Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 13


Raina Kama Book 2 Page 13
Viral

Book 2~ ????1?3?

……………Muna tsaka da hira saiga Aunty salamah tazo, daga ni har Munubiya da Ayusher rungumeta mukayi.
Cikin tsokana ta ture Munubiya da Ayusher tana fad’in “ku matsamin, kullum Ku ina ganinku, kewar gambo nakeyi”.
Gwalo na shiga yi musu, mama Rabi’a da Feena namana dariya.
Bayan mun zauna Aunty Salamah ta shiga yaba canjawar danayi tanamin shak’iyanci, nanfa su Munubiya ma suka samu abinyi, sosai suka tasoni gaba sai mama Rabi’a ke kareni.
Can muna tsaka da hira takamo hannuna tana fad’in “zo nabaki wani sirri nan autana”.
Mik’ewa mukayi inamasu Ayusher gwalo, yayinda suma suka tubure basu yardaba sai an bada sirrin dasu. da k’yar muka samu muka shige d’aki muka kulle.
A bakin gado muka zauna Aunty slamah ta sauke ajiyar zuciya tana kamo hannuna cikin nata, serious nima na zama na maida hankalina gareta.
Tace, “Munaya! Aiki yatafi yanda ya kamata, saidaifa labarin ya canja daga yanda kike zato, Muftahu ba munafuki baneba”.
A matuk’ar razane naja baya ina ture hannunta daga cikin nawa, “Aunty kinsan mi kike fad’a kuwa? Anya yaranki Muftahu suka kama?”.
Hannuna ta kamo tana murmushi, kinga zauna, shiyyasa na saka aka d’auki komai dan kema ki gani da idonki”.
Zaman nayi kuwa, ita kuma tayi ‘yan latse-latsenta a iPad d’inta ta mik’omin. kar6a nayi cikeda fargaba, da kaina nayi playing d’in video n, tun daga fitowar Aunty salmah daga mota har shiganta cikin gidan zuwa shigarta d’akin, tsayarwa nayi na kalli Aunty ina dariya, “kai Auntynmu kinfa iya Acting wlhy, wanifa saiya d’auka da gaske irin mugayen hamshak’an matan nanne”.
Dariya Aunty Salamah tayi, “wlhy koni dai nayi mamakin dakewata, bakiga sai wani hura hanci nakeba, sukuma su Ameer saikace guards d’in irin manyan mutanan nan”.
Dariya mukayi, sannan nakuma playing na cigaba da kallo.
Shigar Aunty Salamah d’akin da tattaunawarsu da Muftahu. gaba d’aya jikina yayi sanyi, zuciyata sai wani tsitstsinkewa takeyi, idona cike da kwalla nace, “anya gaskiya Muftahu yake fad’a Aunty Salamah?, wlhy da gaske fa shine ya saka mana desire tablets, inhar bada wata manufaba miyasa yay haka?, kumafa ni banta6a ganin wani alamar rashin gaskiya ba ajikin Harun”.
Murmushi Aunty Salamah ta yi, ta dafa kafad’ata tana fad’in, “Munaya mugu bashida kama, Ai Muftahu baisan nid’in ba matar sarkin bace ta gaske, mizaisa ya za6i 6oyemin? yanda yanuna akan k’yamar matar sarkin tabbas akwai mai mugun hali a cikin su da gaske, kinga ai kince bakiga fuskar wanda kika kama yana wayarnanba a bayan window d’inki randa kuka iso”.
“Eh hakane, ban ganiba, maganganun kawai naji”.
“to kin gani, kifa tuna kuma firar da kika ta6aji Galadima nayi a asibiti shida aunty Mimi. wad’annan alamomin sun nuna akwai wata a cikin matan Sarki dakeda hannu a ciki, maganar Harun kuma idanu zamu saka masa tamkar yanda mukaima Muftahu, dan ayanzu idan mun saki Muftahu zakiga sun cigaba da takun sak’ar datafi ta da zafi, dan nariga da nasaka rud’ani a zuciyar Muftahu cewar zamu kashe galadima, tabbas ta wannan hanyar Harun zaizo hannunmu. Maganar Galadima kuma har yanzu karki fara kwantar masa da kai, dan kwantar da kanki zai d’arsa masa rashin aiminci a kanki, ke dai kinsan halin mijinki ai yanzu, kinkuma fi kowa sanin yanda yakamata ki cigaba da tafiya da shi”.
Insha ALLAH Aunty zan cigaba da k’ok’ari nakuma gode da gudunmawarki akanmu, sai dai akwai matsala, dan na lura agogon hannun Muftahu kamar akwai wani sirri a cikinsa, dolene a daren yau a fitar da Muftahu daga gidanan, zanma sarkin mota bayanin yanda zai taimakeku a maidashi masarauta kamar yanda yaymana aikin d’akkoshi, shima Galadima zansa ido akansa saboda tsuntsune shi nai azabar wayo”.
“Hakan yayi Munaya, ALLAH ya cigaba da bamu nasara, insha ALLAH zamu gano komai, ALLAH dai yabama Abba lafiya, yasa mu fahimci komai cikin sauk’i, akan Galadima kuma kici gaba da k’ok’arin da kikeyi Fiyeda da, dan dolene saimun samu had’in kansa kafin musan komai, ALLAH ya ku6tar damu baki d’aya, dan kina dai ganin yanda suka maida Abba”.
Hawayen da suka ziraromin a kumatu na share, cikin Murmushin k’arfin hali nace, “insha ALLAH Aunty Salamah, domin raina da farin cikina fansane akan mahaifina, kuma zuwa yanzu Auren Contract bai damuna, sai dai bazan 6oye mikiba aunty Salamah wannan cikin shine damuwata a yanzu, inaji ina gain zan haifishi na barsa inda yafi k’arfina, bansan wace rayuwa zaiyiba a wannan gidan da kowa zuciyarsa takeda k’arancin imani, Aunty Salamah gidan sarauta tsantsar matsalace kawai, bazaki fahimci hakaba saikin tsinci kanki a ciki, Aunty dan ALLAH ki amince na zuba da cikinnan”.
“munaya waishin miyasa bakida hankaline? to idan baki saniba wannan cikin shine zai zamemiki tsanin mallakar cimma nasara, kuma ta hanyarsane kawai zamu samu had’inkan Galadima domin fidda Abba daga wannan matsalan da Ku kanku ahalinsa, kina tsammanin koda Abba mutuwa yay masu farautar rayuwarsa zasu barku Ku6utane? Dolene saisun samu abinda suke nema koda ace dukkan gidanku zai k’are, bak’ya tunanin aurenku yana cikin abinda yakuma hasala zukatansu, a zatonsu Abbanki yasamu damar had’a kan mijinkine, ya ina jinjinama fik’irarki ke da munubiya kuma zaki 6ata shirin, karma ki bari ‘Yar uwarki taji maganar zubda cikinnan, wlhy zaku samu Matsala ne babu ruwana”.
Munaya ta share hawayenta, “shikenan Aunty Salamah nabar maganar insha ALLAH. Amma a yaran nan masu mana aiki bak’ya tsoron wani yaci amanarmu?”.
“komai zai iya faruwa, domin amana tayi k’aranci a rayuwa, tunda yau gashi Harun yafito cikin masu cin dunduniyar Galadima, amma ki kwantar da hankalinki, su duka ukunnan da kike gani amintattunane, kuma Saleem ya saka mana idanu sosai a kansu”.
“to Alhmdllh aunty, ALLAH kamana jagora”.
“amin dai, saikima Munubiya dukkan bayanin da mukayi, ki bata itama ta gani, zuwa gobe zan aiko Bilkisu ta kar6a min, kuma ki fad’a mata yakamata ta koma gidan ta, dan gaskiya aiki bazai cigaba da yuwuwaba tana gidannan, saboda kinga ba ita kad’ai baceba, yanzu haka randa zaku zo da zamu kama Muftahu wlhy nasha wahala wajen nemanta naji kokin iso? dan ta tabbatar min inhar kin iso k’asarnan saitaji a jikinta, amma naita kiranta batayi picking ba, ashe wai wayar na hannun Feena”.
murmushi nayi nace, “sorry sweet auntynmu, insha ALLAH zata koma gobe”.
“shikenan, bara na wuce to”.
“to Aunty ngd sosai, ALLAH ya bada ladan zuminci, ammafa gaskiya kinci zalin muftahu da yawa”.
Dariya tayi sosai, “kibari kawai, nima wlhy ina marinsa tausayinsa Na ratsani, insha ALLAH zan nemi yafiyarsa zuwa nan gaba, ALLAH yasa ya yafemin dai”.
“hhhh zai yafe miki aunty ai duk cikin aikine”.

Mun rakota har tsakar gida, su Munubiya na tsokanarmu wai nad’an sammusu sirrin suma.
Daga ni har aunty Salamah dariya mukayi kawai.
Bayan dawowarmu na turama Munubiya massage akan taje tagani itama.
Sai da taja wasu times sannan tamik’e tana fad’in bara tad’an watsa ruwa. duk muka amsa da to saita fito.

 

**************************

 

Su Abba sun isa lafiya, anzo da motar Ambulance d’in asibiti aka d’auki Abba, yayinda Sauban da baba k’arami da inna khumar yazo d’aukarsu su kuma.
Inna da baba k’arami sai baza ido suke suna kallon gari.
Gida suka wuce kai tsaye, yayinda aka wuce da Abba hospital shikuma.
Sun iske jakadiya a gidan, dandanan aka shirya musu abinci, itadai inna sai jinjina k’yawun wannan gida take, yanzu anan gidan jininta ta rayu?. shi kansa baba k’arami ya yaba, Yakuma k’ara tabbatar da manyan k’asarmu Na hutawarsu.

 

**************************

Babu yanda Muftahu baiyiba dan ya sarrafa agogon hannunsa amma hakan ya gagara, Dan bak’aramin d’auri ya shaba.
Kusan gab da magriba Wanda ke kawo masa abinci ya shigo, ajiye kular abincin yayi sannan ya matsa kusada muftahu zai kwanceshi, cikin murya k’asa-k’asa kamar mai rad’a yace “yalla6ai inhar zaka biyani wlhy zan ku6tar dakai”.
Kallonsa Muftahu yayi sosai nawasu mintuna, “ka tabbatar?”.
“wlhy Oga da gaske nakeyi, Dan wannan matar da kake gani bata wasa bace, duk abinda ta fad’a zata iya aikatashi wlhy”.
Murmushi Muftahu yayi, yace, “nawa kake buk’atar Na baka?”.
“tab aini Oga dubu 100 ma ta wadatar”.
Muftahu yakuma Murmusawa, “zan baka 200”.
Da sauri yaron yaja baya cikin razana, “oga dubu 200 fa? Yo ai sai a d’auka nafara yankan kaine”.
Sosai abin yabama Muftahu dariya, Dan haka ya dara, yo dubu 200 a wajensa ai bata wuce ta siyen agogo ko takalma ba, amma shine shi yake ganin 200k a matsayin wasu kud’in da har za’a iya d’auka yayi yankan kai.
Kallonsa yayi yana murmushi, “karka damu to, amaimakon nabaka kud’in a hannu a zargeka mizai hana Na bud’e maka wata Sana’a da zakabar wannan aikin da kakeyi yanzu”.
“to ai Oga karkaje kasa a kamani wataran, nikuma inhar zan samu Sana’a to zan nutsu”.
“haba abokina, ya zakamin rana nikuma Na maka dare, karka damu kaidai ka aminta dani kawai”.
“to Na amince, yau sai k’arfe 11 zan kawo maka abincin dare, a time d’in sauran sun fita club, insha ALLAH nikuma zan dawo baya nace Na manta da abincinka, daga nan saina ku6tar dakai, sukuma na sanar dasu Na dawo ban gankaba”.
“shikenan babu damuwa, idan zaka dawo kazo da account number, dana koma zan maka transfer insha ALLAH”.
“to Oga Na gode sosai”. Ya fad’a cike da d’oki.
Murmushi kawai Muftahu yayi.
“yauwa Oga bara Na kwanceka kaci abincin to”.
Girgiza kai Muftahu yayi, yace, “a’a ka barsa kawai, banajin ci, in kanaso d’auka kaci kawai”..
“amma Oga ai…….”.
Kai Muftahu ya girgiza masa alamar karyace komai.
Shiru yaron yayi ya d’auki kular ya fice kawai, Muftahu kuma ya bishi da kallo.

 

**************************

Har akayi isha’i Galadima yana birnin gayu, saida aka kira sallar magriba ne yafita zuwa massalacin dake plaza d’in yay salla tare da ma’aikatan wajen masu salla, daga nan ya gaggaisa da makwaftan wajen dakan zo masallacin yin salla suma, bai fitoba saida akayi sallar isha’i. daga nan yacema saleem yaje dasu Aryaan su za6i dukkan abinda sukeso ya mik’a mass ATM d’insa, shikuma ya kuma shiga office ya kulle kansa ya d’ora tunaninsa daga inda ya tsaya.
Ya dad’e yana zagaye office d’in, yayinda zuciyarsa ke k’ulawa da kwancewa, agogon hannunsa ya kalla, ganin time yayi nisa yasashi furzar da huci, kayansa ya tattaro ya fito, dogaransa duk suka mik’e, suna gaisheshi, amsawa ya shigayi tamkar baya so.
d’aya aciki yace, “zamu tafine ranka ya dad’e?”.
Kansa ya jinjina masa alamar eh, sannan yace “ama saleem magana”.
Da sauri suka amsa da to.
Ficewa yayi, sauran dogaran sukabi bayansa. Mota aka bud’e masa ya shiga, za’a rufe murfin ya hana, idonsa akan k’ofar plaza d’in harsu Aiyaan suka fito tare da saleem, dogarai biyu d’auke da manyan ledoji.
Suna hangoshi suka k’arasa da gudu, murmushi yayi ya d’aukesu d’ai-d’ai da kansa ya saka a motar, sannan aka rufe musu k’ofar.
Sudai dogaransa sai mamakin yanda yake sakema su Aryaan sukeyi.
Har sun fara tafiya ya fad’ama sarkin mota suje zasu taho da Munaya.
A ladabce sarkin mota ya amsa da to.

*****************

Muna tsaka da hirarmu aka kira wayata, sharewa nayi tamkar bazan amsaba, Munubiya ta harareni, ramawa nayi nima sannan Na d’aga.
Ciki-ciki nayi sallama, ya amsa daga can, mamaki ya kamani danjin muryar Galadima, katseni yayi da fad’in “ki fito”. Bai jira cewata ba ya yanke wayar.
Kamar zanyi kuka haka naji, Yaa Marwan ya fito daga d’aki yana saka rigarsa, kallona yayi yana fad’in “k ba jiranki akeba ne?”.
Sai da Na kumbura baki sannan Na mik’e. shikuma ya fice.
Da taimakon feena Na had’a komaina, har abubuwan da mama Rabi’a ta bani, sannan suka rakoni. Mun iske Yaa marwan tsaye jikin motan ya dafa k’ofar suna magana da Galadima dake ciki bai fitoba.
Dogari d’aya ya zagaya ya bud’emin, ido muka had’a da Galadima Na janye da sauri, shima janyewa yay ya maida hankalinsa ga Yaa marwan dake masa magana.
Mamaki ya kamani ganin su Aiyaan, suma cikeda d’oki suka fad’amin a jiki suna dariya da fad’in “Auntynmu!”.
Juyowa Galadima yay yana kallonmu, shima Yaa marwan yay dariya kawai, sannan ya rufe mana murfin yanama Galadima sai da safe.
Su Aryaan sun kacame da bani labari, yayinda nikuma naketa musu dariya da biye musu, mamaki ya kama Galadima, bai ta6a tunanin ina magana hakaba, ya lafe jikin seat yana kallonmu cikeda birgewa.
Nikam nama manta ko gaisheshi banyiba, saida yay gyaran murya sannan Na d’ago Na kallesa, murmushi namasa ina fad’in “yalla6ai barka da dare”.
Shima wani miskilin murmushi ya min yana d’agamin hannu batareda yayi magana ba.
Aiyaan yay saurin fad’a “auntynmu bafa yalla6ai sunansa ba, sunansa Uncle”.
Kamar zan harari yaron sai kuma nad’an murmusa ina kallon Galadima dake kallonmu shima. janye idona nayi daga gareshi Na cema Aryaan to naji zanke fad’a.

Har muka kai gida basu barmu mun hutaba, sai surutu suke da bani labarin abinda yafaru a gida bana nan, danaji zasu kauce hanya kuma sainai saurin waskewa.

??*?*??*?*??

Sarkin mota yana ajiye su munaya ya duba gefen seat d’in data zauna, takarda ya gani ya d’auka, dan sanda zasu shige tamasa wata inkiya da hannu.
Dubawa yay yaga mita rubuta. Sallama yayma sauran ‘yan uwansa sallama akan zai shiga gida.
Daga nan ba gidan ya shigaba, saiyay dabarar da yabar masarautar gaba d’aya.
Sun had’u da Saleem a inda suka shirya, saleem Ya bama sarkin mota handkerchief d’in da zasu shak’ama Muftahu.
Sarkin mota ma yaje ya bama Ameer ne, daga nan ya dawo k’ofar fada amma k’aramar k’ofa tacan baya inda keda k’arancin tsaro.
Agaban idonsa su Ameer suka sauke Muftahu a mashin yana cikin yanayin barci saboda abinda suka shak’a masa, saida ya tabbatar sunbar wajen sannan shima ya koma ciki.

Yau dai kam ni kad’ai Na kwanta a d’akina, Galadima ko lek’e bai lek’oba, yana can tare da su Aiyaan a d’akinsa.
Nima kawai saina kira Momma mukasha hirarmu, tana bani labarin yanda jikin Abie yaketa k’yau a tsakaninnan, dukda kar yanzu maganar bata fita amma yakanyi bamai tsawoba, naji dad’i sosai, na masa addau’a mai tsawo tareda fatan alkairi, daga nan muka cigaba da tattaunawa akan maganar Abbana, da zancen su innarmu dasuka k’i yarda su zauna a gidan, innarmu ta dage bazata zaunaba tunda muma anan muke, saida Momma ta saka baki da mata bayanin da zata gamsu sannan ta amince zata zauna. Nasha dariya, dan dama nasan za’ayi hakan, innarmu kawai kunya da kawaici.
Daga nan har muka dawo kan ta Muftahu, dayake tasan komai a kai, da taimakonta nima nake samun k’arfin gwuywa.
Itama tasha mamakin jin Harun a lamarin, ta dad’e tana jinjina maganar nan. ta bama Samha muka d’ora da hira, saida naga time yaja ga zazza6in fama ya rufeni, sallama mukayi nai addu’a Na kwanta.
Masu iya magana since sabo tirken wawa, saina kasa barcin, naji kawai ina kewar Galadima.

Shima kansa yanacan sai juye-juye yakeyi, yakasa barci, bayan sun gama hirarsu dasu Aryaan yay musu shirin barci da kansa suka kwanta, aiki yad’an ta6a yana Neman dabaru akan binciko Muftahu, baiwani dad’eba ya kwanta shima, amma saiya kasa barci, juye-juye yaytayi agadon, ganindai da gaske ya kasa barcinne saiya mik’e yana jan guntun tsaki, kwanciya ya gyarama su Aryaan ya lullu6esu da bargo sannan ya fito da nufin wai zai duba munaya ????.

Jin shigowarsa yasani k’ara lafewa tamkar nayi barci, ya kunna fitilar d’akin yana kallona, yaja wani dogon lokaci sannan ya kashe ya tako zuwa gadon, “nasan idonki biyu ai, dama kin tashi kinbar wani kumshe-kumshe”.
Shiru nayi nakumak’i motsawa.
Kwanciya yayi a gefena, yaja bargon shima ya lullu6a, tareda juyamin baya, yace “miya hanaki barcine?”.
“farkawa nayi”. Na fad’a batareda ba kalleshi ba.
Murmushi yayi yana fad’inn “ Hummm”.
Daga nan duk mukayi shiru nawani lokaci, kamar an matse bakina nace “yalla6ai na tambayeka please? ”.
Yace, “Uhmm”.
Juyowa nayi ina fuskantar bayansa, a nutse nace, “wai dan ALLAH ina sauran matan Abie yanzu?”.
Da sauri naga ya juyo gareni, ni harma tsoro ya kamani nai baya da sauri, nazata makeni zaiyi, amma sainaji ba hakaba, yace “Munaya mi kika sani a kaina ne?”.
“yalla6ai kamarya mina sani a kanka? daga tambaya?”.
Yace, “Humm yana matsowa gareni, zan matsa ya rik’o hannuna…………….???

 

Kuyi manage da wannan please??????

 

 

 

*_ALLAH ya gafartama mahaifanmu??????_*
*_typing??_*

?? *_HASKE WRITERS ASSO….._*

*_?RAINA KAMA…..!!?_*
_(Kaga gayya)_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply