Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 51


Farhatal Qalb 51
Viral

_PG:51_

___
*Tsaye* take agaban dressing mirror tana mai gyara zaman rigar jikin ta ta uniform. Ta kammala duk wasu aiyuka da suka kamata.

Ta zaro dubu daya daga cikin kudin motar da Haj Hameedah ta bata ta zura acikin aljihun gaban rigar ta.

Ta dakko hadin madarorin turaren ta data saya masu dan yawa a babbar kwalba.  (Arabian perfumed oils) ta shafe jikinta da su.

Ta bude kofar dakin ta leka zuwa parlorn kasa. Tana son tayiwa Ahlam sallama kafin ta tafi makarantar.

Ba kowa a parlorn . Hakan ya sa ta dubi agogon da ke wutsiyar hannun ta don kada ta makara.

Ta dan sake tsayuwar ta kafadar hannun ta daya dauke da jakar ratayawar ta . Dake dauke da notebook da handouts.

Shiru shiru ba motsin su . Haka ta hakura ta bude kofar gidan ta futa.

“Ina kwana Baba..?” Ta tsugunna ta gayshe da baba mai gadi.

“Lapia kalau ‘ya ta. Makaranta za ki?”

“Eh! Baba….”

“Toh Allah ya kai ki a sa’a. Allah ya buda kwakwalwa yasa albarka a abunda ake karanta.”

“Amin!! Amin… Baba. Nagode kwarai.” Ta karasa fada fuskar ta ta fad’aad’a da farin cikin adduoin da yayi mata. Ta fuce daga gidan tana sa masa albarka itama.

Da ke babu nisa da unguwar su. Nan da nan ta haye adaidaita sahu ya kai ta zuwa unguwar su. Gidan su Basira ta dauke ta su ka biyawa Fannah sannan suka nufi makarantar baki daya.

“Kawata kinga yadda ki ka sake shar da ke?” Fannah ta fada tana taba kumatun Waheedah.

“Ke de karyar ki bata sallah ….” Waheedah ta amsa ta tana dariya.

“Allah ba karya na ke ba… Ko ba haka ba Basira?”

“Zancen ki haka yake fannah… Allah gidan nan ya karbe ki Waheedateey… Inji ya Ibrahim . ”

Dan murmushi kawai Waheedah tayi. Tana mai girgiza kai kawai. Haka suka karasa makaranta suna ta wasa da dariya.

××××

Tashin sa kenan. Ya waiga ya dubi alarm da ke gefen bedside drawer. Kallon lokacin yayi yana mai ware idanun sa.

Da sauri ya mike ya gyara zaman bedsheet din da pillows. Ya karkade komai ya mayar da shi muhallin sa.

Bandaki ya faada yayo wanka ya sauya kayan sa zuwa manyan kaya. Samfarin riga da wando wagambari kalar toka.

Ya dora hula akan sa bayan ya gyara karin ta. Hancin sa ya shiga budawa sakamakon kamshin da ke dukan kofofin hancin sa.

“Ahlam….. Ahlam.. Ahlam….” Ya daga murya yanata kwarara mata kira.

Jin bata amsa ba. Ya feshe turare ajikin sa ya fice daga dakin bayan ya dau wayar sa.

Ba kowa a parlorn sama. Don haka ya bude kofar dakin Ahlam din tana kwance. Ya dauka ma bacci ta ke. Har ya juya zai rufe mata kofar. Sai kunnuwan sa suka jiyo masa karar waka ta video

Ya juya da sauri yana tunanin ko data ne a kunne tabar wayar. Ya tafi ahankali da niyyar ya dauka. Ganin ta baya ta juya masa baya ganin gaban ta.

Yana lallabawa a hankali don ya dakko wayar. Idanuwan sa suka sauka akan fuskar Ahlam. Hannu biyu da wayar a hannunta ta fito da kanta da hannuwa. Yayin da sauran jikin ke cikin bargo tana kallon wani biki a Instagram sai murmushi ta ke.

Can ta fita daga handle din ta koma hausaroom tana mai ci gaba da karanta sauran abubuwa tana tuntsirewa da dariya.

Girgiza kai kawai yayi. Ganin tsabar shagala da kallon da takeyi sam batasan shigowar sa ba . Ya fice daga dakin ya sauka kasa

Ko’ina tsaf. Kamshin turaren wuta sai tashi yake yi. Mamaki ne ya cika sa. Lalle ba su Waheedah da akayi ba karamun temako akayi musu ba.

Ko’ina kamshi ne ke tashi mai sanyi da kwantar da zuciya. Ya wuce kitchen nan dinma tas. Ta jere tukwane da sauran kayan amfani duk a muhallin su.

Kan dinning ya wuce. Abinci a jere a food flasks sai kamshi ne ke tashi. Ya bubbude doya soyayyiya an sakata acikin jarida saboda gumi acikin flask din

Sai soyayyyen dankali da kwai da plantain. Dayar food flask din kuma sauce ce ta hanta.

Da shayi a flask da yaji kayan kamshi. Bayaso yaci saboda aqidar sa ta abincin Maa din sa da yake kauna kawai.

Cikin sa ne ya shiga kara . Tabbas yunwa yake ji. Don haka yayi azamar zama akan kujera ya shiga zuzzuba komai a plate iya kacin cikin sa.

Ya yi basmala. Ya diba ya saka a bakin sa. Take idanuwan sa suka ware. Ji yayi tamkar abincin Maa… To ko itace ta bayar a ka kawo musu da sassafe?

Ya daga kai da tabbacin hakan. Ya karasa cinyewa tas. Ya shiga bandakin da ke corridor ya kuskure bakin sa da mouthwash. Ya dauki mukullin motar sa ya fice

“Ranka ya dade … Sannu da fitowa.”

“Sannunmu Baba… Barka da safiya.”

“Barkan mu dai .. An kwan kalau?”

“Lapia kalau Baba … ” Ya sosa keyar sa da kasan mukullin motar da ke hannun sa. Kafin ya sake cewa.

“Ah… Na ce ba.”

“Eh ina sauraron ka mai gidah.”

“Ahh baba nace ka dinga kira da Zayn….”

“Ai sunan na ka ne mai gidah … Na yan gayu ne ”

Zayn ya saki murmushi kawai yace

“An kawo sako daga gidan mu ne?”

“Sakon me ranka ya dade?”

“Sako haka na abinci .. kulolin abinci.”

“Yau kuma?”

“Eh….”

“Gaskia babu wanda ya zo. Ba re kawo sako. Tun wayewar gari na ke anan. Ba wanda ya shigo. Sai yarinyar nan data tafi makaranta ba jimawa .”

“Waheedah??”

“Eh ita…..”

Kasa cewa komai ya yi. Ya wuce mota kawai. Har ya shiga ya fito ya zaro kudi ya mikawa baba mai gadi.

“Godia nake … Yau ma? Allah ya amfana. Allah ya shi albarka ”

“Aamin Aamin Baba… ”
Ya koma mota ya tayar. Baban ya bude masa gate ya fita.

Kai tsaye ya wuce wajen aiki. Zuciyar sa nata tunano masa abincin da yaci. Me kama da na mahaifiyar su Haj Hameedah . Har spices din nan masu kamshi. Duk komai kaman na Maa.

Ko da ya tashi daga aiki gidah ya wuce. Ya ci saa kuwa mahaifiyar tasu na nan. Bayan sun gaysa tace da shi,

“Ya Ahlam …?”

“Tana gidah Maa.”

“Masha Allahu! Waheedah na makaranta ko?”

“Eh… Haka Me gadi yace.”

“Bangane ba… Ku din bakwa nan ne baku sani ba.?”

“Bantashi da wuri ba ne. Amma dai ko’ina naga a gyare….Maa kin aika da abinci ne?”

“Akan wane dalilin zan aika muku da abinci?” Ta tambaye shi fuskar ta dauke da mamaki ..

“No na ga ….. I mean naga..”

“Kaga me?”

“Naji abincin ne kaman na ki ..”

Murmushin fuskar ta ne ya fad’aad’a. Kafin ta ce,

“A’a ….. Waheedah ce tayi ko?”

Ya daga kai sannan yace,

“Amma ban sani ba gaskia .. ”

“Batun kasani ko baka sani ba ma bai taso ba. Itace. Ai dama ta iya girki … Sai kuma lokacin da suka samu hutu kafin ta karasa school tazo nan ta koya wasu abubuwan awaje na. Da su bangaren spices haka… Meya faru?”

Murmushi yayi tattausa. Cikin muryar ladabi yace,

“Naji kamshin komai kaman na abincin ki.. so na dauka ma an aika mana ne…. Masha Allah” Ya karasa fada fuskar Waheedah na masa gizo a idanun sa .

“A’ah…..” Kawai taceda shi. Tana duba wasu folders a laptop din da ke gaban ta.

“Allah ya kara lapiaa Maa.”

“Amin. Allah ya kara mana dika.”

“Aamin.”

Suna zaune ta re. Sai ga shigowar mahaifin su professor Adams Nasser . Da waya a kunnen sa yana amsa wa.

Zayn ya rissina yana gayshe shi. Ya daga masa hannu yana murmushi.

Haj Hameedah ta miqe ta nupi dinning area tana kara turaren wuta acikin electric burner.

“Abiey…. Barka da rana.”

“Barkan mu dai Zayn…Ya wajen su Ahlam?”

“Alhamdulillah…”

“To masha Allah…. Akwai abunda kake bukata?”

Ya girgiza kai da sauri kafin yace,

“A’a Abiey… Akwai komai. mungode Allah ya saka da alkhairi.”

“Amin Aamin Yaa rabbi… Allah ya temaka.”

“Amin Abiey..”

Haj Hameedah ta tarbe shi tanata murmushi. Suka sake gaysawa. Kafin su isa wajen dinning din ta janyo masa kujera ya zauna. Ta shiga serving dinsa. Kallon su Zayn ya shiga yi cikin so da kulawa. Bai taba jin kan iyayen na sa ba. Yana alfahari da su.

Ahlam ta fado masa arai. Sam baya gabanta. Shi baki daya ya kasa gane wane irin so take masa Anya kuwa? Sam bata kula da shi. Ita kanta bata kula da lokacin kanta .. Gaskia ba son gaskiya ba ne.

Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kawai. Ya daga kansa kan saman pop ya zurfafa duniyar tunane tunane. Har mahaifin su yakammala cin abincin ya fita ta kofar gida.

Haj Hameedah ta koma parlor kujerar da ke kallon ta Zayn. Kansa a sama bai masan ta dawo ba. Sau uku tana kiran sa baya ji.

“Zayn….” Ta fada tana mai girgiza hannun kujerar da yake kai.

Ya daga kansa da sauri ya sauke akan ta …

“Maa magana ki ke?”

“Me yake damun ka ne? Ka gayamun gaskiya har yanzu Ahlam bata canza halayen ta ba?”

“Ba komai Maa…”

“Uhm uhm… Zayn!”

“Na’am Maa…”

“Ga yamun gaskia…. ”

Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Yana mai Jan kasan leben sa . Kafin ya furzar da iskar bakin sa. Ya samu kansa da fitowa ya fadaawa mahaifiyar sa gaskia akan dukkanin abubuwan da suke faruwa acikin gidan.

Tayi mamaki kwarai matuka . Domin a nata zaton tuni Ahlam ta canza halayen ta ta rungumi auren su da hannu biyu.. Kallon sa tayi. Ya sake ramewa akan da.

“Yanzu ya kake son ayi Zayn?”

“Maa …. Ku samo mun mafita kawai. Bazan iya boye miki ba Maa. Ahlam ta samun ciwo a cikin zuciyata .. bani da wani sauran FARIN CIKIN ZUCIYAH….”

Kayi hakuri Zayn… Zamu yi magana da Abiey din ku. It shall be well insha Allah…”

Mikewa yayi bayan ya mata sallama. Ya fice daga gidan. Zuciyar sa na masa zugi da rad’ad’i…

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_

💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply