?2?0?
………A cikinmu Fauziyya ce babba, dan haka aka fara d’aura auren ta, daga nan sai ni da Munubiya, an fara d’aura na Hassana Auwal fharuk (munubiya) da yaa marwan Ibraheem, sannan ni Hussaina Auwal fharuk (Munaya) da Muhammad Sameer Saifudden Abubakar (Galadima), saikuma Safara’u, sai Haleematu, Fiddausice k’arshe.
Ana gama d’aurin auren busar algaitu suka fara tashi, sarkin marok’a yafara zuba kirari wa Ango Galadima sarkin gobe a masarautar gagara badau.
Maganar k’yawun da Anguna sukayi ma 6ata lokacine, kowanne yafito angonsa sak abin kallo da birgewar kowa, duk miskilancin yaa Marwan saigashi yana washe hakwara tamkar gonar audiga??.
??ance anguna basa kuka ranar aurensu, to kuwa yau saiga Galadima na share hawaye, dukda auren contract yayi nakuma shekara 1 kacal, saiyajisa wani iri daban, ya kuma zama babban mutum, tuno Abie dayayi yasaka hawaye fitowa daga idanunsa, bazai iya tuna tsawon lokacin dayayi kuka na k’arsheba, amma saigashi yau yanayi acikin d’umbin jama’a, akuma ranar d’aurin auren da ya rad’ama suna na (wucin gadi).
Papi ne yad’an bugi kafad’arsa yana murmushin jin dad’i shima, dajin wata k’aunar jikan nasa ta musamman.
Aikam masu videos da photuna ansamu abinyi, hakama masu d’auka awaya ba’a magana.
Kafin kace mi social media ta d’auka, lungu da sak’o hotunan d’auren aurenne suketa yawo, musamman da jama’a ketajin wai wadda aka bugasu a jarida yana kissing ce ya aura, wayyo ALLAH abin magana yasamu a yanar gizo, kowane polder na charts ka shiga zancen kenan dai.
Daga wajen d’aurin aure tawagar gidan su Galadima k’aton hall d’in da aka tanada domin cin abincin bak’i suka nufa, duk wani maiji da kansa zaka sameshi awajenne, Galadima har kansa yafara ciwo saboda yawan magana ta amsa gaisuwar jama’a da murna da yakeyi.
Ana tsaka da cin abincin Momma ta kirashi, dama shi ba ma abincin yakeciba, zaune kawai yake yana juya spoon a plate, wayarsa yaciro daga aljuhun gaban rigar milk d’in shaddarsa, dan tuni yacire malum-malun d’in tana hannun Harun.
Ganin Momma yasashi mik’ewa yafice daga hall d’in gaba d’aya, can waje yasamu wasu kujeru ya zauna sannan yakirata ta video call, tana d’agawa sai kawai ya fashe mata da kuka ganinta zaune kusada Abie.
daga Momma har Abie d’in sagade sukayi suna kallonsa, saida yayi mai isarsa yasaka handkerchief d’insa ya goge fuska sannan Momma tace “ho d’an nema duk murnar aurence kokuwa shagwa6a ce ta motsa?”.
Tur6une fusaka yayi zai sake wani kukan Momma ta kwashe da dariya irin wadda yadad’e baiga tayiba, Abie ma murmushin sane ya fad’ad’a sosai. saida Momma tayi dariyar mai isarta sannan tace, “Muh’d kafa girma, kai yanzu babban mutumne, nan kuma da wata shekarar kazama baba, amma katasamu gaba kana kuka?”.
Handkerchief yasaka yakuma goge hawayen dasuka taho masa, sannan yace “momma na barka da rana”.
“Barkan ka dai angon d’iyata Munaya, ALLAH ya sanya alkairi yabada zaman lafiya yasa bad’i iyanzu munan muna shagalin sunan jikan mai martaba”. tayi maganar tana kallon Abie daketa zuba murmushi, gira d’aya ta d’aga masa, shikuma ya k’yafta mata idanu.
Dariya Galadima yasaka musu, irin wannan soyayya haka summa manta dashi.
Gyaran murya yayi sannan Momma ta d’ago tana kallonsa, suka saki dariya lokaci d’aya. yayinda Abie ke tayasu da Murmushi.
Galadima ya tsagaita dariyar yana fad’in “my Abie ya jiki?”.
Da idanu Abie ya amsa masa da Alhmdllh, sannan yamasa nuni da ALLAH ya Santa alkairi.
Hannu yasa yarufe fuskarsa alamar jin kunya.
Har aka kammala liyafar cin abincin yana a waje suna hira da parent d’insa, saida papi ya aiko akirasa saboda yanason nunashi wa jama’arsa da basu sanshiba, hakan yabama wasu daga cikin ‘yan masarautar su haushi, sai dai basuda yanda zasuyi da wannan tsohon mai k’arfa-k’arfar tsiya da Nuna Isa.
Bayan ya Yanke call d’in yamik’e yabi bayan d’an Aiken, ya iske a hall d’in kuma papi ya had’a wani video call d’in dasu Momma, domin Abie yaga d’umbin jama’ar dasuka halarci d’aurin auren gudan jininsa.
Aiko yaji dad’i sosai harma Momma, harda hawayen farin ciki Abie yayi.
Nandai a kaita zuba masa addu’ar Neman lafiya ga mummunar addu’a ga dukkan masu hannu na shigarsa wannan halin tsawon shekaru, da idanu yake fad’ama Momma magana itakuma tana fad’a musu. Daga nan Galadima yayi jawabin daya ta6a zukatan jama’ar wajen, wasu harda share hawaye, wasu daga cikinsu dasuka San wasu abubuwan daya faru wa tsohon sarki Saifudeen kam duk sai zukatansu suka karye, musamman masu hannu aciki dasuka bada gusunmawa, jin addu’a da alwashin d’ansa Muhammad Sameer dake tabbatar da bazai bar duk mai hannu acikiba, sai dai shima amasa irin na mahaifinsa, hakanne kawai zai iya dakatar dashi.
Abie da Momma Kansu kuka sukeyi daga can suma.
Taron yatashi zukatan wasu cikeda tausayin Galadima da k’udirin taimakonsa, yayinda yasamu k’yaututtuka daga manyan k’asar.
Masu hannu aciki kuwa suntafi da nufin sake shiri akan Galadima d’in, domin aganinsu sunyi sake d’an zaki ya girma, kuma Galadima na neman zame musu *RAINA KAMA……*
https://2gnblog.blogspot.com/
???.?.?.???
Gidanmu kam tunda aka kammala d’aurin aure labari ya shigo gabana yashiga luguden daka, rungume juna mukayi ni da Munubiya muka fashe da kuka mai ban tausayi, Wanda muka saka jama’a dayawa kukan, ciki kuwa harda Innarmu da mama Rabi’a. babu wanda yace mu bari, aka barmu mukayi mai isarmu, dan kowa yasan dolene muyi irin wannan kukan na rabuwa, dan yau babu fashi dolene mu Rabun, abinda baita6a faruwa agaremuba, kullum a gado d’aya muke kwana muke tashi, kowanne aiki tare mukeyin sa, komai namu iri d’ayane, daidai da pants & bra iri d’aya muke sakawa, idan d’aya bashida lafiya saika d’auka muduka bamuda lafiyar, babu abinda ke banbantamu sai hali, amma yau gashi aure zai banbantamu, jinai inama muma mazane tamkar su Aiyaan, yanda babu mai rabamu d’in.
https://2gnblog.blogspot.com/
Haka dai wannan yinin biki akayishi a wani iri, mu cikin damuwar rabuwa, matan gidanmu cikin hassada da bak’in cikin mun fisu.
danma Su Abba sunyi dogon gargad’i akan wlhy duk wacce tasake tada finina a gidan sai dai ta k’arasa bikin a gidan su.
Wannan furucinne yasaka kowa yin likimo, sai dai fa ta ciki na ciki????.
Hotunama da akayi na family wasu fuskar tasu tamkar kashin farar safiya????, Innaro kam ai mune nagaban girarta a yau, sai dama-dama takeyi damu, dama komai akayi saitace an kaima Ai’sha dai ko, (??su innaro anga banza).
Wannan abun datakeyine keta kuma hasala matan gidanmu da ‘ya’yansu, itakam ko a ha6ar kallabinta, warkajaminta kawai takeyi na murnar auren jikoki.
Yayinmu mazane kawai babu ruwansu, duk suna cikin farin cikin wannan aure.
Bayan la’asar sakaliya saiga sak’o daga masarata mutane biyu d’auke da akwatina biyu wai sun kawo kayan da zansa awajen dinner ni da Munubiya, sun shirya dinner d’inne mu biyu kawai banda sauran amaren.
Wannan lamari kam ya sosa zukatan mutane da yawa, ni kaina banji dad’in hakanba gaskiya, dan banason su d’auka kamar mun banbanta da sune yanzun, gaskiya da ace inada Number Galadima dana kirashi nace a fasa wlhy, saboda muma anan gidanmu yayunmu sun shirya mana dinner d’in gaba d’ayanmu, duk da ni dama ban saka ran zuwan Galadima ba a wajen.
Gashi kuma gate pass guda 30 kacal suka kawo, alamun basa buk’atar mutane dayawa a wajen kenan, ikuma na nace inhar bada sauran ‘yan uwana ba ban zuwa nima d’in.
Lallashin duniya anyi nak’i sauraren kowa, nakafe akan bazan jeba.
Matan gidanmu kam cewa sukayi munafurcine kawai.
Zancensu bai dameniba, nidai ina akan bakana bazanjeba. su Ayusher sun rasa yanda zasuyi dani, dama akwai number Galadima saisu kirasa su sanar masa halin da ake ciki.
Innarmu kam ko k’ala batace daniba, yitaima tamkar batasan mi akeyiba, mama Rabi’a da Aunty Salamah sai fad’a sukemin kamar zasu dokeni, hakama innaro, sai jaraba takemin harda dungure min kai.
cikin ikon ALLAH kuwa ana cikin haka saiga kiran Samha yashigo wayata, Ayusher ta d’auka suka gaisa, azaton Samha nice, saboda muryar Ayusher ma tana kama da tamu. Tace, “Aunty gimbiya ya hidima?”.
Murmushi Ayusher tayi danjin sunan nawa harya canja, tace “ba ita baceba Ayusher ce”.
Cikin jimami tace Aunty gimbiyar fa?”.
Labarin komai Ayusher tabata, sannan tace “dan ALLAH ko zaki had’ani da Galadima?”.
Samha tace “babu damuwa bara na dubashi, duk da nasan yana tare da abokansa yanzun”.
Godiya Ayusher Tamata sannan suka yanke wayar akan idan tagansa zata kira”.
Masifa nahau yima Ayusher akan miyasa zatace saita fad’a masa, nidai koma miye babu inda zanje.
Banza Ayusher tamin tamkar batasan inayi da itaba ma.
Kusan muntuna 7 saiga kiran Samha yasake shigowa, Ayusher ta d’aga, maimakon taji muryar Samha saitaji ta Galadima cikin k’asaitar nan tasa da izza.
Nutsuwa Ayusher tayi sosai ta gaisheshi, sannan ta masa bayanin komai.
uffan bai ceba saida ta kai ayar zancenta, lips d’insa yad’an cija kafin yace “had’ani da ita”.
A kunne Ayusher ta sakamin wayar, yayinda kowa yafice daga d’akin aka barni ni kad’ai saikace wata mayya.
Dagani har shi kowa yayi shiru, shi yanajin kansa nima hakance, kusan minti 4 yaji banida niyyar tankawa saiya yi guntun tsoki, “shin ke baki iya gaisuwa bane?”.
Dukda naji ban k’yautaba saina ta6e baki, cikeda dakiya nace, “ina yini”. muryata a dishe take saboda kukan danaketa sha tun jiya.
Bai amsa gaisuwarba yace “wane sak’o kika bada a bani?”.
Saida na tunzuro baki sannan nace “yoni minace abaka?”.
Lips d’insa ya lasa yana fad’in “nikikema wannan abun?”.
Banza namasa danni bansan mina masaba kuma.
Yaja guntun tsoki, “ki kama kanki fa, karkiga auren contract mukayi, akwai sharid’d’a acikinsa, bana buk’atar ganin kowa awajen inba keda sister d’inki ba, haka na tsara, kuma babu mai canjamin ra’ayina, zuwa anjima wadda zata shiryaku zatazo, idan kin gadama karki bari a shiryaki, nikuma zakiga mi zan yi akai..”.
d’if ya katse wayar, cirota nayi daga kunnina ina dubawa tamkar zan ganoshi acikinta. naja tsaki ina fad’in “aikin banza kaje ka koyo R sannan kamin wannan ikon, nifa baka isa takani ba acikin auren contract…… ”
Sauran maganar ta mak’ale a mak’oshina saboda shigowar munubiya.
Zama tayi akusa dani, “sweetheart zan iya neman alfarma a wajenki?”.
Kai na d’aga mata.
Ta gyara zamanta sosai tareda kamo hannayena duka acikin nata. “inason kima mijinki biyyay kiyi yanda yakeso, yanzu hakkin bin dokarsa tarataya a kanki dole inhar bata sa6ama addini ba, kina kaucewa kuwa zaki had’u da fushin ALLAH, tunda yace haka yakeso ayi kiyarda kawai, awa nawane anyi an tashi kowa yakama gabansa”.
Alk’awarin Dana mata yasani amincewa zanje tilas amma badan raina yasoba.
An tsara wad’anda zasuje, dan haka aka damk’ama kowa gate pass d’insa a hannu ya Adana. dukda wasu gani kwaf zasuje kuwa.
Bayan sallar isha’i saiga masu mana shiri sun iso, babbar magana wai d’an sanda yaga gawar soja.
Jama’a ni kaina bamma gaskata cewar nibace ballan tana Ku ‘yan kallo, saika rantse kace dama can mud’in jinin sarauta ne, munyi k’yau har mun gaji, gashi dandanan akayi aka gama, har kusan 9pm muna jiransu, gidan yayi tsitt duk wad’anda zasuje dinner sun tafi, wad’anda zasu bimune kawai tare damu muna jiransu Galadima, dan shima yaa marwan d’in baikai ga isowaba.
Sai around 9:15pm sannan mukaji dirar mitoci a k’ofar gidan.
Aunty Mimi ce da kanta tashigo itada wasu bayi guda hud’u, saida ta gaisa dasu innarmu sannan aka mata iso d’akinmu, wani dad’ine ya ratsa zuciyarta, dukda batasan wacece matar k’anin nataba acikinmu, amma muntafi da imaninta, jitai inama natane wad’an nan twins, ALLAH yasa haihuwar farko na haifo musu irinmu.
Daga ni har munubiya rissinawa mukayi muka gaidata cikeda girmamawa, dan munsan a haife ta haifemu, dukda bawai sa’ar innarmu bace, ko mama Rabi’a ma ta girme mata.
Hakan damukayi yamata dad’i kuma mun birgeta, ta kama hannayenmu tana yaba k’yawun damukayi, wasu turarurruka ta fidso kala uku a bag d’inta tashiga feshemu dasu, dukda uban turaren da aunty salamah tamana wanka dasu zance, dan itama haka taita zazaga mana su d’azun, ni saima hawarmin kai sukeyi wlhy.
Wasu alk’yabbu masu azabar k’yau iri d’aya aka saka mana, takalman dake k’afarmu kansu abin kallone.
Aikam bamu fitaba saida tamana hotuna, afaloma saida aka mana muda su innarmu.
A waje muka iske motoci guda uku masu k’yau, da alama sauran motocin sun d’auki jama’a sun tafi.
Saida mukaje jikin motocin sannan aunty Mimi tayi murmushi tana kallonmu, to karnayi abin kunya, wacce ta my k’ani? wacce ta Marwan?.
K’asa mukayi da kanmu saboda kunya, saida ta kuma maimaita tambayar sannan munubiya tayi k’arfin halin nunani, kunyarmu takuma birgeta sosai, hannun munubiya ta kama tana fad’in kece babba ai, zoki fara shiga”. a motar farko ta sakata, sannan tadawo takama hannuna ta sakani a ta biyu.
Rufe k’ofar tayi takoma motar bayanmu tashiga. yayinda kuyangin nan hud’u suma suka shiga motar k’arshe.
Tunda nashigo k’amshin turarensa yadaki hancina, ta gefen ido na saci kallonsa, kishin gid’e yake a kan kujerar motar tamkar yasamu gado (dan bansan yama zan musalta muku tsarin motarba nikam, ammafa komai abin kallone) k’afarsa d’aya a k’asa d’aya akan kujerar, kansa na gab dani, dan dazai zame ko motsawa dolene saiya ta6a jikina, sanye yake cikin wasu Fararen suit masu azabar k’yau, sunyi mugun fidda ainahinsa matsayin cikakken namiji mai aji da gayu, aikin danna wayarsa kawai yakeyi tamkarma baisan na shigo motarba, dan ko sau d’aya bai d’ago ya dubeniba.
Nima basarwa nayi nayi tamkar bansan dawata halitta acikin motarba bayan driver.
Shikuwa tun shigowa ta k’amshin turarena yabigi hancinsa tareda shiga magudanar jininsa, a rayuwa yana matuk’ar k’aunar k’amshi, lumshe idanunsa yayi yana lasar lips, amma jinkai da k’asaita ta hanashi d’agowa yako dubeni.
Itakam munubiya tana shiga bayan aunty Mimi tarufe k’ofar yaa marwan jawota yayi jikinsa, tareda sumbatar gefen kumatunta. ta matse jikinta waje guda saboda tsorata, muryata na rawa ta gaidashi.
Ya amsa yana wani kuma shinshina wuyanta da bata wasu kisses d’in.
Mamaki da al’ajabine suka kamata, anya kuwa wannan yaa marwan d’in nanne mai shegen muskilanci da share mutane?, kanta bai ida kwancewa ba saida taji hannunsa indama batayi zatoba, tamkar zatayi kuka tace “please yaa marwan kayi hak’uri dan ALLAH, cikin motane fa”.
Rungumeta kawai yayi batareda yayi maganaba.
A wannan yanayin mukaji motocin sun tsaya.
Bayan an bud’e mana duk muka firfito, tsakanina da Galadima kuwa babu Wanda yacema wani kanzil har muka fito.
Yaa marwan da Munubiya ne agaba rik’eda hannun juna, saini da nawa d’an hayak’in Mr k’asaita abaya, harmun fara tafiya Aunty Mimi tamasa magana. banji mitace ba saboda da Indianci tayi maganar??.
Jinai kawai wani lallausan hannu cikin nawa, dagani harshi babu shiri muka kalli juna saboda shock d’in daya jamu a time d’aya.
Shine yay azamar janye nasa idanun yana cije lips, kafin nima na janye nawa cikeda kasala da luguden zuciya.
Mamakine ya kamani lokacin da muka shigo hall d’in, inda sauran ‘yan uwanmu sukene Ashe, sainaji dad’i sosai wlhy.
Nandanan mc yashiga sanar da isowarmu, tunda muka shigo kallo gaba d’aya yadawo kanmu, musamman mutane dake son ganin Galadima a yau.
Can saman hii table muka isa muma, mazaunin daya kasance namu, su Safara’u tamkar su saka ihu saboda ganin yanda muka had’u tamkar bamuba, duk sai suka raina nasu kwalliyan dukda suma sunyi matuk’ar k’yawu kuwa..
Bayan mun zauna angunan suka taso suna kawo gaisuwa wajen Galadima, fuskarsa d’auke da murmushi yake amsa musu tareda mik’a musu hannu suyi musabaha, koda sun nok’e saiya kamo hannun nasu da kansa.
Bak’in ciki tamkar yakarsu Halimatu, ganin angunansu suna kai gaisuwa wa Galadima, basusan hakan dole bane agaresu kodan kasan cewarsa d’an masarauta wandama ake da yak’inin zama sarkin gobe idan da rai, idanma badan hakan ta kasanceba ta ina suka Isa ganinsa balle ma har suyi gaisuwar Baki da baki harda musabaha. Aishi adaline ma tunda harya iya halartar taron nasu.
Yayunama duk saida sukazo suka gaisa dashi, mazan da matan, sannan mukayi hotuna, su Zarah da siyama matan ‘ya’yan senator kam ai yau saikikaji tsit babu felek’e, dan mazajen nasuma ko zuwa basuyi wajenba, kamar yanda basu halarci tasu dinner d’inba lokacin aurensu.
Aunty Mimi dakanta ta kar6i microphone tabada hak’uri da neman alfarmar tafiyarmu, saboda suma mutanensu nacan suna jiran isowarmu, dama munzone domin kar6ar excuse.
Hakkane yad’an rage fushin wasu, sannan mun tafi dawasu acikin yayunmu maza.
Mun tafi kowa yana yaba tsarin namu.
Yanzuma haka muka tafi tamkar wasu kurame, saidai yanzu a zaune yake, yajingina kansa da kujera ya lumshe idanu.
Nikam gefe na maida kaina ina kallon titi.
Yanzun kam koda motocin suka tsaya bamu fitaba, sai kusan mintuna 10, Ashe lokacin harsu munubiya da yaa marwan sun shiga, saura mu kuma.
Bamu fitoba saida akayi knocking glass d’in gefensa, ahankali ya sauke glass d’in batareda ya bud’e idonsa ba, wanine yalek’o yana fad’a masa mu fito, duk bud’e mana motar akayi dagani har shi sannan muka fita.
Zagayowa yayi inda nake tsaye, a mamakina da al’ajabi sai kawai naji ya sak’alo Hannunsa a k’uguna, cikeda firgici nad’ago na kallesa, saiya sakar min harara dawani munafikin murmushi, saika rantse da ALLAH kallon soyayya yamin, nikam dukda kwarjini dayamin saida na turo baki gaba da hararsa a kaikaice, ALLAH ma yasoni baiga hararba.
Ahankali muke tafiya saboda Alk’yabbata, yayinda kuyangin ke watsa wasu flowers masu k’amshi a inda zamu taka, aunty Mimi kam da wata daban santaba suna feso mana Abu mai k’amshi.
Kai jama’a wajen taronnan fa ya had’u, k’arshen had’uwa kuwa, an k’awata wajen da kwalliyar white and Golden colors, yayinda kwalliyar jama’ar wajenma white and Golden colors ne, (suma mutanemu dasukazo wajen dama ankawo musu kaya irin kalar).
Mazan sunsha wankan white suit, takalmansu da agoguna zuwa tie duk golden, matan kuma white gown ta material sai d’ankwali golden.
Yayinda tamu shigar ta kasance golden gaba d’aya, su Galadima kuma sun saka white suit, komai nasu white ne shida yaa marwan.
Tunda muka shigo wajen ya d’auki tafi, yayinda aka saki wak’ar da aka raira domin mu. (Bara nad’an raira muku kad’an????).
*_Alk’awari yacika munubiya alk’awari yacika…. yacika yacika munaya alk’awari yacika amarya…._*
??iya nan na iya to???????
Gaba d’aya sai wani tsoro da kunya ya kamani, nafara tafiya ahankali tamkar kazar da kwai ya fashema aciki.
Bansan lokacin da Galadima ya rankwafo kainaba, dan tunanina yatafi wajen mamakin yanda suketa shiryama auren shekara 1 wad’annan bidi’oin.
Jinai kawai an d’aukeni cak, ihu kawai aka sanya awajen da uban tafi, yayinda aka kuma sakin sabon kid’a na musamman.
Runtse idanuna nayi kawai zuciyata na kai kawo tamkar zata fito waje saboda mamakin munafuncin Galadima. (Yo inba munafuci ba miye na d’aukata agaban jama’a, bayan ni da shi ko magana bata had’amuba??).
Bai direniba sai a kujerar da aka tanada domin mu.
Anan d’inma zama yayi yasakani jikinsa, kunya da haushi duk sun cikani, wlhy badan karna kunyatashi ba dayasha mamaki. Gashi sai wani magana yakemin k’asa-k’asa kai kace ta arzik’ice, nanko duk gargad’ine wai na kama kaina karnayi abinda wani zai fahimci ba auren soyayya bane a tsakaninmu.
Baki na tunzuro gaba dan haushi, yasaka d’an yatsa ya d’alli bak’in nawa.
Naji zafi wlhy kuma.??
Abun ALLAH wadai bai k’areba saida akazo yanka cake, bayan su munubiya sun gama nasu cikin mutunci da yaa marwan saimuma muka yanka namu, maimakon yabani kamar yanda na bashi sai kawai yasa Wanda yaciro a bakinsa, bayan yayi tamkar zai bani, harna bud’e baki zan kar6a saiya lunk’uma a baki, nanma mutane suka Sanya dariya da tafi.
Wai kawai ina hararsa saboda haushin abinda yayi sai kawai naji fuskata cikin tafin hannunsa, kafin nayi wani yink’uri ya had’e bakina danashi waje d’aya yajuyemin cake d’in daya gama narkewa da yawunsa a bakinsa.
Bai cire bakinsaba saida ya tabbatar na had’iyeshi sannan.
Ai wlhy ihun yanzun yafi na ko yaushe, abokansa harwani kirari suke masa, yayinda wasu keta d’auka a hotuna, Munubiya kanta kunshe fuska tayi a alk’yabba tana dariya, duk miskilancin yaa marwan saida ya dara shima.
Aikam saida nayi hawayen bak’in ciki, mugu kawai yabani k’azantar yaunsa nasha, wlhy badan mutaneba saina k’ak’aro amai kuwa.
Daya bani drink ko k’insha nayi, ya rankwafo kaina bakinsa saitin kunnene yace, “bakiji sharad’inaba kenan? ALLAH shima zan zuba abaki na juye miki shi a bakinki yanzunan. Ai babu shiri na kar6a kuwa.
Daga nanne Samha taje wajen mc ta kar6i microphone wai tanason saka gasa tsakanin Uncle Sam da Uncle marwan, za’a shigar damu wani d’aki, bayan mintuna biyu mu fito, kowa ya nuna matarsa, duk wanda ya canka dai-dai shine yaci gasar, shikuma zata bama k’yautar.
Galadima jiyay tamkar ya mangare Samha, sai antaya mata harara yakeyi itada Sauban, dan yasan wannan munafurcin sune suka kulloshi.
Ai kam k’in kallonsa sukayi sunata k’unshe dariya.
Dole yanda sukace d’in haka akayi, muna shiga aka gyaramin janbakina da Galadima ya tsotse, sannan aka kuma feshemu da turararurruka saboda kowance k’amshin turaren mijinta daya manne mata yabar jikinta.
Kujeru aka ajiye mana muka zauna, kowacce taci serious.
Da Galadima aka fara, gabansa sai dukan sittin-sittin yakeyi, danshi da gske ba iya gane ni zaiyiba, inba na nuna halin nawa bane.
Aiko ya nuna d’aya acikinmu, mik’ewa tayi takoma gefensa ta tsaya, amma bai ta6a ta ba, dan ba’asan wacecenba acikinmu.
Shima yaa marwan rikicewa yayi, dama mafi yawan lokuta ta halayya yake ganemu, shima dai wadda Galadima yabari ya nuna.
Bayan suma sun koma gefe aka koma kan za6in Galadima, mc yace “zamu iya Sanin wacece?”.
Murmushi munubiya tayi, cikin sanyinta tace “Munubiya ce”.
Juyowa Galadima yayi ya kalleta, sanyinta ma kawai ya isa tabbatar da gaskiyarta.
Nima aka tambayeni cikeda Jan aji nace “Munaya ce”.
Nanama ihun akayi, cikinsu babu Wanda ya canka dai-dai, dan haka ni da Munubiya su samha suka bamu wata k’yauta dabamusan ko miye a cikiba, wai mune mukayi wining.
Daga nan aka rufe taro da addu’a aka tashi.
Har gida suka maidamu muda tawagarmu, lokacin 1:15pm.
Muna zuwa kowa makwanci kawai ya nema……………???
Irin wannan dogon page haka??????, shikenan harda na gobe na had’a muku kenan??.
??????????
*_Ya ALLAH ma gafartama iyayenmu_*??????
*_Typing??_*
*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_
*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce????_*
No one has commented yet. Be the first!