Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 58


Farhatal Qalb 58
Viral

PG:58_

___
*Ko da* ya shiga, Ja ya yayi yai turus. Ganin parlorn a hautsine. Tamkar ba gidan da mace ke ciki ba. Bayan dazun da safe kafin fitar sa ya tarar da parlorn baki daya a gyare a kuma tsaftace. Ya yin da komai ya ke muhallin sa. Har da guzurin kamsashshen turaren wuta na kamfamin turarukan yerwa incense and more.

Robar faro ta ruwa a wulle a kasan kujerar da ta ke kwance akai. Gefen robar kuma sachets ne na biskit da ledojin chocolate na maltesers sai gwangwani na Pringles.

Tana kwance akan kujera ta mike kafafun ta a tare ta dora su a hannun kujerar. Hannuwan ta duka biyu kuma ta rike wayar ta tana dannawa.

“Assalamu alaikum wa rahamatul Allah, Wa barakatuh!” Ya daga murya wajen sa ke yin sallama a karo na uku.

Ya yin da ya jingina da jikin kofar parlorn ya zuba mata idanu. Ganin sai a sannan ta daga kai ta dube shi. Wato duk sallamar da yayi bata jiyo ba. Saboda baki daya hankalin ta da nutsuwar ta na kan wayar da take dannawa. ?

Shikenan idan har Waheedah bata gidan ba sauran mutunci da gidan yake da shi? Ba gyara babu kulawa? Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ganin ta kalle shi ta mayar da kanta kan wayar hannun ta

Bai wani damu ba. Domin ya saba da shirmammakin halayen Ahlam irin na ko in kula din da take masa. Tamkar shi din ba miji bane a gare ta.

Kai tsaye ya wuce kitchen, Ko’ina a kitchen din tatas ya ke. Komai a kintse a kuma gurbin sa.

Ya dan dudduba mazuban abinci. Babu komai na abinci. Ya juya ya hango parlor Ahlam na kwance abunta tana karkada kafafu. Wato saboda Waheedah bata nan yau ba abinci kenan?

Ya girgiza kai kawai, Ya bude freezer ya dakko wata fura daya saka jiya . Ya dauki cokali ya haura sama. Kasan zuciyar sa na masa zugi da radadin halin ko’in kula da Ahlam ke nuna ma sa.

Zama ya yi a parlorn saman. Ya bude furar da basmala ya shiga sha. Dadi sosai tayi masa. Ta kuma cika masa ciki. Yana shanyewa ya shige bandaki ya wanko bakin sa.

Ya kunna tv ya lalubo tashar labarai ta BBC yana kalla. Can ya janyo wayar sa ya shiga Whatsapp.

Da status dinta ya ci karo. Ta dora hotunan akwatunan Zainab yar uwarta da aka kawo. Da caption din ‘congratulations dear sis. Allah yasa albarka da alkhairi amin. ‘

Hoto na gaba da ta saka kuma ita da kawarta ne Basira. Dukkanin su sunyi dariya . Samun kan sa yayi da zooming din dai-dai saitin fuskar ta yana kalla.

Tun daga kan girarta cikakkiya mai dauke da gashi baki ya zuwa manyan idanun ta dake dauke da gashin ido zara zara a kanannade suna sheki. Ta saka kwalli da ya karawa idanun annuri. Har ya kan dan karamun bakinta. Da ke da labba pink. Suna sheki saboda pink lipstick din da ta sa ka.

Ya samu kansa da tsurawa hotan nata idanu tamkar yana nazarin wani abun. Can ya ajiye wayar tasa ya mike. Daki ya shiga ba jimawa ya fito ya sauka kasa bayan ya dauki wayar sa.

“Zayn….” Ahlam ta kira sunan sa. Tana zaune akan kujera. Kalba biyu ce akan ta sun mimmike.

Gata da cikar gashi amman ba kula. Ya kalleta ya kauda kansa zai fita ta sake kiran sunan sa.

“Zayn.”

“Ya akai?”

Ta turo baki gaba .

“Subscription dina ne ya kare. Na ke so kayi mun renewing ”

Girgiza kai kawai yayi. Ya kalleta sosai kafin yace da ita,

“Kin gama?”

“Me fa?”

“Maganar”

“Eh…”

“Toh.” Ficewa kawai yayi kai tsaye ba tare da ya sake ce mata komai ba.

Baba mai gadi na zaune akan kujera . Hannun sa dauke da yar rediyon sa ya saka ta a saitin kunnen sa.

Yana hango Zayn ya tashi da sauri ya shiga tura gate.

Zayn din ya nufe shi yana murmushi,

“Sannu da kokari Baba.”

“Yauwa sannun mu.”

Hannu ya saka ya zaro dubu daya ya mikawa Baba mai gadin.

“Kayi mana gafara Baba. Bamu kyauta ba. Ga wannan kaci abinci yanzu da daddare ma . Dan Allah”

“Ah kar ka damu ranka ya dade. Kudin da ka bani jiya ma har yanzu da shauran su. Na ci abinci na dadewa awajen me sayar da abincin tsallaken titi , Ga kudin ka.”

“A’a Baba. Ka bar su ka sake sayan me nauyi kaci sosai dan Allah. Ni zan fita ”

“To shikenan. Nagode Allah ya saka da alkhairi.”

“Amin Amin.”

Mota ya koma ya shiga ya tayar da ita ya fita. Kai tsaye ya wuce gidan su. Dai dai kofar gate din layin ya tsaya da motar sa. Ya janyo wayar sa ya tura wa Ahlam data ta bank.

Kafin ya karasa gidan na su. Masu gadi suka bude masa gate ya shige da motar sa.

Dakin sa ya shiga da yake na kwanan sa a da kafin yayi aure. Dan lokaci zuwa lokaci ya kan je ya buda ya shiga ya kwanta.

Domin komai na nan a mazaunin sa baa cire ba. Sannan wasu kayayyakin na sa suna nan bai dauka ba.

Kwanciya yayi akan gadon sa bayan ya karkade da addu’oi. Wayar sa dake gefen sa ce ta shiga kara. Tamkar ba zai dauka ba. Sai kuma ya daga yana kallon screen din don ganin me kiran. Abiey din su ne, Don haka da sauri ya dauka ya kara a kunnen sa.

“Wa’alaykm Salam… Barka da yammaci Abiey.. Eh, Eh… Ina daki na, Okay tohm, Gani nan ”

Mikewa yayi da sauri. Ya fita daga cikin dakin bayan ya kulle shi da mukulli.

Kai tsaye ya wuce sashen mahaifin na su. Bakin sa dauke da sallama ya shiga. Da ke transparent sliding door ce a babban parlorn. Ta nan ya hango har da mahaifiyar su aciki da kuma Ummimi.

Ya shiga parlorn bakin sa dauke da sallama. Ya tsugunna har kasa ya gayshe su cikin girmamawa.

Suka amsa fuskokin su a sa ke. Haj Hameedah sai kallon Zayn ta ke ta gefen idanu. Ya faada sosai tamkar wanda ya tashi daga ciwo.

“Ina Ahlam …? Tana gidah?”

“Eh Abiey…”

“Fatan kowa da komai lapia dai ko?”

“Alhamdulillah Abiey…..”

“To masha Allahu .”

“Zayn… Kasan akan meyasa na sa aka kirawo mun kai?”

“A’ah Ummimi ..”

“Kayi hakuri da hadin auren ka da na saka akayi da yar uwar ka Ahlam…”

“Haba Ummimi. Hakurin me kuma? Dan Allah ki dena cewa haka. ”

“Dole na fara da ba da hakuri Zayn. Domin ni ce maqasudin shigar ka wannan mawuyacin hali. Dubi yadda ka rame ka fice daga hayyacin ka. Kasancewar ka mai dimbin zurfin ciki. Baka fadin damuwar ka. sai an tasa ka agaba an maka tilas. Banyi zurfin tunanin mabambamta halayen ku ba. Na yi amfani da kasancewar ku a dangi daya. Ka gafarce ni kaji?”

Zayn yayi murmushi kawai kafin yace,

“Allah Ummimi ba komai. Kuma ba kiyi lefi ba. ”

“Ka dai yi hakuri. Ka kuma yafemun. Kaji?”

“Tohm ”

“Allah ya maka albarka ..”

“Aamin Ummimi.”

“Yauwa .. Sai batun yarinyar da kace kana so. Wacece? ”

“Wata ce..” Ya fada ahankali.

Ya daga idanu ya dora akan Maa data murtuke fuskar ta. Tana cilla masa kallon kashedin kada ka kuskura ya ambaci Waheedah.

Saukar da kansa kasa yayi sosai. Gaban sa na tsananta bugawa,

“Yar gidan wacece? A’ina take? Ina fatan kuma ta fito daga tsatso masu dattako da sanin ya kamata. Sannan mai hankali ce da wadatar zuciya… Toh Alhamdulillah. ” Ummimi ta karasa fada tana kallon farfesa Adams Nasser.

“Haka zancen ki yake Ummimi… Zayn kaaji dukkanin abubuwan da Ummimi ta fada. Ina fatan kamar yadda Ummimi ta fada yarinyar na da hankali da sanin ya kamata. Sannan wacece?”

Zayn yayi shiru. Rashin sanin abunda zai fada.

“Magana ake ma ka.”

Kansa a kasa yace,

“Wata ce…. Ummimi”

“Budurwa ce ko bazawara.? Karka ji komai dan na tambaye ka ha ka.. Dukkanin su da za’a aura ne. Sai dai bazawara ana son aji dalilin da ya fito da ita daga gidan mijin ta na baya ka gane?”

“Eh! Ummimi.”

“To masha Allahu. Waccece daga ciki?”

“Bu… Budurwa ce.”

“To masha Allahu. Allah ubangiji yasa kayi zabi na kwarai. Allah kuma yasa haka ne yafu alkhairi. Kaji ko?”

“Eh..Aamin Yaa Rabbi. ”

“To Insha Allahu. Manya zasu shiga cikin zancen. Sai dai har yanzu baka fadi yar gidan wacece ba ”

Hannuwan sa a hade yana harhade su . Rashin sanin abunda zai fada. Ganin sun zuba masa idanu suna sauraron cewar sa . Hakan ya sa shi yanke shawara kan cewar,

“Ba …. Ba mu. … Bamu gama… ”

“Baku gama dai-daita tsakanin ku ba kakeson cewa?”

Ya daga kansa alamar eh.

“To ku dai-daita din. Kada abun ya dau lokaci. Saboda manya su shiga ciki kaji ko?”

Ya gyada kansa sama. Kafin yace da su,

“Toh! Insha Allah.”

“Masha Allahu. Allah yayi muku albarka baki daya, Amin.”

“Allahumma Aamin.”

“Zaka iya tafiya… ”

Durkusawa yayi ya musu sallama. Ya fice daga sashen. Kai tsaye ya shiga motar sa ya bar gidan.

Bayan fitar Zayn ba dadewa.. Ummimi ta dubi Haj Hameedah .

“Menene Hameedah?”

“A’ina Ummimi?”

Ummimi ta danyi murmushi,

“Akwai abunda ki ke boyewa. Naga kallon da kika yi wa Zayn shi ya hanashi furta komai akan yarinyar da ya ke so. Shin akwai wata matsalar ne a tattare da yarinyar?”

Haj Hameedah ta girgiza kai. Cikin sanyin jiki ta dubi farfesa Adams da shi dinma ita yake bi da kallon karin bayani.

Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Kafin cikin sanyin murya tace,

“Gaskia akwai matsaloli Ummimi . Domin na farko ma dai yarinyar da yake ikirarin yana so zai aura. Bata masan yanayi ba. Babu wata soyayyah dake tsakanin su. Ihu yake a ….. A ..”

“Ihu a bayan hari” ummimi ta karasa mata.

“Yauwa!ihu yake a bayan hari. Ya sameni da maganar nace masa kada ya kara taso da ita. Domin abune mai wahalar yiwuwa. Bazan bari ya tauye wa yarinya hakki ba. Dubada suna kasa da mu. Tanada damar kulawa ga wanda take so. Kuma yarinyar nan a matsayin wa ta dauke shi. Auren su ba zai yiwu ba ne Ummimi. Idan aka tilasta an tauye mata hakki. Dan ba zata rasa manema da ke son auren ta ba. Wanda suke son ta take son su. Kuma Zayn yarinyar da ya ke so Ahlam ta dauke ta a matsayin yar uwa ta jini. Ta kaunace ta. Ga shi yarinyar nan awaje na akasan ta. Ummimi me kike ganin zai je ya dawo? Kowa gani zai yi ni na shirya hakan. Ni na saka ya auro ta. A dangi yawo za’ayi tayi da ni gani za’ai da hannu na aciki…. Ko da ya same ni da maganar nace masa karya so ma nema na da zancen. Ya je ya nemi wata daban ya auro. Ummimi yarinyar nan ba kowa bace. Fyace diyar Hadiza dake tayani aiyuka. Yarinyar ta dai da muka bawa Ahlam take zaune da su tana tayata aiyuka. Waheedah…. ”

Tun da ta fara magana daman Ummimi ta kawo Waheedah ce. Don haka ta sauke zuciya kawai . Farfesa Adams yace ,

“Ummimi ya kike ganin za’ai kenan? Ina tunanin kamar yadda Hameedah ta fada. Maganar nan a bar ta kawai ko? Yaje ya nemi wata daban. ”

Ummimin ta dan ni sa kafin tace,

“Idan da alkhairi acikin auren su, Allah ubangiji ya tabbatar da kasancewar hakan. Domin alkhairin Allah ake bukata a komai. Musanman lamarin daya shafi dangartakar aure. Idan ka nemi ka hana idan da rabo sai kuga wanda yayi hani ya rasa ran sa. Kuma Ahlam da ta riki rayuwar auren na su da hannu biyu ta mutunta martabar aure me daraja da dukkanin haka bata taso ba. Zasu zauna kalau. Amman tayi wasarairai. Ta saka wasa da shirme a rayuwar auren.. Yanzu gashi nan a abubuwan da suka biyo baya. Saboda haka.. Ba zamuyi kasa a gwiwa ba. Zamu cigaba da addu’oi na fatan zabin alkhairin Allah ga lamarin. Sannan zamu nemi manyan ita wannan yarinya Waheedah mu tuntube su. Idan batada wani a kàsa da take muradin aure. Za kuma tayi biyayyah ta auri Zayn duk babu matsala. Domin budurwa daman anfi kaunar a zaba mata mijin aure. Ya yin da bazawara kuma ke da ikon kawo wanda take so. Ahlam ita tayi washarere. Ita kuma wannan yarinya Waheedah ta iya yiwuwa kyawawan halayen ta da kokarin aikace aikacen da take musu ne hakan ya sa Zayn nuna kauna agare ta. Ba akan auren su farau ba ko kuwa?”

“Me fa? Ummimi ?”

“Mata dake ajiye duk wasu hakkokin auren su a gefe. Ina nufin kadan kenan daga cikin, Sakacin wasu matan akan bai wa yan aiki ragamar komai na rayuwar aurensu…. Matar gidah ta ajiye duk wasu hakkokin da ke kanta ta dorawa masu aiki ragamar komai. Su ke yiwa masu gidah komai na aikace aikacen yau da kullum. Kowacce zuciya na kaunar me kyautata mata. Don haka Zayn bai yi laifi ba don ya nuna Waheedah a matsayin wadda yake kaunar samu amatsayin matar sa. Hakan zai zamo aya ko iznah ga Ahlam da ma ire iren ta. Mu dai namu addua ce. Sannan ina son manya su shiga zancen nan. Don a san a matsayar da ake.”

“Insha Allahu…. Ummimi hakan za’ai.” Farfesa Adams ya fada. Cikin girmamawa ga mahaifiyar ta su.

“Karki ji komai Hameedah. Ki cire waswasi aran ki. Idan Allah yayi wannan aure sai anyi shi to fa babu tsimi babu dabara. Ki ma toshe kunnuwan ki da dukkanin surutan da zasu je su da wo. Idan da akwai isashshen da ya isa hanawa sai ya zo mu ga ni. Ni da kai na zan tara kowa na sanar da su yadda ake ci idan har magana ta tabbata. Kinji ko?”

“Toh. Ummimi insha Allah hakan za’ayi ”

“Yauwa! To Allah yayi muku albarka baki daya, Amin ”

“Amin Ummimi ”

“Amin.”

Daga nan suka cigaba da tattaunawa akan maganar.

Ko da Zayn ya fita. Kai tsaye ya wuce unguwar shurah ta su Waheedah. Ya samu kansa da faka mota. Ya kwantar da kan sa akan sitiyari. Ya yinda idanuwan sa ke lumshe wa su bude..

Ya samu zuciyar sa da nutsuwar kasancewar hakan. Ji yake tamkar waheedan sa na kusa da shi. Ya yi murmushi kafin ya janyo wayar sa.

Ya shiga kan contact din ta ta WhatsApp suka cigaba da hirar su amatsayin Dawood. Lokaci zuwa lokaci yakan daga idanuwan sa ya sauke akan kofar gidan su Waheedan.

Sun sha hirar su ta WhatsApp yana mai gaya mata kalaman zuciyar sa. Kafin ya kunna motar sa yabar unguwar. Ya wuce majalisar su anan sukayi sallar magriba da ishai kafin ya musu sallama ya koma gidan sa..

Bayan ya karasa kallon news ya yi alwala ya kwanta. Ba dadewa bacci ya dauke shi mai tattare da mafarkai barkatai akan Waheedahn sa.

====

A ranar da Waheedah zata koma gidan su Zayn . Mahaifiyar su Basira ta hai hu. Ta haifo ya mace.

Don haka Waheedah bata koma gidan ba. Sai ma kaya da taje ta dakko ta kara wasu kwanakin. Ran Zayn bai so hakan ba amman dai ya kyale kawai don kada ta harbo jirgin sa.

Waheedah bata koma gidan ba har sai bayan da akayi suna. Yarinya taci sunan mahaifiyar mahaifiyar su Basira (kakar ta) da za’a dinga kiran ta da suna Ilham.

__

Shirye-shiryen bikin Zainab da zahara’u aka shiga yi agidan na malam na lado.

An yanko atamfar ankon kawaye suna ta saya. Waheedah ma Umma Hadiza ta saya mata. Itama ta saya don kada ace bakin ciki suke.

A kuma satin ne Ummimi ta samu Umma Hadiza da maganar Zayn akan Waheedah. Umma Hadizan ta yaba kwarai da kyawawan halayen Zayn din. Sai dai itama tamkar yadda Haj Hameedah ta fada haka ta fada. Kan yarinyar nan Waheedah ta dauki Ahlam da Zayn a matsayin iyaye tunda sune marikan ta. Uwa uba kuma Ahlam din ta zama tamkar babbar yaya awajen ta. Tasan Waheedah ba zata amince ba. Duk kuwa da Waheedah bata da tsayayyen manemin data tsayar a wanda zata aura. Tasan ba zata amince da auren Zayn din ba.

Amman dai idan Allah yayi auren meyiwuwa ne batada ja akai. Ta kuma san manemin auren Waheedahn yanada halayen kwarai da dukkanin kowacce mace zata amince da kokon barar auren sa

Ummimi ta sake zurfafa zancen. Har ya kasance Umma Hadiza ta ce mata zata nemi yayar ta da ke amatsayin uwa agareta. Dukkanin abunda ta yanke idan yayi to sai anemi mahaifin Waheedah a tattauna da shi.

Ummimi ta roki Umma Hadiza da kada ta fadawa Waheedah Zayn ne ke neman auren ta. Ayi komai cikin sirri.

Hakan kuwa akayi . Umma Hadiza ta samu gwaggo haule da maganar. Tashin farko gwaggo haule ta nuna amincewar ta. Don gidah ne da suka san mutunci da darajar dan adam.

Ba tare da bata lokaci ba. Ba kuma da sanin Zayn ba. Su farfesa Adams suka samu mahaifin Waheedah wato malam na lado.

Ya shiga gida ya sanar da Marka. Kan wasu sunzo neman auren Waheedah. Ta amince bugun farko ba tare da bin diddigin su waye ke neman auren ba. Ita dai burinta su rabu da ‘kaya.

A kuma lokacin su Alhaji Nouh da Nouruh suka bada shawarar su bada kudin aure kawai. Nan da nan akayi komai aka gama.

Daurin auren zai kasance tare da na su Zainab da zahara’u. Daman saura yan kwanaki.

Gefe daya cikin dabara gwaggo haule ta shiga gyare Waheedah da magunguna na sanyi . Hadi da temakon kayan gyaran fata dana kariya daga sharrin sihiri da ma aljanu. Waheedan nata mamakin gyararrakin da ake sata yi. Ta kuma dau ruwan tofin da take sha a matsayin tofi na adduoin sihiri da kambun baka ..

××××

Ranar wata jumu’ah bayan anyi sallar jumu’ah an idar. Dubban mutane suka sheda daurin auren Bashari da Zainab. Sai Na’Ateeku da zahara’u. Daga karshe kuma Waheedah da angon ta Zayn Adams Nasser. Bisaga sadaki mafi daraja… Auren Waheedah ya kasance cikin sirrin da ba kowane ya sani ba. Ciki har da waheedan kan ta.

Waheedah na bandaki tayi wanka dakyar. Wani zazzafan zazzabi ne ya rufe ta. Ta haura kan katifa ta kwanta daman agidan gwaggo haule ne. Nan da nan tafara rawar sanyi. Idanuwan ta suka shiga kawo ambaliyar hawaye. Gashi yau partyn su Zainab. Bataso tayi latti. So take ta shirya ta tafi gidan su daga can zasu wuce…..

#ZAINUL-WAHEEDAH!!! A FATED LOVE💕

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply