Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 65


Farhatal Qalb 65
Viral

PG:65_

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA…_

____

*A kwance* Marka ta ke, Ya yin da ambaliyar hawaye ke tsiyaya daga idanun ta. Jikokin ta , Yaran wajen Zahara’u na kewaye a dakin suna wasan oji-oji.

Tsakar gidan kuma yan biyun Deluwa ne akan katifa an kwantar da su. Dayar jaririyar idanunta a juye. Makauniya ce bata gani. Anyi maganin anyi sai addu’oi da ake bin ta da shi.

Shigowar Najib kenan gidan ya hangi Marka tana kokarin motsa bakin ta ta kaa sa. Ya yinda ambaliyar hawaye ke tsiyaya daga idanunta.

Da sauri ya karasa wajenta. Ya tattake ya daga ta dakyar yana sauke numfashi. Ya tokare ta da bango. Ruwan shan ta da ke kofi ya dauko yana mai mata nuni da shi.

“Ruwa?”
Ya tambayeta yana mai binta da kallon tausayi. Domin kwarai matuka Marka ma cikin halin haulai na kakanikani.

Marka rigimammiyar tsohuwa da bata ganin kan kowa da gashi. Wai itace cikin wannan halin. Da bakinta ma ta bude tayi magana ta kasa. Sai dai a kwantar a kuma tayar.

Bakin kofin ya kafa mata a baki . Ta shiga sha tamkar zata hadiye har kofin.

Cikin haka sai ga Zahara’u ta rafka sallama. Ta shiga gidan tana tafe tana taunar cingum ..

“Sai kira na ake ta wani faman yi. Kai innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Ni dai da wannan jinyar dama warewa kikayi yasin.” Ta fada cikin ko in kula da gabatarin maganar da tayi. Ba tare da ta auna zancen ba.

Cikin yatsina ta shiga dakin ta zauna tana jan kwan cingum.

“Ina wuni anti zahara’u?”

“Lapia… Kai kuma yaushe ka zo?” Ta tambayi Najib.

Duk kuwa da ya koma gidan gwaggo haule wajen Umman su da zama. Kullum safe da rana yana gidan na su na malam na lado.

Duk kuwa da kyama tar su da muzantawa da marka tayi wa rayuwar su a baya . Hakan bai hana shi kula da ita ba. Dai dai karfin ikon sa.

“Ban dade da shigowa ba. Anti.”

“Okay.,”

Zahara’u ta zauna a kàsa. Ta yage dankwalin kanta tana sosa gashin ta.

Marka na biye mata da kallo. Wani kwaro dai dai saitin marka . Zai shige jikin ta. Cikin wauta ji ka ke tas. Zahara’u ta wanke fuskar Marka da mari. Kwaron ya fadi kasa matacce.

Marka ta fashe da kukan zafin mari. Najib dariya ta so kufce masa ya danne kawai.

“La. Sattin ta ubangiji don na cire miki kwaron ne. Ashe ke zan samu . Kai Allah ya shirya ni. Yi hakuri marka ta”..

Sai da Marka ta sha kukan ta. Tukun sannan tayi shiru tana jan majina.

Marka ta kaikaice tana dan yamutsa fuska. Ji kake sirr ta iska ta fito. Zahara’u ta mike da sauri tana mai toshe hancin ta da bayan kasan hijabin ta.

“Kai Kai Kai. Haba Marka. Na gaya miki ki dai na baje duwaiwai kina bada iska. Ko kashi zaki?”

Nan ma Marka ta bude idanaun ta ta lumshe. Hakan ya bawa zahara’u damar ciccibar markan ta ajiye ta gefe.

Sannan ta dakko fo na manya ta dora marka. Najib ya fice daga gidan da sauri yabar Marka a kan fo.

Ta karasa yi. Dakin ya budade da hamamin bahayar Marka. Dakyar zahara’u ta mata tsarki ta fita da fon zuwa bandaki. Dakin ya dau tsami.

Ta dawo ta tsaya kerere a kanta.

“Zulfa’u ta zo kuwa?”

Nan ma Marka ta lumshe idanu ta bude alamun a’ah.

“Zabba’u fa?”

Nanma Marka ta mata alama da bata zo ba.

Ta dora hannunta akan cikin ta. Tana shafawa. Can ta mike bayan ta gantsare.

“Bari na tafi . Idan Malam na lado ya zo ya karasa miki wasu abubuwan.”

“Ah Zahara’u.. Yanzu kika shigo?”

“Eh na zo ni Deluwa… Tafiya ma zan. Zan dora sanwa.”

“Allah sarki ”

Zahara’u ta fi ce. Ya yinda Deluwa ta tsugunna gaban wuta tana gyaggyara ledojin da zasu kama mata gaushin.

Ba jimawa malam na lado ya shiga gidan . Bayan sa kuma Malam Ubaliyo ne malamin masallacin arewa.

Gaishe da Marka malam Ubaliyo yayi ya tsugunna yana bin ta da kallon tausayi. Wai Marka ce a kwance bata iya daga yatsanta ma.

Ciwon ya faru ne baki daya cikin kwanaki uku. Dan ko a satin da cutar zata same ta ma. Taje bakin kasuwa ta surfawa wanzam damuna ashariya ratsa ratsa da aibace aibace.

Malam na lado ya kalli malam Ubaliyo. Malam Ubaliyo ya sauke zuciya kafin yace,

“Ubangiji Allah ya yaye miki Marka. Ya sa zakkar jiki ce. Allah yasa wannan cuta ta ki.. Kankarar zunubai ce. Amin. Yauwa kafin ki kwanta ciwo ki gafarce ni. Du bada ba zaki iya magana ba ko ambatar wani abun. Malam na lado ya sanar mun damuwar sa ta,

“Kan lalle kin tsaya kan bakan ki na cewar ya aiwatar da shika uku ga Deluwa matar sa. Dan Allah Marka kiyi hakuri ki janye zancen ki. Wannan tsauraran hukunci duk basu kamata ba. Yarinyar nan Hadiza itama ashe auren tuntuni babu kin saka ya shikata Marka. Aka dawo kan Sa’adatu itama ga abunda ya dawo akan diyar ta da ita kan ta . Na lado yace kince kar su soma dawowa gidan nan. Bayan har yanzu da aure a tsakanin saadatun da na lado. Marka kiyi hakuri da abunda labbana zasu furta. Amman bakya ganin wadannan hukunce hukuncen da kike yankewa suna tsauri da kaucewa aqidar islama Marka? Astagfirullah ki dubi zancen da zan fada da idanun Basira… Marka”

Duk kuwa da a kwancen da ta ke. Hakan bai hana Marka dankara masa harara ba. Ji take tamkar inama zata iya mikewa. Ta yi kutufo da shi.

“Marka… Dan Allah ki dubi komai yadda yake ki mayar da shi muhallin sa. Kiyi Imani da Allah da haqiqar sa Marka..Imani na gaskiya shi ne rayuwa da farin ciki. Ba a samun kwanciyar hankali sai dai imani da Allah mai girma da buwaya. Duk zuciyar da ba ta da imani za ta zauna cikin tsoro da rudani da rauni da rashin kwanciyar hankali. Imanin da ake samun tsira da shi shi ne imani da Allah, wanda ma’anarsa shi ne gaskatawa da yankewa cewa Allah shi ne Ubangijin komai, mamallakinsa, mahaliccinsa, kuma shi kadai ya cancanta a kadaita shi da ibada, ta sallah da azumi da addu’a da fata da tsoro da qasqantar da kai, kuma shi ne ya siffatu da siffofin kamala gaba daya, ya tsarkaku daga dukkan wani aibi da tawaya, mai girma da buwaya.Imani da Allah haske ne mai kaiwa zuwa ga adalci, haske ne zuwa ga ‘yanci, haske ne zuwa ga ilimi da sani, haske ne zuwa ga shiriya, haske ne zuwa ga nutsuwa da kwanciyar hankali Marka…

“Imani da Allah ya qunshi imani da Mala’ikunsa, da littattafansa, da ranar lahira, da imani da qaddara, alkhari ko sharri. Irin wannan imanin shi ne samun arzikin mutum, kai shi ne ma Aljannar duniya ga mumini, wanda qarshensa Aljannar lahira ce Insha Allahu. Ashar’ance: Shi ne qudurcewa da zuciya, da furtawa da harshe, da aiki da gabbai, yana qaruwa da da’a ga Allah, yana kuma raguwa da sabon Allah. Idan an gane wannan to a sani tushen karbar ayyuka a wurin Allah shi ne Imani, saboda fadin Allah mai girma da buwaya : “Duk wanda ya yi ayyukan qwarai yana mai imani”. (Al-anbiya’a : 94) Mahimmancin Imani

“Haqiqa mafi falalar ayyuka da tsarkinsu a wajen Allah shi ne Imani, saboda hadisin da Abu Zarrin – Allah ya yarda da shi – ya tambayi Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ya Manzon Allah, wadanna ayyuka ne suka fi falala? Sai ya ce, “Imani da Allah da jihadi a kan tafarkinsa” (Muslim ne ya rawaito shi)Shi ne sababin shiriya da samun arzikin duniya da na lahira, saboda fadin Allah mai girma da buwaya : “Duk wanda Allah ya yi nufin ya shirye shi sai ya yalwata zuciyarsa ga musulunci” (Al-an’am : 125).Kuma imani yana kawar da mumini daga sabon Allah, saboda fadin Allah Ta’ala, “Wadanda suka yi taqawa idan wani mai kewaye daga shaidan ya shafe su sai su tuna Allah, sai ga su suna gani” (Al-aaraf : 201)
Imani sharadin ne na karbar aiki, Allah yana cewa : “Haqiqa an maka wahayi da wadanda suke gabaninka cewa lallai idan ka yi shirka, to tabbas ayyukanka za su rushe, kuma wallahi za ka zama daga cikin masu hasara” (Azzumar : 65).

“Tsarkaken Imani, Allah yana sa albarka a cikin aikin da aka yi a cikinsa, yana karbar addu’o’i da shi, “Haqiqa an maka wahayi da wadanda suke gabaninka cewa lallai idan ka yi shirka, tabbas ayyukanka za su rushe, kuma wallahi za ka zama daga cikin masu hasara” (Azzumar : 65).
Tsarkaken Imani, Allah yana sa albarka a cikin aikin da aka yi a cikinsa, yana karvar addu’o’i da shi. Kiyi imani da Allah Marka. Ki mayarda dukkanin damuwar ki ga Allah. Domin shi din majibancin lamura ne. Ki roke shi domin shi din buwayi ne gagara misali. Ki tsame hannun ki ga dukkanin abubuwan da ba hurumin ki bane. Ki kyale malam na lado da harkar iyalan sa dan girman Allah Marka ..Ko kema Allah zai dube ki da idanun rahama ya yaye maki dukkanin abubuwan da ke damun ki…”

Mugun kallon da ta watsa musu duka su biyun ne yasa Malam ubaliyo hanzarin mikewa tsaye ya kade jikin sa

“To Allah ya kara lapia Marka. Biyu kyautar Allah, Kuna wasa? To Allah ya muku albarka duka. ”

Cewar malam Ubaliyo daya kallo yan biyun Deluwa da ke kan yar katifar su.

Sallama ya sake musu kafin ya fi ce daga gidan. Malam na lado na biye da shi. Hakika malam Ubaliyo ya kambama taurin rai da kafiya irin Marka. Rai a hannun Allah amman taki saduda?

Yayi Allah ya kyauta. Kafin suyi musabaha da malam na lado ya yanki layin gidan sa ya tafi .

**THE ADAMS FAMILY**

karfe tara saura kwata ya shiga gidan. Har karfe shadaya saura bai fita ba. Yana zaune a parlor. Kwanaki 4 kenan a jere yana yiwa sashen Haj Hameedah zaman dole.

Maa na hankalce da shi. Amman tayi biris da shi. Har aka ja tsawon kwanaki 4.

Haka zai karaci zaman sa yana soshe soshen keya. Waheedah kuwa da wuri take shigewa daki ta murza mukulli.

Da ke an musu hutun second semester break. Tana gidah babu inda take zuwa. Zayn dinma bata bari su kebance su kadai.

Gashi ya tsiri wani feleke agaban kowa ya rika nan nan da ita . Don haka take kauracewa ganin sa. Don tsaf zai iya aikata wani abun kunyan agaban Maa. Domin yayi na farko wancen satin bata kaunar amaimaita na biyu.

Haj Hameedah na zaune a parlorn tana danna system din gabanta. Gefenta kuma tarin littattafai ne da suka danganci fannin tiyata.

Ta daga idanu ta dube shi. Yana zaune ya tsurawa kafar bene idanu. Tamkar waheedan ce a wajen. Yadda ya mayar da hankalin sa kacokam wajen.

“Nadra…”

“Naam Maa.”

“Je ki kirawo Waheedah. ”

“Bari na kirata Maa.” Cewar Zayn.

Kallon da Haj Hameedah ta bishi da shi ne yasa shi komawa ya zauna yana mai sosa keyar sa.

“Okay Maa.”

Mikewa Nadra tayi. Zayn ya gyara zaman sa yana hasaso ta inda zata sakko.

Can Haj Hameedah ta mike itama tayi saman. Sun dan jima tukun kafin ita ta sakko ta koma parlor ta cigaba da aikin da take a kwamfuta.

Can kuma Nadran ta sakko da wani akwati a hannun ta. Daga karshe kuma Waheedah ta sakko.

Sanye cikin laffaya baka data sha aiki pink. Ta bala’in kata’in yin kyau. Da har Zayn ya kasa dauke idanun sa daga kanta.

Ga wani kamshi da ke tashi daga kayan nata. Na turaren turara kaya na kamfamin yerwa incense and more.

“Ta shi ku tafi ..” Haj Hameedah ta fada tana kallon Zayn.

Bakin sa ya wangale FARIN CIKI marar misaltuwa ya wanzu a ZUCIYAr sa. Ya kasa boye wa . Ya zube gwiwoyin sa yana mai yi wa Haj Hameedah godia. Kai kace wata babbar kyautar aka masa.

Zayn ya mato akan kaunar Waheedah. Ta masa muguwar shigar zurfin da baya iya boye kaunar da yake mata a ko’ina.

Waheedah dai tana tsugunne. Yatsunta ta hade su tana matsawa. Kunya duk ta ishe ta.

“Allah ya saka da alkhairi Maa. Allah yaja kwanan ki. Ya biya miki dukkanin bukatin ki Maa. Allah ya shi albarka.* Zayn ya shiga yi wa Maa sumbatun godiya.

Nadra nata dariya. Lalle Yayan na su ya zauce akan soyayyah.

“Amin… Allah ya muku albarka duka. Ka riketa amana Zayn. Na baka amanar Waheedah kai ne mahaifin ta kai ne mahaifiyar ta a yanzu. Ka sani ranka zai yi mummunan baci idan har kayi mata wani abun. Waheedah kibi Zayn. Ya zama miji agareki. Duk abunda yace kiyi. Idan har bai sabawa addinin musulunci ba. Yi nayi bari na bari. Aljannar ki na ga karkashin kafar sa. Allah ya kauda fitinah a tsakani ya baku zuriya ta gari. Ku tashi ku tafi dare yana ja ”

Waheedah ta shiga tsiyayar da hawayen data rasa na menene ma. Amman dai yanada nasaba da nasihar Maa. Ta goge hawayen na ta. Haj Hameedah ta rungumeta jikin ta tana mai cigaba da saka musu albarka.

Nadra ta rakasu har wajen motar. Zayn ya karbi akwatin ya saka a booth. Sannan ya bude gidan tuki ya shiga.

Sai bin Waheedah yake da kallo. Ta sunkuyar da kanta ta cikin laffayar. Ya tashi motar suka bar gidan .

A rahama suya ya tsaya. Ya siyo kaji da tsire. Ya sake tsayawa a wani shopping mart ya saya su fruits da yoghurt. Alokacin har an fara yayyafi na ruwa.

Ya bude motar ya shiga yana murmushi. Ya rankwafa saitin ta. Da har tana jiyo numfashin sa.

“My love….. Kinga an fara yayyafi na masoya.. Allah ya bamu albarkar wannan dare da zamu raya… Ki ce Amin ”

Bata ce kanzil ba. Daman yasan ba zatayi magana ba. Ya ja motar suka dauki hanyar gidan sa.

Baba mai gadi ya bude gate suka shiga ciki.

“Tsaya Ina zuwa ..”

Booth ya bude ya dakko akwatin na ta ya bude gidan ya shiga da shi ciki. Ya koma ya bude motar.

Ya tattake ya sunkuci Waheedah a hannu sai nishin nauyi ya ke🤣

“Ka sauke ni please ..” Ta fada ahankali. Kasan zuciyar ta kuwa kunya ce duk ta cikata ta tumbatsa.

Bai direta a ko’ina ba . Sai dakin kasa. Wanda ke a matsayin nata tun ada. Amman yanzun an canza furnitures din gidan baki daya.

Saboda gudun abunda zai je ya dawo. Zayn din da kansa ya canza komai har ta cokali. Don kada Ahlam ta dawo gori ya shiga tsakani.

A tsakiyar gado ya ajiye. Ya zare takalman kafarta ya ajiye a gefe Durkusawa yayi agaban ta. Ya dage laffayar data rufe kanta da shi.

Fuskarta ta bayyana. Idanuwan ta sun kumbura da hawayen da take ta zubarwa.

“Waheedah…Ki amince mu yi tsaftatacciyar soyayya. Sai yanzu
na gano cewa a duniya babu abun da ya kai
samun masoyiya dad’i, a duk lokacin da na rasaki
ban san halin da zan shigaba, buri na yanzu bai wuce na ganin kyakkyawar fuskar ki dauke da FARIN CIKI har ya zuwa ZUCIYAr ki ba, ina alfahari da ke Waheedah, A duk inda na kasance, Ina mai son ganin FARIN CIKIN ki a koda yaushe.

“Waheedah, I dreamt that you were mine, and then I woke up smiling because I realized it was not a dream. You are already mine! Waheedah You are that woman who transformed my imperfections into perfections, just by the touch of your love. Love you my dearest wife!”…”

Ya karasa fada yana mai sumbatar hannuwanta da yatsun ta ke dauke da lalle sunyi maroon. Sai kamshin khumra ne na dufra ke tashi daga hannuwan ta. (yerwa incense and more)

“Waheedah, Your heart is full of love and affection. Your hands are always caring. I am lucky to have you as my wife. ke ce FARIN CIKIN da ke cikin ZUCIYA tah ,It was always you Waheedah ♥️I love you soo much…”

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply