Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 47


Farhatal Qalb 47
Viral

PG:47_

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA…_

___

*GIDAN MALAM NALADO*

Karar gudar shigowar mutane ce ta sa inna Sa’adatu hanzarin toshe kunnuwanta. Duk a tunanin ta amarya aka kawo a layin bayan su

Cikin bacci karar ta isheta. Ta kuma tabbatarwa kanta tabbas yar iskar rediyon Marka ce ke yi.

Don haka cikin fushi ta mike ta fita daga cikin dakin nata.

Ja tayi ta tsaya a lokacin da dandazon wasu mata suka tunkari dakinta suna sallama.

Ta bisu da idanu tana mamaki. Auren wa akeyi haka?

“Shiga da kafar dama….” Matan su kace da matar da ke lullube cikin mayafi wai ita amarya

Daurewar kai tasa inna Sa’adatu ta basu hanya suka shiga dakin nata. Suka gaysa ita dai tanata binsu da kallon mamaki

“Allah ya baku ikon zama tare da juna, Allah ya kauda fitina a tsakani…”

Cewar wata babbar mata dake tsugunen a bakin kofa.

“Eh wallahi delu batada hayaniya. Da yardar Allah zaku wanye kalau. Amatsayin ki na babba kima matar farko dan Allah kece agabanta. Ki dubi girman Allah idan tayi ba daidai ki tsawata mata…”

“Bangane ba…” Inna Sa’adatu ta tanbaye su cikin karshen gaskiyar ta.

“Wannan din abokiyar zaman ki ce.”

“Abokiyar zama….?” Ta sake maimaitawa tana tauna maganar.

“Allah de ya hade kan ku ya kauda fitinah a tsakani .”

“Ah wai wace irin magana ce wannan? Idan batan kai kukayo ku tambaya a nuna muku inda zaku je. ”

“Banan ne gidan malam na lado ba?”

“Nan ne…Ya akai?”

“To shine dai aka kawo masa amaryar sa. ”

Inna Sa’adatu ta ja tsaki ta fice daga dakin tana mai dokawa sunan Marka kira.

“Marka .. marka… Kina Ina ne wai?”

“Ga ni nan…” Marka ta amsa ta. Tana tsakiyar sauran yan kawo amaryar sunata hira.

“Bangane ba .. waye yayi aure?”

“Mai sunan malam mana..,”

“Kan babban bala’in can .. Au me?”

“Aure .”

“Aure fa kika ce? Malam dinne zai yo aure? Meya ke da shi meya tara da hat zai karo aure.?”

Marka ta ja tsaki tana girgiza kai…

“Zancen dai kenan… Yayi aure.”

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun…Muga wacce shegiyar ce .” Ta kwasa a guje tayi cikin dakin ta.

Tsakiyar mutanen taje. Ta yaye mayafin da ke jikin amaryar. Wa zata gani?

Deluwa dai wadda ta kama hayar daki. Ta Kuma ke sayarda abincin sayarwa. Wadda sukayi fada akan buta, Ta zubar mata da kwabin danwake. 🤣

‘bangane ba….,” Inna Sa’adatu ta fada. Hannunwanta biyu dafe da kirjin ta . Ranta amatikar razane. Duk ta firgice. Wannan shine babu zato ba tsammani.

“Kai ! Kai!i Kai… Wannan ba karamar kasurgumar munafuka ba ce ke…. Kinada hassada da tsantsar mugunta.. Na meye zaki auren miji? Akan wane dalilin?… Iyye? Daman can daya bakin ku daya. Da Markan da shi malam din. Wallahi ni daman na san wannan rawar takashin da Marka keyi akan ki na san da kwai wani abun a kàsa. Wohoho. To ta yanke ta gille dai. Ba dai kin shigo gidan ba? Mu zuba mu gani. Wuya tallan turmi.”

“Allah ya baki hakuri Yaya…”

“Yaya? Na hada ki da yayar na kwarfe. Kiji Wani sabon salon munafurci. Wai Yaya.? Allah ya Yayaba miki masifa da balai.”

Yan dakin suka mata caaaaa. Takaici yasa inna Sa’adatu jan hijabin ta dake jikin kofa ta fice daga gidan.

Ya yinda aka raka Deluwa dakin ta . Sannu ahankali yan uwanta da abokan arzuka suka fara watsewa . Har dai gidah yazama sai yan gidan kawai idan ka tsame inna Sa’adatu da bata nan.

Tana fita ta wuce majalisar su malam na lado. Mutane nata yi màsa Allah ya sanya alheri.

Inna Sa’adatu ta kutsa ta cikin mazan ta ta shiga ta janyo malam na lado daga cikin su . Yanata janye hannun ta dada kama masa aljihu tana jansa.

“Menene hakan wai?”

“Gaskia malam kai bakin munufiki ne.”

‘haba Sa’adatu. Wanmnan wace itiyar rayuwa ce haka. Zaki wulakanta ni acikin abokai na. Dubi yadda sukayi cirko cirko suna binmu da kallo. Suna kuma sauraron abunda muke fada.”

“Kunyar duniya kenan ma. Kafin kaje ka hadu data azabar lahira saboda baqin halin ka da muguntarka. ”

‘cikani wai menene haka wai?”

“Allah ya kwashe maka albarka malam.”

“Sa’adatu wai meye haka eh…?” Ya fada da karfi

Abokan sukayi kansu. Ta daga musu hannu tana nuna shi.

“Munafiki ne. Annamimi ne, Kuma bakin mugu..”

“Assha. Assha. Dan Allah ki dena fadar haka. ” Cewar malam Isubu mijin naja.

“Idan ba tsabagen tsagwaren rashin mutunci da tsantsar butulci ba. Me na rage shi da zeyi aure? Kuma ze karo din be fadamun ba. Ina cikin bacci ma jiyo hayaniyar yan kawo amaryar.. Wannan ya dace.?”

“Kiyi hakuri…..” Suka shiga bata baki suna bata hakuri.

Tayi kwafa kawai ta juya ta koma gidah. Tana shjga zaure ta hadu da Deluwa.

Ta gogeta zata wuce . Deluwar ta hana ta hanyar riko gyalenta.

“Cika ni….”

“Dan tsaya mana… Yayata.”

“Algunguma ..”

“Kash Ina ki tsaya kin ki. Bakyacin ribar zance….. Ina kwanaki da mukayi cacar baki da ke akan butar ki da Marka ta kawo?.”

“Matsalar ki ce ni sau ni dalla …”

“Ki saurara .. Idan baki mance ba . Kin kirani da shashasha matsoraciya.. Na ce miki ki jira ramuwa ta… Dan ramuwar gayya tafi ta gayya zafi… Wannan itace ramuwar da na ce ki tsumayi zuwan ta . Na aure miki mjii har gidah.. sirikar ki da mijin duk sun juya miki baya…. Gidah yazama namu gaba daya…. Daga haya na haye igiyar auren me gidan..🤣. Me yafi wannan ramuwar dadi? Uhm…. Yayasko… Yayata mai buta.”

Inna Sa’adatu maganganun Deluwa sun tsaya mata a rai. Sun taba mata zuciya. Sun raunata damuwarta. Hawaye ya taho ta danne hade da cijewa tace,

“Miji ne dai ko? Gaki nan ga shi… ”

“Miji, uwar miji da gidan baki daya…Ga kuma karin ki amatsayin abokiyar zama na.. Riba uku”

Inna Sa’adatu ta tattare ta fisge mayafin ta da Deluwa ta riqe tayi gaba tashige dakinta tanata mita kasan makoshi.

Baki daya tun daga ranar ta nemi farin cikin zuciyar ta ta rasa. Zuciyar ta ta rubanya da baqi mai ciwo da tsantsar na dama…

To haka rayuwar take.., sai dai fatan Allah ya yayi mana me kyau Amin…

*BAYAN SHUDEWAR WASU LOKUTA*

*Dare* ya zama safiya. Safiya ta zama rana, Ya yinda rana kan zamo yammaci. Kwanakin mu nata shudewa. Lalle Allah buwayi ne gagara misali. Kuma mai kowa da komai .

Cikin ikon sa da qudurar sa hadi da buwayar sa. Waheedah Nalado ta kammala zana jarabawar makarantar kare sakandire. Wato ssce. Wanda ake kira da senior secondary school examinations na waec da neco.

Da rarrafe yaro kan girma. To hakan yake a bangaren na waheedah. Ta zama cikakkiyar budurwa mai jini a jika. Kyawunta ya kara yalwatuwa.

Hakama cikar gashin kan ta. Hasken fatar ta. Dara daran idanun ta. Dan karamun bakin ta. Bugu da kari ta sake tsawo tubarkaAllah.

Duk wanda ya daga kai ya kalli Waheedah a karo na farko. To babu shakka sai ya sake daga idanu ya kara kallon ta a karo na biyu. Sam ba gajiyawa. Tanada shiga rai ga duk wanda ke tare da ita ko ya santa.

Mutane na yabawa da dimbin hankalin ta da nutsuwar ta da kaifin girmamawa da tarbiyyar ta. Ga fara’a da ta wuce duk inda mutum kan tsammata.

Waheedah na da ilimi na boko dana islama. Domin har sun sauke Qurani a tahfiz din su. Hakama ranar asabar da lahadi tana zuwa wata islamiyyar ta matan aure.

Ranar litinin zuwa jumu’ah tana zama da kwana ne awajen gwaggo haule. Yayin da ranakun asabar da lahadi tana kwana ne agidan su na malam na lado….

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply