Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 61


Farhatal Qalb 61
Viral

PG:61_

___

*Gefen* gado taje ta zauna tana faman sauke ajiyar zuciya, tana sane taki sanar dashi cewar Maa ta tafi yayi ta zama a bathroom ɗin ita ba ruwanta. Kafin ta gama zancen zucin da takeyi kawai taga ya fito sukai ido hudu, ta janye nata gefe tana cizon farcen yatsanta.

A hankali ya karasa inda take zaune ya tsaye yana kare mata kallo. Shikam me zai yiwa wannan baiwar Allahn ta yadda cewar shi din yana sonta da gaske ba wai wasa ba? Me zai mata ya tabbatar mata da cewa be aureta dan ya cusgunawa Ahlam ba?

Muryarta yaji tana cewa.

“Yah Zayn zaka danneni fa..” Zayn ya kalleta, gani yai sauran kiris ta fada kan gadon. Maimakon ya matsa sai ya dora kafarsa daya a gefen gadon, Waheedah ta zaro ido, d’an rankwafawa yai ya sata a tsakiyarsa kamar mai san yi mata rada.

“Please Ya Zayn bana so.”

Ga mamakinta sai taga ya sake rankwafawa kawai sai ta kwanta akan gadon tare da kauda fuska cikin ranta tana fadin kaci kanka.

“Oh Masha Allah dan naga kin fiso muyi maganar a kwance ko?”

Bata kulashi ba saboda bata san hirar tasu tayi tsayo, so kawai take yabar mata dakin amma bashi da niyar yin hakan. Ji kawai tayi ya kwanta a bayanta tare da rikota ta hanyar sanya hannu ya riko shafaffen cikinta. Waheedah tayi saurin zaro ido kirjinta yana wani irin bugawa, gani kawai take Ahlam tana kallan irin cin amanar da suke yi mata.

Idanuwanta a lumshe sakamakon wani irin yanayi da ta tsinci kanta, murya na sarkewa take faɗin.

“Yah Zayn k…”

Tattausan tafin hannunsa taji a saman lebenta, ji tayi yana kokarin juyo da ita wajansa, da sauri ta tirje tana girgiza kai.

“Yah Zayn bazan iya ba, dan Allah kadena tabani bazan iya wannan cin..”

Zayn ya sake katse mata hanzari ta yadda yake goga mata dogon hancinsa da tattausan lips dinsa akan fatar wuyanta, gabaki daya numfashinsa dake fitowa ta hanci da lallausan gashin daya kaawata wajan bakinsa zuwa habarsa sai sake kashe mata jiki suke, banda tsuke kafafuwa babu abinda takeyi. Zayn ya dan rintsa ido yana girgiza kai, husky voice dinsa ne ya daki cikin kunnanta inda yake cewa.

“FARIN CIKIN ZUCIYA tah (My Farhatul qalb) kina tunanin na aureki ne dan wata manufa tawa akanki ko akan Ahlam?”

Waheeda tayi shiru ta kasa cewa komai, Zayn ya dan saki murmushi tare da janyota, gabaki daya sai ta juya suka fara kallan juna tayi saurin rufe ido. Bazata iya kura masa ido sosai ba saboda wasu sirrika dake cikinsu, ya hadiye wani mugun saliva wanda tsagwaran san ya mallaki lips din ta dake ta faman motsawa tamkar wata mai shan sweet. Yaci gaba da cewa.

“Ki cire tsoro da duk wata shakka da kike yiwa Ahlam kizo kiyi biyayyar aure, na dade ina jiranki, zuciyata ta jima a cikin so da kaunarki, ki tausaya min ki shigo cikin rayuwata ko zan samu jin dadi da kwanciyar hankali.” Ya karasa maganar yana shigar da fuskarsa gefen wuyanta. Wasu hawaye ne suka dinga bin kyakkyawar fuskar Waheedah, ta shiga girgiza kai tana zamewa daga jikinsa, ganin ya hanata yasa ta fashewa da kuka, Zayn ya rintsa ido kukan ta yana jinsa har cikin ransa, ba zai iya jurewa ba dan haka yai saurin matsawa daga jikinta, muryarsa tana sarkewa yace.

“Ki gaya min abinda kike so nayi wanda zai sa ki kasance a cikin rayuwata ta har abada, sanar dani please but banda saki bana san jin kalmar nan daga cikin bakinki.”

Yadda Waheedah taji yayi maganar ne yasa kirjinta bugawa, tunani ta farayi, yanzu me zatayi wanda zai sa ya kyaleta? Share hawayen tai tana fadin.

“Ina so kaje wajan Aunty Ahlam ka tambayeta, idan har ta amince dani a matsayin abokiyar zamanta ina mai tabbatar maka zanje gidanka a matsayin matarka. Idan kuma bata amince ba ina so dan Allah ka rabu dani kaje ka rungumi matarka, dama a duniya ba komai mutum yake samu ba.”

Zayn yai mata wani mugun kallo wato sai da ta tabbatar da cewa Ahlam ba zata taba yadda da ita a matsayin kishiya shine tace haka. Bazai mata dole ba hakan yasa shi tashi zaune yana jan dogon hancinsa wanda tsarin yanayin halittarsa ya karawa fuskarsa matukar kyau.

Tsaye ya mike yana so ya kalleta sai dai zuciyarsa na san ta koyi yin hakuri da kasancewa da ita har zuwa lokacin da zatayi hankali ta gane cewa shi din mijinta ne mai tsananin kaunar ta.

“Shikenan zanje, ina san kiyi addu’a ki roki Allah abinda kike so, ni kuma zan tayaki da amin koda kuwa rabuwarmu itace ta ratso tsakanin mu.”

Hanyar fita yayi, har ya kama hannun kofar ya murda sai yaji kamar ya koma, ya juya tare da kallanta, tana kwance idanunta a rufe, girgiza kai yayi kawai ya fice zuciyarsa na tsananta harbawa. Yayi sa’a parlorn babu kowa har ya fice daga gidan. Mota ya shiga tare da dora kansa jikin glass door yana jin wani irin yanayi, harga Allah yana matukar san ganin Waheedah a tare da shi, sai dai yaga alamar samunta lokaci guda zai bashi matukar wahala dan yana hango tsoran Ahlam a can cikin idanuwan Waheedan. Dakyar ya iya samun damar kunna motar ya wuce gidansa cike da tunaninta.

Fitowa yayi daga motar hannunsa rike da briefcase dinshi ya nufi cikin gidan kansa tsaye.

Zaune a kasan carpet ya tarar da Ahlam tana waya, ya karasa ya zauna kan daya daga cikin kujerun parlorn, kallanta yai yaga fuskarta tayi wani iri alamar taci kuka har ta godewa Allah. Inda yake zaune bata kallaba ballantana yasa ran zata amsa masa sallamar da yayi. Yanata zama a wajan amman Ahlam bata da niyar katse wayar da takeyi, ran Zayn ya fara sosuwa cikin bacin rai yake kallanta yana fadin.

“Bansan wace irin mata bace ke, kina ganin na shigo har na samu guri na zauna amma baki san ki ajiye wayar ba, a haka kike tunanin zan yi rayuwa dake ke kadai? Bakisan yadda zaki kula da mijinki ba bare ki bashi girmansa na matsayin miji?”

Cikin rashin damuwa Ahlam ta katse wayar tana yi masa wani irin kallan raini take faɗin.

“Oh wai kai har yanzu kana tunanin zan yi maka wani abun? Zayn ka manta cewa amanata kaci ta hanyar auro wacce ta gama sanin sirrina? Kun gama cin amanata kake tunanin zan baka muhimmanci?” Ta saki wani murmushin takaici tare da gyada kai tana cizon lebenta na kasa.

“Wallahi indai sai a waje na zaka samu farin ciki zaka dade Yah Zayn, kaje can ita munafukar ta yi maka duk wani abu da kakeso, amman indai nice nagama.”

Tana gama maganar ta sake bude wayarta, wannan karan chatting ta ci gaba da yi tana dariya. Wani irin bacin rai ya bayyana a fuskarsa ya mike tsaye yana girgiza kai irin na takaicin nan yace.

“Dama can mekike yi min Ahlam? Tunda mukai aure mekikai min da zan iya nunawa nace naji dadi?”

Bata kulashi ba ya cije lips zuciyarsa na zafi, cikin son ya bata mata rai shima yace.

“Ko yanzu daga wajanta nake, kuma Alhamdulillahi sai da na samu fiye da abinda baki san matan aure na yiwa mazajensu ba. Ke kuma ki zauna a haka kicigaba da chatting dinki har zuwa randa zamuga ribar yinsa.” Yana kaiwa nan ya juya zai bar mata parlorn yaji tana cewa.

“Ai dama na gane cewa ba tun yau ta fara baka abinda bana baka ba, ni tunda naji kace ita nasan dama kun dade da mallakar juna a watse, gwarani sai da mukai aure ita kuwa fa? Yanzu na san ragowar abinda ka rage a wajanta shi kake son kwakulewa daga nan sai na fara jin kace zakai wani auran.” Habawa Ahlam ta sosa

masa zuciya, metake nufi da kalamanta? Zarginsa takeyi kome? Lallai dole ya takawa Ahlam burki akan tunaninta. Juyowa yai yana sake kallanta, tana zaune a inda take tana murmushi tare da danna waya.

“Koma dai menene kekika janyo, idan ma iskancin nayi tabbas yayi min dadi tunda gashi har na aureta ta zama kishiyarki sai ki gaya min dame kika fita? Kuma bari kiji na gaya miki na dena wani lallabaki akan kiyi hakuri, kar Allah yasa ki hakura. Waheedah kuma matatace wacce tasan darajar aure tasan darajar miji, ba irinki ba da chatting kawai kika bawa duk wani lokaci naki.” Yana kaiwa nan yai tafiyarsa, kalamansa kuma sun konawa Ahlam rai da zuciyarta. Afusace ta mike tabiyo bayansa, kofar ta murda taji an rufe ranta na suya take fadin.

“Wallahi karyane Waheedah ba zata taba zama matsayi irin nawa ba, Waheedah yar talakawace wacce bata san komai ba sai wahala da kauyanci. Kuma kaima nasan ka aureta ne kawai dan tazo tayi maka bauta tunda kasan ita din yar wahalace.”

Kafa tasa ta buga masa kofar dakin sannan ta juya tana masifa da bala’i, ji take kamar ta tsaga kofar ta shiga cikin dakin tai masa shegen duka ko zuciyarta zatai sanyi.

Zayn kuwa yana shiga kamar yasan zata iya biyoshi ya murzawa kofar mukulli, briefcase dinshi ya ajiye akan madubi shi kuma ya karasa wajan gado, a hankali ya fada saman shi tare da rintsa idanuwa, tunani ya fada yana jin zuciyarsa tamkar wuta, sam baya cikin jin dadi saboda ta ko’ina baya samun farin ciki, duk inda yake babu farin ciki gaba kura baya sayaki, dama haka mata suke? Waheedah dan yana santa sai gwarashi takeyi yadda taga dama? Ahlam na gwarasa cikin borin kunyarta da babu gaskiya a ciki, yanzu ya zai yi? Ta ina zai fara yiwa Ahlam bayanin cewa sai ta yadda sannan Waheedah zata amince masa? Gashi yanzu yazo ya sake damula komai.

“Ya Allah.” Ya furta yana rintsa idanuwa. Yana jin muryar Ahlam harta gama ta bar wajan, kansa ne yaji yana masa wani irin nauyi kamar an dora masa dala da gauran dutse.

“My love..” Ya fada yana hango hotan Waheedah acikin idanuwansa. Maimakon yaji soyayyarta na raguwa a’a sai yaji ana sake ninka masa. Wayarsa ya zaro daga cikin aljihu ya lalibo sunanta, kamar ya kira sai kuma ya fasa besani ba ko tana tare da su Maa. Online ya hau ko zai ganta yana kunnawa yaga Ahlam is online, yaja dan siririn tsaki, shi kam be taba hawa yaga bata kai ba saboda tsabar jarabar santa da chatting. Contact din Waheedah ya duba yaga ta dade bata hawa WhatsApp din, ya dan duba abinda zai iya dubawa ya sauka tare da kifa kansa akan pillow….

Zayn yayi iya yinsa wajan ganin bacci yazo masa amman ya kasa, banda juyi akan gadon babu abinda yakeyi. Yadda zai yiwa Ahlam magana akan ta amince Waheedah ta zama mallakinsa ita kawai yake nema, ya rasa dalilin da yasa Waheedah ta bashi wannan sharadin, gashi daga shigowarsa ya batawa Ahlam din rai. Juyawa ya sakeyi yana mai rintsa idanuwa tare da tunanin anya zai biyewa Waheedah? Gaskiya ba zai biye mata ba dan ya gaji da zama babu ita a tare dashi, idan kuma ba so takeyi zuciyarsa ta samu matsala ba akan soyayyarta. A ranar haka Zayn ya karaci juyi a gado, gashi ko aikin office da ya taho dashi gida kasa yi yai bare ya rage.

Tashi yai ya gabatar da sallar nafila, ya dade yana addu’o’insa kafin ya tashi, gado ya koma tare da janyo wani english novel yana karantawa, sai dai tunaninsa gabaki daya yana kan matarsa abar so da kaunarsa sannan kuma FARIN CIKIN ZUCIYAR sa. Bashi da wani buri irin yaga itama ta sakko daga dokin tsoran Ahlam da takeyi, wanda yake neman ya hanata ciki umarnin ubangiji. Har aka kira assalatu bai rintsa ba haka ya tashi ya sake yin sabuwar alwala ya fito ya tafi masallaci. Bayan sunyi sallah ya dawo yaje ya yiwa Ahlam knocking dan ta tashi itama tayi, bai jira ta bude ba ya nufi bedroom dinsa ya fara shirin fita.

Yasan dama ba wani breakfast zai samu ba a wajanta hakan yasa yana gama wanka yasa kayansa yai duk abinda ya zame masa al’ada ya feshe jikinsa da turaruka na musamman, fitowa yai kafadarsa rataye da briefcase yana danna waya. Ahlam ya gani tsaye a bakin kofar dakinta tayi kicin-kicin da ita Zayn ya kauda fuska yana nufa hanyar fita yaji tana cewa.

“Za’a fita inda aka saba zuwa?”

Ya dan yi murmushi, kallanta yai yana lumshe idanuwa yace.

“Kwarai da gaske kina da sautu ne?”

Rai a bace take yi masa wani kallo mai nuna bacin rai Ahlam ɗin ke cewa.

“Wallahi Zayn ka badani, ni wallahi kacuceni ina jin bakin cikin irin yarinyar da zaka auro min matsayin kishiya sai Waheedah, duk yan matan dake fadin jihar Kano. Ina gaya maka ni bazan iya kishi da yarinyar nan ba wacce a gabana ta fara sanya bra, ta fara sanya kaya na alfarma, a gabana ta fara iya sanya lipstick ace kuma ita zaka kawo min a matsayin wacce zan hada miji da ita, tabbas ka yaudareni.”

Zayn ya dan lashi kasan lips din shi tare da sauke numfashi yana murda handle zai fita yake cewa.

“Dama bake na aurowa Waheedah ba, na aureta ne saboda ina santa, itace zata iya bani duk wani hakki na aure ba wai kyal-kyal banza ba.”

Kamar yasan zataji haushi, yana gama magana yai saurin ficewa ya rufe kofar da key din hannunsa. Yana jinta sai murda kofar take yaje ya bude mota wace tuni an gama wanketa sai sheki takeyi tana walwali. Briefcase din ya ajiye a back seat tare da jan numfashi yana girgiza kai, motar ya kunna ya fice daga gidan gaba daya. Kai tsaye gidan Maa ya wuce, a waje yai parking saboda yana son fitowa ya tafi aiki. Yana shiga mai gadi ya gaishe dashi Zayn ya amsa cikin sakin fuska ya shiga sashen Maa. A parlor ya tarar dasu Waheedah kuma tana kitchen ya gaishe da Maa kannansa suka gaishe shi.

Idanunsa na hanyar stairs yana son zuwa wajanta kawai yaji motsi ta bayansa, be juya ba har ta karaso parlorn rike da wani jug mai kyau ta ajiye a kan center table. Ido ya zuba mata yana kare mata kallo tana sanye da hijab har kasa. Bata bari sun hada ido ba ta durkusa tana gaishe shi.

“Ina kwana Ya Za..”

Ta kasa karasawa saboda kunya, Zayn ya cije lips. Muryarta yaji tana yiwa Maa magana.

“Maa an kammala kawo komai bari naje daki zan watsa ruwa.”

Cikin fara’a Maa ta ce.

“Shikenan Waheedah idan kin dawo sai kiyi breakfast din.”

Da sauri Waheedah ta wuce Zayn yana bin ta da kallo har ya dena ganinta. Kunun gyada ne Maa ta zuba masa dan tasan beci a gidansa ba, da awara wacce tayi irin ruwa-ruwan nan tasha eggs akai mata wata hadaddiyar sauce din kwai ga yankakkun veggies a kai. Ci ya farayi amman duk hankalinsa yana kan yadda zai shiga gurin matarsa, Maa ta mike da sauri tana cewa.

“Oh na manta Abiey yasani abu, kai Allah ya kyauta min yanzu abubuwa saurin mantasu nake.” Tana fada tana wucewa wajan maigidan.

Zayn ya dire cup din da sauri ya haye wajan Waheedah. Da sauri ta juya jin yadda aka rufe kofar, ganin Zayn yasa ta ware idanuwa, batayi aune ba kawai ta ganshi a gabanta, hannu yasa yaja mata hanci ganin yadda ta kame a guri guda yana cewa.

“Zuwa nai ki gaidani.”

“Gaisuwa kuma? Nafa gaida kai a parlor.” Tayi maganar tana kauda fuska.

“Wata nake so kiyi min.” Ya fada yana sake matsawa kusa da ita.

“Please Ya Zayn bana so, shin matarka ta amince da aure na da kayi?”

Zayn ya lumshe idanuwa yana tuno yadda ta kasance tsakanin shi da Ahlam. A hankali ya bude ido yana kallan Waheedah da idanunsa masu cike da zallar kaunarta. Hannu yakai zai kama nata tai saurin jan baya.

“Please Ya Zayn ka tafi wajan aikinka.”

Rintsa ido yai yana jin wani irin babu dadi a ransa, ya gyada kai ba tare da ya iya cewa komai ba ya bar mata dakin. Ko Maa be yiwa sallama ba yabar gidan, mota ya shiga tare da figarta yana mamakin lamari irin na mace.

Koda ya dawo gida ya wuce saboda yana san ya bawa Waheedah fili karyaje ya sake sanya tsanarsa a zuciyarta. Ahlam ma bata san ya shigo gidan ba saboda be nemeta ba tana cikin daki tana bacci.

Zayn kam mazewa kawai yake yi na rashin sanya Waheedah a idanunsa yanzu. Yana kwance ya tasa laptop a gaba, shi beyi aikin ba sannan ya kasa rufewa. Har akai sallar isha yana jin zuciyarsa tana tunzura shi akan zuwa gidan Maa amman yana daurewa. A ranar dai shima be samu wani bacci mai dadi ba, ya bari kawai da safe dole zaije gidan dan ba zai cuci kansa ba akan sharadin da ta bashi……

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply