Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 55


Farhatal Qalb 55
Viral

PG:55_

*Tun* asubah daya tashi bai koma ba har gari yayi haske. Already yayi wanka. Mai ya shafa da dangin su turare ya taje kwantacciyar sumar kan sa.

Ya sauya kaya zuwa manya . Riga da wando na shadda. Kalar toka. Samfarin Bauchi style. Ba kadan ba kayan sun amshi zatin haibar sa.

Fita yayi daga cikin dakin. Ahlam na parlorn sama a zaune. Idanunta sun kawo ruwa sun kumbura. Da alama kuka taci ta koshi. Hakan yaso bashi dariya ya danne.

Ya zagaya ya zauna shima akan kujerar .

“Ciwon idanu kike?”

Kallo ta watsa masa. Ta mayar da idanunta gefe.

“Harara kuma….. Meya faru?”

“Au tambaya kake yi me ma ya faru? Kan babban bala’in can.”

Wayar sa ya ajiye a gefe ya koma ku sa da ita ya zauna. Hade da janyo hannuwanta cikin nasa yana matsawa. Yayin da idanun sa ya narkar da su akanta. Duk janye janyen ta sai da ta hakura ta sallama.

Rungume ta yayi a jikin sa yana shafa gadon bayan ta da hannun sa.

“Meya faru …. Uhm?” Ya rada mata acikin kofar kunnenta.

“Ni ka rabu da ni…..” Ta shiga tirjewa.

“Sssshhh… Calm down! Ahlam, Yanzu abubuwan da ke faruwa da mu. Bakya ganin maslaha shine mu zauna mu biyu mu kamo bakin zaren? Ba ruwan third party….ki ce wani abu mana… Banason wannan kawar ta ki tana shiga al’amuran mu. Kinji dear wifey.?”

“Kawata ce ta rai da rai… Wani baren na gayawa? Kai ma kasan kai ne mara gaskiya. Kana treating dina kaman wata baare. ”

“Ahlam… Meyasa ba zaki amince ke me laifi ba ce.? Okay fine! Ni na yadda nima me lefi ne. Allah ya baki hakuri. To me zai hana ke ma ki fito ki bada hakurin? Ki sauya halayen ki. Ki rungumi igiyoyin auren da ke tsakanin mu? Eh Ahlam… Why ?”

Ya ki ce jikin ta tayi daga nasa. Tana hura hanci.

“Ni babu wani laifi da na ke da shi. Kai ne me laifi. Don haka kai zaka canza. Ba ni ba. Atoh.”

“Haka kika ce?”

“Eh…”

“Okay fine…” Ya fada hade da mikewa ya koma cikin dakin sa ya janyowani dan box ya dauki abunda zai dauka ya zura a aljihu.

Har zai sauka sai kuma ya juya ya dube ta,

“Akwai wani abun da kike bukata babu? Ko na abinci haka?”

“Subscription dina na Netflix za kayi renewing. Sannan data plan dina ma has exhausted … Sai ka mun renewing. ”

Wayar sa ya duba ya yi renewing mata dukkanin abunda ta fada. Sai kuma ya zaro dubu biyu ya ajiye agaban ta.

“Gashi ko zaki bukaci wani abun daban. Na fita aiki ”

Ba godiya baare Allah ya dawo da kai gidah lapia. Ta cigaba da danna wayar hannun ta. Girgiza kai kawai ya yi. Ya karasa sauka .

Su kayi kicibus da Waheedah da ke gyara zaman sandal din kafarta zata fita

“Ina kwana…?” Ta gayshe da shi cikin zazzakar muryar ta mai dadin sauraro da dimbin ladabi.

“Alhamdulillah… Kina lapia?” Ya amsa. Ya kuma ji dadin gayshe da shi da take yi. Ya manta yaushe rabon da Ahlam ta gayshe shi tun satin biyu farko na auren su.

“Alhamdulillah…..” Ta amsa shi. Hade da bude kofar.

Ya fita. Ita ma ta fice. Cikin zuciyar ta tanata kwarara adduar Allah yasa ba zai dauke ta ba. Bata karasa adduar ba tajiyo shi yana cewa,

“Muje ko? Motar awaje nayi parking tun asubah.”

Ta kasa cewa komai. Tamkar ta fasa ihu saboda takaici. Ta daga hannu tana nuni da yatsan ta cikin gidan.

“A…an..abincin safe.” Ta samu kanta da amsa shi da haka.

“Oh abinci ko. Ko zaki mun packaging ?sai na tafi dashi office. ”

“Toh..” Ta fada, Hade da juyawa ta koma cikin gidan.

Ta harhada komai ta saka acikin kwando . Komai tsaf tsaf. Kamshi sai tashi yake yi.

Already ya fita yana jikin motar sa awajen .

“Gashi ..”

“Alright… Thank you! ”

Ya shiga motar ya tashe ta.

“Shigo mana…”

“Okay ..”

Shiga tayi . Kanta a kàsa sai murda yatsunta take. Ta rasa madafa.

Har sun hau kan titi ya juya ya kalleta. Kafin ya zaro wayar da ke aljihun gaban rigar sa.

“Rike…. Naga ba ki da waya ko?”

Ta daga kai alamun eh. Kafin ta danyi jim kuma. Can ta ce,

“A’a ka bar shi..”

Ya danyi murmushi. Kwarai matuka yana kaunar halayen Waheedah. Yarinya mai nutsuwa da cikar kamala. Ga ladabi da biyayya.

“Ni ba yayan ki ba ne?”

“Shi ne…”

“Tohm dan Yayan ki ya baki waya wani abune?”

“A’ah.”

“To saboda emergency issues haka dai bama fata. Amma ai ya kamata ace da waya a hannun ki. Ko dan saboda pdfs na books da assignment haka na school. Ko?”

“Eh…”

“Yauwa to rike.”

Karba tayi da hannu biyu. Waya ce Samsung mai kyau purple color. Daga gani kuma sabuwa ce.

“Nagode Allah ya saka da alkhairi ya kara yalwar arziki.”

“Aamin Amin. Ban kuma ce kije kina yadawa ba kan na baki waya da sauran su. Ga wani charger nan idan kin bude wajen nan zaki ganta type c ce. Akwai sabon sim aciki. Allah ya bada sa’a .”

Sai jujjuya wayar ta ke. Ba kadan ba wayar ta tafi da ita. Ga ta da kyawu kuma sam babu nauyi.

Ta janyo charger ta rike hade da wayar. Gaba daya dimbin farin ciki ya mamaye mata zuciya da duk wasu gabobi na jikin ta.

“Nagode…. Nagode Allah ya saka da alkhairi. Allah ya kara budi. Nagode ”

Yadda fuskar ta ta mamaye da farin ciki ne ya samu kansa shi ma da yin murmushin.

Har suka karasa layin su fannah sam Waheedah hankalin ta na kan wayar ta. Sai danne danne ta ke. Zayn ya yi parking a kofar gidan . Ya zuba mata idanu

“Banda dai kule kulen samari. Ki tsayda hankalin ki akan karatu kinji ko? ”

“Insha Allah…” Tana daga kai taga ai har sun karaso

“Laaa” ta fada da sauri ta fice. Ta shige gidan su Basira suka biyawa Fannah.

Waheedah ta zaro wayar tana nuna musu. Suka shiga tsalle suna masu tayata murna sosai suma.

Nan take taji kaso goma sha biyar acikin tsanar da tayi masa ya goge a zuciyar ta.

Suka shige motar ya ja su sai school of nursing.

Har kofar twin theatre da za suyi lectures din ranar ya kai su. Waheedah ta shiga rudani mai tattare da mamakin Zayn .

Ta kasa gane kan yadda yasan komai na daga harkar karatun su .

“Suna jiran ki fa…” Ya fada yana nuna mata su Basira da ke tsaye suna jiran tafuto daga mota su tafi aji.

Ta kasa ce masa komai. Ta fita daga cikin motar tana waiwayon sa. Murmushi ya sa ki kawai. Ya ja motar sa ya fita daga cikin harabar makarantar. Ya yin da su kuma suka shige ajin da zasu dauki darussan ranar.

××××

Sannu a hankali haka kwanaki ke ta tsere mana. Waheedah sunyi sabo kwarai matuka da Zayn. Ta dauke shi tamkar madadin yayanta Kamal.

A nasa bangaren kuwa dakon jidalin kaunar ta ne kullum ke dada tasiri a zuciyar sa da gangar jikin sa.

Yana kaunar Waheedah fiye da yadda alƙaluma zasu rubuta. Zuciyar sa na begen samun Waheedah a matsayin matar aure.

Gangar jikin sa na ingiza da kwadaituwar kasancewar Waheedah a tattare da shi.

Amman gaba daya ya kasa sanar mata. Ta kuma kasa gane inda ya nufa. Ta riga da ta dauke shi a matsayin dan uwan ta na jini. Tamkar babu aure a tsakanin su.

Ganin yadda kullum ya ke dada karewa a tsaitsaye. Gashi Maa ta ki zama ta fuskanci maganar. Ranar da ya sake zubewa ya nemi rokon alfarmar samun Waheedah. Ta wanke fuskar sa da gigitaccen marruka a dama da hagu na gafen fuskar sa.

Bai sake bi ta kanta ba da maganar. Kai tsaye ya samu mahaifin sa ya sanar da shi. Alokacin kuma Ummimi mahaifiyar mahaifin su ta zo .

Zayn ya kasa cigaba da boye maganar. Daman Ahlam ta karasa kai shi karshe da halayen ta. Tamkar zaman haya haka suke yi a gidan na su. Ta tattara shi ta watsar a gefe.

Hakki na rayuwar aure ma sai ya ta rokon ta zata bashi dama. Idan kuwa bataga dama ba sam bata bari ya kusance ta.

Dukkanin abubuwan da ke faruwa daman dangi sun sani. Don haka zuwan da Ummimi tayi ta kirawo dukkanin sauran yaran nata da ke kusa da matayen su. Ciki har da mahaifiyar Ahlam.

Ummimin tace gwara ayi me yiwuwa. Ta yanke ta gille. Ahlam dinma Ummimi ta sa Zayn ya kawo ta gidan na The Adams Family.

A babban parlorn gidan duk suke a zazzaune. Ahlam sai wani fiffika ta ke yi. Ummimi tayi gyaran murya ta fadi komai a takaice. Kasancewar kowa ya san masaniyar tsakanin Zayn da Ahlam .

“To ni Ummimi menene laifi na? Shi ne tun farko dama ai ba kauna ta yake ba. Bayan munyi aure halayen sa suka fito ” Ahlam ta fada tana hararar Zayn.

“To naji mu dauka ace hakanne. Ke menene yasa kike tauye masa hakkokin auren sa da ke kan ki? Eh? Tsinke wannan bakya dauke wa karya nayi?”

“A’a…”

“Toh kadan kenan daga cikin sakacin wasu matan akan bai wa yan aiki ragamar komai na rayuwar aurensu……🤸

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_

💞

_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply