Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 50


Farhatal Qalb 50
Viral

PG:50_

___

“Waheedateey……!!!” Ibrahim ya kira sunan Waheedah , Cikin karya harshe da jan sunan ya kara masa gard’i..

Juyawa tayi don gayshe shi. Saboda baki dayan unguwar su shi kadai ne ke kiranta da Waheedateey..

“Ina kwana Ya Ibrahim…?”

Karasawa yayi ku sa da ita. Ta matsa gefe. Suna tafiya tare. Ahankali tamkar rad’a ya ce da ita,

“Alhamdulillah…. Waheedateey…. Masha Allahu!! Naji a unguwa kun samu gurbin karatun nursing ko?”

“Eh….”

“Na tayaki murna sosai wallahi…Na kuma yi farin ciki. Allah ya cika miki sauran burukan ki Waheedateey. Ya bada sa’ar karatu. Aamin.”

“Aamin Ya Ibrahim….”

Suka cigaba da tafiya cikin silar kurame da basa magana. Sanye cikin takalmi dan Madina. Ya zube hannuwan sa acikin aljihun wandon sa.

A haka suka karasa gidan na su Fanna. Wanda sunci saa . Fitowar ta kenan itama cikin uniform. Ta yi kyau kwarai matuka itama . Suka dashare wa juna baki kafin su rungume junan su cikin tsantsar so da shakuwa.

“Kawata…. Lamarin ba sauki….” Cewar fannah… Ta karasa fada tana tafawa da Waheedah…

Waheedah tayi murmushin da hakoran ta suka bayyana… Ibrahim ya dashare nasa hakoran yana kallon Waheedah cikin tsantsar so da kulawa.

“Kema tawaje na kin fito shar da ke na ke gaya miki….”

Suka sake tafawa. Sai a sannan fannah ta dubi Ibrahim da ke gefen su ya zubawa Waheedah idanu ko kyaftawa ba ya yi..

“Ina kwana Ya Ibrahim…?”

“Lapia Lau fannah .. Ina taya ku murna.. Allah yasa kun shiga a sa’a.”

“Amin Ya Ibrahim ..”

“Aamin Aamin…. Muje Allah ya sa dai Basira ta shirya ”

“Amin dai…”

Mikewa suka sake yi ba ni sa da gidan su Fannah. Suka karasa gidan na su Basira.

“Bari na kira ta..” cewar fannah….

Ta shige cikin gidan da sauri.

Ibrahim ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Guguwar so na da ‘da kada shi. Yau ga shi ga Waheedateey din sa a tsaye su kadai.

Ya lankwasar da kai. Cikin salon soyayya yace da ita.

“My life …..”

Wayaga an tsikari kakkausa. Sam bata ma san wai da ita yake ba. Sai da ya sake cewa,

“Waheedateey…. My life.”

“Ya Ibrahim ..”

“Ki tema ka ki agaza ki dena fakewa da Yayan nan…. Kinji?.”

“Uhum…”

“Haba mana…. Wai Yaya .. ki dena kallo na a matsayin Yayan ki .. Kaunar ki na ke… Kauna ta gaba da yan uwantaka.. Kauna ta soyayyah .. Kaunar aure. Ta hanyar zama daya. Kinji?”

Ta rasa abun da zata ce da shi. Tamkar ta kurma ihu haka take ji. Allah da ikon sa sai ga fitowar Fanna da Basira. Basira ma ta shirya tsaf. Uniform dinnan ya dau guga. Ko’ina tsaf tsaf.

“Shegiyar gari… Kawalliya. Umma tace tana bin ki bashin wankan yau.” Basira ta fada tana nuna Waheedah..

Hakan da Basira ta fada. Ba karamun mafaaka ya kawowa Waheedah ba. Tayi saurin shigewa cikin gidan na su Basira tana cewa,

“Tuba nake .. Kai na bisa wuya. Dole na gayshe da ummah…” Ta karasa fada hade da shigewa dakin Umman Basira tana gayshe da ita.

Sannan ta fito suka dauki hanyar makaranta. Ibrahim na biye da su yaki komawa gidah. Suka tsaya a bakin titi suna jiran dan adaidaita sahu.

“Ya Ibrahim da ka koma….”

“Haba Waheedateey… Ai ba zan iya tafiya ba na bar ki… Zuciyata ba zata samu sukuni ba.”

Fannah da Basira suka tsunkuli juna suna dariya. Waheedah kuwa ta kasa cewa komai ba. Saboda rashin abunda zata ce da shi

Sun kai mintina ashirin kafin su samu adaidaita ya tsaya.

“School of nursing…..” Suka hada baki wajen gayawa mai adaidaita sahun.

“Dari shida….” Ya basu amsa yana karo wakar Abba gidah gidah da ke tashi a gidan rediyon daya jogana.

“Haba malam….”

“Haba Yayanaa… 600 fa ka ce.”

“Kaga mai gida nawa zasu bayar?” Ibrahim da ke gefe ya tambaye shi.

“Ah aboki na. Saboda kai su bada 500. Shine gaskiya.”

“To godia muke .. ku shiga Waheedateey ..” ya karasa fada yana mai laluba aljihun wandon sa.

Ya ciro nera dari biyar data hade jikin ta ya mikawa mai adaidaitan.

“Sannu da kokari … ” Basira ta fada. Hade da shigewa ciki.

Fanna tabi bayan ta. Ta zauna a tsakiya itama. Tana wa Ibrahim din godia

Daga karshe kuma Waheedah ta shiga .

“Mungode kwarai Ya Ibrahim… Allah ya kara budi.”

“Aamin Aamin…” Ya fada yana doka murmushi. Tamkar fatar bakin sa zata yage.

Har mai adaidaitan ya ja suka tafi. Ibrahim bai dena daga hannu yana musu bye-bye ba.

Mai adaidaitan ya duba mudubin yana murmushi . Can ya karya wuya ya juya. Yana cewa da su,

“Amma fa gayen can yana kaunar ki kanwata . Allah sa dai ba wanke gara kuke masa ba. Dari biyar zuwet a marrar nan a biya maka kudi ai sai mai kaunar ka…”

Waheedah dai murmushi kawai tayi. Batace komai ba. Fanna uwar magana ta shiga labarta masa komai. Basira na tayata.

A haka suka karasa makarantar. Har kofar gate ya kai su. Suka sauka suka shiga ciki. Bin kowane lungu da sako suka shiga yi da kallo.

Sabbin dalibai irin su gasu nan birjik. Kowa cikin uniform dinsa fari. Sai daukar idanu suke yi. Lamarin sai wanda ya gani kawai.

School bulletin suka je. Suka kwafi time table. Karfe takwas da rabi suka shiga class bayan sun tambaya an nuna mu su.

Babu bata lokaci kuwa. Bayan sun kammalu a lecture hall. Malamin da zai koyar da su ya shiga. Ya gabatar da kan sa. Ya kuma raba attendance sheet kowane row. Sannan ya shiga yi musu introduction na course din da zai dauke su. Ya basu course outline. Nan ta ke ya fara lecturing din su.

Cike da kwarewa da sanin kan aikin. Turyan turyan yake yi. Daki daki da kuma tsayawa yayi bayanin inda yaga kamar ba zasu gane ba. Yanayin yadda yake koyar da su baki dayan su suna ganewa. Yanayi ana wasa da dariya. Babu bata rai na wasu malaman.

Ya kammala musu darasin ya fita. Nan take kuma wata lecturer din ta shiga. Bayan ta gaya musu sunan ta. Sai kuma ta juya allon ta rubuta sunan course din da zata musu na: Legal and ethical aspects of professional development in nursing….. Lamarin sai sam barka kawai. Domin itama suna game koyarwar ta. Ciki harda su Waheedah da ke jotting key points da take fada acikin littattafan su…

Sannu ahankali haka suka karasa duk wasu lakcoci na ranar. Sun kuma gane kowanne. Bayan an tashi suka hau dan sahu suka koma unguwar su. Kowannen su cikin zukatan su chunkushe da farin cikin kasancewara rana irin ta yau. Mai dimbin tarihin da ba zasu taba mantawa ba.

×××××××
×××××××

Fitowar sa kenan daga bandaki ya wai ga inda ya ajiye wayar hannun sa bai gani ba.

Girgiza kai kawai ya yi. Ya karasa closet dinsa ya sauya kaya. Ya feshe jikin sa da turaruka masu madaukakin kamshi .

Ya taje kwantacciyar sumar kansa da comb. Ya goga chappete na mint a leben sa.

“Ahlam…. Ahlam…. Ahlam..!!” Ya shiga kiran ta yana gyara button din jikin hannun rigar sa.

Shiru bata amsa shi ba. Ya fice daga dakin ya fara sauka kenan a bene ya jiyo muryar ta tana kuka.. Wayar da take yi kuma a speaker.

“Wallahi kinga matan da yake chats da su?…. Banda ma WhatsApp har da sauran social media apps… Baki ga mata friends din sa..”

“Kiyi hakuri Baby A .. Ai dai komai abunsa bai isa ya kara aure ba. Bakwa auren wadanda ba yan cikin dangin ku ba. Kuma dangin na ku bakwa mata biyu ballanata yace zai auri wata cousin din. Rabu da shi. Uban girman kai.”

Zayn ya ja kasan leben sa yana taune wa. Yana mamakin har kawar ta tsabar guts take kiran sa da uban girman kai? Kasa karasawa yayi. Ya jingina a bango kawai ya harde kafafu

Yana sauraron su ta kammala wayar. Still wayar tasa na hannunta tana daddannawa. Dan balai ga tissue a gefenta tana goge hawayen da ke kwarara.

Shi abun ma sai ya so ya bashi dariya. Yayi ta maza kawai ya karasa sauka kasan. Alokacin ta kifa kanta a cinyar ta tana kuka. Sanye cikin kayan bacci.

Karasawa yayi ya zauna a kujerar gefen ta bayan ya dauki wayar sa. Yayi scrolling ya na duba chats dinsu da Asiye da Hazan da Leyla yan ajin su da sukayi university tare. Wanda biyu daga ciki an kawo kudin auren su ma. Dayar kuma baa kawo ba. Amman tanada wanda ta tsayar.

Cikin kakkausar murya ya dube ta yace,

“Meyasa kike son daukar waya ta ne Ahlam? Ina tunanin wannan shine karo na 7 ina ce miki ki dena dauka mun waya kina bincike. ”

Ta dago ta gantsara masa harara kafin tace,

“Saboda bakada gaskiya shi yasa. Kana chats da yammata har wani hirar dramas kuke yi.”

“To haramun ne dan nayi chats da su? ”

“Eh tunda ba matan ka bane.”

“Ke ko…kinada issues wallahi. Yanzu ke da wani banzan halin na ke zan bari ki san inda wayata take ma? Amman har password na wayata kinsa ni. Kin uzzurawa rayuwar ki akan wasu banzayen dalilai… Dan nayi hira da su haramun ne? Ko kuwa iskanci kika ga munayi? Ahlam kin fara kai ni karshe… Bakida sirri kwata kwata. Komai kankantar zance sai kin kwasa kin gayawa kawar ki. Ga abubuwan da ya kamata ki gyara kin ki.”

“To ka aure su mana…Dama nasan ai ba kaunata kake ba..”

“Na taba daukar wayar ki na duba? Amman ke ba kida aiki se bincike binciken da ba zasu qare ki da komai ba. Kece bibiyar location dina. Ina hankalce da ke kyale ki kawai na yi. Sai bin diddigin wayata kina dubawa. Ban isa na danna waya ba sai ki fara lekowa kina ganin abunda zanyi. Wannan wacce iriyar rayuwa ce da kika dauka kika dorawa kan ki eh…? These should be the very last time Ahlam da zaki dauka wayata kina bincike….” Cikin fushi ya mike ya fuce daga gidan.

Ya yin da ita kuma ta dauki wayar ta tasake kiran aminiyar tata tana gaya mata abubuwan da ya fada.

××××

Haka zaman na su ya cigaba da kasancewa. Sam lamarin Ahlam kara bunkasa yake babu gyara aciki . Har yau bata abinci. Ragamar gyaren gidan ta bai wa almajirai. Kullum ba kyakkyawar shiga sai kayan bacci. Safe rana dare tana kan kujera ko gado a kwance. Kullum tana kan Whatsapp tana chatting da kawayen ta. Babu wani saurin hakki na miji da ke kanta da takeyi dai dai. Sam sam ba bu.

Hakan ya kasance har the Adams family sun fara lura da zamantakewar Zayn da Ahlam. Manya sun tsawatar amman lamarin yaci tura.

Zayn bai karasa hasala da lamarin Ahlam ba. Sai da idanuwan sa sukayi masa tozali da contraceptive pills (maganin hana daukar ciki) din da Ahlam ke sha. Kwali biyu ta gama da daya. Daya kuma sauran rabi ta karasa shanye kwalin duka.

Tsabar tsagwarar bacin rai har kuka Zayn yayi. Na ganin kullum ya kan hana idanun sa bacci yana rokon Allah ya basu albarkacin yara su ma. Amman Ahlam ashe munafurtar sa take tana shan maganin hana daukar ciki.

Ya dafe kansa da hannu biyu. Ya kuma kasa barwa kansa sanin hakan. Ya tunkari Maa yasanar mata. Nan ma manya suka sake shiga tsakanin su. Ahlam sai da tayi sati biyu tana gaba da Zayn .

A cikon sati na ukun ne dakyar da digon goshi malam na lado ya amince da zaman Waheedah agidan Zayn. Bisaga hukuncin duk karshen sati asabar da lahadi zataje gidah ta kwana.

Waheedah bata so hakan ba. Sam tafu kaunar gidan su duk kuwa da talakawa ne. Bata kaunar komawar ta can.

Amman tunda Umman su ta amince da hakan. Batada ja. Ta hada kayanta a babban akwatin da Haj Hameedah ta bata.

Ranar talata aka kaita gidan na su Zayn. Dan taya Ahlam kula da harkar gidah. Musanman abinci da sauran abubuwan da suka kamata. …

 

#FARHATAL QALB
#FARIN CIKIN ZUCIYA
#ZAFAFABIYAR2022

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply