Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 68

Farhatal Qalb 68
Viral

PG:68_

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA…_

_AREWABOOKS👇_

https://arewabooks.com/book?id=63397750fbef002844646ad3

__
“Lallai wajibine muyi adalci a tsakanin mata. ga wanda yake auren mace sama da daya dole yayi adalci a tsakaninsu, ya sani dukkan abinda yake gudana Allah yana sane kuma yana ganinsa kuma wallahi sai Allah ya tambayesa akan zaman da yayi dasu a gobe alqiyama.

“Manzon Allah SAW yana cewa;
(Dukkan wanda yake da mata guda biyu sai ya karkata ga daya baya yiwa dayar adalci,zai zo a ranar alqiyama bangaran jikinsa guda a shanye)
@رواه أصحاب السنن الأربعة،واللفظ للنسائي وصححه الألباني.

“Malamai sunce karin aure ba wajibi bane ba mustahabbine ga wanda yake da iko ya kara,amma wajibine kayi adalci,idan har kasan bazakayi adalciba to kada ka fara neman kara auren ma domin karin zai iya kaika zuwa ga halaka.

“Manzon Allah SAW yana cewa;(Dukkanku masu kiwone kuma dukkan ku abin tambayane akan abinda aka baku kiwo agobe alqiyama……….)
@صحيح الجامع.

“Allah acikin alqurani yayi hani akan kada mai gida ya karkata gaba daya zuwa ga wata daga cikin matansa ya kyale sauran mata saboda rashin adalci.Allah yana cewa;
(وَلَن تَسْتَطِيعُوا أَن تَعْدِلُوا بَيْنَ النِّسَاءِ وَلَوْ حَرَصْتُمْ ۖ فَلَا تَمِيلُوا كُلَّ الْمَيْلِ فَتَذَرُوهَا كَالْمُعَلَّقَةِ ۚ وَإِن تُصْلِحُوا وَتَتَّقُوا فَإِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَّحِيمًا)
@النساء(129 Nisaa

“Ma’ana
(Kuma bã zã ku iya yin ãdalci ba a tsakanin mãtã kõ dã kun yi kwaɗayin yi. Sabõda haka kada ku karkata,dukan karkata,har ku bar ta kamar wadda aka rãtaye.Kuma idan kun yi sulhu,kuma kuka yi takawa,to, lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin kai)

“Adalci shine bai wa kowacce hakkin da Allah ya daro maka na zaman aure,wanda ya hada da ci da sha da kula da lafiya da tarbiyyah da bada ilimi da raba ranar girki da sauransu.Amma baya cikin adalci ace sonsu ya zama daya wannan babu wanda zai iya yin hakan saboda Allah bai halicci dan adam da wannan dhabi’a ba,shiyasa Manzon Allah SAW duka cikin matansa yafi son Nana Khadija R.A amma cikin mata guda tara da suka zauna lokaci guda yafi son Nana Aisha R.A.Allah ne mafi sani.

“Maigida a kowane lokaci shi ne jag­ora kuma kashin bayan gina iyalinsa da dora su a kan turba mai kyau. Shi Allah Ya dora wa nauyin aurowa da kuma kula da abin da ya aura din.A addinin Musulunci an ba shi damar auren fiye da mace daya, amma ba a bar shi haka ba sai da aka saka masa dokoki da iyakoki, don haka ne ma wasu mala­man ke ganin auren mace fiye da daya ba na kowane namiji ba ne.

“Mata da dama a wasu lokutan da suke su biyu ko uku ko hudu a wajen maza­jensu, kan yi korafin cewa rashin adalcin da wasu ma­zan ke nunawa shi ke kawo rarrabuwar kawuna da rash­in zaman lafiya.Akwai gidajen da tsabar tsananin kishin da ake yi sai ka rasa gane ko son mijin ne ya jawo hakan ko kuwa ma dai ba sa son sa ne. Wasu gidajen kuma sa­lon yadda masu gidan ke tafiyar da shi zai sa ka dinga tunanin anya wannan mijin ba shi ne silar matsalar gi­dan ba?To ko ma dai mene ne akwai hanyoyin da za a iya bi a inganta zamantakewa a gidan mai mata biyu, ko uku ko hudu, kamar yadda ma­sana da kwararru suka ce.

“Akwai wasu muhimman batu­tuwa da za ka kula da su… Ina fatan ka na saurare na ko Zayn”.

“Eh Baaba…”

“Tohm Masha Allah, Kar ka je kana aibata matarka a gaban daya matar ta ka. Kar ka zama mai kawo wa uwargida hirar amaryarka, Idan ka shiga gida, duk abin da zai jawo fitina kamar waya da amarya, ka daure ka guje shi. Ka ga wadannan kananan abubuwan, kar ka raina su wallahi suke tunzura mata wasu lokutan. Idan gida daya za ka hada su, ka tabbatar ka kiyaye muhimman sharuddan za­man tare. Kar ka dinga fifita daya a gaban daya, ka zama adali a kowane fanni. Kar ka yarda ka zama munafukin mata, kuma kar ka bari karfar baka ta rude ka. Dole ka iya takunka sosai. Kar ka zama munfukin mata. Ka zama tsayayyen maigida, jajircacce, wanda zai dinga wanzar da adalci a duk harkokinsa…

“Sai da ga karshe ka zama mai basirar gano karfar baka, wato kisisina irin ta wasu matan. Don wata kan zauna ta kalallame ka da zance ta hada wa abokiyar zamanta tuggu, kai kuma ka hau ka zauna ba tare da bincike ba… Ubangiji Allah yasa dawowar ku baki daya shine ya zama mafificin alkhairi. Allah ya baku zaman lapia mai dorewa . Ya kauda fitnu. Ya sanya tarin albarka da yalwar arzuka. Ciki harda yara masu albarka Allahumma Amin. Ke Ahlam sai kija girman ki a matsayin ki na babba. Da kuma matsayin na ke ya fara aurowa. Don haka ki dinga kauda kan ki a wasu abubuwan.kinji ko?”

“Tohm…. Insha Allahu ” Ta fada kanta a kàsa.

“Haka zalika Waheedah… Kema ki ja kankantar shekarun ki. Ki bata girman ta. Kinji ko?”

“Eh. Insha Allah. ”

“Tohm Masha Allah. Allah ya maku albarka . ”

“Allahumma Aamin.”

Haka dai aka shiga jan kunnen su. Kowanne yana tofa albarkacin bakin sa. Daga karshe a ka kira Ummimi a waya na fefen bidiyo wata video call. Itama ta tsawatar musu sosai.

Sai bayan sunyi ishai tukun sannan suka dauki hanyar gidah. Ahlam ce agaban motar. Ya yinda Waheedah ke zaune a baya.

Zayn yana tukawa. Saitin mirror din sa na kallon Waheedah. So yake kawai su kebe da ita ya rarrashe ta.

Ya gano tsantsar fargaba acikin kwayar idanun ta. Ya tsaya a tukubar mai kazar hausa. Fita yayi zuwa tukubar ya tsaya suna ciniki da me naman.

Gaban Waheedah na tsananta bugawa. Ji ta ke tamkar ta bude kofar motar ta fita wajen Zayn ta tsaya.

Ahlam ta saka hannu ta kara volume din radio da ke yi ahankali. Wa’azin marigayi sheikh Ja’afar Adam ne ke yi. Mai taken: ILLOLIN CIN AMANA…

Waheedah wani abu ya tokare mata a makogaro ganin Ahlam din yadda take kwafa tana mai sake karo volume din gidan rediyon. Ta kuma san saboda ita tayi hakan… Wato taci amanar ta data auri Ya Zayn..?

Allah ya temaka Zayn ya dawo cikin motar. Bayan ya ajiyewa Ahlam leda daya agabanta. Daya ya mikawa Waheedah. Ta hanyar ajiye mata a gaban kafafun ta..

Zayn ya rage sautin rediyon. Kunnuwan sa suka jiye masa wa’azin da akeyi a kan illar cin amana. Ya kuma gano saboda Waheedah tayi hakan.

Ya tashi motar suka hau kan titi. Har suka karasa gidah kowannen su da sake saken da yake yi acikin zuciyar sa.

Har wani sara masa kan sa ya shiga yi. Yar ledar da ke hannun sa karama ya mikawa baba mai gadi. Baba mai gadin nata doka musu gaisuwa.

Suka tunkari kofa. Waheedah na daga gefe. Zayn ya matsa zai kamo hannunta ta matsa da sauri.

Yana karasa bude kofar. Ahlam ta shiga ciki. Ta tsaya tana bin kayan gidan da kallo. Ta tabe baki ta haura sama abun ta.

Waheedah ta shige cikin dakin ta da sauri. Zayn ya bi bayanta.

Idanuwan ta ta sauke akan sa . Gaba daya a tsora ce ta ke. Ya tunkare ta. Ta shiga ja baya har ta jingina da jikin drawer.

Tururun numfashin sa ya doki kofofin hancin ta. Ya saka hannun sa ya daga fuskar ta da ta saukar kasa.

“My baby…..” Ya fada ahankali yana mai yawo da yatsan sa daya a tsakanin girar ta.

Ta kasa jure salon sa. Ta juyar da fuskar ta gefe. Ganin haka yasa ya janyo hannunta ya zaunar da ita a bakin gado.

Hannun ta cikin nasa …. Ya shiga matsawa ahankali. Hawayen da take ta makalewa ne suka shiga zurara a fuskar ta.

“Dan Allah ki dai na zubar mun da tsadaddun hawayen nan naki… Kina daga cikin mutanen da ba zan taba mantawa da su ba a rayuwata. Kin zamo cikin tunani na. Bana fatan zuwan wani abu da zai zamo silar rabuwar mu, ko da a ce mutuwa ce. .. Kar wani abu ya daga maki hankali ko ya saka maki tsoron wani abu a QALBin.. ki sani FARHATAL ki shine nawa….” Ya karasa fada hade da rungumar ta tsam a jikin sa…

Ya saka hannun sa daya yana mai shafa gadon bayan ta. Ahankali cikin muryar lallashi da tausasar wanda ake lallasa ya cigaba da cewa,

“Ki kasance mai daga kanki ki kalli sararin samaniya a cikin kowane dare, karda ki furgita a lokacin da kika hango wata mai tsananin haske, ni ma na yi hakan kuma na samu ganin wata tauraruwa mai haske idaniya da kore damuwar QALBi tah wato ke. …”

Dan murmushi ta yi. Ya lakuce mata kumatun . Hade da sumbatar gefen kumatun ta.

“A kullum na kan kwanta da tunanin ki, na kuma farka a cikin mafarkina, na gan ki zaune kusa da ni, a cikin wani lambu ma’abocin tsintsaye da furanni. Tabbas a lokacin murmushinki ya fi komai jan hankalina, muryarki kuma ke samar da nutsuwata….”

Ta daga kai ta kalle shi ..Dai dai lokacin da shi ma ya sauke na sa idanun akan tah.. Idanuwan su suka sarke waje daya…. Kallon kauna suka shiga yi wa junan sa. Ya yinda idanuwan su ke bawa juna labarin zukatan su .

Ya rankwafar da kan sa. Ya yi na sarar hade bakunan su waje daya. Ya yinda dayan hannun sa ke tallafe da ita a jikin sa.

Sumbatar ta yake cikin so da kauna,. Bugun zuciyoyin su ya tsananta. .. Tamkar zasu faso saboda yadda suke bugawa a tare.

Sun dau tsawon lokaci a haka… Kafin ya zare bakin sa ahankali. Ya tallabo fuskar ta. Idanun sa zube acikin nata ya cigaba da cewa,

“Duk inda ya tafi, ko me yake yi yana tunanin ki. Ko bacci yake yi ko a farke yake, yana hasaso murmushinki. A dukkan lokacin da kika yi nesa da shi, wajen ganin fuskarki ba ya bukatar hotonki. Karda ki yi tunanin wani ne na daban face ni. Ina matumar son ki… Ina kaunar ki… If you replace L in life with W, you get wife. That is because life isn’t worth living without a lovely wife like you. I love you darling….”

Dan murmushi tayi. Tamkar ana ingizata. Ta samu kanta da daga hannun ta ta dora a kumatun sa. Ya langabar da kansa bayan ya saka hannun sa akan nata hannun…

“Ka tashi….. Ka.., Ta fi.” Ta fada masa a rarrabe..

“No ba inda za ni…”

“Please ..”

Ya sauke zuciya kawai. Yana mai jan kasan leben sa.

“Me zaki bani na goodnight? Uhm?”

Mikewa tayi. Ta riko hannun sa. Yabi ta.. Suka wuce kofar bandaki kenan ya tirje..

“Ba wanka za mu y…”

Bai karasa ba ta dora yatsanta akan labban sa…

“Sai da safe …. ” Ta bude kofar dakin don ya fita .

Ya tura kofar da kafar sa. Ya jingina da bayan sa ajikin kofar. Bayan ya rungumo ta tsam a jikin tamkar za’a kwace masa ita..

“Ya zanyi da rashin ki a kusa da ni daren yau…. Uhm? My baby…” Ya fada yana mai showering mata kisses .

“Dare yana ja….” Ta fada murya kasa kasa. Kafin ta sake cewa,

“Ka je…. Ka ki tafiya ..”

“To bani abunda ko na kwanta zan dinga tunawa .. Kinji my baby?”

Dan murmushi ta kakaro ta saki. Ta kamo hannun sa daya. Bayan ta zuba masa manyan idanun ta akan sa.

Cikin murya cunkushe da sakon da kauna ke kwarara a zuciya. Cike da lafuzza masu tarairaya ta samu kanta da cewa,

“Rayuwata ta kasance rataye cikin tarkon soyayyar ka, ka ‘dana kuma ya kama ni. A dukkan lokacin da na kalli kwayar idanuwanka, na kan ji wani shauki mara misaltuwa. Inaa kaunar ka har cikin QALBi tah .. Domin kai din FARHATAL QALBi ne agare n….”

Bata karasa ba. Ya burkita ta . Ya samu kansa da bata rantsattsiyar sumba mai gauraye magudanar jini da tsoka. Mai kuma bayyana sakon ZUCIYAr sa agare ta. Hadi da jin dadi da yabawa bisaga kalaman ta. Sun matukar sanya shi cikin FARHATAL QALB…..

Ta zame kanta daga jikin sa. Ta fuce daga dakin. Ya bita da sauri. Kitchen ta nufa ta zuzzuba girkin da tayi acikin freezer ta rufe. Sai bin ta yakeyi. Data tsaya zai naniketa ta hanyar rungumar ta ta baya.Tanata yakice shi ya ki Ta koma daki . Ya sake bin ta

“Dare fa yana ja…”

“Wai meyasa kike korata ne? Bayan yau ma fa akwai karatun dana ce zan kara miki haske ..” Ya karasa fada yana mai daga mata girar sa daya . Da lumshe idanu yana sakin wani shu’umin murmushi .

Tayi saurin turashi wajen parlor ta rufe kofar da mukulli. Ya saki tattausan murmushi kawai. Ya haye saman wajen Ahlam

Ya yinda Waheedah ta jingina da kofar dakin..Hawaye daya na bin daya. Bata taba sanin zata zubar da hawaye akan hakan ba. Menene hakan? Ta tambayi kanta. Wata zuciyar ta bata amsa da kishi ne……🤣🤸

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply