Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 29


Raina Kama Book 2 Page 29
Viral

Book 2~ ????2?9?

…………..Harmun kwanta zuciyata ta kasa samun nutsuwa, inason naje naga halin da yake ciki, Dan koda su Nuren suka wuce ban komaba, sakkowa nai daga kan gadon, laraba dake a tsakar d’akin kan katifa tace, “ranki ya dad’e lafiya kuwa?”.
Banason ta kalli abun da wata manufa, dan haka nad’an murmusa, “uhmm iya inason duba Abbansu ne, ban saniba koyasha maganinsa kafin ya kwanta”.
“eh lallai hakan yanada k’yau, badan ma jego ba ai bai kamata ya kwana shi d’ayaba”.
“aiba shi kad’ai baneba iya, Sauban ne zai tare dashi ”.
A to hakan yayi.

Bance komaiba Na kar6i gyale wajen Samha Na saka na fita.
Masarautar tayi tsit, da alama kowa yasamu nutsuwa a sashensa, ban tsaya knocking ba na shige kawai, a falo na iske Sauban zaune yana kallon ball, cikin tsokanar da ya iya yace, aunty gimbiya kin kasa barcine?”.
Nayi murmushi, “yaa Sauban matarka taga ta kanta wlhy”.
Dariya yayi kawai, nikuma na wuce abina.
Saida nayi sallama kusan uku banji an amsaba, saina shige kawai. Zaune na iskeshi a bakin gado ya jingina da fuskar gado, hannunsa d’auke da Qur’an yana karatu a hankali, idonsa cikin medical glasses, gakuma system a gefe itama a kunne. naji dad’in yanda na sameshi, Addu’a da karatun Qur’an babban jigone dake wanke zuciya da damuwar d’an Adam (duk lokacin da ranki ya 6aci d’auki Qur’an ki karanta koki saurara, wlhy zakuji sassauci mai yawa).
Har zan juya na fita sai naji yay gyaran murya, juyowa nayi na kallesa, har yanzu dai karatunsa ya keyi. na dawo na zauna a bakin gadon ta d’ayan gefen, shikuma ya cigaba da karatunsa, kusan mintuna 6 kafin ya rufe Qur’an d’in ya ajiye, ya cire medical glasses d’insa shima ya ajiye yana kallona, ko kad’an fuskarnan babu walwala, nuni yamin da inzo.
Ban musaba na tashi nadawo 6angaren inda yake, zama nai d’an nesa dashi kad’an.
Ya lashe le6ensa da cizarsa kad’an yana hard’e hannayensa a k’irji.
Muryata can k’asan mak’oshi nace, “yaya jikin?”.
Kansa kawai ya jinjina min cikin lumshe ido, sannan ya motsa baki kamar zaiyi magana saikuma yay shiru, saida yaja wasu seconds sannan yace, “Munaya!?”.
“Na’am”. Na amsa ina kallonsa da janye idon lokaci d’aya saboda ya tsareni da nasa.
Huci yad’an furzar, ya cire hannayensa daga k’irji yana gyara zama, “Nayi nazaci sosai akan maganganun ki na d’azun, nakuma fassarasu aji-aji, na fahimcesu a yanda tawa fahimtar take, so a wannan karon rok’o nake miki na k’arshe akan ki fad’amin abinda kika sani, ni d’an Adam ne, ban isa cewa komai na sanshi a rayuwaba ko na iyashi, sai abinda Ubangiji yaso in sani kawai, Munaya ada ba haka rayuwata takeba, mutumne ni mai yawan raha dason nishad’i, amma daga lokacinda nafara sanin kaina da matsalar mahaifina sai komaina ya canja, nazama mutum mai yawan rashinson magana, nafison kullum na kasance ni kad’ai a kuma ke6antaccen waje” yay murmushin takaici sannan ya cigaba da fad’in “Bawai hakan Na birgeni baneba ko a San raina, saboda Ina shiga k’uncine, amma banida za6in daya wuce hakan. nasha wahalhalu Na rayuwa kala-kala kafin na tsaya da k’afafuna, zuciyata ta bushe namance daga wane tsatso na fito, domin idan kinganni a lokacin da nake karatu da koyan sana’oi bazaki ta6a kawo ni jinin sarauta baneba, ko d’an wani, nayi gwagwarmaya sosai irin wadda d’a Mara gata yakeyi, badan mahaifiyata bata sona bane ta tsaya tsayin daka wajen ganin na horu kona nemi na kaina, hikimarta itace nazama jarumi mai yawan juriya, nakuma kwato mana y’ancinmu a lokacinda ya dace, duk wannan fad’i tashin da kikaga inayi wlhy badan nayi mulki baneba kamar yanda su suke tunani, Burina kawai nasan miyasa aka durk’usarmin da mahaifi? Tabbas ni jinin sarautane gaba da baya, kuma yana yawo a cikin jinina, amma rashin kwanciyar hankalin dake cikin sarauta baya birgeni, kallon kitse kawai akema rogo, ayau inason Kituna kema kin haifi yaranda sun rigada sun shigo cikin wannan harmutsi, tunda tazama jininsu, ki fad’amin kodan mu gyaramusu gobensu su rayu cikin salama koda bama numfashine, nasan hakanan bazakima Harun abinda kikai masa d’azunba saboda son zuciya kawai, please miyasa kika hanashi d’aukar Abdurraheem ne? Miyasa kikak’i barina na fad’a masa gaskiyar abinda ya faru?”.

Shiru nayi nakasa cewa komai, sai faman had’iye abinda ya tsayamin a mak’oshi nakeyi, Dan bansan yanda zai kalli abunba koya fahimceshi, babu Abu mafi saka rud’u irin cin amanar makusanci, gashi dai a Ransa shifa ba k’aunarka yakeba, amma kulum yafi kowa kusanci da kai, da Nuna girmama alak’ar tsakaninku. (ALLAH ka Shiga tsakaninmu da duk wani Wanda yake tare damu a matsayin fuka biyu, Dan yanzu abinda yafi komai yawaita kenan a rayuwar d’an adam???).
Cikin katsemun tunani Yace, “please my friend say Something mana”.
Kaina na jinjina masa, cikin nutsuwa nafara masa bayani, Dan yau nayi alk’awarin sanar masa komai, koda zai samu wani haske akan lamarin, shima yasamu nutsuwa a rayuwarsa.

“Tabbas kamar yanda kake zargi aiki nakema wani, saidai fahimtar wanene d’in shine mai wahala, na fad’a maka tun farko a dalilin bak’on Abbanmu naji wani yankin matsalasa da bai ta6a sanarma waniba a ahalinsa, a lokacin da wancan abin yafaru Abba yak’i fad’ama kowa dalilin fishinsa a kanmu, dakuma abinda muka masa, hakanne yasaka innarmu zuwa tasamu baba mai kanwa abokin kakanmu na k’ut da k’ut ta sanar masa fushin da mahaifinmu keyi damu, ankuma bashi hak’uri yak’i sauraren kowa, gashi ba dad’in zama takejiba cikin matan gidanmu, wannan Abu daya faru sai sukejin dad’i damata arashi da habaici, harma damu kanmu. baba mai kanwa yace taje zai masa magana, bayannan bamusan misuka tattaunaba. Sai da bayan komai ya lafa harma mun fara karatu sai sanata halluru ya buk’aci abbanmu yabama y’ay’ansa biyu auren yara cikin yaransa, sunzo gidanmu har suka nuna mune za6insu, a lokacin tabbas naji a raina Sa’eed yamin sosai a rai…..”
Galadima ya tsuk’e fuska yana taune lips dajan k’aramin tsaki.
‘Dagowa nayi nad’an kallesa, amma saiya basar tamkar bashine yayiba, nima sharewa nayi na cigaba, “bamusan miya faruba sukace Zarah da siyama sukeso, wannan Abu ya 6atama Abbanmu rai, dan aganinsa anyi wani abune domin k’untatama mahaifiyarmu, hakkane yasashi zuwa ya sanarma Baba mai kanwa, dama duk dai wani Abu dazai taso gidanmu shine ake sanarmawa, yayi sasanci koya tsawatar, koda kuwa innro ce. bayan Abbanmu yaje da kwana d’aya, sai innarmu ta aikemu wajensa muka kaimasa goro da y’ar sayayyar da takan masa lokaci-lokaci, saboda yamusu hallaci a rayuwa a yanda take bamu labari, shiyyasa a kullum take d’aukarsa uba”.
Mun iske baba mai kanwa a d’akinsa na zaure kamar ko yaushe, muka gaidashi cikin girmamawa da tsokanarsa a matsayinsa na kaka, shima ya tsokanemu tareda sakamana albarka kamar yanda ya saba, saiya murmusa tareda gyaran murya, hakanne yasaka muka nutsu dan fahimtar magana mai muhimmanci zaiyi, ya nisa cikin dattako na tsufa ya fara fad’in___”.

_“yarana kuyi hak’uri da damuwar da kuka tsinci kanku a ciki, wadda tunkafin Ku mahaifiyarku a ciki take, amma nasan watan watarana kuda ita duksai kunci ribar wannan hak’urin, karkuyi bak’inciki akan hanaku wannan auren da akayi na y’ay’an halluru, dama can sud’in ba mazajenku baneba, hasalima aurensu ba alkairi baneba”._.
“A razane duk muka kallesa baki bud’e”.
Yayi murmushinsu na manya, _“abin ya baku mamaki ko? Humm ba abin mamaki baneba, yau zan fad’a muku wani sirrin dabaku saniba, domin ina hango wani tarin alkairi tattare da rayuwarku, inakuma ji ajikina kune wad’anda zaku fidda mahaifinku daga wata sark’ak’iya daya Shiga a dalilin taimako tun kafin a haifeku. Alhaji halluru da wata manufa ya nema ma y’ay’ansa auren d’iyan mahaifinku, amma Shifa na fuskanci bai fahimci hakanba, sabo da ya aminta da amintar dake tsakaninsu ta tsawon shekaru. Alhaji halluru yanason shiga jikin mahaifinku ne sosai danya kar6ama iyayen gidansa wani sirri dake hannun Auwalu, ina k’yautata zaton shine kukaji wani Abu a ciki, shi kansa Auwalu baisan minene a ciki ba, domin kuwa bashi akai amana ya Isar dashi ga Wanda yadace, kuma baita6a yunk’urin ya duba ba ya barsa a yanda aka bashi. Kuyi hak’uri akwai wasu k’alubale dake tunkaro rayuwarku, kuma yanada tsananin sark’ak’iya, saidai insha ALLAH zan baku dikkan gudunmawa inhar ALLAH yabani tsawon ran kaiwa wannan lokacin, Ku dage da yawan sadaka kudai da mik’a lamuranku ga ALLAH mai kowa da da sirrin komai, ALLAH kuma ya cigaba da tsareku.”_
“duk cikin tsantsar damuwa muka amsa masa da amin, haka muka baro gidan jikinmu duk a sanyaye, dan har innarmu tata bincikarmu a lokacin, sai muka fake da ciwon mara. sati biyu da faruwar wannan lamari sai Munubiya tafara min k’orafin yawaita mafarkin wani bawan ALLAH, kullum takan gansa ne a cikin dokar daji zagaye da wasu irin halittu masu ban tsoro suna kaimasa hari zasu halakashi, yakanyi k’ok’arin kare kansa amma saiya gaza, idan yanemi taimakonta kuma bata zuwa, saboda tsoro suke bata. Duk sanda tafad’amin wannan mafarki sainace bata addu’a ne, shaid’anune kawai. haka taita jera wannan mafarki kullum dare, kuma da gari ya waye bazata fasa fad’aminba, tundai abin na damunmu har muka watsar muka cigaba da harkokinmu. Ranar kuma sai nima nayi mafarkin makamancin na Munubiya, saidai nikuma na shige ina taya wannan mutumin kare kansa ga wad’annan halittun kamar yanda ya buk’ata, na jigata sosai dan harnatashi jikina duk yayi week, nima ban 6oyema Munubiya komaiba na sanar mata, abin yabata mamaki, kuma tundaga sannan nima na cigaba da mafarkin, kullum kuma ina taimakon wannan mutumin dako fuskarsa ban ta6a ganiba, itako Munubiya takan cemin saidai ta tsaya kallonsa daga nesa yana bata tausayi, kuma yana shan nuna mata tazo ta taimakesa, amma saitak’i ta nok’e kafad’a. nikam a nawa mafarkin duk lokacin da ya nuna na taimakesa nakanje nashiga muyita fama da wad’annan halittu, ita Munubiya tana ganin fuskarsa, amma da zaran ta tashi, saita manta, niko ban ta6a ganin fuskarsa ba ko sau d’aya. Muna cikin halin wannan mafarki ne aka shiga bikin salla, tabbas randa muka had’u dakai a asibiti sainaita jin haushinka akan dalilin da ni kaina nasan bai isa daliliba, (dan kawai ina maka kallon mai girman kai bai kamata naji haushinka ba, tunda bawai hud’ace ta had’amuba, banikuma da tabbacin akanka abbanmu ke a had’ari), saidai had’uwarmu ta filin idi tasha banban data asibiti, dan a filin idi tsoro-tsoro mai gauraye da mamakinka ne suka zaunemin a zuciya, bayan kabani wayarka kabar wajen inata mamaki da juyata da tambayar kaina kaid’in wanene? Sai wata murya ta bani amsa da cewar *Galadima!* saidai koda na waigo banga kowaba sai alamar gittawar mutum mai jajayen kaya, na dad’e soaai wannan al’amiri bai bar rainaba, a haka muka shiga shagalin bikin y’an gidanmu, harda kuma su siyama, anan ne muka had’u da Fu’ad, harga ALLAH bansan wanene Fu’ad ba, bankuma San daga wace tawagar ango ya fitoba, amma amamakin kaina lokaci d’aya na aminta dashi, dukda kasancewata mutum mai masifar tsarta, cikin kwana d’aya kacal na saki jiki dashi, dukda ban amsa masa Cewar na kar6i soyayyarsa ba, daga ni harsu Ayusher bansan miya shiga kanmu ba muka yarda ya kaimu birnin gayu plaza ba, dukda kowannenmu ransa akwai fargaba, musamman ni danakeji kamar akwai wani gagarumin Abu dake tunkaro rayuwata. hardai muka shiga muka fito abinda ya faru ya faru a tsorace nake. fitowar wannan jarida a washegari yasaka dukkan wani ahalinmu a rud’ani, Wanda bansan yazan musalta makashi ka fahimtaba, lokaci d’aya da akazo bincikar wacece a cikinmu na amsa, dan jinai bazan iya bari Munubiya ta amsa laifinba, saboda tanada hak’uri, amma tanada tsauri Wanda nikad’ai da mahaifiyarmu muka San wannan tsaurin nata, dan sometimes takanyi mugunta amma tayi tamkar ba ita baceba, kai tsayema sai’a zargeni ita ba’ayi tunanin zata iyaba….”
Galadima ya katseta da fad’in, “kina nufin bakece kika kusa fad’iwaba a plaza?”.
Nad’an murmusa ina gyaran mayafina dake zamowa saboda kayan sunada santsi, “tabbas bani baceba yalla6ai, Munubiya ce, tausayi. Y’ar uwata yasani kar6ar laifin. Bayan wannan Abu ya faru nanma kowa yata fushi damu musamman Abbanmu, haryace saina nemo miji cikin 2weeks kacal, wannan ya d’agamin hankali, dan nikam kaf samarina babu Wanda yamin, amma sainaga kamar zan iya auren Fu’ad, wannan dalilin yasani kiransa bisa shawarar su feena, amma saiya toshe sukkan hanyar dazamu iya yin magana. bansan yazan misalta maka halin dana tsinci kaina a tsakaninba, naji natsani Fu’ad matuk’a, a wannan time d’inma na cigaba da wancan mafarkin, amma yazomin dawani sabon salo, sannan ita kuma Munubiya ta daina, mafarkin ya canjane zuwa salon da mutumin kanyi yunk’urin ta6ani, amma nakan hanashi damar hakan ta hanyar ja baya da masa gargad’i, shikuma saiya ringa rok’ona da cemin karna masa haka, ni fitilarsa ce. Har sannan kuma still bana ganin fuskarsa, abubuwa da yawa sun had’u sun dagulemin, dukna fige na fice hayyacina. A lokacin da baba mai kanwa yaje dubani asibiti bayan maganar aurenmu da haidar ta rushe saiyake magana cikin murmushi, k’asa-k’asa kuma ta yanda wani bazai jimu ba”.
_“Ki kwantar da hankalinki Hussaina, har yanzu dai mijinki bai kai ga zuwaba, kuma bayan wannan ko 10 zasu k’ara zuwa saisun barki, dan akwai k’alubale a gabanki kafin kisamu nutsatstsiyar rayuwa._”
“Da mamaki na kallesa, amma saiyak’i bani damar neman k’arin bayanin komai a wajemsa. Bayan na warke nadawo gida kuka saka aka saceni kaida Muftahu, na koma gida mangariba ta rufa a ranar, ashe wai baba mai kanwa yaga sanda na shiga gida a firgice, sai’a washe gari ya aiko a kirani, innarmu da Munubiya sunyi mamakin kiran, dan cayay Hussaina taje, (shi dama baya kiranmu Munubiya da Munaya, sai Hassana da Hussaina). Haka na saka hijjab naje, a yau baiyi wasan daya sabayi da niba, kai tsaye yafara maganarsa”.
_“Hussaina jiya daga ina kika dawo a firgice?”._
“A tsorace na kallesa, dan lallai tsohonnan yafara bani tsoro, dama tun muna yara mukanji ana cewa tsoronsa akeji, saidai bamusan manufar tsoronba, murmushi yayi yana gyara zama da cigaba da gyaran wasu takarsu Dana tarar yanayi, yace___”.
_“karkiji tsoro, nimai taimakonki ne gwargwadon abinda ALLAH yabani ikon sani, dan haka ki fad’amin gaskiya_”.
“dak’yar na iya had’iye yawu, sannan na fad’a masa abinda yafaru tsakanina daku. Murmuahi yay mai matuk’ar sauti, wanda ya bayyana fararen hak’oransa da basu wuce goma sha ba da suka rage, wad’anda a kullum zaka sameshi da ashuwaki yana d’abbak’a sunna, yace___”.
_“Hussaina ni bazance ki amince ko karki aminceba, saidai nabaki dama kije ki duk’ufa rok’on ALLAH, a cikin kwana ki biyu rak ALLAH zai nuna miki mafita da abinda zai zama alkairi a gareki, sannan karki sanarma Hasaanar ki, danna kula bazata amince ba tacikin sauk’i, tashi kije”._
“A wannan ranarma haka baba mai kanwa ya sakani cikin rud’ani, nazo dukna hana kaina nutsuwa da kwanciyar hankali, saidai nabi shawararsa ta mik’a kukana ga Ubangijin al’arshi, dan shine gatana kuma fitilata, a kwana na biyu kuwa saiga dalilin dayasani amincewa da buk’atarka ya faru, na amince maka badan hankali na ya kwantaba. tunda kuma lokacin baba mai kanwa bai kuma min maganar data shafi auren ba, harma na d’auka duk mafarki nayi, har maganar da mukayi d’in dakai. Saida ana gobe d’aurin aurenmu da safe na fita yin wani Abu na gamu da baba mai kanwa, shine yace na biyoshi gida. Mun Isa gida a d’akin zaurensa, yabani wasu abubuwa dabansan mineneba na sha, sannan yabani turare kashi biyu, yace ni 1 Munubiya 1, yace____”
_“Hussaina kimin wata alfarma mana?”._
“A sanyaye nace kabani Umarni akwai baba. Yay murmushi da fad’in___”.
_“ALLAH ya yimiki Albarka Hussaina, ina tausayinki ta wani fannin, ta wani fannin kuma murna nake tayaki, duk abinda nake hasashe a kanki nasan zaki iya, dan kinfi y’ar uwarki wayo, ni dake zamu had’a kaine wajen fidda mahaifinku a sark’ak’iya, su a gangancinsu sun tozarta kune domin tunzura mahaifinku da karyar masa da zuciya, amma basusan Ubangiji mai hikima baneba, yafisu sanin akan abinda su bai basu damar saniba, kiyi hak’uri inata miki magana a cirkud’e, zaki fahimci komai anan gaba kema, alfarmar da zakimin shine dukkan abinda kikaci karo dashi a rayuwar aurenki ki sanar min shi, insha ALLAH Zan miki fashin bak’i gwargwadon abinda na fahimtar nikuma, maganar zaman aurenku da yanda kuka ginashi kuma ya rage naku bayan warwarewar komai, wannan ba hurumina baneba, tashi kije, daga nan dai zamu dinga tayaku da du’ai”._
“Dukda banida tabbacin mijin dazan aura wannan magana tashi tamin nauyi da wahalar fasaara, da y’an gidanku suka kai lefena kuma saina kuma tsintar kaina a rud’ani da firgici, ban kuma fita daga wannan firgicinba har aka kawoni wannan masarautar. Saka pills da Muftahu yayi mana shine k’alubale na farko dana fara cin karo dashi Wanda nake k’yautata zaton baba mai kanwa ya hangomin, hakanne kuma ya sakani tada hankali nace nafasa auren, dan a zatona kun had’a bakine da Muftahu, amma sai maganar tafiya India ta datse dukkan hanzarina, ko kad’an banyi yunk’urin sanarma baba mai kanwa wannan batunba, dan aganina baya cikin abinda shima zaiso Sani. Idan baka mantaba a lokacin da ka kaini sallama gida da kuma gidansu Munubiya ka barni a can?”.
Kansa ya jinjina mata idonsa a lumahe ya jingina da gado, kai kace ba saurarenna yakeba barci yakeyi.
Ajiyar zuciya na sauke, na cigaba da fad’in “Aunty Salamah tazo gidan ta sameni ai, saboda Munubiya ta sanar mata zaka tafi dani, wannan itace damar farko dana samu na rok’onta yimin bincike akan Muftahu da Saleem yaronka na plaza, (abinda yasa Saleem yashiga Layin zargina saboda randa abinnan ya faru bayan fitowarmu shikuma naga ya fito daga tsakanin wasu motoci a firgice, dayake a time d’in bamusan mizai faruba ban kawo komai a rainaba sai washe gari, danayi bincike a kansa saina gane yaronkane na shago kuma amintacce) daga ita har Munubiya a lokacin basusan dalilina nason amin bincikenba, saidaga baya Munubiya ta fiskanci komai, dayake tanada kaifin basira, amma batasan tsakanina da baba mai kanwa ba. mun tafi India nabar Aunty salamah da wannan aikin”.
Knocking k’ofa da akayine ya saka Munaya yin shiru bata cigaba ba, na kalli Galadima da har yanzu idonsa a lumshe, batareda ya bud’eba yabada izinin shigowa, yasan dai bazai wuce Sauban ba.
Samha ce ta shigo, ta risina tana gaidashi, sannan tace, “Aunty Amaturrahman ta tashi itada Abduraheem”.
Yunk’urawa nayi zan mik’e galadima ya katseni ta hanyar fad’in “jeki kawosu”.
Na kallesa da mamaki, yayinda Samha ta fice abinta, “amma yalla6ai darefa yayi, mubari mu k’arasa zuwa gobe mana?”.
“uhm-uhm”. Kawai ya fad’a.
Shiru nayi nakasa cewa uffan, har Samha da Sauban suka shigo d’auke da yaran duka uku, kar6ar Abdurraheem nayi, dan yaron tausayi yake bani saboda rashin kuzarinsa (karku manta har Yanzu Munaya batasan yaron yanada irin ciwon mahaifinsa ba), su kuma Sauran ya kar6esu. Sauban da Samha suka fice sudai suna tunanin wannan zaman nasu, komi suke tattaunawa oho.
Bayan fitarsu a cikin gyale na fara shayar da yaron, Galadima dai baice dani uffanba, sai kallon yaransa kawai yakeyi, na cigaba da fad’in “Abu na biyu dana fara cin karo dashi shine ganin Abie a halin daya tsinci kansa, wannan lamari ya d’aga hankali na, amma a lokacin banida wayar kiran baba mai kanwa na sanar masa, ina tsoron na saka a wayarka kuma ka gano wataran, sai kuma tarihin masarautar nan da Momma ta bani…….”
Cikeda mamaki Galadima ya kalleta, dak’yar ya bud’e baki cikin yamutse fuska yace, “Momma!?”.
Nace, “eh lallai Momma da kanta, dukkan rayuwar dakasha ta gwagwarmaya ta sanar min, tundaga yarinta zuwa girmanka, ta sanarmin hakanne danna lura da abinda ban saniba a masarautar, kar wani yayi amfani dani wajen cutar dakai. Bayan nan babu dad’ewa kabani waya, daga nan nasamu damar sanarma baba mai kanwa sirrinan guda biyu, ciwon Abie da tarinku. shine yabani dukkan addu’oin da maganin daza’a nema arink’ama Abie, kuma Alhmdllh munakan ganin haske. daga nan kuma na cigaba da samun haske game da dukkan Motsin Muftahu, amma kuma babu wani abinda bai daceba ko cin amana tattare dashi, damukaga mun shiga kokwanto saimuka saka Sarkin Mota da Saleem suka sace manashi a randa kaje d’akkomu a airport ni da Sauban lokacin da Abba yay accident ”.
“ya salam! Kina nufin kece?”.
Murmushi na masa, nace, “kwarai nice, hakan shine kawai mafita agareka damu kanmu, dan satar nashi ya zame mana haske, aunty salamah taje masa a amatsayin d’aya daga cikin matan Abie, ta hakanne kuma muka ji sunan Harun a bakinsa. daga nan muka sakama Harun ayar tambaya, su Ameer suka cigaba da bibiyar Harun d’in, kayi hak’uri ka gafarceni da abinda zan fad’a yalla6ai”. ‘nai maganar ina kwantar da Abdurraheem na d’auki Amaturrahman dake cinyarsa, itama na fara shayar da ita.
“ki fad’i komi ke bakinki, na shirya kar6arsa da makamin HAK’URI”.
Murmushi nayi cikin nisawa, “yalla6ai akwai sirrin dabaka saniba Wanda ya banbanta Muftahu da Harun, Muftahu shine masoyinka na gaskiya, Harun kuwa akwai manufar ra6arka tattare dashi, yasan kuma komai game da satar yarannan, akwai dalililai masu yawan gaske dazan iya kare kaina dasu, amma nabaka dama kayi wannan binciken da kanka. Sannan k’arin bayanin dazan maka shine, mak’iyane zagaye dakai, sannan kowanne akwai manufar sa a kanka, abinda yasa suka taru maka da yawa akwai k’iyayyar mahaifanka data dawo kanka a yanzu, wasu saboda tsoron ta6argazar dasuka aikatane basason kayi mulki ka yak’esu, wasu y’ay’ansu sukemawa, wasu iyayensu ne, wasu kuwa kansune, dukkuma akan inhar kahau mulki zaka iya canja komai da hukunta kowane ya sakasu wannan k’iyayyar a gareka, a yanzu dai kanada Avedance guda hud’u zuwa biyar a hannu, na farko sune wad’anda ka kama da yaran nan, yakamata kasan wanene ya saka su kafin kasan dalilin sasun, na biyu Harun, yakamata kasan miyasa yake tad’eka bayan ka yarda dashi Yakuma San airrinka, na Uku shine Saleem, dolene a wannan karon kasan wanene ya sakashi aikin tsaida CCTV cameras a waccan ranar, na hud’u shine SD minene had’insa da mahaifina, na biyar shine Fu’ad wanene ya sakashi kaimu birnin gayu a waccan ranar, sai Malam saminu driver Alhaji balala dan akwai abinda ya Sani tabbas, hakama farhat ku sake bata tsaro sosai, dan mahaifinta zai kawo kansa gareka cikin sauk’i saboda k’aunar dasuke mata, Sauran kuma zuwa nan gaba zan baka haske a kansu, wad’annan dai ka gaggauta sanin abinda suka Sani a cikin kwanaki biyunnan kacal, dan mak’iya bazasu zauna kallonka ba suma, sunacan suna had’a kayan yak’i. zanje na kwanta, saboda yakamata zuwa gobe mu fara shirye-shiryen komawa gida bisa al’adar haihuwar Fari, yau Munubiya tana can ma ita”.
Ido kawai ya tsura min yakasa koda motsi, na d’auki Amaturrahman Na Goya, sannan Abdurrahman da Abdurraheem kuma a hannu nayi ficewata. Sauran bayani na k’ok’arin mahaifiyarsa Momma kuwa bazan fad’a masa yanzuba, sai komai ya lafa, saboda suna tattarene da sirrikan dasuka shafeni wad’anda bazan ta6a yarda ya sansuba…………….???

 

*Kudai k’ara hak’uri dani, nasan a zak’e kuke da sonjin Galadima ya fara caskale, komai a sannu-sannu ne, dama ba tufk’ar keda wahala ba warwarar, babu abinda yakai k’arshen Novel da saka ciwonkai irin k’arshe, musamman ma mai sark’ak’iya, idan kuka cigaba da hak’urin bina kamar yaune komai zai k’are, shiyyasa nakebi daki-daki yanda kuma zaku gamsu cikin sauk’i.*

_lallai Comments naku nasakani nishad’i, musamman addu’oin Ku gareni ni da mahaifina??, harma nakan Gaza sanin yanda zan nuna muku jin dad’ina, amma ina kallon kowa wlhy, saidai idan bana cikin group d’in kuwa, ALLAH yabar zuminci, ina yinku irin Trillion’s d’innan, I love you all wujiga-wujiga wlhy????????????????????????????????????????????_.

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*??????
*_typing??_*

?? *_HASKE WRITERS ASSO….._*

*_?RAINA KAMA…..!!?_*
_(Kaga gayya)_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply