Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 70


Farhatal Qalb 70
Viral

PG:70_

*_FINALE/END (KARSHE)_*

_______

**Jikin na Marka ya sake saaki. Baki daya sai dai a kwantar a tayar. Sauki daya ta samu ta hanyar maganar ta da ta dawo. Amman itama dakyar maganar ke fita. Cikin wata iriyar murya mai wahalar wa.

Najib kusan kullum yana gidan. Daya dawo daga makarantar boko zai je gidan. Da ke yana ajin karshe na babbar makaranta ta sakandire.

Umma Hadiza na kokarin temakawa da su Marka da yan kudade na daga ribar kasuwancin tah. Tana yi ne kawai saboda Allah da albarkacin yaranta da haifa daga gidan.

Haka ma Deluwa da ke kokarta wa a nata bangaren. Don itama tanada marar lapia acikin yaranta yan biyu.

Zahara’u kuma ta nuna gajiyawa. Ba sosai take zuwa gidan ba ma. Ta kance Na’Ateeku ya hanata. Ko kuma yara ba lafiya.

Malam Nalado ya tsaya tsayin daaka akan rashin lafiyar mahaifiyar sa Marka.

Duk kuwa da ba tsayayyakin aiki ne da shi ba. Da ake biyan sa, Aikin karfi ya saka a gaba ka’in da na’in.

Ya kan je kasuwa ya yi wa yan kasuwa daako su dan bashi na cin abinci. Sai ya soke kudin sa a aljihu. Ya sake gangara wa wajen maagina yayi musu leburanci. Ko na ebo musu ruwa su ko kasa da daukar bulalluka.

Ta hakan ya ke samu ya rufawa kansa asiri da kula da lafiyar Marka. A boye kuma ya kan bawa yaran inna Sa’adatu su kai mata gidan su.

Deluwa kuwa wani lokacin ma ita kan temaka masa. Idan tayi cinikin abincin sayarwar da ta ke.

Su zabba’u kuwa daman ba sa bi takan yiwa Marka wani abun arzikin. Kan su kawai suka sa ni. Su kance a baya ai dama Nalado da zahara’u ta nuna tafu kauna. Don haka su babu ruwan su da harkokin ta.

Su kanzo dai su dubata da dan lemo da ayaba. Wataran kuma su karkade jikin su su tafi. Babu ko sisi.

×××

Marka na tsakar gidah kaman kayan shanya akan tabarma .

Daga gefen wajen dakin girki kuwa Deluwa ce tanata jefa danwake.

Wani yaro dan gidan zahara’u yana wasa da wani kara ya daga shi sama ya cilla. Bai fadi a ko’ina ba sai fuskar Marka .

Ta ke ta kece da kuka. Cikin dashasshiyar muryar ta mai fita a sarke ta ce,

“Shege, Dan iska… Ka ci malafar kan uban ka Adamushe. Matsiyaci. Gayyar masifa.”

Gashi ba dama ta saka hannu ta mulmula wajen. Yaron ya kece da dariya.

“Yi hakuri marka ..” ya fada yana sake tuntsirewa da dariya .

“Kai mekayi Abbati? Matsa daga nan, Sannu Marka ..” cewar Deluwa da sai da ta jiyo maganganun Marka ta gano wani abun abbatin ya aikata.

Dai dai lokacin da malam na lado ya shiga bayan sa kuma wani tsoho ne mai farin gemu yana dogarawa da sanda.

“Assha. SubhanAllahi Marka. Menene kike kuka. Deluwa menene?”

“Yo ka tambayi matsiyaciya.?  Ai so ta yi karan ya chake mun idanu nima na dai na gani tamkar yar wajen ta. Wannan mata, wannan mata, Allah dai ya kwashe miki albarka…”

“Assha marka bar cewa haka…. ” Malam na lado ya fada. Kafin ya sake cewa,

“Ga malam me carbi na kofar dawanau ya zo duba ki.”

“Ayho to .. Sannu malam ..”

“Yauwa sannu Marka … Ina wuni?”

“Alhamdulillah Malam.”

“Ya karfin jikin na ki?”

“Da sauki ”

“Masha Allahu… Ubangiji Allah ya baki lafiya. Yasa zakkar jiki ce. Allah yasa wannan ciwo na ki kankarar zunubai ce. Allah ya tashi kafadun ki.. Ya sa…

Bai karasa ba zahara’u ta shigo cikin gidan tana koke koke.

“Marka Allah ya isa tsakani na da ke. Wayyo Allah na. Wayyo . Wayyo …”

Duk suka tsaya suna bin ta da kallo. Malamin ya sake mayarda zaman gilashin kara masa gani cikin idanun sa.

“Assha…. Wacece wannan din?”

“Zahara’u ce autar mu.” Malam na lado ya fada yana matsa yatsun sa.

“SubhanAllahi…. Ki ke fadaawa mahaifiyar ki wadannan tsauraran kalamai haka? Assha assha.”

Zahara’u ta zube a jikin bango tana mai harba kafafun ta.

“Ya shika ni …. Shi ma ya shika ni. Shika 3 kuma. Yace ba zai iya dawainiya da yara majinyinta har biyu ba. Munje asibiti an gwada su. Suna da ciwon amosanin jini ta sikila (sickle cell..) wayyo Allah na… Marka kin cuce ni.. Kin ha’ince ni. Allah ya isa tsa…

Malam na lado ya samu kansa da faskara mata zafafan maruka har biyu hagu da dama na fuskar ta.

Marka ta sandare da jin bayanin zahara’u. Ciwon amosanin jini yaran zahara’un ke da shi? Maganganun Najan Isubu suka shiga dawo mata na shekarun baya.. Alokacin da zata hada Waheedah da shi. Inda Najan ke ce mata Na’Ateeku fa shima ba lafiyar ce dashi ba. Wani tokararren abu ya tokare mata a makogaro . Sai dai idan Hadiza ce ta kai sunan ta gidan boka.

Dattijon ya dube su duka. Yana wa malam na lado kallon karin bayani. Nan dai Nalado ya sheda masa komai . Tun faruwar neman da Na’Ateeku yayiwa yar wajen sa Waheedah. Da yadda auren ya koma kan zahara’u. Da tarihin ciwon da ke kan Najib da ma marigayi yayan su Waheedah, wato Kamal.

Marka ta kece da kuka… Cikin muryar me cunkushe da damuwa tace,

“Ko kaffara ba zan ba sai dai idan Hadiza ke bibiyar mu da sihiri. Ta jefe rayuwar mu baki daya…. Ya zaai ace. Da fari bayan da nace tabar gidan nan tin da dama auren ya kare tuni. A ranar data tafi Adamushe ya zo ya sau zahara’u saki 3 agaban mu. Yace yara ba nasa bane. Gasunan zube muna zaune da su. Mai sunan Malam ya zo ya auro Deluwa itama gatanan yara biyu du ba lafiya. Waçcen dayar makauniya ce ma tamkar dai diyar Hadiza da ke saka gilashin kara gani to ita wannan yarinyaa ma baki daya bata gani. Akazo ranar daurin auren zainabu yar Sa’adatu a ranar mijin itama ya sauta… Sannan kuma auren zahara’u na biyu dan ana bakin ciki ta haifo har biyu shine Hadiza ta shiga ta fita ta sanyawa yaran irin ciwon yaranta su biyu. Ciwon da ya kashe dan ta na fari kamalu. Gashi Najib yana da shi shi ma. Sannan ace yaran zahara’u na wajen Na’Ateeku suma du su biyun suna da shi? Bayan ciwo ga shika har 3? Ni ma bata bar ni ba. Ta kassarani gashi nan ta lalatamun rayuwa sai dai a kwantar a tayar. Baki daya malam wannan matar ta batamun rayuwa ta da ta iyalina gaba ki dayan mu… ”

Malam me carbi na kofar dawanau yayi murmushi kawai. Yana mai girgiza kansa,

“Ki sauri ki ce Astagfirullahi…. Wani bai isa yayi wa wani wani abun ba. Ba tare da Allah ya rubuto haka kaddarar sa zata kasance ba…. Kuma in dai Hadiza dai kike nufi wacce ke wajen haulatu yayar ta. Matar Nalado ta fari. Maganar gaskiya ba zata aikata mugun abu ba… Dukkanin abubuwan da kike fada ya shafeta haka zalika kema ya shafeki Iya. Yaranta sunada ciwon sikila. Diyar ta ya macen kuma bata gani sai da temakon gilashi. Haka zalika ke kika sanyaa Nalado ya rabu da ita..Yaran nan nata jikoki ne agare ki Marka. Ko ba komai itama uwar ‘yayan dan cikin ki ce.

“Kada ma ki sake cewa wani ya tozarta miki rayuwa ta hanyar sanya miki ciwo ko gurbata rayuwar ahalin ki. Wannan ba dai dai ba ne. Baki imani da kaddara ba Iya. Babu hutu da kwanciyar hankali ga bawa a wannan rayuwa ta duniya sai yayi imani da qaddarar Allah. Wato ya sakankance cewa duk abinda Allah ya qaddara mai aukuwa ne, kuma abinda be so faruwar sa ba, to haqiqa bazai faru ba. Haka kuma lallai al’umma da zata taru gaba daya domin ta cutar da bawa da wani abu, to ba zasu iya ba sai dai da abinda Allah ya rubuta zai same shi. Hakanan da zasu hadu domin su amfanar dashi, ba zasu iya ba face da abinda Allah ya rubuta.

“Ma’anar Imani da Qaddara:
Imani da qaddara na nufin yarda tare da gaskatawa cewa, babu wani alhairi ko sharrai da zai sami dan Adam face bisa qudura da hukunci na Allah Madaukakin Sarki. Sarki ne kuma shi, da yake aikata abin duk da ya so; ba abin da zai iya kasancewa, face da sani, da kuma yardarsa. Babu kuma wani abu a faadin duniyar nan, da yake wajen qarfin ikonsa, Madaukakin sarki ta fuskar samuwa ko rashi; shi yake samarwa da sarrafa shi. Amma, tattare da haka, ya shimfidaa wa bayinsa wasu umarce-umarce da hane-hane, wadanda a cikinsu, ya ba su cikakkiyar damar tsare alfarmarsu ko tozarta ta; babu wanda zai tilasta su. Iyakar abin da yake wurin shi ne, al’amurran za su ci gaba da gudana ne gwargwadon iko da zabin ransu. Amma, yana da kyau a sani cewa, da su bayin nasa, da wannan dama da iko da suke da su, duk Allah Madaukakin Sarki ne ya halicce su. Saboda haka duk wanda ya shiriya daga cikinsu, rahama da jinqai ne, na Allah ya sauka gare shi. Haka kuma duk wanda ya bace, hikimarsa ce Madaukakin Sarki, ta tabbatar da haka. Babu kuma wanda ya isa ya tambaye shi dalili a kan haka. Amma, baya gare shi subhanahu wa ta’alah,  kowa abin tambaya ne.

“Iya, Imanin nan kuma da iko da qudura irin na Allah Madaukakin Sarki, Daya ne daga cikin rukunnan imani, kamar yadda jawabin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya bayyana a lokacin da mala’ika Jibrilu ya tambaye shi a kan abin da imani ya qunsa. Sai ya karba masa da cewa: “Shi ne ka yi imani da Allah, da Mala’ikunsa, da littafansa, da Manzanninsa, da Ranar Qarshe. Ka kuma yi imani da qaddara ta alhairi da ta sharri.”[Muslim:8]

“Ina fatan wannan dan karin haske daga cikin dan ilimin da na sani zaki duba agare shi. Ki kuma tabbatar wa kan ki da bawa baya tsallake kaddarar da Allah ya ketara masa. Imani da ita kawai zaki. Ki karba da hannu dubu. Sai Allah ya dube ki da idanun rahama ya kawowa rayuwar ki sauki… Kar Allah ya karbi ranki acikin wannan yanayin da kike ciki. Kinsan kuma Allah baya yafe zaluncin da kayiwa bawan sa. Hakanan kuma adduar wanda aka zalunta batada hijabi ga Allah .. Ki roki dukkanin wadanda kika aibata wa rayuwa ko kika zalunta. Ko Allah zai dube ki da rahamar sa. Ya sassauta maki halin da kike ciki.”

Hawaye suka shiga zurara daga idanun Marka..

“Allah na tuba Astagfirullahi… Ka yafe ni. Allah na karbu kaddara tah. Allah kasa hakanne mafificin alkhairi agare ni da iyali na baki daya .. Deluwa, Mai sunan Malam, Zahara’u da ma su zabba’u dan Allah dukkanin ku ku yafe mun .. ”

“San samu gaba daya ahalin na ki su taru waje daya. Ki nemi gafarar su. dukkanin su manya da kankana… Kinji ko?”

“Insha Allahu malam… Amman bana jin zasu yafe mun. Na aikata abubuwa marasa dadi ”

“Zasu yafe miki insha Allahu… Domin Allah ma kullum cikin yi masa laifuka muke. Kuma idan muka roke shi yana yafe mana. Ballantana mutum dan Adam. Insha Allahu dukkanin su zasu yafe miki… Allah ya yafe mana baki daya.”

“Aamin Yaa rabbi.”

“Aamin..”

“Sai ku tsayar da rana nan kusa ku tara iyalan baki daya. Insha Allah nima zan zo don tausasar harsuka. Allah ya ara mana rana yasa muna da rabon haduwa.”

“Amin malam. Nagode Allah ya saka da alkhairi. Ya kara lafiya.”

“Amin Amin tare da ke da sauran baki daya..”

Yayi musu sallama ya tafi. Bayan ya kara jawa zahara’u kunne ya tsawatar hadi da mata fada sosai akan muhimmancin girmama iyaye da tausasar harshe idan zaa yi musu magana. Ya kuma saka ta bawa Marka hakuri hade da neman yafiyar ta.

Malam na lado ya shige gaba yayi masa rakiya…

Marka nata tsiyayar hawaye. Idan ta kallo yaran Deluwa marasa lafiya da daya makauniya. Ga tulin yaran Adamushe ga biyu na wajen Na’Ateeku masu dauke da cutar amosanin jini.

Ta sake fashewa da kuka. Ganin dukkanin aibatawar da takewa yaran Hadiza . Gashinan nata ma sun samu. Gaba da baya kowanne na da irin na sa ciwon. Ga ita kanta data zama jangwam sai dai a kwantas a tayas. Gefe daya zahara’u na rera nata kukan.

Baki dayan su dai zukatan su ba dadi. Damuwa ta taru ta tumbatsa ta kuma gauraye ilahirin jini da tsokar su Basu da wani sauran FARIN CIKIN ZUCIYAH..

To dama hakan abun ya ke. Idan kana yiwa kaddarar wani dariya. Sai Allah ya jarabceka da irin ta ko ya ninka maka fiye da ita.

Wani tun a doron duniya yake fara ganin hukuncin Allah akan sa. Shi yasa duniyar nan kayi me kyau. Ka kyautata mu’amalar ka da kowa. Kada ka zama silar da wani zai kai kukan sa wajen Allah akan ka… Allah ya raba mu da mummunar kaddara. Yasa mu wanye kalau. Allah ka kare zukatan mu da gangar jikin mu wajen fadawa kogin aikata haramun. Ka nesanta mu da haramun ka kuma kusanta mu da aikata mekyau cikin halaliyar ka me dimbin rahama… Domin kai din mubuwayi ne gagara misali.. Allahumma Aamin.

××××

IYALAN MALAM NA LADO ME IGIYA

Bayan sati da faruwar mutuwar auren zahara’u. Kuma wanda yayi dai dai da lokacin da Marka ta saka wanda zasu hallara da ahalin ta baki daya don neman gafarar su da yafiyar juna baki daya. …

Hakan kuwa akayi. Ranar dukkanin su kwan su da kwarkwatar su sun taru a tsukukun gidan na Marka.

Ciki harda Umma Hadiza da nata iyalan su biyu. Waheedah da Najib.
Duk wanda ya dora idanun sa akan Umma Hadiza da iyalanta sai ya sake mayarwa ya dube su.

Gamin yadda suka yi bulbul da su. Fatar su na sheki, Gefe daya da nutsuwar zuciya. Musanman Waheedah da tayi wani irin fresh tamkar a tsaga jikinta jini ya fito.

Sanye cikin kayan alfarma. Kana ganinta kasan ta samu gidan hutu da wadatar zuciya. Dubada yadda komai na jikinta mai kyau ne da tsada. Wai ahakan ma bata kure adakar ta ba. Tayi saisa saisa. Gudun kada suyi ta yada maganganun ta zama yar karya da sauran su.

Bata zo hannu biyu ba. Ruwa leda leda na pure water. Sannan na cartons cartons na roba da lemo. Gefe daya ga kayan abinci buhun shinkafa ta dafawa data tuwo, Da kayan shayi da jarkar mai. Wannan kayan abincin Haj Hameedah ce ta bata tace ta kai gidan su.

Baki daya sai aka yayyabe ta. Kowa na yabawa da alkhairin da tayi. Marka tsabar dimaucewa kuka kawai take. Ganin wadanda ta muzantawa a rayuwa a baya. Sune a yanzun suke temakon ta da karfin su da gumin su da kuma aljihun su. Hawaye take tsiyayar wa sosai na nadama… Hakika tayi dana sani da abubuwan da ta aikata a baya…

Zuwan malam me carbi ba dadewa … Ya bude taron da addu’oi sosai. Sannan ya shiga yin wa’azi mai ratsa jiki da fadakarwa ga dukkanin su yan wajen baki daya ….

Daga bisani kuma ya bawa malam na lado dama shima ya fara tasa maganar. Daga karshe ya shiga neman yafiya da afuwa ga dukkanin su. Da su yafe masa akan dukkanin abubuwan da ya aikata wa kowannen su na bacin rai akan sani da na rashin sani …

Bayan ya gama nasa bayanin. Marka ta karba. Muryar ta na rawa da kakkarwa. Idanuwan ta taf da ruwan hawaye. Ta shiga bawa daya bayan dayan su hakuri akan dukkanin muzgunawa da tayiyyi musu. Hususan (musanman) Umma Hadiza da ahalin tah.

Marka ta sake fashewa da kuka… Hakuri sosai take basu. Numfashin ta na fuzga. Neman yafiyar su ta ke. Nadama sosai take yi. Ji take dama a tariyo baya . Ta goge halayen da ta aikata ta musanya wa kowannen su da alkhairi ..

Wasu daga cikin su hawayen suma suka fara, Musanman Umma Hadiza, Waheedah, Najib, Nalado, inna Sa’adatu da kuma Deluwa.

“Yanzu ba gashinan ba ? Na girbi abunda na shuka. Duk wasu sharruka dana aikata daya bayan daya sun dawo mun. Daman ance sharri dan aike ne. Duk inda ya zaga ya zagaye da aiken da ka yi ma sa. Sai ya dawo gare ka ko ga wanin ka.. Dukkanin mugayen alkaba’en dana dinga yi wa Hadiza da yaranta yanzun ba gashi nan ba. Sun dawo gare ni da na wa yaran da jikokin? Ciwon da nake musu dariya ina zunde gashi nan akan nawa jikokin na wajen Zahara’u. Makantar Wahidin… Au Waheedah da na ke aibata gashi nan Deluwa ta haifo yara daya makauniya ce. Baki daya ma ita bata gani kwata kwata. Sakin da na saka mai sunan Malam ya yiwa Hadiza gashi nan an sako tawa ‘yar har sau biyu. Yara kuma dukkanin mazajen sunce basa ra’ayin su. Jikar da na fi kauna na fifitata akan Waheedah. Nake ganin Waheedah itace me budadden idanu ta iskance akan karatun da take. Sai gashi ana zaton wuta a makera… Naga aya akan wadda na zaba… Ranar daurin auren an daura nan mijin ya zo ya saketa kan zubar da cikin ta uku bata gari bace… Sa’adatu ta yanke jiki ta fadi ana fadar hakan. An kaita asibiti zaa dawo da ita nan nace ban amince ba.. kaya zata zamar mana.. Sai gashi ita Allah ya warkar da ita. Ni ce na zama kayan. Sai dai a kwantar a tayar… Nayi kurakurai da manyan laifuka da baki ba zai iya fade su duka ba. Saboda girman haramcin su .. Ni dai ku yafemun… Dan Allah ku yafe mun..”

Kuka ne yaci karfin kusan dukkanin su. Ciki harda malam me carbi da ke gefe… Daya bayan daya suka shiga cewar sun yafe

Inna Sa’adatu ta tashi daga inda take. Duk ta yamutse. Ta motse ta lalace. Kamar ba wannan saadatun me tsiwa a baya ba.. Gaban Umma Hadiza ta tsugunna ta shiga rokan gafarar ta. Hawaye suka shiga reto a jemammiyar fuskar tah.

Umma Hadiza tayi murmushin yake. Hannunta daya na kan na inna Sa’adatu.

“Na yafe ma ki Sa’adatu . Allah ya yafe mana gaba daya.. Nima ina neman yafiyar dukkanin ku. Wadanda nayi wa lefi akan sani ko akasin sa. Ni da yarana baki daya mu na neman afuwar ku. Allah ya yafe mana baki daya Amin.”

Haka dai suka shiga neman afuwa da neman yafiyar junan su. Alhamdulillahi kowa ya yafewa kowa acikin su baki daya. Wannan yasa Malam me carbi sa ke jan kunne agare su .. Kafin yayi musu zai tafi

Marka ta saka aka deba masa lemuka da ruwan da Waheedah ta kawo. Da rabin kwanon kayan masarufin. Yayita godiya ya yi musu sallama ya tafi. Najib ya rike masa kayan yayi masa rakiya..

Waheedah da zainab ne suka hada wuta suka dora taliya yar kakkaryawa da miya🤸 Ranar anci an gyatse… Anyi wasa da dariya… An saada zumunci sosai. Harda hotunan tarihi suka yiyyi…

Da Waheedah ta tashi tafiya. Ta dakko yan kudaden ta na sadaki da taketa ajiyar su. Duk kuwa da tayi amfani da wani kaso daga ciki ..Ta dankawa mahaifin ta .. Don FARIN CIKI fashewa yayi da kuka. Ya rungume ta yana sanya mata albarka ,. Tace yaja jari da su.

Yana kaunar iyalin sa. Da matar sa ta baya Hadiza. Dan dai auren ya rabu ne. Ya so tayi komai . Sai aka dakatar kan dukkanin su AS ne.. Don haka kar a mayarda auren tarihi ya maimaita kansa . Kar su sake samun wasu iyalin wadanda zasu zo dauke da cutar amosanin jinin suyi ta wahala har karshen rayuwar su .. Don haka ya hakura ..

Har mota suka raka Waheedah wadda Nassem kanin Zayn ya zo daukar ta. Shima ya gayshe da su cikin girmamawa… Taro ya watse . Kowanne ya koma muhallin sa cikin FARIN CIKIN ZUCIYAH…..

××BAYAN SHUDEWAR WASU LOKUTA××

Anyi bikin Nadra an gwangwaje… Dangi zumunci ya kara bunkasa . Zuciyoyin su sun samu farin ciki da kara kusanta a tsakani..

Allah ya azurta Waheedah da karuwa. Ba karamin kyau baby bump din ya mata ba. Idan ta saka uniform din school of nursing sai kuga yayi das das ajikin ta. Gwanin ban sha’awa..

Soyayyar duniya Zayn ya dauka ya dorawa cikin Waheedah. Ta kara samun kulawa da tarairaya daga dangin ta da na sa. Ciki kuwa harda Ahlam . Domin yanzu tuni komai ya wuce sun dedeta kansu. Suna kuma ziyartar gidajen juna. Wani lokacin har tsokanar su Zayn yake .. Yana cewa suna hade masa kai bai yadda ba.

Itama Ahlam ta koma makaranta karo karatu na digiri na biyu. Ya yinda Zayn arzikin sa ya yalwata. Ya hada da aikin office da kasuwanci.

Ya mallakawa matan na sa biyu mota iri daya. Ta Ahlam fara ta Waheedah ja. Lamarin sai godiyar ubangiji.

Fannah da Basira ma lokaci daya aka saka bikin su. Ibrahim ne ya auri fannah. Ya yin da Salman lecturer dinsu na school of nursing kuma ya auri Basira. Waheedah ita ta zama uwar biki. Babbar kawar amare.

Gidan su wajen Marka ta koma ta tare har aka kammala shagalin bikin na tsawon kwanaki uku. Ya yinda gefe daya bangaren na ahalin malam na lado ma sai sam barka komai yana tafiya ahankali cikin nutsuwa da kwanciyar hankula… Da waraka ta fannoni da dama…

Don Umma Hadiza ma wani mutumi mai rufin asiri a gidan da ke kallon na gwaggo haule. Matar sa ta rasu ta bar masa yara biyu. Shekara daya kenan da wata uku bayan rasuwar ta. Ya samu mijin gwaggo haule da zancen neman auren Umma Hadizan.

Da fari Umma Hadizan ta ki. Kasancewar ga yara manya agabanta auren me zatayi? Da kyar da sudin goshi gwaggo haule ta shawo kanta.

Aka daura auren ranar wata jumu’ah. Ta tare agidan. Mai gate da dakuna uku da parlor har biyu. Kuma Alhamdulillahi yaran mutumin na kaunarta.

Ta rike su tamkar yaran data haifa daga cikin tah. Ta kance ai ‘da na kowa ne.. Hakan yasa dangin sa dana marigayi ya matar sa suka sake kaunatar Umma Hadizan. Suna masu yabon ta a ko’ina…

××ZAYNUL_WAHEEDAH××
(DESTINED LOVE)💕

__
Samun karuwar da tayi … Yazo mata da lauyi kala kala. Ciki harda kasala da bacci uwa kasa. Da tayi ishai take zubewa tayi bacci..

Kusan ko yaushe sai ya dawo da daddare ya ke tashin ta … Taci abinci sai ta sake komawa baccin.

Yau ma hakan ta ke. Mai gadi na bude masa gate ya shiga da motar sa ya yayi parking awajen adana motoci.

Ya bude kofar da zata saadaka da cikin gidan da spare key din da ke hannun sa.

Bakinsa dauke da sallama ya shiga. Sai kamshin turaren wuta ne ke tashi . Ya sake bude kofofin hancin sa yana mai shakar niimataccen kamshin.

Hannu ya saka ya bude dakin ta. Tana kwance akan gado tana bacci. Ya danyi murmushi hadi da ajiye yar jakar da ke hannun sa a gefe .

Ya zare safar kafar sa ya isa ga gadon da take kwance. Ya yaye duvet din ahankali ya shiga ciki.

Ya shiga unbutton din maballan jikin rigar sa. Ya cireta ya ajiye a gefe. Jikin Waheedah ya shige sosai tamkar za’a kwace masa ita…

Ya saka hannuwan sa akan rassan jikin ta yana mai mata tafiyar tsutsa.. Cikin wani salo na tafiyar da soyayyah . Ya dan saka hakoran sa ahankali ya ciji kunnenta..

Ta shiga ture shi daga jikinta. Idanuwan ta a rufe. Baccin ya ki sakin ta..

“Kasa uwar bacci …..” Ya fada ahankali cikin kunnenta…. Yana mai yawo da harshen sa acikin kunnenta.

Da sauri ta farka daga baccin. Ta shiga ture sa da iya karfin ta . Ya hanata, Ta hanya sake makaleta. Yana mai shafa gadon bayan ta,

“FARHATAL QALBi nahhh, A yayin bayyana miki adadin yadda nake jin son ki a zuciyata, zan iya yin amfani da kalmomi irin su…….hmm ko dan ina ganin cewa babu wata kalma da za ta iya wakiltar matsayinki a gare ni. Sai dai a yau a kuma yanzu ina mai kara sanar da ke cewa, ina kaunar ki .. Irin son da gangar jiki ke wa zuciya. Zuciya ta ke wa rai… Kin zamo mun FARIN CIKIN da ke cikin ZUCIYAH marar misaltuwa..”

Yana magana yana zame rigar da ke jikinta a hankali. Dama ta bacci ce iya cinya. Ya sake jan bargo ya rufe su yana mai aikawa wasu rassa na jikinta sako da suke tafiyar da shi a koda yaushe.

Ta shiga ture hannuwan sa. Tana mai turo baki gaba.. Cikin kwarewa ya burkito ta .. Ya kamo bakinta ahankali ya hade da nasa waje daya . Sumbatar ta yake cikin kwarewa da nuna tsantsar kaunar sa agare ta …

“Ka bari …..”

“Sshhhh…… Please Waheedah…. Please” Ya shiga rokonta ta hanyar sanya idanun sa cikin nata.. Baki daya ya narke mata.

Wasu zafafan sumba ya shiga aika mata tun daga tafukan kafafuntaa zuwa kirjin ta. Wanda suka haddasa mata tashin tsigar jiki. Kofofin jikin ta suka shiga budewa da son kasancewa da shi. Suna mai maraba da sakonnin da ya ke aika musu

Hakan ya sa Zayn sa ke kai mi wajen. Zare rigar tata gaba daya ya jefar. Ya kashe fitlar bedside ya sake kankame ta ajikin sa.

Duk kaucewar Waheedah sai da ta kasa hakuri. Ta bashi hadin kai. Suka shiga nunawa juna bajinta..

Bayan sun samu nutsuwa ne. Zayn ya dauki Waheedah suka shiga cikin bandaki. Ya sakar musu shower akan su.

Suka tsaya ruwan shower din na zuba ajikin su. Ya shiga kwaranya akan sumar gashin Waheedah… Zayn ya saka hannu yana shafa gashin na ta.

“Waheedah nah.. I never loved you any more than I do, right this second. And I’ll never love you any less than I do, right this second…”

Ta dago idanunta da suka jike da hawayen FARIN CIKIN kalaman sa da ke tsuma ZUCIYAr ta a koda yaushe… Ya gyarda mata kai, Ya sanya harshen sa yana mai goge mata hawayen da harshen sa, Hadi da cigaba da cewa,

“I love you and I don’t want to lose you. Because my life has been better since the day I found out….. You are my sunshine, My moon and all my stars💕”

Da wannan kalaman ya hade bakunan su waje daya .. Daga wanka kuma suka shiga bude shafin wata kaunar. Dakyar Waheedah ta yageshi daga jikin ta … Suka shiga mayar da numfashi.

Daga karshe dai sukayi wankan me dalili dana tsarki. Kafin su sanya wasu kayan baccin su koma parlor .. Tv suka kunna suna kallon wani American film ‘legally blonde..’

Rayuwar su gwanin sha’awa… Tamkar irin masoya dinnan da suka shekara dari suna bawa soyayya hakkin tah. Zaman su suke lapia kalau ba wanda ke jin kansu . Ko sun haura da kansu suke shiryawa ba tare da kai wa wanin su kara ba…

××Bayan wucewar watanni… Allah ya sauki Waheedah lafiya.. Ta haife santalelen jariri kato. Kyakkyawa tamkar Zayn ne yayi kaki ya tofar.

Kwayar idanun ce kawai irinta Waheedah… Da dan karamin bakinta masu dauke da labba jajaye .

Daga ita har jaririn suna cikin koshin lafiya. Zayn ya yiwa yaro huduba ya sanya masa sunan mahaifin sa wato farfesa Adam. Amman daman sun tsara idan mace ce sunan Maa ne zasu kira ta da Hayfa. Idan namiji ne kuma Adam za’a dinga kiran sa da Sultan ..

Asibitin ya cika makil da yan uwa da abokan arziki. Kowa ya zo yi musu barka. Ko dan bedrest ba su bari tayi ba. Saboda surutu, Likitan ya tarkata ya basu sallama.

Gidan Maa suka wuce. Sai da tayi wa zayn jan ido da ya kafa ya tsare agidan ta zata zauna baa ko’ina ba.

Ba yadda ya iya haka ya hakura. Maa tatafi da Waheedah da ke masa gwalo. Aka gyara mata daki daya.

Kan kace me ko’ina an cika sa da kayan baby da gadon baby. Umma Hadiza kuwa tunda tazo tayi barka ta tafi ko jimawa batayi ba saboda kara da take musu. Gefe daya farin ciki ya cikata na sake ganin sabuwar tarairayar da ake bawa Waheedah…

Ranar suna aka hada hadadden taron suna. Da decoration, Mai dauke da hotan baby sultan da sunan sa.

Abinci kala kala da masu hoto da kayan rabo. Nadra ma tazo sunan itama da nata kayan barkan himili guda.

Akayi hani’an da abinci da kayan rabo. An sha hotuna. Kafin baki kowa ya watse. Ahlam ma ta bada kayan barka kala kala. Gwanin ban sha’awa… Yan uwa kowa yaji dadin haduwar kawunan su.

×××

Ranar da Waheedah ta cika kwana arbain da daya… Hutu na musanman Zayn ya dauka awajen aiki. Ya murje idanu ya tafi gidan Maa.

Allan ya temaka tana asibiti. Sai Waheedah da Najan Isubu da ke tayata reno. Itama Najan tayi bulbul da ita.

Ba abunda ta nema ta rasa. Ga Isubu ya dawo daga tafiyar tashi da ya yi. Alhamdulillah kuma ya samo alkhairai. Rayuwar su ta kara bunkasa.

Najan na ganin shigowar sa ta goye baby sultan tayi sashen Haj Aisha bayan sun gaysa.

Hakan ya sake masa dadi a zuciya. Ya shige gidan wuf yayi dakin Waheedah. Tana tsaye agaban mudubi da daurin zani..

Juyawa yayi ya saka mukulli ya kashe fitila . Ya rufe labulaye. Dariya ce ta taho mata ta danne kawai ,

‘ina wuni?”

“Yana wajen ki …. ”

Ya karasa wajen ta . Ya janyota jokinsa na ta rawa tamkar mazari.

Ya shiga kokarin cire zanin nata ta hana shi tana turo baki gaba…

“I love and miss you soo much…. Kaman zan zauce ” Ya fada yana lalubar bakin ta.

“Naga dazu ma ka zo…”

Ya lakuce mata kumatu kafin ya rada mata cikin kunnenta,

“Kinfi kowa sanin abunda nayi missing… ” Ya karasa fada yana rungumar ta tsam a jikin sa.

Ba tare da bata lokaci ba… Ya kwantar da ita akan gado shima ya kwanta… Yana mai aika mata da sakonni kala kala, Sai da suka samu nutsuwa tukun sannan ya sake rungumar ta. Bayan ya sumbaci gefen fuskarta,

“If I had a flower for every time I thought of you, I could walk in my garden forever. I don’t care how hard being together is, nothing is worse than being apart. Nayi kewar ki kwanakin nan arbain da daya… In a sea of people, my eyes will always be searching for you. Waheedah…. Enta FARHATAL QALBI– Kin zamo mun FARIN CIKIN da ke mamaye da ZUCIYAH tah. Sometimes, I knock on the doors of your heart, just to make sure I still live there. Wifey.. No matter what has happened. No matter what you’ve done. No matter what you will do. I will always love you. I swear i…I’ve never had a moment’s doubt. I love you. I believe in you completely. You are my dearest one. My reason for life… 🥺😍”

“I love you with every fiber of my being… Ina kaunar ka fiye da yadda kake tunani .. I love you more than life itself.. You’re my answered du’ass.. Allah yabar mun kai miji na… Muradin rai na… Mamallakin zuciya da gangar jiki na… Allah yabar mu cikin lumana da kaunar junan mu . Har gaban abadan…..”.

“Aamin Yaa Rabb Baby boo… Allah ya raya mana Sultan.”

Da haka suka sake shiga wata shafin kaunar. Kafin daga bisani su faada bandaki su tsarkake jikin su..

Bayan sun dawo cikin daki ne aka shiga bugo kofar

“Waheedah …. Kin tashi?”

Waheedah ta bude baki, Kafin ta tattake ta ruko hannun Zayn da iya karfin ta ta tura shi cikin bandaki ta bude kofar Maa ta shiga.

“Ina Sultan ko yana wajen Naja?”

“Eh” Waheedah ta amsata tana sosa habarta.

Kai tsaye Maa tayi hanyar bandaki tana

“Bari a tara ruwan wanka ko?”

“Akwai …. Ka….”

“Na ce kibar kunyar nan Waheedah.. Kayan undies kuma ai ba wani abu bane. Ko ni sai na wanke m….

Tana bude kofar sukayi ido hudu da Zayn dake sosa keyar sa. Ta maze kawai ta shiga cikin bandakin.

“Ina wuni au kwana Maa?”

“Kalau …”

Ta harhada abun da zata hada a bandakin ta fita daga ciki. Waheedah tuni ta sandare a tsaye kunya duk ta kamata.

“Idan anyi ishai sai ka zo ka dau matar ka Zayn….”

“Nagode Maa Allah yaja kwana..”

Maa ta girgiza kai kawai ta fice daga cikin dakin. Ya yinda Waheedah ta zube akan gado tana rufe kanta da pillow kunya dukta isheta

Zayn kuwa ko a jikin sa… Daman haka yake so… Bai je ko’ina ba. Har akayi ishai. Suka tarkata suka koma gidan su.

Baby sultan ne kawai ke ceton maman sa awajen Zayn. Duk inda Waheedah ta saka kafa Zayn na like da ita kamar super glue. Ta kance,

“Dan Allah Darling ka kyale ni …. Kabari nayi feeding baby sultan .”

“Ki sassauta mun kada ki manta ke ce FARHATAL QALB na… Kin gama zama mun dukkanin wani FARIN CIKIN ZUCIYAH… ”

Tare sukeyin renon. Lamarin nasu sai masha Allah….

Bayan wata 9 da haihuwar sultan. Allah ya albarka ci Ahlam. Itama ta haife sankacececiyar jarirya mai kama da Zayn . Wadda taci sunan Ummimi suna kiran ta da Daneen..

Burin Zayn ya gama cika.. Matan sa masu kaunar sa. . Da kuma arzikin iyali masu tarin albarka .. Alhamdulillah!

Hakika dukkanin wani bangare ya samu wadatar ZUCIYA da FARIN CIKI. Allah ya albarkan ce su ta fannoni da dama. Lamarin sai godiya ga Allah domin shidin mubawayi ne gagara misali….

*ALHAMDULILLAH!!*

*_DUKA DUKA ANAN NI NANA HAFSATU ZAN DASA AYA… ABUN DA NAYI KUSKURE ACIKI RABBANA YA YAFEMUN WANDA NAYI DAIDAI ALLAH YA BAMU LADAN DUKA AMIN ..GODIA GA TARIN MASOYA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR WADANDA SUKA SAYA. DAMA WADANDA SUKA SAYA TULAREN WUTAN YERWA INCENSE AND MORE. ALLAH YA KARA ARZIKI MAI ALBARKA . SAI MUN HADU A ZAFAFA NA GABA IDAN MAI DUKA YA KAI MU. AMIN💕💕_*

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply