Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 59


Farhatal Qalb 59
Viral

PG:59_

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA…_

____

*Cikin* matotowar rawan darin da take yi ne Gwaggo Haule ta shiga dakin ita da Umman su.

“Ah’aha… Waheedah? Meya same ki?” Gwaggo haule ta tambaye ta.

So take ta amsa. Amman bakin ta ya gaza, Sai sassarke hakoran ta ta ke yi. Sakamakon gabobin ta da suka dauki rawa baki daya.

“SubhanAllahi… Hadiza taimaka mun dan Allah.” Cewar gwaggo haule.

Gwaggo haule ta karasa kusa da Waheedah. Ta tallafota jikin ta ta rungumeta.

“Samu abu Hadiza da ruwa a rage mata dumin jikin. Za kiga panadol akan gefen tv a parlor ki dakko ..”

Umma Hadiza ta mike da sauri. Itama jikin na ta sai rawa ya ke. Kasancewar cutar da zata kwantar da Waheedah ba karama ba ce.

Ta ya zasu sanar da ita auren da ke kanta yanzu…? Umma Hadiza ta sauke zuciya kawai

Ta dakko maganin ta kai dakin da Waheedah da gwaggo su ke. Ta koma ta debo ruwa da dankwali. Gwaggo haule da kanta ta shiga tsama dankwalin cikin ruwan ta matse sai ta dora akan Waheedah. Ta shiga matsa mata jiki da haka. Har zazzabin ya dan ragu.

Sannan ta ballo mata maganin da ruwa ta bata ta sha. Ta ke bacci ya dauke Waheedah.

Ganin ta samu bacci. Hakan ya sa suka koma tsakar gidah sukayi zaman curko-curko.

Cikin haka sai ga Najan Isubu ta shiga gidan. Bayan ta kuma fannah da Basira ne kawayen Waheedah.

“Kin dawo Naja’atu?”

“Na dawo gwaggo… Ai badan mun tsaya kan Marka da saadatu ba ma da tuni mun dawo tun dazu.”

“SubhanAllahi… Fatan dai komai kalau?”

Najan Isubu ta girgiza kai kawai. Ta zauna akan wata kujerar tsugunno ta sauke zuciya.

“Waheedah bata nan ne?”

“Tana ciki. Zazzabi ta ke .Amman ta samu bacci ma yanzu ya tsurga.”

“Allah sarki Allah yabata lapia.”

“Aamin..” suka hada baki.

“Wai Najaatu wani abunne ya faru a gidan su Markan? Kinsan gaba nayo ai. Tun ranar da naje dinnan tace wallahi babu lefen da za’a karba a gidan… Yau kinga zasu kawo. Daman ranar daurin aure akace. Niyyata yau na samu Waheedah da maganar batun daurin auren nan fa ba kowa bane fyace Zayn . Da shi aka daura ”

“Wai daman Gwaggo ba ku sanar mata ba? Tabbas nasan kince mata wani yazo kan maganar aure an bashi. Amman batun wanene? Da ranar daurin auren shine ba’a sanar mata ba… To yanzu ya kuke ganin zata fuskanci lamarin? Anya bamu shiga hakkin yarinyar nan ba?”

Gwaggo haule ta sauke zuciya kawai. Ta leka ta windown dakin ta hango waheedan nata baccin ta. Ta na mai sauke numfashi ahankali.

“Babu wata tarzoma da zata taso insha Allahu a wannan aure. Yadda aka daura lapia. Ubangiji Allah yasa mutuwa ce zata raba su. Duk wata husuma da sharrace sharrace Allah ya kauda shi. Waheedah bata da matsala. Nasan ba zata taba bijirewa zabin da mukai mata ba…. Insha Allahu ”

“Insha Allahu .. Aamin ”

“Amin Gwaggo.”

“Amin…”

Dukkanin su suka shiga amsa addu’oin Gwaggo. Kafin Najan Isubu tace,

“Ni da Ramman Ukashatu da Hindu ungozoma ne muka karbi haihuwar Deluwa. Don na fito daga gida na kenan zan wuto nan din. Sai ga Ramma da sauri. Shine muka nufi can din baki daya. Allah ya temaka Deluwa ta haifo jarirai mata har biyu, To dai tunda aka shedawa Marka abunda aka samu take kumbure kumbure. Kadaran kadahan. Don na tabbata da ba biki ake ba sai ta saisaye mu da zagi da cin mutunci.”

“SubhanAllahi…. Albarkar karuwar haihuwar ce bata so ko kuwa?”

“Hmm ina kai ki Gwaggo.”

“Ina sauraron ki ”

“Yauwa…. Tayi ta cika tana batsewa. Kinsan Allah kin karbar jariran tayi. Tun dai da ta leka ta gano su da idanun ta. Kum baki gansu ba. Yadda kikasan Markan ce tayi kaki ta tofar gwaggo. Kamar su daya. Har bajajjen hancin nan na Marka da bakar fuska..”

“Wani abun Markan tayi?” Gwaggo Hadiza ta tambayi Najan Isubu.

“Wallahi bata leka dakin Deluwa ta mata barka da arziki ba. Gashi daya jaririyar kwata kwata idanuwan ta a rufe su ke bata bude ba. Numfashin ta wani iri yake fita. Dayar ma bata cika lapiya ba . Amman wallahi ko kadan Marka bata ce kanzil ba. ”

“SubhanAllahi.. wannan bakar zuciya ta Marka dai Allah ya yaye mata. Tun kuruciya har tsufa ace baka sauya halayen ka ba? To ubangiji Allah ya yaye ma ta yasa ta gane gaskya.”

“Amin. Amin Gwaggo…”

“Amin”

“Amin… ”

Suka shiga amsa addu’oin da Gwaggon ta yi. Najan Isubu ta sake karkacewa kafin ta cigaba da cewa,

“Ana cikin haka….. Sai ga shigowar Bashari da wasu abokan sa su biyu. Sallau dan gidan batayya da Harisu dan Malam me gero. Kawai kai tsaye ya dora takarda akan kafar Sa’adatu. Alokacin ta bararraje tana raba abinci. Marka ta shiga tsokanar sa tana ya tsaya su dau hotuna. Zainabu shigowar ta kenan itama gidan ta caba ado cikin wani samfacecen leshi ruwan bula. Iya ganinta sai ya sauya fuska. Ya dage kai zai fita mutane baki daya muka tsaya saroro muna bin su da kallon me ke shirin faruwa. Kai gwaggo kaji tsoron rayuwa. Wato wasu tun a gidan duniya zasu girbi mugayen nufin da suka shuka Gwaggo.”

“Ina sauraron ki Najaatu…. Zancen ki haka yake. Wasu a duniya Allah ke fara nuna ishara a kansu. Wasu kuma Allah zai musu talala komai nasu yayita tafiya dai dai. Ya yin da rayuwar su babu wani mishkila aciki. Aganin su hakan sunyi nasara basa duba da mugayen abubuwan da suke yi meyakwan su nemi gafara. To wadannan shine zakiji ana wata shari’ar sai a lahira. Suji dadi a duniya su sha wahala a lahira. Allah ya nesanta mu daga aikata mugayen alkaba’i ya kusanta mu da rahamar sa. Allahumma aamin.”

“Aamin…” Suka amsa ta baki daya.

“To na karkare miki zance dai. Takarda da Bashari ya ajiye kowa ya kasa dauka. Basira ce ta dauka ta karanto ko?”

Basira da ke gefe ta daga kai. Kafin ta ce,

“Eh… Fanna ce ta dakko akan cinyar inna Sa’adatu. Saboda Basharin yace a karanta kafin ya fita. Abunda takardar ta kunsa shine, Assalamu alaikum bayan gaisuwa da kuma fatan alkhairi ga zainabu a gaba. Ni Bashari na saki zainabu saki 3. Allah ya gyara mata halayen da zasu sauya ta ta dawo ta kwarai. Idan ta gyaru Allah ya dube ta ya bata miji nagari amin. Ina karasa karantawa inna saadatu ta yanke jiki ta fadi. Hakama zainabu data zube a kàsa tana shure shure kamar sabuwar tabi. Marka kuwa ta sankare a tsaye… Gidah dai ya hautsine… Sai awajen raude nake jin wai zainabun ashe sau 3 . Daniel likita na cire mata ciki. Wai an gaggays masa bai yadda ba. Sai da yaje aka tabbatar masa… ”

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun….. Ke duniya!!” Gwaggo haule ta fada cikin mamaki da kambama zancen da Basira ta fada

“SubhanAllahi.. SubhanAllah.” Gwaggo Hadiza ta shiga maimaitawa.

Baki daya jikin su yayi sanyi. Cikin haka sai ga shigowar su Haj Aisha abokiyar zaman Haj Hameedah mahaifiyar su Zayn.Da Haj Hameedah Bayan ta kuma su Nadra ne da wasu maza ciki harda Nassem dauke da akwatuna manya manya masu sheki. Irin customized boxes dinnan masu hashtag na #ItWasAlwaysYou:W💕

Da sauran dangin su carpets, Kayan shayi, Gishi da sugar buhu da sauran kayan masarufi ciki harda su indomie da cartons na kayan bacci. Umma Hadiza ta mike da sauri ta shige daki. Ya yinda gwaggo haule ta mayar da hijabi daman tana da alwala ta dubi gabas ta zuba sujjadar godia ga Allah. Hawayen farin ciki daya na bin daya

Najan Isubu ta tare da fara’a da wasa da dariya. Ya yin da Basira da fannah suka shimfida tabarmu baki daya suka zazzauna akai.

Daga nan aka shiga gayshe gayshen juna. Fannah da Basira sai murna suke suna bin kayan auren Waheedahn da kallo. Kaya ne wanda alkalami yayi kadan wajen zayyano tsaruwar su. Komai na kayan me tsada ne da kuma daraja.

“Kaman Hadiza na gani ta tashi ko?” Haj Hameedah ta tambaya tana dariya.

“Itace… Kunya take ji.”

“Kunya kuma? Ai an zama daya. Dabi’ar hausawa ce ai wannan na iyaye su buya ranar karbar kayan auren su. Bayan rana ce ta farin ciki .”

“Gaskiya kam.” Gwaggo haule ta amsa ta tana dariya.

Da kanta ta mike ta kirawo Umma Hadiza da ke cikin daki. Umman ta fito tana sunkuyar da kai. Ta tsugunna suka gaysa baki dayan su.

Haj Hameedah sai tsokanar ta take. Fanna da Basira suka shiga dakko kayayyakin da aka tanadar wa zuwan su Haj Hameedah. Dai dai iya karfin su. Da cartons na ruwa da lemuka.

Haj Hameedah bata ji dadin kashe kudin da Umma Hadiza tayi ba . Na yin toye toyen kaji da su meat pie. Sun karba da hannu biyu. Sannan aka fara bude akwatuna ana bin kayan da kallo

Alokacin Haj Hameedah ke tambayar ko an sanar wa Waheedah wanda aka aura mata? Su Gwaggon suka amsa mata da a’ah… Alokacin da sukayi niyyar fada kuma zazzabi yaci karfin ta don har tasha panadol ta kwanta bacci tun dazu.

Haj Hameedah da kanta ta mike ta shiga daki wajen Waheedah ta tattaba jikin ta zafin ya ragu. Don haka ta dan tashi waheedan. Dakyar ta iya gayshe ta saboda yadda kanta ke sara mata. Ta dauke MacLean da brush dinta ta nufi bandaki tayo brush. Ta gayshe da mutanen tsakar gidan tana bin su su da kayan da kallon madaukakin mamaki.

Ta koma daki ta sake gayshe da Haj Hameedah . Sannan ta zauna tana matsa yatsun hannuwan ta. Maa ta leka da kanta ta kira su Gwaggo da Umma Hadiza.

Tsakar gidah ya zama sai su Najan Isubu dake kirga kaya. Ta dora dan karamun kit din da sakar gold ke ciki dauke da zobuna da awawwaraye manya manya…

“Waheedah ya jikin naki?”

“Da sauki Maa.”

“Akwai inda ke miki ciwo?”

“Babu sai kai na kawai da ke sarawa kadan kadan..”

“Masha Allahu. Sannu kinji?”

“Yauwa.. Maa”

“Waheedah Ina son ki bamu aron hankalin ki. Ki kuma tsayar da shi waje daya. Ki kuma ajiye zantukan da zamuyi a mizanin hankali . Kinji?”

“Insha Allah Maa.”

“Ki sani har gaban abadan ba zamu miki zabi da zai cutar da ke ba. Ina nufin ba zamu zaba miki abokin zama wanda ba nagari ba ne. A har kullum adduoin akan ki basa wuce Allah ya hada ki da abokin zama na gari. Inda zaki je ki huta wani naki ya huta. Ki samu nutsuwar kwanciyar hankali. Kina fahimta?”

“Eh…”

“A baya kinsan mahaifin ki ya karbi kudin auren wanda ke neman ki amatsayin abokiyar rayuwa ta aure ko?”

“Eh….”

“Bakisan waye ba kika amince ko? Saboda biyayyar iyaye da amincewa da zabin su da yafi son rai ko?”

“Eh Maa ” Ta amsa gabanta na tsananta bugawa ..

“Tohmmm… A yau an daura aure ke da yan uwan ki ku uku idan har ban manta ba…. Ko Hadiza?”

Waheedah da sauri ta daga kai ta dubi Haj Hameedah. Tabbas tasan an karbu kudin auren ta don har ciwo tayi amman ta hakura ta amince . Ko dan farin cikin mahaifiyar ta. Amman bata taba zaton da ita aka hada aka aurar yau ba…

“Kiyi hakuri Waheedah…” Umma Hadiza ta fada kanta a gefe.

Waheedah gabanta ya sake bugawa. Ta mayar da kallon ta kan Maa data daga mata kai ta sauke itama,

“Yadda kika bi umarnin mahaifan ki. Kikayi hakuri da sa hannu biyu ki ka karbi zabin da suka yi miki. Ina fatan Allah yasa wannan shine matakin farko na shiga sabuwar rayuwar ki mai tattare da FARHATAL QALB!! (FARIN CIKIN ZUCIYA…) Daga yau kin dinga samun FARIN CIKI a ZUCIYAr ki har ya zuwa ranar da zaki koma ga mahaliccin ki Waheeda.. Allah ya saka miki da alkhairi ya hade kawunan ku. Amin”

Hawaye ne suka shiga reto a kyakkyawar fuskar Waheedah masu dumi. Hakika dukkanin wanda ke jiyo sautin kukan Waheedah dole zuciyar sa ta karaya. Da tausayi matuka ga dukkanin wanda ya samu kansa a halin da Waheedah ke ciki. Hawaye ne mai dauke da labarai masu tsuma zuciya acikin sa…

Wanda take so da kauna daban … An raba su ta hanyar auren dolen da akayi mata da wanda batasan awacce nahiyar yake ba. Ta karbi kaddarar ta da hannu dubu duk kuwa da bata da tabbacin hannun da zata faada. Ta samu FARHATAL QALB da Dawood wanda suka yiwa junan su alkawarin aure don cigaba da gina soyayyar da suka fara… Duk kuwa da bata haduwa da shi ba tun bayan bikin su Zayn amman kaunar sa tayi tasiri a zuciyar ta alokacin da suka fara magana ta WhatsApp har suka dai-daita kan su. (Gara🤣)

Ta saka kasan hijabin ta ta share hawayen da ke tsiyaya daga fuskar ta. Sai shessheka kawai da take yi.

“Kiyi hakuri Umma. Na kasa tsayar da hawayen ne” Ta fada ahankali don kada ta raunata ran mahaifiyar ta. Zatayi zaman auren ne kawai saboda farin ciki ya wanzu a zuciyar mahaifiyar ta ta dama sauran yan uwa da masoyan su

“Ki yafe ni Waheedah. Ki yafe mana baki daya kinji?” Umma Hadizan ta fada itama muryar ta a raunace.

“Ba abunda kuka mun Umma…. Allah ya yafe mana baki daya.”

“Amin Allah ya miki albarka. Allah ya saka miki da mafificin alkhairi. Allah ya shiga lamuran ki baki daya.”

“Amin Umma.”

Haj Hameedah ta janyo Waheedah jikin ta tana mai shafa bayan ta. Har cikin magudanar jininta take jin kaunar Waheedah. Can ta nisa kafin tace,

“Waheedah…”

“Naam Maa.”

“Kiyi hakuri da abunda labbana zasu furta…Don bamuyi wannan hadi dan munantawa rayuwar ki ba.”

“Tohm Umma… Au Maa ”

“Zayn shine wanda aka daura miki aure da shi yau. Kinji Waheedah..”

Ai baki daya…. Ji da ganin ta ne suka dauke na yan wasu dakikai ta zama tamkar mutum mutumi….

#DESTINED LOVE…

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

______

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply