Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 11


Raina Kama Book 2 Page 11
Viral

****************************

Dakatawa yay daga abinda yakeyi, ya bud’e idanu a hankali akan fuskata, murya k’asa-k’asa ya furta “camera?”.
Kaina na d’aga masa batareda na bud’e idoba.
Bai kuma cewa komai ba ya koma ya kwanta yana furzar da huci mai zafi daga bakinsa, sai kuma ya cije lips yana gyara kwanciya da sake rungumeni kawai.
Idona na bud’e a tsorace, azatona zai cigaba ne, sainaga ba haka bane.
A cikin kunnene ya furta “barci please”.
Kallonsa nayi ta gefen ido sai naga idonsa a rufe, nima banida za6in daya wuce na rufe nawan, dan haka na lumshe kawai.

Ni sai barcin ya d’aukeni, amma shi ya k’auracema idonsa, mamakin furicina ya dami zuciyarsa, dama yadad’e yana zargin akwai camera a d’akin nan nasa, sai dai bawai ya tabbatar bane, kuma bai ta6a yunk’urin dubawa ba. da wad’annan tunanin ya cinye lokacin barcinsa har aka kwala kiran sallar la’asar.
Bud’e idanunsa yayi akan fuskata, yad’an tsuramin ido nawasu time’s, sai yaga barcin yamin k’yau, kauda idonsa yayi cikeda basarwa, saikuma ya janyeni daga jikinsa yana yunk’urin tashi, hakanne ya sakani farkawar nima, na tashi da hanzarina ina gyara rigata, sai kuma na sauka na fice batareda nako waiwayoshi ba.
Bina yay da kallo harna fice sannan ya janye yana ta6e baki.

Ban kuma jin labarin Galadima ba har dare yayi, nafito wanka ina shirin barci ya shigo, yau dai babu laptop d’in kaddara, dagashi sai phone guda d’aya ma, yana sanye da kayan barci kalar gwaiduwar kwai masu duhu.
Zama yay a kujerar dake cikin d’akin, yayinda ni kuma na k’arasa saka hijjab d’in dana jawo, babu walwala ko alamar wasa kwata-kwata a face nashi, dan haka nima saina kama kaina.
cikin k’asaitarsa yace “muyi magana mana”.
Kallonsa na d’anyi, saikuma na amsa da “ina jinka”.
d’ago ido yay muka kalli juna, da ido yay min nuni da bakin gadon.
Ban musaba nazo na zauna, amma sai nayi k’asa da kaina ina wasa da zoben hannuna.
Maida kallonsa yayi ga zoben danake jujjuyawa, kusan mintuna 4 harna d’auka ya ma fasa maganar, na d’ago na kalleshi.
Ya kauda kai gefe yana fad’in, “waya fad’a miki da CCTV camera a d’akina?”.
Nima ban kalleshi ba na bashi amsa a tak’aice, “bakai ka saka kayarka ba danni?”.
Da mamaki ya kalleni, sai kuma ya kausasa muryarsa, “Munaayaa seriously nake miki magana!”.
nad’an razana, amma saina dake, nace “kana nufin bakasan da itaba?”.
“idan nasan da ita mizai sani aikata wani Abu na sirrina a d’akin”.
da mamaki na kalleshi domin tabbatarwa, tsantsar gaskiya na hanga a idonsa, dan haka na danna yatsun hannuna da k’arfi suka bada sautin “k’asss!, k’asan zuciyata na tunanin minene sirrin nasa?”.
Idonsa a kaina ko k’yaftawa bayayi, nima na d’ago mukaima juna kallon ido cikin ido, dukda tsorata danai da hango masifa cikinsu ban janyeba, nafara fad’in “tabbas naga camera a falonka, tana nan saitin hotonku kaidasu momma, inda flower d’in nan take, hakanne yasani zargin kai ka saka kayarka saboda tsaro”.
“hummm”. kawai yafad’a yana janye idanunsa, sai kuma ya taso ya dawo inda nake zaune, ganinai kawai ya rungumoni jikinsa, na waro idanu dan mamaki, shikuma ya lumshe nasa tareda sumbatar goshina a hankali, shigar sumbarce tasakani lumshe nawa idanun nima tareda k’ank’ameshi.
Cikin kunnena ya furta “i’m proud of you my friend”.
Da sauri na waro idanu ina kallonsa, saiya d’agamin gira d’aya yana wani miskilin murmushi, sannan ya tadani zaune shima ya tashi ya fita.
Baki da idanu da hanci duk na saki ina binsa da kallo, a k’asan raina ina tambayar mike damun guy d’innan ne wai?.
Banida mai bani amsa, dan haka na mik’e na cire hijjab d’in nai kwanciyata.

d’akinsa ya koma ya d’akko wani Abu kamar k’aramar ball?? ya ajiye saman table d’in gaban gadon, sannan ya manna wani dogon Abu a jikin ‘Yar ball d’in, ya d’akko laptop d’insa ya kunna. shiru na kusan mintuna uku ya k’urama abinnan ido, zuwa can yafara wata k’aramar k’ara d’i! d’i! d’i!, sai kuma k’aramar danja ajikin abinda ya manna d’in shima tana kawo haske jaa da d’aukewa.
Murmushin takaici kawai yayi, a zuciyarsa yanama ALLAH godiya dabai ta6a kusantar Munaya a d’akin nanba. dan tabbas ga CCTV camera ya gani a d’akin, an sakatane can ta saman wardrobe, yanda ko alama hankalinsa bazai kaiba, baiyi yunk’urin cirewa ba, ya d’auki kayan aikinsa ya koma parlour, dan yaga itakuma tanan a ina take?. yanama shigowa tun’a k’ofar tsakanin bedroom da falon ya gani, baima k’arasaba ya koma ciki, kashe laptop d’in yayi ya d’auke k’aramar ball d’in ya 6oye.
Duk wannan hidimar da Galadima keyi Sauban na kwance bisa gadonsa yayi d’ai-d’ai yana kwasar barci.
Gyara masa bargo yayi saboda tasowar hadarin farkon damina da iska tafara kad’awa sanyi ya busa. daga nan ya kashe masa fitila ya fita zuwa d’akin Munaya.

Ita harma tayi barci, tana k’ank’ame da fillo saboda sanyin hadarin dake busawa, gadon ya hau tareda warware bargon ya lullu6a musu. dai-dai iska ta taso mai azabar k’arfi, a rikice Munaya ta juyo ta k’ank’amesa saboda tsorata.
Rik’eta yay sosai yana fad’in “uchh! Karki karyani”.
Babu shiri munaya ta bud’e idonta, tana k’ank’ame da shi tace, “wai miyasa bazaka ke kwana naka d’akinba ne?”.
“k miyasa time d’in da kikaje India kika gajemin d’akina?”.
Shiru tamasa bata amsaba, amma yanajin alamar murgud’a bakinta akan k’irjinsa.
“punishment ya tabbata agareki yalla6iya”.
Da sauri nace “wlhy a’a, inba hakaba zaka koma saman sofa ne, ai kaima haka kamin a d’akinka”.
“uyim Madan tsiwa, to ai nima dankar ki murk’ushemin abin cikin kwan cikin barci yasani kwantawa anan?”.
Zan bashi amsa aka kwad’a wata tsawa data sakamu ruk’unk’ume juna babu shiri, sai kuma ruwa ya 6alle.
Da wannan damar Galadima yay amfani wajen canja salon kwanciyar tamu, tun ina nuna banaso har salonsa ya sakani sakin layi, (??anya munaya wannan cikin naki bashine tarkon da Galadima ya d’ana miki ba???).

Da asuba tashi nayi inata zum6ure-zum6ure, baice dani uffanba yashiga toilet ya tsarkake jikinsa. Bayan yafito nima na shiga.
Baki ya ta6e yana wani d’age gira d’aya tamkar ina kallonsa ya fice.

Saida nasha kukana sannan nayi wankan tsarki, narasa mike sakani biyema Galadima? insha ALLAH zan d’auki mataki (??idan babu abin cikin kwan ba??, nasan inhar yana nan babansa zaita samun bonus??).

Bayan na idar da sallar ban koma barciba, saina gyara d’akin nayi wanka, shirin fitarma na sake yi yau, dan baba k’arami yacemin k’arfe goma na safe zuwa 11 zasu tafi.
Kammalatawa kenan ya shigo, ko kad’an banji alamar shigowarsa ba, saida na gama fesa turare ina k’ok’arin ajiyewa na hango kamar mutum tsaye a bayana.
Da sauri nayi azamar juyowa, dayake yana gab dani kad’an ya rage na fad’a masa a jiki, na dai samu nad’anyi baya na jingina da mirror ina tura baki.
Ko motsi baiyiba shikam, bai kuma janye idonsa daga kallona da yakeba.
Haushi ya kamani, nima nabi jikin nawa da kallo kozanga abin da yake kallon, ganin babu wani Abu daya faru na d’ago na kuma kallonsa, “wai yalla6ai mi kake kallone haka?”.
d’an yatsansa d’aya yasaka yad’an shafi girarsa yana gyara tsayuwa, “abin cikin kwan mana”. ‘ya fad’a cikin basarwa’.
“ta gefensa na ra6a zan wuce ina fad’in “ai lokaci kad’an ya rage maka ka bar ganin nasa”.
Da sauri ya rik’o hannuna, na juyo muka kalli juna, mayun idanunsa ya saka cikin nawa, “kina zaton idan nabar ganinsa kema za’a cigaba da ganinki?”.
Guntun murmushi nayi ina janye idona daga cikin nasa, nace “kana zaton kasheni zakayi nima?”.
“cire maganar ma zato”.
Kallonsa na kuma yi, cikin yanayin da shi kansa bai ta6a zaton ina dashiba nace “saika fara shiri”.
Shima a dake yace “dama a shirye nake kullum”.
Na murmusa ina k’ok’arin cire hannuna daga cikin nasa, amma ya hanani damar hakan, kallonsa na kuma yi nace “ko har lokacin yayi ne?”.
Fisgoni yayi na koma da baya, ya mannani jikin mirror d’in tare da maida hannuna baya ya rik’e, ya matseni da jikinsa, fuskarsa gab da tawa tamkar zai had’a bakinmu, yayinda idonsa ke cikin nawa, wani miskilin murmushin gefen baki yayi, yasaka yatsansa yana zagaya janbakin dake kan la66ana a hankali, cikin muryarnan tasa mai kama da an masa dole ya fara magana cikin karsashi “ko Ubangiji yakanyi hukuncine ga bawan daya bijirema umarninsa, koda ace zubarda wannan cikin kikayi dolene saikin kuma d’aukar wani, zubar da shi na dai-dai da haihuwar yara goma anan gidan kafin na aikaki inda shima ya tafi” ya matsa la66ana da k’arfi, wani zafi ya ratsani saiga hawaye a kumatuna, murmushi yayi, yasaki la66an ya dangwali hawayen a d’an yatsansa, nunamin yay yana fad’in “lallai momcyn abin cikin kwan kin cancanta 100%, amma bayan abin cikin kwanfa akwai k’annensa, please bar kuka my dear friend”. ‘ya k’are maganar da sumbatar la66ana sannan ya sakeni yaja baya.
Koda ya sakeni sainayi murmushi kawai, sannan na juya ina fuskantar mirror, foda na d’auka na gyara fuskata, na sake saka jambaki kad’an kamar yanda na saka d’azun.
Tsayawa yay cikeda mamakin abin da nayi na ko inkula yana kallona, mi wannan yarinyar take shiryawa ne haka?…..
Kafin ya samu amsa Na juyo gareshi, fuskata d’auke da murmushi na ra6a zan wuce sa, bina kawai yay da kallo, naje gaban wardrobe na bud’e, alk’yabba na d’akko na sanya, sannan na d’auki handbag ina kallonsa har yanzu fuskata d’auke da murmushi.
Gira ya d’agamin shima yana wani k’asaitaccen murmushi, ya juya ya fita batareda yakuma magana ba.
Yana fita na sauke ajiyar zuciya ina dafe k’irji, wlhy ni kad’ai nasan dukan da zuciyata takeyi, kad’an yarage ya ranfo a tsorace nake, kalamansa ne suka shiga dawomin cikin zuciyata, mi wannan yake nufine wai……….?
“Shin bazaki bane?”.
Muryarsa ta daki dodon kunnena, da sauri na gyara yanayina na d’ago muka had’a ido, Ashe yana bakin k’ofar bai tafiba.
Bance komai ba na biyo bayansa.
A falon farko na iske kuyangina suna gaidashi, hannu kawai ya d’aga musu ya fice abinsa.
Tsayawa nayi muka gaisa, d’aya a cikinsu ta yunk’urin k’ar6ar handbag d’ina.

Na iske harya shiga mota, nima aka bud’emin na shiga, handbag d’ina ta mik’omin tana fad’in “ranki ya dad’e ana buk’atar rakkiyarmu ne?”.
Murmushi namata, na juya na kalli Galadima danjin mizaice, kansa ya girgiza alamar a’a.
Juyawa nima nayi na girgiza mata kai, tamana addu’a tana rufe k’ofar.
Tunda muka tafi babu wanda yace uffan, yanata latsa wayarsa.
Airport muka nufa kai tsaye.
Bayan motocin sun tsaya sarkin mota na yunk’urin fita yace “2 minutes ”.
Sarikin mota yace “to ranka ya dad’e”.
Ni ban fahimci mi suke nufiba, naga dai sarkin mota ya fita mukuma ba’a bud’e mana ba, sai kawai nakai hannu zan bud’e.
Hannuna ya rik’o, na juyo ina kallonsa, har Yanzu idonsa nakan waya,, ajiye wayar yayi ya juyo yana fuskantata, ina yunk’urin tambayar lafiya naji la66ana cikin bakinsa.
Ya salam, na fad’a a zuciyata, saida ya shanye janbakin la66ana tas sannan ya sakeni. yanda kukasan gunki haka na koma masa, ya buga yatsunsa biyu saitin fuskata suna bada k’arar d’as d’as yace “gargad’i, first and last dazanganshi abakinki yayin fita”.
Harya fita ban iya motsawa ba, saida aka bud’e murfin 6angaren danake sannan na iya sauke numfashi, na kasa fahimtar damuwar guy d’innan kwata-kwata. fita nayi nima, yana tsaye yana jiran fitowata. a tare muka jera muna tafiya, yayinda dogaransa ke take mana baya. ya wani miskile fuska tamkar bashine yagama ta6argaza ba a mota yanzun.
Mutane sai kallonmu suke, masu gulma nayi masu nunamu nayi, ni dai duk sainaji wani iri, shima tsaki yayi danya tsani kallo.
A mamaki na duk sai naga ‘yan gidanmu ma a wajen, gaggaisawa muka shigayi, muka rik’e hannun juna nida munubiya muka k’arasa inda innarmu take, gaisheta nayi, nace “su Aiyaan fa?”.
“suna gida zasu zauna da mamanku mana”.
“kai innarmu, ya zaki barsu wajen muguwarnan, bama gara Maman fauziyya ba komu suzo wajenmu”.
Murmushi kawai innarmu tayi, tace, “ashe bazaki canjaba Munaya?”.
6ata fuska nayi, ina fad’in “kai inna, duk canjawarnan danayi”.
Murmushi sukayi itada Munubiya. akuma dai-dai time d’in Ambulance ta shigo airport d’in, sai mota biyu a bayanta sai motar police guda d’aya.
Gaba d’ayanmu hankalinmu saiya koma can, Galadima ya k’arasa wajen Ambulance d’in, yayinda sauran motocin biyu Sauban da Nuren baba k’arami Dady ya Shafi’u da yaa Naseer yaa hameed suka fito.

Zuwansu baifi da mintuna 15 ba aka fara kiran sunan wad’anda zasu tashi a jirgin.
Sai kuma ma’aikatan wajen mutum uku suka iso wajen Ambulance d’in aka fara k’ok’arin fidda Abba. Hankalin jama’a da yawa ya tashi a airport d’in nan saboda tausayin Abba, mukam kuka ma wasunmu sukeyi ai, muna kallo aka gungura gadon da aka d’oroshi har zuwa ga jirgin.
Suma su innarmu suka shiga itada baba k’arami da Sauban.
Rungume juna mukayi nida munubiya muma muna kuka.
Galadima bai fito cikin jirginba saida yaga komai ya dai-daita. yana fitowa babu dad’ewa jirgin ya d’aga zuwa sararin samaniya, yayinda mukuma muke binsu da addu’oin fatan alkairi da samun sauk’i……………..???

??kutt harda na gobe nayi???????????????????????????.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu??????_*
*_typing??_*

?? *_HASKE WRITERS ASSO….._*

*_?RAINA KAMA…..!!?_*
_(Kaga gayya)_

*_Bilyn Abdull ce????_*

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply