Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 28


Raina Kama Book 2 Page 28
Viral

~Book 2~ ????2?8?

…………A yanda Na kula har yanzu bayajin dad’in jikinsa, dan komai a d’an wahalce yakeyinsa, koda ya fiddo kayan daga wardrobe saiya dawo bakin gadon ya zauna ya dafe Kansa, kallonsa nayi cikin damuwa nima, Na cire Abdurraheem Na kwantar, sannan Na mik’e zuwa garesa, durk’usawa nayi Na d’ora hannayena akan gwiwarsa, “yalla6ai lafiya?”.
Shiru yamin kusan minti 1, harna fidda ran samun amsa ma na yunk’ura na mik’e da nufin barin masa d’akinma duka.
Hannuna ya rik’o, na juyo na kallesa, har yanzu yana yanda yake baiko d’ago motsa ba.
Na cije lips ina had’iye kukan dakeson zubomin, rayuwar nan tasa bana sonta wlhy, ni y’ar dangi Ce, nariga natashi gidan yawa, dukda gidanmu bahagon gidane mukanyi hira koyayane, amma shifa magana ma idan bai ra’ayiba wahala take masa, Abu na damunsa a rai amma bazai iya fiddashi yaji sauk’iba, Momma ta had’ani da aiki, a watannin baya kad’an kamar yafara canjawa, amma gashi yakuma birkicewa yanzu, tayaya Momma take tunanin zan iya canja Galadima? murd’ad’d’en mutumne shi mai wahalar sha’ani, ga tsantsar mulki da k’asaita da suka zama jinin jikinsa, s………
Tunanina ya katse lokacin danaji an jawoni, nai firgigit saboda fad’awa danayi jikinsa, shikuma yay baya ya fad’a kan gadon, kad’an ya rage mu danne Amaturrahman, yad’an kauce kad’an yana sauke ajiyar zuciya.
Uffan bai ceminba ya maida idonsa ya lumshe.
Mamakin wannan lamari ya kamani, hannu yasaka ya kwantar da kaina a k’irjinsa yana d’an buga bayana da d’ayan hannun, zanyi magana ya d’ora yatsunsa hannunsa uku na tsakkiya akan bakin alamar nayi shiru. banida za6in daya wuce yin shirun, nabisa yanda yakeso.

Yanayin da zuciyarsa ke bugawa sai yabani tsoro, na saka hannuna na danne wajen sannan na d’ora kaina bisa hannun, ajiyar zuciya yayi yana cizar lips..
Tsawon mintuna 3 muna a haka, har knocking d’in k’ofa akayi amma baiko motsaba bai barni na motsaba, na yunk’ura zan tashi ya maidani.
Munkai mintuna 7 sannan ya zameni ya kwantar ya mik’e zaune, batareda ya kalleni ba ya sauka daga gadon, bathroom ya Shiga, babu dad’ewa ya fito, nidai kallonsa kawai nake da mamaki, Dan fuskarnan amatuk’ar d’aure take tamkar baisan minene dariyaba a rayuwarsa, ya shinfid’a abin salla, domin rama sallolin da suka riskesa yana barci.
6oyayyar ajiyar zuciya na sauke, na tashi zaune idona akan yaran, duk sun koma barci, na tsurama Abdurraheem ido, saboda fitar numfashinsa ta banbanta dana y’an uwansa, tunani nai ko yanayin nasa barcin kenan shikuma, saboda wahalar da suka sha,
d’aukar ledar kayan da mom ta kawo nayi, na fiddasu na saka, ban jira ya idarba na fice abina.
Nayi mamakin da yanzu babu kowa, harsu Munubiya sun tafi, haushi ya kamani kamar zanyi kuka, aidai sa jira na fito mu gaisa ko? hawayen da suka zubomin a kumatu na share, namafi jin haushin Munubiya wlhy.
Sallamar da akeyi na amsa da k’yar, sannan na bada izinin shigowa, cikin bayina ne guda biyu, zubewa k’asa sukayi suna gaisheni.
Cikin girmamawa d’aya tace, “dama ance mu gani idan kin fitone”.
Nace, “Hummm”.

Fahinmatar iya amsar dazan iya basu kenan ya sakasu mik’ewa suka fita, zamewa nai na kwanta cikin kujerar ina cigaba da zirar da hawaye.
Kusan mintuna 5 saiga Samha ta shigo, ta durk’usa gaban kujera tana sharemin hawayena, d’ago ido nayi na kalleta, namata murmushin k’arfin hali ina tashi zaune.
Muryarta da alamun tasha kuka itama tace, “Aunty Uncle Sam na kiranki”.
Kai na jinjina mata kawai, na tashi gaba d’aya na d’auki mayafi muka tafi tare.
Koda mukaje k’ofar falon bata Shigaba, nikad’ai na Shiga ita kuma ta juya ta fice daga sashen gaba d’aya.

A falo na iskeshi cikin doguwar kujera a kwance, ya kifa yaron d’aya a k’irjinsa Wanda nake k’yautata zaton Abdurraheem ne, wayace manne a kunnensa, amma a hankali yake magana koni danake tsaye cikin falon banaji, na kalli abincin da aka jere a tsakar falon ina zama a kujera.
Bai dad’eba ya kammala wayar, idonsa dake jajir har yanzu ya d’ago yad’an kalleni, jijiyar kansa dukta tashi rud’u-rud’u. saida yad’an lumshe idanu kafin ya motsa la66ansa ahankali yace, “kici abinci inji inno”.
Dukda maganar taban haushi haka na danne, wato inji inno ma ba injishi ba ko?. Sakkowa nayi k’asan lallausan carpet d’in, d’aya bayan d’aya na bubbud’e kulolin da kwanikan, a rai na ina tunanin ina zamu kai wanna abincin haka?.
Tashi nayi zuwa ga show glass d’in dake falon, wadda aka jera mugs and glass cups, mug d’aya na d’akko, naje wajen wanke hannu dake a wajen dinning, Wanda babu tebirin cin abincin ba’a sakaba, bansan dalinsa nak’in sakawarba, wanko mug d’in nayi na had’o kayan tea a ciki dake a wajen show glass d’in suma, na zubo ruwan zafi daga dispenser na dawo, yana kwance yanda na barsa, yanzuma garda su lumshe idanu yanata shafa kan yaron zuwa bayansa.
Na kallesa a d’arare Dan yaune karan farko dazan aikata hakan, komi yake buk’ata yakan yi da kansa, ko ruwa wannan inhar bana manta ba bai ta6a cewa na d’auka masaba, sometimes ma sai idan yasaka Samha ko Sauban su masa Abu saini na tashi nayi idan naga rashin dacewar hakan, amma dai dakansa yace Munaya yimin kaza, gaskiya bai ta6aba. muryata na rawa nace, “bismillah”.
Shiru kamar bazai bud’e idonsa ba saikuma ya bud’e d’aya yad’an kalleni ya kauda kansa. cikin k’asaitar nan tasa yace, “miyasa?”.
“miyasa kuma?”. ‘nakuma maimaita maganar ina k’ok’arin janye hannuna’.
Carab ya rik’e hannun nawa, ni tsoroma ya bani, na kalli hannunsa da nawan ga mug cikeda ruwan zafi yanata turiri, kuma zafin yana ta6amin gwiwar yatsuna, idonsa a lumshe har yanzu, idona harya fara tara kwalla, nayi alk’awarin koda hannun zai toye gaba d’aya bazan tanka masaba, ai yasan abinda yake dai-dai da akasin haka.
Saida mukayi 1minute a haka kafin ya maido face d’insa inda nake yana kallona, ya d’age gira d’aya yana fad’in “da zafi ne?”.
Humm lallai Galadima akwai rainin wayo, na fad’a a zuciyata, janye idona nayi daga kansa na maida kan Abdurraheem dahar yanzu yake kwance a bisa cikinsa.
Ya yamutse fuska yana sakin hannun, cikin basarwa yace, “inason jarumta”.
Had’iye kukan dake k’ok’arin tahomin nayi, na ajiye Mug d’in na cigaba da zuba masa farfesu a k’aramin bowl batareda nayi koda tariba.
Tashi yay zaune yana jije lips, yayinda hannunsa ke rik’e da yaron, d’ayan kuma ya dafe saitin zuciyarsa, a wahalce yake fisgo numfashi kafin ya fesoshi, tun kuma d’azu na lura da hakan, kalmar zafi daya fad’amin na shiga fassarawa, har na fahimci da manufa ya fad’a, hakanne ya Sani murmusawa batareda na d’agoba ina zuba masa farfesun nace, “tabbas duk zafi sunansa zafi, amma akan samu banbance-banbance wajen banbancesu, wani zafin a gangar jiki muke jinsa, wani ko tawani sashen jikin ake samunsa, wani zuciya, wani rayuwarma gaba d’aya Ce ke tsintar kan a zafi, saidai babu zafi mafi rad’ad’i daya kai na Mutuwa, idan da zamuyi nazari zamu fahimci rayuwa tana a tsare ne mataki-mataki, sannan iri d’ayace ga kowanne launin halitta na mutum ko aljan ko dabba, Dan mukan tainci kanmune akusan mizani d’aya, dukda ubangiji ya banbantamu ta halitta da ayyuka da tunani ko nace kaifin basira, ko’a jinsi launi biyune, akwai namiji akwai mace, dukkan rayuwa takan farane da mafari yalla6ai” na d’ago ina sake mik’a masa mug d’in tea d’in again, a mamakina a yanzu saiya kar6a, na lashi lips d’ina na k’asa ina gyara zama sosai da maida hankalina wajen juya kunun dana zuba a cup da tsokali, cikin nisawa nacigaba da fad’in, “mafarin rayuwa shine dasuwar bawa a cikin mahaifiya, mukanyi wannan rayuwarne a cikin halin su wanene mu? daga nan sai matakin haihuwa, shigowa duniya a bisa bigiren wane ahali muka kasance, dukkan ahalin daka Sani sunada matsalarsu, saidai tawasu tafi tawasu zafi, daga ranka ka iso filin gwagwarmaya wato duniya, shikenan littafinka dayazama rubutacce tun a cikin mahaifiya saiya fara aiki, mala’iku masu kula da fitar numfashi su dasa alk’alaminsu, masu kula da abinci suma haka, masu kula da ruwa ma haka, masu kula da magana ma haka, masu kula da kallo ma haka, masu kula da ji ma haka, masu kula da duk wani motsinka ma haka, tafiya, zama, kwanciya dadai sauransu, kowa ana haihuwarsa tsaftatatccene, iyaye suke fara juya akalar rayuwa, walau mai k’yau ko sa6aninta, (kaga kenan akwai hisabi tsakanin iyaye da y’ay’a ma kenan?) daga nan rayuwa zata cigaba da yad’o kamar d’an duma, tun ana maka, harka koma koya, harka fara iyawa da kanka, harma ka kware ka koyama wani, (wanne ka iya? ko ka koya? yarage ruwanka) duk Wanda kaga an masa a farko to tabbas za’a k’ara masa a k’arshe, kodai silar tsufa, ko ciwo, kokuma iftila’in rayuwa, kokuma na k’arshe shine hidimar gawarka, a dukkanin dunk’ulalliyar rayuwar da kowanne bawa yakanyi zakaga cike take da k’alubale masu zuwa da zafi kala-kala, yalla6ai kasan mike taushe wannan rad’ad’in zafin kuwa?”. nayi maganar ina d’ago ido na kallesa. A mamakina sainaga ya girgiza min kansa. na murmusa ina janye idona daga kansa na maida ga kofin tea d’in ina masa alamar yasha mana.
Yamutse fuska yay irin kalar tausayinnan.
Nima sainayi kwal-kwal da ido kamar zanyi kuka, na had’e hannayena waje d’aya alamar rok’o????..
Lips d’insa yad’an ciza kafin yafara shan tea d’in. Nayi salute nashi ina masa jinjina????.
Basarwa yayi, nima saina kad’a ido ina tunzura baki gaba, sannan nacigaba da fad’in, “Abinda ke taushe wannan rad’ad’in zafin shine *_HAK’URI_*. hak’uri muhimmun sinadarine dake jagorantar garkuwar jiki ta kowacce launin halittar jiki na d’an Adam, walau a fili take ko a 6oye take, saidai babban makarinsa da taskar adanashi shine *_ZUCIYA!_* a duk lokacinda k’arfin zuciya ya raunana to zaka samu madarar hak’uri ta salwanta, idan zafi yanata yawa babu wannan hak’urin bugu d’aya take duk wani ma’adani na cikinta saiya tarwatse, saikaga an rasa ayyukan jiki dana ruhi, shikenan wane yazama labari. daga lokacin da rad’ad’in fitar rai ya kusanci bawa dukkan mala’ikunan da suka kasance tare dakai a randa kazo duniya saisu fara janyewa daga gareka, wani bawan kafin ranar mutuwarsa zakaga ya daina cin abinci, hakan na nufin mala’ikan dake kula da abinci ka yagama aikinsa, domin ya zagaye duniya kaf duk yawan abincin dake cikin ta babu rabonka koda kwayan gero ne, ka gama cinyewa, wani kafin ranar Mutuwa ya daina shan ruwa, aikin mala’ikan dake kula da ruwa shanka yagama k’arewa kenan, duk yawan koramu da tafkuna na duniya bakada sauran rabo na ruwa, ka shanye naka, wani kafin Mutuwa ya daina magana, mala’ikan dake kula da furucinka yagama aikinsa, babu sauran wata kalma data rage harshenka ya furta, wani kafin Mutuwa ya daina ji, mala’ikan dake kula da jinsa ya gama aikinsa, babu wata kalma data rage kunnensa zaiji, wani kafin Mutuwa ya daina gani, mala’ikan dake kula da ganinsa ya gama aikinsa, kwayar idonsa bazata sake kallon wani abuba, wani kafin Mutuwa ya daina tafiya, mala’ikan dake kula da tafiyarsa ya gama aikinsa, haka-haka wad’annan mala’ikun zasuyita ja baya suma barinka, har yarage sai mai kula da fitar numfashi kawai, daga ranar da UBANGIJI yace yana buk’atar ganinka shikenan takuma k’are, sai rundinar mala’iku su had’u su takewa kwamandan mala’ikan d’aukar rai baya, idan kai mutumin kirkine fararen mala’ikune, idan na banzane mala’iku masu azaba zasu take masa baya, sauran al’amari kuma sai Wanda ya haliccemu yasan ya zata kasance??. zakasha mamaki idanfa nace maka duk wannan zafin k’aramin zafine acikin kashi-kashin na abinda ya shafi haluttu, shi wannan zafin ana kiransa zafin na za6in kai, kokuma zafi na a haka tsarin yazo, ma’ana kaine ka had’ama kanka wannan zafin, kokuma wanine ya had’a makashi. Abu na biyu shine zafi na rad’ad’in Mutuwa, dolene kowa saiya d’an d’anashi, walau kafiri ko Musulmi, saidai akwai banbance-banbance na awanne tsari ka koma ga ALLAH, ba wannan zafinne kawai ke jiran d’an Adam ba, akwai zafin na *_BARZAHU_* shi ake kira kwanciyar kabari, mika tanada, mi zaka tarar shine abin tambayar, wannan kam ALLAH ne mafi sanin wad’anda zasu d’and’ana wannan zafin (ALLAH ka datar damu??)”.
Akan la66a Galadima ya amsa da amin, Munaya ta share hawayenta, ta cigaba da fad’in sai zafi mai gaba d’aya, shine na makoma, *_WUTA KO ALJANNA_*, yalla6ai wad’annan jimullar zafin ga d’an Adam tilas ne, na cikin rayuwa shine zafin da zaka iya controlling nashi ta hanyar hak’uri, to Ashe bai kamata ka tasirantar da wannan zafin ya cigaba da k’onaka ba, musamman idan zakayi dubi dawasu ni’imomin da ALLAH yamaka a cikin wannan zafin, ka kasance mai yawan hak’uri saikaga kanka cikin masu yawan riba, wlhy ta wannan hanyarne kawai zaka zama mai *_NASARA_* akan mak’iya ni……….”.
Maganata ta katse saboda knocking d’in k’ofar da akayi, kallon juna mukayi ni da shi, yay wani luuu da idanunsa ya lumshesu, hakanne ya sakani bada izinin shigowa kawai batare da na jira amsa daga garesa ba.
Sarkin k’ofane ya shigo, ya zube yana gaishe mu, nice kawai na amsa, boss kam hannu kawai ya iya d’aga masa, yay mana ya jiki again, nanma nice nakuma amsa shi, cikeda girmamawa yace, “ranki ya dad’e yalla6ai harun ne ke buk’atar iso”.
Saida gabana ya fad’i, na had’iye wani yawu mai kauri ina kallon galadima dayay biris damu yanata shafa kan d’ansa, bud’e idonsa jajaye yayi akan Sarkin k’ofa, ya jinjina masa kai alamar ya shigo dashi.
Kallonsa nayi tamkar zanyi magana saikuma nai shiru, a raina ina mamakin wannan munafukin dami yazo kuma?….. ban kai k’arshen zancen zucin ba Harun yay sallama, nid’ince dai na amsa cikin danne zuciya da fushina.
Ya zauna fuskarsa d’auke da murmushi.
Nima saina saki tawa ina fad’in, “barka da hantsi ranka ya dad’e”.
“Barka dai gimbiyarmu, ya jikin ki dana yalla6ai?”.
Na kalli Galadima dayay shiru kansan jingine da kujera ido a rufe, “da sauk’i”, na fad’a ina mik’ewa na koma saman kujera, dan bazan ta6a barin falonba sainaji uwarmi ya kawosa.
Ya amsa da “masha ALLAH, ALLAH ya kiyaye gaba ya k’ara lafiya”.
“humm” na fad’a ina amsawa da “Amin dai”.

Hankalinsa ya maida ga Galadima, “Sameer ya jikin?”.
Bud’e idonsa yayi shima, ya ajiye mug d’in hannunsa a teble d’in dake gefen damarsa, batare da yace uffanba ya sauke ajiyar zuciya yana taunar lips.
Banga alamar damuwar rashin amsawar tasaba a fuskar Harun, dan yariga ya saba da halinsa.
Saidai idonsa k’uri akan Abdurraheem dake cinyar Galadima d’in yana barci, mik’ewa yay yana fad’in, “my son zo mu gaisa ko?”.
Ganin haka nima nayi azamar mik’ewa nakai ga Galadima kafin shi ya isa, na d’auke Abdurraheem d’in ina fad’in “ai barcima yake ranka ya dad’e”.
Ba Harun ba hatta da Galadima saida yaymin kallon mamaki, nakoyi cid’in-cid’in da fuska yandama bazaice nabama Harun d’inba.
Baki ya bud’e kamar zaice wani Abu saikuma yay shiru yana kauda kansa daga kallona, nima saina ta6e baki ina barin falon da harar Harun ta gefen ido.

Gaban Harun ya fad’i, mi yarinyarnan take nufi?……
Kafin ya lalubo amsar ya tsinkayi maganar galadima yana cewa, “sorry Harun, kasan har yanzu a tsorace take, duk wani motsinsu akan idontane”.
Murmushin basarwa harun yayi, yace, “ai dolene hakan ranka ya dad’e, abinne akwai tsoratarwa, wlhy jiya tashin hankalinnan ne yasaka azababben ciwon kai rufeni, shiyyasa ko ganina ba’ayiba, yanzu police d’in ina suka samosu?”.
“humm” Galadima ya fad’a cikin tsananin taune lips da k’unar zuciya, ya bud’e baki a hankali zaiyi magana nida ke bayansu basu saniba nai saurin tareshi da fad’in “a hannun wasu munafukaine ranka ya dad’e, ai koni daza’a bani baiwar nan da aka kama da yaran wlhy saina tsoma kanta cikin drum d’in ruwa harsaita daina Numfashi zan barta, kafin sannan kuma nagamajin labarin Wanda ya sakata, amma shi my boss ai a station suka zauna har aka kawo yaran, badasu akaje farautarba”.
Tsuramin ido Galadima yayi cikin tsagwaron mamaki, miyasa to zanzo na kasa na tsare dukkan wani motsin Harun d’in? ya kula satar yaran tana Neman ta6a tunaninta takasa banbance Wanda zata zarga, ai Harun yawuce ya 6oye masa wani sirri na sashen rayuwarsa, tun da babu abinda bai saniba na baya, saidai abinda ba’a rasaba kam, danne ransa yayi ya nuna hakane, yabari har Harun d’in ya tafi sannan yaji dalilinta.
Ina kallon Sassanyar ajiyar zuciya da Harun ya sauke a 6oye, sannan yace, “ai police d’in sun cancanci Babar k’yauta, shiyyasama na shirya musu ita, sunyi aiki irinnan jaruman masu tsaro”.
“hakane wlhy ranka ya dad’e ”. Na fad’a cikin murmushi.
Dukfa yanda Harun yaso bugar cikin Galadima yaji yanda abun yake, na kafa na tsare, dayayi tambaya nike bashi amsa, saiya d’auka kodan Galadima bashida lafiyarne shiyyasa bai iya amsawa, tun da tunda ya shigo baice k’ala ba, kuma yasan yanayin ciwonsa, a baya ma shikan bashi taimako, baidai tsinci komai ba yay mana sallama ya fita, da k’udirin anjima ma zai dawo ne.
A sace na raka bayansa da harara, sannan na kalli Galadima na basar, dukda kallon tuhuma dayake jifana dashi kuwa.
Wani farfesun na sake zuba masa na mik’a masa.
Batare da ya kar6aba cikin k’ank’ance idon bala’i yace, “mikikayi haka? kinsan waye Harun a wajena?”.
Kaina na girgiza masa.
Yaja tagwayen tsaki yana hararata, “halan satar yaranki yafara shafar tunaninki ne? kina tunanin akwai abinda Harun zai iya gazaji daga sirrina?”.
Na d’an ta6e baki ina jawo teble d’in gabansa, na d’ora bowl d’in dana zuba farfesun, baki ya bud’e kamar zaiyi magana saikuma yay shiru. nima bance uffanba na ajiye masa sannan na koma k’asa Na zauna na zuba sabon kunu nahau sha.
Kwafa yayi, yace, kinma maidani d’an iska ko?”.
“Hummm” na fad’a kawai, naimasa kallo d’aya “yalla6ai wani karatun akan barsane a yanda yazo, sai idan lokacin fasaarashi yayi amasa fashin bak’i, nasan darajar alak’ata dakai batakai koda rabin tsakaninka da Harun ba, domin ni alak’ar wucin gadice ta had’amu, k’iris ma ya rage ta k’are, saidai inason nabama y’ay’ana kamar yanda ka fad’a kariya koda sau d’ayane a rayuwarsu kafin na barsu, dan haka maida wuk’arka a kube, lokacin zareta baiyiba, sometimes kalmar Mahangi da mai hange takanyi kamanceceniya, dan bakowa ke iya rarrabata wajen fasaara ba, amma kalmomine duka masu harshen damo, wani k’alubalen saida tunanin mai zurfi, wata k’oramar ruwan mutanen dake zagaye da ita sukanyi imani bazata balle harta cisu ba, saboda sun yarda sud’in masuntane da kullum suke rayuwa cikin wannan k’oramar, abin mamaki saikaga wataran an wayi gari da mutanen da muhalansu duk wannan ruwan ya had’iyesu, abinda basu ganeba bakowacce irin alak’a bace ake kulla amana da ita, wani farin idan yashiga cikin fari banbance k’arkonsa saidai ALLAH”.
Tashi nayi nai shigewata bedroom d’insa.

A fusace shima ya mik’e zai bini, kad’an yarage ya zubda farfesun dana ajiye masa, ALLAH dai ya kiyaye ya shallakesa ya wuce.
Hucin mutum kawai naji a bayana, hakan yasani waigowa da sauri, hannu ya dunk’ule zai kaimin naushi, nai azamar fad’awa saman gadon ina zaro ido waje, a lallai Abu ya girmama, nikuma miye nawa da zai sauke fushinsa a kaina? nai maganar a zuciyata.
Janye hannunsa yayi yana ciza lips d’in sa da k’arfi, idonsa dukya kuma rinewa, ya dunk’ule hannun ya daki d’ayan dashi, muryarsa har rawa take yace, “Miyasa zaki kuma hargitsan tunani ne? Minene laifin Harun shikuma? kuna nufin duk Wanda na yarda dashi shine mak’iyina? Kai impossible wlhy, Munaya wakikema aiki a kaina? ya rankwafo kaina, kaikace cinyeni d’anya zaiyi, saikace zaki yaga bandar nama, da k’arfi yace, “bazaki sanarmin ba saina k’arar da numfashinki ne waishin Ubanwa ke fad’a miki wad’annan maganganun da kike d’aureni dasu a ko yaushe?!!!”. Ya k’are maganar cikin tsananin tsawa da k’araji.

Ba k’aramin firgita nayiba, badan karnayi k’arya ba danace har wutar bala’i Nagano a idonsa tana ci, wannan bawa akwai zuciyar tsiya, idan zai zama jami’in tsaro da k’asarmu ta amfanu da yawa………
Da k’arfi ya girgizani, saboda ganin saboda rainin wayo tunanima na tafi……….
A firgice nace “yi hak’uri zauna zan fad’a maka”. na fad’i hakanne dan kawai ina ganin itace mafitar dazan nema ya fasa had’iyeni. a mamakina kuwa saiya tashin ya zauna yana dafe k’irji hawaye nabin kumatunsa.
Tsantsar tausayinsa ce ta kamani, na tashi na d’akko ruwa na dawo kusa dashi na zauna, addu’oi na shiga tofawa a ruwan, yana zaune dafe da kansa, da alama kuka ma yakeyi, dan ajiyar zuciyar da yakeyi ta yawaita.
Saida na gama na dafa ka fad’arsa, tamkar bazai d’agoba saikuma ya kalleni, ruwan addu’ar na basa, babu musu ya kar6a ya shanye, duk da baima san mita bashiba, idanma poison ne dai gara ma yasha ya mutu ya huta.
Mintunansa biyu zuwa uku dasha yafara sauke ajiyar zuciya mai k’arfin gaske, saiya zame kuma ya kwanta, kafin kacemi barci ya saceshi a haka.
nima ajiyar zuciyar nayi ina girgiza kai da share hawayen dake silalomin, ina rok’on ALLAH ya kawoma wannan bawan nasa sauk’i da rangwame cikin gaggawa da warwarewar al’amura.
Dagashi har yaran tausayi suke bani, nayi zurfi a tunani wayarsa tayi ring, kamar zan share saikuma Na tuna maybe Momma ce, tashi nayi zuwa inda wayar take, aikam dai itace, nayi picking jiki a sanyaye, dan tunanina kota gamajin komai, amma sainaji sa6anin haka, da y’ar raharta ma tace, “Muh’d duk hidimar sunance haka?”.
“Uhm Momma bashi bane nice”.
“a’a d’iyata kece?”.
“eh Momma, kuna lafiya? ya jikin Abie?”.
“Alhmdllh d’iyata, ya k’arfin jikinki kema? ina yaran?”.
Gabana ya fad’i, Na had’iye wani yawu da k’yar, cikin in ina nace, “lafiyar kowa k’alau Momma, shima y… yana barcine”.
Dagacan Momma ta murmusa tana gyara zama a harabar asibitin, dan batason Abie yaji wayar da zatayi, tace, “humm d’iyata kema 6oyemin zakiyi kenan? yanzu koda mutuwa yaran sukayi dashi kansa kowama saiya shiga fargabar gayamin?”.
Na had’iye yawu dak’yar, “kiyi hak’uri Momma, ki gafarcemu” https://2gnblog.blogspot.com/.
“Bakumin laifin komaiba ni, hakan da Muh’d yay shine dai-dai, dan lokaci yayi dazai daina zama jiran sak’on mak’iya ko zuwansu, shine yakamata ya fita farautarsu domin kawo k’arshen komai, na yarda dake 100% Munaya, nakumayi imani insha ALLAH kece zaki sauyamin yaro daga k’uncin dayake ciki zuwa farin ciki, tamkar yanda Na fad’a miki tun farko karki ta6ama Muh’d sanya ko nuna tsoronsa, lokacin dazaki kwantar masa dakai kizama kowacce irin mace a agidan mijinta har yanzu baiyiba, kada ciwonsa yasakaki fargabar fad’a masa gaskiya, rayuwa da mutuwa duk Na ALLAH ne, ko ayanzu Muh’d yabar duniya bazanyi bak’in cikiba, domin ya nuna musu shi jarumine, kuma ya haifi wad’anda zasu iya zama magadansa su sauya komai koda ba’aso, nanda kwanaki biyu komai ya gama lafawa ki tabbatar kin masa maganar tafiya wanka gida, wannan shine target d’inmu Na k’arshe akan rayuwar zaman aure na dindin, kowacce irin birkicewa zai miki akan bazaki jeba, kema ki birkice masa, dan nasan abinda yafaru zaisashi dagewa akan yaran bazasuyi nesa dashiba, idan kuma har aka cigaba da tafiya a haka, kowane irin dana Sani zai iya biyo baya”. Momma ta share hawaye dake kwarara a idanunta, taci gaba da fad’in “ALLAH yayi miki albarka Munaya, dake da abinda kika haifa, yanda kikamin biyya wajen k’autata kar6ar Abu mai wahala (duk da bani na haifekiba) kema ALLAH yasa y’ay’anki sumiki biyyaya fiye da wannan, ALLAH yasaka hannu adukkan lamarinki keda mijinki da sauran y’an uwansa, nusar dashi abinda duk baki gamsu dashiba shine zai rage ma zuciyarsa baraza, dan tarawar yagani a lokaci d’aya shine mafi had’ari Munaya, zuciyarsa zata iya bugawa a lokacin, kiyi hak’uri nasan bak’yajin dad’in zama da Muh’d ko kad’an, domin ni kaina mahaifiyarsa wataran gaza gane kansa nakeyi, amma inaji a jikina akwai sauyi maiban mamaki dazai zo ya rusa komai, ki sameshi fiyema da yanda kikeso, ALLAH yayi muku albarka, idan ya tashi ki kirani naji ya jikin nasa”.
Bata jira nayi magana ba ta yanke wayar, da alama kukane yaci k’arfinta. nima saina fashe da kukan ina kallon Galadima, insha ALLAH zan cikama baiwar ALLAHr nan burinta, koda ace mun rabu dashine, dan maganar gaskiya bazan iya rayuwa da mutum murd’ad’d’e mara yarda irin Galadima ba, labarinsa kawai kukeji, amma halinsa saika zuna dashi, Mara hak’uri zai iya gundurarsa ne cikin awanni biyu kawai, dan zaka dinga kallonsa a matsayin mai wulak’anci ko dizgi, girmankai da sauransu. Na sauke ajiyar zuciyarsa ina maida kallona ga Abdurrahman dake motsin tashi, nasan dukansu saisun tashi inhar d’aya ya tashi, saina lalla6a na kwanta kusa dashi na saka masa nono a baki.

********************

Har akayi la’asar Galadima bai farkaba, Nuren yazo shida Sauban, da Saleem har sau biyu suka iske yana barci, hakama Mom da inno da mama Fulani. Gashi su inno 4:30pm zasu wuce ma, laraba tazo tama yaran wanka, dan tuni sun farka, Nima nakumayi sannan naci abinci, kaina ciwo yakemin sosai, dan haka Sauban yafita ya samomin Magani nasha na kwanta, munyi sallama dasu Mom, zasu dawone kawai idan Galadima ya farka kafin su tafi. yaran kam duk d’insu suna can an kaima papi su tun d’azun.
Nidai barci yay awon gaba dani, daga nankuma bansan wainar da aka cigaba da toyawa ba a gidan.

*******************

Bayan la’asar kad’an Galadima ya farka, ganin shi kad’aine a d’akin ya tashi zaune bakinsa d’auke da addu’ar tashi barci, jin k’irjinsa yayi sakayau yasaki babu nauyin kamar d’azun, saidai abinda ba’a rasaba, yatashi zuwa bathroom yay wanka da alwala.
Sallan zuhur da la’asar ya rama, tareda addu’ar neman sauk’i akan wannan lamari da samun k’arfin zuciya, dolene saiyayi yak’i da dukkan abinda zai zama makamin barazana a agaresa inhar da gaske aikin zaiyi, falo ya fito bayan ya kimtsa, zamansa da mintuna baifi 2 ba saigasu inno.
Basu jira isoba suka shigo, a zatonsu yana bedroom yana barci, sunsan Munaya kuma tana d’akinta tana barci tunda daga can suke. ganinsa a zaune ya saka fuskar kowannensu fad’ad’a da murmushi. Shidai kallonsu kawai yake d’ai-d’ai.
Inno ta mangari kansa tana fad’in “ja’iri baka sanmu bane halan?”.
Hannunta ya rik’e yana kallonta, cikin maganarnan tasa ta k’asaita yace, “Inno wai ina zakuje ne?”.
“inda muka fito mana”. Inno tafad’a tana zama kujerar kusa dashi.
“saikace wad’anda ake kora?”.
“A’a wazai koremu nida gidanmu, komawar dai ne yafi cancanta, dan takawa ma yace a gaisheka basai ya shigoba, zakuyi waya, idan ka murmure kaje yana nemanka”.
“To shikenan ALLAH ya tsare hanya, mun gode sosai da sosai”.
“Amin” inno tafad’a tana shafa kansa ta ciga da kwararo masa addu’oi shida matarsa da yaransu, falon kowa tana amsawa da amin, itama mom tayi nata.
Yace, “mom hada ke wai?”.
“eh mana Sameer, zaman mi zanyi to? tunda ALLAH ya iyakance komai cikin sauk’i, nanda y’an kwanaki kuma basai na zagayo naga masu jego ba da jikin naka, a dai dunga kulawa sosai, gasu laraba nan da bayi 2 anbar muku, dukdai wata kulawa insha ALLAH zasu taimaka wajen badata akan yaran, dan yakamata dukkan bayi da kuyangin sashen nan naka ka sallamesu kawai”.
Kansa ya jinjina mata alamar amsawa.
A gurguje sukad’an kuma tattaunawa da kwantar masa da hankali suka fito, dukda yaso musu rakkiya suka dakatar dashi. Abincin da mom ta zuba masa takumace yamata alk’awarin zaici ya dage yaci sosai, sannan Sauban daya dawo rakkiyarsu d’auke da y’an uku shida bayinnan biyu yabashi magani yasha, kar6ar Amaturrahman yayi, Sauban kuma na zaune dasu Abdurraheem yana musu wasa wai dole sai sunyi dariya, (nace, “aiki jaa kenan, inba dariyar k’udaba ta jarirai idan suna barci keyi aiko ka dad’e baka ganiba Uncle triplets??).

Galadima ma madai yatsansa d’aya ya saka cikin hannun Amaturrahman yana wasa dashi, dukda idonsa a lumshe yake ya jingina kansa da kujera, maganganun Munaya na d’azun kawai yake nazari dalla-dalla.
Ana cikin haka Samha tayi Knocking, Sauban yace ta shigo, saida ta gaida Galadima damasa ya jiki.
Ya amsa mata batareda ya kalleta ba, tareda tambayarta Khaleel fa?. Tace, “yana 6angaren Ummu hasheem”.
Baice komaiba, itama ta k’araso ta d’auki Ammaurrahman data rik’e yatsansa gam tak’i saki..
d’agowa Galadima yay yana kallon yarinyar, Samha dai dariya takeyi, har Sauban shima ya farga da abinda ke faruwa ya shiga tayata. Galadima ya zare yatsansa yana murmuahin gefen baki da lakatar hancin Amaturrahman.

Har Magriba suna nan sun shashance akan yaran, yayinda Galadima ke zaune yanata cud’awa da tantancewa, lokaci-lokaci yakan kallesu dagasu har yaran. Tunda ya tambayesu Munaya sukace tasha Magani tana barci bai sake tambaya ba.

********

Ban tashiba saida suka fara kuka, a time d’in har magrib tama wuce, nagama shayar dasu na lek’a Galadima, na iske doctor jalal tareda Dr Yaseen da Akash Wanda yake shirin komawa gobe, sai Muftahu da Nuren.
Muka gaisa dasu suka kuma tambayata jikinsa? na Amsa musu da Alhmdllh. fitowa nayi na barsu, da aka kawo mana abinci ma can nace akai musu, Sauban yazo ya kwashi yaran bisa Umarnin Galadima, doctors zasu kuma duba lafiyarsu.

??????

Tunda Harun ya fita saiya kira wata Number lokacin daya k’arasa d’akinsa, dukkan abinda ya faru ya labarta mata, daga can tace k’aryane bahaka akaiba, ita an sanar mata lallai da Galadima aka kar6o yaran, babu wasu police, amma itafa kamar tafara saka alamar tambaya akan wannan ficikar matar tasa.
Harun yace, “haba dai, wannan y’ar yarinyar mizata iya, akwai dai abinda bamu saniba, yanzu dai kibari zamuyi maganar daga baya, zand’an bincika yarannan danni na lurama kamar ba wad’anda muka saka bane sukayi aikinnan?”.
“sunefa gaskiya, abinda dai na lura dashi sun had’a aikin da wasune, shiyyasa suke 6oye mana Kansu, tunda kaga mudai baiwarnan bamu muka sakata ba, amma shi namijin yana cikinsu, nasan sunyi luff ne sai k’ura ta natsa su fito”.
“ok shikenan to, zandai sake bincikawa, dan Sameer yanada wayo, shiyyasa naso bugar cikinsa akan batun, amma wannan shegen k’asaitar tasa ta rainin hankali ya hanashi tankamin, sai matarce ke bani amsa”..
“karka damu zamu sauke masa shine ai”……………???

 

 

??abin dariya, ku a naku zaton yaranku sun 6oye Kansu be?, to suna hannun Galadima, lafiya kawai muke jira ya samu ya yagalgalasu kuma ya cafkoku munafukai????.

 

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu._*??????
*_typing??_*

?? *_HASKE WRITERS ASSO….._*

*_?RAINA KAMA…..!!?_*
_(Kaga gayya)_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply