Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 56


Farhatal Qalb 56
Viral

PG:56_

_____

Ahlam ta daga idanu da sauri ta dora akan Ummimi. Kafin cikin bacin rai da takaici tace,

“Bangane ba Ummimi…. Sakacin me nayi?”

“Da fari kafin ma a samo miki me tayaki aiyukan. Ba almajirai kika dauka har biyu ba yara suke gudanar da aikace aikacen gidan baki daya?”

Ba tare da ta ce komai ba. Ta zumbura baki gaba tana mai yatsina fuska. Ummimi ta sake zare mata idanu,

“Tambayar ki na ke kinyi shiru. Haka ne ko ba haka ba ne?”

“To ai aiyukan ne sunyi yawa ba zan iya ba .”

“Haba Ahlam, To menene ladan da zaki samu na rayuwar auren idan har bakya aikace aikacen gidan da mijin ki zai sanya miki albarka? Kullum kina kwance kamar ruwa lamama. Da waya a hannun ki hannu bibiyu. Tunda na ke ban taba ganin me danna waya a duniya irin ki ba Ahlam. Na hane ki tun kafin auren nan ashe baki dai na ba? Kinyi uwar watsi da zance na…. ”

“Ummimi please … Abar zancen nan.”

“Ba za’a bari ba. Ummimin kike kalla kina abar zancen nan? Wacece ke? Shashasha, sakarya. ” Cewar alhaji nouh mahaifin na Ahlam kuma da ga Ummimi.

“Yi hakuri Baba. Kiyi hakuri Ummimi.” Ahlam ta basu hakuri. Kanta a kàsa. Ya yinda kasan zuciyar ta ke mata zugi.

“A mata afuwa Ummimi…” Farfesa Adams ya fada yana murmushi

“Ai ni baki daya ba ni da tace wa… Sai fatan shiriya. Allah ya kuma ya huci zukatan dukkanin mu Amin.”

“Amin Ummimi.”

“Amin.”

“Zayn wane hukunci ka yanke akai eh.?” Alhaji Nouh mahaifin Ahlam ya tambaye shi.

Kan Zayn a kàsa cikin ladabi yace,

“Duk hukuncin da kuka zartar ya yi.”

“A’ah ai ba zamu tauye maka hakki ba son. Kuma magana ta gaskia duk wanda ya zauna ya auna rayuwar da kukayi da Ahlam zai ga kana cutuwa aciki sosai. Ba bu kuma iyayen da zasu so haka ya faru da dan su. Dan haka ni de a nawa ra’ayin. Rabuwa da Ahlam shine mafi alkhairi a tattare da kai.”

Da sauri Ahlam ta daga idanu ta sauke akan mahaifin ta jin abunda ya ke cewa. Saboda bata taba zato ko tsammanin haka daga gare shi ba.

“No kar ka ce ha ka dan uwa. Ni tunanin da na ke ma Allah yasa laifin ba daga Zayn ba ne. Saboda yanada zurfin ciki matuka.” Farfesa Adams ya fada yana kallon Zayn

Shi dai Zayn kanzil bai ce ba. Alhaji Nouh ya girgiza kai kafin cika daga yatsa ya nuna Ahlam yace,

“A’ah zancen nan fa ba sabo bane. Anyi fadan Anja kunnen yarinyar nan yafu a kirga. Ni da kai na gata ba karya nake ba wallahi sai da na kirata waya video call lokacin ina Cappadocia. Na ja kunnenta sosai tace mun ta dai na . Ashe ashe labarin kanzon kurege ne. Don haka babu ruwan Zayn wallahi. Ai dama na sha jiyota da mahaifiyar ta ga tanan tana mata fada akan yin aiki da dai na sangarci saboda aure zatayi. Amman taki yi. Ga banzan halayen data tsira na gayawa kawa komai. Da turawa bloggers neman shawara duk fadin dangin da muke da shi ba mu isheta ba mu sai iyayenta na waya. Na karanta writeups dinnan ba adadi wallahi. Ina mamaki wanda ko a mafarki ban taba zato ko tsammanin haka ba. Kuma wallahi wallahi yarinyar nan ba ta kaunar Zayn.”

Baki daya sai akayi masa caaaa jin abunda ya fada a karshe kan Ahlam din bata kaunar Zayn.

“Zancen ka na karshe da gyara ….” Ummimi ta fada tana murmushi.

Alhaji Nouh ya girgiza kansa kafin ya cigaba da cewa,

“To bata kaunar tara iyali da shi. Wai kamar Ahlam har ta san ta dinga shan contraceptive pills? Kuma guzurin su tayi ta tafi su da gidan. To Ummimi bata kaunar karuwa da shi ai bata kaunar shi wallahi. ”

“Eh to da wannan gaskia…”

“Yauwa ..Ni dai idan ana neman shawara ne.  Shawara daya zan bayar itace ta rabuwar su. A raba auren nan dubi yadda yaron nan ya zama fisabilillahi. Tamkar ba Zayn ba. Ita kuma dubi yadda take hawa kamar farashi. Idan aka bar shi ya cigaba da zama da ita tabbas an cuce shi. A cire batun zumunci a dubi hanyar gaskiya. Idan ya cigaba da zama da ita Allah karasa illata shi zata yi. Tunda dukkanin abubuwan da suke faruwa ma ba shi yake fada ba tursashi ake idan an ga damuwa a tattare da shi. Kuma ace kaman Ahlam kuna garin nan unguwa ma kusan daya amman bata san ta zo nan gidan ta gayshe da surukan ta ba? Kafin ku zama surukan natan dan uban ta ai iyayen ta ne ku. Kullum 24/7 yarinyar nan tana online tana chatting. Gaba daya rayuwar auren a wasa ta dauke ta da kuma shiririta. Saboda haka gwara a kawowa tufkar hanci. Dan Allah Ummimi.. ko kuwa Yaya?” Ya juya saitin Yayan su mahaifin su Zaid . Alhaji Nouruh.

Alhaji Nouruh ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin ya dubi Ummimi can ya ce,

“A duk sanda akayi saki al’arshin ubangiji na girgiza. Aure martaba ne raya sunnah ce ta manzo SAW. Sannan rabuwar sa kuma ba’aso idan har ba da wani kwakkwaran dalili ba. Sannan wannan aure dai na zumunci ne akayi. Ba kuma a kansu aka fara ba. Ba kuma zaa dena a kan su ba. Insha Allah, Sai dai zance na gaskiya auren Zayn da Ahlam zamantakewar su tazo da tangarda. Kamar da cutuwa acikin sa. Kada rayuka su zo suna baci gaskia. Ba fata muke ba. Kada alakar su ta janyo barakar rabuwar zumunci.” Cewar Alhaji Nouruh

“Haba haba su din banza. Mu muka haife su fa ba su suka haife mu ba dan uban su. Aure kuma ma dena zancen rabuwar sa. Haka zasuyita zama dole su hakura.” Farfesa Adams ya karasa fada cikin fushi a hasale.

Ummimi da ke gefe tana sauraron dukkanin su. Har suka karaci hayagagar su kafin tace,

“Duk naji bayanan ku….. Kusan wannan shine karo na farko da muka fara samun sabani a aurarrakin zumuncin da muke hadawa. In dai ban manta ba ko?”

“Zancen ki haka yake Ummimi.”

“Hakane Ummimi.”

“Tabbas…”

Baki daya suka shiga amsa ta. Ta gyada kai kafin ta cigaba da cewa,

“Ya ku ke ganin zamu shawo kan wannan matsalar iye?”

Alhaji Nouh ya numfasa kafin cikin matsa hannuwan sa biyu yace,

“Tunda abun ya fara zuwa da haka, Ummimi me zai hana …” Sai kuma yayi shiru bai cigaba da fada ba.

“Ina sauraron ka … Me zai hana me?”

Hannun sa ya daga tamkar zai yi nuni da wani abun sai kuma yace

“Me zai hana abar hadakar auren nan da akeyi. A dan dakata haka. Tunda ‘baraaka ta fara shigowa ciki . Ko kuwa?”

Alhaji Nouruh ya kada kai da jin abunda dan uwan na su ya fada. Kafin shima yace,

“Gaskia hakan ya kamata. A dakata din. Allah sa hakane yafu alkhairi.”

Farfesa Adams yayi shiru bai ce komai ba. Fyace muzurai da yake ta faman yi. Domin bayasan rabuwar auren nan na su Zayn.

Cikin kufulewa yace,

“Ga Jannat nan da Zaid suna zaman su cikin lumana da kaunar juna. Ku yarda wannan dinma ba lefin Ahlam ba ne. Sai dai Zayn. ”

Haj Hameedah na daga gefe ita da sauran matan. Sai dai su saurara su kuma bi su da kallo. Su kara da Amin idan hakan ta kasance.

“A’a Adams. Dan Allah ka dai na dorawa yaron nan lefi. Wallahi kaji rantsuwar musulmai? Yarinyar nan Ahlam itace me lefi. Duk duniya kaga ba wanda zai darani saninta sama da mahaifiyar ta ko? To ga mahaifiyar ta a zaune . Wallahi ko ita ta fada lefin Ahlam ne. Wannan yarinyar da kakeji da gani batada mutunci. Akazo aka hadata da yaro mara hayaniya taketa cutar sa. Zaki dai na kallo na ko sai na zo na buge kan ki anan wajen? Shashasha, sakarai da batasan me yake mata ciwo ba. ”

“Kayi hakuri … Dan Allah kayi hakuri.” Zayn ya shiga bashi hakuri .

Saboda magana yake tamkar zai tashi ya bugeta…

“Yanzu ya muke ciki ne ?” Ummimi ta sake fada .

“Duk yadda kika tsara Ummimi. ”

“Abunda kika yanke shi za’ayi.”

Ummimi ta daga idanu ta sauke akan Ahlam dake zaune a gefe. Ta sakala wayarta dan balai ta kasan kujera tana dannawa. Ya yin da shi kuma Zayn ke gefe ya rakube. Ya rame ainun tamkar majinyaci da yayi shekaru yana ciwo. Yayi bakikkirin da shi tamkar ba Zayn ba.

Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin tace,

“Dama wannan tsari na hada auren nan ni ce na kafa shi. Kuma Alhamdulillahi dukkanin aurarrakin da muka hada akayi har yau kowanne suna cikin zaman lapia da dadi babu dadi dai sun rungumi tasu kaddarar. An kuma samu zuri’ah mai tarin albarka ta hakan. Hakika baki yayi kadan wajen zayyano godia ta agare ku. Ubangiji Allah ya saka muku da alkhairin sa mafifici. Kun bani dama batare da gazawar ku ba. Dukkanin ku da yaran ku. Duk wadanda na hada aure sun karba basuyi musu ba. Alhamdulillahi wallahi ina alfahari da hakan. Ko bayan rai na na san zuriyata yan albarka ne. Nagode muku. Godia mai kima da dimbin fatan alkhairi da albarka.”

“Amin Ummimi .”

“Amin Ummimi ”

“Amin Amin”

“Allahumma Aamin.””
Dukkanin yan cikin parlorn suka hada baki wajen amsa adduoin Ummimi.

Ta kurbi ruwan da ke hannun ta. Kafin ta cigaba da cewa,

“Zayn da Ahlam suma basuyi musu ba sun bi umarnin mu. Sun amince an musu auren nan ba tare da wata husuma ta taso ba ko baraka da za’ai auren nan. Lamun lapia akayi biki aka kare. Don haka ko yanzu kasuwa ta tashi dankoli yaci riba. Alhamdulillah Allah yayi musu albarka. Wannan sabani da suke samu a tsakani. Ina fatan Allah yasa hakane yafu zaman alkhairi. Sannan kamar yadda kuka fada din. Nayi dan nazari naga hakan zai fi. Tunda yanzu komai yana tafiya ne da zamani. Kuma bazeyiwu mu dinga tauye hakkuna ba gaskia. Daga yanzu maganar auren zumunci da muke na tsakani an soke .  Tunda al’adace ba jazaman ba ne. Dukkanin wanda ke raayin karo aure daga wani dangin sai ya karo. Wanda ba suyi ba dake shirin yi kuma sunada wasu daban a waje da suke so. To suma duk mun lamunce mun amunce su auro su. Wadanda kuma suke da raayin auren na gidah sai su aura. Amman ba takura. Daga yau na cire wannan takunkumin na auren dangi. Wadanda mukayi a baya idan har an shiga hakkuna muna neman gafarar Allah ya yafe mana. Kuma kuma ku yafe mana baki daya. Allah ya karawa zumuncin mu kwari da karko. Allahumma Amin.”

“Amin …” Baki dayan su suka hada baki wajen amsa ta.

“Saboda haka zancen cigaba da zaman su tare. Gaskia babu lallai babu kuma dole. Idan dukkanin su sunyi naam da cigaba da zama to sai a sake jan kunnuwan su. Idan daya baya raayi ko kuwa dukkanin su basayi. To gaskia gwara a raba din shi zai fi zama alkhairi. Sannan Zayn bazamu tauye maka hakki ba idan kanada wadda kake so ka karo aure karkaji nauyin komai ka yi magana manya su shiga ciki kaji?”

Da sauri ya samu kansa da daga mata kai alamun eh. Kafin cikin ladabi yace,

“Eh Ummimi… Tohm, In sha Allah. ”

“Yauwa. .. To Allah ya muku albarka amin. Ka nada wadda kake so a tambayo maka aurenta ka auro ko?”

Nan ma ya daga kansa alamar eh. Ahlam dake gefe ta bude baki,

“Kishiya? Kishiya? Ummimi zaki bari ya karo aure? Yamun kishiya?”

“Ke ummimin ki ke fadaawa magana haka?” Zai tashi ya bugeta suka riko shi. Daman alhaji Nouh akwai saurun fishi da hawa doron zuciya.

Kuka ta saka. Tanayi tana bubbuga kafafu ita ga shafaffiya da mai da ba zaa karowa kishiya ba.

“Wallahi sai dai a raba auren . Ni ba zan zauna da kishiya ba. ” Kuka take sosai harda shessheka.

Ummimj ta kalleta ta tabe baki. Ta dubi Zayn kafin tace dashi,

“Wacece?”

Ya samu kansa da yin murmushi kafin yace,

“Wata ce Ummimi… Ba yar uwa ba ce.”

“Masha Allah….. Amman dai tanada hankali ai”

“Tanada hankali. Ga nutsuwa, Tanada tarbiyyah . Tanada kulawa kuma sosai. ” Yanata magana yana murmushi shi kadai. Tamkar Waheedah ce agaban sa.

Ummimi tanata nazarin sa. Ta kuma tabbatar koma wacece yarinyar gasksia Zayn yana kaunarta. Sai fatan Allah yasa aurota da zaiyi ya zama alkhairi.

Haka suka cigaba da zama anata zantawa. Daga karshe dai aka tsaya akan barin auren Zayn da Ahlam bisa rokon da farfesa yai ta yi. Amman da sharadin inde Ahlam ta sake wani lefin to auren su ya kare zaa raba igiyar auren.

An kuma lamunce Zayn ya auro koma wacece yake so. Ba shi ba har sauran yan uwa na dangi kowa zai iya auro wanda yake so daga wani tsatson.

Suka ci abinci. Aka dau hotuna na tarihi. Kafin daga bisani wadan da zasu bi jirgi a ranar su kuma gidajen su duk suka tafi. Wanda zasu kwana su tafi da safe kuma suka koma cikin gidah.

×××××××××

*Yana zaune a parlorn sama shi kadai. Domin Ahlam fushi take dashi sosai bata shiga harkar sa tun da suka baro wajen su Ummimi ta kulle kanta a daki tana kuka.

Wayar sa ya janyo. Daman jikin sa sai ingiza shi yake da yayi mata magana. Ya danna button din WhatsApp ya shiga ciki.

Yana dubawa ya ganta online. Dp (display picture) dinta kuma hotan wani namiji ne da yake da tabbacin shine ya Kamal din da ya rasu. An rubuta rest in jannatul frdws. ajikin about din ta.

Sai ya danna salam sai ya goge. Ya saka hi nan ma ya goge. Sai cije labe yake yana tunanin yadda zai mata magana.

Ya daure ya cije ya danno kan number ta ta. Ya tura mata da,

“Assalamu alaikum..”

“Wa’alaykm Salam….” Ta bashi amsa

Murmushi yayi. Ya kwantar da kansa akan kujera yana wani lumshe idanu,

“Waheedah ya gidah?”

“Lapia Lou… Da wa na ke magana?”

Shiru yay ya kasa mata reply. Yanata tunanin sunan da zai fada ba. Kawai sunan Dawud abokin sa yazo masa. Ba tare da bata lokaci ba ya tura mata da,

“Dawood ne… Kin tuna ni?”

Fuskar bude baki ta tura masa

“😱”

“Kingane ni?” Ya tura mata yana gyara zaman sa. Sai wani annashuwa yake ji.

“Abokin Ya Zayn ko?”

“Yes … Shi. Ashe kin tunani. To ya samarin ki?”

“Samari kuma? ”

“Ehmanaa. Ai nasan kina da su ko?”

“Noo. Ina dai karatu tukun.”

“Masha Allah… Allah yasa albarka ”

“Amin… Amin”

cikin kankanin lokaci, Da haka da haka dai Zayn ya samu da wayo ya cusa sakon zuciyar sa ga Waheedah amman ta sigar Dawood. Ta kuma amsa da hannu biyu. Kullum cikin chatting suke shi da da ita. Duk a zuwan Dawood ne abokin Zayn wanda suka hadu a bikin Zayn din…,

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: *FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_

💞

_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply