Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 16


Raina Kama Book 2 Page 16
Viral

~Book 2~ ????1?6?

……………..“Kin shirya taimakon Mijinkine Munaya?”.
A salon da yay maganar saida tsigar jikina ta tashi, nad’an lumshe idanu sannan na bud’e a kansa, muryata na rawa nace, “ni bansan komaiba. kuma ina ganin a wajen Abie yakamata ka k’ara samun haske ai, tunda yanzu yana magana”.
Murmushin takaici yayi, sannan ya kamo hannuna cikin nashi, “Kinsan miyasa nabaki dukkan wannan labarin daba kowanne mahaluki ya sansu baki d’aya ba?”.
Kaina na girgiza masa a sanyaye.
Ya murmusa, tareda d’ora hannunsa saman cikina, hannun nasa na kalla, shima idonsa na a wajen, yace, “saboda kece wadda zata zama uwar d’ana ko ‘yata, ina fatan koda nabar duniya ban cimma burina ba kibama duk abinda kika haifa labarinnan domin ya ida cimma manufata, wannan wasiyyace ga abinda zaki haifamin, dan inaji a jikina komi zaki haifamin insha ALLAH ba zai zama ragoba, sannan kuma tabbas kin cancanta, domin kece mutum ta farko dana ta6a yarda bazataci amanata ba bayan Mahaifiyata da kakannina da yayata da k’anina. daga k’arshe ina rok’onki girman ALLAH ki sanarmin da abinda kika Sani game dani, dan tabbas nasan kinsan wani Abu, nasha auna fik’irarki a ma’auni kuma ina samunta dai-dai, dan haka batun 6oyemin ma kibarsa zuwa yanzu, kinga Abba jibine zasu koma, to lallai rayukansu tana cikin had’ari kuma komai zai iya faruwa, saboda a yanzu mak’iyansa sunyi shirin dayafi na farko ma, a zatonsu Abbanki yasanar dani komai ne. ni kuma ban ta6a wannan maganar dashiba, sannan Abie da kike magana likitoci sunyi gargad’in kar’a tuna masa da abinda ya wuce yanzun, saboda gudun dawo da hannun agogo baya, kuma kodama na tambayesa zai iya dakatar dani yace ya yafe, ni kuma nariga nataso da BURIN ‘DAUKAR FANSA, a cikin zuciyata da kwanjina, Ni nasan Yaya nayi jiyana, yau d’ina ma a wahale take kasantuwa, dan haka nakeson gyara gobena da goben ‘ya’yana da dukkan ahalina, inason sanin dalilinsu nama mahaifina hakan, inba hakaba bazan ta6a samun kwanciyar hankaliba”.
Nad’an muskuta domin gyara zamana, ina fad’in “shikenan, amma kabani lokacin please”.
“Nabaki”. yafad’a yana mik’ewa tsaye.
Binsa kawai nayi da kallo, saiya kuma bani tausayi, dukda kasantuwar rayuwarsa cikin Rud’ani, hakan bai habashi zama kamilin mutum mai tarin Nutsuwa ba, gashi da sauk’in kai, saidai idan baka fahimceshi baneba, kamar yanda na kasa fahimtarsa a farko, saika masa kallon mai girman kai.

A gaba d’aya yinin wannan ranar cikin nazarin maganganun galadima na yisu, tabbas abotar Alhaji Mamman kurfe da Senator Halluru da Abbana abin dubawace, na shiga tunano wasu abubuwa danaita karo dasu a d’akin Abbana ni da Munubiya, a wani time d’in da Innarmu ta sakamu masa wani gyaran d’aki, Wanda shine sanadin shigowarmu wannan cakwakiyar kuma, na dafe kaina saboda saramin d’in da yakeyi, motsin da d’an cikina yayine ya sakani dafe cikin ina lumshe idanu, gaba d’aya kaina yana Neman kullewa, har a washe garin ranar haka naita fama da tunani, danma yana hanani, amma danaga ya matsa zan d’ora daga inda na tsaya, yanzu ma dazai fita aiki saida yamin gargad’i, yace na sauka k’asa wajensu innarmu nayi hira, to kawai nace masa, amma yana fita ban fasaba, ganin lokaci na k’ara k’urewa saina d’auki waya na shiga rubuta massage mai tsawo dazan turama Munubiya.

Duk abinda takeyi a idon Galadima ne, tun d’azun yana lura da dukkan motsita ta camera d’in daya ajiye a d’akin wadda koda wasa Munaya batasan da zamanta ba, ya murmusa tareda godema ALLAH, dan yasamu damar kamata a hannu, ta wannan hanyarce kawai zaiyi amfani da ita wajen samun abinda yake buk’ata ga Abbanta, dan Abba yak’i bashi kowacce k’ofa dazai san wani abinda ya sakashi shiga wannan halin, alhalin yaga tarin damuwoyi a idanunsa, masu kuma matuk’ar muhimmanci a aikinsa.
Wayarsa tai ‘Yar k’ara alamar Munaya na sarrafa wayarta, saurin saita abinda ya saka mata a wayarta bata saniba yayi, harta gama typing ta tura sak’on akan idonsa, shiga yayi ya duba, saiyaga Munubiya ta turama sak’on, yay hanzarin bud’ewa. (Galadima ya had’a wani tarko a wayar Munaya batareda ta saniba, dukkan wani Abu dazai shiga wayarta ko fita saiya gansa a wayarsa, ta wannan hanyarne yaga na yanzu, saimu bishi muga abinda Munayar ta rubuta to).

_“ ‘Yar uwata, tabbas Allurafa na shirin to no galma, anzo ga6ar da lallai yakamata mu sanarma Galadima komai akan abinda muka Sani, danna fahimci lallai zatonmu yazama gaskiya, wannan sunedai ahalinnan da mukaga bayanai a Kansu, dukda nakula Abbanmu nasan basarwa, saidai bansan manufarsa tayin hakanba, bayan wannan itace damarsa ta k’arshe dazai yadda kwallon mangwaro ya huta da k’uda, sweetheart minene shawararki? dan burina dana haife cikinnan auren contract ya k’are a tsakaninmu, domin babu alak’a kuma kenan, kinga nima na samu ‘yancin kaina, nayin auren din din din kamar kowacce mace”._

Babu shiri Galadima ya mik’e tsaye, jikinsa har wani tsuma yakeyi, lallai anzo ga6ar Ashe, hasashensa yazama gaskiya kenan kokuma zai zama, tomi wad’annan yaran suka sani? kenan Munaya Nada dalilinta na yarda da auren su na Contract? Mi Muftahu ya Sani gameda Munaya dahar ya d’anata a gareshi a matsayin tarko?, bayan shi yana nan yana ik’irarin yima Muftahu tarko da auren Munayar. Lallai kan yakula itama Munaya da ‘Yar uwarta da Muftahu suna Neman zame masa RAINA KAMA.

Baifi mintuna 15 ba da tura sak’on da Munaya tayi, saiga Munubiya ta kirata, duk Galadima yana kallo daga camera d’insa da kuma saitin wayarsa, dukda kuwa yana office ne, Munaya bata d’aga kiranba, saida ya katse sannan ita ta kirata, munubiya na d’agawa Munaya race, “Sweetheart kinga sak’ona kuwa?”.
“Na gansa sweetheart, amma fa ni duk kin rikitani, kinga wata alamace data tabbatar miki ahalin Galadima ne?”.
“Munu, tabbas alamomi da yawa sun nunamin hakan, sannanfa shima yasan Alhaji Mamman k’afur fa, kuma kinga ai a takardarnan munga sunan Alhaji Mamman k’fur d’in, gashi abokin Abbanmu sosai, nifa yau wlhy abubuwa masu yawa ya fad’amin game da sirrinsa, dukda kasancewarsa mutum mara yarda, duk dai da inaji a raina kamar ya fad’amin wani yankin sirrinsane danya bigi cikina be, amma ni wlhy tausayi guy d’innan yake bani da gaske”.
Munubiya tayi murmushi daga can, cikin tsokana tace, “to ALLAH yabar k’auna dai, sweetheart”.
“ban ganeba, k’aunar mi zai bari?”.
“keda Galadima mana, ai soyayya kan fara da tausayine”.
“Mtsoow dan ALLAH muyi magana mai amfani Munu, yanzu ya kika gani, danya rok’eni ALLAH akan nafad’a masa mina Sani, nikuma ina tsoron koba akansa d’in baneba Abbanmu yake cikin damuwar, karmuzo kuma muyi aikin Baban giwa”.
Ajiyar zuciya Munubiya ta sauke, ta gyara kwanciyarta tana fad’in Munaya kodai mu sanar da innarmu ne kozata bamu shawara?”.
“kai amma bakida hankali yasin, sokike innarmu taci k’aniyarmu Ashe, zatace miyasa tun a farkon lamarin bamu sanar mataba, k’ilama tayi fushi, Dan nima wlhy ayanzu ina ganin munyi wauta fa”.
“to komadai miye munrigada mun aikata. Yanzu mafita zamu nema, mizai hana ki rok’eshi inhar bashi bane kokin fad’a Dan girman ALLAH karya tada zancen kawai, yakuma rik’e mana sirrinmu, idan kuma zai taimakemune akan Wanda kema Abbanmu barazana da mutuwa ai kingani munsamu madafa muma, kinga dai yanda sukaso cin galaba wajen kashesa, wlhy Munaya jinake kamar kar Abbanmu su dawo k’asarnan”.
“Ni kaina tsoron dawowar tasa nakeji, musamman da jiya Yakuma maimaitamin, shiyyasa kawai na Yanke shawarar mu fad’a masa, idanma ba shi bane saiya taimakemu wajen gano wanene”.
“to shikenan, sai naji yanda kukayi kenan, Yaya unborn d’inmu?”.
“gashi nan ya isheni da motse-motse wlhy, na k’agara ma ya fito na huta, kema Yaya namu da lafiyarki?”.
Cikin tsokana Munubiya tayi dariya, “aikoya fito nanda wata shekarar Munafata wani ya Shiga sweetheart”.
“wlhy na kula bakida man kai Munubiya, sai anjima”. Munaya tafad’a tana yanke wayar.

Galadima daga can yay wani k’asaitaccen murmushi yana shafa Kansa da cije lips, ya koma jikin kujera ya lafe yanamai lumshe idanu.

??
??Galadima Kodai-kodai??

************

Muna gama waya da Munubiya na sakko k’asa, babu kowa gidan dagani sai su innarmu sai jakadiya, a falon k’asa na iskesu suna hira.
Jakadiya tace, “ranki ya dad’e kin fito?”.
Murmushi namata, ina fad’in “na fito jakadiya, ya k’ok’ari?”.
Tai ‘yar dariya tana cewa “kuke fama da k’ok’ari ai, ALLAH dai ya raba lafiya”.
Bance komaiba na zauna ina gaida Innarmu ta amsa tana tambayata ya jikin.
“da sauk’i” na fad’a kaina a k’asa, nace, “innarmu Abba fa? ko barci yakeyi?”.
“A’a sun fita ai shida Sauban tunda safe, zasuga likitansa daga nan sud’an zaga gari”.
“Oh ALLAH ya dawo dasu lafiya to, zaisha yawo kam indai fita da Yaa Sauban ne”.
Dariya jakadiya tayi, tace, “ai mai sunan manya sai a hankaki, shibama ya gajiya”.
Inna tace, “a baya gajiya kam, ni ai birgeni yakeyi, babu ruwansa, sai tsokana da barkwanci”.
“Ai tamkar gadone abin nasu, dan mai martaba lokacin yanada lafiya, dukda kasancewarsa shugaba hakan baya hanashi barkwanci da mutane lokaci-lokaci, to hakama magajin gari yake, daga bayane shi sai nasa halayyar suka canja, yazama shiru-shiru, amma shi mai sunan manya saibai canjaba kuma”.
Ina jinsu nidai bance komaiba, sai murmushi danake tayasu dashi kawai.
Mun dad’e a falon har su Abba suka dawo, masaukinsu ya wuce, Sauban kuma ya zauna muka cigaba da hira, tashi innarmu tayi tabi bayan Abba.
Sauban ya mik’e yana cewa zaije ya watsa ruwa, itama sai jakadiya tashiga domin nunawa kuku abinda zai dafa, ganin haka natashi na nufi masaukin su innarmu.
Nakama handle d’in k’ofar zan murd’a tareda yunk’urin sallana sainaji muryar innarmu kamar tana kuka, “Haba Abbansu dan ALLAH ka sanarmin damuwarka, Yaya kana cikin matsala amma ka gaza fad’ama kowa?, tunda tafiyarnan tamu ta gabato ina lura dakai baka ko barcin kirki, sannan inajinka kana sambatu cikin mafarki jiya da asuba akan kozasu kasheka bazaka bayarba, shin wai minene? kuma su waye?, nidai tun bayan haihuwar su Munubiya na fuskanci kana cikin wata damuwa, amma kullum cikin k’ok’arin 6oyewa kake, bansan minene kake 6oyewarba, haba Auwal, a tunanina yanzu munzama irin d’ayan da bazaka 6oyemin matsalaba kowacce irice, a nawa tunanin munkai bigiren raba farinciki ko sa6aninsa, ko kasan ranar da muka fita da dasu Samha naga lokacin da wani bak’in mutum yazo kuka ke6e gefe, kana kuma magana tsakaninka dashi cikin fushi”……
A rikice naji Abba ya katseta da fad’in Ai’sha kenan ido kike sakamin ban saniba?, dan kawai kin ganni da mutum saiki fassara da wani Abu, Toni banma sanshiba, dan kawai ya ganni bak’in fatane shine yake tambayata, amma daga hakan babu komai, tunba yanzuba kikemin tambayar mike faruwa ina baki amsa babu komai, miyasa bazaki yarda babu komai d’inba, ni nama matso da tafiyar tamu baya, dan doctor yakuma tabbatarmin da babu wata sauran matsala, ki sanarma Munaya ta sanar da mijinta gobe zamu koma kawai”.
“gobe kuma Abbansu?”..
A fusace yace “eh!”.
Ni kaina saida na razana da tsawarsa naja baya daga jikin k’ofar, da sauri nabar wajen jin alamun za’a bud’e k’ofar, tabbas akwai abinda Abbanmu ke 6oyewa da gaske, to wanene bak’in fatar da innarmu tagani tare da Abba ranar? a ranar tare dasu muka fita, saidai sun rigamu tafiya, saboda ni da Galadima mun biya asibiti wajen awo, saida akamin sannan mukabi bayansu, kenan kafin muje abin ya faru? dan tabbas na tarar Abba baya cikin walwalarsa, harna tanbayesa ko jikinsa ne? Amma yacemin a’a kansane kawai ked’an ciwo.
Bansan na iso bedroom d’inmu ba saboda zirfi danayi a tunani, ko hawan benen ma bansan nayoba, juyowa nayi da sauri saboda jin an kama hannuna. ganin Galadima saina rajaza zanyi baya, da sauri ya rik’oni da k’yau yana fad’in “Nutsu mana”.
Da k’yar na tattaro nitsuwa ta, shikuma ya zaunar dani gefensa, hawayrne suka shiga ziraromin a kumatu, Abbana yana cikin matsala, amma wani dalili ya hanashi fad’a, takai har inda yake jiyya ana bibiyar rayuwarsa kenan?.
Ido Galadima shidai ya zubamin, bai hanani kukanba baikuma tambayeni dalilin yinsa ba, kusan 5minutes sannan ya kwanto da kaina jikinsa, jina a k’irjinsa saina fashe da sabon kuka, nanma k’ala bai ceminba, yadai cigaba da bubbuga bayana alamar lallashi, saida nayi mai isata nayi shiru sannan ya d’agomin kaina, dukkan kumatuna ya rik’e cikin tafin hannunsa, Kafin yay k’ok’arin saka idanunsa cikin nawa, cikin k’asaitacciyar muryarnan tasa mai kama da anmasa dole yace, “Haba yalla6iya, sokike ki haifamin abin cikin kwan mai saurin kuka irinkine wai shin?”.
Bansan Sanda murmushi ya su6ucema fuskata ba, na lumshe idanuna saboda bana da jimirin jure kallon da yakemin, shima murmusawa yayi, sannan yakai fuskarsa dab da tawa yana huramin iskar bakinsa a saman ido.
Ban iya hanashiba kusan mintuna 2 sannan ya daina, bud’e idona nayi nad’an kallesa, ya d’agamin gira yana fad’in, “ya dai?”.
Cikin tunzuro baki nace, “babu komai”.
“To miye abin jin haushi daga tambaya”. ‘yay maganar yana sakin kumatuna’.
Binsa nayi da kallo, ganin zai fara k’ok’arin cire kaya, na mik’e zan fice, dan yanzu na lura lamarinsa kullum k’ara girmama yakeyi, baya shakkar cire kaya a gabana ko sakawa, sai dai ni na fita na bashi waje.
Hannuna ya rik’o, na waro ido waje cikin mamaki.
“ina zaki?”. ya fad’a cikin tsare gida.
“ba wanka zakayi ba?, idan kagama zan dawo ai”.
“toni dodone?”.
“A’a na fad’a ina ta6e baki”.
“to koma ki zauna ki kalli sadakinki”.
Idanu na waro masa waje da hangame baki.
Yiyai kamar bai ganniba ya basar. bai sakeniba yakuma cigaba da cire kayansa da hannu d’aya. Ni daifa k’in kallonsa nayi, dan wlhy kunya nakeji sosai, dukda ‘yar shak’uwa ta shiga tsakaninmu hakan bai sa mun saki jiki da junaba, garama shi idan rashin kunyarsa ta motsa yakanyi abinda ya gadama yana basarwa a dole kar’a kawo masa raini. Yakan bani dariya sometimes, amma nima saina Basar saboda Jan aji.
Iska kawai naji a cikin kunnena, da sauri na waigoshi, ganin sa dagashi sai boxer sai na juya fuskata.
Bayana ya koma ya zagayo da hanayensa duka akan cikina, yayinda kansa ke a kafad’ata, muryarsa can k’asan mak’oshi yace, “miya sakaki kuka?”.
Salon da yay maganar ya sakani lumshe idanu saboda tsigar jikina data tashi.
Nace “kabari ka gama zan fad’a maka”.
“miyasa ba yanzu ba?”.
“ka saka riga to”.
Murmushi yayi yana shafa cikina, “my friend sarkin tsiwa sarkin kuma Kunya, akwaiki da abubuwan bi……..”
Saikuma yay shiru yak’i k’arasawa, hannuna na saka na rik’e hannunsa da ke yawo saman cikina, nace, “ka k’arasa mana, akwaini da mi?”.
“Humm” kawai ya fad’a yana sakina, yaja bathrobe d’insa dake jikin hangar ya sanya, saida naga ya fara k’ok’arin d’aure igiyar sannan na d’ago na kalleshi.
“To mikuma kike kallo?”. Ya fad’a cikin tsare gida.
Baki na ta6e ina fad’in, “miye abin kallon to?”.
Ya d’an fiddo ido sannan ya matsoni, “zona nuna miki”.
Nasan ko guduwa nayi saiya kamoni dan haka na duk’e ina fad’in “wash ALLAH cikina”.
Tsayawa yay cak, saikuma ya tako da hanzari yana tambayar lafiya?.
cikin marairaice face nace “Motsi yakeyi ALLAH”.
rankwashina yayi aka yana cewa “ke d’inan ko”.
Dafe wajen nayi, bai kulani ba ya shige bathroom, na harari bayansa ina masa gwalo, nasan inda banyi hakaba bakina ne zaisha wahala.

Ina zaune ya fito, na d’auke kaina tamkar ban ganshiba, shima hakan yayi, ya wuce wajen frigate ya d’akko ruwa da Kofi, kujerar dake wajen karatunsa ya jawo ya zauna yana fuskantata, batareda yayi yunk’urin cire bathrobe d’in jikinsa ba, yanzun kam babu wasa a fuskarsa, ban damuba dan nasan halin kayana yanzu, yanzu zakiga yasaki jiki yana magana kamar ba shiba, anjima kad’an saiya koma Asalin Galadimansa dana fara gani a Hospital, Mara dariya mara later r??.
K’afarsa d’aya ya d’ora kan d’aya yana shan ruwa, yasha kusan rabi sannan ya cire, batareda ya ajiye kofinba ya maido dukkan hankalinsa kaina, “A kwana biyunnan kokin lura Abba yana cikin damuwa?”.
d’ago idanuna nai na kallesa, a sanyaye nace, “abinda naji innarmu na masa Complain kenan yanzu, amma saiya nuna fusata”.
“shine kika shigo kina kuka?”.
Na jinjina masa kai batareda nace komaiba.
Shima bai sake cewa komanba ya kauda idonsa daga kaina yana kur6ar ruwansa. kusan 2minutes sannan yakuma kallona, “Munaayaa mukawo k’arshen 6oye-6oye mana”.
Kallonsa nima nayi, nace, “kamar ya?”.
“humm” yafad’a yana cije lips, mik’ewa yayi tsaye ya ajiye cup d’in hannunsa a gabana, sannan ya shiga zagaye d’akin hannunsa goye a baya, nikam dai binsa kawai nakeyi da kallo kamar na samu television, maganarsa ta katsemin tunanina.
“Munaaya! Mikuka ta6a gani a d’akin Abba ke da ‘Yar uwarki?”.
Zumbur na mik’e dan mamaki, “yalla6ai a ina kasan wannan?”.
batareda ya kalleni ba yace “Munaya Sameer ya wuce dukkan tunaninki, dan haka fad’amin?”.
Ajiyar zuciya na sauke, wadda ta tilasta masa juyowa ya kalleni, nace, “yalla6ai ba fad’a maka bane matsalar, kuskuren muhallin fad’arne da kuma makomata”.
“bakida dukkan Matsala da wad’annan, idan bai danganceni ba zan d’auki matakin taimakon sirikina, makoma kuwa inada yak’inin kare martabar matata uwar d’ana ta kowanne hali”.
Furicinsa yaban mamaki, dan haka nace, “matar Contract ko?”.
“Well Duk yanda kika fassara dai-daine, abinda na Sani kawai wannan maganar batada nasaba da waccan, dan haka kibar kowanne a muhallinsa sai lokacin yinsa yayi”.
“humm” kawai na fad’a na koma na zauna inda na tashi.
Idonsa a kaina ko k’yaftawa bayayi.
Na nisa sannan nafara fad’in,

_“Na tabbata tunkan ka k’ulla alak’a dani saida kasan koni wacece, dan babban mutum irinka bazaiyi Abu babu wani tanadiba, banida matsala wajen maimaita maka sunana ko tarihin ahalin dana fito, kamar yanda kasani mu ‘yan biyune hakan yasaka ba’a banbancemu ni da ‘yar uwata, sai dai hallaya takan banbantamu ga Wanda ya sanmu, Munubiya mutumce mai hak’uri da yawan kawaici, a wajen gadon hali tabbas ta biyo mahaifiyarmu ne, sa6anin ni Munaya mai zafi da yawan tsokana, a lamarina babu ragi ko d’aga k’afa, inhar kaga nayi dogon zama da mutum babu sa6ani to ka tabbata ya tanaji matakan iya zama danine, basai amfad’a ba nima kaina nasan halayena na kamanceceniya dana Mahaifina da kuma kakata innaro, a wata litinin d’in da bazan ta6a mantawa ba sai mahaifinmu yayi wani bak’o, matsalar da aka samu shine yazo bai iske Abba a gidaba, a wannan ranar innarmuce da aiki, dan haka hak’in tarbar wannan bak’o saiya rataya a wuyanta, maimakon tayi da kanta saita saka cikinmu ni da Munubiya wani yayi”._…………………..???

 

 

Mu had’u a page na gaba??

 

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu??????_*
*_typing??_*

?? *_HASKE WRITERS ASSO….._*

*_?RAINA KAMA…..!!?_*
_(Kaga gayya)_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply