Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 62


Farhatal Qalb 62
Viral

PG:62_

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA…_

______

*A* hankali ya fara zura fuskar sa ya leka cikin dakin. Kafin gangar jikin sa ta biyo baya.

Gabansa na tsananta bugu. Hamdala ya saki ganin babu kowa acikin dakin. Haka ma parlorn kasan. Dan haka ya murza key ya koma bakin gadon ya zauna

Motsin ruwan dake zuba a bandaki ne ya tabbatar masa tana ciki. Don haka ya gyara zaman sa. Ya janyo wayar sa a aljihu ya shiga dannawa.

Bayan ta kammala wankan. Ta sake tara ruwa ta zuba masa after bath khumrah na kamfamin turaren yerwa incense and more. Ta dauraye jikin ta da shi. Take jikinta ya fara kamshi sosai.

Ta daura bathrobe a jikinta ta fito daga cikin bandaki tana adduar fitowa daga cikin bandaki.

Kai tsaye ta wuce wajen mirror ta zauna bayan ta dauki wata kulaccam ta kamfanin turaren yerwa incense and more . Ta shafe jikin ta da shi. Lungu da sako na bayan kunnen ta da kasan maman ta da cinyoyin ta.

Zayn ya zuba mata idanu. Sam batasan yana dakin ba. Sai data tsiyayi khumra a tafun hannunta tana shafawa a jikinta. Tana daga idanuwa ta sauke akan mirror ta hango shi ya mayar da nutsuwar sa da tattaro hankalin kansa baki daya ya dora akan ta. Ta janyo glass ta zura don tabbatarwa.

Wani abu ya taso ya tokare mata a makoshin ta. Ta janyo hijabin da ke sakale a gefe ta zura.

Dan murmushi ya bi ta da shi yana mai lashe kasan leben sa.

Drawer ta bude ta dakko kayanta ta koma can karshen closet ta zura su. Ta zura hijabin ta ta rataya Jakarta a kafada.

“Ina kwana?” Ta gayshe shi kanta a gefe.

Ya mike ya isa inda take a tsaye ya riko ta. Ta shiga zillewa. Amman da ke karfin ba daya ba ne… Sai ya sake tukwikwiye ta . Sam ta kasa kwatar kan ta.

“Makaranta…..?” Ya tambayeta cikin muryar rada. Ta hanyar dora bakin sa akan kofar kunnenta .

“Uhmmmm” Tace dashi, Domin baki daya ya kashe mata jiki. Ta kasa tabuka komai.

Janyota yayi suka zauna a bakin gadon. Ya yinda ya riko hannuwanta ya saka acikin nasa. Idanuwan sa na sauke akan ta. Ta kasa hada idanu dashi saboda kwarjini da girman sa daya kamata..

“Waheedah…..” Ya kira sunanta cikin kwarewa da jan haruffan karshe.

“Na’am…”

“Bazan gushe ba fa-ce na cigaba da baki hakuri …. Ko kinsan Dawood?”

Yana karasa fadar sunan Dawood gabanta ya yanke ya fadi. Daman jikin ta ya soma raya mata wani abu game da chatting dinsu da Dawood…

“Kinyi shiru …. ”

“Zan makara ne a school..”

Ya dan matse hannunta da har sai da tayi yar kara. Ya kuma saka hannu ya lakuto kumatun ta. Kafin yace,

“Saura 1 hour 30 minutes ku shiga lectures… Ai inada timetable dinku. Dan Allah kiban hankalin ki nan. Ki auna zance na. Tabbas ni me lefi ne awajen ki Waheedah… Nayi miki lefuka da dama wadanda na ke neman gafara awajen ki a koda yaushe. Amman this particular one da nake jajantawa Waheedah ki yafe mun. Soyayyarki ce ta jawo haka. Na dade zuciyata na neman begen kaunar ki. Na kasa sukuni. Waheedah kece FARIN CIKIN ZUCIYA tah.. kaunar da nake miki Waheedah dadaddiya ce,.. Har hankali na ya gushe na nemi samun soyayyar ki ta hanyar fito miki a zummar ni…. Ni….ne Dawood.” Yana karasa fada ya runtse idanun sa. Hawaye suka shiga kwarara daga idanun sa…

Ya zare ta daga jikin sa. Ya zube gwiwoyin sa a kàsa ya durkusa agabanta. Ya janyo hannuwanta duka biyun ya rike .

Ahankali cikin murya tamkar ana busa sarewa. Cikin wani salo ya shiga cewa,

“Soyayya na iya chanja mutum, domin ita soyayya ba’a ganin ta balle a koreta ko a hana ta shiga ZUCIYA. Ba’a cewa soyayyah ga yadda ake so, sai-dai kayi yadda take so. Ba’a shiryawa soyayya, ko babu shiri
Idan tazo kamar mutuwa haka zata shiga ZUCIYAr mutum. Duk wanda yayi so dan Allah to shine keda riba, Waheedah soyayyar ki ce ta dasar mun da FARIN CIKI har tayi tsiro ta yi reshe a cikin ZUCIYA tah .. Kwarjini da fargabar ki suka hana ni fitowa na nuna miki ni ke kaunar ki… Hakan yasa na fito da dabarar shiga zuciyar ki da sunan Dawood. Tabbas nayi babban lefi agareki….. Kauna ce ta haddasa hakan ba komai ba. My prayers were answered the day that I met you. Tun kallon farkon da nayi miki…”

Ya karasa fada yana murza hannunta. Hade da sunkuyawa ya sumbaci tafukan hannayen nata. Dai dai lokacin da ta daga idanu ta sauke akan fuskar sa. Ta ke ta tuno ranar da suka taba haduwa sukayi gware.. Girar sa da suke cike da gashin da suka kusa hadewa saboda yalwar su…

Ya sake daga kansa ya sauke akan idanun ta. Ta janye nata da sauri. Ya cigaba da cewa,

“Waheedah .. You are a blessing in my life, and I’m so lucky to call you my partner for the rest of our lives. Your smile is my everything. Cikin soyayyar ki babu sirki, na gani kuma na gamsu kuma na tabbatar da ke me kauna tace ta… Ko bakya mun kallon miji kina mun kallon dan uwa. Waheedah, hakika, ki sani, ni bazan taba son wata ya mace wacce bake ba, domin zuciyata bazata taba jindadin zama da wata ya sama dake ba, duk wani jin dadin duniya bai damen ba indai babu ke….”

Kalaman sa suka sata dariya. Wasu mazan iyayen karya, Sam ba ta ido.. Ta yamutsa fuska tana mai sake dunkufar da kanta gefe… Kafin tace da shi,

“Ni kuma? Ai na dauka ba zaka iya soyayyah da karamar yarinya ba .. Renon ta zakai ko? Domin karamar yarinya ai ba matar da zaa aura bace. Ballantana har ayi rayuwar aure ta re…”

Nan da nan Zayn ya harbo jirgin maganar ta. Ranar da kishi yasa yayi barambarama. Da event din bikin sa ne. Alokacin da Dawood abokin sa yace yana kaunar Waheedah da aure. Shine Zayn din yake bashi amsa da wannan karamar yarinyar ze aura? Kasan leben sa ya kamo ya cije. Ya sosa keyar sa yana marairaicewa,

“Allah… Ba wai har zuci maganata take ba. Na gaya miki tun kallon farko da nayi miki zuciyata ta kamu da kaunar ki… Kishin kaunar da nake miki ne. Ina burin na mallake ki ki zama a matsayin matata… Sai kuma dawood din ke nuni da yimin shigar sauri. Wallahi kishi ne da kaunar ki suka saka na fadi haka a lokacin. Ba wai har zuci da gaske nake nufi ba. Ki mun afuwa my love…. Ai laifukan da nayi da yawa ..” ya karasa fada yana mai saka hannuwan sa akan kunnuwan sa alamun ban hakuri . Kafin ya cigaba da cewa,

“Rayuwata fansarki ce, Zuciyata tuni ta rikirkice, Kunnuwana sun ki karban zance, idanuwa na sun so su makance. Duk sanadin ki amshi soyayyar tawa da zaki kokarta ki amince mini, Mulkin ZUCIYAr ki shine aiki na, samun FARIN CIKIN ki jindadi nane, Murmushinki anashuwa ce ga zuciyata, Waheedah… Ni bawa ne ga zuciyar ki…..”

Agogon da ke daure a wutsiyar hannun ta ta kalla. Ta mike da sauri . Ya tashi shima a tsayen yana jiran ta.

“Muje na sauke ki….”

Ba ta ce masa komai ba. Ta bude kofar da mukulli ta fice .

Tana sauka kasan ta ja ta tsaya. Ganin Maa da tayi itada Nadra . Ta kakaro murmushi ga kunya data ishe ta. Bayan ta kuma Zayn ne.

Me su Maa zasu zata. Wayyo! Inama kasa ta tsage ta fada, Haka takeji saboda yadda kunya ta dubibiyeta. Ga haushin Zayn da duk shi ya ballo wannan babban aiki.

“Maaa..” Ta fada a kunyace. Hade da tsugunnawa har kasa.

“Naam yar gidan Maaa. Har zaki tafi?”

“Eh.. Barka da safiya! An tashi lapia?”

“Alhamdulillah Waheedah .. Allah yabada sa’ar karatu.”

“Aamin… Ai yanzu ya zo….”

“Wa?” Maa ta tambaya .

Hannu Waheedah tasa ta nuna bayanta. Gaba daya a kunyace ta ke.

Haj Hameedah tayi murmushi kawai. Kafin tace,

“Allah sarki… Allah ya miki albarka.”

“Amin Maa.”

“Aunty Waheedah nah. Barka da safiya.”

“Barkan mu sis Nadra.”

“Maa Ina kwana?” Ya tsugunna har kasa shi ma.

“Alhamdulillah.. Fita zakai?”

“Eh… Zaz..zan…zanje office. Na shigo zan gayshe ki ai naga ba kowa a parlorn ”

“Masha Allah… Ya Ahlam din?”

“Alhamdulillah…… ”

“Okay kaje ka dawo zamuyi magana.”

“Okay Maa.”

“Zaka ajiye Waheedah ne. Ko driver ya kai ta?”

“No! Zan kai ta”

“Alright…”

Fita suka yi.. Yana gaba tana biye da shi a baya. Suka karasa wajen motar. Nadra ta nata kallon su ta window tana murmushi.

Ya bude mata kofar ta shiga…Sannan ya koma matakin driver ya zauna . Ya tashi motar da addua suka fice daga gidan…

Akan hanyar tafiyar su. Go slow suka hadu da shi. Zayn ya saki tsaki kawai. Yana kallon waje. Dandazon yan makarantar su Waheedah ta sakandire a baya sunata wucewa.

Ya saki murmushi kafin ya juya ya kalleta. Ya kamo hannunta daya yana mai jan yatsun.

“Haduwar da nayi miki ta biyu anan ce… Kun taho ke da kawayen ki ku uku an taso ku daga makaranta…. Ina gano ki bugun ZUCIYA ta ya tsananta Waheedah…

“Ya kamo hannun ta ya saka a saitin zuciyar sa …

“My love for you knows no borders, knows no limits, never fades, and will last forever. Insha Allah … Waheedah, Your happiness means everything to me.I would cross a hundred oceans just to be with you and hold you in my arms. I would climb the tallest mountains just to fall asleep next to you. I would do anything for you. I love you long time … 💕”

Waheedah ta sauke zuciya…. Kalaman sa na dada ratsa duk wasu sassa na zuciyar tah. Ba karya ya iya kalamai masu ratsa ZUCIYA da yalwatar FARIN CIKIn tah.. Mamaki ya dada mamaye ta. Ita kanta ta kasa gane wacce irin madaukakiyar kaunar da Zayn ya ke ma ta.. Kauna ce ya ke mata tacacciya marar gauraye. Ita ba yar kowan kowa ba. Gaba da baya yar talakawa ce. Batada wani usuli na manyan gidah. Ba ficacciya ba ce a gurbin karatu yanzu ta sanya kafafu. Ita ba shahararren kyau ba da zaa ce ya mato akan hakan. Duba da shi din da tsatson sa gaba da baya larabawa ne. Amman sai ita? Ita tasan ba dan sharrin soyayyah ba. Ita din ba ajin Zayn ba ce. Da har ko da yaushe sai ya roketa da ta tallafa ta amince da kokon barar soyayyar sa… Wani sashen na zuciyar ta ya hasaso mata Ahlam… Ta runtse idanun ta da sauri tana mai cije lebe. kunyar Ahlam kadai ta isa ta hanata nunawa Zayn kaunar da take masa. Duk kuwa da bata kai tasa ba.

Har an basu hannu. Don haka ya gangara gefen titi yayi parking motar. Ya mayar da nutsuwar sa da kallon sa kacokam akan ta. Hawayen dake tsiyaya ahankali. Ya janyo tissue ya goge mata. Ta kalle shi da sauri tana gogewa kafin ta mayar da zaman gilashin idanun nata… Shiru ya biyo baya. Kafin Zayn ya tada motar. Suka koma kan titi suka cigaba da tafiya.

Ya kai ta har cikin makarantar. Har kofar twin theatre inda zasuyi lectures… Zata fita taji kofar a rufe. Ta juya ta kalle shi ya daga mata gira yana murmushi. Murya kasa kasa yace,

“Kin hakura….? Maganan Dawood? Ki yafemun please…. Da maganar da nayi kan cewa ba ki isa yin aure ba. Kai na bisa wuya ki mun afuwa.”

“Allah ya yafe mana baki daya…”

Ya zare seatbelt dinsa ya matsa . Ya sakar mata peck a gefen kumatun ta.

“Wannan turaren na ki kullum cikin tunanin sa na ke…. Waheedah, I am forever thankful to have met you. You are my breath and my light. You are the reason my days are filled with happiness. I love you more than I knew possible. You are my soulmate.You bring me to life! I’ve fallen in love many times – and always with you! Allah ya miki albarka… Wannan soyayyar ta mu daga Allah ce… DESTINED LOVE….💕”

Tayi murmushin jin dadin kalaman sa da adduar da yayi mata.

“Amin…. Nagode”

Ya zaro 1500 cikin aljihun sa ya zura mata a jaka. Zatayi magana ya dora yatsan sa akan labban ta

“Ayi karatu lapia…”

Ta sauka daga cikin motar. Kai tsaye ta shige cikin theatre. Ya dan jima a zaune cikin motar yanata murmushi kamar sauna. Tukun sannan ya tada motar ya wuce ofishin su kai tsaye..

#FARHATAL QALB

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply