Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 13


Raina Kama Book 1 Page 13
Viral

??1?3?

…….Mun d’anji sanyi a ranmu, ganin kiran bamu kad’ai baneba, hardasu Safara’u Ashe, waje muka samu muka zauna, sannan muka gaidasu.
Fiddausi kad’ai ake jira, itama babu jimawa sai gata ta shigo da sallama, duk muka amsa, ta gaida su Abba.
Falon yay tsit Na mintuna biyu, sannan Abbanmu yay gyaran murya, kallonmu yake mu duka cikin nazari, ganin muduka mun hallara yace “mun kiraku nan ne saboda dalilin abinda yafaru kwanan nan, hankalina yakasa kwanciya da zamanku a gabanmu, mun yanke shawara nida ‘yan uwana zamu aurar daku duka kawai, kowace saita cigaba da karatunta a d’akinta, muma hakan zai sama mana kwanciyar hankali. dan haka kowacce saita sami mai zuwa wajenta ta sanar masa munason ganin magabatansa inhar da gaske yakeyi”.
gaba d’aya muka amsa da to abba kanmu ak’asa.
Wasunmu murna suke da hakan, amma banda ni da Munubiya, dan bamuda wasu tsayayyu a hannu, bawai samarinne bamu dasuba, a’a wad’anda zamu kawo amatsayin Na aurene matsalarmu.
Maganar Dady ce ta katsemin tunani, danaji yana fad’in su sutashi suje, amma ni Na tsaya.
Haka suka fice suka barni, duk tsoro yakuma cika zuciyata. bayan fitarsu baba k’arami yanuna min gabansu alamar Na matso.
Tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki haka natashi Na isa gabansu, na zauna kaina ak’asa.
Baba k’arami yace “Munaya!”.
Muryata Na rawa Na amsa da “na’am baba”.
Ya gyara zamansa sosai, “Munaya na sanki bak’ya k’arya, kifad’a min tsakaninki da ALLAH miye had’inki da Galadima?”.
Gabanane yafad’i daaam!, nai k’ok’arin had’iye kukan daya taho mini “wlhy Baba banida had’in komai dashi, hasalima ban ta6a saninsaba sai awajen hawan sallah, shima ba ganin fuskarsa na ta6a yiba, sai kuma randa mukai karo dashi a filin idi ina neman su kamal, kuma wlhy aranar hak’uri kawai nabashi, koma amsamin baiyiba yatafi, ni banma san shibane alokacin”.
“amma miyasa aka buga hotonku kuna cikin plaza d’insa?”.
“Dady kuyi hak’uri, tabbas nasan munyi laifi anan, amma Ku yafemin, dan nasan da bamuje plaza d’inba a daren da k’ila hakan bai faruba, amma wlhy abinda yafaru shine……………….., cikin nutsuwa ta zayyane musu komai, saidai batace Munubiya ce zata fad’inba, tace itace.
Koda basuga ainahin abin da idonsu ba sai zukatansu sukayi sanyi, baba k’arami yace “to ALLAH ya k’yauta, wannan akwai wani Abu daban dabamu saniba acikin lamarin, ALLAH ya warware komai cikin sauk’i”.
Duk mukace amin.
Dady yace, “Munaya! bisa hak’uri damukaita bama yaya kin sami sassauci akan sati 2 daya ce ki fidda miji, yanzu saiki nutsu ki kawo kamar sauran ‘yan uwanki, insha ALLAH bayan babbar salla zamu aurar daku gaba d’aya kawai, ALLAH yayi muku albarka kinji, kucigaba da kare mutuncinku, sannan Ku koma zuwa makaranta tunda abin ya lafa”.
Kai na gyad’a sannan nayi godiya.

Na iske innarmu da Munubiya jigum-jigum a falo suna jiran dawowata, nasami waje na zauna jikina a sanyaye.
Innarmu tace, “miya faru kuma?”.
Guntun murmushi nayi INA share kwallar data zubomin, “babu komai innarmu, sun tanbayeni gaskiyar abinda yafaru ne, sannan since sun janye maganar sati biyu nafiddo miji da sukace nayi. nima za’a had’a danawa zuwa bayan salla kamar su Munubiya, kuma since mukoma makaranta”..
Daga Munubiya har innarmu ajiyar zuciya suka sauke, “to Alhmdllhi, ALLAH yabaku mazaje na gari”. ‘cewar innarmu’.
A zukatanmu muka amsa mata da amin.

Washe gari.
https://2gnblog.blogspot.com/
Mukayi shirin zuwa makaranta, gudun abinda zaije yadawo sai muka saka nik’af dagani har Munubiya kamar yanda innarmu tabamu shawara muyi.
Alhmdllh tunda muka fita bamuci karo da abinda ya Sosa zuciyarmu ba, saboda fuskokinmu arufe suke.
A ajima babu Wanda ya shaidamu sai Bilkeesu, nanma dai munyi mun fito lafiya babu wata damuwa. amma saboda a d’ar-d’ar Muke bamu wani sakeba, ana fitowa lectures muka nufi gida.
Haka muka cigaba da zuwa makaranta kulum fuska arufe, ko cikin anguwa za’a aikemu saimun saka nik’af, dan yanzu fuskokinmu sunrigada sun zama sannanun fuskoki….

https://2gnblog.blogspot.com/
??????????

Yana gama kimtsawa yafice, ko abincin da Samha ta shirya nasa bai sauraraba, kai tsaye yanufi Hospital d’i. da Abie ke jinya.
da jakadiya yafara cin karo tana rik’e da Khaleel a hannu, khaleel yakwace yataho da gudu yana fad’in “Uncle oyoyo”.
Hannayensa ya bud’e masa yafad’a jikinsa, ya shafa kan yaron yana fad’in “my boy ykk?”.
“lafiya Uncle Sam… yaushe kadawo?”.
Murmushi Galadima yayi, yad’an ja kumatun khaleel “to maganatu yau na dawo”.
Dariya yaron yayi, zai sake joho wata maganar Galadima ya d’ora yatsansa akan bakin yaron alamun yayi shiru. Shirun kuwa khaleel yayi dan yasan halin Uncle Sam.. saraii.
Jakadiya ta rissina tana gaidashi, amsawa yayi fuskarsa da ‘Yar fara’a, ya tambayeta ya jikin Abie.
“jiki Alhmdllh ranka ya dad’e”.
Kansa kawai ya jinjina mata yay gaba rik’e da hannun Khalel.
Da sallama ya shigo d’akin da Abie ke jinya, d’akine babba kamar Bana asibitiba, daka gani Kasan anyisane saboda manyan mutane irinsu, Momma na zauna akujerar gaban gadon da Abie ke kwance, gadon Kansa bawai ainahin gado bane na asibiti, duk wasu na’urori ne ajikinsa, da alama sune suke taimakama jikin Abie d’in, k’umba Momma ke yanke masa.
Aunty Mimi na zaune bisa kujerun da aka shirya a gefe tamkar falo, System Ce agabanta tana danne-danne.
Sallamar Galadima yasata d’agowa tana murmushi, “My k’ani oyoyo” tafad’a tana ture system d’in daga cinyarta.
Murmushi yamata shima, cikin maganarnan tasa ta k’asaita maikama da anmasa tilas yace “my dear aunty barkanki”.
Hannu tasa tad’an bigi damtsen hannunsa, cikin wasa tace barka zakace ba bagyka ba”.
Shafa Inda tad’an bigesan yakeyi yanda 6ata fuska kamar wani k’aramin yaro, “ALLAH akwai zafi aunty Mimi, wai har yanzu ban girma da buguba awajenki?”.
“tab ai da sauranka, sai randa kayi aure zan daina”.
Bakinsa ya ta6e yak’arasa inda Momma take yana fad’in, “aiko k’yadad’e baki barinba kenan”.
Momma dake murmushi saboda drama d’in tasu ta kalli Abie da shima fuskarsa take a washe alamun yayi farinciki da ganin d’an nasa.
Gabansa yaje ya durk’usa, saitin Face d’insa, ya saka hannunsa cikin NASA fuskarsa d’auke da murmushi yace, “my Abie barka da rana”.
Da idanu Abie ya amsa masa, dan sune bakin maganar yanzu.
Yakuma masa magana da ido alamar yaka barosu?.
Murmushi Galadima yayi na takaici, sannan yace, “mai martaba na gaidaka, shima zaizo nextweek”.
Farin cikine Yakuma fad’ad’a a fuskar Abie, dasu sukasan yanayinsa, sukad’ai zasu iya fahimtar farin cikinsa ko damuwarsa, musamman ma Momma.
Momma dake kallonsu tayi murmushi, Galadima ya maida kallonsa gareta, “Momma na yana sameku?”.
“Alhmdllh Muh’d, yaka barosu?”.
Baki yad’an ta6e sannan yace “lfy lau, ya jikin Abie?”.
“jiki Alhmdllhi, dan randa ka tafi yatsun hannun damarsa sund’an motsa”.
Da Sauri Galadima yace “da gaske Momma?” yay maganarne yana kallon hannun Abie d’in, sannan cikeda farin cikin ya sumbaci hannun yana fad’in Alhmdllh ala kulli halin, ALLAH yabaka lafiya my sweet Abie”.
Lumshe idanu Abie yayi farinciki na k’ara fad’ad’a a face nashi, aunty Mimi da momma da jakadiya suna kallonsu cikeda tausayi suka amsa da amin. khalel yata6a kafad’arsa, juyowa yayi yana kallonsa. yaron yakai hannu yana sharema Galadima hawayen dasuke kwance a kumatunsa. galadima yajawosa ya rungume yana sumbatar kan yaron, fuskarsa d’auke da murmushi.

???

Yau mune k’arshen tafiya school, saboda lectures d’in yamma ne damu, Fauziyya kuma batada lafiya bazatajeba.
Kasancewar abubuwa sun kuma lafawa yau sai bamu saka nik’af ba, amma yana rik’e a hannunmu idan mun shiga cshool zamu saka.
Mun fito bakin titi muna jiran taxi ko napep saiga wata bak’ar mota wulik ta faka agabanmu, dagani har Munubiya d’auke kanmu mukayi gefe.
Mai motar ya sauke glass d’in yana kallonmu, sallama yayi mana, Munubiya ta amsa, nikam koma kallo bai isheniba.
Ganin haka saiya bud’e motar yafito, matashin saurayine bak’i k’yak’yk’yawa mai yawan fara’a. Yace, “haba ‘yan mata, babu fad’a miya kawo gaba”.
Cikeda tsiwa nace “sai aka cemaka mu ‘yan matane? to matan aurene”.
Murmushi yayi, sannan ya gyara tsayuwarsa, “dear hakan ma dakikayi yakuma tabbatar min da Bahaka baneba”.
d’an hararsa nayi na d’auke kaina, danni yanzu maza duk haushi suke bani wlhy.
Dariya yayi, “oh sweety karkisa na sume mikifa a titinnan”.
Ganin yana neman shiga hancinmu yasani jan hannun Munubiya muka bar wajen, k’yalemu yayi Yakoma mota ya zauna. har muka sami abin hawa yana kallonmu. haka yayta bin mai napep d’in har k’ofar makaranta, daga nan kuma bamusan ya akayiba mudai muka shige.

Kwana biyu da faruwar haka muna wanki a tsakar gida saiga ya Anas yashigo, ya kallemu yana murmushi, twins cikinku waye mai saurayi mai bak’ar mota?”.
Mu duka kallonsa mukayi, gwaggon Haleema da maman safara’u dake aiki a tsakar gidan suma duk suka kallemu.
Da sauri Munubiya tace “munaya Ce yaa Anas”.
“kije to yana jiranki a k’ofar gida”.
harara na dallama Munubiya “wlhy Munubiya k’arya dai babu k’yau”.
Dariya tayi tacigaba da wankinta, “kitashi kije kina 6ata masa lokaci”.
Hijjab na d’auka nafita danufin zuwa na sauke masa masifa na dawo.
Gwaggon Haleematu da maman Safara’u suka bini da kallo cikin wani yanayi. oho ni bammasan sunayiba.

Jingine da motarsa na gansa, sanye yake da shadda ruwan zuma, harda hula, sa6anin ranar damuka gansa da k’ananun kaya, kwarjini yamin nakasa masa masifar danayi niyya, namasa sallama sannan nace “miya kawoka k’ofar gidanmu? waya nuna maka ma?”.
Yad’an murmusa, “miyake kawo saurayi gidansu budurwa?”.
“oho maka” Nafad’a cikin kauda kai gefe.
“kimga baby sorry, mu ajiye wannan drama d’in, ni bada wasa Nazo nanba, tun randa na ganku keda ‘yar uwarki kuka rikatani, nasa a raina duk wadda ALLAH yabani cikinku tamin, bansami kwanciyar hankaliba saida na binciko gidanku, sunana Haidar Mustapha”.
Shiru nayi ban tanka masaba.
Yay murmushi yana matsowa kusa dani, “please mana baby, kimin magana?”.
Da k’yar ya sami na amsashi sannan nima nafad’a masa nawa sunan. abinda na fuskanta da haidar shi mutumne mai sauk’in kai, sannan ko kad’an banga alamun yaudara ba tattare dashi.
Cikin kwanaki kad’an mungama sabawa da haidar, sabawa maiban mamaki, wadda nikaina har mamakin kaina nakeyi wlhy.
Alokacinne kuma yaa Marwan shima ya nuna yanason Munubiya, wayyo zokuga farin ciki wajen iyayenmu, tamkar su zuba ruwa a k’asa susha dan dad’i.
Wannan Abu fa ya bak’anta ran ‘yan gidanmu, sunso ace munyi kwantai, har agama sakama ‘ya’yansu rana mu babu mazaje a hannu, amma ALLAH ya fisu ai.
Kud’in Munubiya aka fara kawowa gidanmu, daga nan saina Safara’u. nima saiga iyayen Haidar sunzo, ranar har kukan dad’i mukayi muda innarmu, duk wani masoyinmu zai tayamu murna akan wannan al’amari, dan ba’a ta6a tunanin zamu iya samun mazaje da wuri ba saboda abinda yafaru.
Sauran ‘yan uwanmu ma duk ankawo kud’ad’en aurensu, dandanan aka tsaida ranar aure, watanni uku kacal, bayan salla babba da wata biyu.
Zuwa yanzu kam hankalinmu ya kwanta, sai dai matsaloli na gidanmu da basa k’arewa, saikuma abinda yafaru tsakaninmu da Galadima, wani lokacin mukan fuskanci tozarci daga wasu jama’a idan mun fita, tunma muna zama muyi kuka har zukatanmu suka fara dakewa.
Galadima kam bamu sake koda jin d’uriyar saba, hakama Fu’aad, tunima Haidar ya mantar dani wani Fu’aad gaba d’aya.
Ahaka babbar Salla tafara gabatowa. Masu shiri natayi, nikam dai babu mu aciki, dagani har Munubiya munyi alk’awarin babu inda zamuje sai gidan mama Rabi’a……..

Munshiga bikin salla lafiya, inda iyayenmu sukayi layya kamar yanda kowacce shekara suka saba, itama innaro anmata, babu inda mukaje wannan karon, su Safara’u dai ansha yawo, ranar suyar nama kuma saiga dukkanin amare sunzo yawon salla, abin tamkar had’in baki, kowaccensu tayi 6ul-6ul da ita, harma damasu tsarabar ciki.
Kowacce jinta take a sama, mijinta yafi na kowa, iyayensu kam anata baza hak’wara da tink’aho ana zuba mana habaici.
Babu Wanda ya tanka musu acikinmu, dan innarmu ta hana.
wajen Ayusher mukejin wai babu Galadima a hawan salla wannan karon, hakan bai dameniba, danni baya gabana, nama manta dawani Galadima can.
Bayan gama bikin salla da kwanaki uku saiga wani tashin hankali.
Iyayen Haidar sunzo wai abasu kayansu sun fasa, ance musu ni ‘Yar iskace.
Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un. Yau munga tashin hankali muda innarmu, kuka da hawaye innarmu keyi itada mama Rabi’a, haka aka had’a kayansu aka basu.
Innaro tashigo tafara tata tsiya babuji babu gani, sai zuba cin mutunci takeyi ga innarmu, ‘yan gidanmu natajin dad’i, jisuke kamar anmusu gafara da fasa aurennan nawa, aganinsu yaza’ayi ‘ya’yansu suna auren masu kud’i nima na auri mai kud’i, ai bazai yuwuba..
Cikin kuka nakira Haidar ina tanbayarsa miyasa zaimin haka, yasan tun farko ba sona yakeba miyasa yazo gidanmu har iyayensa suka shiga.
“k dalla malama yimin shiru, ni mahaukacine zan auri yarinyar da aka buga hotonta jikin jarida wani na kissing d’inta, ok da an 6oyemin za’a bani sauran wani Ashe ked’in karuwar Galadima ce, to ALLAH ya toni asirinku dagake har iyayen naki, ko a hanya muka had’u karki kuma nuna kin sanni ma”.
Baki na bud’e da nufin maida masa murtani ya yanke wayar, nayi saurin kuma kira amma sai najita arufe.
Kuka na fashe dashi, bansan miya faruba sai dai najini ak’asa kawai.
Cikeda tashin hankali Munubiya tayo kaina tana kuka da girgizani.
Dandanan d’akin yacika dasu Dady, babu alamar rai atare dani, hakan yasa aka d’aukeni da gaggawa sai asibiti………

 

?????

A 6angaren Galadima kuwa wasu ayyukane suka d’auke hankalinsa, gaba d’aya yayi busy saboda kamfaninsu na k’ok’arin fidda wata waya sabuwar k’ira.
Abinda ya faru kuwa a Nigeria ya watsar dashi gefe, saboda gargad’in da doctor d’insa yamasa akan yarage yawan damuwa, saboda ciwonsa yana k’ok’arin tashi.
Haka yadage yacire komai d’in, amma har yanzu yasaka amasa aikin bincike ta k’ark’ashin k’asa, sannan iyalan manager sun ku6uta suma, yabar Nigeria da sati biyu suka sakosu.
Gaba d’aya ya ajiye duk wani abinda yashafi Nigeria a gefe, ko bikin salla bai hakarta ba, sannan zuwan dayankan yi duk karshen wata ma ya daina, Momma batace dashi komaiba akan k’in zuwan nasa.
Dan lokacin da mai martaba (mahaifin momma) yazo sun tattauna sosai akan abinda yafaru, shine yace Galadima yad’an tsahirta da zuwa Nigeria nawani lokaci, idan komai ya lafa sai acigaba da bincike, dan wad’anda suka aikata sumafa baza suyi barciba, yanzu idonsu abud’e yake akan komai, amma idan anyi burus dasu komai ya lafa sai a d’auki mataki. Wannan yasa bai sake zuwaba, gameda business d’insa nacan kuwa Harun yana tsaye akan komai.

Fitowarsa kenan daga office zaije gida yad’an kimtsa sannan yaje asibi, wayarsa tashi ruri, zarota yayi daga aljihu ya duba, ganin Muftahu a kan layi saiya maida wayar cikin aljihu kawai batare da ya amsaba.
Hannu yabama beejay abokin aikinsa sukayi sallama akan saikuma gobe. yana k’ok’arin shiga motar kiran yakuma shigowa, shiga yayi ya zauna sannan ya d’aga, suka gaisa da Muftahu, ya tambayesa jikin Abie.
Shikuma ya amsa da Alhmdllh.
Muftahu yace, “ALLAH yasa ban takuraka ba? Inason muyi magana ne dama”.
Kwantar da kansa yayi jikin kujera ya lumshe idanunsa, cikeda k’asaita ya furta “ina saurarenka”.
Daga can Muftahu yay murmushi, sannan yace “dama akan yarannan ne, d’aya daga cikinsu an fasa aurenta, wai Wanda zai auretan yace yafasa sabo…da sa… sa…. yakasa fad’a saboda maganar tamasa nauyi abaki”
Galadina yace “kafad’a mana, kasanfa bana son kwana-kwana a magana ni”.
“wlhy maganarce babu dad’in ji, ca yayfa wai ita karuwarka ce, yanzu haka yarinyar tana asibitima”.
Da k’arfi ya cije lips d’insa, zuciyarsa na suya, saikuma ya saki guntun murmushin takaci, yatashi zaune yana bud’e idonsa, “humm Muftahu waye shi yaron dazata aura d’in?”.
“wlhy ban saniba nima”.
“o right karka damu, zanyi tunani akan lamarin, ni bamma duba bayanai daka turomin akan yarinyarba fa, abubuwa sunmun yawane wlhy. amma masu bibiyar tata basuga wani abunda ya shafi waccan maganarba?”.
“Gaskiya basuga wani abuba sa6anin tunaninmu, ammafa bama yarinya d’aya bace ba, twins ne, kaduba bayanan kagani”.
“ok sai munyi magana kenan”.

Bayan sunyi sallama yay shiru yana tunani a ransa, da gani kasan ransa a6ace yake, ya furzar da huci daga bakinsa sannan ya tada motar yatafi. idonsa yayi jajir saboda bak’in ciki, yanzun har takai wani yafasa auren wata akansa? waye yamasa wannan abin? miya masa ne da zafi haka ya tozartashi? wlhy yayi alk’awarin duk Wanda keda hannu akan wannan tozarcin da akai masa bazai d’aga masa k’afaba, dolene yayi dana sanin saninsa.
Da wannan tunanin ya k’arasa gida.
Babu kowa a gidan sai jakadiya, su Sauban suna makaranta, Aunty Mimi da Momma kuma suna asibiti, jakadiya ta rissina tana gaidashi, hannu kawai ya iya d’aga mata ya haye sama.
Binsa tayi da kallon tausayi, hakan da yayi mata ya nuna ransa a 6ace yake, danshi mutum ne mai girmama nagaba dashi, dukda tana a k’ark’ashinsu bai ta6a wulak’antata ba, wannan tarbiyar mahaifiyarsu ce kuma.

Koda yashiga rigarsa kawai yacire ya zauna a bakin gado, medical glasses d’insa yasaka sannan yajawo System yabud’e, Emailil na Muftahu ya shiga.
Dukkan bayanai da tarihin su Munaya ne awajen.
Gaba d’aya ya nutsu ga abinda yake karantawar, shi mamakima abin yabashi, sukuma wane irin gida wad’annan yaran suka fito haka? Wani abun yakan bashi dariya (sai dai yakanyi dariyar ne a zuciyarsa), wani kuma haushi, tsaf yagama karanta tarihin yaran masu kama da juna.
Ya mik’e yana zagaye d’akin da tunanin miye mafita, har yanzu zuciyarsa bata bar karanta masa da hannun wad’an yaran aka masa wannan abunba, sai dai shi kansa yana tambayar kanasa mizaisa su aikata? miye kuma ribarsu bayan suma hardasu aka tozarta?. yanzu kuma zuciyarsa na masa wani tunani daban bayan yaji tarihinsu.
Zuciyarsa na cigaba da tunzurashi akan yayi amfani da damar k’arshe wajen bincikensa, tunda yabi dukkanin sauran bai samu wani bakin zareba.
To amma kuma wannan ai ba tarbiyyar Malam bahaushe baceba, daga baya kuma idan komai yafitofa? wane kallo kuma za’a masa?, shinma zata iya fahimtarsa kuwa? dan irin wannan abun yakan farune a labaran films ko Novels, to amma wannan ce damarsa ta k’arshe ai kawai, dolene ya jefi tsuntsu biyu da dutsi d’aya kenan?………….???

 

Tirk’ashi, Nikam dai nakasa fahimtar wannan cirkud’ad’d’en tunanin na Galadima?, fan’s koku kun fahimta Ku fassara mana???.

 

 

 

*_Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu??????_*
*_Typing??_*

 

*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_

 

*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply