Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 12


Raina Kama Book 2 Page 12
Viral

~Book 2~ ????1?2?

……………Maman Fauziyya tamatso ta kama hannunmu ni da Munubiya tana lallashinmu, da fad’a mana mu bisa da addu’a, insha ALLAHU da k’afarsa zai dawo.

Ganin mun fara shirin tafiya na taka inda Galadima yake tsaye da Nuren suna magana, tun d’anzun ina lura dashi ya kafeni da idanu, yanzunma suna maganar amma idonsa na kaina na k’araso garesu.
Nuren daketa fara’a yace, “gimbiyarmu barka da hantsi”.
Murmushi nayi sannan na gaisheshi, ya amsa yana tambayata yaya jikina?.
Nace “Alhmdllh na warke ai”.
“to ALLAH ya k’ara afuwa gimbiya”. ‘yafad’a yana matsawa gefe domin bamu waje.
Galadima dake kallona hannunsa duk biyu cikin wandon sky blue d’in shaddarsa da tsawon rigar iyakarsa rabin cinyarsa, yace, “Lafiya?”.
Dakewa nima nayi, cike da jan ajina nace “k’alau. Dan ALLAH zanbi Munubiya please yalla6ai”.
Janye idanunsa yayi daga kaina yana fad’in “awane farashi?”.
“kamarya farashi? ciniki mukeyi?”.
Hannunsa d’aya ya fiddo daga aljihu ya shafa sajensa zuwa gemu, cikin kafeni da idanu yace “kusan haka, kinsan rayuwar bani gishiri in baka manda akeyi yanzun”.
Cikin son tura masa haushi nace “Ai ni bana gane Hausa cikin hausa”.
“really? lallai kin fad’o kuwa, kuma saiki ce ke bahaushiyace?”.
Baki na tunzura masa saboda haushin rainin wayon da yake min, gasu Munubiya kuma shirin tafiya sukeyi.
“Kinsan wannan bakin kika bari na kamashi a airport d’innan….., hummm”.
Idanuna na waro, “mi kake tunanin zakayi kenan?”.
“kuma turowa saina nuna miki”. ‘yafad’a yana matsowa’..
Baya na matsa da sauri zuciyata na harbawa, anya kan Galadima d’aya kuwa?.
Kwafa yayi yana kallon agogon hannunsa yana k’ok’arin zaro waya daga aljihun gaban rigar datake ring.
Nikuma na hararesa a zuciyata ina fad’in mara kunya ai nasan zaka iya. A fili kuma nace “please yalla6ai nidai badan halina ba”.
Bai bani amsaba, sai sallamar danaji yayi wayarsa akan kunne.
Jinai kawai yace, “Harun kana inane?”.
Bansan wace amsa ya bashiba, naji yana fad’in “ok idan ka tashi saimu had’u”. daga haka ya yanke wayar sannan ya kalleni.
“uhm mikike cewa?”
Haushi tamkar zai karni nace “please mana autan Momma”.
Murmushi yayi yana cije lips, “wlhy yarinyarnan kin gama rainani, ninema Autan?”.
“lah nama manta ashe kaifa na tsakkiyar momma ne, karma Yaa Sauban ya jini”.
“kinsan ALLAH na damk’eki a airport d’innan saikin fad’amin dawa kike”.
Dariya nayi ina d’aga masa yatsu biyu, “karka damu yalla6ai zanyo maka tsarabar sweet and biscuit yeah”.
Da sauri yay yunk’urin damk’o hannuna ganin zan gudu. yana rik’owa mukaji ance “hallo”. A bayanmu.
Batareda ya saki hannuna ba duk muka waiga ni da shi.
Matashiyar budurwa fara k’al, kuma k’yak’yk’yawa masha ALLAH.
Dan danan ya tsuke fuska, tamkar ba shine yagama murmushiba yanzun.
Nima bansan murmushi ya gushema tawa fuskarba, baiyi magana ba, sai nice nace “lafiya kuwa?”. yanda nayi maganar cikin rainin hankali yasaka yarinyar rik’e ha6a tana ta6e baki tana fad’in “ke kuma fa?”.
Kamar zanyi magana saikuma Na shareta kawai, galadima Na kalla fuskata a cunkushe alamar fushi, d’ayan hannunsa ya d’agamin yana ta6e fuska alamar shifa babu ruwansa.
Na tura baki tareda juyawa zan bar wajen.
Hannuna dake cikin nasa ya kuma damk’ewa da k’yau, hakan yasani dawowa baya tamkar zan fad’a jikinsa, amma nayi jarumtar tirjewa kodan jama’ar gidanmu.
Dama ajikin wasu motoci muke, sai kawai ya fisgi hannuna muka shige tsakkiyarsu ya mannani jikin mota shikuma yamin rumfa. ban ankaraba naji bawan ALLAHnnan ya ha…….??.
Jikina kawai rawa yakamayi saboda tsoro, wlhy ban ta6a tunanin da gaske yake zai iya hukunta bakin nawa a airport d’inba.
Ita kanta budurwarnan idanu ta zaro waje cikin wangale baki.
Nuren dashi kad’ai yake saitin dazai iya ganinmu saikuma wasu tsirarun mutane dake nesa damu, wad’anda ba lallaine ma su fahimci abinda akeba, kaucewa kawai yay daga wajen yana tuntsura dariya.
‘Yan gidanmu sunga lokacin da Galadima yaja hannuna muka shige tsakkiyar motocin, amma basa hangomu. tsabar gulma irinta mamansu Yaa Hameed da Momy da Maman Safara’u sai suna shiga k’ok’arin son ganin mi mukeyi a wajen??? su duk tunaninsu wata maganar banza nama budurwarnan yake shukamin rashin mutunci Dan duk agaban idonsu tazo wajen har rik’omin hannu da yayi, dukda basa jin mi Muke fad’a Dan muna nesa dasune.
Yaa Sabi’u dabasu lura da abinda ke faruwa ba suka Shiga musu maganar INA zasuje? suzo su ajiyesu gida sufa wajen aiki zasuje.
Ina basu saurareshiba saida sukazo saitin dazasu iya ganinmu.
A tare suka zaro idanu, Baki da hanci, duk sun shiga mamakin ganin Galadima Na kissing d’ina, ai babu shirin suka koma baya zukatansu Na tukuk’i da jifanmu da kalmar ‘yan iska fitsararru.

(??Yo wayace kuje gani? kazantar dabaka ganiba sunanta tsafta????).

Yana Sakina kunya tasakani fad’awa k’irjinsa Na 6oye fuskata, hannayensa yasaka ya zagaye bayana yana dallama yarinyarnan wata muguwar harara data saka hanjin cikinta kad’awa, babu shirin tabar wajen tana mak’yark’yata da tunanin Galadima ko dai kurmane da gaske.

Driver d’inta dake kallon komai tun d’azun ya tuntsure da dariya yana fad’in ALLAH ya k’ara, bana fad’a miki Shiba Na wasan yara bane ba, banda jaraba kinbi kin nanik’ema bawan ALLAH daga had’uwa a jirgi, kinbi kin addabi rayuwata saina nemo miki number sa, aini nama godema ALLAH da kuma sake had’uwa ya kuma nuna miki ainahin halinsa, saida Na fad’a miki baima dad’e dayin aureba, ke gadararriya kikace aurensa bai damekiba……..
Yanda ta daka masa tsawa yasakashi firgita ya russuna yana Neman afuwarta.
Cikeda masifa tace “tada mota mukoma gida”.
“Amma ma’am kin manta jirginku yakusa tashi?”. A tsorace yayi maganar.
Harara ta Dalla masa tace “Ubanka ne ya viyamin kud’in jirgin”.
Wasu yawu masu rad’ad’i driver ya had’iye yana girgiza mata kai, ya bud’e motar ta Shiga sannan ya rufe shima ya zagaya mazauninsa suka koma Inda suka fito??.

Nasan dai kun fahimci yarinyarnan Ce da suka zauna waje d’aya a jirgi itada Galadima randa zaizo????.

Ganin tabar wajen Galadima yay murmushi sannan yafara k’ok’arin d’agoni daga k’irjinsa, ban yarda mun had’a idoba na bar wajen.
“Saikin dawo” ya fad’a a hankali.
Kasa daurewa nayi saida Na waigo Dan tabbatar da shine yay maganar kokuwa dai wanine?. Ido muka had’a ya janye nasa cikeda basarwa yana la6e baki.
Nima harara Na watsa masa ina barin wajen.
Tunda Na taho Maman safara’u da mamansu Yaa hameed da Momy suka zubamin ido.
Nikuma fahimtar kallon k’urillar da sukemin saina canja salon tafiya da kuma had’e fuska na nufi zuwa wajen gungun yaran gidanmu masu aure dasuke hira.
Suma duk kallona sukayi, namusu murmushi ina fad’in “lallai munada cin ragunan suna kwannan nan ashe”.
Dariya duk sukayi, Fiddausi tace “yariman namu shikuma da kwad’ayin naman suna yazo?”.
Harara Na zuba mata ina kai mata bugu ta waske itama tana dariya, yayinda su Munubiya ke tayata.
Mun gaggaisa tareda tambayar lafiyar juna, muka d’an ta6a hira kad’an da alk’awarin duk zanje mu gaisa, suma sukace zasuzo tunda ba yanzu zan koma ba. daga nan mukai shirin tafiya, Siyama da Zarah anata mana iyayi su masu motar hawa, (dayake kowacce a motarta tazo).
Ni dai ni da Munubiya Yaa Marwan ya d’aukemu muka tafi.

____________________________

Tunda nabar wajen Nuren yazo ya tasa Galadima da tsiya, wai dama haka yake ashe?, rashin kunyar tasa har agaban surukai?.
Banza Galadima yamasa yay shigewarsa mota yabarsa yana iskancinsa.
Anan suka tafi suka barsa dayake da mota yazo shima.

Galadima na barin airport gidanmu ya nufa shima.
A lokacin ‘yan gidanmu suma sun Isa gida, sunata k’ananun magana akan abinda Galadima da munaya sukayi, dan saida suka bama sauran labari, nanfa suka kacame da zancen harda k’arin k’arya akai wai ba kiss kawai sukaiba (‘yan gidansu munaya annamimatu??????).
Itadai Maman Fauziyya batace k’alaba, saima dariya da zancen ke bata, Dady kuma bai dawo gidanba, daga nan wajen aiki ya wuce, yaran gidan ma kowa gidanta ta koma basu biyo nanba. Innaro da gwaggo Safiyya kam gida suka shige ana saukesu, dan haka basuji komaiba.

Galadima bai shiga gidan ba, saiya nemi iso gidan Innaro, Habiba ta fito tamasa jagora.
Innaro na falo tana cika da batsewa gwaggo Safiyya na lalla6ata akan ta kwantar da hankalinta.
Koda Galadima ya shigo innaro sai antaya masa harara takeyi, yana kula da ita ta gefen ido, ya murmusa yana zama saman kujera, cikeda tsokana yace “Sweet Granny Yaya dai?”.
Harara innaro ta zuba masa sosai, tana fad’in mikuma kazo min nan?”.
Galadima ya murmusa yana maida hankalinsa ga gwaggo Safiyya, gaisheta yayi ta amsa masa cike da kulawa, sannan ta d’ora da godiya da kwarara masa addu’ar fatan alkairi.
Yaji dad’i sosai, ya amsa cikin fara’a, sannan yace, “Granny ina furar tsufa?”.
“ai bazaka shata ba ”.
Nanma murmushin Galadima yayi yana mamakin wannan rikitacciyar tsohuwa. Yace “tunda bazan shaba Ashe kema kuwa bak’yaje India ba”.
Zabura innaro tayi, ta maida hankalinta ga Galadima tana fad’in “da gaske kake ko shak’iyancine?”.
Mi su Naja’atu zasuyi inba dariya ba, Galadima ma handkerchief ya saka ya rufe bakinsa kawai. Gwaggo Safiyya kanta saida ta dara.
Galadima ya gyara zamansa yana fad’in “karki damu Granny ninmu, insha ALLAH tare dake zamu tafi idan zamu koma”.
Dad’i ya kama innaro ta shiga sakama Galadima albarka.
Shidai murmushi kawai yakeyi. saida yaga sun nutsu sannan yace yazo tafiya dasu Aiyaan ne, babu musu innaro ta mik’e da kanta zuwa gidan danta kawo masa su.
Bayan fitarta gwaggo Safiyya tabama Galadima hak’uri akan darun innaro.
“karki damu gwaggo, ai dama kowa yasan idan sunkai irin wannan age d’in saida lalla6awa, ALLAH dai yaja mana ransu”.
Amin gwaggo Safiyya tafad’a cikin jin dad’i.
Tunda ‘yan gidansu Munaya sukaji wai Galadima ne da kansa yazo tafiya dasu Aryaan sai zukatansu suka kuma tunzura, kowa tana ganin hakan salon munafurcine, Maman Fauziyya ta kawoma innaro su, dama suna d’akinta, dan mamansu yaa hameed suna dawowa ta d’auki jakkarsu Aiyaan ta kaimata, wai sai dai su zauna wajenta ita d’akinta babu fili.
Maman Fauziyya batace komai ba ta kar6i su Aiyaan tana jinjina bak’in hali irinnan jama’ar gidan.
Amma kuma yanzu sai gasu sune dajin haushi.
Ita dai innaro ko’a kanta ta jawo hannunsu Zainab ta d’akko jakkar kayansu suka taho.
Koda sukazo ma sai Galadima yace abar kayan nasu su kad’ai yake buk’ata. ya ajiyema Gwaggo Safiyya da innaro alkairi ya fito rik’e da hannun su Aiyaan daketa murna.
Innaro har wajen mota ta rakosu, bata komaba saida taga tafiyarsu. tana komawa gida tahau had’a kayan tafiya, wai gara ta had’a ta huta, duk randa Galadima yazo sai tafiya kawai.
Ita dai gwaggo Safiyya dariya kawai tayi, dan maganar Galadima gaskiyace, lamarin innaro yana buk’atar uziri, ta tsufa sosai, kawai dai ALLAH yabata lafiyane, dan da wuya kaga innaro na kukan wani waje namata ciwo irin na tsufa. (masifarta kam dai kunsan ance abinda kayi a k’uruciya shi kake maimaitawa lokacin tsufa, ALLAH ka azurtamu da k’yak’yk’yawar k’uruciya to??????).

????)(?)(????

A k’ofar sabon matsakaicin gidan motocin biyu suka tsaya, cikin wad’anda suke a motar baya d’aya ya fito ya bud’e motar farko, hamshak’iyar macece mai ji da mulki da kud’i ta fito, kallo d’aya zaka mata ka tabbatar tagama samun duniya, cikin tsantsar tink’aho da homa take zuk’ar iska tareda taku d’ai-d’ai irin na manyan mata.
Cikin sauri aka bud’e mata k’ofar gidan ta shiga guard d’inta na take mata baya.
A tsakkiyar tsakar gidan taja tunga, sai hura hanci takeyi tana harare-harare.
d’aya a cikin guards nata yace, “ ma’am nan shine d’akin da yake”.
Batace uffanba taci gaba da takawa d’ai-dai har zuwa k’ofar d’akin, hannu ta d’aga musu alamar su dakata. Dukkansu baya sukaja domin cika umarninta.

Zaune yake a kujera an d’ad’d’aureshi, kallo d’aya zaka masa ka tabbatar a galabaice yake.
Shigowarta baisa ya d’aga kai ba balle ya motsa, yasan dai bazai wuce k’artan dasuka kawosa wajen baneba. sai dai jin k’amshin turaren mace yabashi mamaki, hakanne ya sakashi d’ago idanu domin tabbatar da yaren hancinsa.
Bakinsa na rawa yace, “Wacece ke?”.

Bata bashi amsaba, saima kujera data ja irin wadda yake kai ta dinning ta zauna, k’afa d’aya ta d’ora akan d’aya tana wani cika da batsewa. “yaro baka isa sanin ni wacece ba, Sai dai cigaba da 6atamin aiki zai sakaka sanina”.
Murmushi Muftahu yayi, ya d’ago idanunsa yana mata kallon rainin wayo, “Saninki dama aikin banzane a gareni, aikin ki kuma da kike ik’irarin ina 6atawa duk da ban sanshi ba, kisa a ranki yanzu ne na fara 6atawa, saiki shirya nunamin ke d’in wacece?”.
“hahaha, yaro baisan wutaba saiya taka”.
“Humm, wuta bata san yaroba saisu k’ulla”.
“karan farauta yaushe uban gidan naka yafara koya maka irin izzarsa haka?”.
“Kinsan zama da mad’aukin kanwa aishi ke kawo farin kai”.
“lallai zan had’a da kanwar da mad’aukin nata duk na koyar dasu darasi. Shi kansa Sameer d’in baikai darajar karen gidana ba balle kai yaronsa”.
Murmushi Muftahu yayi, “ Uhmm sai yanzu na fahimta, sai dai zan tunatar dake abinda kika manta, Wanda kikeyi danshi baima San da zamanki ba, kinga ashe ihu kikeyi bayan hari……….”.
“hhhhhhhh! Abin dariya, inbai fahimta ba ai zai fahimta lokacinda sak’on sunana da gawarka suka isa a gareshi, yanda ban haifi magajin masarautar gagara badauba, zeenah bata isa haihuwar magajinta ba wlhy”.
Idanu Muftahu ya tsura mata, sai yanzu yafara hango kamannin d’aya daga matan tsohon Sarki Abie da suka bar masarauta bayan shekaru biyu da fara jinyarsa, bashida wayau a time d’in, Dan dagasu har Galadima bazasu wuce 7-7 year’s ba, saida suntaso sunji labarin bijirewar matan a lokacin da za’a tafi da Abie India, dama shekaru biyun da suka zauna basu ta6a saka hannu a jiyarsa ba, sai Momma keta fama………..
Marin da aka zuba masane ya sakashi dawowa daga dogon tunanin daya tafi….
“tunanin mi kakeyi Karen farauta?”.
Jajayen idanunsa ya zuba mata, sai kuma ya kwashe da dariya, saida yayi mai isarsa sannan ya dakata tareda tsuke fuska, “ina tunano mummunan fuskarkine, in banda abinki miye na kishi da abinda kika bari da kanki? nasan dai Momma ba itace ta hanaki haihuwa ba ai, inason kisan ni ban isa kare Galadima ba dama, amma kulum cikin kariyar Wanda ya haliccesa yake, a tunaninki 6ata sunansa da kikayine ke nufin bazai mulki masarauta mai d’unbin tarihi da girmaba? kinyi kuskure babba wlhy, Dan kinsaka kanki a ramin damisa. duk ranarda Galadima ya gane kece kika saka amasa 6atanci a jarida wlhy saikinyi nadamar rayuwarki……….
Bayan Hannu tasaka ta bugi bakinsa, gefe yay da kansa yana murmushi, ga jini na zuba a gefen bakin, dayake hannunsa a d’ure suke.
Tace, “kafin ni nayi nadamar kai ne da shi zakuyi, Dan yanda kake a tarkona shima yanacan a cikinsa, wawa kawai, kai aboki mai gaskiya ko? zan shayar dakai mamaki, domin saikaga gawar Sameer a gabanka kwance kafin kaima kabishi baya”.
Dawo da kallonsa yayi gareta yana murmushi, “miyasa kika tsorata tunban k’arasaba, Galadima maruci ne, kuma kainuwane, gashi dakalin majina, kina hawansa zamewa zakiyi wlhy, ina tausaya miki yayinda tunaninsa ya waiwayo kanki, Dan yanzu aikin manyanki ne a gabansa ba nakiba, d’ana masa tarkonki kuwa tamakar kin tado damisane daga barci, hakan kuma fitinace babba a gareki da shi kansa Karen farautar taki Harun, tirrr da zuciyarki, ni kaina danasan ma kece bazan 6ata lokacina wajen bibiyar ki ta hanyar Harun ba, amma banyi bak’in cikiba, ko babu komai na ribantu da abubuwa masu yawa, domin ta silar hakan na had’a auren sunna, gashi harda ribar ciki, magajin Galadima Sameer kenan…….
A fusace ta d’aga kofin glass zata kwala masa.
Yace, “relax relax mana giwar mata, ai bangama fad’aba OK?” ba kince zaki kawomin gawar Galadima ba sannan, to miye kuma na fusata haka da wuri?, ni ina kuma tabbatar miki indai Galadima ne zaizo, daga lokacinda yasan ina nan tabbas zai zo, banza karyar farautar wasu, na tabbata k’arya kikeyi ba aikin kanki kikeba kema, sakaki akayi, lallai ke farashinki ya fad’i k’asa, matar sarki mai fad’a aji irin Sarki Saifudden Ce ta k’are ahaka? Abin kaico abin jaje, tirrr”.
Dariya ta kwashe da shi tana tafa hannaye, saikuma ta matsa gabda Muftahu tana magana cikin kunnensa “lallai bayan Sameer akwai magajin sa a gagara badau ashe?”.
“oh sai yanzu kika fahimta ashe?”.
“karen Sameer zaka mutu kaida uban gidan ka, saina saka wannan zuciyar tasa ta buga wannan shine k’udirina”.
“hhhhhhh abin dariya, kudirin wasu dai, danke naki bamai muhimmanci baneba, tunda kuka kasa saka zuciyar Sameer bugawa a lokacin da k’uruciya da rashin sanin kansa ke damunsa, miyasa kuke tunanin zata buga a lokacin da yagama tanadar makaman yak’insa, ranar shiga filin daga kawai yake jira, nagaji da tattaunawa dake please”.
“kaima kace wani Abu yaro, Dan haka mu zuba, kwana uku kawai zakaga gawar Sameer a gabanka!!!!!”.
Bata jira yabata amsaba ta fice daga d’akin, tareda jan k’ofa da k’arfi.
Idanunsa kawai ya rintse. Baya tsoron makircinta, amma yana tsoron na Harun, dan Galadima ya rigada ya yarda da Harun 100%, bazai ta6a kawo zai cutar da Shiba. Waige-waige yashiga yi, yasan babu wani abunda Galadima zai iya bibiya tare dashi.
Da sauri ya girgiza hannunsa saboda tunowa da agogo, jin agogon tare dashi ya sakashi lumshe ido yana ambatar Alhamllh. Matsala d’ayace baya ganin agogon, saboda hannunsa yana a baya ne. Amma dukda haka zai gwada idan za’a dace.

___________________________

Yau na kasance cikin farin ciki, saboda gani tsakkiyar ‘yan uwana, dukda ma zazza6ine mai zafi ke nuk’urk’usata, amma kewarsu ta hanani gajiyawa, mun bud’e babin fira a tsakkiyar falon mama Rabi’a, duk abinda akayi bana nan shine ake labarta min, yayinda Nima nake basu labarin India da nuna musu hotuna.
Haka mu kai wannan yini cikin farin ciki da annashuwar kasancewa da junanmu, musamman ma ni da ‘Yar uwar tagwaicina da k’addarar aure ta tilasta mana nisantar juna, ji muke tamkar mun shekara ba’a tareba. Kowannenmu k’ok’arin ganin farin cikin d’an uwansa yakeyi.

_____________

Tunda Galadima yabaro gida dasu Aryaan saiya wuce wajen wani hutawa dasu, ya yawata dasu sunata farinciki, yayinda shi kuma yake biyema shirmensu dan d’auke musu kewar mahaifiyarsu, yana son yara, shiyyasa ko yaushe Khaleel d’in aunty Mimi zakigansa manne dashi, sa’annin Khaleel dasu Aiyaan kuwa zai iya zuwa d’aya.
Cikin lokacin k’ank’ani suka saki jikinsu dashi.
Daga nan plaza ya nufa, haka kawai zuciyarsa keta tsikara masa zancen 6atan Muftahu, dukda k’ok’arin wofantar da lamarin da lamarin da ya keyi.
Waya ya d’auka ya shige danne-danne, alamu sun nuna masa wayar Muftahu na cikin masarauta, kenan bai d’auki wayarba, yad’an murmusa kawai yana cije lips, yayinda idonsa ke kansu Aiyaan da Saleem yazo d’auka suje wajensa danya huta.
Bye suka masa, shima ya d’aga musu hannu yana murmushi.
Suna ficewa ya sauke ajiyar zuciya tare da mik’ewa tsaye. zagayen office d’in ya farayi hannunsa goye a baya, a wannan karon bazai ta6a k’yale Muftahu ba, dolene yayi wani Abu akansa, dama yana d’aga masa k’afane domin son ganin gudun ruwansa kawai, yanzu kuma lokacin yayi dazai San mi yake k’ullawa………..???

*_Duk Wanda yaga ban amsa massage nashiba yamin afuwa, cakwakiyar network tasani clearing charts d’ina batareda na dubaba, tun around 3:47pm nayi posting amma yak’i tahowa._*

Dan haka ina gayyata kowa gobe a court, zamu shiga shari’a ni da network ne??.

Wad’anda suka ga basa ganin posting d’ina gaba d’aya a satinnan duk aikin network ne??.

*_ALLAH ya gafartama iyayenmhiyayenmu??????_*
*_typing??_*

?? *_HASKE WRITERS ASSO….._*

*_?RAINA KAMA…..!!?_*
_(Kaga gayya)_

*_Bilyn Abdull ce????_*

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply