?1?8?
https://2gnblog.blogspot.com/
……….A Asibiti gado suka bani, sunata fad’an yanda jinina ya hau sama, su mamakima suke yi ‘yar k’aramar yarinya dani amma inada hawanjini, shin miyayi zafi haka?.
Su Abba dai kasa cewa komai sukayi, dan su kansu abin na yata6a zuciyarsu.
Wannan karonma Mama Rabi’a da Munubiya ne suka kwana a wajena, washe gari da yamma saiga ‘yan gidanmu wai sunzo dubani, bamuyi mamakiba Dan munsan ba domin ALLAH sukazoba, kawai sunzo ganin kwafne.
Duk suncika d’akin da surutu akan wai suna mamakin miya samin hawan jini?. daga mama Rabi’a har Munubiya babu wanda yabasu amsa.
Doctor ne yashigo yace sud’an ragu wasu su fita baranda dan ALLAH, duk fita sukayi harda mama Rabi’a aka barmu iya mu yaran kawai, dansu Fiddausi duk hadasu akazo.
Ina daga kwance kan gado ina sauraren hirar dasukeyi, wai safara’u da Halimatu ne sukaje gidan su Siyama tai tamusu yatsina da d’aukar kai, saikace ba ‘yan uwanta ba, mijinta yadawo sukayi shigewarsu suka barsu afalo har yamma sannan suka fito, mai makon tabasu hak’uri sai cewa tayi wai dama basu tafiba??.
Wannan abun daya faru shine yajawo rigima a gidanmu jiya da daddare, har saida su Abba suka tsawatar.
Murmushi kawai nayi Na gyara kwanciyata, a zuciyata ina fad’in maganinku ai, baku masu dangiba……….gabana yafad’i, saboda jin tamkar k’amshin turarensa. da sauri Na d’ago kai saboda jin su Fauziyya ma sunyi tsit daga surutun dasukeyi suna kallon bayanmu.
Wani yaam naji a raina domin ganin Galadima da tawagar dogaransa, sai wani dake gefensa amma ba muftahu bane, (Harun ne). Sanye cikin k’ananun kaya wad’anda suka fidda ainahin k’irarsa ta cikakken namiji, fuskarnan kamar kullum babu walwala.
Mu 4 ne kawai a d’akin, dan haka yana tsaye a gadon farko da alama tanbayoyi yakema matar dake jiyya a gadon. gani nai yasaki wani guntun murmushin gefen baki sannan ya kalli harun, bansan miya cemasaba nagadai yabaro wajen yana tunkaro gado Na biyu.
A hankali Na lumshe idanuna wani Abu Na tsikarar zuciyata mai kama da tsoro da rud’ani.
Sauran ‘yan uwana kam sun zuba masa idanu tamkar zasu cinyesa, kowacce takasa furta komai a fili saida a zuciyarta take tattaunawa da yaba Galadima d’in.
Annanma yayi kusan mintuna hud’u sannan ya tunkaro gadon takusa damu, dan nice ta k’arshe. duk da akusa damu yake banajin miyake fad’a, saidai motsin la66ansa kawai nake gani, tabbas Galadima naji da Girman kai da mulki, kallo d’aya zaka masa ka tabbatar da tsantsar sarauta da mulki dake yawo a jinin jikinsa……. tunda naga yanufo inda nake sai kawai narufe idanuna gaba d’aya.
Su Munubiya duk suka risina suna gaidashi.
Hannu kawai ya d’aga musu yamatso jikin gadon danake.
Tsantsar mamakine ya bayyana a fuskarsa, yad’anyi kamar zai nunani da hannu saiya kuma fasa, su safara’u kam duk sun zubo mana idanu suga yanda za’a kwashe.
Munubiya ce cikin k’arfin hali tace “Munaya ki tashi ana miki magana fa”. daka ganta kasan a tsorace take maganar.
Shima juyowa yayi ya kalli Munubiyar domin jin kuma Muryata, maganar Muftahu ta fad’o masa arai dayace yaran twins ne, kuma ba’a iya banbancesu.
Suma Kansu dogaran NASA da Harun duk sunyi tsuru suna kallonmu, domin babu wanda baiga jaridarba a wancan lokacin.
Maganar sace tasaka kowa maida hankali a kansa, nidai har yanzun idona arufe suke, cikin basarwa da nuna halin ko in kula yace, “ya jiki?”. tamkar bayaso haka yayi maganar.
Nima cikin dakiya da shariyar kamar yanda yamin nabud’e idona nace “Alhmdllh”.
Kamar yanda yake tambayar kowa nima haka ya tambayeni miye matsalata?.
Na d’a6e baki sannan nace “masassara”.
Harun ya kalla, danshi baima fahimci minake nufiba.
Murmushi harun yayi, danya fahimci bai ganeba, cikin gyara tsayuwa yace “tana nufin fever”.
Caraf fiddausi tace, “ranka yadad’e k’arya take hawan jinine”.
Juyowa yayi ya kalli fiddausin da fararen idanunsa wad’anda suka nemi zautata, bai Ce komaiba ya janye ya maida kan Munubiya, “Sister naga drugs d’innan?”. yafad’a kamar anmasa dole.
Ko kad’an Munubiya bataji maiya fad’aba, dan a saman la66ansa yayi maganar, tana shirin sake tambayarsa d’aya daga cikin dogaran ya maimaita mata a tsawace.
Nikaina saida Na bud’e ido saboda tsawar, Na bankama dogarin harara ina magana k’asa-k’asa yan da babu mai jina, kajimin shegen dogari, dan tace batajiba zakawani daka mata tsawa?, shi mizaisa bazai bud’e baki yayi magana yanda kowa zaijiba? Mutum sai azabar Girman kai mtsoww, koma R bai iyaba.
Duk maganar danake la66ana ne kawai ke motsawa, shikuma idon nasa nakan la66ana, dukda duba kwalin drugs dayakeyi, tsaf ya karanci duk maganar danakeyi. yayi wani munafukin guntun murmushi yana mik’ama Munubiya magungunan.
Juyawa yayi yama Harun magana, sannan ya juyo ya kalleni yana fad’in “ALLAH yak’ara lafiya”.
Harara Na zuba masa batare da tunanin zai ganiba, amma sai caraf muka had’a idanu.
Janye idanunsa yayi a kaina yajuya yabar wajen yana cije lips d’insa da mamakin yarinyar nan da batada tsoro.
su Safara’u Na zuba masa godiya, duk da zukatansu Na mamakin yanda yanuna tamkarma bai sanmu ba.
Ko kallonsu baiyiba ya d’aga musu hannu, sukuma sunyine dama danya tanka musu.
Harun ya tambayi Munubiya wane doctor ne ke dubani?.
Ta Sanar masa.
Addu’a yaymin sannan yabar wajen shima.
Lumshe idanuna nayi zuciyata Na kaikawo, yanda Galadima yayi, saiya kuma tabbatar min da mafarki dai nayi kenan, bawai gaba da gaba ba yace muyi Auren Contract ba kenan.
Innalillhi, mike shirin faruwa danine ni Hussaina, hawayen dasuke neman zubomin nai k’ok’arin had’iyewa, Munubiya kanta tashiga kogin mamakin yanda Galadima yay tamkar ma komai baita6a faruwaba, shin kodai shi baiga abinda yafaru a jaridar baneba?….
Batada mai bata amsa, su safara’u ma magana suketayi k’asa-k’asa a tsakaninsu, alokacinne kuma matan gidanmu suka shigo.
Mamansu yaa hameed take tambayar wai wananan bashine Galadima ba na jikin jaridar nan?.
“wlhy shine kuwa mama”. cewar Fiddausi.
Haleematu ta kar6e da fad’in “mama kinga yanda ya nuna kuwa? tamkar ma bai gane su twins ba balle ya nuna yama San abinda yafaru a bayabaya tsakaninsu”.
Murmushin mugunta mamansu ya hameed tayi, “yo ai dama saboda irin haka ake cewa Ku kare mutuncin kanku, danshi namiji komi yayi adone, sannan shi d’an manyan mutanene, ko kallonsa da abin babu mai sakeyi, amma Ku gashi har ana fasa aure, kamun kai dai dad’i gareshi ai dama, kum…….”
Shigowar doctor tasaka maman su yaa hameed yin shiru, korarsu yayi gaba d’aya, yace subarni Na huta.
Basuso hakanba, dan shirya cin zarafinmu maman yaa hameed tayi.
Daganan gida suka wuce suna ‘yan gulmace-gumacensu da dariyar mugunta.
?????
Galadima kuwa yana gama zagaye-zagayensa a asibitin na duba marasa lafiya gida suka wuce.
Bayanin doctor yabashi mamaki, wai wannan ‘yar yarinyar keda hawan jini, itako miyayi zafi haka a rayuwarta”. wani sashi na zuciyarsa yabasa amsa da (6atancin da akai muku).
Lips d’insa ya cije yana jan dogon tsaki, shikad’ai yasan burin daya d’auka akan dukkan Wanda yasamu da hannu a wannan lamarin.
Sun biya birnin gayu plaza yaga komai yana tafiya dai-dai, daga nan suka koma masarauta.
????
Nima a ranar da daddare aka sallamoni, nadawo gida nacigaba da shan Magani, yayinda biki keta gaba towa kuma.
Har yanzu innarmu tana cikin damuwa dani kaina akan zancen aurena daba asan taka maimai angoba.
Zancen galadima kuwa ai tini na shareshi, dan nabarsa amatsayin mafarki nayi, musamman kuma dana bincika banga number wayan daya baniba, a wayata kuma tun randa na tura masa massege na gogeta dama gudun kar wani yagani.
Yanda ‘yan gidanmu suketa rawar kai akan bikin saran ‘yan uwanmu innarmu batayi, bazama ka ta6a d’auka itama zata aurar da ‘ya’ya har biyu baneba.
Mama Rabi’a ce ke tsaye akan komai, sai aunty salamah datazo da magunguna ta d’id’d’irka mana, mu bamusan namiye ba, takumace mudinga sha, saikuma had’ad’d’en sabulun wanka da mai data had’a mana, ga wasu turare masu sirrin k’amshi, takuma gargad’emu daga yanzu muna saka hijjab duk inda zamuje da nik’af, domin fatarmu tasami nutsuwa kar rana ta maidamu gidan jiya.
Ni dai dagani har munubiya da to kawai muke binta, kuma duk abinda tace muyi munayinsa.
Abbanmu yakira mama Rabi’a yabata wasu kud’i akan tak’ara amana siyayyar kayan kitchen da ‘yan uwa keyi, tunda ita innarmu bawasu dangi ne da itaba dazasu tara mata.
Sosai tamasa godiya, sanan tasanarma innarmu, ko babu komai taji dad’i, harma tamasa godiya itama.
Tafiya mama Rabi’a tayi da k’ud’in, washe gari suka Shiga kasuwa itada inna lami, kaya masu k’yau suka sissiya mana dai-dai gwargwadon k’arfinmu. aka adanasu gidan inna lami duka.
*_kwanci tashi_*
Babu wahala wajen ubangiji, yau gashi abinda kowa yake jira yazo, domin kuwa ankawo lefen Haleematu, gaskiya angonta yayi k’ok’ari, akwati 5 abinta, kuma kaya masha ALLAH, sai-dai hakan bai hana ‘yan gidanmu gulmaba, washe gari kuma aka kawo kayan Safara’u da Fiddausi.
Suma dai kam saidai mak’iyi, amma jikin maman safara’u yayi sanyi, dan gaskiya kayan sauran duk sunfi nata. Itama dai akwati biyarne, amma kayan cikine basukai na sauranba.
Again washe gari saiga na Fauziyya da Munubiya, mama Rabi’a tasan komai dake wakana a gidanmu, dan haka suka dage sukaima Munubiya lefe na ‘Yar gata, wlhy ba fariyaba lefenta yafi na kowa, ranar har kukan dad’i nayi, domin banyi zaton hakanba. itama dai fauziyya angonta yayi k’ok’ari gaskiya.
Tuni hassadar matan gidanmu tafito fili suka fara yada habaici wai an aro kaya anzo ana musu burga, da anyi aure sai ake maidawa d’ai-d’ai.
Dagamu har innarmu babu Wanda ya tanka musu, dan munsan yau dai mune aciki sune a kwana????.
Rashin kawo nawa lefen kuwa ko a kwalar rigata bai dameniba, dan bama sanin mijin nayiba balle nadamu dawani lefen banza. saima Munubiya ce harda kukanta rurus akan wai saidai araba mana kayanta mu biyu.
Nifa dariyama tabani wlhy.
Ganin ni babu lefe yasaka su baba k’arami siyomin kaya masu k’yau na fitar biki har kala 10, aka d’inka min, sai takalma da bags da veils masu k’yau suma.
Habaici dai kam munshashi wa su innaro da matan gidanmu, danma ita innaro gwaggo Safiyya na hanata ne, da bamu san tijarar dazata zubarba a ranar kam.
A haka aka shiga satin biki, mu bamu wani gayyaci k’awayeba, daga Bilkisu sai su Ayusher, ashe Ayusher ta buga invitation na k’awaye suka raba itada Bilkisu bamu saniba.
Abin mamaki ranar kamu sai ganin k’awayenmu mukayi harna secondary.
munji dad’in hakan sosai kuwa.
A ranar kamun saiga wasu mata hud’u sunzo wai dangin miji nane, su mama Rabi’a sukayi musu tarba ta mutunci, ba a nuna musu komaiba kuma, dukda a yanayin shigar talauci da sukazo, saidai zund’e da gulma irinta ‘yan biki. Matan gidanmu kam komai ya kaimusu dai-dai, sai dariya da yada magana a kaikaice sukeyi. Da aka kaisu su gaisa da innaro taita musu yatsine-yatsine, harda tanbayarsu waisu garinsu ba’a lefene? dabasu kawoma jikartaba?.
Basuce komaiba sai murmushi kawai da sukayi.
Washe gari kuma akayi k’unshi, mudai namu aunty Salamah ce tamana, tana tsaye akan komai namu tamkar yayarmu ciki d’aya.
A ranar kuma akaje a kaima sauran amaren jere, harda Munubiya, amma ni banda ni, tunda ba’asan ina za’aje ayiba.
Aranarma Munubiya tayi kuka, nidai ina k’ok’arin danne zuciyata, saboda nabama innarmu kwarin gwuywa karta tada hankalinta.
Aiko Alhmdllh ta dake tamkar komai baya damunta, tashige cikin abokan arzik’inta sunata harkoki. kowanne 6angare yacika da dangin matan gidanmu, abin tamkar fariya, namu 6angarenne kawai keda sauk’in jama’a, hakama gidan innaro yacika da danginta da dangin kakanmu.
Tunda aunty Salamah tagama yimana k’unshi da gyaran kai dana jiki sai muka nufo hanyar gida, saboda yaa marwan yazo neman Munubiya harsau biyu, sai kiran wayarta yake yana masifa saboda tare yake da abokansa. hakan yasa muka taho gida.
Gashi Yau zamuyi sister’s and brother’s day, duk da dai saima da yamma.
?????
Galadima dake zaune a makeken falon Ummu hasheem, yanata bin jerin akwatinan da kallo, ga wasu daga ‘yan uwansa zazzaune sunata kuma kimtsa kayan, aunty Mimi ta kalleshi, “kunga zanma mantafa, my k’ani ina kayan dana baka kayo gaba dasune?”.
Yatsine fusaka yad’anyi yana gyara zamansa, “nifa nama manta inda suke, shiyyasa nace bazan d’akkoba ai”.
Wata uwar harara ta watsa masa tace, “lallai bakada kai yaro, bar ganin matarka za’a kaimawa, suka 6ata biyana zakayi ehe”
Murmushin gefen baki yasaki yana lumshe idanu, cikeda k’asaitarsa yace, “Samha! jeki bedroom d’ina ki duba, maybe suna can“.
“bama kada tabbas kenan?” cewar mom.
Bud’e idanunsa yayi yana murmushi, “no mom insha ALLAH sunama can. ni yanzu kam kun sallameni natashi natafi? dan zansa aje a d’auko su Akash a airport ”.
Ummu Hasheem tace “kaje kawai, dama dan kaga kayanne, tunda kuma kace komai yayi ai shikenan”.
Mik’ewa yayi yana fad’in “thanks you Ummu, nabarku lafiya”.
Tunda yasamu yay escape sai ya sauke ajiyar zuciya, shi dariyama suke bashi dagasu har su papi, su Dan basu san auren shekara d’aya bane dabasu dinga wannan rawar k’afarba, sun wani zauna sun had’a uban kayan lefe, yad’an ta6e bakinsa kawai yana nufar sashensa.
Komai na gidan sarauta mai tsarine, dan haka kai lefen MUNAYA da suke shirin yima a tsare akayisa, (papi ne yace Subari sai yau ana gobe d’aurin aure sai akai, tunda gidan su munaya basusan kosu su wayeba).
An tsara iya wad’anda zasu kai lefenne.
Bayan an gama zuba akwatunan a wata farar mota mai k’yau sabuwa dal aka rufe, driver ne kawai zai shiga cikin motar.
Sai kuma motoci 6 da aka zaba wad’an da zasu kai lefen.
Motar farko dogaraine, ta biyu kuma kuyangi ne, sai guda biyu ‘yan cikin gidansu Galadima ne su hud’u, ko wacce mota mutum biyu, sauran biyun kuma ‘yan 6angaren masarautar su Momma, suma su hud’u, kowacce mota biyu. sai Samha datasa kuka saitaje taga matar Uncle Sam.
Aunty mimi harta korata da zare mata idanu saiga Galadima motocin na niyar tashi.
Da kansa yabud’e mata gaban motar da aka saka akwatinan yace tashiga nan, idan taje ta gaida masa matarsa.
Cikeda d’oki tace zataji Uncle Sam, bazaka bada komai akai mataba.
Kansa yad’an dafe dan yakula Samha na neman k’uresa, shikuma yafad’a mata maganarne domin yanason agaban jama’a yadinga yana tsantsar k’aunar Munaya, a bad’ini kuma suna zaman aurensu na contract, shiyyasa ko lefennan baiji tsadar kud’in saba yabud’e bakin aljihu aka zuba kaya masu azabar k’yau, gakuma kud’in da Mai martaba yabada shima, dakuma sauran k’annen mahaifinsa.
Hannu yasaka a aljihunsa yana duba kozai samu wani Abu, amma babu komai sai wata chocolates guda biyu, wadda ya d’akkota ne zaiba khaleel d’azun yama manta, mik’ama Samha yayi yace “gashi kibata”.
Da dariya samha ta kar6a tace “Uncle ta gode to”.
Kansa kawai ya jinjina mata ya shirin barin wajen.
motocin suna fita daga masarautar saiya sauke ajiyar zuciya kawai.
????
Gidanmu ya cakud’e da hayaniyar da akasan gidan kowanne biki da ita, bare mu daya kasance har auren mutum 6, dukda sai gobene d’aurin aure kuwa, yara sunata wasansu da tsalle-tsalle.
A jere motocin suka shigo cikin anguwar, jama’a sai binsu da kallo sukeyi, dai-dai k’ofar gidanmu driver daya san gidan yay parking.
Babu Wanda yay mamaki a ‘yan kawo lefe, domin kuwa dama labari ya karad’e masarautar cewar Galadima’yar talakawa zai aura.
Dogarawa da kuyangi suka fara fitowa, sannan suka bud’e motor da akwatina suka suka fara fitarwa. Nanfa jama’ar anguwa sukayi cirko-cirko suna kallon ikon ALLAH dan ganin akwatinan da aketa fitarwa daga mota.
Batare da neman isoba Kuyangin suka fara kwasar akwatinan suna shiga dasu gidanmu…………..???
??????
Team innaro kufito mu caskale yau????????
???????????????
Asha weekend lafiya?????
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu??????_*
*_Typing??_*
*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_
*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce????_*
No one has commented yet. Be the first!