1?9?
Khulud ta kuma zaro idonta waje tace ” kai my Sanah,
cikin dariya Sanah tace ” eh mana,
” ni dai please kiyi man alk’awarin baki kuma ramawa please,
tayi maganar cikin sanyinta,
Sanah ta kuma yin dariya had’i da dafa kafad’ar Khulud tana kallanta ido cikin ido,
cikin marairaicewa Khulud tace ” please tana langwab’ar da kanta gefe,
Sanah ta d’an k’ura mata ido kana ta sauke ajiyar zuciya had’i da cewa ” nayi miki alk’awarin daga yau har abada duk abinda zai man ban kuma ramawa,
cikin jin dad’i Khulud ta rungume ta tana cewa ” yawwa my Sanah thank you so much,
murmushi Sanah tayi kawai batare datace komai ba,
ta rok’o hannun suka nufi part d’in kakannin su.
Fitowa Hanash yayi zuwa harabar gidan,
su Wajnah na biye dashi a baya,
Papu yace ” au kinga na manta Hanash zai fita batare dana aike shi bank d’in bako?
Yayi maganar yana kallan Mimmee,
tace ” kaga kuma yau Friday ba,
da idan ya aje su sai ya biya bank d’in,
kafin su gama walimar shi yaje yayi abinda zayyi,
Mimmee ta fad’a idanta kan Papu,
” kuma daga yau ba bank har sai Monday,
ga time na tafiya naga yanzu wajen 4:30pm,
yayi maganar yana mikewa had’i da kallan agogon hannunsa,
da sauri ya fita daga parlor’n yabi bayan su Hanash,
Hanash na niyyar yiwa mota key,
yaga Papu ya nufo su da sauri,
a hankali Hanash ya fita ya nufi Papu,
check Papu ya mik’ewa Hanash yana cewa ” idan ka aje su a gidan walimar ka biya banki ka amshi wad’annan kud’in,
sai ka saka su a account d’ina ko naka,
Hanash yayi murmushi yana kallan Papu zayyi magana drivers biyu suka shigo gidan a lokaci d’aya,
Papu yace ” yauwa ga drivers nan sun dawo,
bari na saka d’aya daga cikin su ya kai su gidan walimar,
kai kuma sai ga je bank d’in,
Papu yayi maganar yana nufar wajen drivers d’in,
cikin taushi Papu ya fad’a musu,
sannan ya sanar dasu Zohal su fito su shiga motar driver shi zai kai su,
kana ya koma wajen Hanash dake tsaye inda ya barshi,
Papu ya lura da yadda yanayin Hanash ya canja sosai,
sannan walwalarsa da sakin fuskarsa ba kamar da ba,
kallan Papu Hanash yayi kana yace ” Papu wannan kallan fa?
Ya fad’a yana dariya,
shima Papun dariya yayi yana dafa kad’afar Hanash yace ” bakomai kawai ina kallan d’ana ne,
in kuma za’a hana ni ne to,
yayi maganar cikin barkwanci,
Hanash yayi dariya batare dayace komai ba,
Papu yace ” kaje maza ka dawo zamuyi magana da kai,
Hanash yayi dariya kana yace ” hala Papu ya manta yau Saturday?
Papu ya zaro ido had’i da cewa ” what! haba dai?
Hanash yayi murmushi yace ” Allah kuwa Papu yau Saturday,
hala ka shafa’a ne?
” Ka manta jiya mukaje sallar juma’a?
Papu yace ” na manta,
kasan tsufa ya fara kamamu ,
abinka da tsoho, Hanash kuma yin dariya yace ” kai Papu wanne irin tsufa kuma?
“Bayan gaka nan kamar matashin sauryi kamar mu,,
Hanash ya fad’a cikin tsokana,
dayake sun saba wasa da dariya sosai da Papu,
dan wani lokacin idan ka gansu sai ka rantse abokanai ne,
Papu yace ” kayya wanne matashin sauriya,
muda samartaka ai sai dai a lahira a aljanna,
jiya ai ba yau ba ,
tunda na haifi k’aton saurayi kamarka ai na tsufa,
ko yanzu Alhamdulillah dan na mori k’uriciya ta,
kai ma sai kayi k’ok’ari ka mori taka k’uruciyar,
sanda nake kamar shekarunka na haifeka,
amma kai gaka nan har yanzu 30yrs baka da ko budurwar,
ko rowa kake man dan karna ga ‘ya’yanka oho,
inaga sai na mutu sannan zakayi aure ka haihu,
Jadda dake jiyo su ta window ta,
suka jiyo muryarta tana cewa ” kyale ja’iri wallahi idan na gaji sai dai ya shigo gidan ya iske matarsa a b’angarensa,
imma bak’in ciki kake man dan kar naga yaranka ehe,
daga Papu har Hanash duk suka sanya dariya,
Hanash ya shafa kansa yana kallan Jadda,
Papu dake tsaye a wajen shiya hana shi ce mata komai,
sai murmushi da yayi tayi shi kad’ai yana shafa kai,
kallansa Papu yayi yana nazarin yanayinsa ya tabbatar akwai abinda yake damunsa,
amma sai ya sabar yace ” ka rik’e check d’in a hannunka,
ranar Monday sai kayi kamar yadda na saka ka,
“tom Papu ba damuwa Allah ya kai mu Monday,
Papu ya amsa da ” amin yana komawa part d’in Mimmee,
iske ta yayi tana k’ok’arin shigewa bedroom d’inta,
ganinsa yasa ta jiyowa tana kallan shi,
yace ” wai meke damunsa ne?
Tace ” wa?
Yace ” Hanash mana,
naga kwana biyu yanayinsa duk ya canja,
Mimmee tace ” nima dai haka nagani kwana biyun nan,
kamar yana cikin damuwa,
Papu yace ” kin tambaye shi ne?
Tace ” eh,
“Ok meya ce maki?
” Wai bai jin dad’in jikin sa ne,
Papu yace ” ok mu barshi zuwa nan da kwana biyu mu gani,
Mimmee tace ” Allah ya kai mu,
muje ciki kayi wanka ko?
Bayanta yabi yana cewa ” kamar ko kinsan zafi nake ji,
Hanash na komawa b’angarensa ya kuma zubewa kan sofa,
had’i da runtse idannuwansa,
shi har yanzu bai san so da soyayyar Khulud ke d’awainiya dashi ba,
ta hana shi sakat, ta hana shi walwala da farin ciki,
haka nan kullum yake jin damuwarsa na k’aruwa,
babban burinsa a rayuwa yanzu bai wuce na sake ganinta ko sau d’aya ne a rayuwarsa ba.
part d’in Ganez suka fara shiga suka iske Nisah zaune kusa dashi,
Sanah tace ” oh! ashe dai har yanzu ana tsinkar korawayen fure?
Duk sukayi dariya kana Ganez yace ” a’a aini idan bada ku zan tsinki korayan fure ba,
ai a banza, Khulud tace ” kinji shi zayyi mana wayo kullum yayi ta cewa idan ba mu ba sai rijiya,
Sanah tace ” kuma yana tsoran matarsa ba,
Nisah tayi dariya kana tace ” oh! kuji man yara,
wato kun saka mana ido, ai irin haka ake so,
Khulud tace ” mijin ya rink’a jin tsoran matarsa?
Nisah tace ” eh mana,
Sanah tace ” ina fa dad’i miji ya zama mijin tace,
an dai mayar mana da kakanmu tace kawai,
Nisah tace ” wannan ai kan tace ne ma,
duk sukayi dariya kana suka fita suka nufi part d’in Danish,
ganin Erum tayi kwalliya yasa su yin dariya,
Khulud tace ” wato ke har yanzu baki dai na kwalliyya bako?
Erum tace ” ina ni ina daina kwalliya,
Sanah tace ” kici zamaninki kici na wasu ko?
“Sosai ma kuwa cewar Erum,
” a’a kace yau amare nane a gidan,
cewar Danish dake fitowa daga bedroom d’insa,
Sanah tace ” mune, munzo a bamu abinda akaci aka rage,,
Danish yace ” ku da kuke amare ina ku ina raguwa,
ai sai dai sabuwar dahuwa,
Khulud tace ” ai dama kun saba yi mana wayo,
bayan duk tsoron matan ku kukeji,
Erum tace ” ai irin wannan k’arshen ake so ayi yara,
ku ma kuyi addu’ar Allah ya baku ita mu,
Sanah tace ” wai ma duk ba wannan ba,
ina zaku na ganku duk kunyi kwalliya?
” Mu da muke da walima yau har a tambaye mu inda zamu dan munyi kwalliya,
Erum tayi maganar tana dariya,
Khulud tace ” a she walima ce daku,
a ina kuma?
Erum tace ” sosai ma, kuma a nan gidan,
Sanah tace ” tab wai wacce walimar kuke nufi?
Badai tamu ba ko?
Tayi maganar a lokaci d’aya,
Erum tace ” walimar ku ko tamu?
“Ai muke da walima kuwa,
tunda mune manyan k’awaye,
tayi maganar tana dariya,
Khulud tace ” mu dai bamu gayyace ku ba,
kuma bamu san gayyar sod’i ehe,
duk sukayi dariya kana suka fita,
part d’in Juju sukayi,
da sallama suka shiga,
Didi ya amsa musu cikin fara’a,
kana yace ” ‘yan candy ne yau a gidan namu?
Sanah tace ” mu ne,
Didi ya kalli Juju yace ” ina kika b’oye mana su ne?
Juju tace ” wacce ni?
” Ai sai dai ka tambaye Mamun su,
ni tunda sukayi candy ban sa su ido na ba,
sai yau, ko irin kayan kayan candy nan ba’a kawo mana ba,
balle muce mu shaida anyi candy,
muce Allah ya sanya alkhairi,
Khulud tace ” kai Juju Allah bamu zauna bane,
mu ta yawan zuwa saloon da k’unshi,
Sanah tayi dariya kana tace ” Juju ku da zaku bawa wasu ma,
kayan candy kuma ga walima nan kun shirya ku da kanku,
sai ku shaida anyi candy kuyi addu’ar Allah ya sanya alk’airi,
Didi yayi dariya yace ” wai Sanah baki abin magana,
ke dai ba’a tab’a k’ure ki ta wajen magana,
Juju tayi dariya tace ” ai ni nayi shiru tunda an fini baki,,,
dama hausawa sunce dokin mai baki yafi gudu,
Didi ya kuma yin murmushi kana yace ” Sanah yaushe jamb d’inku zata fito?
Sanah tace ” naji ance this coming Monday,
Juju tace ” wacce university kika cike?
“First choice BUK second kuma ABU Zaria,
Didi yace ” masha Allah Ubangiji ya taimaka, Allah ya bada sa’a,
duk suka amsa da Amin,
har Khulud dabata zana jamb d’inba,
dan cewa tayi ita ta gama karatun boko har abada,
Juju ta kalli Khulud kana ta mayar da kallan ta ga Didi tace ” ‘yar Abbu da Mamu ita aure take so,
Khulud ta d’ago kanta da sauri suka had’a ido Juju tayi saurin sadda kanta k’asa tace ” Allah Juju ba haka bane,
tayi maganar a shagwab’e,
Juju tace ” idan ba haka bane to yaya ne?
Khulud tace ” Allah ni ban san cigaba da karatun ne kawai,
ni kwata-kwata ban tab’a sha’awar yin karatun boko mai zurfi ba,
Juju zata kuma yin magana,
Didi yayi saurin cewa ” haka ne ai kowanne mutum yana da nashi ra’ayin,
hakan ma da kikayi dai-dai ne dabaki yaudare iyayenki kin shiga jami’ar ba,
kana kik’i yin karatun ko wata matsala ta faru,
so ni ina ganin kinyiwa kanki da Abbunki adalci,
Allah ya zab’a maku abinda yafi alkhairi a rayuwarku,
ya haskaka rayuwarku ya sanya albarka acikinta,
duk suka amsa da Amin,
fita sukayi suka nufi wajen da aka tanada dan yin walimar da tuni k’awayensu sun fara zuwa,
sosai walima ta kankama haik’an,
aka ci aka sha sosai dan sosai Abbu ya saki bakin aljihunsa dan nuna tsantsar farin cikinsa na kammala karatun yaransa lafiya,
sosai aka rarraba kyaututtuka,
kana kowa ya watse cikin farin ciki aka gama walimar lafiya.
https://2gnblog.blogspot.com/
Sannu a hankali matsanannaciyar soyayyar Khulud tayi mugun kama Hanash,
ta addabi ruhi da gangar jikinsa,
kwata-kwata ya rasa sukuni da walwalarsa,
ya rame sosai dan raban dayaci ishashshen abinci ko ya samun bacci har ya manta,
kullum yana cikin bedroom ko parlor’nsa,
dan ko fituwa sosai ya dainayi sai dai ya fito ya gaida iyayshi ya koma,
yauma kamar kullum kwance yake a d’akinsa ya tsunduma duniyar tunaninta,
idanshi rufe babu abinda yake gani sai ita tsaye a gabansa,
tana sakar mishi k’ayataccen murmushinta,
jin knocking yasa shi bud’e shu’uman idanuwansa,
k’ofar ya zubawa ido na tsayin lokaci,
batare da yayi wani yunk’uri ba,
sake knocking akayi a karo na biyu,
dakyar ya iya cewa ” waye?
Muryar Papu yaji yace ” mu ne,
dan sun kasa jurewa ganinsa cikin wannan mawuyacin yanayin,
da sauri ya mik’e ya bud’e musu k’ofar suka shigo,
akan sofa duk suka zauna, a hankali Mimmee ta d’ora hannunta akan kafad’arsa,
had’i da zubawa d’an nata ido,
Papu ma ya zauna kusa dashi ya zuba masa ido,
kansa ya duk’ar dan ya san kwanan zancen,
muddin akace bashi da lafiya ko yana cikin damuwa to gaba d’aya gidan babu mai yin walwala,
a hankali Papu ma ya d’ora hannunsa akansa kana ya kira sunansa,
” Hanash,
“na’am, Hanash ya amsa cikin ladabi,
” meke damunka?
Cewar Papu a tak’aice,
murmushin k’arfin hali Hanash yayi kana yace ” babu abinda ke damuna Papu,
yayi maganar while kanshi k’asa,
Mimmee ta shafa kansa kana tace ” Hanash please karka b’oye mana abinda yake damunka,
ka daure ka sanar damu koda babu wani abu da zamu iya yi akai,
sai mu tayaka da addu’a,
ta fad’a cikin damuwa,
murmushi Hanash ya kuma yi kana yace ” ba ni da lafiya ne,
Mimmee zazzab’i da ciwon kai ke damuna,
ido Mimmee ta zuba mishi tana nazarinsa dan ita kwata-kwata bata yarda da abinda yace ba,
Papu yace ” kaje hospital?
Hanash yace ” eh Papu,
“me sukace yana damunka?
Papu ya kuma tambayarsa,
d’an shiru Hanash yayi kafin yace ” Malaria,
” to ikon Allah kai ko ina kaga sauron daya cije ka?
Mimmee ta fad’a tana kallan kwayar idansa,
murmushi yayi kana yace ” Mimmee, cikin shagwab’a,
Papu yace ” shi ciwo ai daga Allah ne, ba ta inda baya shiga jikin mutum ko son?
Yayi maganar cikin tsokana,
dan shima yadai ji Hanash ne kawai,
amma bai yarda da abinda ya fad’a ba,
babu yadda Papu da Mimmee basu yi akan Hanash ya sanar da su damuwarshi ba, amma yak’i yace babu abinda yake damunsa,
Papu yace ” Allah ya sauwak’e,
ya amsa da ” Amin, kana suka fita,
suna fita Hanash ya koma ya kwanta,
had’i da rufe idansa.
Ranar Monday jamb ta fito,
Sanah cikin murna da d’oki suka je ita da Aarib & Khulud suka duba,
a cafe, aiko taci sosai dan ta samu 251,
tsalle ta buga ta rumgume Khulud da Aarib cikin matsananciyar murna,
motar su nayin parking a harabar gidan ta fito,
ta shiga kwalawa Halan kira,
da gudu ta shiga part d’in Halan,
ta iske ta parlor zaune ita da Ziyad,
cikin murna ta fad’a kanta, ta ma manta da tsohon cikin dake jikin Halan,
Ziyad ya daka mata tsawa had’i da cewa ” ke baki da hankali ne ko baki ganin abinda ke jikinta?
Bata kula da tsawar daya daka mata ba,
sai ma kiss datayi mishi a kumatu,
cikin murna tace ” Yaya naci jamb,
ta fad’a tana tsalle,
dariya Halan tayi tace ” kai masha Allah gaskiya nima nayi murna,
badan kayan dake gaba na ba,
da har dani za’ayi tsallan,
Ziyad yayi dariya yace ” bani abu na inyaso sai kije kiyi tsallanki,
Halan ta kalleshi had’i da zumb’uro baki tace ” Allah da ana bayarwa ai bama sai ka tambaya ba,
Sanah da Khulud suka fita da gudu suka nufi part d’in Mamu,
suna zuwa Sanah ta fad’a kan Abbu,
yace ” kai Sanah ke dai baki girma,
naga alamar so kike ki karya ni tunda baki ganin na tsufa yanzu,
Sanah tayi mishi kiss tace ” Abbu albishirinka,
yana dariya yace ” goro,
tace ” fari ko ja?
Yace ” fari tass,
tace ” Abbu na ci jamb,
Abbu yace ” wai dole ayi murna,
Mamu tace ” masha Allah,
saura waec & neco,
Abbu yace ” suma duka za’a cinye su,
in sha Allah,
fita sukayi suka nufi part d’in Juju,
nan ma aka sanar mata anci jamb,
murna kam ba’a magana,
a week d’in waec ta fito,
Sanah ta samu result mai kyau,
result d’inta yayi mugun kyau,
bayan two weeks BUK ta kira su first UME,
bayan week nan ma result ya fito,
ta samu taci, suka bata Admission letter na BSC COMPUTER SCIENCE.
Kullum Hanash bashi da wani aiki sai mafarkin Khulud,
da tunaninta ko idansa ya rufe ita yake gani,
koyaya ya rufe idansa ita yake ya gani,
abun duniya duk ya dame shi,
ba shi da wani burin daya ce na sake ganinta a yanzu,
ko da sau d’aya ne a rayuwarsa.
Yau itace rana ta farko da Sanah zata fara hallartar BUK,
ta gama shirinta tsaf cikin riga da siket na material red color d’inkin yayi masifar yi mata kyau,
ya amshi jikinta sosai, ta saka high hill shoe ta yafa mayafinta mai kyau kalar flowers dake jikin material d’in black,
sosai Sanah tayi shegen kyau,
duk da ba wani make up tayi ba,
ta dayyi simple make up abinta,
wanda ya bayyanar da tsantsar kyauta,
har cikin makarantar Aarib ya kaita,
sai da yayi mata fad’a sosai kana ya tafi,
sannu a hankali take tafiya harta isa department d’insu,
tambaya tayi,
aka nuna mata, inda zasuyi lectures yau,
dayake tana da time table na duka courses & time d’in su,
a hannunta tasan Computer lectures zata fara attending,
zama tayi a inda taga students na zama,
zamanta ke da wuya ta fara jiyo hirar students,
” yau fa Sir Aryan ne damu,
kasan ko ba sauk’i, d’ayan yace ” wallahi ko ni gaba na ma sai fad’uwa yake yi,
tun jiya dana duba naga shine damu hankali na yake a mugun tashe,
wani daga gefe yace ” kai ai Malamin nan bai da kyau,
d’ayan yace ” kaga fito sak a mutum kai tsaye kace bai da mutunci,
d’ayan yace ” ni fa yana mugun ban mamaki shi ko irin na sauran lectures d’in nan bayyi,
d’aya yace ” me?
” San mata mana,
d’ayan yace ” kai tanan wajen ai Sir Aryan yayi wallahi,
ba ruwanshi da mata, duk kyanki yanzu zai yarfa ki,
ba kamar sauran lectures d’in ba,
shegu da sunga mata sai suyi ta rawar jiki,
idan mune ‘yan uwansu maza tsakanimu dasu ba mutunci,
sai su rufe ido su karta mana,
amma shi kwata-kwata mace bata isheshi kallo ba,
naga ‘yan mata dayawa sunyi mugun matuwa akansa,
d’ayan yace ” aiya had’u ne ga kyau ga kud’i, kaga kuwa ai dole mata su matu,
tunda ready mate ne,
d’ayan yayi dariya yace ” aiko suna shan dizgi da wulak’anci a wajensa ba,
dan yanzu zai kartawa mutum rashin m,
idan ta kama ma ya yarfa maka mari ba ruwanshi,
shege ga girman kai da d’agawa da jan aji dan sai kayi mishi magana goma amma dakyar idan yaga dama zai amsa maka d’aya ,
d’ayan yace ” kai ai ya iya d’aukar wanka dacin uwar sutura,
yana zagin gizna ta asalimma,
ni na rasa uban me yake yi a makarantar wallahi,
“hmmmm ga babu ruwanshi da ke wai mace ce,
shi hukunci d’aya yake yi tsakanin mace da namiji,
idan ya riga ka shiga class ko waye ubanka kuma ko uban ya tsaya maka ya d’aure maka gindi baka shiga,
d’ayan ya duba agogo yace ” sauran just 5 minutes ya shiga fa,
kusan kuma baya African time,
d’an tsaki Sanah tayi a hankali kana ta mik’e tabar gurin,
saboda duk gurin wajen mutum 100,
maganar mutum d’aya suke tayi Sir Aryan,
duk inda students sukayi d’an group,
maganar shi kawai sukeyi mata da maza,
daga maganar had’uwarsa kyansa, gayu, ajinsa,
sai ta wulak’anci da dizginsa da kuma girman kansa,
da yadda mata suka mato akansa yake wulak’antasu,
shiyasa duk randa yake da lectures dasu suke kaffa-kaffa.
Can gefe ta koma ita kad’ai ta zauna,
ita kad’ai kasancewar yaune farkon zuwanta bata san kowa ba,
tana daga zaune taga wata matsiyaciyar had’add’iyar mota ta danno kai cikin makarantar,
students na ganin motar suka kai duba zuwa number motar dan su tabbatar idan shi,
saboda baya hawa motar d’aya,
duk nacinka baka isa kace ga yawan motocinsa ba,
ta number motarsa kad’ai suke gane shi ne,
saboda sunan family d’in su ne a duka number motacinsa,,
ai students na tabbatarwa shine,
suka fara gudu maza da mata ana rige-rigen shiga class.
Yana yin parking, ya zare key d’in tare da komawa ya kishink’id’a jikin kujerar, ido ya lumshe tare da fesar da numfashi mai sanyi, a hankali ya kuma bud’e idon tare da sauk’e ajiyan zuciya, yana mai shak’ar k’amshin jikinsa dana mortar, a hankali ya sa hannun damanshi ya dafe saitin k’ahon zuciyarshi dan jin gabansa yana muguwar fad’uwa da k’arfi,
bugun zuciyarsa ya k’aru sosai,
zuciyarsa ta rink’a bugawa so past,
idansa ya kuma lumshe yana k’ara d’an kishingid’a akan kujerar motar,
a hankali ya furta ” innalillahi wa’inna ilaihirraji’un,
saboda yadda yake jin
duk ilahirin jikinsa ya mutu, gabansa na mugun fad’uwa zuciyarsa na bugawa da tsananin k’arfi, addu’ar yayi ta maimaitawa dan baya son ayi mishi African time shiyasa shima baya son yayiwa d’alibanshi, bere daga inda yayi parking yana iya hango yadda suke sassarfan shiga class, sharshesa ya fitar tare da d’an laso lips nashi, hadi da d’an cizawa dan kauda kasalar dake saukar mai a jiki,
a hankali ya b’alle marfin motar tare da zuro k’afarshi d’aya woje, baki ya d’an tab’e ganin yadda wasu matasa suka wuceshi da sassarfa, gudun karya rigasu shiga class, ya hanasu shiga, fitowa daga cikin motar tare da jawo laptop nashi, ya bud’eta tare da dorata kan hannunshi daya mik’ar, yana kuma d’an lallatsashi cikin k’orewa, ajiyan zuciya ya sauk’e tare da fara takawa zuwa class d’in yana mai jin dad’in iskar dake busawa sirrai da fawowi suna shawagi tsuntsaye na kai komo ga k’amshin furanni dake ratsashi.
Cikin takunsa na isassun maza masu haiba da kamala ga tarin nagarta yake tafiya cap-cap sautin takalminshi ke ratsa wurin in dalibai sun hangoshi sai suna rusunawa tare da ratse mishi.
Ganin yadda students ke gudu yasa Sanah kai idanta kan motar dataga kamar an saka MOLI’S 15,
amma data duba so sai taga kamar ba haka bane,
baki tad’an tab’e kana ta mik’e cikin takunta mai daukar hankali tabi bayanshi,
ta nufi class itama,
daga bayansa ya rink’a jin kamar takun mutum a bayansa k’at-k’at,
Fuska ya kuma had’ewa dan ya gane mace ce, daga k’asa ya kalli k’afarta data sha kunshi mai ja da bak’in lalle yayi masifar yi mata kyau,
gabansa ne yayi muguwar fad’uwa lokacin daya d’ora idansa akan k’afarta, sake had’e rai yayi , kana ya cigaba da tafiya,
yana tafiya tana binsa a baya,
har suka zo gaf da isa class d’in,
Kai ya d’an jinjina tabbatarwa da yayi class d’in sa zata shiga , hankalin shi na kan laptop d’inshi, hannunshi mai yin typing d’in ya d’an d’aga shi saman kafadarshi ta yadda zata gani, sanan ya had’e doguwar yatsarsa ta tsakiya da babbar yatsarsa ya kettasu sau d’aya ta yadda ya bada sauti, sannan ya had’e yatsunsa biyu ya kad’asu kamar mai buga fiyano ya mata nuni data tsaya inda take karta biyoshi,
batare daya juyo ya kalle ta ba bai kuma tsayaba yaci gaba da takunshi zuwa cikin class,
Itako Sanah bata gane abinda yake nufi ba,
dan haka taci gaba da binsa a baya,
Kai ya jinjina tare da yin gutun murmushi, mai dauke da alamar zaki gane kurenki,
kana ya cigaba da tafiya har suka k’arasa cikin class d’in,
Sanah tazo zata wuce mazaunin d’aliban, *”Keeh”* kamar daga sama sautin muryarsa ya ratsa shirun daya ratsa ajin,sai sautin takalminta dake amsakuwa, shirune ya sake ratsa ajin duk sunsha jinin jikin su, ita kuwa Sanah kai ta d’ago ta kalleshi ,Amman bata ga fuskarsa ba dan baya ya bata, sai gashin k’eyarsa da ta tsurawa ido ganin shi a kwance lub sai wani lauyewa a yayi ya bi k’eyan nashi yana Shek’i, tana cikin nazarin da me tayi mishi ta kuma jiyo muryarshi na ratsa ajin baki d’aya taji tajiyo muryarsa nacewa yana cewa, *”kneeling down,”*
ya fad’a still bai jiyo ya kalle ta ba,
juyawa tayi bayanta taga babu kowa sai ita kad’ai,
cikin mamaki ta kalli bayansa dan ita a iya saninta tasan ba’a saka Patick a jami’a.
Cikin mamaki ta kuma kallan bayansa,
batare daya jiyo ba taji yace *”ko bazaki kiyi bane?”*
Muryar dataji ta daki dodon kunnenta,
tasa gabanta mugun fad’uwa a razane ta kuma kallan bayansa,
babu damar taga fuskarsa saboda ya juya mata baya,
a hankali Sanah ta d’an zumb’uri baki kana tayi kneeling down d’in,
gaba d’aya students mamaki ya gama cika su,
duk da sun san halinsa, sun tabbatar zai iyin abinda ma yafi hakan,
dan sun san mari ko dizgi abu ne mai matuk’ar sauk’i a wajensa,
amma basu tab’a ganin yasa wata ko wani kneeling down ba,
sai yau kuma daganinta new comer ce,
students suka rink’a yin dogon wuya suna l’eka ta,
jin muryarsa ta fara explanations yasa duk suka shiga hankalinsu.
Sanah na nan har ya gama lecture tana ta zumb’ure-zumb’uren baki,
Cikin k’asaita ya fito zai tafi , ganin ya wuce ta gabanta amma bashi da niyyar ce mata komai,
yasa ta cewa *”Sir to ni wuni zanyi a nan ne? “*
Tsayawa yayi cak a inda yake,
kana ya juyo da fuskarsa a hankali ya zuba mata ido,
had’i da hard’e hannayensa a k’irji,
mik’ewa Sanah tayi batare daya bata umarnin tashi daga kneeling d’in ba,
kanta durk’ushe tana kakkab’e siket d’inta,
tana yin magana k’asa-k’asa, “eh wato kai zaka fece gidanku ni kuwa in zauna a nan, sai kace baiwar gidan ku ko, hegen k’eya! da nad’edd’en gashi.”
dan ita a tunaninta ya tafi shiyasa ta d’anyi halin, baki ta murgud’a tare da mik’ewa tsaye,
d’ago kan da zatayi, keda wuya sexy eyes d’inta,
suka sark’e cikin na *SIR MOLI* dayake tsaye hard’e da hannuwa yana kallan ta………………
_Aunty AISHA ALIYU GARKUWA_
_kina tambayar inda nakai miki Sir Molinki to gashi nan na maido miki abinki_
~To fans masu tambayar ina nakai Sir Moli na b’oye har tsayin six years, gashi nan ya dawo~
~sai a cigaba da gashi a d’ora daga inda aka tsaya~
*_Typing??_*
*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_
*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce????_*
No one has commented yet. Be the first!