Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 26


Raina Kama Book 1 Page 26
Viral

?2?6?

……….Da kuka na farka, duk da naji dad’in jikinna kuwa, dan banajin azabar kamar jiya, tashi nayi zuwa toilet danna d’auro alwala, na tuna labarin da wata k’awarmu ta ta6a bamu akan yanda taita ciwon jiki, saida mijinta yata mata ruwan zafi a ranar, ruwan mai d’an zafi na had’a na shiga ciki, nasha zafi kuma naji dad’i, amma inajina kamar ba a dai-daiba maganar gaskiya, haka dai nasamu nayi sallar asubahi, ina tsaka da sallar yashigo da nufin tadani, ganin na tashi ma saiya juya yafice abinsa zuwa masallaci shima.
Koda na idar kwanciya nayi saman abin sallar nacigaba da kuka na, ina kuma tunano abinda yafaru a jiya tamkar a films ko novels ko mafarki, babu abinda zuciyata keyi sai tsinemar, a yau d’inan dolene saiya bani Sakina natafi gidanmu, nafasa auren Contract d’in ma, da dai na zauna da mugunnan gwamma nakoma gidanmu nacigaba da rayuwa dasu innaro yafimin….

Tun d’azun yana tsaye a kaina, tausayina yakamashi, dan yasan shine silar kukan mawa, bayason zalunci ko kad’an, amma saigashi shine da aikatawa kuma, zama yayi a bakin gadon, cikin muryar nan tasa mai kama da anmasa tilas yace “tashi zaune muyi magana”.
“baza na masa, a zuciyata nace bazan tashiba mugu kawai, bakada abinda zaka fad’amin na yarda, azzalumi, dama abinda ka shiryawa rayuwata kenan? Dan kaganni d’iyar talakawa banida k’arfin gogayya da kai, tabbas nayi kuskuren yadda da Wanda shikansa ma bai gama yadda da kansaba, ALLAH ya Isa wlhy tunda ka ketamin mutunci har abada bazan yafe makaba, kullum cikin sallata saina sakoka da neman sakkaya ga mahaliccina akan zalincin dakami………
A fili kuma nace, “kagama zalintata kazo kanamin mazurai da mulki, ank’i tashin”. a hankali nake maganar banyi tunanin yana jinaba, sai tsawa kawai naji ya dakamin
“k!!!!!”.
Yafad’a cikin daka tsawa, Ashe tunda nafara maganar ya rumtse idanu saboda yanda Kalmar zaluncin suke sukarsa a zicciya, ban ta6a ganinsa a wannan yanayinba, a cikin fad’a yace, “Niba azzalumi baneba, zina nayi dakene!? dazaki dunga aibantani damun duk furucin dayazo bakinki? to bara na tuna miki idan kin manta, SADAKI na biya na auroki! tun jiya kike fad’an magana amma na shareki, ni sa’an kine? wlhy idan bakiyi wasaba zan koya miki hankali! danaso muyi magana ki saurareni mana kiji mizance?………”
Zumbur namik’e zaune, duk da azabar da k’asana kemin, na kallesa ido cikin ido ina zubda kwalla nace, “bakada abin fad’a shiyyasa bazan saurarekaba, bar ganina ‘Yar talaka bana d’aukar raini wlhy, mina maka ne? miye had’ina da kai kaketa bibiyar rayuwata da bala’i, tunda na had’u da kai ban kuma samun nishad’iba, wlhy bazan yafe makab…….
Jikake bamm! ya make bakina da bayan hannunsa, cikin zazzaromin ido yace bazaki nutsuba Ashe?”.
Naji zafi sosai, dan haka nafashe dawani marayan kuka mai ban tausayi, ga wani bala’in tsoronsa daya kuma shigata, maganar ma a tsorace dama nayita, Dan tsabar bala’i na hango cikin idonsa Dana kallesa.
Kansa ya dafe da hannu, jiyake tamkar ya tariyo jiya a rayuwarsa ya goge dukkanin abinda yafaru
Ganin bazan sauraresan ba da gaske saiya tashi ya fice yabarmin d’akin.
Nakuma 6arkewa da kuka.

Koda yafita a falona ya zauna, ya dafe kansa daya koma masa ciwo k’asa-k’asa yau, tunaninsa yafara komawa baya daga jiya zuwa yau, shin miya sakashi wannan matsananciyar sha’awar ne wai? dan bai ta6a jin makamancin feelings irin na jiya ba, da sauri yamik’e yanufi sashensa, a falo ya tsaya, ya d’auki kwalin hollandia fresh milk d’in jiya yana dubawa, shi dai yasan shine last abu daya sha a jiya, to kenan koma miye daga cikinsa yake?. to amma ai ba yaune yafara shan fresh milk ba a gidannan balle yace kuma shine. kwalin ya ajiye yakuma dafe kansa, gaba d’aya tunaninsa ya kulle, dama shi indai yana cikin 6acinrai to komai nasa birkicewa yakeyi, dolene saiya kwantar da hankalinsa zai iya kamo bakin zaren. a kujerar Yakoma ya kwanta, ko azkar yakasayi yau, babu dad’ewa barci yakuma kwasheshi anan.

Itama Munaya daga kuka barci yay awon gaba da ita a wajen.
Har Samha suka kawo abinci duk barci suka Tatar sunayi, tasan halin Uncle Sam shiyasa bata tadasu ba, kad’an daga aikinsa ya mammaketa a safiyarnan.
Su duka sai wajajen 12 suka farka, kowanne yatashi da damuwarsa.
Tunda nayi takun farko nakuma tabbatar da akwai matsala, dan ruwan zafin da yaymin jiya kad’ai ya isa na daina jin zafinnan irin haka, balle kuma nima nayima kaina da safennan, amma maimakon k’asana yabar zafin saima zugi yake k’arawa, gashi idan nashiga ruwan, zafi nakeji sosai.
Yanda nake takawar ina hawayene yabashi mamaki, dan aganinsa yakamata nasamu sukuni saboda yanda yamin jiya. bansan yashigoba, maganarsa kawai naji..
“Wai mike faruwane? Ko dai kinji ciwone?”.
Wata uwar harara dataso bashi dariya na zuba masa, amma saiya danne baiyiba, takowa yayi har inda nake yakama hannuna na fisge, ya d’aure fuska shima yana hararata, “k! Wlhy kinutsu kafin na canja miki kamanni”.
“yo kammani na yaushe kuma zaka canja min? bayan Wanda ka canja min yanzu? dama haka kake? a fuska kamar babu ruwanka amma sai zalunci taf zuciyarka”.
Idonsa ya runtse dan bayason Kalmar zaluncin nan danake jifansa dashi, jinai kawai an fusgoni an zaunar a bakin gadon, nakuwa fashe da kuka ina fad’in “wayyo zafi, munubiya Azalumin nan zai kashe miki ni”.
Ko kallona baiyiba yafice, ina nan ina kuka saigashi yadawo da wayarsa a hannu, ya zauna saman sofa batareda ya kalleninba, bashida mafita saita kiran Akash, dan yanason sanin minene matsalar datake sakani wannan kukan da complain d’in zafin, yasan koya tambayeni ba fad’a masa zanyiba..
Da turanci suka gaisa, amma da zaiyi tambayar saiya canja harshe zuwa yaren daban saniba.
Akash yace saidai idan ciwo taji, dan bai kamata ace tana Complain zafi irin haka ba, zataji ciwo kam amma bawai yanda yake nuna masa yanzun ba.
Galadima ya gyara zamansa sosai yace “to ai na sanar maka fyad’e akama yarinyar fa”.
Akash yace “zata iya kai shekara nawa yarinyar?”.
‘Dago ido yayi ya kalleni kafin ya janye yana fad’in “Maybe 19years ko 20 kawai”.
“ai bama yarinya baceba can sosai, inaga taji ciwone gaskiya, yakamata doctor ya dubata gudun samun matsala, amma kabada gudunmawa a hukunta Wanda yay abunnan my man, please ka kwatarma yarinyar hak’k’inta wajen azzalumin nan”.
lips d’insa kawai ya cije maganar Akash na sukar zuciyarsa, da Akash yasan shine yay aika-aikar dabai ce hakaba. sallama sukayi ya yanke wayar, saikuma yafara tunanin doctor d’in dazai nemo ya dubani, dan bashida damar fita dani a gidan yanzun.
Can doctor Hafsat ta fad’o masa a rai, ita kad’ai zai iya aminta tasan matsalarsa, dan ya yarda da ita sosai, yasan zata masa k’yak’yk’yawar fahimta.
Kiranta yayi bayan sun gaisa cikin mutunci ya fad’a mata matsalar ta yanda zai iya, dukda ya 6oye mata wacece keda matsalar ta fahimcesa, d’an murmushi kawai tayi tana girgiza kai da tausayin yarinyarnan data shiga hannun Galadima, duk abinda zata buk’ata tagama had’ashi sannan ta fito, matsalar gidansu data Sani yasakata yin shiri tamkar ba doctor ba.
Shiru d’akin yayi, sai kukana dayake fita a hankali, shikam ya zubamin idanu yana kallona k’asan ido, zaune yake k’afa d’aya akan d’aya, ya jingina da kujera, saika rantse idonsa a rufe yake, amma yana kallonane ahaka.
Bayan doctor Hafsat tazo k’ofar fada saita kirashi, dan baza’a barta kai tsaye tashigaba.
Ina kallonsa ya fice bayan ya yanke wayar daban San dawa yakeyinta ba.
Kusan mintun 20 saigasu sunshigo dawata mace, ba yarinya baceba can gaskiya, zasu iya zama sa’anni da Galadima d’in, dan haka na tashi zaune na gaidata cikin girmamawa.
Ita kuma ta amsa cikeda fara’a.
Kallon Galadima tayi dayake tsaye yana kallonmu, “ranka ya dad’a kozaka bamu wajene”.
Murmushi yad’anyi yana fad’in babu damuwa.
Yana fita matar ta zauna kusa dani a bakin gadon, fuskarta d’auke da murmushi tace, “sunana doctor Hafsat Abu, friend d’in Galadima ce tun a primary school”.
Murmushi nayi mata na yak’e kawai.
Takuma gyara zamanta tana kallona, please dear karkiji nauyina, ki fad’amin matsalarki kai tsaye, dan ba’a wasa da wannan matsalar, takan zama babban Abu anan gaba ga d’iya mace”.
Kai na jinjina mata ina hawaye, sannan nace “inajin zafin wajen sosai”.
“ok kozaki iya kwanciya nagani”.
Ido na waro waje a tsorace, sai kuma nayi k’asa da kaina saboda kunya.
Tayi murmushi tana kama hannuna, “karkiji kunya akan lafiyarki dear, please ki daure kinji”.
Kai kawai na gyad’a mata sannan na kwanta, babu yanda zanyi dole na yarda ta duba, kanta kawai ta girgiza da mamakin Galadima, saikace Wanda ya kusanceni da k’arfin tuwo?, ai wannan kam da wani doctor d’inne saiya yima Galadima fad’ama wlhy, dan ko kad’an bai bini a hankaliba, amma ciwon daya jimin bazai zama mai cutarwa ba insha ALLAH.
da kanta yanzu ta had’amin ruwan zafi tazuba wasu magani, sannan ta taimakamin har zuwa bayin ta nunamin yanda zanyi. ban cutar da kainaba na nutsu nayi komai yanda tace, dukda inajin zafi kuwa, bayan nafito saina sameta zaune ta gyara gadon tsaf, gakuma abinci a ajiye, da alama Galadima ne ya kawo, tsareni tayi da lallashi naci abincin ma yanzun, sannan tabani magunguna nasha, ta kalleni da murmushi, “ALLAH yak’ara lafiya gimbiyarmu, indai zaki cigaba da kulawa kamar yanda na nuna miki insha ALLAH nan da 2days zaki dawo normal, ga drugs d’inan saikina sha, shima wannan cream d’in kina matsi dashi awajen a koda yaushe”.
Kaina na jinjina mata sannan nace “ nagode Aunty”.
Sallama tamin tafice.

A falo ta iske Galadima, bayan tamasa bayanin yanda yakamata a kula dani saita kallesa cikin tsokana, “ranka ya dad’e kafayi 6arna gaskiya, Shifa wajenan ba a nuna masa k’arfi, please a kiyaye”.
Murmushi kawai yayi baice mata komaiba.
rakiya yamata tareda mata alkairi sannan yadawo.
A kwancen data barni ya iskeni, zama yayi gefen gadon yad’an kalleni ya janye idonsa “yaya kikeji yanzun?”.
Baki na turo masa, amma ban tankaba. shima bai damu da amsawar tawaba, ya basar kawai ya d’akko wata maganar.
“nasan babu abinda zan fad’a ki yarda dani tabbas, sai dai zankuma maimaita miki SAMEER BAYA ZALUNCI, koda wasa ban ta6a kawo zan aikata hakan agarekiba har kibar k’ark’ashin kulawata, bansan miya shiga kainaba a jiya”.
Kallonsa nayi ina hawaye da takaicin maganarsa, nace “bakasan miya Shiga kankaba ka d’auki fresh milk kabani? bayan kasan mika zuba”.
Shima kansa ya d’ago yana kallona, cikeda k’asaitarsa yace “ban fahinceki ba, mikike nufi? dan ina son na kusance ki sainayi amfani da wani abu? da hakan naso daret zanzo gareki tunda nasan nabiya sadaki ai, tunda ba tsoranki zanjiba ko?”.
“dama ai bazaka fahimceni ba tunda Kasan ka aikata ai, kuma ai alk’awarin zama tamkar abokai kamin ba irin wannan ba”, na had’e hannuna alamar roko???? ina kuka nace “dan girman ALLAH ina rok’onka kabani Sakina a yau natafi gidanmu, wlhy nafasa auren Contract d’in, koma waye yayi abun ni na yafe masama, kawai ka sallameni”.
Yama rasa mizai cemin shi, ajiyar zuciya yad’an sauke, kafin ya cije lips nashi, “shikenan, zan miki yanda kikeso, amma kibari ki warke, bai kamata ki koma gida ahakaba”. ‘yana gama fad’ar haka yatashi yafice batareda yaji amsa taba.
Duk da naso yabani sakina a yau, amma zanyi hak’uri na warke d’in kwana nawane.

******

Yinin yau haka mukayishi duk zukatanmu babu dad’i, Galadima kam ai ciwon mara saiya nemi dawo masa sabo, jiyayi kawai yana sake buk’atar kasancewa dani, haka yayta dannewa har zuwa dare, dan bazai kuma yarda yin gangancin nanba. ganin yana neman mutuwa yay shiri a gaggauce yafito domin zuwa hospital.
Tunda yafito suke zubewa gaisheshi, hannuna kawai yake iya d’aga musu, dan kallo d’aya zaka masa ka tabbatar yanada damuwa, da sauri sarkin mota yazo yabud’e masa ya shiga, suma dogaran dakan bisa idan zai fita sai duk suka taso.
Tundaga fitarsu gidan Muftahu na kallonsu, yad’an murmusa kawai abinsa. (??wlhy Reader’s suka kamaka zaka gane bakada wayo??)

Shi kad’ai yasan azabar dayakeji a jikinsa, yana kwance cikin kujerar ne sai faman cije lips yakeyi.
Tunkan sarkin mota ya tambayama ya sanar masa asibitin da zasuje.
Sarkin mota ya amsa cike da girmamawa da tausayin shugabansa, dama shi tunda yaga yafito ya fahimci akwai matsala.
Tun amota yakira wata number yana tambayarsa ko yana asibiti?. Dr Jalal ya amsa da eh yana nan.
Yanke wayar yayi kawai baisake cewa komaiba. Dr jalal yabi wayar da kallo yana mamakin Galadima da halinsa, kiransa yakuma yi shi dan bai fahimci inda maganar tasa ta dosaba. sai dai harta yanke bai d’aukaba, yana k’ok’arin sake kira yaji ana Knocking d’in k’ofar.
Amsawa yay da yes tareda izinin shigowa.
Wani dogari ya bud’ema Galadima k’ofar yashiga, da hanzari Dr Jalal yamik’e yana murmushi da masa welcome.
Hannu kawai ya iya d’aga masa ya zauna kujerar gaban decks d’in.
Shima Dr jalal saiya zauna, “ranka ya dad’e lafiya dai ko?”.
Saida yaja wasu Seconds sannan yafara ma Dr jalal bayanin damuwarsa, ya sanar masa mararsa namasa ciwo tun jiya, kuma ada bata masa kamar hakan.
Shiru Dr jalal yay yana nazarin maganar tasa, saida yakai aya sannan yace “ranka yadad’e kokasha pills ne?”.
Kallonsa Galadima yayi, “pills kuma? wane irin tambaya kakemin haka?”.
“afuwa ranka ya dad’e, matsalar taka tayi kama da wanda yasha tablet ne, mikaci na k’arshe jiya?”.
cikeda nazarin maganar Jalal yace “fresh milk ne last abinda nasha jiya da daddare”.
“to amma bayan shi kafara jin matsalar?”.
“kusan haka gaskiya”.
Dr jalal dai shiru yayi, dan ya tabbatar wannan aikin desire tablets ne, amma koya fad’a dawuya Galadima ya yarda, sai kawai yashare ya had’a masa drugs da injection yamasa, yace yad’an kwanta na kamar 20 minutes a office d’in. bai musa masaba ya shiga inda jalal kan huta idan yaso, saiya kwanta kawai, dan shima bazai iya tafiyarba, d’akin ma da taimakon jalal d’in yashigo.
Ni bansan hidimar da akeyiba, dan rabona dashi tun bayan munyi maganar saki, abinci ma tun Wanda doctor tabanine a cikina, sai kusan 8 Samha takawo min kayan fruits dawani Abu mai dad’i daban san mineneba??.
Ta zauna mund’anyi hira kafin tafice. a bakin ta nakejin wai jibi Friday zasu koma India.
Na danci abinda takawo nasha magani nayi kwanciyata cikeda kewar ‘Yar uwata dana kanyi akowanne dare.

Galadima kam bai dawo ba sai kusan 1pm, yana shigowa sashensa yawuce yay shirin barci ya kwanta, Alhmdllh zuwa yanzu yaji k’arfin jikinsa, sai dai zuciyarsa nata cud’a masa tunanin ina yasamo pills? dan shima yafara yarda da maganar jalal, musamman idan ya tuno furucin Munaya na d’azun da safe.
To kenan wani ya zuba masa bai saniba? to amma wazai zarga shikam? duk wad’anda suka shigo wajensa a jiya amintattun sane, Sauban, Samha, Harun, Muftahu, duk sun shigo wajensa a jiya, amma Muftahu shine last shigowa, shiru yay yana nazari, can kuma saiya cije lips d’insa ya lumshe idanu yana shafa gurin Dana cijesa.
A haka barci ya kwasheshi.

????

Munubiya tashiga damuwa sosai akan rashin jina a waya, takira number ta yafi sau goma amma switch up, gashi yaa Marwan ya hanata kiran number dana kirasu a ranar, yace wai number Galadima ce bai kamata su damesa ba.
Haka taci kukanta a yinin ranar, saikace mara lafiya haka ta yini, zuwan su Ayusher ne ma yad’an sanyaya ranta har suka janye mata hankali da yawan tunani, a ranar gidan suka yini cir, sunsha hira da labarina, kowacce tana missing d’ina.
Sunce suna son zuwa amma an hanasu, wai gidan danake ba gidan da ake zuwa any how bane ba, babu yanda suka iya haka suka hak’ura.

*********

A gidanmu ma yau sukayi niyyar kawo min akwatinana da abinda ba’a rasaba, amma ankira wayata akashe, wannan yasa Abba yace abarni akaima su fauziyya nasu. ni daga baya idan an sameni akai min nawa d’in.
Duk inda akaje da innaro ake zuwa, kowacce ta taima gidanta kallon kwaf kenan, sotake taga gidan wacce tafi acikin sauran ‘yan uwana.
ALLAH ya taimaki munubiya lokacin dasukaje gidanta yaa Marwan yana gidan, hakama su Ayusher.
Fita yayi yasiyo musu abubuwa yakawo, sannan suka zuba musu girkin da sukayi, babu ko kunya suka mik’e kafafu suka ci abinsu, to dama gidan Fauziyya ne kawai suka samu sukaci abinci, su Safara’u kam casukai basu fara girkiba, dan ita haleematu ma ruwa wannan bata basuba, banda innarmu akaje, dayake kowacce idan za’aje gidan ‘yarta banda ita ake zuwa.
Zasu taho kuma yaa Marwan yabasu kud’in mota, dukda kuwa a mortar Dady yaa Anas ya kaisu.
Tunda suka dawo gida aka shiga labarin yanda aka iske gidan kowa, nanfa wad’anda gidan ‘ya’yansu ba’a samu wani abun kuzo aganiba sai suka fusata, kunsan dai halin jama’ar gidan namu??, wannan Abu saida yakawo rikici, fad’a sosai sukasha abinsu, itadai innarmu k’ala bata ceba, saima ta maida hankalinta ga girkin dare datakeyi, ga innaro sai habaici takeyi, saida gwaggo Safiyya tazo da k’yar ta lalla6ata tafita.
Matan anguwa makwafta kam sun masa kunne suna saurare da kwasar dariya, dan lamarin gidanmu yazama kamar na ‘yan wasan kwaikwayo.
Duk tsiyar dasukeyi dady yana gidan yana jinsu, amma ko lek’owa bai yiba, danshi bashida hayaniya ko kad’an, balle daya fahimci abin yashafi ‘yan bani na iya d’in gidan ne, dariya kawai yayi yace ALLAH ya k’yauta. kad’anma kenan ai, bakuga komaiba tunda yanzu kuka fara aurarwar, kuma har yanzu da sauran 6ur6ushin amarci ga yaran harsu Aunty khaleesa kam dake cikin watanni na hud’u da auren.

?????

Alhmdllh yanzu kam naji dad’in jikina, dan ko ciwonma banaji, sai shirye-shiyen kayana nakeyi dan yau nakeson tuna masa batun sakina, tun shekaran jiya rabona da ganinsa, harma na d’auka baya gidan sai d’azun da safe Samha take cemin ai tare suka fita itada Uncle Sam da Sauban birnin gayu da asibiti zagayen marasa lafiya, sune har Asibitin mahaukata, tace duk atsorace take ALLAH yasa kartayi mafarki.
Ni dariya ma tabani yanda take bani labarin kamar a firgice take.
Komai nagama had’ashi tsaf, Galadima kawai nake jira, amma abin haushin har kusan 4pm babu labarinsa, gani nayi zan zauna jiran gawon shanu, dan haka na mik’e zuwa sashensa.
Nayi sallama yafi 7 amma babu amsa, sai kawai natura na shiga, a zatona rainin wayonsane da mulkin ya motsa, babu kowa a falon sai wani k’amshi dake tashi na musamman, ko ina kuma need a gyare,, a yanda naga yanayin falon kamar babu kowa a sashen gaskiya, dan komai akashe yake har AC, dawuya kuma yana nan kaga AC n sa a kashe, duk da haka saina d’an zauna ina k’arema ko ina kallo, kai kace yau nafara shigowa, hotunansa da bana gajiya da kallo naketa kallo yanzun ma, idona nacikin zageye-zagaye saina hango wani k’aramin frame na photo, bana ganin mutanen jiki sosai dan haka namik’e tsaye, ga hoton na isa, yana a kusurwar d’akinne ta gabas, saman wani d’an katako da aka k’awata wajen, bayan foton akwai flower babba mai k’yau, sai aka jigina hoton jikin flower d’in.
K’yak’yk’yawan mutum ne ajiki Wanda kallo d’aya zaka masa ka hango tsantsar kamaninsa da Galadima, saikuma mace a gefensa itama masha ALLAH, Galadima kuma yana satar kamanninsa da ita, musamman idonsa ha6arsa dawasu abubuwa, saikuma wadda nake k’yautatama zaton aunty Mimi Ce kusada matar, shima namijin ina tunanin Galadima ne, yana cinyar mutumin, bazai wuce 5 to 6 years ba a picture d’in, Anty Mimi kuma bata wuce 10 ba, sai tsohon ciki ajikin matar, dukda ban saniba sainayi tunanin iyayensane, duk cikin kayan sarauta suke.
Samha ta fad’amin iyayensa suna india, Abbansa bashida lafiya, ban wani tambayeta komaiba, iyanan naji kawai.
Hoton na maida na ijiye ina murmushi, sun birgeni gaskiya sosai, flower d’in nabi da kallo, itama tamin k’au, gawani k’amshi mai dad’i datakeyi, kuma nalura da dare kamar tana wuta haka. Hannuna na kai na ta6a ganye d’aya ajiki, sainaji Ashe ta roba Ce ma, mamaki ya kamani, banyi zaton ta roba bace wlhy, dan tayi k’yau.
Har zan bar wajen, kamar ance na d’aga kaina saman p.o.p d’in ta jikin kusurwar sainaga tamkar CCTV camera, amma bakowa zai iya fahimtar hakanba, domin ansata cikin tsantsar kulawa, gabanane yafad’i, nayi azamar kauda idona tamkar ba ita nake kalloba, saina d’an gyara zaman flower d’in kawai nabar wajen zuciyata na tsitstsinkewa, toshi miye nawani saka CCTV camera a falonsa?, komawa nayi na zauna, zuciyata nawasu tunane-tunane daban.
Sai lokacin tunanin koma bayanan yazomin, abinda Nagano ya hanani lek’a bedroom d’insa, dan nasan zai iya ganin komai ta CCTV camera d’insa.
Sai kawai natashi na fice nakoma nawa d’akin………….???

Hum masu karatu kuna zaton Galadima bai fahimci Muftahu namasa zagon k’asaba kuwa???. kuduba yanda ya shashantar da binciken ya akayi yasha desire tabs a fresh milk??.

To koma dai miye kumuje zuwa, ai masu iya magana kance *Karshen alewa k’asa*??????.

Humm ya kuke ganin sakin da Munaya ta nema? Shin zata samu? kokuwa zai bita bazai bayarba???.

Kumuje zuwa dai a page nagaba my guys?????????????????

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*??????
*_Typing??_*

*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_

*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce????_*

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply