Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 14


Raina Kama Book 2 Page 14
Viral

~Book 2~ ????1?4?

…………….Yanda ya rik’e hannun yasani fad’in “please yalla6ai akwai zafi fa”.
Sassauta rik’on yayi, ya sauke ajiyar zuciya, muryarshi a sanyaye yace, “Miyasa kikeson 6oyemin abinda kika Sani? shin bak’ya tausayinane? kullum cikin aiki kwakwalwa ta take, aikin Neman kud’in da zan taimaki kaina da ahalina, aiki akan mak’iyana, ya kike tunani a kaina? yanzu haka ji nake tamkar kwalwar kaina zata tarwatse saboda damuwa da abubuwan da suka sakata matuk’ar nauyi, ta6a kiji yanda zuciyata takoma bugawa a slowly”. ya kamo hannuna ya d’ora a k’irjinsa, saitin zuciyarsa. da gaskiyarsa kad’an-kad’an zuciyarsa ke aiki, ba kamar kowanne bugun zuciya dake tafiya normal ba. Sai naji tausayinsa ya kamani, cikin sanyin murya nima nace,
“yalla6ai kayi hak’uri da abinda zan fad’a maka, inhar ka kawoni gidanka ne domin muyi aiki tare a matsayin Friend bai kamata ace ka gaza yarda daniba akan sirrinka. kasan minene yake saka kwalwarka da zuciyarka wannan nauyin kuwa?”.
Kansa ya girgiza mini.
Na gyara kwanciyata ina kallon p.o.p, “Matsalarka d’ayace baka yarda da kowa ba sai kanka, mu cire Momma da papi, dansu aiyukansu sunkai amusu uzuri, Momma hankalinta akan jiyya yake, dan haka kana k’ara mata damuwa, papi kuma babbane shawara da dabarun manya kawai kake buk’ata daga garesa. Sai kuma Muftahu da Harun nakula suma kakan d’an saki jiki dasu akan wasu abubuwan, to amma fa………”.
Saitayi shiru bata k’arasaba.
Ya matso jikinta sosai, tare da d’ora hannunsa saman cikinta, murya k’asa-k’asa yace, “Harun da Muftahu amma fa mi? Please ki k’arasa mana”.
Kad’an Na juyo nad’an kallesa, Na d’ora hannuna nima akan nasa daya d’ora akan cikina. Janye fuskata nayi Na koma kallon p.o.p d’in. “kayi hak’uri da abinda nake fad’a, badan ina zarginsu bane zan fad’a d’in, dama zancene Harun da Muftahu kuma kamar bai kamata 100% susan komaiba, dan za’a iya sayensu ko tursasasu suci dunduniyarka. domin koba komai har yanzu bakada tabbas d’in cewar babu hannun wasu a cikin masarautar nan. amma kayi hak’uri idan na shiga hurumin daba nawaba”.
Shiru yay baice komaiba tsawon lokaci, har nayi zaton nayi laifi ko yayi barci, a sanyaye nakuma fad’in “please & please kamin afuwa yalla6ai”.
“is okay”. ‘kawai ya fad’a yana kuma sakani a jikinsa, tareda d’ora ha6arsa saman kaina.
Babu Wanda yasake magana a tsakaninmu, kowa yay shiru yana k’ullawa da kwancewa, har dai barci yafara fisgata.
“Kina ganin su Aiyaan bazasuyi kuka ba idan suka farka sukaga su kad’aine?”.
Naji maganarsa cikin kunnena.
“a’a” na fad’a ina girgiza masa kai, “ko’a gida sukad’ai suke kwana dama”.
“okay”.
Saikuma muka kuma yin shiru, har barci yakuma fara d’aukata yakuma fad’in “kozaki sha Magani ne?”. ‘yay maganar yana ta6a gefen wuyana’.
Kaina Na girgiza masa batareda nace uffanba. shima bai sake cewa komaiba..

Yanda numfashina ke sauka a hankali sai ya fahimci nayi barci, shiko gaba d’aya yakasa nasa barcin, tunanin wani Abu daya ta6a faruwa a baya ya fad’o masa, dukda shi ba yayi imani da hakan baneba.
????
*_Wata ranar juma’a a India, sai suka tashi da matsananciyar damuwar motsawar ciwon Abie, a time d’in ma sun zata rai zaiyi halinsa, hankalin Galadima ya tashi har ciwonsa shima yakai ga motsawa, amma yak’i yarda doctors su dubashi, yace abarsa kawai gara ya mutu ya huta, hankalinsu momma ya tashi, amma Galadima yak’i sauraren kowa, daga k’arshema saiya sulale daga asibitin ya fice abinsa, haka yayta tafiya rik’e da k’irjinsa saboda azabar ciwon da zuciyarsa ke masa, mutane sai kallonsa sukeyi, shiko baimasan sunayiba, yayi tafiya mai nisan gaske batareda yasaniba. k’arfinsa da kuzarinsa sukai gazawar da bazai iya cigaba da tafiyanba, shine yazube a wajen ya fad’i._*
*_bai tashi farkawa ba sai awani d’aki mai kama dana bunu, ya yunk’ura zai mik’e amma saiya kasa, wani tsoho ba indiye, a cikin indiyawan ma irin masu k’yawunnan sosai, ya dafa kafad’arsa, cikin harshensu yace ma Galadima “koma ka kwanta d’an saurayi, bakada lafiyane”. Galadima yace “kayi hak’uri baba gida zanje nasamu sauk’i, zamana annan bak’aramin tashin hankali bane ga ahalina”. tsohon yay murmushinsu Na manya, yace “zakaje gida d’ana, ni da kainama zan kaika, amma lallai kai acikin al’amuranka akwai abubuwan ban mamaki da al’ajabi, gakuma tsantsar rud’ani, saidai komai yanada lokacinsa, kuma lokaci zai tabbatar maka hakan, albishir d’aya zanmaka, nanda wasu shekaru dabasu Gaza 7 ba mai taimakonka zatazo, kwarai zatazo gareka, ba lallaine ka fahimci abinda nake fad’aba ko yarda dani, Dan Na lura kaid’in musulmine, kuma bad’an wannan k’asarba, amma wannan mai taimakon naka itace zata zama fitilar haska maka hanya kakai ga cinmma burinka, domin taurarinta da naka sunada matuk’ar k’arfi, harma suna gogayya da juna, zaku zama sh……..”. Saikuma yayi shiru yana murmushi, ya shafa kan Galadima yana fad’in “tarin Albarka sucigaba da baibaye rayuwarka data zuri’arka”._*
*_daga wannan maganar sai barci mai nauyi ya kwashe Galadima, koda ya farka saiya gansa a asibiti tareda su Momma, yata tambayarsu INA tsohon yake sukace su basu San wani tsohoba, wasu samarine su biyu suka kawoshi asibitin, wai sungansa yafad’i a gefen hanya, zancen tsohon yata damun Galadima a time d’in har yayta bincike kozai gansa amma ko alamun mai kamarsa bai ta6a ganiba, daga hakama saiya cire abin a ransa yacigaba da harkokinsa._*

Ajiyar zuciya ya sauke, tareda kuma rungume Munaya, a kan la66ansa ya furta “ALLAH kaine mafi sani”. daga haka yay shiru tareda lumshe idanunsa, barcine yayta fusgarsa harya samu nasarar sacesa.
Can gabannin asuba yay wani mafarkin daya sakashi farkawa a firgice, har itama Munaya ta farka tana tambayarsa lafiya?.
Kansa ya dafe, da hannu yaymin nuni na bashi ruwa.
Sauka nayi daga gadon dan zazzza6inna ya fara hucewa nima, freight na bud’e na d’akko masa ruwa, na had’o da Kofi, zama nayi kusa dashi a gefen gadon na tsiyaya ruwan a Kofi na mik’a masa. kar6a yayi ya shanye, ya mik’o min kofin, zan kar6a ya girgiza min kai tare da min nuni da in k’ara masa.
Kuma tsiyaya masa nayi, yakai rabi ya d’aga min hannu alamar ya Isa, bayan yakuma shanyewa ya mik’a min kofin yana fad’in “Thanks”.
Kar6ar kofin nayi, ba tareda na tashiba nace “Yalla6ai lafiya kuwa”..
“Mafarki”. ‘yafad’a yana komawa ya kwanta’.
Idanu kawai Na zuba masa, kusan 4minutes ya juyo da kansa ya kalleni, “kizo ki kwanta mana”.
K’aramar ajiyar zuciya kawai Na sauke Na mik’e, Na d’ora ruwan da Kofi a dirowan gefen gadon na koma inda nake na kwanta.
Ganin ya sauya hannun da yay mafarkin kuma yana addu’a sai ban sake cewa komaiba, na kwanta shiru ina sak’e-sak’e a raina mafarkin mi yayi to? da har yasakashi firgita irin haka?. banida mai bani amsa dan haka nayi shiru.
Saiya zamto da asuba na rigashi tashi, harma saida nayi alwala sannan na tadashi, da k’yar ya iya tashi yana dafe kai, binsa nayi da kallo kawai harya shige toilet.
Lokacin daya fito na fara salla, dan haka saiya fice kawai. A mamakinsa saiya iske Aiyaan da Aryaan sun tashi suna alwala, hakan ya Burgesa sosai. Sai kawai ya kama hannunsu suka tafi massalaci.
Bayan an idar da salla bai yarda sun had’u da Sarki ba, ya gudo. Sai dai abinda bai saniba shi Sarki ya gansa, dan yau ya makara salla shima.

Wajen Around 9am nagama gyaran d’aki nayi wanka, saina d’an fito falon domin duba dubawa, natarar sabbin kuyangina suma komai sun gyarashi k’al, harma da mana break fast, banyi yunk’urin bud’ewa ba ma balle tunanin son ci, dukda kuwa natashi da yunwa, to amma Momma ta gargad’eni sosai akan cin abinci wani a masarautar, dan haka na fito daga kitchen d’in kawai.
Tunkan na shigo nake jiyo maganarsu Aryaan, zaune na iske Galadima su Aiyaan na kusa dashi suna bashi labari, anmusu wanka tsaf, sunsha sabbin kaya iri d’aya.
Har yanzu Galadima bayada walwala, na zauna ina gaisheshi, batareda yabar latsa wayarba ya amsa min, su Aiyaan suka dawo kusa dani suna gaisheni, kumatunsu naja ina murmushi, “oh my guys kunsha k’yau, waya muku wanka haka?”..
Atare suka amsa min da fad’in “Uncle ne, kuma ya saka mana tirare yanda kuke mana”.
Murmushi nayi, na saci kallon Galadima da yay biris damu kamar baya d’akin, alhalin sanda na shigo na iske suna hira shidasu ‘yan 2.
Sallamar da wata baiwa keta kwad’awa na amsa, sannan na mik’e na fita dannaji minene? A k’ofar falona na isketa, nace, “miya farune?”.
Duk’ewa tayi ta gaisheni, sannan ta mik’omin ledojin hannunta tana sanarmin Sarkin motane yace “na kawo wannan ranki ya dad’e”.
Kar6a nayi, na koma ciki.
Ajiye ledojin nayi a gabansa, “gashi wai inji sarkin mota”.
Idanunsa ya d’ago ya kalleni, yace, “breakfast d’inku ne”.
Tashi yay ya fita yana fad’in na shirya zaije ya dawo mu shiga cikin gida gaida mutane.
Na amsa masa da to.

 

___________________

Tun a daren jiya wasu bayi sukaga Muftahu, dan haka suka shiga ihu, dandanan sauran bayin dake kusa da wajan suka firfito, manyan bayin cikinsu ne suka kai maganar cikin gida, shine akasakasu d’aukar Muftahu su shiga dashi.
Lamarin yabama kowa mamaki, babu wani mummunan rauni a jikinsa, inbanda d’an jini dake gefen bakinsa, saidai sun sami kwanciyar hankali ganin yana numfashi.
Maganar dawowar Muftahu bata baje masarautar ba sai washe gari.
Bayan Galadima ya fito daga sashensa zaije fada yaji anata k’ananun magana akan dawowar Muftahu, saidai kuma miskilancinsa bai barsa ya tambayi kowaba ya nufi Fada.
Ya isa mai martaba baikai ga isowa ba, dan haka suka gaisa da ‘yan majilissar Sarki dake fadar, sannan ya nemi mazauninsa dake gefen Sarki Na dama ya zauna.
Zamansa baifi da mintuna 10 ba Mai martaba ya iso, gaba d’aya suka mik’e tsaye, dogaran Sarki sunata kirari da fad’in gyara kintsi da k’yau, duksun baza riguna ba’a gani mai martaba, basu bar kowa ya gansa ba har saida ya zauna a kujerarsa.
Baya suka mammatsa mai martaba ya bayyana, atare su Galadima suka rissinar dakai alamun girmamawa, sannan kowa yafito tsakkiyar fada ya mik’a gaisuwarsa ga Sarki, yayinda fadawa ke faman amsawa, tsakanin Sarki dasu kuwa shine d’aga hannu.
Mai martaba yayi mamakin ganin Galadima yau azaman fada, bawai baya zaman bane, sai dai yakan dad’e bai zaunaba, an masa uzurine kasancewar ansan ba zaune yake dindin dinba, kuma idan yazo akwai harkokinsa Na kasuwanci da yakeyi, sai dai dolene yakan shigo yayi gaisuwa.
Bayan fada ta nutsu aka fara fadanci.
K’a idane fadar gagara badau takanyi fadancine a sati sau hud’u kawai, litinin ba’a zaman fada, domin ranace da ake tunawa da abinda ya faru ga tsohon Sarki mahaifin Galadima, talata, laraba, alhamis, asabar, sune ranakun da ake fadanci, ranar juma’a ma ba’ayi saboda muhimmancin ranar ga al’ummar musulmi. A wad’annan ranakun akanyi zamanne daga 10am zuwa 12:30pm, da an tafi sallar zuhur ba’a dawowa, idan kaga anwuce wannan time d’in a fada to tabbas akwai abinda ya farune.
A wannan zaman fadancine maganar dawowar Muftahu ta fito, sun tattauna akai harda shirin kuma d’aukar matakai Na tsaro a masarautar.

Bayan anyi sallar zuhur ne Sarki ya shige gida, sauran fadawa ma kowa ya kama gabansa, Galadima bai shiga gidaba saiya nufi sashen su Muftahu domin dubashi.
Bayan an masa iso ya shiga, ya iske mahaifiyar Muftahu da ‘yan uwansa zagaye dashi, har yanzu kuma yana cikin yanayin barci.
Ya jajanta musu, Yakuma kwantarma da mamansu Muftahu hankali, kusan mintunsa talatin ya fito ya koma sashensa.
Ya iske su Aiyaan kawai a falon Munaya suna kallo, suka taso da gudunsu suka rungumesa, fuskarsa cikeda fara’a ya tarbesu, ya tambayesu ina Auntynsu?.
A tare suka bashi amsa, “Uncle tana d’aki ta kwanta kuma tace karmu tadata, inba hakaba jiki magayi”.
Murmushi yayi yaja kumatunsu, “kuce zatayi zana kenan idan aka tada ita?”.
Nanma atare suka amsa da “eh Uncle, kasanfa Aunty Munaya tacika fad’a, gidanmu tsoron masifarta akeyi, amma ita Aunty Munubiya babu ruwanta”.
Galadima yace, “da gaske?”.
“ALLAH kuwa Uncle, idanfa mukayi rashinji ita ke zanemu ba innarmu ba, kuma dukanta da zafi, gashi taita hararmu da katun-k’atun idanunta nan”.
Sosai abin yabama galadima dariya, dan haka ya dara sosai abinsa yana fad’in, “kubari tajiku to, idan ta zaneku babu ruwana nidai, kunga bara naje naga kota tashi, karfa Ku shigo, dan zata iya zaneku”.
Sukace “ai bazamu shigoba Uncle”.
Yace, “good boys”.

Da sallama ya shigo, amma saiya isketa baje a gado tana shak’ar barcinta, yad’an murmusa kafin ya k’arasa ya zauna a bakin gadon saitin fuskarta, yatsunsa biyu yasaka a gefen wuyanta dan yasan da wahala wannan barcin ya kasance na lafiya, aikam jikinta ringim yake da zazza6i, tausayinta ya kamashi, lallai uwa dabance acikin al’umma, Ashe haka sukeshan wala, tundaga d’aukar cikinma zuwa rainonsa, akoma rainon yaro, daganan tarbiyarsa, lallai masu raina mata ko kallonsu masu k’arancin tunani sune masu k’arancin tunanin ai, ya d’an lumshe idanunsa yana cije lips, ganin ta dunk’ule a waje d’aya saiya ja bargo ya lullu6a mata, harya mik’e ya koma ya zauna, risinowa yay kanta a hankali ya mannama goshinta kiss, sannan yamik’e ya fice.
Koda ya dawo saiya wuce d’akinsa, yabar su Aiyaan suna kallonsu.
Kayan jikinsa ya cire ya kwanta shima, dan yana buk’atar hutawa kona 2hours ne, kwanciyarsa kuwa babu dad’ewa barci ya saceshi.

Kiran sallar la’asarne ya tashesu kusan lokaci d’aya, Galadima yatashi da k’yar, a mamakinsa sai yaga Aiyaan da Aryaan kwance a gefensa suma suna barci, murmushi kawai yayi yasako, saida ya watsa ruwa sannan yay shirin tafiya massalaci cikin k’ananun kaya.
Harzai fita saiya dawo yashiga wajen Munaya. tana tsaye gaban wardrobe tana neman kaya, da alama wanka tayi, dan daga ita sai towel.
Banji sallamarsa ba, saboda shi idan zaiyi magana bayason bud’e baki, ganin batajishiba saiyayi gyaran murya, a tsorace na waigoshi, ganin shine nai saurin saka kayan dana d’akko ina kare k’irjinna da tura baki, bakinsa ya d’an ta6e, sai kuma ya shiga takowa inda nake, duk takun da yayi sai gabanna ya fad’i, na waiga kozan samu nabar wajen ko abinda zan suturta jikinta sosai, amma sainaga babu a kusa, kuma ina jikin wardrobe d’inne sosai ai. ban gama yanke shawara ba ya k’araso daf da ni, kuma matsawa nayi na matse jikinna sosai a drowa d’in, shikuma yawani had’e gabas da yamma, wannan ne yakuma sakamin tsoronsa a raina, na zata kowata tsiyarce ta kawoshi.
Hannu yasaka ya d’ago da ha6arta muka kalli juna, ya tsareni da idanu yanda nakasa janye nawa cikin nashin, munkai kusan 2minutes a haka, kafin yakumamatsoni sosai, ya kai fuskarsa gab da tawa tamkar zai had’e bakinmu, dan haka saina lumshe idanu, murmushi yayi ya hura mata iska akan idanun, ta rumtse idon sosai, ya d’an ja baya yana ta6e baki, kafin yasaka hannu ya cire nata dataketa faman kare k’irji da kayanta, still ya kuma matsawar saitin kunnenta yana fad’in “wane darene jemage bai ganiba yalla6iya”. ‘ya k’are maganar da shafa kirjina ya fice abinsa.
Kad’an yarage namasa ihu wlhy, aiko yana fita na durk’ushe a wajen ina sauke numfashi, sometimes nakan rasa yazan fassara Galadima da ayyukansa.
Da k’yar Na iya tashi nayi sallar nakoma kan gado Na kwanta.

Galadima kam daya fita dariya ce taita cinsa, ya kula Munaya akwai tsoro, kuma haryanzu a tsorace take dashi, cikinnan ne kawai kanci galaba akanta yake samunta cikin sauk’i, ya girgiza kansa kawai yana murmushi.
Bayan ya dawo massalaci d’akin nata ya dawo, dan yanason suje su gaida jama’ar gidan, maybe gobe suje masarautar papi ma.
A kwance ya iskeni, nak’i kallonsa, jingina yay da mirror yana fad’in “yaya jikin naki?”.
Ban kalleshinba nace, “da sauk’i”.
“ALLAH ya k’ara sauki, idan zaki iya tashi ki shirya muje cikin gida, kafin waccan tsohuwar tafarama mutane surutu”.
“to” nafad’a ina mik’ewa, Na sakko a gadon, harna nufi wardrobe zan d’auki alk’yabba saina tsaya, batareda Na kalleshi ba nace, “toka fita Na shirya”.
Hard’e hannayensa yayi a k’irji yana fad’in “ashe bazaki shirya d’inba, dan bazanje ko inaba”.
“karkaje d’in, ai akwai bayi” nayi maganar a zuciyata.
Kayan Na d’auka na shiga toilet, shikuma ya ta6e baki.

Babu dad’ewa na fito tsaf, nayi k’yau, nazo ta gefensa na d’auki turare nasaka kad’an sannan na kallesa nace, “na shirya”.
Baice komaiba ya nunamin hanya, gaba nayi yana bina a baya muka fice.
Kasancewar tazarar dake d’an tsakaninmu da sassan nasu muka shiga mota, dan banajin dad’in jikinna, bama zan iya tafiyarba.
6angaren Abba hayatudden muka fara zuwa, daga nan sai sashen matan mai martaba, soyayyar da uwargidansa ke nunamin yasani k’ara k’aunarta, sai addu’a take zabgamin akan ALLAH ya saukeni lafiya. Galadima kad’ai ke amsawa, amma ni saidai a zuciya kawai. daga nan muka d’an shishshiga wasu sassa, 6angaren mama fulani shine k’arshen zuwanmu.
Kunsan dai mutuniyar taku akan mulki, tana kishingid’e kuyanginta nata bauta, mai matsa kafa daban mai firfita daban, ga masu bata labarai, tufa takeci cikeda k’asaita da izza.
Amintacciyar baiwarta data mana iso tana gaba muna biye, mama Fulani ta d’agama kuyanginta hannu alamar subata waje.
Rige-rigen ficewa suka, yayinda mukuma muka k’arasa gareta, idonta a kammu ko k’yaftawa batayi, nidai tsarin ALLAH na nema daga sharrinta, ina dalili wannan kallon k’urilla haka?.
Galadima yace, “barka da yammaci”. nima saurin fad’a nayi.
A yatsine ta amsa mana, ta d’ora da fad’in “Saraki kayi wuyar gani?”.
Galadima ya murmusa yana kallona, “Ranki ya dad’e kinsan mai amarya ai yafi dubu wahalar gani dama”.
“Humm” kawai tace batareda ta amsaba.
Sai zuwa can tace “nafa manta, ina tayaku murnar samun k’aruwa”.
“mun gode ranki ya dad’e, amma taki murnar itace tazo a latti, gashi kuma idonkine yafara hango abin cikin kwan tun a india”.
Mama Fulani ta tsatstsare Galadima da idanu, shikuma yay salute nata yana murmushi.
Jitai kamar zata makesa dan haushi.
Ya lura da haushin da taji, dan haka ya kama hannuna muka mik’e tsaye yana fad’in, “bara mukoma inda muka fito ranki ya dad’e, a huta lafiya”.
Bai jira amsartaba mukayi fitowarmu.
Da kallo kawai ta bimu, takasa koda motsawa, tarasa miyyasa yau Galadima da matarsa suka mata wani mugun kwarjini? batada mai bata amsar tambayar tata…

Yini guda yau Galadima a gida yayishi, baije ko inaba, sai da daddare Nuren yazo sukayi magana, daga nan yace ya nema mana tickets d’in zuwa masarautarsu.

Washe gari muka tashi da shirin tafiya masarautar su papi, mukad’ai muka tafi, babu kuyangi babu dogarai, dagani sai shi dasu Aiyaan, sai Nuren………………???

 

 

 

*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu_*??????

*_typing??_*

?? *_HASKE WRITERS. ASSO….._*

*_?RAINA KAMA…..!!?_*
_(Kaga gayya)_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply