Hausa Novels Raina Kama Book 2 Hausa Novel

Raina Kama Book 2 Page 1


Raina Kama Book 2 Page 1
Viral

Book 2~ ????1?

………….Tunda mukayi maganar nan dashi banyi k’asa a gyuwa ba wajen dagewa da addu’oi wa mahaifinsa, ina buk’atar ruwan zam-zam, dan haka yau nashirya fad’a masa ya nemomin. tunda safe ya fice, dan haka bamuga juna ba.
Yauma dai haka Na tashi banida wata isashshiyar lafiya, Na tak’ark’ara nayi gyaran d’akin har zuwa falo, sannan Na had’a ruwa mai zafi nayi wanka dashi.
Ina cikin shiri najiyo sallamar Samha a k’ofar falon, rigar dana fara sakawa Na k’arasa, sannan nace ta shigo.
“humm Aunty gimbiya kina kallon kanki a mirror kuwa?”.
Cikeda mamaki Na kalleta sannan Na kalli jikina, nace, “kamarya?”.
Zama tayi a sofa tana ‘yar dariya, sannan tace, “wlhy kinyi k’iba, sati uku kacal da zuwanmu India kin koma wata madam”.
Nad’an fiddo idanu waje, sannan Na harareta, “lallai Samha nagode da zagi to”.
“tab wlhy babu wani zagi gaskiya Na fad’a, halan Uncle Sam bai ta6a fad’a mi ki ba……..”
Ta k’arasa Maganarta da d’ai-d’ai saboda shigowarasa d’akin da sallama ciki-ciki.
Suna had’a idanu ya watsa mata harara, hakan ya tabbatar mana da yaji maganar tata, da sauri tamik’e ta fita, Nikuma najawo gyalena na yafa sannan Na kallesa.
Saman sofar ya zauna ya dafe kai, kallo d’aya zaka masa ka karanci damuwar dake shimfid’e bisa fuskarsa.
“yalla6ai lafiya kuwa?”. ‘nafad’a cikin tausayawa’.
Shiru bai amsaniba, banyi zuciyaba nataka a hankali zuwa gabansa, durk’usawa nayi a gaban nasa, a d’arare nasa hannu Na najanye nasa dayay tagumi dashi.
Ya d’ago idanunsa da sukai jaa yana kallona. kasa jurar kallon cikin idonsa nayi, Na janye nawa gefe, cikin dakiyar zuciya nakuma fad’in “bakada lafiya yalla6ai?”.
Yanda nayi maganar a marairaice saiyaji yakamata ya fad’amin, kodan nuna damuwar danayi akansa……
Ganin yamin shiru nikuma saina yink’ura natashi ina fad’in “kayi hak’uri idan nashiga hurumin daba nawab……”
Bankai k’arshen maganarba naji tattausan tafin hannunsa cikin nawa.
Rintse idanuna nayi, saboda wani yarrr da tsigar jikina tayi, shima agaresa saiya lumshe idanu kawai. najuyo danufin zare hannun kawai ya fisgoni na fad’a saman kujerar, rabin jikinna duk yana a jikinsa, yayinda sauran rabin nake a kan kujera.
Bansan nawani lumshe idanuba saboda daddad’an k’amshin turarensa d’aya ratsa hancina zuwa magudanar jinina. shikuma ya sauk’e 6oyayyiyar ajiyar zuciya.
Ya karkato da fuskarsa inda tawa take a gefen kafad’arsa har inajin saukar numfashinsa saman face d’ina, mayun idanun nan nasa suka kuma shiga cikin nawa, na janye da sauri, sannan nafara k’ok’arin cire kannawa daga kafad’arsa.
Hannunsa na dama da nake jiki ya sak’alo ta bayana, ya maida kai na ya kwantar a kafad’ar tasa, cikin muryarnan tasa mai kama da anmasa tilas yace, “jikin Abie ne ya motsa, Ashe tun jiya basuyi barciba gaba d’aya, da safennan Akash yakirani yake sanarmin, nakasa kallon halin da mahaifina yake ciki Munaaya! Abie na yana cikin mawuyacin hali..” ‘yak’are maganar cikin zirarowar kwallar data cika masa idanu tunda yafara maganar’.
Wani matsanancin tausayinsa ne ya ratsani, duk jarumtar Galadima kaga yana kuka ai kasan lamari ya 6aci gaskiya, nima hawayen suka fara gudun fanfalak’e a kumatuna, tashi nayi zaune sosai, cikin wata jarumtar da bansan inada itaba nasaka hannu Na kamo hannunsa cikin nawa. Sai kawai naga ya zame sosai ya kwantar da Kansa bisa cinyata, tareda hard’e hannayensa a k’irji. duk da kujerar tama tsawonsa kad’an, dan ma Love’s chair ce.
Kansa nafara shafawa a hankali, hawaye na zirara daga idona har yanzun.
Shikam idanunsa a lumshe suke.
Cikin tausasa harshe da tsantsar Nuna kulawa da tausayawa nace, “Yalla6ai kayi hak’uri, Abie d’inmu yana buk’ar addu’armu ne fiye da kukanmu, sannan itace jarabawarsa, wad’anda suka aikata masa hakan summa kansune, domin ALLAH bazai barsuba. idan ka amince akwai wasu addu’oi Dana Sani, Nina kakanmu ne yabama innarmu kafin yarasu, shine ta koya mana, mizai hana ka samo mana zam-zam muma mu farayima Abie su, Ubangiji gafurun rahimunne, babu abinda ya gagaresa, kuma shine yace mu rok’esa zai amsa mana”.
Tunda nafara maganar bai bud’e idonsa ba, nikuma ban fasa shafa masa kaiba. Saida nakai k’arshen zancen sannan ya bud’e lumsassun idanunsa dasuka koma launin jaa a kaina. yamotsa baki kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru.
Nima shirun nayi ban sake yink’urin yin magana ba, nadai cigaba da shafa kan nasa a hankali. ba akai 3minutes ba barci ya d’aukesa, sai numfashinsa danaji yakoma sauka a hankali.
Ajiyar zuciya na sauke kawai, na tsurama fuskarsa ido, yaune ranar farko dana ta6a nutsuwa namasa kallon tsaff, sosai yake kamanni da dukkan iyayensa, Abie da Momma, amma yafi tsananin kama da Momma gsky, duniyar tunani nafad’a batare dana fargaba, tausayin Galadima da families nashi yana cukurkud’ar ruhina, insha ALLAH nayi alk’awarin bada gudun mawa a duniyarsu har zuwa lokacin da aurenmu zai k’are.
kaina na jingina da jikin kujera, nima sai barcin ya kwasheni, dama bajin dad’in jikina nakeyiba.

********

Bayan anma Abie allurar datake temaka masa yin barci mai nauyi idan jikinsa yamotsa irin haka su Momma suka sami nutsuwa, dan yayi barci.
Sai alokacin hankalin Momma yadawo kan Neman Galadima, tabbas taga yafita hankali a tashe lokacin da Abie ke fidda numfashi a wahale, amma hankalinta bai koma kan Galadiman ba.
Aunty Mimi ta kalla tace, “Mimi ina d’an uwanki?”.
Itama aunty Mimi sai yanzu hankalinta yadawo ta farga babu Galadima d’in, hankalinta a tashe tace, “Momma inagafa ya fita, bara na duba”.
Bata jira cewar Momma ba tafito daga d’akin da sauri. ganin babu Galadima a wajen hankalinta yak’ara tashi, fitowa tayi harabar asibitin tana tambayar securitys d’in wajen.
d’aya ya sanar mata ya fita a rikice gaskiya, dan suma sun nemi su taimaka masa amma baima tanka musuba.
Innalillahi tashiga ambata. Bata koma wajen Momma ba tashiga mota tanufo gidan.
Ta iske Samha a falo kwance, ko sauraren sannun datake mata batayiba tace, “k ina Uncle d’inku?”.
Samha tace, “yana sama Mummy”.
Da sassarfa ta haye step’s d’in, itadai Samha da mamaki taringa binta da kallo.
Ko knocking bata tsaya musuba ta turo k’ofar ta shigo.
Ajiyar zuciya ta sauke dan ganin Galadima kwance, kansa bisa cinyar Munaya, hannunta d’aya na bisa Kansa, yayinda shikuma yarik’o d’ayan hannun munaya ya had’e da nasa ya d’ora kan kirjinsa, suduka barci ya kwashesu a haka. cikin sand’a ta juya ta fita taja musu k’ofar tana share hawaye dayima ALLAH godiya d’aya bama d’an uwanta mace tagari wadda take kulawa dashi. inda dane kafin yayi aure shima sai ciwonsa yatashi saboda damuwar dazai saka Kansa akan motsawar jikin Abie, amma gashi yanzun yasamu mai kwantar masa da hankali, suma kuma nasu ya kwanta suji da Abie kawai.
Momma ta kira ta fad’amawa dan hankalinta itama ya kwanta.
Momma harda hawayen farinciki, tana godema ALLAH.
Aunty Mimi bata zaunaba suka koma asibitin itada Samha da tace zata bita, itama sai yanzu takejin jikin Abie ya motsa.

*************

A k’alla munyi barcin 47minute’s, Galadima ne yafara farkawa, ya bud’e idanunsa a hankali, hannuna dake rik’e a nasa yafara kallo, kafin yad’ago ido zuwa kaina, yamin kallo kusan na 2minutes sannan yad’an motsa da nufin gyara kwanciya, saina bud’e idona, ido muka had’a, kowa yay saurin janyewa cikin basarwa, hannuna dake kansa na cire, sannan nazame Wanda yarik’e d’in, dan wata matsananciyar kunya ce kuma takamani.
Shima sai ya tashi zaune sosai, a hankali yacemin “thanks”.
Daba kusa dashi nakeba ma bazanjiba. Bance komaiba, shima bai sake cewa komaiba yamik’e tsaye. takalmansa kawai yacire ya d’auki jallabiya a wardrobe d’insa yashige bayi.
A hankali na sauke ajiyar zuciya, tareda janye idona daga k’ofar bayin, komai banceba nakuma zamewa saman kujerar na kwanta.

Ya d’auki adadin wasu mintuna masu tsawo kafin yafito sanye da jallabiya ruwan toka, da alama wanka yayi, kallona yayi batareda yayi magana ba ya nunamin agogon dake ajiye a drowan gefen gadon alamar time d’in salla yayi.
Kaina kawai na girgiza na mik’e, zuciya ta na mamakin hali irinna Galadima.
Shikam turare kawai ya d’auka ya fesa yafice salla.

??? ((?))(())((?)) ???

A gidanmu kam hankalin mamansu yaa hameed da Zarah a tashe yake, dan babu Sa’eed babu labarinsa, kira Zarah tamasa yafi 50 amma yak’i d’agawa, ta tura massages babu reply, bata aikin komai sai kuka, ga ciki.
Abbanmu kuma jin sanadin sawowar tata gida yace bazai kira Alhaji halliru ba har sai Zarah tafad’i ainahin gaskiya, danshi bai yarda ba itace ta d’auki kud’inba..
Innarmu dai dasuke zagi suna kallonta mak’iyarsu batakai komaiba itace tashiga lalla6a Abba damasa magiya.
Itama da farko buris yay da ita, saida yaga tanace sannan yace, “wai kekam Ai’sha miyasa kika damu kankine? kinbi kin damu da lamarin wad’anda basu damu dakeba, na tabbatar da Munaya ko Munubiya ke cikin wannan halin su murna zasuyi a gidannan”.
Murmushi innarmu tayi, cikin kwantar da murya tace, “Alhaji ai daga Zarah harsu munubiya duk d’ayane a wajena, domin kaine mahaifin Zarah, dukkan abinda kuma yakasance naka ina kaunarsa fiye da zatonka, a duba lamarin yarinyar kodan abinda ke gabanta, ba’a son mace mai ciki da shiga tashin hankali, muyima tufk’ar hanci tun munada sauran dama, basai Abu yayi tsamariba kuma muce zamu nemo mafita, hannunka baya ru6ewa ka yanke kayar alhaji, dan ALLAH kayi hak’uri kaji”.
Jawota yayi jikinsa ya rungume yanamai saka mata albarka da aminta da buk’atarta na kiran senator halluru da safe insha ALLAH.
Innarmu tamasa godiya itama.

**********

“Babyna wai mike faruwane haka?”.
Da gyar Munubiya ta d’ago ido daga kwancen datake a kujera ta kalli yaa Marwan dake mata tambayar.
Ta shagwa6e fuska tace, “wlhy Yaya jikinne babu dad’i, kamar jiya sai kwankwatsa kasusuwane keyi”.
Zama yay kusada ita, yad’ago kanta ya jinginata a jikinsa yana ta6a wuyanta, “please ki yarda muje asibiti adubaki mana?”.
“a’a dan ALLAH Yaya, wlhy banason zuwa, kabari muga kwana biyu idan bai dainaba saimuje d’in”.
“Amma kuma k’ya zauna da ciwo, ki daure dai, kinga ko abinci kin kasa mana fa”.
“babu damuwa Yaya, yanzu zan tashi na d’ora, dan zazza6inma ya sauka ALLAH”.
“Ana dai so aima Yaya wayo kawai”.
Murmushi tayi tana tashi daga jikinsa,, takama hannunsa ta sumbata sannan tatashi tafice daga falon.
Binta kawai yay da kallo yana murmushi, yana k’aunar matarsa kuma ‘Yar uwarsa, gaba d’aya Munubiya ta canjashi, dukda bawai miskilancinsa yabariba, itace kawai yanzu baya iyama miskilancin nasa, komai a d’auren da fuskarsa take da zarar ya tunkaro gida zakiga yafara sakin murmushi, balle yay tozali da fuskar tauraruwar nan tashi mai haske da kawalwalniya a zuciyarsa.
Mik’ewa yayi yabi bayanta zuwa kitchen d’in danya taimaka mata da aikin, dan yau d’in weekend ne baije aikiba. dan yayi resume tun last week.

((?))*((?))*((?))*((?))

Tunda na idar da sallar nazame a wajen na kwanta, bawai barcin nakeba, jikinane kawai da baya min dad’i, jinake kamar ana kwankwatsamin kashin jiki, sallamarsa tasakani d’ago ido na kallesa, sannan na amsa ciki-ciki nima.
Frigate ya bud’e ya d’auki ruwa yakoma saman sofar ya zauna, murfin kawai ya 6alle ya hau kwankwad’a, saida ya shanyeshi tas sannan ya ajiye goran yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. nikam na k’ura masa idanu nakasa janyewa. saida yad’ago muka had’a idanu sannan nayi saurin yin k’asa da nawa.
Shi bai janyeba yana kallona yace, “tashi muje hospital d’in, daga nan saimu samo zam-zam d’in”.
Tunkan yakai k’arshen maganarma na mik’e tsaye, hijjab kawai nasaka nad’an gyara fuskata, shikuma ya d’auki kaya yashiga bayi ya canjo sannan muka fice.
Jin gidan shiru yasashi d’aukar waya yakira sashen bayin gidan, babu dad’ewa saiga d’aya acikinsu tazo.
Zubewa tayi tana gaishemu, ya d’aga mata hannu yayinda nikuma na amsa. yace, “ina Samha?”.
“Ranka ya dad’e sunfita suda mummy”.
Yasan aunty Mimi take nufi, dan haka bai sake cewa uffan ba yafice abinsa. sai nice nace tatashi taje, sannan nabiyoshi abaya.
Sai da yasakama k’ofar security sannan muka nufi wajen motarsa, bayin dake zaune a harabar gidan maza sukazo da sauri suna gaishemu, hannu kawai suma ya d’aga musu muka shiga motar, suka bud’e mana gate d’in muka fice.
Tunda muka fita babu Wanda yay magana tsakanin ni da shi, yana aikin tuk’insa da sauraren redio daya kunna a motar, nikam ina lafe a kujera ciwo ya isheni, dan bana fahimtar yaren dasukeyi a redio d’in, tunda ba English baneba gaskiya.

Mun Isa wani babban shagon Islamic camix, komai zaka iya samunsa daya shafi maganin muslinci.
Abinda ya kaimu muka shigayi, yad’ebo zam-zam dayawa, sannan ya kalleni yana fad’in “saikuma mi?”?
Shiru nayi ina nazari. Dame yakamata muk’ara?, zuwa can nad’an hau duddubawa ina karanta sunayen magungunan ajikin kwalin, duk maganin danaga zai iya shafar jinnu ko sihiri, saida na d’akkoshi, (a tunanina idan mun dawo gidan zan d’auki hotunansu na turama Munubiya ta bincikamin yanda yadace ayi amfani dasu.
Duk abinda nake yana a tsaye yana kallona, saida na kammala sannan nasanar masa na gama.
Mun k’arasa wajen biyan kud’i, bayan yabiya yaran shagon d’aya ya d’aukar mana zuwa mota.

Daga nan asibitin muka nufa, mun tarar har lokacin Abie yana barci, sai gaisawa nukayi da momma da aunty Mimi, duk sunji dad’in yanda sukaga Galadima cikin nutsuwarsa. Zama yay kusada Abie yana mai tsurama masa idanu da masa addu’oi samun lafiya a zuciya, da kuma kudirar binne Wanda ya cutar masa da mahaifi da ransa idan ya kamashi a hannu.
Momma tayi farinciki da yanayin Galadima d’in cikin k’oshin lafiyarsa, dan da a dane da yanzu shima yana gadon asibitin, amma Alhmdllh yanzu gashi normal.
Mukam ni da Samha muna gefe zaune muma, ba hira mukeba, kowa yayi shirune yana tunanin duniya.
Sauban ma yana dawowa daga school shida Khaleel nan suka taho.
Bamu bar asibitinba sai dare, harda Momma muka wuce, dan yau suna buk’atar Abie ya kwana tare da ma’aikatansu.

Koda muka shigo Galadima sama ya wuce abinsa, ganin haka Momma tace natashi na naje nima na kwanta na huta hakanan.
A kunyace na mik’e domin cika umarninta.
Na iske yana cire kaya, dan haka nakoma da baya zuwa falo, saida na kintaci yagama sannan na shigo, na iskeshi yashiga wanka, nima natu6e nawa na d’aura zani nasaka hijjab tareda d’aukar kayan barcina ina jiran fitowarsa.
Bai dad’eba sosai kuwa yafito, sanye yake da bathtub fara tas, ban yarda na kalleshi ba natashi nashige nima.
Mai makon yayi shirin barci saiya kwanta a bakin gadon a haka, k’afafunsa na k’asa, ya tsurama rufin d’akin idanu alamar yatafi duniyar tunani.
Nikam ruwa mai zafi na had’a nashiga koda zanji dad’in jikina, na dad’e acikin ruwan kwance, jinakema kamar karna fito. shikansa yafara tunanin lafiya kuwa?, lokaci-lokaci yakan kalli k’ofar bayin, Amma babuni babu dalilina.
Yana shirin zuwa yamin knocking sai gani nafito kuma, janye idonsa yayi daga saitin k’ofar cikeda basarwa.
Ni bammasan yanayiba, dama nayi shirin barcina tun aciki, saina d’auki zani na d’ora a saman kayan nasaka hijjab nayi sallar shafa’i da wutiri, bayan na idar nad’akko roban zam-zam d’in d’aya na zauna nafara karatu Qur’an acikin ruwan zam-zam d’in. a hankali nake karatun cikin nutsuwa, dukda barcin dakecin idona.
Har cikin 6argonsa da jini yakejin sautin karatuna, ya lumshe idanu yanamaijin kamar mu kwana a haka inayi. mik’ewa yayi shima yayo alwala yazo yay shafa’i da witiri yay joining d’ina muka cigaba da karatun a tare.
Bamu kwanta ba saida mukayi sallar asubahi. (da yake sai zuwa 1 zasu bari ashiga wajen Abie, yau kuma babu aiki).

____((()))((*((()))*))((()))____

Yauma dai haka innarmu tadagema abbanmu saida yakira Senator Halluru agabanta, dan Zarah tana kwance babuma lafiya, ga mamansu Yaa Hameed ita kanta kallo d’aya xaka mata kagane abirkice take.
Innarmu duksai suka bata tausayi, matan gidanmu kuwa abin magana yasamu, sai gulma da dariyar gatsatsa, ita kanta Momy Hadiza ta hannun damar mamansu yaa Hameed d’in dad’i takeji, tanadai nuna damuwarta agaban mamansu Yaa hameed d’inne.
Bayan Abba sun gaisa da Senator halluri sukad’anyi barkwancinsu na abokai sannan yasakko xancen Zarah.
Hankalin Senator halluru yatashi, danshi koda wasana baisan Zarah bata nanba, yadai lura kullum Sa’eed saiyaje gida yaci abinci, shi duk zatonsa Zaran bata iya girkine saboda ciki.
Hak’uri yashiga bama Abbanmu yace wlhy shi baima saniba, amma insha ALLAH zai bincika, zuwa dare sa’eed d’in zaizo ya d’auki matarsa.
Dahaka sukai sallana da Abba kowa nakuma bama d’an uwansa hak’uri akan lamarin.
Innarmu bata buk’atar jin k’arin bayani dantaji komai, takumaji dad’i sosai.

()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()

Jikin Abie dai kam yayi tsanani a tsakaninnan, yau kwana biyar kenan lamarin sai addu’a, dan baisanma Wanda yake a kansa ba, mai martaba Sarki Abdul’fatah ma yazo shida inno matarsa, (wannan ne karon farko dana gansu ido da ido), mutanen kirki masu d’aukar kowa nasu, duk da d’ar-d’ar danai tayi haka sukaita jana ajikinsu. yanda Galadima yake zubama inno da papi shagwa6a sai abin yaso bani dariya, amma dai sun birgeni, mu a gidanmu wazaima innaro wannan ta6arar bata k’arema uwarsa tanadiba, ba kamarma mu ‘yan d’akinmu.
hakama sarki jalalludden shida uwargidansa sunzo da mama Fulani.
Ranar momma har tausayi tabani, kai mama Fulani batada kirki wlhy, idan kunga yanda take shinfid’a mulki a asibitin nan. Hummm??????.
Galadima ne kawai maganinta, tamasa magana ya dage ya ya6a mata bak’a shikuma.
Ba gidan suka saukaba, a hotel suka sauka, dan haka yau mun iskesu a asibitin sun rigamu zuwa.
Tunda muka shigo mama Fulani ta zubamin ido, Galadima ya gaida mai martaba da matarsa yakoma kusada Abie ya zaina.
Nima k’asa na durk’usa na gaidasu su dukansu har Momma da aunty Mimi.
Momma ta nunamin kusada ita alamar nazo na zauna kusada. banyi musuba naje na zauna, dan kallon k’urillar da Mama Fulani kemin duk sai na takura.
Tad’an ta6e baki sannan ta gyara zama idonta na kaina, tace “toke amarya halan saikin tashi haihuwa zaki koma mana? daga zuwa dubiya kuna Neman share wata 1 a india”.
Gaba nane yafad’i, dan nafahimci dani take, saina rasa amsar dazan bata..
‘Yan d’akin kam kowa ido ya zuba ma mama Fulani har Galadima.
Aunty Mimi ce tace, “Ranki yadad’e Kodai kina Kishine haka? Amarya ta kwance Miki fada wajen mai gidanki?”.
Ajiyar zuciya Momma ta sauke a hankali, taji dad’in yanda aunty Mimi ta mayar da maganar wasa, ko nad’an batason abinda zai munana Munaya ko muzantata, dan bataso yarinyar taji kamar ita dabance a cikinsu………
Wani munafukin murmushi mama Fulani tayi, ta kalli Galadima da zuciyarsa tafara hasala akan tsohuwar, kamar daga sama sukaji tace, “cikin namu wata nawane Galadima?”…………???

E me???? mama Fulani mai gani har hanji??????.

*_ALLAH ya gafarta na iyayrnmu??????_*
*_Typing??_*

*_Haske writer’s asso…._*??

*_?RAINA KAMA……?_*
_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull Ce_*????

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply