Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 67


Farhatal Qalb 67
Viral

_PG:67_

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA…_

_AREWABOOKS👇_

https://arewabooks.com/book?id=63397750fbef002844646ad3

___
Yana zaune a ofishin sa. Kasancewar ba wasu aiyuka da zai yi ya gama kammala komai. Hakan ya sa ya sake barrarrajewa a kujerar sa . Yayinda ya dora kafafun sa akan table din gaban sa.

Folder din Waheedah da ke cikin wayar sa na tarin hotunan ta ya shiga. Kallon hotunan ya shiga yi tamkar zai mayar da ita cikin sa don tsananin yadda yake kaunar ta.

Wayar sa ce tayi karar shigowar sako. Dan haka da sauri ya buda ya karanta sakon. Abiey dinsu ne ke naman sa cikin gaggawa.

Don haka ya mike ya fice daga ofishin bayan ya dauki dukkanin abubuwan sa. Gidah zai wuce daga gidan su. Yanata sauri.

Ya shiga mota ya dauki hanyar gidan su saboda Abiey din yace anan zai same shi.

Kai tsaye ya wuce sashen Abiey din na su. Ya na zaune akan doguwar kujera. Ya yin da Haj Hameedah ke dispenser tana matso ruwa.

Ta ajiye agaban mai gidan na su. Zayn ya durkusa har kasa ya gayshe da dukkanin su. Duk kuwa da yadda zuciyar sa ke bugawa. Tana mai sako masa abubuwa kala kala. Wanda kowanne dai yafu karkata ga fannin da zuciyar sa ke tabbatar masa da hakan.

Farfesa Adams sai bayan ya shanye ruwan da Haj Hameedah ta bashi. Sannan ya dubi Zayn ya shiga gaya masa abunda yake makasudin na kiran sa da yayi. Ya karkare da,

“Ta dawo ma… Ko ince mun dawo da ita. Yanzu haka ma tana sashen Aisha. (Kishiyar Haj Hameedah.) Ba sai mun ja magana ba. Komai ya karasa wucewa. Da kai na na je summit din da nake gaya maka da taura biyu a baki na naje. Hususan don kan maganar ka da Ahlam … Sai fatan Allah yasa hakane mafificin alkhairin sa Amin. ”

Kan Zayn a kàsa. Zuciyar sa na hasaso masa zaman yan borin da za’ayi na Ahlam da Waheedah a gidah daya. Ba zai iya musu ba da mahaifin na sa. Ko ya nuna turjiya akan kin sahalewar sa. Don haka ya kakaro murmushi.

“Tohm Abiey .. Duk abunda kuka yan ke yayi.”

“Masha Allahu.. Allah ya muku albarka baki daya. Amin. Saboda naga na isa da kai ne. Na san kuma kai kan ka san ba zan taba muzantawa rayuwar ka ba ta hanyar da zan cuceka. Na dau hakan ko ince na yanke hukuncine ba tare da na bi takan ka ba. Amman ba zan kware ka ba. Idan har baka amince ba ka fada kaji ko?”

Zayn yayi murmushi kafin yace,

“Wallahi dukkanin hukuncin da ka zartar Abiey na aminta da shi. Dari bisa dari.”

“Masha Allahu. Toh Allahumma amin. Allah ya saka da alkhairin sa. Amin”

“Amin..”

“A kirawo su ne Abiey?” Haj Hameedah ta fada .

“Eh .. Yauwa itama Waheedah din ya kamata ta zo din. Saboda aja kunnen su tare.”

“Tohm insha Allah.”

“Zayn jeka dakko waheedah din. Kaji ko?”

“Eh Abiey. Tohm ”

Da sauri ya mike ya fita. Kai tsaye ya yi gidan sa.

Zuciyar sa tamkar zatayi zillo ta fado. Ya zaro wayar sa da ya saka a silent lokacin da Abiey dinsu yana masa magana. Missed calls din Waheedah yaci karo da su har uku. A jere .

Ya danna hancin motar sa a gate din. Sai kuma ya tuna ai komawa zai sake yi. Sai ya faka ta a waje. Ya shiga gidan yana mai rubutawa Waheedah message.

“Yan mata na kiyi hakuri ba, Wayar na saka a silent ina tare da Abiey ne alokacin muna magana., I’m deeply sorry… I love u”

“K..…” Ta mayar masa da sakon da ya tura mata.

Dariya sakon ya bashi. Ya daure ya mayar da wayar aljihu ya bude ya shiga cikin gidan.

Yana shiga parlorn. Sanyayyan turaren wutan sandal munawwara na kamfamin turaren yerwa incense and more ne ya masa sallama. Kamshin irin mai ratsa ZUCIYA da sanya FARIN CIKIN ga dukkanin wanda ya shake shi.

Gefe daya kuma karatu ne suratul baqrah ke tashi ahankali. A kitchen ya hangota a tsaye tana goge kitchen cabinets din da duster.

Duk kuwa da a goge suke sunata kyalli. Sanye cikin rigar atamfa mai zanen tsintsiya. Da ta sha torches din kalar shudi.

Tayi daurin ture kaga tsiya. Ya yinda tulin gashin data daure sa ya fito ta kasan dankwalin.

Tsayawa yayi ya tokare daga bakin kofa yana bin bayan ta da kallo. Tamkar yar tsana saboda yadda tayi kyau. Kayan sun amshi zatin halittar jikin ta.

Ahankali ya nufeta. Tana tsaye agaban sink tana dauraye hannuwan ta. Takun takalman sa yasa ta juya da sauri.

Ya narke mata idanun sa shanyayyu akanta. Yana mata wani irin kallo da ita kadai tasan fassarar sa.

“Barka da dawowa.” Ta fada cikin kulawa da bacin rai.

Matsawa yayi daf da ita. Ya zura hannuwan sa ta ruwan cikin ta ta baya ya sakale ta. Ya yinda ya dora kansa akan wuyan ta …

Ya saka labban sa. Ya sumbaci gefen wuyan ta da ke tashin kamshin oud kulaccam ta kamfanin turaren yerwa.

Cikin kasa kasa da muryar ban lallashi mai tattare da nuna kauna ga wanda ake sanarwa ya ce,

“Inaga nine yakamata nayi fushi dake saboda yanayin yadda kika kasa nunamin soyayyah… Amma kuma banyi ba, ki yi hakuri my love..Amincin Allah ya tabbaata ga ZUCIYAr da bata fushi akoda yaushe tana cikin yarda da aminci.,” Ya karasa fada yana mai bata peck a gefen kumatun ta…

Ta dan turo baki gaba kawai cikin shagwaba..

“Me kika dafa ne uhm? Ina shigowa kamshin turaren wuta dana girki ne suka fara mun sallama… Sannu da kokari my better half.. Allahumma bareek.”

Waheedah ta dan kauda kai. Bayan ta rausayar da shi. Cikin sake turo baki gaba da shagwaba tace,

“Fried rice ce kawai da sauce….”

“Uhmm… Sannu da kokari. Kinji?”

Ta samu kanta da daga wa sama alamar eh.

Zayn ya ja hannun ta suka shiga daki. Drawer ya bude ya dakko hijabi kalar kayan har kasa ya zura mata. Ta zuba masa sarautar Allah idanu.

“Abiey yace na dakko ki…..Idan muka dawo zanci abincin.”

“Allah yasa lapia….”

Yana so ya sanar mata zancen dawowar Ahlam ne kuma sai bakin sa ya masa nauyi. Dakyar dai yace,

“Amin.”

Mota suka nufa suka shiga. Waheedah nata sake saken zantukan da Abiey zai sa a nemota. Ta tabbatar wa kanta zancen Ahlam ne. Don haka ta sauke zuciya kawai. Tana mai zurfafa zantukan lamarin.

Zayn yana tuki .lokaci zuwa lokaci yakan juya ya dube ta. Cikin son ya kawar mata da damuwar yace

“Waheedah… Son ki tamkar wani fure ne da idanuwana suke qawatuwa da kallon sa, hanci na ya ji daddadan qamshin ki.. ruhi kuma ya samu nutsuwa. Idan rayuwa ba za ta yiwu ba tare da ruwa da iska ba, haka ni ma ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba. Jin dadi da walwala da FARIN CIKIN ba za su taba samuwa a tattare da ni ba matukar babu soyayyarki a cikin ZUCIYA ta. Kin zama tauraruwa da ke haska ilahirin bishiyoyi da furannin da suke a lambun zuciyata…”

Dan murmushi kawai ta kakaro tayi. Zayn ya numfasa kawai. Kafin ya saka hannu daya ya riko nata hannun cikin nasa. Sakon ZUCIYAr sa ya ke sanar mata ta ruhi da gangar jikin sa.

Ta dan juya ta kalle shi. Ya kanne mata ido daya yana lumshe mata idanun sa akan ta.

“Wifey na… I don’t need the heavens or the stars. I don’t need gold or riches. I gained everything I could ever want the day that I met you: I gained a steady hand, a kind soul, and someone who I will fall asleep with and wake up next to for the rest of my life. You are my heart – you are my everything. Your love has transformed me!…”

Bata ce da shi komai ba. Ba kuma ta kalle shi ba. Hakan yasa Zayn matse hannun ta da har sai da tayi yar kara. Ya daga hannun nata ya sumbace shi yana murmushi.

A haka suka karasa gidan na The Adams Family. Kai tsaye suka nufi sashen Abiey din su Zayn.

Abiey. Maa. Ahlam. Haj Aisha . Dukkanin su suna parlorn. Ba dadewa kamar tare suke . Sai ga alhaji Nouruh ya shiga shima.

Aka dai yi dan gaishe gaishe. Waheedah ta tsakure a gefe. Gabanta na tsananta bugawa. Tana kaunar Ahlam tamkar yar ta ta jini. Amman auren Zayn ya bata zumuncin da ke tsakanin su

Ta sunkuyar da kanta kasa kawai. Tana lankwasa yatsin hannun ta.

Yayin da Ahlam din gefe. Duk ta sauya tamkar ba ita ba. Ba tsiwar nan. Kawai dai taki kallon wajen Waheedah ta Zayn. Kanta na kan su farfesa Adams .

Zayn yayi shiru bai ce komai ba. Har Abiey dinsu yayi gyaran murya ya fara magana kan jadawalin dukkanin maganar da zai yi. Tundaga kan dawowar Ahlam dakin ta ya karkare da.

“Sai jan hankali da zanyi maka akan adalci tsakanin matan nan naka su biyu. Kar ka duba dan Ahlam kanwa ce ta jini agare ka. Kuma zabin magabanta ne suka hada auren. Kar ka dubi hakan ka muzantawa Waheedah. Wannan ba adalci ba ne. Sannan ka da ka dubi Waheedah ka fifitata akan Ahlam saboda ita din zabin ZUCIYAr ka ce. Kafi karkata akanta. Hakan ya sa ka bakantawa Ahlam … A’ah kar ka soma yin haka. Dukkuwa da nasan ba zaka taba aikata wannan halayya ba. Amman dai na ja kunnen ka ne saboda ZUCIYA bata da kashi. Ko kuwa?”

Ya juya yana kallon dan uwan sa Nouruh bayan ya karasa magana. Alhaji ya kada kai kafin ya shiga cewa,

“Zancen ka haka yake .. Nima bari na ba shi tawa yar gudunmuwar ta tsawatarwa ko ince wani dan haske anawa dan karamin ilimin akan adalci a tsakanin matan da ake aure….

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply