Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 2


Raina Kama Book 2 Page 2
Viral

~Book 2~ ????2?

…………..Shiru Galadima ya mata, da ace babu Momma daya ya6a mata maganar da har tabar India tana mata zafi kuwa. amma duk da haka maganar ta daki zuciyarsa, bai saniba ko zancen tsohuwarnan gaskiyane.
Momma da Aunty Mimi da matar sarki kuwa kallona duk sukayi, nayi k’asa da kaina gabana Na luguden duka, saboda zancen tsohuwarnan yana son tsoratani.
Shigowar Sarki Abdul’fatah (papi) da inno matarsa da mai martaba Sarki Jalaluddeen ce ta tak’aita zancen. dan daganan kowa yasaki maganar, saidai munata juyata a zukata ni da Galadima, yayinda aunty Mimi da Momma ke fatan ALLAH yasa hakane.

_____________________________

Misalin 8:pm saiga Sa’eed yazo gidanmu, a time d’in gwaggon Haleematu da mamansu yaa Hameed suna ta hayaniyar fad’a, wai mamansu yaa Hameed ce takama gwaggon Haleematu tana kallon Zarah dake alwala a fanfo tana dariya.
Shinefa mamansu yaa Hameed tace gwaggon Haleematu taci kanta tasha bak’in ruwa, karta lashe mata jika tun yana a ciki.
Wannan kalma ta mamansu yaa Hameed itace tajawo fad’a, Dan gwaggon Haleematu tace mamansu yaa Hameed tace mata mayya bazata yardaba. Fad’a sosai sukeyi suna cin zarafin juna da gori, dama kowa kishi Na cinta a zuciya.
Matan gidanmu duk sunyo waje anrasa masu dakatar dasu sai innarmu dake cewa suyi hak’uri Dan ALLAH, darene fa.
Amma Sam sunk’i saurarenta.
Innaro dataji hayaniyar tundaga gidanta yasata d’akko fayafi tafito, kamar anjehota haka tashigo gidan.
Sa’eed da Sulaiman suna awaje a mota, duk badak’alar da akeyi daga cikin gidanmu suna jiyowa, har shigar innaro kuwa suna kallo. Dayake su Abbanmu suna masallaci.
Innaro tanata magana sunk’i saurarenta, saiyi sukema kamar zasu fara danbe.
Mamansu yaa Hameed Na k’ok’arin kwalama gwaggon Haleematu ludayin miya dake hannunta innaro takawo jiki zata kare sai a goshinta, jikake kwarrrr!.
Tako dafe goshi tafasa k’ara..
Hakan kuma yay dai-dai da shigowar su Abba gidan, su duka ukun, tunkan sushigo sukejiyo hayaniyar dama, dukansu rai a 6ace suka shigo. Dan iskancin matan nasu ya ishesu hakanan, idonsu yarufe ko ganin motar su Sa’eed basuyiba.
Ran Abba yakuma 6aci, Dan ganin duk matansa ne ma masu hayaniyar, ga abinda sukaima mahaifiyarsa akan idonsa. batareda yabi ba’asiba yace duk sufice su bar masa gida.
Ananne kowa yay tsitt, yadaka musu tsawa yana fad’in wlhy idan basu fitaba zaisa a fiddasu, ko d’akunansu bai yarda wata takomaba kuma.
Dole sai ‘ya’yansu suka d’akko musu hijjabai suna kuka da bama Abban hak’uri.
Amma yak’i sauraren kowa, daddy da baba k’arami kuwa babu Wanda yay yunk’urin hanashi.
Innarmu tamatsa kusadashi tana rok’onsa karyayi haka, yazauna ya sauraresu tukunna, Hararar daya zuba matace yasata jada baya tai 6am da bakinta.
Innaro kuwa maman safara’u ce takamata ta zaunar, goshi harya fara kumbura????.

(((+)))***(((+)))***(((+)))

Kafin mu baro asibitin nama manta da maganar mama Fulani, saboda murnar bud’e ido da Abie yayi ta d’aukema kowa hankali kuma, gaskiya ina tausayin bawan ALLAHn nan sosai.
yauma bamuyi k’asa a guywa ba wajen cigaba da addu’oin damukeyi cikin zam-zam ni da Galadima, somuke muyi na 1week sannan afara bashi.

Washe gari Alhmdllh jikin Abie yayi k’yau sosai, Dan inka gaidashi yakan maka murmushin sa Na dattako, hakan ya sanya su papi sukayi shirin tafiya da yamma.
Ni da Galadima da Sauban muka musu rakkiya, sainaji tamkar nabisu. Harda ‘yar kwallata kuwa. Inno tanata tsokanata, Dan tsohuwar tashiga raina sosai.
Tunda muka d’akko hanyar dawowa asibitin nakife kaina a cinya inata hawaye, sauban ne kawai ke tsokanata, amma Galadima tamkarma baya cikin motar. hakan saiya k’ara tunzura zuciyata, nakuma k’ara k’arfin kukan nawa.

Sauban yasamu guri yay parking, da hannu Galadima yamasa alamar yaje.
Fita yay yana k’uk’uni da k’umshe dariya, wai “su boss za’ayi lallashi shine aka koroni”. Saida yay nisa da motar sannan yasami damar dariyar, har yashiga wajensu Momma.
Daga Momma har Aunty Mimi kalli
onsa sukeyi,, aunty Mimi tace, “Auta lafiyarka kuwa?”.
Saida ya zauna sannan yashiga kora musu bayani, dariya kawai sukayi, sunsan Sauban babu sauk’i wajen taso mutum agaba.

Tunda Sauban ya fita sai Galadima ya gyara zamansa kawai ya zubamin ido, mutum ne shi dabaya son shiga hak’in wani, ko kad’an baiso ace wane yana cikin damuwa ta dalilinsa……
Wayarsa aka kira, ya kalli wayar kafin yakai hannu ya d’auka, salamar da akayi daga can ya amsa suka gaisa.
Jin ya ambaci Nuren nagane da Wanda suka ta6a yin waya kwanakine, nad’an tsagaita da kukan ina sauraren mizasu tattauna. Galadima naji yace,
“miya farune kakeson nazo Nigeria haka da gaggawa Nuren”.
“no babu wani damuwa, driver da yarinyar nanfa suna hannu, so yakamata ka shigo muyi abinda yadace ko?”.
“ok babu damuwa, insha ALLAH zuwa Wednesday idan jikin Abie ya kuma lafawa zan shigo”.
“O right, ALLAH ya k’ara masa lafiya, a gaishesu”.
“zasuji insha ALLAH, bye”.
Wayar ya ajiye a tsakkiyarmu ya maida hankalinsa kaina.

Cikin wani salo yace, “Munaaya!”.
Wani Yarr naji a jikina, karo na biyu kenan danaji sunana a bakinsa, sainaji sunan nawa ya canja kamar ba shiba, danya iya sarrafa sunan a harshensa….. ganin ban d’agoba yakuma kiran sunan.
Kasa jurewa nayi nad’ago idona na kallesa, ganin ya tsareni da idanu saina janye nawa. yad’an lumshe nasa ya bud’e a kaina ya furzar da huci “kina ganin haka abokai yakamata su kasance? ni friend nakine, miyasa bazaki iya fad’amin damuwarki ba? kiyi hak’uri nasan kina buk’atar zuwa gida, last week naso maidaki Nigeria, amma sai jikin Abie Daya motsa ya dakatar dani”.
Tausayi yabani, nad’ago na kallesa, mutumne shi mai sauk’in kai, saidai idan baka fahimceshi ba zaka sameshi a amurd’e, domin yanada wahalar sha’ani, hawayen dasuka ziraromin na goge, muryata na rasa nace, “kayi hak’uri ina kewar su Munubiya ne, insha ALLAH bazan sake yin kukanba amma”.
Murmushi yaymin yana jinjina kai, yad’an shafa girarsa zuwa kai sannan yace, “kinada tsiwa, amma wani time d’in kinada kirki”.
Bansan lokaci da dariya tazominba, nad’an dara sannan nace kaima ai hakan kake, kanada tsauri kanada sauk’i”.
Yawani k’ank’ance idanu cikin wani salon kallon yace, “really?”.
Gira d’aya na d’aga masa nima nace, “yaah”.
Murmushi mai k’ayatarwa yayi yakwashi wayoyinsa yabud’e motar yafita batare data sake cewa komaiba.
Ganin haka nima saina fito fuskata washe da murmushi, kamar banice nagama kukan shagwa6a ba??.
Tunda muka shigo aunty Mimi da Momma suka zubo mana ido, Sauban kam dariyar shak’iyanci yafara k’asa-k’asa.
Momma tace, “ina kuka mak’ale haka?”.
Murmushi yayi yana zama kujerar dake kusada Abie yace, “ba ko ina Momma”..
Momma tayi ‘yar dariya tace, “shikenan tunda ba’aso muji”.
Sauban da Aunty Mimi ma dariya sukayi, nikam kunya tasani k’asa da kaina inad’an murmushi.

__((*))__((*))__((*))__((*))__

Abba dai bai yarda su maman yaa Hameed su kwana a gidanba, a daren kowacce tanufi gidansu, yayinda baba k’arami ya d’auki innaro zuwa asibiti.
Su Sa’eed kam zare jiki sukai suka koma gida, zukatansu tab da mamakin wannan lamari.

A ranar zarah sai sashenmu ta kwana a tsohon d’akinmu ni da munubiya, saboda Aminu ya sanar mata yaga Sa’eed da mijin Siyama a k’ofar gidanmu.
Gaba d’aya saitaji yau tanajin haushin mamansu, dan daba ta tanka dariyar da gwaggon Haleematu tamata ba ai dabasuyi rigima har Abba ya korasu gidaba, dayanzu gidanta zata kwana jikin mijinta itama, wane irin abin kunyane wannan kai kana gida uwarka na gidansu itama??????.

%%%%%%%%%%%%%%%

Dawowarmu kenan ni da Sauban da Samha daga zagaya gari, nagaji ovar, jikina sai ciwo yakemin, dama Yaya lafiyar giwa, saman sofa na zube Ina sauk’i numfashin wahala, wani zazza6ima nakejin yana neman rufeni, harna rufe idanu naji wayata na wringing, lalubowa nayi na duba mai kirana, nasan dai duk Wanda zai kirani to daga Nigeria ne, dan su Samha duk suna gida, Galadima kam bai ta6a kirana a wayaba, banmayi tunanin yanada number ba duk da shine ya sayi layin.
Sunan munubiya dana gani yasani fad’ad’a murmushina, saida nabari ya katse sannan na kirata.
Bugu biyu ta d’aga, jin muryarta can k’asa sai hankalina ya tashi, nashiga tambayarta ko lafiya.
“sweetheart wlhy banajin dad’i, ko school nakai sati banjeba, ya kuke?”.
“ayya sorry sweetheart, mike damunki?”.
“wlhy zazza6i, kema naji muryarki wata iri ai?”.
“nima lafiyar sai a slow wlhy, ina yaa marwan?”.
“tofa, ciwo a time d’aya mu duka? ALLAH yabamu lafiya to, yaa marwan yafita gaida su mama, ya jikin Abie da Galadima?”.
“everything Alhmdllh dear, jikin Abie ma yanata sauk’i, sun fara masa amfani da addu’oin, amma naji kamar doctors d’inshi suna complain wai abar shafa masa abinda ake shafa masa”.
“karku wani sauraresu, Ku cigaba kawai, ALLAH yasa muji alkairi”.
“insha ALLAH dear, dama haka Galadima yace shima”.
“ALLAH ubangiji yabashi lafiya, bara na barki ki huta, a gaida minsu”.
“ok sweetheart bye”.

Ina ajiye wayar na mik’e, bayi nashiga nahad’a ruwa mai zafi nagasa jikina kozanji dad’i, haka nake kusan yini wanka da ruwan zafi, wai ko zan dainajin ciwon jiki, amma a banza, danayi wanka bana wuce mintuna talatin ciwon yake dawowa sabo.
Wani ash d’in wando da Riga na jawo na saka, kayan basuda nauyi sosai, wandon kad’an yawuce guywata, rigar kam hannunta iya kafad’a ya tsaya, kamardai vest d’in maza take, saidai daga gaba tanada banbanci data maza. nasan Galadima bazai dawo gidan yanzuba saboda koya tashi aiki saiya biya ta asibiti kafin yazo gida, yanzu kuma akayi isha’i nasan sai zuwa irin 11, shiyyasa nayi tunanin sakasu ko zan ragema kaina nauyin jikin. komawa nayi saman sofa data zama gadona na kwanta, amma sai naji dukna takura, najujjuya naji babu dad’i kwanciyar, tsaki nayi namik’e nakoma saman gadon na kwanta, insha ALLAH kafin maishi yadawo dai natashi??.
Banfi 5minutes ba da kwanciya barci ya d’aukeni.

*****
Kansa daya fara matsa masa da ciwone yasashi tattara kayansa yabaro office, Dan yau sunyi overwork ne, suna shirin fidda laptop sabon k’ira, saida yashiga office d’in vijeey da Alexander yamusu sallama sannan yanufo gida, ko asibiti bai biyaba, Dan har wani jiri-jiri yake gani a idonsa, yasan barcin dabasa samun yine ya haddasa masa ciwon kan, bama kamarshi, Dan gara ni idan yafita nakan kwanta nayi barcin.
Da k’yar ALLAH yabashi Damar isowa gidan. Ko rufe motar baiyiba sai a cikin bayin ne wani yataso yarufe, a falo ya wuce Samha na barci itama, tunda muka shigo ta zube a wajen, tun yana taka steps d’in yafara cire bottom d’in Indian suit d’in dake jikinsa white color, burinsa yana shiga d’akin yagansa a gado kawai.
Ganina baje a gadon yasashi yin turus yana kallona, yay saurin kauda idonsa gefe saboda kayan jikina sun kamani sosai, sun mugun fito da surar jikina d’as, gashi sun bala’in min k’yau, yau da ace matar dayake soce babu abinda zai hanashi yabawa harma yabata tukuycin wannan kwalliyar, tsigar jikinsa sai tashi takeyi, gashin jikinsa duk ya mimmik’e, rigarma yakasa k’arasa cireta, ya dafe kansa yanajan guntun tsaki, miya kawo yarinyarnan gadonsa?. Yayi maganar cikin zuciyarsa.
Jin jiri na neman zubdashi a k’asa yay saurin zama bakin gadon, samu yay ya lalla6a ya ida cire kayan, duk da yafi buk’atar kwanciyar haka ya daure yad’an watso ruwa, sannan yafito yasha magani, koma shafa’i da wutiri baiyiba, a nufinsa sai zuwa anjima zai farka yayi.

Abin dariya, saiya jawo dogayen filullukan gadon yajerasu a tsakkiyar gadon sannan ya kwanta can k’arshe, shima babu dad’ewa barcin yay gaba dashi. (Wlhy kafad’o babu ruwana fad’ama fans zanyi Galadima ya tik’o k’asa ehe????????)
Can cikin barci Galadima yafara juye-juye, yasaba shi kad’ai yake kwana abinsa, jin fillos a gabansa yasa hannu ya d’aukesu yayta wurgawa k’asa cikin barci, sannan yay juyi zuwa tsakkiyar gadon.
Munaya kam tasaba da kwanciyar mutum biyu. dan haka ko juyin zatayi bata barin inda take kwance, duk da ma batasan da Galadima a gadon ba, tunda batasan ya shigoba.
Barci yay barci saiga su yalla6ai Galadima masu jera fillos a jikin munaya??, d’umin jikinta yasashi kuma nanik’e mata, saboda zazza6in daya rufeta, kasancewar yanajin sanyi-sanyi sai jikinta yamasa dad’i.
Itama saita kuma lafe masa a jiki saboda jin sanyi-sanyi da k’amshin turarensa kuma, sunbi sun k’adandane juna kaikace ana shirin rabasune, kowa yana amfanuwa da yanayin jikin d’an uwansa.

Humm, bara na lek’o su innaro ‘yan Nigeria suma??, mai tuk’ulluma a goshi ba????, ni nama godema mamansu yaa Hameed?? dama k’afar suka karya??.

_____________________________

Anbama innaro magani a wani camix suka dawo gida, gidanta aka kaita, innarmu tad’an dafa ruwa tazauna kusada ita tasaka k’aramin towel danta gasa mata goshin koza’a samu yarage tukullumar dayayi.
Innaro ta 6ata fusaka zatama innarmu tijara.
Baba k’arami yay saurin tareta da fad’in “haba inna, Dan ALLAH kibari tamiki, naga wad’anda suka miki abunma ko kallo baki ishesuba balle su nuna damuwarsu akai, wai shin minene laifin Ai’sha agarekine?”.
Abbanmu da daddy suna zaune basuce uffanba sudai. Harara innaro tazuba ma baba k’arami kawai amma batace komaiba, itakuma innarmu ta saka towel aruwan tafara gasa mata.
Tanama innarmu masifa dai har akad’an gasa mata, aikam saigashi wajen yad’an saki, baba k’arami yamik’a mata kofin tea d’in da maman fauziyya ta had’a.
Kar6a tayi tana yatsine Baki, amma saigashi ta shanye tas, aka bata magani shima tasha ta kwanta.
Basu bar gidanba saida tasamu barci, da innarmu tace zata kwana annan, sanin halin innaro Abba yace a’a tatashi suje gida tunda ga habiba d’iyar gwaggo safiyya dabata komaba.
Badan innarmu tasoba tahak’ura, Dan aganinta innaro itama uwace agareta, kodan hallacin da mijinta yama iyayensu da darajar abbanmu, amma takula ran Abba a 6ace yake, kad’an yake jira a ta6ashi ya fashe, shiyyasa bataja zancen yay tsawoba ma.

Koda suka shiga gida kowa sashensa yayi, innarmu harta kwanta saiga Abba yashigo d’akinta, abinda bayayi kenan, yakan shiga sashen matansa amma baya kwana, saidai mace tabishi nasa d’akin.
Tana yunk’urin tashi zaune zata tambayesa lafiya? ya d’aga mata hannu kawai ya hawo gadon tareda janta a jikinsa suka kwanta.
Bai bata damar maganaba Dan haka tayi shiru kawai kamar mai barci.
Kamar yanda Abba bai isashen barciba hakama innarmu batayiba, Zarah ma kwana tayi kuka akan rashin shigowarsu Sa’eed.
Hakama mamansu yaa Hameed da Gwaggon Haleematu basu rintsaba dasukaje gida.

Kwana biyu da faruwar lamarin Abba yak’i cewa komai, yakuma k’i sauraren wayar da ake masa daga gidan matan nasa.
Innaro harta fara samun sauk’i itama.
Sa’eed kam dadynsa ya taso k’eyarsa washe gari gidanmu, an tattauna akan maganar, yafad’i dukkan abinda zarah ke masa, wani ta amsa laifinta wani kuma ta musa ba ita tayiba, sai wani cikin iyayenmu ya harareta take shiru.
Nandai aka musu fad’a bayan itaba dad d’insa yace tafad’i abinda yake mata, saboda kar ahanata komawa saitace ita baya mata komai, wannan yasa aka musu fad’a da nasiha kawai akace yad’auki matarsa su tafi.
Dad’i tamkar zai kar zarah kuwa, saitaji zuciyarta wasai, bata tareda damuwar komai, (kota manta uwarta bata gidansu itama a dalilinta kuma???).

Washe garin rana ta uku tunda safe saiga mamansu yaa Hameed tareda yayanta ya maidota, (dayake babanta ya tsufa sosai, komai nasu yanzu sai yayan nata, ko kud’inma dashi suke tak’ama yanzun, duk da mahaifinsu ya tara musu).
Abba dai k’in saurarensa yayi, saida yaje ya kama k’afa da baba mai kanwa aminin marigayi mal. faruku, daddyne yamasu jagora zuwa gidan innaro dake kwance tana jiyyar goshi, damma kullum sai innarmu ta gasa mata safe da yamma, duk da masifar innaro da take sha batayin zuciyar ko nuna gazawa.

Ansha fama akan Abba kafin ya sauraresu, danma akwai baba mai kanwa ne a zancen, amma ya tabbatar musu da Cewar shifa yagaji da iskancin dasuke masa a gida, tun zamanin k’uruciya har girma yafara kamasu sun k’asa canjawa, yabama kowaccensu damar k’arshe inhar suka kuma Tayar masa da rikici agida kowacce zata nemi hanyar gidansune, kuma tatafi kenan har abada, Dan bazai duba ‘ya’yan dake tsakaninsuba ma.
Tunda ga ranar mamansu yaa Hameed tadawo gidan, Gwaggon Haleematu kam bata dawoba, itada iyayenta sunce sai Abba yazo da Kansa koya turo anbasu hak’uri.
Shikuma ya rantse saidai tayita zama inhar saiyaje bikonta.

Gidanmu dai kam kwana biyu tsit kakeji, Dan baba k’arami da daddy ma summa matansu kashedi da sharad’in barin gidan gaduk wacce tasake fad’a da wata, wannan dalilin yasaka gidan yin lafiya, ‘yan anguwa da makwafta sukaji kasiririt.

Innaro ma ta warke abinta, saidai kam sun k’ulla da mamansu yaa Hameed, Dan yanzu ko ‘ya’yanta basuda farinjini wajen innaro, ko Naziru autansu yamata Abu saita makeshi (ho innaronmu ta mutunci????).

***************

Zazza6i dai yahana Munubiya sakat, yaa marwan yagaji da lalla6ata ga ciwo na cinta, yau dai yakwasheta zuwa asibiti tana kukan batason zuwa, amma yak’i saurarenta.
Haka dai sukaje, bayan yankar kati dabin layi suka sami ganin doctor, gwajin farko doctor yabasu albishir d’in samun rabo na wata d’aya kacal (yaa marwan sharpshooter??, Munubiya dai inaga tuntu6e akayi????).
Wayyo zokuga murna wajen ogan miskilanci, babu kunya yakira Abbansa ya sanar masa, shima murna yaytayi ata cikin waya, kafin kace mi zance yabaje dangi, har innarmu labari yakai kunnenta.
Harda kukan dad’i tayi, ikon ALLAH kenan, ita saida ta jera shekara 20 tana kuka da shan gori kafin ta samesu, amma ga Munubiya wata 1 da sati d’aya da aure har ALLAH ya kawo rabo. Saura munaya, k’ila itama d’indai an samu, tunda shekaran jiya dasukai waya take mata complain batajin dad’i. haka innarmu taita murnarta a d’aki ita kad’ai, babu Wanda ta sanarmawa tabarma cikinta, a cewarta idan yafita ko Munubiya tazo gidan sagani.

Abin nema yasamu fa, yaa marwan tamkar zai maida Munubiya ciki, kokuma ya maido cikin nata jikinsa yarage mata wahalar laulayi haka yakeji, Dan tana d’an shan wahala gaskiya. ko girki yanzu bata iyayi balle gyaran gida.
Hakanne yasaka mama rabi’a cewa yadawo da Munubiya wajenta harta samu sauk’i.
Saiya fara fushi da rok’on tabarta Dan ALLAH shima zai kula da ita ai, abasu Ayusher ko feena takoma wajensu saita taimakawa Munubiya da aikin gidan.
Mama Rabi’a tace a’a, Ayusher itake taimaka mata itama, feena kuwa ba cikakkiyar lafiyace da itaba, ba kowanne aiki take iya yiba ko agida (kunsan masu sikila dai??????, ubangiji ALLAH yabama dukkan masu irin wannan ciwo lafiya, ALLAH yasa yazamema rayuwarku kaffara kuda iyayenku da kullum suma hankulansu ba a kwance sukeba??, duk mai wannan ciwon ina tsananin tausayinsa wlhy??).
Babu Wanda yaa marwan ya iya, dole ya tattaro kayansa shida Munubiya suka dawo gidan kawai, ai ko su Ayusher sunci dariya, danma fadeel bayanan, saidai a waya suka bashi labari.
Munubiya tacigaba dasamu kulawa wajen mama Rabi’a, bata aikin komai saidai amata, sai idan boss nason rage nauyi ya janyeta d’akinsa da wayo ya kashe arna????.
Mama Rabi’a duk tana kula da su, amma saitayi kamar batasan bikin dasukeyiba, Dan taga idon yaa marwan a tsakar goshi yake????.

??kai jama’a mu koma India.????????????

…………………………………………….
______________________________
…………………………………………….

Zafin jikinane yafara masa yawa, dan yafara shiga sosai jikinsa, cikin barci ya laluba danson jin minene mai zafi ya rungume haka? jin kamar mutum yasashi k’ok’arin bud’e idonsa dasukai masa nauyi saboda barci, dishi-dishi yafara ganin fuskar munaya, hardai yasamu nasarar bud’e idon gaba d’aya a kanta??……………..???

_ALLAH ya gafartama iyayenmu?????????_
*_Typing??_*

*_Haske writer’s asso…._*??

*_?RAINA KAMA……?_*
_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull Ce_*????

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply