Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 20-21


Raina Kama Book 2 Page 20-21
Viral

~Book 2~ 👉🏻2⃣0⃣➖2⃣1⃣

 

 

…………….Tafiyar su Abba dai ta kankama, dan Abba ya matsa ainun, dole Galadima ya musu dukkan shirin daya kamata, zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu jirginsu zai d’aga.

Da yake yau Saturday ce babu aiki, amma hakan bai hana zama gidan shiru ba, su Sauban da innarmu sun fitane, nikad’aice a gidan sai jakadiya, nima barci nake suka gudu suka barni a gidan.

Yunwar dana farka da ita ta tilastamin sakkowa k’asa neman abinci, dan a ‘yan kwanakinnan nazama wata acici, danaci abinci danaji sabuwar yunwa, narasa wannan dalili.

Bannemi kukun gidanba ma ko cikin bayi, nahau dafa abinda zaimin saurin dahuwa, kafin ya dahunma saida na d’umama madara nad’ansha sannan ‘yar nutsuwa tazomin. ina sauke abincin kuwa Na juyoshi a plate na koma sama. tun a hanya naji k’amshin turarensa, ban kawo yashigo gidan bane nidai na ida hawa. ban tsaya faloba na shige bedroom.

Galadima dake zaune a sofa yana kwance igiyar takalminsa ya d’ago ido yana kallona da amsamin sallamar danayi.

Sandunan wasan Golf d’insa daya shigo dasu ya zube a carpet d’in gaban gadon na janye gefe na zauna, dan nafijin dad’in xaman k’asan yanzu.

Shidai bai fasa kallona ba baikuma bar cire takalman ba,  dan abincin dayaga ta zubo yakema kallon mamaki, kafinfa yafita harda kukanta ta farka wai yunwa takeji, haka dole yafita yasaka kuku dafa mata abinci, baibar gidanba saida taci takoma barci, da fitarsa kuwa baifi 3hours ba, amma jita yanzu dawani abincin.

Ya janye takalaman daya gama cirewa a gefe ya zubamin ido kawai, dukda abincin nada zafi haka nakecinsa da sauri-sauri.

Janye plate d’in yayi daga gabana, fuskarsa babu walwala yace, “waike mike damunki hakane?”.

Idona harya fara tara kwalla cikin marairaicewa nace, “dan ALLAH kabani, wlhy yunwa nakeji bata wasaba”.

Rasa ma mizaicemin yayi, ya zubamin ido kawai yana kallona. a mamakinsa saiyaga ma ina hawaye, abincin ya tura min yana fad’in “wannan cin naki yayi yawa, gama muje wajen Akash ya dubaki”.

Uffan bance masaba, shima bai sake tankawa ba yanufi bathroom, yaja wasu mintuna saigashi ya fito d’aure da towel, kallo d’aya namasa na janye idona, wannan abun nasa yafara damuna, yanzu baijin kunyar yafitomin a duk yanda yaso, ko yana mantawa bashi kad’ai bane a d’akin oho.

Shima dai kallonta kawai yakeyi, dan nacinye abincin plate d’in tas, a ransa yace shiyyasa taketa zama k’atuwa, irin wannan ci haka.

Oho bansan yanayiba, nidai mik’ewa nayi nashige bathroom abuna, nasamu nai wanka da ruwa mai sanyi dan naji dad’i. lokacin dana fito yagama shiryawa cikin ainahin kayan malam bahaushe, blue d’in shaddace akaima d’inkin wando da ‘yar shara, saidai tasha aikin sarauta d’an asali da d’aukar hankali, ya kawo bak’ar hularsa ya d’ora, itama dai irin ta mutanen dace *dara* (irin wadda su ibro suke sawa), saidai wannan batakai waccan tsawoba, dai-dai take kamar sauran huluna. harga ALLAH kwalliyar tasa tamin k’yau, dan yafito a cikakken bahaushensa, turare yake fesawa amma nakasa d’auke idona daga kansa.

Duk kallon k’urillar datake masa yana kallonta ta gefen ido, wani miskilin murmushi yayi Na gefen baki, ya juyo muka had’a ido, saurin janyewa nayi cike da basarwa.

Shikuma ya ta6e baki yana takowa inda nake. tuni zuciyata harta fara tsitstsinkewa, dan ayanzu babu abinda nake gudu kuma irin yace zai ra6u jikina koya nunan buk’atar wani abu, shima inaga fahimtar hakanne yasa a kwanakinnan bai cika takurani kamar abaya danake kawo kaina ba.

Ganin yanda ta tsorata sai abin yabashi mamaki, waskewa yay yafasa zuwa gareta, ganin ya canja hanya Na sauke ajiyar zuciya wadda har fitar sautinta saida yaji.

Kansa kawai ya girgiza ya zauna a bakin gado yana fad’in “kishirya mana”.

Bance komaiba nawuce Na d’auki Arabian gown da zan saka, dan yanzu sune kawai kayan dakemin dad’in sakawa, bathroom nakoma Na saka, Na fito Na iskeshi yana waya da Akash dake fad’a masa inda zamu iskeshi. wucewa nayi nad’an gyara fuskata, inason shafa mai a k’afa amma ina tunanin yanda zan sunkuya.

Lura da yay da hakan yasashi mik’ewa, wajen takalmanmu yanufa ya d’aukamin masu taushi cikin wad’anda ya siyamin saboda naji sauk’in tafiya.

Kafad’una ya kama ya zaunar dani ga stool d’in mirror, sannan ya d’auki man ya duk’a k’asa a gabana yakamo k’afata yana shafamin, nidai kallonsa kawai nakeyi, harya gama yasakamin takalman ya d’auran igiyar yana fad’in “yakamata ma mufara fita kina motsa jiki, dan k’afarnan kamar tana d’anyi fushi a kwanakin nan”.

Nace, “ai bata ciwo”.

Baice komaiba yamik’e yana kama hannuna ya mik’ar dani.

 

A falo muka iske jakadiya tana kallo, tamin sannu sannan ta gaida Galadima.

yafad’a mata zamu fita, tabimu da addu’ar dawowa lafiya.

Tafiyar tamu takasance shiru kamar yanda muka saba inhar ta had’amu mu biyu, maimakon muje asibiti sai gamu awani gida mai k’yau da tsari, kafin nasamu damar tambayarsa saiga Akash yafito yana zabga murmushi, rungume juna sukayi da Galadima, kafin ya d’ago yanamin sannu da zuwa.

Fuskata da murmushi Na amsa masa tareda gaishesa.

A tsararren falon gidan muka yada zango, komai ya birgrni dan an tsarashi yanda ya kamata. dandanan Akash ya tara mana kaya a gaba, sannan ya zauna muka sake sabuwar gaisuwa. Suka d’ora da barkwancinsu irin Na abokan da suka shak’u. A firar tasune nakejin Auren Akash d’in ya matso, dan zasuyi baiko next week da wadda zai aura, Na tayashi murna da fatan kaiwa da rai. ya amsamin bakinsa har kunne.

Bayanin yawan cin abincina Galadima yamasa, Akash yay dariya, “to inbanda abinka Sameer ai dole taci abinci fiyeda da, karka manta yanzu ba ita kad’ai bace, kuma saitaci abin cikinta zai samu shima, kunk’i yarda ayi scanning muga adadin ‘ya’yan namu ko jinsun su”.

galadima ya murmusa kawai, karka damu, miye Na zazzari, kwana nawane insha ALLAH zaizo ko zatazo duniya, yanzu dai tunda ba Matsala bane cin abincin ai Alhamdllh”.

“no babu wata Matsala, abindama yasa zakuga yanzu takanyi saurin jin yunwa cikinta ya tsufa, shima yak’ara girma abin cikin nata, dan zama ta dingajin idan bataciba ana motsi da harbe-harbe a cikin, idan da zaka kalli cikin a time d’in datakejin yunwar sosai har yanda yake wuntsilniya saika gani kaima, Madam ko hakan baya faruwa?”.

Nace, “yana faruwa sosai, amma da zaran naci abincin sai a nutsu”.

Akash yay dariya, “Alamun yana cikin k’oshin lafiya kenan, abincinne kawai buk’atarsa”.

Galadima ya juyo muka kalli juna, gira ya d’agamin nikuma nayi murmushi ina kauda idona gefe.

Daga nan wata hirar suka koma, wadda nake zargin akan Abba nane, dan naji Akash Na fad’in doctor Johnson yabama Abba glasses d’in amatsayin medical glasses, kuma ya gargad’esa karyayi wasa dashi saboda jijiyar idonsa nason samun Matsala, to sunason glasses d’in yazama riga kafine, dayake da turanci suke magana sai yazam inaji nima.

Murmushi Galadima yayi yana jinjina kai.

A raina nace mikuma Galadima ya shiryama Abban?. banida mai bani amsa, dan haka nayi gum.

Muna niyyar tashi Akash yace bamu isaba, bazamu tafi bamuci komai a gidansa ba, kodan munga bashida matane.

Badan munsoba mukad’anci abinda zamu iya, sannan yayo mana rakiya har wajen mota.

Saida munaya tashiga mota sannan Galadima ke fad’ama Akash yayi mantuwa.

Akash yace “tami?”.

Babu kunya Galadima yad’an ciza lips yana tambayar Akash wai miyasa yanzu take gudunsa?.

Akash yabashi amsa da maybe salon cikine, danshi babu yanda baya zuwa ma mace, wani yasata sha’awa wani kuma akasin hakan, amma idan na haihu zan iya komawa normal. Galadima ya basa hannu sukai musabaha sannan ya shigo mota yana masa godiya.

Tunda muka fara tafiya saina kasa jurewa, na jeho masa tambaya muryata a sanyaye.

Kad’an ya juyo ya kalleni ya maida kansa ga tuk’i, saida yaja wasu mintuna kafin yasaki ajiyar zuciya tareda cizar lips nashi, batareda Yakuma kallonna ba yace, “Friend! Wani karatun baya buk’atar fashin bak’i,  akan karantashine a barsa a yanda yazo”.

Murmushi nayi ina maida hankalina gareshi, nace “yalla6ai koda shi wannan karatun zai iya fita a jarabawa?”.

“Humm” yafad’a yana rage gudun motar, yanzunma bai kalleniba, yad’an zakud’a jikin sitiyarin sosai, “sometimes akanyi burin cin jarabawane domin canjin aji ko gama makaranta ko shiga, saidai awannan karon ni nawa jarabawar da banbance-banbance tazo, dan bana buk’atar cin jarabawar kai tsaye, har sai harsashina ya isa ga zukatan malaman”.

“to amma yalla6ai karka manta Hasashefa ba shi bane yak’ini”.

“wannan gaskiyane yalla6iya.  Saidai yak’ini kuma baya amsa sunan tabbaci, daga lokacinda kika shiga fili wasa kika saka aranki bazakiyi nasara ba, to da kamar wahala kiyi nasarar, duk abinda zanyi nakan rok’i ubangiji nasara Kafin yinsa, sannan na cika zuciyata da kwad’aituwar samun wannan abin, lokuta da dama mutane kan Gaza tsarkake zuciya kafin su cikata da buruka, shiyyasa kikaga duk gudun jirgi a samaniya wataran gaggawa nasakashi tarwatsa a filinda ba muhallin saukarsaba, kiringa zama mai yak’ini saikiga kin tabbata a jerin masu samu”.

Murmushi nayi har hak’orana na bayya, nace, “dakai kanarine danace kafi dukkan halittar kanari iya raira zance, dakuwa mawak’ine saina saka a jerin masu zak’ak’an murya, inkuwa a Marubuci kazo to tabbas kai Kanada yawan fik’ira, domin hikayarka zata yawaita saye zukatan mabiyanka ne”.

Gefen hanya ya gangara, ya kashe motarma baki d’aya ya maido hankalisa gareni.

“Munaaya!” yakirani cikin wani yanayi kuma murya ahankali.

nima saina amsa masa a sanyaye.

Hannuna ya kamo cikin nasa yana mirza yatsun a hankali, yaci gaba da fad’in “A shekarun baya ni mutumne mai ra’ayin Kansa, ma’ana murd’ad’d’e mai wahalar sha’ani, sannan mai zama a bisa tsarinsa, kece mutum ta farko dana fara doguwar magana da ita koda bana so, nakanyi mamaki a duk lokacin da kika taya nazamo mai sallama miki, anya kuwa bakizo da wani Siddabaru ba?”.

Idanu nad’an fiddo waje, nace “siddabaru kuma yalla6ai? to ai awajena ni har gobe kana akan wad’annan ra’ayoyin naka, dan banga canjin dakake hasashen kasamu ba, amma miyasa kace hakan?”.

Numfashi ya sauke ahankali, kafin ya ciji gefen lips nashi yana Sosa girarsa d’aya da d’an yatsa “wannan sak’on zuciyane, kibata dama, zata tabbatar miki da cewar wannan Muhammad Sameer d’in yasha banban dana shekarun baya”.

“sak’on zuciya kuma?”. nafad’a cikin hasashe, dan nikam Yakuma dilmiyar dani.

Mortar ya tada yana fad’in “well basai kin zurfafa ba, dan haryanzu akwai sauran dama”.

Baki na d’an ta6e ina gyara zama, “har walau zancen “dama! dama! dai again?, bana son saka baki a hurumin daba nawaba, amma abinda nasani dama dai duk damace, sannan mai ita yakan tanadar mata dukkan muhalin daya tadace da ita, damarmu ce mu damata takowane

hanya mukaso”.

Idanunsa ya lumshe yana sakin wani k’asaitaccen murmushi daba koyaushe yake irinsaba.

Jin Sautin murmushin ya sakani juyawa na kallesa, ya d’agamin gira yana maida hankalinsa ga tuk’insa.

Babu Wanda yasake yin magana har muka Isa gida. har yanzu babu Wanda ya dawo, dan haka muka haye sama kai tsaye. dama na k’agara na cire rigar jikina saboda azababbiyar zufar danakeji, danma ya tausaya min yad’an saka AC a mota, ban iya zama ba saida na watsa ruwa, nifa abubuwan sunmin yawa, nice jin zafi nice ci kamar gara, harda alwala nayo, Dan magriba tayi.

Ina fitowa shima yashiga yayo alwala. Koda yafito saiya wuce masallaci.

 

Ina jiyo hayaniyar su Samha dasuka dawo amma nakasa sauka, ina kwance abina, hawa da saukarnan bak’aramin wahal dani yakeba yanzu, ahaka Galadima yadawo ya iskeni, sallamarsa kawai na amsa, amma ban iya d’agowa na kalleshiba. Saida ya sauya kayan jikinsa zuwa marasa nauyi kafin yazo ya zauna kan sofa yana fad’in “lafiya dai?”.

d’ago ido nai namasa d’an murmushi, nace, “babu komai, gajiya ce kawai”.

Shima murmushin yamin, cikin lumshe ido yace, “Sorry friend, saura k’iris insha ALLAH”.

“Humm” kawai nafad’a batare da nace masa komaiba.

Daga nan muka d’anyi shiru, kusan mintuna 3 yanata latse-latsen wayarsa, batareda ya kalleni ba yace, “Abba kuwa yana saka zobe?”.

Kallonsa nayi, amma hakan baisa ya kalleniba, a d’arare nace, “eh yana sakawa amma miyasa kamin wannan tambayar?”.

Wayar ya ajiye yana sauke ajiyar zuciya, ya saka d’an yatsansa yana bubbuga la66ansa ahankali, yayinda idonsa yake a kaina tamkar mai nazari, “kina ganin idan kika bashi zai saka?”.

Yunk’urawa nai na tashi zaune sosai, “dan sakawa zai saka, amma kana ganin bazai zargi wani abuba kuwa?”.

“miyasa kikace haka?”.

Shiru nad’anyi, dan ganin ina neman zirma kaina, saina d’an murmusa kawai cikin basarwa, nace, “waynot abashi ba kai tsayeba”..

Murmushin gefen baki yayi, yace, “y’ar tsuntsuwata wai mikike tunanine? da har kiketa kwana-kwana haka?”.

Baki na tunzuro gaba, ina fad’in “nidai ba tsuntsuwa bace ba”.

Dariyace ta kufce masa babu shiri, yasaka hannu yana rufe bakinsa.

Haushi ya kamani na d’auki filon dana kwanta na jefa masa. da sauri ya cafe yana cigaba da dariyarsa, hakan yasa najawo na kujerar ina cigaba da kai masa duka yana karewa da wancan. daga k’arshe sakkowa yay yahad’a nida filon ya rik’e yana fad’in “sorry sorry na bari, ba ‘yar tsuntsuwa ba giwar mata”.

Hararsa nayi nafara kukan shagwa6a kuma.

dariya Yakuma sakawa yana fad’in “toni bansan mikikeso nace mikiba kuma?”.

“ni banaso duka”.

“to shikenan nabari, yanzu dai yaza’ayi Ring yaje yatsan Abbanmu to?”. ‘yay maganar yana d’ora kaina jikin kafad’arsa’.

“saika fad’amin sirrin sannan zan fad’a nima”.

Ya murmusa yana jan hancina, “kin cika wayo yarinyarnan wlhy”.

K’aramar dariya nayi nace, “ai awajenka na koya”.

Murmushi kawai yay baice komaiba, ya jawo wata ‘yar k’aramar bag mai k’yau fara ya mik’omin.

Kar6a nayi ina tashi zaune sosai na bud’e jakkar ina fiddo kayan ciki, agogone mai masifar k’yau da tsari, na azurfa ‘yar asali mai tsada, sai wani d’an akwati da ring mai k’yau na azurfa shima, an masa ado da farin stone mai garai-garai tamkar diamond, na jujjuya zoben kafin na d’ago mu kalli juna ni da Galadima, ido d’aya ya kashemin😉.

Janye idanuna nayi nakuma maidawa ga zoben ina k’ok’arin sakashi a yatsana, saidai yamin yawa sosai, na cire ina fad’in “amma gaskiya zobenan ya had’u sosai yalla6ai”.

“duk haduwarsa bai kaikiba ai”. ‘yay maganar acikin kunnena’.

Kallonsa nayi, amma saiya basar tamkar bashi yay maganar ba.

Lips na cije na d’an hararesa.

Shikuma ya ta6e baki.

Na maida kayan duk a cikin bag d’in dad’an hanzari ina rik’e cikina dayay wata wuntsulawa.

“lafiya?”. ya fad’a yana rik’o hannuna.

‘Dagowa nayi na kallesa da k’yar, da hannu na nuna masa cikina dake juyamin, jinake kamar numfashine zai bar jikina.

Babu shiri ya dire wayar hannunsa ya rik’oni jikinsa da k’yau.

Sosai na fara murk’ususu ina kuka da k’ank’amesa, dukya rikice, yama rasa mi zaiyi?.

Ana cikin haka saiga sallamar Aunty Mimi dataga shirun yayi yawa sun dawo ban sakkoba, saitai tunanin kobana jin dad’ine, sallama tayi Galadima ya amsa murya a rikice, hakanne yasakata shigowa batareda jiran isoba.

Da hanzarinta ta k’araso tana tambayar miya faru?. nidai kuka kawai nake ina kuma k’ank’ame Galadima.

Shine yasamu damar mata bayani sama-sama, yak’are maganar da fad’in “Aunty mutafi asibiti please, maybe haihuwa Ce?”.

Da sauri tace, “badai haihuwaba Sameer, cikin dake wata takwas, kaga ina zuwa”. Ta fita a hanzarce.

Babu dad’ewa sai gata tadawo da innarmu da jakadiya, dak’yar innarmu ta amince ta hawo, danma taga tsantsar rikicewar da aunty Mimi tayine. har yanzu dai kukan nake ina jikin Galadima dashima dukya koma kalar tausayi kamar zaiyi kukan.

Ganinsu a haka yasaka innarsu munaya k’ok’arin komawa da baya, dan saitaji kunya ta kamata, dukda tasan suma bada son ransuba ne. ita kanta jakadiya taji kunya. ganin innarsu munaya zata gudu Aunty Mimi tayi azamar rik’o hannunta. “please inna karki duba ta kunya, halen datake cikine abin dubawa, kowa yasan dai ba haihuwa baceba tunda da saura”.

Ajiyar zuciya inna ta sauke, batare da ta motsa daga inda takeba takuma musu kallo d’aya ta d’auke kanta, tace, “inaga juyine ai, zai lafa insha ALLAH”. ‘tana gama fad’a ta fice abinta’.

Jakadiya da aunty Mimi suka kalli juna, murmushi jakadiya tayi, tace, “gaskiya ta fad’a, juyine, amma nadad’e banga uwa mai kawaiciba irinta a wannan zamanin”.

Murmushin itama aunty Mimi tayi, ta maida kalonta kansu, yafara lafawa sosai, dan haka munaya tafara tsagaitawa da kukan.

Galadima yakuma k’ank’ameni a jikinsa sosai yana shafa kaina, nikam sai ajiyar zuciya nake saukewa tareda shashshekar kuka, ya manna min kisses a kaina idonsa a lumshe, danshi yama manta dasu Aunty Mimi a d’akin.

Jakadiya ma dai lalla6awa tai ta gudu, dan taga magajin gari yau sai a hankali.

Aunty Mimi ta tako inda suke ta zauna a sofa tana fad’in “sannu Munaya”.

Bud’e ido Galadima yayi, harsun kad’a zuwa launin jaa, yad’an furzar da iska yana lek’a fuskarta, barci ya d’auketa. ido ya d’ago yana kallon aunty Mimi dake kallonsu cike da sha’awa, tamasa murmushin kwantar da hankali, ajiyar zuciya ya sauke yana cije lips da jinjina mata kai.

Tace, “tayi barcine?”.

Nanma kansa ya jinjina mata, yana gyarama Munaya kwanciya a k’irjinsa yanda zataji dad’i, yace, “Aunty Mimi amma yakamata muje asibiti aga miye matsalar?”.

“karka damu my k’ani, juyine kawai, insha ALLAH babu wata damuwa. bara inje nima saida safe, idan kuma kaga dawata matsala saika kirani muje asibitin tunkan dare ya kumayi”.

 

Bayan fitar aunty Mimi kuma k’ank’ameta yayi yanamai jin tausayinta na ratsashi, ya sumbaci goshinta, kafin ya d’auketa dukda nauyin datayi ya maidata saman gadon, yanzunma a jikinsa ya sakata, yaja bargo ya lullu6esu tareda musu addu’ar kwanciya.

Cikin barci ta farka da wata matsananciyar yunwa, k’irjin Galadima na shiga girgizawa ina kuka.

Galadima ya farka a firgice yana rik’e hannunna, ya yunk’ura da k’yar ya tashi zaune, “miya faru?”. ‘yafad’a cikin muryar barci’.

“yunwa yalla6ai,  abinci xanci, kafad’a masa magana yabar halbina”.

Dukda tabashi tausayi saida ya murmusa, sauka yay yafita, k’asa ya sauka zuwa kitchen, yau saiga Galadima  a kitchen🤣, rasa mizaimayi yayi, ganin yana 6ata lokacine kawai dan ba iya uwar komai yayiba saiya fice, dole yaje ya tado kukunsu.

Mai aiki da aikinsa dannan saigashi ya had’a mata Abu mai sauk’i, Galadima ya kar6a da kansa Yakoma saman.

Isketa yayi zaune tsakkiyar gado tana kuma rurus, saita k’ara bashi tausayi, ya haye gadon da abincin, da kansa yabata yana lallashi. saida tayi nak sannan ya sauka da tiren yana sauke tagwayen ajiyar zuciya.

Nikam hankalinna kwance nazame na kwanta, barci ya sake kwasheni.

Mamaki yasakashi tasata gaba yana kallo, saikace wata mai aljanu, lallai duk namijin daya kasa tausayawa matarsa lokacin da ciki yake jikinta yacika mara tausayi number d’aya, babu abinda miji zai iya biyan matarsa dashi akan rainon cikinsa datayi da tarbiyyar ‘ya’yansa, amma a wannan time d’in wani namijinma rashin tausayinsa ke tashi akan matar, ALLAH ya ganar dasu to.

 

Amin galadima🙁😔.

 

 

 

**********************

 

Washe gari

 

 

A safiyar yau su Abba suka tashi da shirin komawa Nigeria, gaba d’aya saina tashi duk babu dad’i, jinake kamar karsu tafi, dana tuna yaune zasu barmu sai hawaye ya zubomin, inama zai amince nidai nabisu mu tafi tare?.

Agogo da zoben jiya na d’auka nafita masaukin su Abba, dan Galadima ya fita tunda sasaafe, bansan ina yajeba.

Saida nayi sallama aka bani izinin Shiga sannan na shiga,  Abba na zaune a bakin gado agogo rik’e a hannunsa suna magana da innarmu dake tsaye ita kuma tana zuba sauran kayansu a k’aramin akwati.

Abba yay murmushi yana fad’in “sannu munaya kinji”.

Murmushi nayi a kunyace, na dafa gadon zan durk’usa k’asa na gaidasu amma saiya dakatar dani ta hanyar rik’e hannuna, “kinga zauna, inake ina durk’uso yanzu”. da taimakon Abba na zauna a kujerar dake kusada gadon, sai faman jeran sannu yakeyi, nikuma ina amsawa cikeda jin kunya. gaishesu nayi, suka tambayeni yaya jikin? na amsa da “Alhmdllh”.

Jakar hannuna na mik’ama Abba, ya amsa yana fad’in “minene kuma?”.

“Abba ka bud’e to”. ‘nayi maganar a shagwa6e’.

Dariya yayi yana k’ok’arin bud’ewa, “yanzu dai fitinarki k’aruwa ma tayi Munaya”.

Innarmu dake ta6e baki tace, “ai bamaka san fitinarta ta zarce tadaba sai jiya, juyi kawai ta zauna tana rusama mutane kuka a gidannan, yo ke aibama asan abin fad’in dazaki bariba ranar haihuwar?”..

“babu abin fad’in dazata bari insha ALLAHU”. cewar Abba yana juya agogon fuskarsa d’auke da murmushi.

Nima sai ban kula zancen Innarmu ba nace, “Abba yayi k’yau?”.

“sosai kuwa Munaya”.

“Abba kawo na saka maka to”.

“to amma kekuwa ina kika samu kud’in sayen wannan agogon da zoben mai tsada haka?”.

Murmushin nayi, nace, “Abba awani shago mukaje sayen kaya tun kwanaki dashi, daga nace agogon yamin k’yau shinefa yace na d’auka to”.

“Amma munaya yayi tsada da yawa, karna sakejin irin haka, dan takurawace ai, idan kuma bashida k’arfin siyen abunfa? Karki sake kinji ko?”.

“inasha ALLAHU Abba bazan sakeba, amma dan ALLAH karkace bazaka kar6i wannanba, dan shima bazaiji dad’iba”.

Murmushin Abba yayi, yashiga sanya albarka a garemu da abinda ke cikina, hardama addu’ar d’orewar lafiya ga Abie shima. cikeda d’oki naita amsawa da amin, da kaina na saka masa agogon da zoben.

Daga nan muka d’an ta6a hira. Dan akwai sauran time sosai na tafiyarsu. Mun dad’e muna hira, dan ko break fast yau tare dasu na sakeyi, dama tun asuba ni yanzu nakeyin nawa🤭, sanda kowa zai k’ara sainayi na biyu.😂

Galadima ma daya dawo ya kimtsa nan yazo ya samemu,  yanda suke sakin jiki da juna shida Abba abin na bani mamaki, Galadima yakuma yima Abba bayani sosai akan yanda zaicigaba da tattalin lafiyarsa da kulawa da dukkan dokokin da sukai masa, daga nan muka cigaba dad’an ta6a hira, itadai Innarmu duk adabaibaye take, danma taga yau zasu wuce da bazata zaunaba.

 

Wajen 12pm mukabar gidan zuwa asibiti, a asibitine akayi dogon zama, dan godiya ta musammance tashiga tsakanin surukan guda biyu, Abba kuma yay alk’awarin kuma tsayawa wajen dagewa da addu’oi na musaman ga jikin Abie da alk’awarin kawo wasu taimakon na tsarin jiki, dan sunga fa’idar addu’a sosai.

Kowa jiyake tamkar karsu tafi, saboda shak’uwace ta musamman tashiga tsakanin wad’annan families guda biyu, zaman mutunta juna ya gudana sosai a tsakani.

Kuka na shiga rairawa lokacin danaga tafiyarfa da gaske yinta za’ayi, sai alokacin muka san ashe wai harda Sauban, zai rakasu saudiyya suyi umrah ta kwana 10, daga nan saisu wuce shikuma yadawo. na kama hannun Abba na rik’e gam nak’i saki zai hau jirgi, su Sauban suka tasani da dariya kuwa, oho ban kulasu ba, Galadima ya girgiza kaiwai yana murmushi, yarinyarnan ta6ararta tayi yawa, yafad’a yana takowa inda muke da Abba yana lallashina.

A     Kallonsa Abba yayi sukayi murmushi, Abba ya zame hannunsa a hankali yajuya zuwa ga jirgi, yunk’urin binsa nayi Galadima yay azamar rik’o min hannu batareda yayi magana ba, juyowa nayi na fad’a k’irjinsa ina kuma sakin sabon kuka.

Hannu biyu ya saka ya rungumoni yana guntun murmushi.

Innarmu dake hangenmu ta cikin jirgi ta share hawayenta itama tana murmushi, banda aure waya isa ya rabaka da ‘ya’yanka. Abba daya zauna kusada ita ya saka hannunta cikin nasa yana murzawa, juyowa tayi ta kallesa, yamata murmushi yana share mata hawayen da har yanzu sun kasa tsayawa, jikin kafad’arsa ta d’ora kanta kawai.

Sauban dake kallonsu yay murmushi, lallai Aunty gimbiya ‘yar gatace a gidansu.

 

Saida naji alamun jirgi zai tashi sannan na d’ago kaina, inaji ina gani jirgin yafara shawagi a samaniya harya shilla da iyayena.

A motama haka naita sharar hawaye, dayake dagani sai shi da Samha a motar, cankuma Aunty Mimi da Khaleel da jakadiya.

Samha tana ta bani hak’uri, amma tamkar tana zuganine, saida Galadima ya harareta yana mata alamar tamasa shiru sannan tayi shiru, shikam ko sau d’aya baicemin uffanba..

Asibiti muka koma, tunda muka shigo Momma ta taso ta rungumeni a jikinta tana lallashi.

Galadima ya jingina da bango ya hard’e hannayensa yana kallonmu, a haka sauran suka shigo suka iskemu, Abie ma kallonmu yakeyi cike da tausayina.

Saida nasamu na tsagaita da kukan sannan nacema Momma zanci abinci.

Galadima yaje kusada Abie ya zauna yana k’aramar dariya, “dama kice yunwa kikeji kika zauna kinama mutane ta6ara?”.

Hararsa Momma tayi tana masa dak’uwa, hakama Abie, aunty Mimi kam saida ta rankwasheshi akai.

Gurin ya dafe yana fad’in “a’a yazaku tararmin ne kuma?, gaskiyafa na fad’a ko Samha?”.

Samha tace, “Uncle nima dai ina bayan aunty gimbiya”.

Idanu ya kwalalo alamar tak’aremin.

Muka had’a ido na hararaesa.

Lips d’insa ya ciza yanamin alamar zan kamakine da ido.

Na ta6e bakina nikuma. Dolenesa yatashi yanemomin abinda zanci.

 

 

 

★★★★★★★★★★

 

Tunda su Abba suka tafi lafiya tamin k’aranci, bana iya tsinanama kaina komai sai kwanciya, dukna fita hayyacina na canja kamanni, ga cikifa sai kuma bud’ewa yake yana k’ara girma. Kai kace ba halitta d’aya bane a cikinsa.

Galadima dole ya d’auki hutu a office, idan abinda yazama dolene saiyaje Office kam yakanyi shine ta yanar gizo.

Gakuma nasarar jikin Abie daketa k’ara k’yau, dan wasu sassan jikinsa suna nuna alamun fara aiki kamar yanda doctors d’insa suka sanar mana.

A kwana na 8 da tafiyarsu Innarmu ranar a asibiti na kwana, saboda jiki dai yak’i dad’i, ga masifaffen cin abinci abin babu arzik’i.

 

 

★★★★★★★

 

Su Abba sun gudanar da ibadar Umrah cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, ga Sauban dake nuna musu komai yanda bazasu wahala ba.

Suna cika kwanaki goma yasakasu a jirgi suka nufi k’asar haihuwa Nigeria kenan, sun rabu cikeda kewar juna suna saka masa albarka.

 

Sun isa Nigeria batareda sanin kowa namuba sai Yaa marwan da Galadima yakira ya sanarma yaje ya d’aukesu a airport.

Isowarsu gidanmu tazama a bazata, hakan yasaka gidan rikicewa da murna, dukda kishin daya cika matan gidan ganin innarsu munaya takoma wata d’anya shakaf saboda Hutu da canji wajen zama data samu, dandanan ‘yan anguwa suka shiga shigowa taya murna dama Abba jajen ALLAH ya kiyaye gaba.

Innaro babu kunya taketa haba-haba da d’anta, kota innarsu munaya batayi, dan haushinta takeji taje ta zauna a India itako an maidota gida. (Babu mai iyama Innaro dai sai ALLAH🤦🏻‍♀🤣).

 

Su Ayusher da sukazo suka zage suka gyarama inna d’akinta, komai ya koma need, tamkar ba shineba ya had’a uban datti na tashin hankali.

 

Tafiyarsu Abba Nigeria da kwana 5 Sauban ma ya dawo India, ya iske ina asibiti, dan gado suka bani dole, babu ranar sallama ma, k’ila saina haihu.

Saidai randa mukayi waya da Munubiya nake fad’a mata tace ai gidama yakamata na dawo na haihu, itama batada lafiyar sosai.

Da to na amsa mata kawai, amma ina tunanin yanda Galadima da ahalinsa zasu amince da zuwana haihuwa Nigeria, kuma tunda ‘Yar uwata ta ambata dolene hakan za’ayi,  kona so koban soba kuwa.

 

 

___________________________

 

 

*_Two months ogo_*😬🤭

 

 

Watanni biyu kenan da tafiyarsu Abba, tunda sukatafi kuma babu wani Abu mara k’yau kona Sosa zuciya dayay gamo dashi, harma ya koma wajen aikinsa hankali kwance.

Jama’ar gidansu Munaya kuwa sunyi haushin da nuna hassadar ga inna harsun gaji sun bari, dan sudai san ba kulasu zatayiba, ita yanzu babbar damuwarta ma ‘ya’yanta su sauka lafiya, dansu Safara’u duksun haihu sukam, kuma dab da dab sukaita kancamo ‘ya’yan, ayanzu haka sunan d’an Fauziyyane kawai yarage gobe idan ALLAH ya kaimu, dan itace k’arshen haihuwa..

Su fiddausi duk suna gida sunzo wanka, iyayensu kowa ta zuba k’arya a hidimar sunan ‘yarta, yanzu maman Fauziyya da innarsu munaya kawai aka zubama ido aga yanda zasuyi nasu.

Inna dai bata d’ad’ara kanta da k’asaba, iya abinda ALLAH ya hore mata iya shine tai k’udiri yi a hidamar sunansu Munubiya idan sun haihu. Fatantama su sauka lafiyar, dan gasu suna neman share watanni na goma haihuwa babu amo babu labari.

Mama Rabi’a cema kawai keta k’ok’arin ta na ganin sun tanadi dukkan abin fita kunya, sai Aunty Salamah dake taimaka musu, wadda a yanzu tazama ‘Yar uwa agaresu makusanciya, dan komai nasu tana tsaye a akai tsakaninta ga ALLAH.

 

WASHE GARI akasha sunan d’an Fauziyya. Wanda mijinta da mamarta suka bada mamaki, masu shirin asha kunya sai aka barsu su dajin kunyar da shak’ar bak’inciki irinna masu hassada.

Itama tamkar su Haleematu gida ta taho wankan jego.

 

 

 

**************************

 

 

A wata ranar talata datai dai-dai da cikar cikunanmu wata goma da sati biyu natashi da matsanancin ciwo, Wanda ya rikita Galadima da ahalinsa, nan take doctors sukace haihuwace, aka fara shirin kar6arta amma ina, gadai haihuwar gadan-gadan da gaske amma kuma nagagara haihuwar har washe garin laraba.

Nayi masifar galabaita, Galadima yace sumin cs idan bazan iya haihuwa da kaina ba.

Amma sukace zan iya haihuwa.

Ranar laraba da daddare Galadima da Momma na kusadani suna ta tofamin addu’a saboda zufar danakeyi, nace su kiramin munubiya, babu musu Galadima ya kira Yaa marwan.

Shima dakaji muryarsa zakasan a rikice yake, hakan yasaka Galadima tambayarsa ko lafiya?.

Yaa Marwan yace, “dadai sauki ranka ya dad’e, tun daren jiya Munubiya ke nak’uda amma haihuwa shiru, sai sunan Munaya kawai taketa kira”.

Mik’ewa Galadima yayi tsaye, yace, “muma ai halin da ake ciki kenan, yanzuma itace tace akira mata ita, please kakai mata wayar”.

“ok”. Yaa marwan ya amsa yana nufar d’akinda Munubiya take……………✍🏻

 

 

 

 

 

Barkanmu da dawowa.🤩✋🏻

 

 

 

 

 

 

 

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻

*_typing📲_*

 

 

💡 *_HASKE WRITERS ASSO….._*

 

 

*_♦RAINA KAMA…..!!♦_*

_(Kaga gayya)_

 

 

 

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

 

_________________________

 

*_HASKE WRITERS…._*

 

_gaisuwarku ta musammance, alkairin ALLAH ya baibayeku aminan kwarai abokan tafiya👍🏻😽._

 

I love you manya-manya fa🥰🥰🥰🥰🤩🤸🏻‍♀

 

________________________

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply