Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 57


Farhatal Qalb 57
Viral

PG:57_

*GIDAN MALAM NALADO*

Zahara’u ce a tsakar gidan su tana wanke kanta da kumfan los. Marka na daga gefe akan yarkacacciyar kujerar ta.

Mikewa tayi daga zaunen da take. Ta shiga kai da kawowa tana daga hannuwa sama.

Zahara’u ta mike da jikakken diddigaggen gashin kanta. Daya zama kuda kuda duk ya gwaigwaye.

Ta ja dankwali ta daure kan nata tana gyara zaman zanin jikin ta.

“Ban hamsin Marka. ”

Marka ta kalleta sama da kasa ta tabe baki.

“Ke kuma me zakiyi da hamsin?”

“Zuwa zan a kitsen kai na mana. Dan Allah bani kar na tarar da layi.”

“Ah kiji ki. Ina da kudin ne? Zaki tsaya gansan gansan akai na ki ce na baki hamsin. ?”

“Na fa ga kudi a karkashin tabarmar ki.”

“Wannan yarinya bansan yadda zan da halayen ki ba. Au dan uban ki caje kike mun? Ajiya kika ban?”

Zahara’u ta ture baki gaba. Tana yatsina can ta banka kasar tabarmar ta kwashe chanjin ta zura a rigar mama.

Marka ta bude baki kafin ta yo kanta tana zuba hannuwa sama.

“Bani dan uban ki. Na ki ne? Da zaki saka hannu ki dauke mun? Ajiya kika ban?”

Suka shiga kokawa kacar kacar. Zahara’u ta fincike Marka daga jikinta tana sauke numfashi.

“Sanda ina gidan Adamushe wata rana ta laraba munzo kikace a sayo miki ruwan leda . Na ciro dari biyu ta kenan na baki da niyyar kiban chanji na. Har muka tafi baki ce mun gashi ba. Alhalin ba baki nayi ba duka. Don haka dole ne na dauki abu na. ”

Tana karasa fada ta fice waje da sauri. Ya yin da Marka ta shiga tafa hannuwan ta tana salati.

Bata rufe baki ba badamasi dan Zahara’u ya bugo yar randar ta ta fashe a kàsa.

Ya kwasa a guje ta bi bayan sa tana kururuwa

“Sai kaci malafar kan uban ka. Dan kwal uba da rafkeken kai. ” Tana tsaki tana tattare gutsattsarin fashasshiyar randar. Sai mita take tana zundumawa sunan sa ashariya

“Randar nan jaka biyu na saye ta tun duniya na kwance. Amma saboda tsabar kiriniya da rashin ji irin na ka sai da kasa kafa ka shure mun ita..” Ta ja dogon tsaki ta shuri mayafi ta fice waje.

Daga can nesa ta hango Deluwa da malam na lado suna tahowa. Ya riko mata wata leda fara ta asibitin malam aminu kano.

Turtsetsen cikin ta ya fito tamkar zai yago ya fado. Dakyar take iya tafiya saboda cikin nata yana da girma ta kuma kusa haihuwa.

Marka ta kwasa da sauri ta isa gare su tana mai dokawa Deluwa sannu.

“Allah dai ya raba ku lapia . Sannu Deluwa.”

“Amin Marka.. Sannu da kokari . Unguwa zaki je ?”

“Barka da rana Marka.”

“Yauwa mai sunan Malam. Eh Deluwa fitowa nayi ko zan ga zahara’u. Yarinyar nan ta dauka mun kudi ta tafi kitso. Shi ne zanje na rutsa ta ”

Deluwa tayi murmushi. Ta karbi ledar hannun malam na lado . Markan sai kallon gefen ido take yi wa Deluwa.

“Bari na ta fi.” Ta fada tana tafiya.

“Kai dan Allah Marka ki kyaleta.. Har nawa ne kudin?”

“Kai Deluwa. Allah karki biya mata. Rabu da ita. Ni da ita ne.”

“A’ah dai Marka dan Allah. Kawai dai ca nai ki kyaleta. Ga dan chanjin da yayi ragowa ” Ta mikawa Markan nera dari biyar.

“Ayi haka? Deluwa.”

“Dan Allah.”

Da sauri Marka ta karbi kudin ta soke a kullin zanin ta. Ta sake dashare hakora tana murmushi tamkar zata yage bakin ta.

“Ga ruwa can na doran ki. Muje na sauke. Ki samu ki gashe jikin ki . Allah ya sauke ki lapia Deluwa. Ya kawo malam tsalha ko mai sunan Malam lapiya cikin aminci. Dan ni dai ina kan gabana. Na’urar baturen karya. Wagga ciki na ki yan biyu zaki haife. Maza. Ba guda daya ba.”

Deluwa ta kakaro murmushi kawai. Kafin tace,

“Sannu da kokari Marka . Nagode da adduoin ki gare ni.”

“Ba godia tsakanin mu. Mai sunan Malam yo sauri ku karasa gidah mana.”

Malam na lado ya riko hannun Deluwa suka dauki hanyar shiga gidah. Ya yin da Marka ta lelleka bata hango zahara’u ba ta koma cikin gidah.

A yammacin ranar aka kawo kudi da kayan sa rana ta Zainab ‘ya ga malam na lado da Inna Sa’adatu. Bashari magini zata aura .

Yan ganin kaya sai zuwa suke suna yaba kaya. Akwatuna 3 da kit. Inna Sa’adatu sai yatsine ta ke tana hura hanci yar ta tayi goshi

Haka ma Marka da ke ta sakin guda tana mai kuranta kudin kayan. Kawayen ta tsofi duk sun zo ganin kaya.

“Gaskia zainabu tayi goshi. Kaya maya maya gasu nan.” Cewar lawuri kawar Marka.

“Wallahi ga bashari sharfacece dashi. Du kayan da zai saka sai ya hada da shawul kalar kayan. Zaki ga ya dora a wuyan sa🤣 Wannan yarinya zainabu na da kashin arziki. ” Indodo ta fada

Marka ta mike daga zaunen da ta ke. Ta daga hannu ta saka akan hancin ta. Ta saki katuwar gud’a tana taka rawa .

Sai da ta yi mai isar ta tukun sannan ta zauna tana mai rangada wata gudar.

“Jika ta kam tayi goshi. Tun zamanin adaman badamasi baa taba kawo kayan aure irin wannan ba na Zainab. Sai ma kunga gidan. Dakuna biyu dandatsa dandatsa ga uwar falo da dakin girki. Bandakin ta fa irin na korawa dinnan ne masan. Kur’an ga rijiya tafkekiya harda murfin ta. Ga ruwan pampo. Ai zainabu ta gama da ce ”

Inna Sa’adatu da ke gefe aka hura hanci ita ga uwar ‘ya. Can wata cikin yan ganin kayan ta ce,

“Ina Hadiza ne. Da yarinyar wajen ta?”

Marka ta ja tsaki tana yamutsa fuskar ta,

“Waya sani ne? Yarinyar dai ta kan zo nan ta kwan. Ta zama yar kwalta. Suna fakewa da boko ta ke. Can ta matse musu.”

“Na gama ta kara zama sharfaceciya ”

“Yo a banza ai. Girman shirme ba namijin aure? Gansansan da ita. Sai ma kunga yad da tayi kwailin taci uwar sabada na bilicin.”

Lawuri ta kece da dariya. Suka hada hannu da Marka. Ji ka ke raf sun tafa.

“Bangan su ba.”

“Kayya rahanatu ni kin ishe ni da maganar gayyar tsiya wallahi. Yo ta yazasu zo? Suna bakin ciki da hassada. Ile kuma wahidin din ta sani. Don an gayan ta sanda tazo nan din kwana ki ”

Matar ta jinjina kai kafin tace,

“To Allah ya kyauta .”

“Salama alaikum ” Najib yayi sallama ya shigo cikin gidan hannun sa dauke da rake yana sha

Matan wajen suka amsa. Ya hanga ya gano Marka. Daman wajen ta aka aiko sa,

“Marka ”

“Ya akai? Ba abinci. Ka shigo kana rurruntuma kai. ”

Murmushi yayi kawai kafin yace,

“Na’Ateeku ne ya ke kiran ki awaje.”

Mikewa tayi da sauri. Zanin ta saura kadan ya fadi don sauri dakyar ta gyara ta fice wajen tana dashare baki tamkar gonar auduga

“Na’Ateeku…”

Zubewa yayi a kàsa duk kuwa da shekarun sa.

“Barka da yammaci Markan mu.”

“Barkan mu dai Na’Ateeku. Iyalin kalau?”

“Alhamdulillah wallahi ” ya amsata yana sosa keya.

“Masha Allah ”

“Allah ya sanya alkhairi zainabu na zo miki.”

“Allah sarki Na’Ateeku. Godia na ke. Allah ya saka da alkhairi.”

“Amin…” Ya dan sake sosa keyar sa.

“Ina sauraron ka Na’Ateeku.”

“Marka …. Dama nace…. Zan… Zan zo da kai na. Domin zuwa da kai yafu sako. Dan ba na so abun yadauki lokaci ne.”

Marka ta sake gyara tsayuwar da tayi kafin tace,

“Eh .. Ina sauraron ka Na’Ateeku. Allah sa muji alkhairi.”

“Amin. Alkhairi ne ya kawo ni ….Magana ce akan zahara’u yar wajen ki ”

“To… Ina sauraron ka dai Na’Ateeku. ”

“Wato hakika banji dadin abunda Adamushe yayi mata ba. Ga yara ga wanda aka yaye ko?”

“Kwarai… Ai bashi da mutunci. Kakan sa ma haka ya dinga shikan matan sa. Gado ne.”

“To Allah shi kyauta …”

“Aamin Na’Ateeku.”

Ya sake sauke zuciya ya cigaba da cewa,

“Wato idan ba damuwa… Ni ina bidar auren ta. S”

Bai karasa ba Marka ta dora hannu a hanci ta saki guda

“Na’Ateeku dagaske kunnuwa na suke jiye mun?”

“Kwarai Marka … Ta kwanta mun, Ta yi mun. Don na kammala dakin da na ke ginawa acikin gidah na ma. Bani kuma da matsalar komai. Ita kawai zaa daura aure a kawo. Idan da son samu ne ma a hade da na zainabu. Ance farkon watan gobe ne ko?”

“Kai naji dadin zancen nan. Na’Ateeku da ma da tsinanniyar yarinyar nan ta ki ka har ciwon kirji nayi saboda takaici. Kai din babu macen da zata ki ka. Kuma kanta tayi wa. Yanzu bagashi ba. Ta rasa mijin auren tana yawon rariya? An gama. Zahara’u ta zama ta ka Na’Ateeku. Ba ka da shauran damuwa. Ka samu mai sunan Malam ku tsara komai.”

“Godiya na ke Marka. Allah shi saka maki da alkhairi. Kifin gwangwani, Shayi da biredi mai yanka yanka, Ga tsiren kasuwar dare ba fashi zahara’u kullum idan aka yi auren nan sai taci. Ranar tuwon laraba kuwa indomi din haladu mai shayi da lafceciyar wainar kwai da lemon kwalba zata ci babu ita babu tuwo. 😂 Ga wannan kya ci goro ba yawa.” Ya karasa fada hadi da ciro gudar dari biyar ya mika mata.

Tamkar Marka ta zuba ruwa a kàsa ta sha don farin ciki. Su kayi sallama da Na’Ateeku. Ta zura kudin ta a zani tanata murna.

Da guda ta koma cikin gidah. Ta kamfaci ruwa a cikin jarka ta zuba a kàsa. Tayi goho ta dukar da kan ta ta shiga shan ruwan kasan .

Ta dago bayan ta sha. Ta sake dora hannu a hanci ta saki guda.

“Menene Marka.?”

“Shafa mana Marka.”

Duk matan suka shiga tambayar Marka . Fuskar ta kumshe da farin ciki marar misaltuwa ta ce,

“Zahara’u ce akazo neman auren ta. Auren kuma tare akeso a daura da na zainab. ”

“Barka Marka… Barka.”
Suka shiga tayata murna.

“Wanene manemin Marka?”

“Hmm abu kamar almara. Na’Ateeku dai in karkare muku zan ce. Yace wanke zahara’u zaai kawai a mika ta. Shirgegen dakin daya gina acikin gidan sa na ta ne ya ce. Baya bukatar komai daga gare mu. Ya ce, Kifin gwangwani, Shayi da biredi mai yanka yanka, Ga tsiren kasuwar dare ba fashi zahara’u kullum idan aka yi auren nan sai taci. Ranar tuwon laraba kuwa indomi din haladu mai shayi da lafceciyar wainar kwai da lemon kwalba zata ci babu ita babu tuwo… Na san kuma taliya ma yar kakkaryawa zasu dinga ci.”

Baki daya sai gidah yahautsine da ife-ifen farin ciki. Zahara’u da ke daki sai murmushi ta ke. Idanuwan ta na hango mata kifin gwangwani da wainar kwai da tsiren da zata dinga ci.

Duuu yan wajen tsakar gidah suka shige daki don taya zahara’u murna.

Marka nata taka rawa da sakin guda . Hadi da tattaro tsinuwa da mugayen alkaba’i tana dorawa a sunan Adamushe mijin zahara’u na da .

“Mummunan banza mummunan wofi. Da hanci bajajje a saman fata. Baki uwa bayan tukunya. Yana tafe yana hankada kirji sama. Dan iska matsiyaci. To ga naateeku nan zai share mana kukan mu. Ahh shokeeei.” Ta kwarfata hannuwa kasa ta mayar sama wai ita nan rawar shoki ta ke kwasowa.

×××××

Ba wata kwalliya tayi ba. Ta zura doguwar riga baka da dankwalin ta. Wadda Haj Hameedah ta bata.

Ta shafa man lebe da farar hoda hade da dan zizara kwalli a idanun ta

Ta dauki sabon medicated glasses din ta ta saka shi a fuska.

Ta dauki yar karamar jakar data zura kayan ta ta fita daga cikin dakin da ya ke a matsayin na ta.

Tana bude kofar parlor ta hangi Ahlam malale akan kujera hannunta rike da waya tana dannawa

“Sis…”

Sai da ta fada sau biyu sannan Ahlam ta farga.

“Naam dearest one … Sai ina?”

Waheedah tayi murmushi kafin tace,

“Kinsan dama na gaya miki zanje gidah, za’a kawo kayan auren yayata. Ranar Monday insha Allah zan dawo nan din daga school. ”

“Oh haka fa. Allah sarki, Ki gayshe su please ”

“Zasu ji, In sha Allah… Sai na dawo.”

“Okay dear sis ”

Waheedah ta fita daga cikin gidan bayan ta kullo kofar.

Su kayi sallama da baba mai gadi ta futa don hawa dan adaidaita sahu da zai kai ta gidah

Tana tafe cikin nutsuwa akan hanya. Sai ga dosowar Zayn Adams. Tun daga mudubi yake hango ta.

Tana tafiya ahankali tamkar mai tausayin kasa. Ya samu kansa da kallon gefe. Yar majalisar mazan layin sun zuba mata idanu

Kishi ya taso ya harde masa a wuya. Tsayawa yayi chak da motar ta sa. Ya kira number dinta da dayan layin sa da yake a matsayin Zayn ba wanda suke chatting da sunan Dawood ba.

“Assalamu alaikum” sanyayyar muryar ta. Ta doki kofar kunnen sa.

“Wa’alaykm Salam…. Ina zakije haka?”

Dan daga kai tayi ta hango shi a mota

“Zanje gidan mu ne …”

“To karaso ..”

Karasawa tayi. Ya zuba mata idanu. Da har sai data janye idanun ta akan sa.

“Shigo na ajiye ki.”

“Ka bar shi Ya Zayn . ”

“Shigo na ce ”

Bata sake musu ba. Ta bude murfin mota ta shiga tana adduar hawa abin hawa

Ya juya ya kalli jakar da ke hannun ta . Kafin ya tambaya ta yi saurin gaya masa duba da a karkashin su ta ke,

“Zanje gidah ne sai Monday zan dawo insha Allah …”

“Meyasa?” Yayi subutar baki wajen tambayar ta.

“Zaa kawo kayan yayata ne…. ”

“Okay…. Allah ya sanya alkhairi ”

“Amin….”

Yaja motar suka dauki hanya. Na’urar sanyi nata busa su. Ya yin da wakar forever ta gyakie ke tashi ahankali.

Yana so yagaya mata sakon zuciyar sa amman zuciyar sa ta hana shi. Sai jan kasan leben sa ya ke yana taune shi.

A haka suka karasa har layin su wajen gidan su Basira.

“Ajiye ni anan ma .. Nagode.”

“Ba gidah kika ce ba?”

“Zan karba notebook dina ne awajen Basira ”

Ibrahim da ke zaune acikin yan majalisar su hangen Waheedah da yayi ya mike da sauri sai murmushi ya ke.

Zayn ya samu kan sa da sauya fuska.

“Kawai dai wajen saurayin ki kika zo.”

“Haba Allah ya kiyaye … Nagode bari na sauka. ”

Zayn yaci magani,

“Shiga ki karbo na sauke ki agidah ”

“Ai zan…”

“No buts …. Plz”

Ta shige gidan su Basira ba dadewa suka fito tare da ita. Ta tsaya suka gaysa da Ibrahim. Zayn na ta aika mata da sakon harara.

Suka shiga ya sauke su a kofar gidan su Waheedan.

“Mungode sosai…”

Har zasu shiga gidah yasamu kansa da cewa,

“Waheedah….”

Ta juya da sauri .

“Naam Ya Zayn…”

“Shikenan ma, Take care ”

Sukayi waving ta shige gidan su dasauri. Shi kuma ya ja mota ya koma gidan sa.

Ransa duk ba dadi. Ya kara tabbatarwa kansa lalle Waheedah FARIN CIKIN ZUCIYAr sa ce. Gashi daga rabuwar su. Ya samu zuciyar sa da radadin rashin ta …..

A haka ya karasa parking a harabar gidan sa ya shiga ciki bakin sa dauke da sallama….

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: *FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_

💞

_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply