saina yafo k’aramin Vail Na cire hijjab d’in.
Yabud’e idanu kad’an a kaina, batare da yayi magana ba ya nunamin mug d’in daya had’a tea a ciki. nad’an yatsine fuska da marairaice murya tamkar xanyi kuka, “ALLAH yalla6ai banajin yunwa”.
Shiru yay kamar bazai tankaba, saida yaja kusan 2minutes sannan yatashi zaune sosai, batare da yayi magana ba ya d’auki mug d’in da drug’s d’in ya taso inda nake zaune a kan sofa, saman k’aramin table d’in gaban kujerar ya zauna yana fuskantata, d’an gaf d’in daya bari tsakanina dashi bai wuce tafin hannuba, Dan har inajin saukar numfashinsa, baya nad’anja kad’an Na jingina da jikin kujerar, amma hakan bai hana kusanci sosai tsakanina da shiba. babu magana babu komai naji dirar cup a bakina, d’ago ido nayi tamkar zan fasa kuka, danni wlhy banajin shan shayinan, yamin hararar data saka ‘yan cikina harmutsawa, babu shiri nabud’e baki na kar6a, ya had’e girar sama da k’asa, baibar ko k’aramar k’ofar dazan kawo masa wargiba, haka naita kar6a ina hawaye, saida yaga Na shanye tas sannan ya barni yana hararata, nidai yau babu k’arfin mayarwa, yabani maganin, shikam babu musu Na kar6a nasha. ganin yanda naketa hawaye saiya zubamin ido kawai yana kallon ikon ALLAH, nikam banida niyyar daina kukan nawa, kuma nima bansan dalilin kukanba, kawai dai jinake hawayen Na tahowa.
Ya zuba tagumi abunsa yana kallona kamar yasamu television. kallon dayake min saiya k’ara tunzurani, nafara kuka mai sauti harda shashsheka.
Tagumin yacire yana wani k’asaitaccen murmushi, ya mik’e tseye yakoma kan gadon, filolin dasuke k’asa ya d’auka ya jera a tsakkiyar gadon kamar d’azun. nidai duk ina kallonsa, saida ya lullu6ama k’afafunsa bargo zuwa cikinsa sannan yace, “taso ki kwanta sarkin arhan hawaye”.
Harara Na zuba masa batare da Na shiryaba, sai kawai ya ta6e bakinsa yay kwanciyarsa ya barni, tareda kashe fitilar ya maida ta barci.
Kusan mintuna 4 Na zame Na kwanta a kujerar, amma sainaji duk babu dad’i, saboda maganin bai fara tasirin da jikina zai bar ciwonba, tashi nayi nakuma zama, kusan 5munutes sannan natashi sad’af-sad’af tamkar munafuka na haye gadon. Ni duk tunanina yayi barci. Ashe duk abinda nake yanajina da kallona. murmushi yayi kawai yana lumshe idonsa, a ransa yana jinjina irin rashin wayona.

Ajiyar zuciya Na sauke a hankali, sannan naja bargon dayake babbane Na lullu6a, mintuna kad’an nafara zufa, alamar zazza6in ya sauka. Bargon na janye don insha isaka, bansan sanda barci ya saceni ba.
Juyowa yayi ya kalleni, yaga ina sauke numfashi a hankali alamar nasamu barci, k’aramar ajiyar zuciya ya sauke kafin yasake addu’a shima ya gyara kwanciyar sa.

???????

Yau gidanmu sun tashi cikin tashin hankali, Abbah yay Accident yayin dawowa gida daga wajen aikinsa, innarmu Na kwance ciwon kai dukya isheta, tunda ta tashi da safe dashi ta tashi, gasu Aryaan sun isheta da ihun fad’ansu, sai mugun wasa sukeyi suna guje-guje a falon, amma takasa d’aga kai ta tsawatar musu.
Zuciyarta cike da kewar su Munubiya, inda suna nan da yanzu suke bata taimako, koyaya tace batajin dad’i zasu rud’e, amma gashi yau ko wanke-wanke tama rasa mai matashi, sai Zainab maman fauziyya tasaka tayi mata, amma 6angarenta ko shara bai samuba yau, kuma tun d’azun tafara jin mamansu yaa hameed tana k’ananun magana akan tak’i fitowa ta aza musu girki, maimakon sunga shiru su lek’o suji ko lafiya? A’a su babu ruwansu, kawai a dafa abasu suci da ‘ya’yansu…
Wayarta dake ring ta katse mata tunani, ta kalli su Aiyaan dake danbe Aryaan Na kuka saboda dukansa da Aiyaan yayi a baki. “wani cikinku ya d’akkomin wayata saman freight”.
Cikin kuka Aryaan yace “Innarmu kingafa ya dokarmin baki”.
“kukuka Sani, nidai nace wani ya d’akkon waya acikinku, idan kuma kuka bari Na tashi sai jikinku yagaya muku”.
Aryaan ya d’akko mata wayar ya kawo mata, lokacin harta tsinke, ganin Abbanmu ne yasata bin kiran, bugu biyu aka d’aga, ko gaisuwa bai bari sunyiba, yace mai wayarne yayi Accident, yanzu haka suna general hospital.
“innalillahi wa’inna’illaihirraji’un” innarmu tafad’a tana mik’ewa zumbur, ga wata zufa Na karyo mata, batasan tayo waje tana kwalama matan gidan kiraba.
Kowacce tafito jiki Na 6ari, azatonsu wata acikinmu aka sako, musamman ma ni dasuke kiran aurena auren d’ori d’afini.
tana hawaye ta sanar musu da abinda yafaru. Nanfa gidan ya rikice, yara suka garzaya suka sanarma innaro.
Ko takalmi babu haka tanufo gidanmu tana shar6ar majinar kuka da kiran tashiga uku, Awwalu zai mutu ya barta. wannan kwakwazon natane ya ankarar da jama’ar anguwarmu.

A rikice baba k’arami da Dady suka nufi asibitin, Dan matan gidanmu sun kira suma sun sanar musu abinda ke faruwa.
Kafin wani lokaci jama’ar gidanmu sun gama cika asibitin, sai koke-koke sukeyi suna son ganin Abba, amma an hanasu, Dan bak’aramin buguwa yayiba.

______________________________

Alhmdllh natashi jikina da sauk’i, Dan kuwa babu zazza6in da ciwon jikin, hakama ciwon kan babu, bai tadani ba saida yadawo massalaci, lokacin har gari yafara haske ma.
Na idar da salla ina zaune ina addu’a yafito daga bathroom, da alama wanka yayo, Dan sanye yake da bathrobe sky blue, yana rik’e da k’aramin towel a hannu yana goge ruwan fuskarsa.
Kallo d’aya namasa Na d’auke kaina, shikoma bai kalleni ba ya wuce gaban mirror ya zauna, saida yafara shafa mai sannan Na tsinkayo muryarsa yana fad’in “ya jikin naki?”.
Yanda yay maganar a cinkushe yasakani d’agowa Na kallesa, ganin hidimarsa kawai yakeyi saina d’auke kaina, nace “da sauk’i”.
Bai sake magana ba, harya kammala yabar gaban mirror d’in, wajen wardrobe yakoma, nidai kaina Na k’asa bansan hidimar dayakeba.
Koda ya d’auki kayan saiya koma bayi ya saka tamkar yanda ya saba, ya fito ya iskeni ina gyaran gadon, ta gefen ido Na kallesa, yayi k’yau cikin wani bak’in lallausan yadi, Wanda akaima ado da jan style, nakula yanason kayan al’adarsa, dukda baitashi ya girma cikin k’abilar tasaba, sock’s ya d’akko da bak’ak’en takalma sau ciki ya zauna saman sofa, yana sakawa yana magana, “uhm Zanyi wata ‘yar tafiya Na kwana 2 kacal, mikike da buk’ata?”.
Tsayawa nayi daga gyaran gadon danake, Na d’ago ina kallonsa kawai, jin nayi shiru kuma yanajin alamun ana kallonsa ya d’ago shima. Ido muka had’a saina janye nawa.
“kallon fa?”. ‘yafad’a yana k’ok’arin saka d’ayan takalmin’.
Cikin la6e baki nace “yoni yalla6ai mizan kalla anan?”.
Banza yamin, saida yagama saka takalminsa sannan yamik’e tsaye yana fad’in “hakanefa, Ashe babu abin kallo anan”.
Nima shiru namasa ban tankaba, ya saka laptop d’insa dawasu ‘yan abubuwa a k’aramar briefcase d’insa, ya zuge zip d’in yana fad’in “ki shirya muje kiga likita kafin Na wuce”.
Da sauri nace “a’a kaje abinka, Indai nice Na warke”.
Idanu ya tsuramin alamun tuhuma, nikuma nak’i kallonsa, ya girgiza kansa kawai sannan ya ajiye min kud’i akan gadon, “ni Na tafi, a yafi juna”.
‘Dagowa nayi ina kallonsa da mamakin kalmarsa ta k’arshe, bansan sanda bakina ya su6uce nace “ALLAH ya tsare hanya, ya dawo dakai la fi ya”. ‘na k’are maganar da d’aid’aya’.
Cak ya tsaya abakin k’ofar, saboda yanda addu’ar tawa tazo masa a bazata, dan bai tunanin hakan daga gareniba, yajuyo a hankali tamkar maison gaskata abinda yaji, kallona yayi muka had’a ido, amamakina saiya sakarmin wani tsadajjen murmushi, irin Wanda zan iya rantsuwa ban ta6a gani daga garesaba. Baice komaiba yajuya yafice da sauri.
Yabar zuciyata da luguden dabansan dalilinsa ba. Wata ajiyar zuciya Na sauke, tare da zama jagwaf a bakin gadon na dafe kaina da mamakin murmushin da Galadima yamin.

Bai dad’eba sosai a hospital yamusu sallama yafito, dama tun a daren jiya ya sanar musu zaiyi tafiya, ga jirgi kuma ya kusa tashi. yafito sunata binsa da addu’oin dawowa lafiya, yayinda shikuma yake amsawa cikeda murmushi. Saida yafara xuwa sukayi magana da doctors d’in dake kula da Abie, yaji babu wata Matsala sannan yafito.
Dama Khumar ne ya kawoshi, Dan haka yanzu ma shine yatafi kaisa airport d’in. Zaman da baifi 30minutes ba jirginsu yataso zuwa 9ja.
Zaune yake kusa da window, yayinda wata matashiyar budurwa ke gefensa, tunda tazo da nufin zama yawani kuma had’e fuska, a d’age ma ya amsa mata sallamar data masa, yasaka belt tareda bud’e Newspaper yahau karatu.
Budurwar sai satar kallonsa takeyi, tanason masa magana amma bataga fuska ba. Sai da akazo tambayar misuke buk’ata?, yace Coffee.
Itama da sauri tace Coffee d’in. juyowa yayi ya kalleta, ta sakar masa wani tsadajjen murmushi.
Janye idonsa yayi yanajan tsaki a zuciyarsa. duk yanda taso yamata magana ko sau d’ayane Galadima yak’i yayi, ya had’e gabas da yamma abinsa. Haka kawai sai tunanin tahowarsu da Munaya ya fad’o masa a rai, yatuna yanda tadinga wani dakewa irin itafa ta saba da hawan jirgi. jaridar yasaka ya rufe fuskarsa yana murmushi da jinjina jan aji irinnan yarinyar, ita bata yarda aga marenarta ba. ya tuna diramarsu ta daren jiya, wani murmushin yakuma saki…… haka abubuwa da yawa sukaita dawo masa akan Matar tasa ta auren Contract. wani abun nata abin dariya, wani Na mamaki, ita bata yardaba adole big girl Ce.
Koda suka sauka baiko kalli inda yarinyar nan takeba, da sauri tabi bayansa tana fad’in “haba yayana babu sallama? Ai kodan darajar makwaftaka mayi sallama”.
Yana sauka daga step d’in k’arshe Na jirgin ya juyo ya kalleta, aransa yace yarinya sai nacin jaraba. Ta kuma fad’in “kozaka bani Number ka muke zuminci”.
Yanzu kam wata uwar harara ya zuba mata kafin yay gaba abinsa. tsaye tayi tana binsa da kallo, jitake kamar ta tsala ihu, harma tafara tunanin ko shid’in kurmane?. cikin matuk’ar mamaki ta hango wasu masu kaya iri d’aya sunyo wajensa, daka gansu kaga jama’ar masarauta. da k’yar ta had’e yawun bakinta, kenan shid’in jinin sarautane?. Batada mai bata wannan amsar, Dan haka taci gaba dabin motocin Galadima da kallo har suka fice abinsu.
Driver d’in da yazo d’aukarta yak’araso inda take, gaisheta yafarayi kafin ya k’ar6i handbag d’in hannunta. amota take tambayarsa koya San wanene Wanda masu kaya iri d’aya sukazo d’auka?.
Yace, “ma’am Galadima Sameer kenan, d’an tsohon Sarki, kusan 1month kenan da aurensa ai”.
Hararsa tayi cikin daka tsawa tace “ina ruwana dawani aurensa, bashi Na tambayeka ba. Punishment d’inka Na fad’amin abinda ban tambayeka ba shine ka nemomin number sa”.
“ALLAH ya huci zuciyarki Ma’am”.
Banza tamasa, yayinda shikuma zufa keta karyo masa dukda AC n dake motar, tunaninsa a ina shikuma zai Samo number babban mutum irin Galadima Sameer shikam? yasan idan bai samo d’inba yashiga uku, dan yarinyar nan ba mutunci gareta ba.

*********************

Tun bayan tafiyar Galadima saina zama wata sukuku, abin mamaki saigani da kewar Galadima wai, gaba d’aya yinin sai nayishi wani babu dad’i, ga gabana yanata yawan fad’uwa, jinake kamar wani al’amari yana shirin faruwa da rayuwata.
Sauban ma sarkin tsokana kasa shiru yayi saida yay magana.
Bayan ya dawo school sai muka tafi asibiti, tunda Na gaida Abie da Momma da Aunty Mimi saina koma gefe nayi shiru abina, ciwon jikine kawai ke nuk’urk’usata, dan ga6o6ina masifar ciwo sukemin, narasa wannan dalili? zazza6inma banaji yanzun, ga yawan fad’uwar gaban dana yini inayi, sai kasa kunne nake naji ko Galadima zai kira wani a ‘yan uwansa yace ya sauka lafiya, dan zuciyata tafi karkata da fargaba a kansa.
Shirun da Sauban yaga nayi shine ya kalleni yana dariya k’asa-k’asa. “Aunty gimbiyarmu har kin fara kewar Hubbin naki halan?”.
Idanu nad’an waro ina kallonsa, ganin su Momma Na dariya saina 6oye face d’ina cikin veil d’ina ina fad’in “kai yaa Sauban ALLAH a’a”.
Dariya suka kuma sanyamin, Abie nata murmushi shidai, Momma tace, “A’a Mrs Galadima kifad’a gaskiya dai?”.
Kunya takuma lullu6eni, saina k’udundune kaina gaba d’ayama a gyalen saboda. ina k’aunar wannan family sosai a raina, saboda nima suna nunamin tsantsar k’auna, ko yau nabar cikinsu auren contract d’inmu yak’are bazan manta da alkairinsuba a gareni.
Haka nagama shirin barci Na kwanta a gadonsa ina shak’ar k’amshin turarensa danakejin dad’insa fiye da da. nadad’e ina juye-juye banyi barciba saboda damuwace cinkushe da raina, ga zazza6i mai zafi ya rufeni, bansan ina Galadima yajeba balle nayi tunanin samun number na kirashi, Na gwada number shi ta nan India tak’i wucewa, dama a wayar Samha Na d’auki number bama ta saniba, yau babu mai kulawa dani, sainaji wata kewar innarmu da Munubiyata sun dawomin sabo fil a zuciya. Sai da dare yakusa rabawa kafin barci mai nauyi ya d’aukeni.

_____ .?. _____ .?. _____

Har yamma ba’abari kowa yaga Abba ba, ‘yan gidanmu sunci kuka harsun gode ALLAH, Su Munubiya da dukkan yaran gidanmu Na ma’auri tuni labari ya iso musu, kuma duk sun tattara a asibitin suma.
Doctor d’in dayake kan Abbanmu ne yafito yana basu hak’uri akan suje gida hakanan, dan gaskiya baza’a bari suga Abba ba a yau.
Sabon kukane yatashi, musamman ga innaro, idan ka kalleta dolene tabaka tausayi wlhy, yau babu jarabarnan da rashin mutunci, kuka take da fad’in Auwalu karya tafi ya barta……….
Sambatunta yakuma raunana zukatan mutane da yawa a wajen.
Munubiya tayi yunk’urin kirana amma network yahana, da Yaa marwan yakula da hakan kuma ya hanata, yace karta sake ta sanarmin yanzu. Wannan dalilin yahana a sanar min d’in.
Kowa zuciya babu dad’i suka tattara suka tattafi gida, dady da baba k’arami, yaa hameed yaa shafi’u da ya Naseer aka bari a asibitin zasu kwana.
Ranar duk Wanda yasan gidanmu yasan babu lafiya, Dan gidan yayi tsitt, kowa tashi ta isheshi a zuciya, barcima k’alilanne daga cikinsu suka yisa.

___________________________

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply