Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 10


Raina Kama Book 2 Page 10
Viral

Book 2~ ????1?0??1?1?

……………….Koda motocin suka tsaya sarkin mota ya bud’e masa k’ofa yakai tsawon lokaci baiko motsaba, saboda tsantsar tunani da zuciyarsa ta lula, aduk sanda zuciya take cikin matsanancin matsi gangar jiki ma gazawar karfin ikon jini dana 6argo sukan mata k’aranci, shi kansa yasan yanada buk’atar mataimaki a kan wannan lamarin, amma k’arancin rik’on amana Na d’an Adam ne yake yawan gargad’arsa da taka masa birki, ba kowane zai fahimci ma’anar nok’ewar tasaba, sai mutum daya tsinci kansa a makamancin halin da yake ciki………
“Ranka ya dad’e mun iso”. Sarkin mota yasake fad’a cikin taraddadi da taka tsantsan.
A hankali Galadima ya bud’e idanunsa da suka koma launin jaa saboda damuwa a kan sarkin mota, batareda yace uffanba ya ziro k’afarsa k’asa yana cije lips da had’iye wani kududun damuwa a mak’oshi.

Tunda ya fito ma’aikatan wajen suketa masa sannu da zuwa, dan tunda ya shigo k’asar sai yanzu ne zai shiga cikin plaza d’in.
Hannu kawai yake iya d’aga musu, amma bakinsa yay masa nauyi, kallo d’aya kuma zaka masa ka nazarci damuwa da buk’atar hutun dake tartare da kuzarinsa.
A cikin plaza d’in ma bata sauyaba, d’aga hannu agaresu shine yazama linzamin amsa gaisuwar dasuke masa.
Da hannu yayma d’aya daga dogaransa nuni da amso masa key.
Da sauri dogarin ya amsa yana mai nufar sashen da zai kaishi office d’in Saleem mai kula da CCTV camera’s.
Sai dai kafinma yakai ga k’arasawar suka had’u da saleem, Wanda tun shigowar motocin Galadima ya gansa.
Keys d’in ya damk’ama dogarin, sannan ya k’araso domin mik’a gaisuwa ga ogansa na wajen aiki kuma magajin garinsa.
Shima d’in dai hannu Galadima ya d’aga masa, hakan kuma ya saka Saleem fahimtar akwai damuwa kenan.
Koda aka bud’e ya shiga saiyayma dogaransa nuni da suje kawai, sannan ya maida idanunsa ya lumshe tareda kwanciya jikin kujerar yana lilawa a hankali.
Shi kansa baisan tsawon lokacin daya d’auka a hakanba, amma tabbas yasan yashiga kudin nazari mai zurfin gaske. Knocking d’in k’ofar da akayi yasakashi bud’ar baki da k’yar ya bada izin a shigo.
Nuren daya shigo ya maida k’ofar ya kulle, kafin ya ida takowa cikin office d’in, idonsa nakan d’an uwannasa.
Zama yay a d’aya daga kujerun dake fuskantar Galadima, “brother what happen?”.
“Northing”. Galadima ya fad’a batare da ya bud’e idonsa ba.
Shiru kawai Nuren yayi shima, ya d’akko laptop a briefcase d’in daya shigo da ita, kunnawa yay, kusan mintuna biyu ya d’ago ya kalli Galadima, sai kuma ya maida kansa ga laptop d’in. “Sameer nasan kaga cigiyar da akeyi takowacce kafar yad’a labarai ta k’asarnan akan d’iyar minister, sannan jami’an tsaro tsaye suke akan binciken inda take. yakamata musan abinyi kafin lokaci ya k’ure mana”.
Guntun murmushi Galadima yayi, batareda ya bud’e idanunsa ba yace “Nuren indai har babu wata waya datake aiki inda kakai yarinyarnan, kuma ka cire sim card d’in phone nata a lokacin daka d’auketa, to babu wata hanya dawani jami’in tsaro zai ganota, dama hanya d’ayace da kuskure zai basu damar bibiyarta, na d’aya lokacin daka d’auketa yazam wayarta na aiki, tabbas zasubi ta wannan hanyar su gano har iya inda ka kashe wayar, hanya ta biyu itace ka kashe wayarta baka cire sim card d’in ta ba daga phone nata, koda wayar a kashe take zasu bibiyeta ta hanyar ?? su ganota” ya tashi zaune sosai yana bud’e idanunsa akan Nuren, “wannan hanyoyin biyu kawai ke garesu saikuma idan da camera tare da ita, idan duk babu wannan basuda wata hanya, ka kwantar da hankalinka my brother, komaina da tsarinsa right?”.
Murmushi Nuren yayi, kafin ya salute d’in Galadima yana fad’in “I thrust to you my dear broth”.
Shima galadima salute d’in Nuren d’in yayi yana murmushi.
Komawa yay ya sake kwanciya jikin kujerar, “yanzu inaga time d’in turama minister Massage yayi?”.
Cikin zaro idanu Nuren yace “baka kallon hakan a matsayin ganganci kuwa?”.
Baki Galadima yad’an ta6e yana crossing k’afarsa, cikeda izzarsa yace “sai idan nabama wani damar hakan ai”.
Nuren baice komaiba, dan yagama sanin hatsabibancin Galadima wajen iya sarrafa Computer, dan haka ya bar wannan zancen ya d’akko wani. “yauwa to maganar Malam Saminu fa? Kasan yana hannunmu fa har yanzu?”.
“wannan barsa saiya kuma magantuwa, dan da alama yasan wani Abu, saidai akwai abinda ya sakashi za6ar 6oyewa. ni yanzu damuwar 6atan Muftahu yafi damuna, nasaka camera’s jikin mutane 10 danake iya zargi a masarauta amma banga alamun da hannun koda mutum d’aya ba, hakan ya tabbatar min da gaske Muftahu na bibiyar lamarina, sai dai bansan dalilinsa ba, ko kuma waye sakashi?”.
Nuren ya jinjina kansa, “brother aini da Harun dama mun dad’e da zargin Muftahu, Kaine kawai kake masa kallon mutumin kirki daman”.
Lips kawai Galadima ya cije, amma baice uffanba, Nuren yaci gaba da ‘yan danne dannensa a laptop d’in, zuwa wasu mintuna batareda ya d’agoba yace, “maganar Sirikinka fa?”.
Shiru Galadima ya masa, saida ya mula dan kansa sannan ya murmusa tareda maida idonsa ya lumshe, “a daren jiya nagama da wannan matsalar, sim card d’insa 3, akwai Contact 300 da 38, mtn yanada mutum 172, ya fara saka credit a layin shekaru 15 kenan, ranar 3/6/2005, glo 107, ya fara amfani dashi shekaru 8 kenan, wad’annan sune Sim card d’insa da yake mu’amulla da kowa a ciki, kuma anfi saninsa da su, akwai 6oyayyen layinsa Na mtn shima, yafara aiki dashi shekaru 13 kenan, kuma mutane 59 ne kawai acikinsa, sannan ba kowane yasan layinba, dan dukkan family nashi basu San da zamansa ba, ita kanta mahaifiyar su Munaya batasan anyi saving number a phone nata ba, suma da suka kirata basusan da number a wayarta ba, dan baita6a kiranta da shiba, akwai matakan tsaro dake tattare da Layin, hakanne ya tabbatar min da akwai abinda yake 6oyewa a Sim card d’in, dan sai time to time yake amfani da shi, kiran matarsa da sukayi da layin wannan shine kuskuren farko da suka tafka da Sameer ya samu hanyar musu takun sauro. zan fara aiki akan layin na shigesu ta hanyar da basu zataba”.
Jinjina kai kawai Nuren yakeyi dan mamaki, Galadima da banne, kamar yanda basirarsa take daban, ya sauke ajiyar zuciya yana kama hannun Galadima da idonsa ke a lumshe har yanzun, cikin karsashi yace “lallai kai RAINA KAMA ne Sameer”.
Murmushi kawai Galadima yayi, amma baice uffanba.

Knocking akayi, Nuren ya kalli k’ofar yana bada izinin a shigo, Sauban ya shigo da sallama, su duka idonsu a kansa, Nuren yace “lafiya kuwa?”.
Zama Sauban yayi yana sauke Numfashi da k’yar, cikin magana d’ai-d’ai da alamar a birkice yake yace, “wlhy Yaya binmu aka ringayi da wata bak’ar Jeep, da k’yar mukasha wlhy, ni dai yau zanbar k’asarnan gaskiya”. Sauban ya fad’a tamkar zaiyi kuka’.
Gani kawai sukai Galadima yana dariya, saida yayi mai isarsa sannan ya tsagaita.
Nuren da Sauban suka tsaya kawai suna kallonsa.
Tashi yayi tsaye yana takawa cikin izzar k’asaita, ya dafa bango yana lek’en waje ta window d’in office d’in, yakai wasu adadin lokuta a wajen, sai kuma ya juyo yana kallon Nuren d’in da Sauban da suma suka zuba masa idanu.
“my dear brother! daka tsaya sun kamaka ai, tabbas da wannan shine kuskuren da zasuyi Wanda bazasu ta6a mantawa da waye Muhammad Sameer Saifudden ba a tarihin rayuwarsu. Waya gaya maka kana yawo cikin 9ja ne batareda idon Sameer ba a kanka?”.
Sauban ya sauke ajiyar zuciya yana share gumin daya jik’a fuskarsa, “wlhy yaa Sam daka fad’amin da bazan tsorata ba”.
Daga Galadima har Nuren dariya suka kwashe da shi, Nuren ya dafa kafad’ar Sauban yana fad’in “matsoracin banza”.
“uhm-uhm yaa Nuren bazaka ganeba wlhy, tsoro halak ne fa”..
Galadima dai baice komaiba ya koma ya zauna yana murmushi.

?)))*(((?)))*(((?)))*(((?)))*(((?

Ganin har anyi sallar Magriba babu baba k’arami balle Dady ya saka Innaro d’aukar gyale ta fito, lokacin gwaggo Safiyya tana salla, shiyyasa batasan innaro ta fitaba, habiba da Naja’atu dake tsakar gida suna tattare kaya saboda hadari na farkon damina dayake nuna alamar zai zubda ruwa. suka kalli juna, Naja’atu tace “yaya habiba tsohuwarnan fa bata da dama wlhy”.
Dariya habiba tayi, “ai kad’anma kika gani Naja’atu, yanzu dai zataje ta tadama baiwar ALLAH hankali”.
“to ALLAH ya k’yauta”. ‘cewar Naja’atu tana rik’e ha6a’.

Lokacin da Innaro ta shigo gidan d’akin Innarsu Munaya ta nufa kai tsaye, sai dai ta iskeshi rufe, kwala kiran sunanta ta shigayi cikin masifa, “Ai’sha!! Ai’sha!! Nasan kina jina, wlhy ki fito kafin yau d’innan igiyar aurenki ta tsinke”.
Mamansu yaa Hameed da gwaggon Haleematu ne suka fito, mamansu yaa hameed tace “aiko tafita fa inna, dan gab da magribar nan naga Fadeel ya shigo sun fita, bansan mike faruwa ba dai”.
“yaza’ayi kusan mike faruwa tunda anyi k’ulle-k’ullen munafunci, lallai jafaru, wai yau da kaine za’a muzantani hannun mak’iyana, to nikuma naga ta yanda Ai’sha zataje wata k’asa jiyyar Auwalu da raina”…….. haka taita zuba banbamin masifa matan gida na saurarenta, daga daddy har baba k’arami suna gidan amma sukak’i fitowa. Jarabar Innaro ta saka kowa na gidan fahimtar mi ake ciki, nanfa hassada da bak’in ciki suka kume zukatansu, dukda kuwa sunsan tafiyar bata dad’i baceba, maman fauziyyace kawai hakan yamata dad’i, koba komai inna ta huta da cin zarafin Innaro koyayane.

Sai da Gwaggo Safiyya ta shigo tama Innaro magana sannan ta tafi gida, su matan gidanma sai yanzu suka San da zuwa gwaggo Safiyya d’in.
Amma sunso ace innarsu munaya na gida Innaro tayi wannan rashin mutuncin.

Hummm??.

****************************

Bayan fitowar su Galadima daga birnin gayu, sun wuce gidane, Nuren kuma yakoma hotel d’in daya sauka.
Galadima kawai ne ya shiga sashensu, amma Sauban 6angaren mai martaba ya nufa neman yarima Mahfuz.

Munaya na zaune a falon farko tareda sabbin kuyanginta guda uku, (dan bata amince su shiga falonta ba, saita gama tantance su sannan) ba wani hira sukeyiba, d’ayace a cikinsu ke sak’a shine abin ya birge Munaya take kallo, tana kwance cikin doguwar kujera ne, yayinda su kuma su ke zaune a k’asan lallausan carpet d’in falon.
Dogarai biyune suka fara shigowa hannunsu d’auke da ledoji, sai kuma mai gayya mai aiki Galadima.
Da sauri bayin suka mik’e tsaye, saida ya ida shigowa sannan suka d’urk’ushe a k’asa suna kwasar gaisuwa.
A la66ansa ya amsa yana d’aga musu hannu, yayinda idanunsa ke kan munaya da itama ke satar kallonsa
Duk d’insu kowa janyewa yayi, yayinda bayin da dogaran suka fice bayan sunkai ledojin falon Galadima.
Baice da ita uffanba yafara takawa zai shige, tamkar mai tsoron fad’a tace, “sannu da zuwa”.
Ysayawa yayi cak, sannan ya juyo da kansa tamkar mai ciwon wuya ya kalleta, bata yarda sun kuma had’a idoba takuma fad’in “nagode sosai”.
“for what?”. ‘ya fad’a cikin isa’.
Shiru munaya tayi, ta kasa cewa komai.
Shima bai sake cewa komai ba ya taka ya shige abinsa.
Harara munaya ta raka bayansa da shi, sai kuma ta sauke numfashi tana tashi itama, bedroom d’inta ta koma, a saman sofa ta zauna tana dafe kai, sosai take buk’atar zuwa sake duba mahaifinta, amma ta kula Galadima bashida niyyar cemata taje, kai itako wannan wane irin abune haka? shi dama gidan Sarautar haka yake bakada ‘yancin kanka?, komai saida k’a’ida. tun d’azu kuma take kiran number inna bata d’agaba, tadai kira baba k’arami da daddy sun gaisa ta tambayi jikin Abba, shine ma har suke kuma sanar mata k’ok’arin da galadiman keyi. tabbas hakan da yayi yasata jin farin ciki, koba komai tasan shi adaline, ko anan gaba ragamar shugabanci ta riskesa zaiyima na k’asa da shi adalci.

Galadima daya shiga tun a falo yafara k’ok’arin cire navy blue d’in jacket d’insa, ya wullata saman kujera, sassauta belt d’in yayi shima amma bai cireba, ya zauna cikin tsantsar nuna gajiya yana furzo iskar bakinsa, remote ya d’auka ya kunna tv, tamkar ya saita lokaci saiga hoton d’iyar minister mai amsa sunan Farhat ana nunawa, an saka 2.5 millions ga dukkan wanda ya kawota koya bada bayanan sirri akan wanda yasan wani Abu akan 6atanta.
Wani mugun tsaki Galadima yaja a zuciyarsa yana fad’in wawaye, saiku k’ara yakai 100millions ba 2 ba, idan ubanta ya shirya kawo kansa gareni nima a shirye nake nabashi shashashar ‘yarsa mai zubin ta6arya, ya kashe TV d’in kawai ya mik’e ya shige ciki.
Ko ina fes da shi, yasan baida Matsala da Sauban a 6angaren tsafta dama. kayan jikinsa ya ida cirewa ya shiga wanka.
Bayan ya fito samu yay yad’an kwanta, dan ya samu Hutu kona 2hours ne, dan yanzu akayi sallar zuhur. aiko kwanciyarsa babu dad’ewa barci yay gaba dashi.

Munaya ta jawo wayarta da nufin kuma kiran inna, amma sai taga Ashe credit d’inta yama k’are, kanta ta dafe dan haushi, zuwa can tamik’e domin bin shawarar zuciyarta. turare ta kuma fesama jikinta ta d’auki gyale ta yafa.
Ta d’an dad’e a k’ofar d’akin tana tunanin idan kuma ta shiga hasashenta bai zama gaskiyaba ya kenan?, wata zuciya tace kije abinki k’ilama wanka yake.
Da sand’a na ida shiga tamkar wata 6arauniya, sai kuma na tuna ai yanada CCTV camera, nutsuwa nayi na daidaita kaina, na koma normal saboda tsaro. Ganin babu abinda naje nema d’in a falo saina zarce bedroom ina wani ciccijewa.
Mamaki ya kamani ganinsa kwance a kan gado yana shak’ar barci hankali kwance, hakan yamin dad’i kam.
Saida nabi ko’ina na bedroom d’in da kallo, ganin babu alamar akwai camera a nan saina ida shiga, wayoyinsa biyu na ajiye gefen filon dayake kwance, rabin hannun damarsa ma nakan d’aya ya d’ora cikin barci halan?.
Dole saina hau saman gadon, dan haka na tsaya tunanin yanda zanyi, banida wata mafita dan haka nahau a hankali, kai kace wata hawainiya ce.
Cikin rintse ido da cije la66a nakai hannu zan d’auki wayar d’aya.
Caraf aka rik’emin hannu, babu Shiri na bud’e idona zuciyata nawani tsitstsinkewa.
Fisgoni yayi na fad’o jikinsa, zafin danaji ya sakani sakin k’aramar k’ara.
Ya matseni a jikinsa batare da ya kula miya aikata ba. nikam jikina sai rawa yakeyi, tsorona karya d’auka ko cutar da shi zanyi ma…….. maganarsa cikin yanayin barci ta Sani kallonsa.
Kad’an ya bud’e idonsa dake jajir, alamar da gaske barci yakeyi, muryarsa a sark’e irinta barci yace, “sata kika koma?”.
Baki na tunzuro ina marmar da idanu da suka cika da kwalla, nace “ALLAH ya kiyaye, arafa zanyi”.
Kuma matseni yayi har saida na rik’e hannunsa,, yace “wannan ba aro bane sata ce yalla6iya, dan haka dolene ki kar6i punishment”.
Jin ya ambaci punishment saina kuma rikicewa, nahau k’yarma ina rantse-rantae da matso kwallan idona.
Bai wani saurareni ba ya hau sumbatar wuyana, tureshi nafarayi amma saina gaza, dan haka na koma mintsini, shima a banza man kare??.
Dukna d’auka wasa yakeyi kawai farfaganda Ce danna tsorata, amma saina tsinci ya fara sakin layi, iya yina da rok’o, yakushi, mintsini, ban samu ku6uta ba, saima salonsa yafara tasiri a kaina, nima nai luf harda k’ok’arin maida murtani. saida naji zai kama wata tashar nai azamar tsaidashi ta hanyar fad’in “please yalla6ai camera”.

Maganinki ai baby??, su Galadima akwai bak’in wayo dai????, idan ta gaskiya za’abi ni banga abin punishment anan ba??, dama yadawo ‘Yar matsalarsa dai tsautsayi ya kawo mai karanbani dason banza ta fad’a tarko??????.

**********?********

Koda inna ta dawo saita had’ama su Aryaan kayansu, da nufin su koma wajen mamansu yaa hameed harta dawo.
Amma suka tibire akan bazasu jeba, su Uncle yace zaizo ya kaisu wajen Auntynsu.
Tun inna na lallashinsu harta kai ga mammakesu suka fara kuka, daga nan sukai barcin dole.
Bata fasa had’a kayanba, tagama tsaf ta d’auki akwatin zuwa d’akin mamansu yaa hameed.
Su Bintu kawai ta iske a falo suna kallo, Aminu ne yace “innar ‘yan 2 ina zaki da daddare?”.
Murmushi inna tamasa tana fad’in “kayansu Aryaan ne Aminu……..”
Bata gama rufe bakiba mamansu yaa hameed ta fito. ganin innarsu munubiya da kaya saita had’e fuska. Inna bata damuba tace “ga kayansu Aiyaan, saisu dawo nan da zama kafin na dawo”.
“to”. Kawai mamansu yaa hameed tace tana kauda kai gefe.
Ran inna ya sosu, amma sai batace komai ba ta ajiye ta fice jiki a sanyaye.
Da murnar Haneeff ya tashi zai d’au jakar yakai d’akinsu, amma sai Maman ta watsa masa harara. babu shiri ya koma ya zauna. Jakkar dai sai anan ta kwana, bata d’auka ba, bata bar ‘ya’yanta sun d’auka ba saboda bak’incikin inna zataje jiyyar Abba ba itaba.

ALLAH ya k’yauta??.

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply