Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 26


Raina Kama Book 2 Page 26
Viral

~Book 2~ ????2?6?

……………….MC yafara shelanta cewa wannan bikin sunafa an had’ashi da bikin birthdays ne, domin ranar haihuwar yaran tai dai-dai da ranar haihuwar iyayensu, dan haka suka had’e wannan biki a yau guri d’aya, dan a waccan ranar murnar haihuwar bata basu damar yanka cake ba??.
Dariya aka sanya, saboda a yanayin barkwanci mc yayi maganar, Galadima kam ai kod’an murmushin ma baiyiba, garama Yaa marwan ya murmusa.
Galadima ya kalli munaya, cikin maganar nan tasa mai kamada an masa tilas yace, “Kina da sa’a”.
“Sa’a kuma?”. ‘Munaya ta fad’a cikin yanayin mamaki’.
Harya bud’e baki zaiyi magana sai kuma ya basar. ganin haka itama Munaya saita sharesa, dan takula yau y’an mulkin ne a kansa.
Saida ya gama shan k’amshinsa sannan yace, “wannan ne karon farko da Sameer yata6a bikin birthday”.
Baki munaya ta d’an ta6e, tana fad’in “Humm, kodai y’ay’anka suna da sa’a?, domin dai a dalilin haihuwarsu ne kayi”.
“ko kina jealous ne?”. ‘yay maganar cikeda basarwa’.
tura baki tai gaba.
Idonsa akan yaransa yace “idan kika bari na kama wannan bakin a wajennan humm.” ya cije lips d’insa.
Sanin k’aramin aikinsane ya akaita abinda ya fad’a d’in ya sata saurin gyara bakinta , tad’an saci kallonsa, ya wani Fiske tamkar ba shine yay maganar ba ma. ita dai tana mamakin kasaita da izza irinna bawan ALLAH n nan, jinin mulki yana da matuk’ar k’arfi a jikinsa. tunaninta ya katse lokacin da hankalinta ya koma kan abinda ke faruwa a hall d’in

Khaleel da Aiyaan, Aryaan ne suka turo cake mai k’yau da tsari, Wanda yasha kwalliyar White and Golden, an saka sunan Galadima da shekarunsa 31years a sama, a jikinsa kuma daga can k’asa ansa Muhammad Sameer (Dadyn Triples), an d’ora candlestick??guda uku, Sai hotonsa da yay k’yau sosai cikin shigar sarauta.
Galadima ya kalli Sauban da Samha, yasan dai wannan aikinsu ne, k’in kallonsa sukayi sukam ballema suyi gamo da tsarabar harara??.
Ita Munaya ma sai yanzu taga Su Aiyaan, batayi zaton anzo da suba, tunda bataga yaran gidansu k’anana ba a waje, sai manya maza da matan Na ma’auri.
MC ya taso k’eyar su Khaleel har inda su Galadima suke zaune, kowanne aka d’ora masa yaro d’aya, suma mik’ewa sukayi bisa umarnin MC d’in, a tare suke takawa ita da shi, sai k’yastu ake zuba musu, masuyi a waya da masu cameras, sai gidajen TVs d’in da aka gayyata suna nuna live. Sun Isa gaban cake d’in hannunsa rik’e da sandarsa, kaikace sarkine da kansa (gaskiyar Munaya Galadima akwai k’asaita, Kodai sarkin da Kansa ya shafa masa lafiya??).
Bayan anmasa wak’ar happy birthday yayma munaya nuni waita hura candles d’in.
Cikin k’asa da murya tace, “yalla6ai bafa haka akeyiba, ka hura abinka da kanka”.
Hannunta ya kama ya matsa yanda zataji zafi, yace, “zakiyi?”.
Ai baima kai k’arshen maganarba ta risina ta hure wutar, hall d’in ya d’auki tafi. cake d’inma dan rigima wai saidai su yanka tare.
“haba yalla6ai, saikace Na wani aure?”.
Cikin ta6e Baku yace, “wama ya sani kona auren ne”.
Shiru tayi bata tanka ba, dan itadai fatanta a rabu lafiya, hannunta ta d’ora kan nasa dake rik’e da wuk’ar suka yanka taren. nanma dai tafin akayi. Ya lakata a d’an yatsa ya duk’o gasu Aiyaan ya daddan gwalama yaransa a hanci da kumatu, sannan ya juyo ga Munaya da haushi ya kamata, ai ita yakamata ma yafara sawa ba yaranba.
Itama akan hanci ya shafa mata yana fad’in “yalla6iya haushi kikajine?”.
Kafin tabashi amsa yakuma lakata ya shafama Aryaan Khaleel da Aiyaan suma.
Dole munaya ta had’iye maganarta. Amma ta kudiri saita rama.

Itama itada Munubiya k’aton cake nasu aka kawo kalar pink and White , Munu da Yaa marwan suka taso a tare.
Munaya da Munubiya suka rungume juna suna maijin dad’in tunawa da ranar haihuwar su, shekaru 20 cif da kwana 7. Sun yanka cake atare suka sakama juna abaki kad’an-kad’an, sannan kowacce cikin son tsokana ta lakatama y’ar uwarta a fuska suka rungume juna suna dariya da k’ananun hawaye, suncika shekaru 20 ranarda yaransu sukazo duniya suma.
Abin ya birge mutane, Munubiya ta matsa ga mijinta ta saka masa a baki kad’an, cikin murmushi yace, “happy birthday my heartbeat ”.
Tace, “Thanks you my luv” k’arasawa tayi ta sakama yaran munaya dasu Aryaan a kumatu, sannan ta sakama nata yaran.
Munaya danta rama abinda Galadima yamata, takai cake bakinsa kamar zata bashi, saida ya bud’e baki saita juya ta shafama yaran Munubiya a kumatu, sannan nata.
Yanda Galadima yay shock akan abinda Munaya tamasa sai mutane suka sanya dariya suna tafa mata, mai martaba da papi ma dai saida suka Murmusa.
Munaya ta dawo ta dangwalama Galadima akan hanci tana masa gwalo.
Shi kansa baisan k’asaitaccen murmushin ya kufce masaba, ya saka handkerchief ya goge yana dawowa mazauninsu ya zauna.

Daga nan aka fara gudanar da wasa, Comedian’s sukazo sukad’an saka mutane dariya, saikuma mawak’a da suka bada nasu salon.
Tun da Galadima ya fara yawaita kallon agogon hannunsa su Muftahu duk suka sake shiri, dan lokaci yana gab kenan.
Galadima yay k’asa da murya batareda ya kalli Munaya ba, yace “ki shirya, shirinsu na farko d’aukewar wutar hotel d’in nan gaba d’aya, na gaba kuma shine banida tabbas. Yara dai ALLAH yana tare dasu, gakuma su Aryaan suma”..
Cikeda mamaki Munaya ta kallesa, sannan ta kalli yaran dake gabansu a wani d’an gado mai k’yau.
Jikinta har rawa yake tace, “yalla6ai mi su Aryaan zasu iya? Please k…..”.
Hannu ya d’aga mata alamar karfa ta ishesa yace, “wani ilimin aduhuwar daji kawai ake laluboshi, kinsan kuwa dolene a gamu da had’arurruka Aciki”.
batada za6i sainyin shiru, ta kalli su Khaleel daketa wasa da abinci a teble da suke zaune hankalinsu kwance. Hawayene ya cika mata idanu, yama za’ayi wad’an can sakarkarun yaran ace suna masu bama yaranta kariya? Yaushe suka gama sanin ciwon Kansu ma balle na waninsu? gaskiya wannan gangancine kawai, tasa handkerchief ta share hawayen da ke k’ok’arin zubo mata.
Duk abinda take Galadima yana kallonta. duk tausayinta saiya kamashi, ya tuna da wahalar datasha, amma bashida za6in daya wuce hakan, kuma itace tabashi k’arfin gwiwa ai, yasaka aransa ko salwanta yaransa sukayi zaiyi tawakkali insha ALLAH.
Duk Wanda yake cikin shirinsu Galadima ya gama shirinsa, haka suma mak’iya masu buri a shirye suke.
Gaba d’aya saura mintuna 25 atashi, saboda gabatowar sallar magrib, a kuma time d’inne Sarki Abdul-fatah da Sarki jalalludden dadai duk wani babba Wanda sukazo tare suka mik’e domin tafiya, ganin haka Galadima yama Yaa marwan sigina da ido akan ya fita da Ameen and Ameena suma, yabi tawagar su papi, dan baya buk’atar a cuta musu..
Jikin Yaa marwan a sanyaye ya d’auki yaran ya fita cikin dabara, yana kallon y’an uku, shidai dan kawai Galadima ya dagene, amma bai kamata a saka yarannan a matsayin tarko ba.
Munaya ma dai ta danne zuciyarta tayi shiru, tanason bama Galadima kwarin gwiwa.
Su papi na fita y’an rawar k’oroso suka fara wasa, mintuna goma da aka basu ya k’are, sai wani mawak’i ya fara nashi, nanfa y’an mata da samari aka samu nayi, dama ganin su mai martaba ne ya sakasu nok’ewa, ana tsaka da cashewa hall d’in yay d’iff, wuta ta d’auke agaba d’aya hotel d’in, mutane aka fara hayaniya kowa na k’ok’arin damk’e dukiyarsa a hannu da k’ok’arin kunna fitulun waya.
Gaba d’aya jikin Munaya yahau 6ari, ta fashe da kuka tana laluben gadon da yaran suke, ruk’ota Galadima yay yasaka a jikinsa, muryarsa na rawa yace, “please ki nutsu”.
“bazan iyaba yalla6ai, karsu……”.
Yay saurin rufe mata baki, da tattausan tafin hannunsa….. A dai-dai wannan lokacinne kuma wutar hotel d’in tadawo.
Hall d’in ya kuma kaurewa da hayaniya, zaram Munaya da Munubiya suka nufi gadon da yaran suke ciki, wayam babu komai.
Munaya tayi luuu zata fad’i, saurin ruk’ota Munubiya tayi, Galadima yataso daga inda yake shima zuwa garesu. hall d’in yagama rikicewa da tsantsar hayaniyar rashin ganin yaran, sai kallon kallo akeyi. Securitys d’in da aka baza sun rikice da wannan tashin hankali, dan sune mutane na farko da za’a fara tuhuma.
Rufe hotel d’in akayi aka hana kowa shiga balle fita,
Galadima ya shafama Munaya ruwa ta kawo numfashi, fashewa tayi da sabon kuka ta fad’a jikinsa, hannu biyu ya saka ya rungume ta shima yana had’iye kwallar bak’in cikin dake Neman zuboma idonsa.
Tausayinsu ya kama mutane da yawa, innaro harda kukanta, hakama inno, abinda yabani mamaki shine tsantsar damuwar da mama Fulani ta nuna, dan itacema tabama Galadima ruwa ya shafama Munaya ta farfad’o.

Da farko Munaya ta d’auka ko Galadima wasa yake mata yasan inda yaran suke, amma ganin damuwar da yake ciki saita kuma rikicewa, dandanan numfashinta yafara gagarar k’irjinta, ta mik’e a kid’ime, dan taji a jikinta kuka sukeyi, nononta sai tsitstsirawa suke, wani jirine yafara hajijiya da ita da zuciyarta ta k’iyasta mata zafa su iya kashe mata yara, luuuu tayi baya Galadima ya ruk’ota. sume musu ta kumayi.
Hankalin Galadima kuma tashi yayi, dole ya d’auki Munaya aka sakata a mota suka bar hotel d’in.
Sauran mutane kam kowacce mota zata fita sai an binciketa.
Yayinda Securitys d’in suka bazu ko ina na hotel d’in ana bincikawa.

Gida aka wuce da munaya, har suka isa tana jikin Galadima, yanata murza tafin hannunta kozata farfad’o, har d’ora bakinsa yayi akan nata ya jawo iskar numfashinta amma a banza, hakanne yakuma tada hankalinsa.
Kai tsaye d’akinsa ya wuce da ita, ya shimfid’eta a kan gadon ya cire mata alk’yabbar jikinta, Akash suka k’araso da hanzari shima, taimakon gaggawa yafara bata shida doctor jalal, cikin amincin ubangiji saigashi takawo numfashi, bama su bari tadawo dai-dai ba suka mata allurar barci.
Suna fita Galadima ya cire rawani da alk’yabbar jikinsa shima, ya sassauta bottom d’in wuyan rigarsa.
Safa da marwa ya shigayi a tsakar d’akin yana Mirza agogon hannunsa Wanda daka gani kasan ba normal agogo bane,.
Wayarsa datai k’ara yay saurin d’auka, d’agawa yayi yasaka a kunne, “Muftahu ya ake ciki?”.
Cikin hakki Muftahu yace, “komai yana tafiya yanda ya kamata ranka ya dad’e, har yanzu gamu muna bin bayansu, amma munkai inda yakamata ka fara Controlling namu, yanzu mun…….”
Da sauri Galadima ya katseshi ta hanyar fad’in “karka damu ina kallon Ku, saidai kilometer’s d’in dake tsakaninku dasu fa yakai 1½, Saleem da Sauban sunfi kusa dasu, dan haka ku k’ara azama. daga lokacin da suka farga da abinda nasaka jikin Amaturrahman tabbas zasu cireshi, kuma zamu rasasune gaba d’aya”.
“Ok babu damuwa, ranka ya dad’e”.
Yanke wayar sukayi, Galadima ya bud’e wani k’aramin akwati ya fiddo kayan aiki wanda a ready dama yagama had’a komai, bajesu yayi akan gadon kusada Munaya, ya zauna yafara Control cikin matuk’ar kwarewa.

Saleem ya kira aunty Salamah wadda itama take tare dasu Ameer yaran da suka sace Muftahu, d’agawa tayi jikinta na rawa, “Saleem kuna inane?”.
“Aunty Salamah gamunan bayansu kad’an, amma mund’an basu k’afa saboda na kula sunfara fuskantar muna bin su, yanzu dai haka mun ajiye motarmu mun samu mashin”.
“Hakan yayi, insha ALLAH indai ta Anguwar da muke tsammanin zasu shigane kamar yanda kaji Harun d’in yay magana to tabbas mu dai mun iso, saidai suzo su iskemu, ka kira yalla6ai ka sanar masa yakamata ya fito yanzu”.
“no Aunty Salamah, bazai yuwu boss yabaro masarauta ba yanzu, saiya tabbatar mun Isa, saboda dukma inda suka shiga yana bibiyarsu, dan bazai saka yaransa a matsayin tarko ba babu tsaro k…….”
Tai saurin k’atseshi ta hanyar fad’in “yauwa ina zargin kamar gasunan a wata bak’ar mota sun wicemu fa”.
“Alhmdllh, su Ameer Susan yanda zasuyi su bisu bara na kira boss”.
“ok”. Kawai Aunty Salamah ta fad’a ta yanke wayar.

Kiran Galadima Saleem yayi, bugu biyu ya d’auka, “Saleem mike faru yanzu?”.
“Ranka ya dad’e gamu dai biye dasu, amma Aunty Salamah tacemin gasu tagansu”.
“wacece Salamah? ”.
Gaban Saleem ya fad’i, dan ya manta Galadima baisan Salamah ba, “Am sorry sir, idan komai ya dai-daita zan maka bayani”.
“Saleem!!!”. Galadima ya kirayeshi a tsawace.
Saida Saleem ya janye wayar akunnensa, muryarsa na rawa yace “ka yarda dani sir, wlhy itama ta kwarai ce”.
Ajiyar zuciya Galadima yayi, muryarshi cikin tsantsar damuwar yace, “wannan anguwar da kuke tanada hanyoyi da yawa, dan haka Ku fara amfani da live GPS navigation maps naku, yanzu zanyi settings komai yanda zaku ringa ganinsu duk layin da zasu shiga insha ALLAH, waye yake driving d’in a cikinku?”.
“nine sir”.
“ok bama Sauban wayar”.
Saleem ya mik’ama Sauban wayar, Galadima na fad’a masa yanda zaiyi, shikuma yana Controlling maps App d’in dake cikin System d’in cikin kwarewa, (dan shima Galadima bai barsa hakaba, dukda bashida ra’ayin karantar wannan fannin saida ya tsaya tsayin daka ya koyan saboda irin wannan ranar).
Saida Galadima ya tabbatar komai ya dai-daita, sannan ya kira su Nuren ma, suma suka dai-daita komai nasu, cikin sauk’i duk suka koma ganin inda yaran suke, saboda Galadima ya saka Abu jikin Amaturrahman, dukda bawai hotonsu ko video suke kalloba kai tsaye.
Duk da haka Galadima ke fad’a musu su shiga layin haggu, ko dama, kosu canja hanya dadai sauransu.

Duk Wanda yake a wannan masarauta yau hankalinsa a matuk’ar tashe yake, saifa kallon kallo da hasashen juna ake a zuciya, kowa yana zargin Wanda ya raina.
Hankalin Abie a matuk’ar tashe ya nemi ganin Galadima, koda sarkin k’ofa yazo yana knocking Galadima bai amsaba, kuma yana kallonsa ta CCTV.
d’an aike ya koma ya sanar Galadima ya kulle kansa a d’aki yak’i bud’e k’ofa.
Papi inno ya kira, yace maza taje sashen Galadima taga mike faruwa.
Ko kuyangi inno batajira sun mata rakkiyaba, hasalima babu Wanda yaga fitowarta a sashen mama Fulani, dan kowa a rikice yake da wannam bak’on lamari na satar yara.
Galadima daya ga sarkin k’ofa yabar wajen ya mik’e shima daga gaban kayayyakin da yake aikin, shaddar jikinsa ya cire yasaka bak’in wando da t-shirt, ya kawo bak’ar jacket mai k’yalli kamar rigar sanyi ya ajiye gefe, a bakin gadon ya zauna yana d’aura takalminsa yana cigaba damasu Sauban da Nuren bayanin hanya, a dai-dai lokacinne Inno ta iso sashen nasa, da hanzari Sarkin k’ofa ya bud’e mata k’ofar, bata jira wani isoba ko masa sallama ta turo k’ofar falonsa ta shigo, babu kowa a falon, komai ma a kashe yake. Bedroom d’insa ta nufa, nandai saida tayi knocking kam, saidai kafin yay yunk’urin tasowa ya bud’e mata ta turo k’ofar ta shigo, mik’ewa yay yana kallonta da d’aukar jacket d’insa zai saka.
Ajiyar zuciya inno ta sauke, saboda ganinsa normal.
“Ranki ya dad’e da kanki? lafiya dai ko?”.
“Inafa lafiya Muhammad? takawa ya aiko a kiraka ance ka kulle kanka, gashi baka sanar mana halinda yarinyar nan take cikiba”.
Galadima yace, ba kulle kaina nayiba, bansan kuma d’an aiken daga papi yakeba” ya juya yana kallon Munaya da cigaba da fad’in, “itama ta farfad’o, amma sun mata allurar barci”. ‘ya k’are maganar da daidaita zaman kwalar rigar jacket d’insa’.
Ajiyar zuciya inno ta kuma saukewa, tace, “to Alhmdllh. ina kuma zaka naga kana shiri?”.
Wani murmushin takaici yayi zuciyarsa dake gudun daya wuce kima da suya ya dafe, Inno dai ta zuba masa ido, takowa yay inda take ya kama hannunta ya rankwafo (dan yafita tsaho) ya d’ora bisa kansa, cikin murya mai nuna tsananin karsashi da alwashi yace, “kisamin albarka inno, zanje farautane”.
Da sauri ta janye hannunta daga kansa tana matsawa baya, “Muhammad mikake nufine? kana ganin tashin hankalin da muke ciki shine zaka k’irk’iro mana wani kuma? kana tunanin wad’annan mutanen zasu barkane? dama kai suke fako, shiyyasa sukayi tarko da bayin ALLAHn dabasu ji ba basu gani ba, su takawa cikin k’ok’arin d’aukar mataki suke, yanzu haka naga IG da kansa gashican ya iso bisa umarnin kiransu”.
Galadima dake tattara abinda zai amfani dashi yana zubawa a aljihu, yace, “inno Muhammad Sameer d’inku ba ragon namiji bane da zai zauna jiran Police d’in da suka gaza gano wad’anda suka durk’usar masa da mahaifi tsawon shekaru a yanzu kuma nayi tunanin zasu iya dawomin da gudan jinina har uku, ba sune sukamin tarko ba nine namusu tarko, idan tsoron na mutu kuke, Ku cire inno, ko babusu mutuwa tabbataccen abune rubutacce a kundina, kimin addu’a saina saina dawo”..
Biyosa inno tayi har babban falo tana Kiransa amma yak’i dakatawa, saima d’aga mata hannu da yakeyi, yana gab da zai fita ya juyo yana fad’in “karki d’aga murya da yawa ranki ya dad’e, dan kunnen magauta a bud’e yake”.

Yana fitowa Sarkin mota ya taso, dan suna zaune jigum-jigum a rumfar bunun dake sashen na Galadima, duk gaisuwar da suke masa babu ta wacce ya amsa, yau kam ko d’aga hannun basu samuba ma.
Basu damuba dan dolene kowa yamasa uziri.
Da kansa ya bud’e mota ya shiga mazaunin driver, Sarkin mota daya k’araso yace, “ranka ya dad’e ka gafarceni gani”.
Da hannu yamasa nuni da gefen mai zaman banza batareda yace uffan ba.
Sarkin mota bashida za6in daya wuce zagayowa ya shiga.
A 360 Galadima ya ja motar, kamarma ya manta yana cikin masarautane, saida suka fito gaba d’aya sannan ya bud’e baki da k’yar yace, “ka dinga kallon bayanmu, dan nasan dole za’a samu masu binmu”.
Da “to” sarkin mota ya amsa cike da girmamawa.
Sarkin mota yace, “tabbas ranka ya dad’e ana binmu”.
Cije lips Galadima yayi, ya canja hanya, cikin salon iya taku suka 6acema su Harun dake bin su tundaga masarauta.
Hankalin Harun ya tashi kwarai da gaske, dan bai shirya fito na fito da Galadima ba yanzu, saiya cimma burinsa, daga nan komai ta fanjama fanjam, iya zagaye-zagayensu baiga ko motar datai kama data Galadima ba.

Shima yana 6ace musu ya dawo kan titi sosai, Maps d’in GPS ne yazama jagoran Nuna masa hanya, da taimakon Sarkin mota kuma dayasan gari. Danshi Galadima ba tuk’i yakeba idan yazo 9ja, saidai idan ta kama tilas babu yanda zaiyi kamar irin haka.
Sunyi tafiya mai tsawo, yayinda yake Communication dasu Nuren dasu Saleem. A haka ya iso inda suke, duk fitowa sukayi daga motocin, shima Galadima ya fito, idonsa akan agogon hannunsa, yad’an kallesu sannan ya koma kan waya yana fad’in, “maps d’in ya nuna suna a wajennan, kunga kenan tsakanin gidajennan guda hud’une dake kallon juna?”.
“kwarai da gaske suna nan”. cewar Muftahu yana furzar da iska.
Galadima yace, “Sauban da Saleem zaku cigaba da Control namu”. ‘yay maganar yana ciro agogon hannunsa ya mik’a musu, “ga wannan kuci gaba da using dashi”.
Suka amsa da “to” suna kar6a. ya mak’ala abinda zai taimaka masa yaji magana, suma su Nuren duk yabasu suka saka.
Har zasu bar wajen ya dakatar dasu ta hanyar d’aga musu hannu, takawa yay gaban k’ofar gidan farko ya haska gaban gate d’in da fitilar wayarsa, babu abinda yake nema, ya matsa na biyu ma haka, komawa yay d’ayan 6angaren, yana haskawa saiga sawun tayar mota data shiga gidan, duk’awa yay ya d’iba k’asar wajen ya shinshina, ya d’ago ido ya kalli gidan yana jizar lips, saiya zubar da k’asar daya d’iba ya mik’e, da hannu yayma Nuren da Muftahu nuni nan ne.
Tahowa sukai garesa, Aunty Salamah datun d’azun suna daga cikin mota suna kallonsu suma suka fito ita da su Ameer.
A tare suka rissina suna gaida Galadima ya amsa yana bin su da kallon mamaki.
Da yake su Saleem sun sanar dasu Muftahu su Aunty Salamah d’in sai Nuren ya kuma yima Galadima bayani.
Aunty Salamah tace, “ka gafarcemu ranka ya dad’e, nasan zakayi mamkin mun shigo abinda ba’a gayyacemu ba, insha ALLAH zakaji dalilin shigowar tamu nan gaba. game da shiga gidan nan mungama komai, maza 5 ne da mata biyu, wad’anda shigarsu ta tabbatar min suna cikin hadiman masarauta su matan kenan”.
Kai kawai Galadima ya iya jinjina masa. daga nan yaymata nuni da zasu iya farawa.
Da taimakon su Ameer suka shiga gidan.

??*???*???*??

Fitar Galadima da kusan awanni hud’u, around 2am Munaya ta farka a firgice, Inno dake zaune akan Sofa, mom da Aunty Mimi kuma a gefen gadon suka kalleta, tashi Mom tayi da sauri ta nufeta tana rik’eta, itama Aunty Mimi ta taso.
Kuka munaya ta sanya tana fad’in “Mom sun mutu ko? Nasan dama kashesu zasuyi, Aunty Mimi dan ALLAH miye laifinsu su? kwanansu 7 fa kacal yau a duniya, mi suka sani game da abinda ake tuhumarsu? An durk’usar musu da kakansu, an hana mahaifinsu nutsuwar zuciya data rayuwa, shin wannan tabon bai Isa a barsu su taso da shiba a rayuwarsu? Har sai an had’a da salwantar dasu kenan?”. ta fashe da kuka maiban tausayi.
Tasowa inno tayi ta zauna a bakin gadon itama, kamo hannun Munaya tayi ta kwantar da ita a jikinta tana shafa kanta, yayinda itama kwallar kebin nata kumatun.
Aunty Mimi da mom ma duk hawayen sukeyi, kalaman Munaya sun ta6a zukatansu.
Lallashinta da magana mai dad’i suka shiga fad’a mata, sai sauke ajiyar zuciya takeyi, ga jikinta yayi ringim da zazza6i saboda nononta sun mata hak’e-hak’e, rabonsu da shansa tunda rana, tausayinsu ya kuma kamata, tasan yunwa da k’ishi ma kawai sun Isa su k’arar da numfashinsu, hawaye masu d’umi suka kuma gangaro mata a kumatu suna sauka jikin inno dake shafa kanta.

Shayi Aunty Mimi ta had’o mata, amma fir tace ta k’oshi, da k’yar inno ta samu ta lalla6ata tasha Quarter d’in kofin.
Mom tace, “wannan nono kid’an matsesu kozasu rage miki nauyi, dan shine yakawo wannan zazza6in”.
Bata musaba aka kawo k’aramin bowl ta matse aciki, Aunty Mimi ta zubar a bayi”..
Tanason tambayar ina Galadima tanajin kunya, sukuma babu Wanda ya sanar mata komai, kodan gudun k’ara tada hankalinta.
Magani suka bata tasha takoma ta kwanta, yayinda sukuma suka mik’e duk suka d’aura Alwala suna mik’ama Ubangiji kukansu, danshi masanin sirrin 6oyene, yana kallon komai, kuma shine zai kawo iyakar komai d’in.

???????

Duk wannan abun dake faruwa su Momma babu Wanda ya sanar musu, saidai sukaji a jikinsu tamkar akwai matsala, sunta kiran numbers amma daga wadda zasu samu a kashe sai wadda network zai hanata shiga.
Sai suka d’aura ko shagalin sunan ne yakawo hakan.

*******************

Tunda Munubiya suka koma gidan kuka takeyi, ko kad’an tak’i sauraren yaran da keta tsula kuka suma, balle tabasu nono.
Ba itaba hatta su Ayusher dasu feena kukan sukeyi, hakama Samha harda shid’ewa, dan itama su tabi bata koma masarauta ba, Yaa marwan da mama Rabi’a ne kawai ke k’ok’arin danne nasu suna lallashinsu.
Yayinda dare yay nisa duk sai suka d’aura alwala suka zo suna mik’ama Ubangijin talikai kukansu da k’ok’on barar bama wad’annan k’anan alhaki kariya da fatan ku6ta.

 

A 6angaren gidan su Munaya kam duk hassadarsu yau dai sun tausayama gudan jininsu da yaranta, sundawo gidane kowa yana sharar kwalla da addu’ar ku6tar yaran.
Ita innarsu Munaya ma ai ba’a magana, ALLAH kad’aine yasan halin datake ciki, ta shige d’aki ta rufe kanta tana jera nafilfili, dan wannance kawai gudunmawar dazata iya bayarwa a garesu akan wannan lamari mai sark’ak’iya da yawa.

Abban su munaya ma yau harda hawayensa, dukda bashi da tabbas akan hasashensa yasan komai zasu iya, saboda SD yanada kusanci da wannan masarautar sosai, duk abinda ke hannunsa da bayanan daya ajiye ya shiga tattarasu waje d’aya……………???

 

??Duk nisan jifa dai k’asa zai fad’o, kwana 99 na 6arawo, 1 kuma tak namai kaya.????

Fans insha ALLAH dai abuwa sun fara warwarar zare, sai mubi su Galadima muga yanda zasu dawo mana da triplets d’inmu gida??, yau Munaya tabani tausayi daga ita har Galadima, dan shima dai dannewa kawai yake saboda jarumta, ALLAH ya rabamu da sharrin mak’iyi komai k’an k’antarsa, Harun da sauran munafukai MAZA BISA KANKU????????????????????.

Barkanmu da dawowa my sweet fans????.

Yau bana cikin yanayin dariya??

 

 

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*??????
*_typing??_*

?? *_HASKE WRITERS ASSO….._*

*_?RAINA KAMA…..!!?_*
_(Kaga gayya)_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply