Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 27


Raina Kama Book 2 Page 27
Viral

Book 2~ ????2?7?

…………….Tunda suka d’akko yaran suketa kuka, musamman Abdurraheem dahar shid’ewa yakeyi, ALLAH dai yabasu sa’a ne saida suka fito suka fara kukan, neman haukatasu ma sukaso yi tun amotar, jisukai tamkar su rufesu da duka, saidai babu damar hakan, dan basuga abin duka jikin wad’annan kwad’unan yaranba.
Da farko sunga kamar ana binsu, sai daga bisani ne sukaga ba haka baneba, har dai suka iso gidan y’an uku basu barsu sun shak’i iska ba.
Suna shiga suka danna musu wasu allurai, cikin mintuna k’alilan jikinsu dukya saki sukayi luf.

ganin lokaci yaja har kusan 10pm babu alamar wani motsi hankalinsu ya kwanta, dan sunsan dai tabbas sun tsira, wayar wadda ta sakasu aikin suka kira, amma tak’i yin picking.
Cikin matan d’aya tace, “kusan dai bazata d’aga ba, saboda nasan masarauta a haukace take yanzu, saidai mubari zuwa safiya”.
Tsaki d’aya yaja, “kai nifa gaskiya a tsorace nake, gara ta d’auka asan mafita, bana buk’atar gawar yarannan takwana a hannunmu, kunsanfa babansu mayene wlhy, tsaf zai bibiyemu”.
“kai dalla ai yanzu bashida wannan damar, caza’ayi a fad’ama police, sukuma aikinsu zai farane zuwa safiya, kafin sannan munma gama binne gawar yaran mun kama gabanmu”…..
“eh kumafa hakane”.

Suna tsaka da wannan hirarne su Galadima suke shigowa, gidan k’aton gaskene dan haka suka kasa fahimtar INA zasu dosa, Galadima Yakuma danne abin kunnensa da d’anyatsa d’aya cikin murya k’asa-k’asa yake fad’in “Sauban kufara muje”.
“yauwa Yaya zaku shiga hannunku Na haggu, duk sunajin maganar dan haka sukabi hannun haggu, yayinda su Ameer ke binsu a baya suma. Galadima dake gaba ya bud’e k’ofar a hankali duk suka shiga, daga can Saleem yace, “duk Ku rarrabu sir, dan abin ya nuna yaran suna ainahin tsakkiyar gidanne”.
Batare da sunyi magana ba duk suka rarrabu.

‘Daya acikin 6arayin yace, “kai nifa kamar motsi nakeji gaskiya”.
“to sannu mai kunnen maciji”. cewar d’aya aciki.
Cikin matan d’aya tayi dariya tana fad’in “nakula kaidai bibo matsoracine halan?”.
Hannu ya d’aga zai kwad’eta, a harzuk’e yana fad’in “k wlhy kacaccalaki zanyi, bar ganin kinfito daga masarauta, kubadan ma an had’amu aiki dakuba kun Isa saninmu ne? jimin y’ar iskar mara kunya”.
Hak’uri y’an uwansa suka bashi, ya mik’e yana jan tsaki ya fito danya duba.
Galadima dake la6e cikin labule yay saurin fitowa, abinka da dogon mutum dan danan yasamu damar shak’osa ya shaka masa abin hannunsa, tun yana k’ok’arin kare kansa har jikinsa ya saki ya kwantar dashi a k’asa.
Jinjina Muftahu dake kusa dashi yamasa, sannan suka cigaba da shiga.
‘Dayar baiwar tana kitchen tare da wani suna iskancinsu Nuren yasamu damar sad’ad’awa, (kunsan dai shahararren kidnapper ne????) yauma tsiyar ya aikata wajen jefa ma namijin handkerchief a fuska, macen tai yunk’urin zuba ihu yasa k’afa ya tad’ota ta fad’in, sannan ya danne bakinta da ya shak’a mata itama.
K’arar fad’uwarta taso fargar da sauran, dan haka duk suka mik’e suna fara lek’e-lek’e, aikam Muftahu yasamu ya tad’e d’aya ya fad’i, Ameer dake bayansa shima ya shak’a masa, harda mangareshi yana fad’in “kwallon shege taka ta k’are, inakai ina satar sarakunanmu insha ALLAH”.
dariya taso kufcema Muftahu amma ya danne bakinsa da hannu yana girgiza kai saboda tsiyar Ameer.
Fad’uwar wani da suka juyo ya sakasu kuma saurin waigawa wajen, Galadima ne ya sakeshi ya fad’i, “shegen k’arfin jinine dashi dak’yar abin yay masa tasiri”. Galadima ya fad’a yana halbinsa da k’afa.
Gaban d’ayar baiwar dake la6e jikin labule ya fad’in, dan tabbas wannan muryar Galadima ce, kowa yasan bai iya R ba, zuface tashiga keto mata jikinta na 6ari, ta to she bakinta saboda kuka daya kufce mata, saigata tana tsilala fitsari saboda ganin Galadima yanufo ta wajen, shikenan itakuma tata tak’e, wannan zakin gagara badau d’in binneta kawai zaiyi da ranta.
Waige-waige Galadima ya fara saboda jin numfashin mutum dayakeyi kad’an-kad’an ta wajen, har yayi gaba ya dawo baya yana yaye labulen wajen. shi da farkoma ya zata aljanace saboda yanda ta zazzaro masa ido. fincikota yayi ya Watso tsakar d’akin, mamaki ya kamashi ganinta da kayan manyan kuyangin gidansu.
“tashi tsaye”. ya fad’a cikin matuk’ar d’aure fuska, kad’an yarage kashi ya kufcemata.
“ina suke!!!”.
Yafad’a cikin matuk’ar tsawa daya firgita hatta su Sauban dake saurarensu a waya.
Wannan tsawar tasa ce ta saka d’ayan fitowa a tsorace da gun a hannu, Aunty Salamah dake bayansa bai saniba ta hankad’ashi yay gaba zai fad’in, Nuren ya ida tad’eshi da k’afa.
Gun d’in data fad’i ta silalo gaban Galadima ya taketa da k’afa yana huci da taunar lips. Handkerchief d’in hannunsa yasaka ya d’auki bindigar, ya saita namijin da ita.
Mazari jikinsa ya fara yana d’aga hannu sama, “dan ALLAH ranka ya dad’e karka kasheni, wlhy bansan komaiba, oganmu ne yasan komai da wannan baiwar”.
Kunamar bindigar Galadima ya d’ana, nanfa su Muftahu duk suka rud’e, Nuren yace, “Brother please karkayi harbi, nasan zasu fad’a mana, dan ALLAH kayi hak’uri”.
Gaba d’aya jijiyoyin kan Galadima sun mimmik’e, sai fidda huci yakeyi a wahalce.
Muftahu ma yashiga rok’onsa, Su Saleem dake sauraren komai dagacan duk suka rud’e, Sauban yace “yaa Sam ALLAH ya huci zuciyarka, amma idan ka aikata haka a wajenwa Zamu samu hasken sauran abubuwan?, dan ALLAH kayi hak’uri badan mun isa mu saka ka ba, saidan halin da mahaifinmu ya tsinci Kansa tsawon shekaru, gakuma dama tazo mana ta Sanin sirrin 6oye, muyi amfani da ita ta sauk’ak’ak’iyar hanya….”
Sakin gun d’in Galadima yayi ak’asa yana dafe k’irji, wani mugun bugawa zuciyarsa keyi, da baya-baya yanemi zubewa a k’asa, cikin hanzari Nuren da Muftahu suka taresa, da taimakonsu ya zauna akan kujera. Yana nuna baiwar da d’ayan hannusa.
Aunty Salamah data fahimci mi yake nufi tace, “ina yaranne?”.
Jikin baiwar Na 6ari ta nuna k’ofar wani d’aki, shiga Aunty salamah tayi itada Ameer suka d’akkosu.
Saidai duk a firgice suke, dan yaran babu alamun rai tare dasu, zufa ta shiga ketoma Aunty Salamah, haka ta fito rungume da Abdurraheem da Amaturrahman, shikuma Ameer ya d’akko Abdurrahman yana fad’in “Aunty kamarfa yarannan sun mutu”.
Wannan kalma caraf a kunnen Galadima.
Wata muguwar zabura yayi yamik’e tsaye, sai ya kuma dafe k’irjinsa da sauri hajijiya tafara katantanwa dashi, basu fargaba sai jinsa sukayi kawai a k’asa.
Gaba d’aya suka kuma rikicewa, sukayi kansa.

Muftahu yace, “bamuda isashen lokaci, asuba ma ta gabato, dolene mubar gidannan dan ko yaushe zamu iya gamo da abinda bamu shirya masaba”.
Duk sunyi na’am da wannan maganar tashi, nan fa suka fara kwasar wad’anda suka sumar suna kaiwa mota, sannan suka tasa k’eyar d’ayar baiwar da wancan, suma.
Yayinda Nuren yad’an bincika gidan, ganin babu wani abunda zasu k’aru dashi yazo suka kama Galadima daya Suma suka fita dashi.
Hankalin Sauban ya tashi matuk’ar tuk’ewa, ya fito yana nufarsu da ta6a jikin d’an uwansa, “Yaa Nuren miya farune? miya faru da Yaa Sam?”.
“Sauban bamu hanya, ba lokacin wannan baneba yanzu”.
Sole Sauban ya matsa baya hawaye Na kwarara a idonsa, suka shinfid’ar da Galadima a bayan mota, sai lokacin Sauban yaga yaran a hannun Aunty salamah da Ameer, da hanzari suma ya nufesu, Aunty salamah ta bashi Abdurraheem, jujjuya yaron yayi yaji kamar baya numfashi, “innalillahi….” yashiga maimaitawa zufa Na keto masa, dolene Yaa Sam ya suma, hawaye yafarayi yana rungume yaron a jikinsa, Tausayin dukkan ahalinsa da suka kwallafa rai ga yaran ya kamashi, musamman ma iyayensu, ya ALLAH nasan bazaka jarabcemu da abinda bazamu iyaba, ALLAH kabamu juriya”.
Muftahu yace, “su shiga mota, duk shiga sukayi, Nuren dasu Ameer suka wuce da wad’ancan sauran wani waje daban, Muftahu kuma ya kira police d’in da suka shirya komai dasu, a hanya suka had’u, sai sukai joining d’insu tamkar tare sukayi aikin, suka kira manyansu suna sanar musu gashifa sun kama wani matashi da baiwar masarauta da yaran….
Wannan labari yama su d.p.o dad’i ya kira IG shima ya sanar masa, yaji dad’i shima, koba komai mai martaba zai yaba k’ok’arin dasukayi, akace yanzu suna inane?.
Amsawa sukai da gasu a masarauta, dan harda Galadima sukayi aikin, yana kuma cikin wani yanayi shida yaran yanzu haka.
Basuda za6in daya wuce suce musu to suma gasunan zuwa masarautar.

Tun’a mota su Muftahu sun gargad’i baiwar nan da d’ayan mutumin akan suce su biyune suka sacesu, inhar sukace basu kad’ai bane wlhy saiya kashesu, sannan su tanaji fad’ar wani abun ba ainahin gaskiya ba, (dan Galadima baya buk’atar police su shiga cikin aikinsa yanzu, yafison saiya kama kowa sannan, dan inhar police suka shiga aikin mutane da yawa zasuyi escape ne) shiyyasa Muftahu yayma wad’ancan gargad’in tunma kan su k’arasa cikin masarauta.

Da yawa wasu basu rintsaba a masarauta gagara badau yau.
Munaya dai dole aka sake d’irka mata allurar barci mai k’arfi, dan kusan kuma haukace musu tayi gabannin asuba, dalilin wani barci daya figeta tayi mafarki mai matuk’ar tada hankali.
Su inno Na zaune har yanzu suna kai kukansu ga ALLAH Muftahu da Sauban suka shigo d’auke da Galadima da suka kamo tamkar gawa, sai Saleem da police biyu dake falo d’auke da yaran sukuma.
Zaram duk suka mik’e suna tambayar lafiya? Miya sami Galadiman?.
Basu sami wata amsaba, saida suka kwantar dashi a gadon sannan Sauban ya share hawayen fuskarsa yana fad’in “suma yayi inno”.
Aunty Mimi da mom sukayi kan Galadima suna kuka, inno tace, “kun samo yaranne?”.
“eh gasu can a falo tareda police, saidaifa duk sun mutu, shiyyasa ma Yaa Sam ya suma”. yak’are maganar yana kuka.
Hawaye suka zuboma inno, waya ta d’auka ta kira papi, Wanda shima dai a zaune suka kwana dagashi har Sarki jalaludden.
A time d’in dama har ankai musu bayanin shigowar su Muftahu d’in.
Yau dai kam tilas Manyan Sarakuna biyu suka nufo sashen Galadima da Kansu, abinda waninsu bai ta6a yiba kenan.
Maganar ganin yara yafara baje Masarautar tun’a daren, dan kowa kunenensa a bud’e yake, da masu fatan a gansun da masu fatan kar’a gansun.

Lokacinda papi da mai Martaban suka iso Inno Na rungume da yaran duka tana hawaye, sukuma su Aunty Mimi suna bedroom wajen Galadima.
Kusan a tare Akash da Dr jalal suka iso dasu papi.
Mai Martaban da papi suka kar6i yaran daga hannun inno, Suna zama bisa kujerun.
Akash wajen Galadima ya nufa, dukda ba shine likitansa Na zuciya ba zai iya bashi taimakon gaggawa, shikuma Dr jalal ya fara kar6ar Abdurraheem dake hannun inno, yan d’ube-dube, yayi Na tsawon lokaci kafin ya ajiyeshi ya kar6i Na hannun mai Martaban, shima yagama duk abinda ya dace ya kar6i Amaturrahman a hannun papi, ajiyar zuciya ya sauke yana fad’in “Alhmdllh duk basu mutuba, allurar barci mai k’arfi sosai suka musu, shiyyasa numfashinsu yay nisa sosai, danta musu k’arfi da yawa, amma idan kuka saka kunne nawasu mintuna saitin jikin zuciyoyinsu zakuji suna motsawa kad’an-kad’an, sai dai ta wannan tafi yin k’asa sosai gaskiya”. Ya nuna Abdurraheem dake hannun inno.
Su mai Martaban suka sauke ajiyar zuciya suna hamdala ga ubangiji.
A cikima Akash nata iya bakin k’ok’arinsa ganin Galadima ya farfad’o, Ahaka su mai Martaban suka k’araso cikin d’akin d’auke da yaran a hannun, Munaya Na gefen Galadima an lullu6a mata bargo batasan wainar da ake toyawa ba, dan barcin nata shine mafita fiye da zama ido biyu.
A gadon suma yaran duk aka shimfid’esu, Dr jalal yad’an musu dabarun likitoci sauran kuma aka barma ubangiji ikonsa Na jiran farkawarsu.
Hankali kuma duk saiya koma ga Galadima da aketa fama.
Har aka kirayi sallar Asubahi babu amo babu labari akan farfad’owar tasa. daga k’arshe dai Akash saida ya kira likitan Galadima na zuciya. Shiya dunga fad’ama Akash d’in yanda yadace yayi, lokacin shiga salla ya saka su mai Martaban fita masallaci dole, sukabar Akash da Dr jalal dake taimaka masa suna aikinsu, saisu Aunty Mimi da suka kasa matsawa ko nan da can, Sauban ma da k’yar su papi suka lalla6asa yabisu salla.

Har gari ya waye sashen Galadima ya cika da manyan masarautar irinsu mama Fulani matan Sarki da sauransu Galadima babu wani bayani, zuwa yanzu ma wasu sun fara tunanin kodai yama mutu ana 6oyewane kawai.
Wajen 8:00am Dr Yaseen Ali Modibbo babban likitan zuciya da akeji dashi ya iso, bisa kiran da Dr jalal ya masa yafad’a masa, dan abubuwan da sukaima Galadima bai farfad’oba Akash yakuma sanarma likitansa, shine yace tofa gaskiya Kodai asamo ainahin likitan zuciya ko kuma su taho dashi kafin cikar awanni 12, idan ba haka ba komai zai iya faruwa.
A k’iyasin da sukayi cikin awanni 12 bazasu Isa india ba, tunda duk tsiya sai an samu jirgi mai tafiya, sannan ma kafin komai ya biyo baya. Hakkane yasaka Dr jalal kiran Dr Yaseen Ali Modibbo d’in, cikin amincin ALLAH kuma ya amsa zaizo d’in, saikuwa gashi ya iso.
Canjama Galadima d’aki akayi, dukkan kayan aikin da Dr Yaseen yazo dasu aka shigo dasu, rufe d’akin sukayi suka duk’ufa su uku kansa suna taimakon Dr Yaseen d’in.
Sun jigata kwarai da gaske kafin zuciyar Galadima tafara bugawa k’asa-k’asa, sai numfashinsa yafara fisga yana k’ok’arin fita. Duk ajiyar zuciya suka sauke. Suka cigaba da aikinsu, ana sakama Galadima wani abu a k’irji kamar dutsin guga, saiya girgiza sannan a cire, akuma maidawa. Basu barsa ba saida yasaki wata ajiyar zuciya mai matuk’ar sauti, harsu mai Martaban dake falo saida suka jiyosa kuwa.
Wannan ne yasaka zukatan doctors d’in uku sanyaya, Dr Yaseen da Dr jalal suka had’a baki wajen fad’in “Alhamdulillah!”.

Numfashin Galadima ya dawo dai-dai, amma sun masa allurar barci danya samu nutsuwa.
Yaranma an kawosu ne Dr Yaseen ya kuma bincikawa, shima dai yace suna da ransu, amma Abdurraheem yanada ciwon zuciya shima, shiyyasa yafi sauran y’an uwansa jigata, ALLAH nema dai yay rabon yanada sauran numgashi, amma allurar tamasa k’arfin da zata iya dakatar da bugun zuciyarsa. Suma dai sun kuma samun taimako, musamman ma dai Abdurraheem da tausayinsa ya kama mutane da yawa a wajen.

*_2:00pm_*

Zuwa wannan lokacin Munubiya da mama Rabi’a da Ayusher Feena duk sunzo masarautar, Hakama baba k’arami da daddy, dan an sanar musu samo yaran da halin da galadima yake ciki.
Amma saboda kara irinta Abba da innarsu Munaya sai suka bar su Baba k’arami da maman Fauziyya da mamansu yaa Hameed, maman Safara’u suka taho, sai innaro da gwaggo Safiyya.
Ba’a barin wani bak’on fuska shigowa masarautar a yau, amma su sai mai Martaban yasa aka shigo dasu, basu samu ganin ko d’aya a cikin su Munaya ba, saidai Munubiya da aka shigar d’akin galadima inda Munaya ke kwance, Sauran kuma sun shiga ayarin y’an zaman jigum-jigum da jiran tsammani.

Har zuwa wannan lokacin Galadima da Munaya babu Wanda ya farka, Amaturrahman da Abdurrahman dai sun farfad’o, sai dai suna kuka ko fita bayayi.
Wanka laraba ta musu aka gasa musu jikinsu sosai, yau dai dole aka nemo madarar da Galadima bayason susha d’in, ita aka dama aka basu sukasha, aiko sun shata sosai dan yunwa sukeji, bayin ALLAH, rabonsu da abinci tun jiya da rana kusan I war haka d’in.
Tausayinsu ya kama Munubiya dake basu madarar, tana yi tana sharar hawaye, da da farko nono inno tace ta basu, sai papi yace, “a’a kar ayi wannan gangancin, dan ba’asan abinda ALLAH zaiyiba wataran, ko akwai k’addarar aure a tsakanin yaransu, kar azo ayi Dana sani a watarar da baza’a iya maido wannan ranarba balle a gogo 6arnar da akayi”.
Kowa ya gamsu da wannan magana, dan haka Muftahu yafita suka nemo madara shi da Saleem.
Shine aka basu.

Baiwar da aka kami da mutumin kuma suna hannun police, kuma kowa yaji cewar tana cikin bayin gidan wad’an da aka aminta dasuma sosai, saidai ba’asan ta wane sashe bace.
Wannan Abu ya tsurar da zukatan Sauran bayin, dan dolene ya shafesu.

Hankalin Uwargidan Sarki Sarauniya Zulfah (mahaifiyar su matawalle) a tashe yake, amma dayake ta iya takunta bazaka ta6a fahimtar haka ba, saima nuna tsantsar damuwarta akan lamarin da tayi fiye da sauran matan Sarki. dama kuma tafi nuna kulawarta ga Galadima kowa yasan wannan, shiyyasa babu Wanda yakawo wani Abu game da ita, saima wasu daban ake zargin.

Munaya da Galadima sun farfad’o ne kusan time d’aya, amma Galadima ya riga Munaya, dama allurar awanni 4 kacal aka masa, da Sunan ALLAH a bakinsa ya farka, sannan yafara kiran yaransa d’aya bayan d’aya yana fad’in karsu tafi su barsa..
Rik’eshi Dr Yaseen yayi yana fad’in “ka kwantar da hankalinka ranka ya dad’e, dan zuciyarka tana cikin yanayin jiran k’iris ne, inamaka albishir da cewar yaranka suna raye, yanzu nan zakagansu insha ALLAH”..
Galadima ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana kallon Dr Yaseen, ya lumshe idonsa a hankali sannan ya bud’e, hanunsa ya d’ora akan saitin zuciyarsa saboda wajen yamasa matuk’ar nauyi.
Ana haka Dr jalal ya shigo d’auke da yaran biyu, dan Abdurraheem shi yanan a d’akin kusa dashi bai farfad’o ba.
Tunda Galadima yaga yaran sa suna a raye saiya kuma rungumesu a k’irjinsa da Dr jalal ya d’ora masa, wasu hawaye masu zafi suka gangara gefen kunnensa.
Dr Yaseen yaji dad’in kukan da Galadima d’in yakeyi, dan zai rage masa rad’ad’in da yakeji da nauyin zuciyar, hakan ya nuna aikinsu zaiyi k’yau insha ALLAH.
Galadima ya dad’e rungume da yaran, saidaga baya ya farga babu guda d’aya.
A hankali ya bud’e baki yana fad’in, “ina d’ayan?”.
Murmushi Dr Yaseen yayi, yace, “gashi a gefenka yana barci shima”.
Juyawa Galadima yay ya kallesa, ganin d’an cikin yaron Na motsi alamar fitar numfaahi sai dad’i ya kuma ratsashi, ya lumshe idonsa yana yun k’urawa zai tashi zaune, taimaka masa. Dr Yaseen yayi, yatashi rik’e da yaransa, kwantar dasu yayi sannan ya matsa ga Abdurraheem hannunsa dafe da k’irjinsa har yanzu, rankwafawa yay kan yaron ya sumbaci goshinsa da kumatunsa, sannan ya shafa kansa la66ansa suna motsawa alamun yana masa addu’ar fatan samun lafiya a garesa shima.

A 6angaren Munaya Itama tana farkawa da kuka ta farka, tana kiran yaranta, itadai afad’a mata idan sun mutu kawai saita hak’ura.
Rungumeta Munubaya tayi tana lallashi da mata albishir d’in dawowar yaran garesu, hakan yasaka Munaya d’agowa da sauri tana kallon Munubiya, “Sweetheart da gaske kikeyi?”.
“da gaske nakeyi Sweetheart, yanzu haka suna tare da mahaifinsu”.
Dad’i ya ratsa Munaya, ta kuma k’ank’ame Munubiya suka rungume juna suna kuka da dariya lokaci d’aya.
Hakan kuma saiya sanya su inno kukan tausayinsu da sha’awar wannan k’aunar juna nasu.
Saboda su mai Martaban sun shiga wajen Galadima sai akace ita Munaya tayi wanka kozataji k’arfi kafin su fito.
Bata musaba ta amince, ruwa mai zafi laraba ta had’a mata, tashiga wankan. Tanayi tana kukan farin ciki. bata cuci kantaba tayi wanka sosai ta gasa jikinta.
Kafin ta fito an gyara d’akin tsaf, sai k’amshin daddad’an turaren d’aki yakeyi, babu kowa duk sun fice.

Su mai Martaban suna tare da Galadima, sunyi farin cikin tashinsa, hakama yaran. sunkuma yima Abdurraheem addu’ar tashi shima. Sun d’an jima a d’akin, dan har saida aka shigo dasu Dady da baba k’arami, Yaa marwan, Yaa Hameed suma suka gaidashi da masa jajen ALLAH ya kiyaye gaba sannan suka fita gaba d’aya.
Daga nan manyan irinsu mama Fulani, inno matana Sarki da sauran su duk suka shigo suma, harda su innaro da akaita kuka.
Galadima dai Kansa kawai yake iya d’agawa, idonsa a lumshe. Baya buk’atar kallon kowa a cikinsu.
Su inno duk tausayinsa ya kamasu.
Innaro aka share hawaye tace, “barka da arzik’i kaji, ALLAH ya kiyaye gaba, ya shiga tsakanin nagari da mugu, ya tona asirin duk makirin dake cikin wannan satar yara”.
Duk da amin suka amsa. Galadima ma yace amin akan la66ansa. sai tunani yake ina Munaya take?, dan hankalinsa yafara tashi da rashin gilmawarta, musamman daya tuna a halin daya tafi itama ya barta.
Yadai kasa daurewa ya bud’e baki da k’yar yace, “Mom ina Munaya wai?”.
Saida mom ta matso da kunnenta sannan tajishi, tasan yana lafiya ma ya aka k’are da k’asaitar magana balle yanzun. Murmushi tayi, tace, “tana d’aki, itama sai yanzu ta farka, dan dole aka sake mata allurar barci bayan tafiyarka, waccan bata dad’eba ta saketa”.
Tausayin Munaya ya kuma kamashi, ya jinjina kai yana yunk’urawa zaune sosai. Cikin yamutse fuska yace, “Mom nima yakamata nayi wanka Na rama sallolin dake kaina”.
Mom tace, “to bara a kira su Muftahu su kamaka ”.
Kansa ya girgiza mata da mata alamar, zai iya da kansa.
Mom tace, “Alhmdllh”. Rigarsa ya jawo yasaka, dan da dagashi sai best. d’aukar Abdurrahman da Amaturrahman yayi ya fito, yabar mom tana gadin Abduraheem dabai farko ba. babu kowa a falonsa Dan duk sun fice.
Da k’afa ya turo k’ofar, Munaya Na zaune a bakin gadon rik’e da mansa zata shafa amma dukta kasa, burinta taga halinda Galadima da yaranta suke ciki kawaine damuwarta, gashi har yanzu babu Wanda yazo yakirata akan su papi sun fita. bud’e k’ofar ya sakani d’ago ido. Zummbur na mik’e tsaye ganin Galadima rungume da yaran, ai yau nama manta dawata kunyar towel na d’aura, hawaye suka shiga zarya tsakanin idona da kumatu, Galadima ya tako a hankali zuwa gareni idonsa a kaina. Da sauri namatso garesa nima, nahad’ashi shi da yaran na rungume ina sakin kuka mai k’aramin sauti.
Shiru yay kawai ya zubama gashinta ido yana tausaya mata daga ita har yaran, ansakasu a yak’in dabasu San mafariba, ya godema ALLAH da yarannan sunada sauran numfashi a duniya. Da baisan yanda zaiyi da munaya ba. Ganin kukan nata zaiyi yawa ya bud’e baki da k’yar yace, “ya isa mana”.
d’ago idanu nayi na kallesa, cikin muryarta data dishe saboda kuka nace, “Nagode yalla6ai, dasun mutu nima mutuwa zanyi”.
Murmushin gefen baki yayi, cikin d’age gira d’aya yace, “dama ana sonmu haka?”.
Sai yanzu kunya ta kamani, nai k’asa dakai ina kallon k’afafunmu.
Bai sake cewa komaiba ya ra6a ta gefena yaje ya shimfid’e yaran akan gado.
bathroom ya nufa yana cire rigar jikinsa, nidai Na k’arasa gadon Na rungume yaran ina sumbatarsu, wani dad’i da tsantsar farin ciki Na ratsani, Na d’aukesu Na fara shayar dasu ko zasu rage nauyin da sukamin, aikam kamar jira sukeyi suka kama sha. Hannun rigar namijin Na d’aga saboda tanan muke gane shaidarsu, ganin Abdurrahman ne saina fara tunanin ina Abdurraheem shikuma?, hankalina yaso tashi amma saina daure ina jiran Galadima ya fito naji daga garesa.
Galadima dake kallonta bata saniba ya d’an cije lips, ya tabbatar yanzu tana son yaransa, amma baisan miyasa take ignoring d’insu ba idan yana waje? Kokuwa tsabar jan ajinne oho?.
Har Lokacin daya fito wankan tana shayar dasu, ta shafa kan wannan ta shafa Na wannan, sosai suka birgeshi itada yaran, jin kamar motsi yasakani kallon wajen, da sauri na janye yaran daga bakin nono naja towel d’in na rufe abinna ina turo baki gaba.
Baki ya ta6e yashiga takowa inda muke, ya rankwafo kaina ruwan fuskarsa yana d’iso min a jikina, a kasalance yace, “wane darene jemage bai ganiba malama, tunkan su sha ni……..”.
Da sauri na saka hannu na toshe masa baki.
Zama yayi yana janye hannunna, cikin waro idanu yace, “to mikike tunanin zan fad’a? lallai kinfi k’arfina, niba can Na dosaba to”.
Sosai naji kunya, na sauke yaran a kan gadon na sakko, zuciyata cikeda mamakin sa, ya d’aure fuska yana basarwa yayta sakin magana kuma kamar bashi yayiba.
Ficewata nayi bayan na d’auki bathrobe d’insa na d’ora akan towel d’in jikinna.
Wani kallo ya bita dashi yana ta6e baki, kafin ya maida ga yaransa daketa kalle-kalle, ya shafa kumatunsu sannan ya mik’e zuciyarsa na tunanin su Momma, addu’arsa d’aya kar wani ya sanar musu.

Kasa fitar nayi saboda jin kamar da mutane a falon da zanbi ya sadani da 6angarena.
Badan nasoba tilas Na dawo baya.
Galadima dake gaban mirror yana shafa mai yana kallonta ta ciki, amma sai yayi biris tamkar bai gantan ba.
Komawa nayi na zauna a bakin gado ina tunanin mafitar yanda zan samu kaya, da jin haushin sharenin da yayi.
Ana haka mukaji knocking, saida ya kalli Computer d’in yaga Mom Ce d’auke da Abduraheem sannan ya mik’e yana amsawa..
Zuwa yay ya bud’e mata, bata shigoba ta mik’a masa yaron da har anmasa wanka Ashe, ta mik’a masa kaya a leda tace na Munaya ne.
Galadima yace, “mom ya tashine?”.
“ya tashi, tunma fitowarka babu dad’ewa, harma an masa wanka”.
Sumbatar kumatun yaron yay yanama mom sannu

Idonsa akan yaron yana kuma sumbatar goshinsa cikin lumshe idanu ya k’araso inda nake dana zuba musu idanu cikeda sha’awa.
Kusa dani ya zauna ya d’ora minshi akan cinya. nima rungume kayana nayi na sumbaci goshinsa, inason bashi abinci amma inajin kunyar Galadima, gashi ya zubamin ido yak’i tashi.
Lura da hakan dayay ya sakashi yin miskilin murmushi ya mik’e yabar wajen.
d’an hararan bayansa nayi ina fad’in mugunta dai babu k’yau a kan la66ana………………???

 

“Hummm fans nasan kwace wai ina Harun ne???, kumuje zuwa dai danjin ina ya shige haka? Ita kuma sarauniya Zulfah (uwar gidan Sarki mike matsalarta)?.????

 

 

 

*_Ya Rabbi ka gafarta ma iyayenmu_*??????
*_typing??_*

?? *_HASKE WRITERS ASSO….._*

*_?RAINA KAMA…..!!?_*
_(Kaga gayya)_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply